TAKUN SAKA 20

Advertisement

 *_Typing📲_*

*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

Advertisements

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azbazb

_________________________

*_Chapter Twenty_*

Advertisements

………….A can wajen ɗaurin aure kuwa babu jimawa ƙanin Momy ya dawo. Ta gefen Sheikh Aliy yaɗan ranƙwafo yana magana a hankali cike da alamar ruɗani. “ALLAH ya gafarta malam akwai matsala fa. Na kira Alhaji Halilu yana faɗa min wai a jirasa kar a ɗaura yana zuwa akwai matsala”.

        Sheikh Aliy da ke saurarensa ya ɗan juyo ya dubesa cike da nazari, dan haka kawai sai yaga tamkar ba’a cikin hayyacinsa yake ba, saɓanin ɗazun da ya fita kiran Abba. Fahimtar hakan da Garba yay ne ya sashi sauri gyaɗa kansa cikin son kauda ma malam shakku. Ya sake buɗe murya da ƙyau yana satar kallon na kusa da shi daya ɗaura masa bindiga a kan gefen cikinsa ta cikin malun-malun . “Inaga fa akwai wani abune da bamu sani ba game da su yaran nan. Dan ƴar uwata ma ta kirani akan a dakata”.

        Cike da wasiwasi Sheikh Aliy yace, “To sai dai mu dakata da su na ɓangarensu ɗin, bara a ɗaura wannan. Idan ya iso kafin a kammala kaga sai muji ba’asi ko?”.

         Garba da ke ta faman sinne kai ƙasa wata irin mahaukaciyar zufa na cigaba da tsatstsafo masa ya gyaɗa kai da sauri. Gaba ɗaya jikinsa rawa yake zuciyarsa tamkar zata tsinke dan firgici. Tabbas da yasan abinda zaiyi gamo da shi kenan idan ya tashi kiran Abba da bai tashinba ya kirasa anan gaban su Sheikh Aliyn.

        Su Sheikh Aliy da basu fahimci halin da Garba ke a ciki ba babu ɓata lokaci suka fara gabatar da ɗaurin aure. An fara ɗaura na Yaya Muhammad da ɗiyar Sheikh Aliyu mai suna Maimunatu, sai Yaya Abubakar da Zahidah. Yaya Umar da tasa amaryar mai suna Farida. Sai yaya Usman da Hafsat. Yayinda Muhibbat Aliyu Hamza Gwarzo da angonta Muhammad Shuraim Aliyu suka kasance a ƙarshe.

        Kowa yasha matuƙar mamakin jin yanda al’amarin ya canja. Musamman abokan Abba da danginsu irinsu Kawu Bello. Cikin yanayin shiga ruɗani Kawu Hannafi yace, “ALLAH gafarta malam yaya akai hakan ta faru?. Abinda mukai tunani ba shine muka gani ba mu anan?”.

      Sheikh Aliy da ya dago ya dubesa cike da kamala da sanin darajar kai yace, “Eh lallai an samu tangarɗa ne a tsarin, amma tun farko a haka yake dama. Gaba ɗaya anguna za’a aura musu mataye bib-biyu ne kamar yanda na sani, idan ka cire Muhammad Shuraim mai auran Muhibbat kawai. To sai kuma na samu bayani da ga ɗan uwanku ga shinan.”

     Ya ƙare maganar da nuna musu Garba da shi kaɗai yasan a halin bala’in da yake ciki. Da ƙyar ya haɗiye bushashshen yawun da ya tokare maƙoshinsa tare da ɗan duban inda Shuraim ya ke zaune. Sai dai abinda zai baka mamaki shi Shuraim ɗin ma bashi yake kallo ba. Hankalinsa ma baki ɗaya yana kan gaisuwa da mutane. Ya ɗan muskuta da duban na kusa da shi a kaikaice kafin ya fara jawabi tamkar zai fashe da kuka a ƙasan zuciyarsa. “Eh na kira Alhaji Halilu ne saboda rashin isowarsa akan lokaci, to to shine yake min bayanin a dakata da ɗaura auren ƴaƴan wajen nasa yana zuwa akwai da… Da damuwa”.

        Damuwa?.

Suka haɗa baki kusan tare wajen tambaya. Kai kawai ya gyaɗa musu yana kai hannu ya shafe zufar da ke tsatstsafo masa a goshi.

        Tsofo mai furfura da ke amsa sunan ƙanin Hajiya mama ya mike a fusace. “Wanann ai zancen wofi ne. Anya kuwa Halilu na cikin hankalinsa. Kunga ku tashi muje gidan sai muji ba’asin wannan lalatar da ga ina ta fito haka ne?”.

        Garba ne farkon mikewa kafin kowa. Cikin rawar jiki ya shiga kutsawa tsakkiyar mutane domin samun damar gujema Idris. Shima ɗin bai bisa ba, sai wani shegen murmushin ƙeta da ya saki a kaikaice yay salute ɗin sauran ƴan uwansa da ke cikin taron a maban-banta waje.

          

      To su dai sauran mutane da basusan mike faruwa ba tuni sun mimmiƙe suna mai mikama angunan da suma suke a daskare da tunanin mike faruwa? hannu da tayasu murna. Cikin yaƙe kawai su Yaya Muhammad ke amsa musu. Dan tabbas sun shiga matsanancin ruɗani da wannan lamari. Tabbas basa tunanin Abba zai janye ɗaurin auren nan babu gaira babu dalili cikin sauƙi haka. A kuma shirin Ummi da Sheikh Aliy babu zancen ruguje auren. Dama sun shirya cewar za’a ɗaura auren, za kuma su zauna da matan bibbiyu. Da ga karshe su ginama Abba gadar zaren amfani da yaran wajen ganin dukiyarsu ta dawo hannayensu. Amma ta yaya Abba zai janye auren a wannan ƙurarren lokacin bayan sun san harda shi aka fito zuwa wajen ɗaurin auren ma.

          Duk yanda sukaso son tsayawa su gaisa da ƴan uwa da abokan arziki da suka taru dan tayasu murna hakan ya gagara. Dole suka kwashi tawagarsu suka nufi gida kamar yanda su Kawu Bellon sukayi. 

          Wani mugun murmushi Musbahu ya saki lokacin da tawagar su Kawu Bello ke rige-rigen shiga motoci domin tafiya gida. Hannu ya kai bisa kunnensa ya gyara abinda ke maƙale, kafin ya fara magana cike da girmamawa. Yanda yake magana  hankali ne yasa babu mai jinsa, sai jinjina kansa da yayi tayi da kai  dubansa ga Zaidu da ke facing nashi. Da idanu yay masa alamar ya bi bayansu. Da alama yayi hakanne bisa umarnin wanda yake wayar da shi.

       Cikin masa jinjina Zaidu ya kaɗa kai tare da saurin buɗe motar gefensa ya shige ya rufama su Yaya Muhammad da suka wuce a ƙarshe baya. 

        Shima janye jikinsa yay da ga cikin mutane yana yima sauran alama cikin inkiya. Motocin da duk sukazo a cikinsu suka shishshiga. Da sauri shima Rabi’u da ya tuƙo Musbahu da ke amsa sunan Shuraim a fuska ya buɗe masa motar da sukazo. Duk wanda ya ga a yanda suka bar massallacin zai ɗauka suma sunbi bayan su Yaya Muhammad ne. Sai dai sam ba haka bane. Dan suna hawa titi duk suka rarrabu.

       Rabi’u da ke ƙara gudun motar yace, “Musbahu kira Habib mu haɗu a roundabout”.

         Musbahu na ƙoƙarin zare malum-malum ɗin jikinsa ya amsa da faɗin, “Okay ka ƙara gudu mu samesu muma, dan Master yace karmu ɓata lokaci”. Yay maganar yana ƙoƙarin kiran Habib ɗin da ke can tare da Hibbah, wadda har zuwa yanzun a cikin sumar abinda suka shaƙa mata take.

        Musbahu ya ajiye wayar da kallon  Rabi’u ta mirror. “Insha ALLAHU zamu isa a tare dan shima yana hanya”.

       Kai Rabi’u ya jinjina masa yana cigaba da tuƙinsa. Yayinda Musbahu ya kuma shiga ƙokarin kiran waya again. Ana ɗagawa daga can ya fara magana cikin tattaro nutsuwarsa. “Master komai ya kammala gamu nan a hanya. Kamar yanda kace kuma Zaidu ya bisu can”. Ya ɗanyi shiru yana sauraren mi ake faɗi da ga can, kafin ya sake faɗin, “Okay sir” cikin girmamawa tamkar yana  gabansa.

       Yana ajiye wayar Rabi’u ya fara dariya. “Angon bogi sai ka cire facemask ɗin tunda mun baro wajen”. Dariya shima Musbahu ya sanya da kai hannu yana ƙoƙarin zame facemask ɗin. “Ai ka bari kawai ɗan uwa. A kullum al’amarin Master ƙara tsoratani yake. Shi wannan auren kuma ko miye manufarsa? Oho. Kaga dai komai ya tafi tamkar yanda ya tsara. Yarinyarnan ta saka kanta a ramin *Damisa*”.

        “Tsundum ma kuwa. Sai dai ALLAH Musbahu har cikin raina ina addu’ar ALLAH yasa mun sami aunty ke nan har abada. Tunda kaga tunda muke bai taɓa saka mace a cikin lamarinsa ba, koda tai masa laifi ne sai dai ya hukuntata ya barta a inda ya ganta. Amma wannan harda su aure”.

       “Ai ni kaina al’amarin na ɗauremin kai. Sai dai kasan shi mutum ne tamkar hawainiya, baka isa gane launin da yake sara ba. ALLAH dai ya ƙarama Master mu lafiya da nisan kwana”.

      “Amin ya Rabbi” Rabi’u ya faɗa dai-dai suna isowa roundabout. Cikin ƙanƙanin lokaci duk suka gane junansu. Gefen titi suka gangara bayan sun shanye roundabout ɗin. Su Idris da ke a sauran motocin suka firfito suka shiga inda su Musbahu suke. Yayinda Habib yake tare da Hibba shi kaɗai. Nan suka bar motocin da su Salis ɗin suke ciki da suka tafi da mota biyu kacal.

★★★★★

        A ɓangaren abokan Abba suma abin dai ya basu mamaki, dan da yawansu sun san wanann aurene na manufa mai muhimmanci ga rayuwar Abban. Musamman ma abokan shiɗancinsu su Alhaji Alu. Gashi tun kiran da Alhaji Alu ɗin yay masa bai daga ba kowama bai sake samun lambar tashi ba. Sai lamba busy ake nuna musu.

      Ran Alhaji Alu ya ɓaci matuƙa, yayinda wani gefe na zuciyarsa ke tunanin kodai ba lafiya ba?. Dan shi kam yasan Abba tamkar yunwar cikinsa. Hasalima shine wanda ya sakashi a harkar Homo tun farkon zuwansa garin. Dan haka yasan sirrinkan abubuwa masu yawan gaske na Abban.

       “Yauwa ga ɗayan layinsa ya shiga”.

     Cewar Alhaji Balele abokin shaidancin su Abban shima.

       Gaba ɗaya su Alhaji Alu suka zuba masa ido dai-dai shi kuma yana saka wayar a kunne kasancewar an ɗaga. Cikin nishin sheɗancin da Abba suke tsaka da aikatawa shi da A.G ya ɗaga wayar da ƙyar yana kaiwa kunnensa. 

       Cikin suɓutar baki da takaicin kishi Alhaji Balele ya ce, “Iyee. Wato kai kana can akan wani ana nan ana dama fura akanka. Halan daɗin abinda kakeyi ne ya sakaka janye ɗaurin auren ƴaƴanka bayan ka taramu anan tamkar wasu marasa aikinyi Alhaji Halilu!!”.

       A wani irin firgici da dukan zuciyar Abba da maganar Alhaji Balele tayi ya sakashi hankaɗa A.G gaba yana janye jikinsa a nashi da faɗin, “What?!, Alhaji Balele mi kake faɗa haka ne?”.

      Tsaki Alhaji Balele yaja tare da yanke wayar. Hakan ya saka Abba sake rikicewa ya ingije A.G da ke ƙoƙarin sake ruƙosa. Wandonsa ya fisga a firgice yana ƙoƙarin sakawa. 

       “Alhaji Halilu wai miye haka?”.

       “Bazaka gane ba A.G.”

Abba ya faɗa yana fincikar tissue ya goge jikinsa tare da ƙarasa saka wandonsa. Sandunan da ke taimaka masa a tafiya ya ɗauka cikin rawar jiki da tsallen da zuciyarsa keyi a ƙirji ya fice.

      Wani irin wawan tsaki A.G ya ja cike da tsantsar takaici yana raka bayan Abba da ke tafiya da ɗangyashi da harara. Ina Abba baima san yanai ba. Dan gaba ɗaya a birkice yake da jin bayanan Alhaji Alu. babu wanda yake zuwa masa cikin ido sai Hibbah da labarin da A.G ya basa akan Hibbah dama tayi agreement da su akan su kamashi da duk mai hannu a ɗaurin auren. Inhar abinda yaji da ga bakin Alhaji Balele gaskiyane kenan matsiyaciyar yarinyarnan bada Jami’an tsaro kawai ta shirya hakanba? Ko kuwa ta fahimci A.G wasa zaiyi da hankalinta shiyyasa ta canja salo. Su suna mata kallon ƙaramar yarinya shakatafi ashe ba haka bane sam, sune takema kallon shakatafin.

         Tun fitowar Abban maigadi ya fahimci babu lafiya, musamman da ba jimawa yay da gama reren gudun bin matar ɗazun ba. ya mike zaram tare da nufar gate danya buɗe ganin mota ya nufa shima. A wani irin mahaukacin gudu Abba ya fice a gidan…………..✍

      

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

Leave your vote

-2 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like