TAKUN SAKA 23

Advertisement

 

*_Typing📲_*

*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

Advertisements

______________________

*_Chapter Twenty Three_*

………….“Kaga wani salo kamar a film”.

Ammar ya faɗa dariya na kufce masa a bazata. Dan haka kawai wasan yay matuƙar birgesa da ƙayatar da shi.

        Su yaya Abubakar kam da gaba ɗaya mamaki da al’ajab ɗin Isma’il ɗin ya daskarar da su a tsaye da ƙyar suka iya fisgo numfarfashinsu sukai azamar zuwa suka sha gabansa ganin Abba ya ke nufa gadan-gadan. Dan su gaba ɗaya abinda zukatansu ke basu lallai Isma’il yana tare da wani bahagon aljani ne ƙila. 

      Idanunsa ya rumtse da ƙarfi ganin sun tare sa. Cikin wata irin murya mai ƙaraji da saka firgici ga ma’abocin saurare yace, “Minti uku na baku a fitar min da wanann sauran gawar anan. Kar kuma na sake ganin ƙafar waninku anan. Inba hakaba…. Ya ƙyalƙyale da dariyar da ta saka su Yaya Abubakar sake zama turus a gabansa.

       Jiki na rawa Momy ta kama ƙafafun Junaid ta fara ja tana kuka. Yayinda tuni Hajiya mama ta fece da gudu har tana cin tuntuɓe zata faɗi. Su kawu Garba da ke gefe a maƙure suma ne sukai karfin halin matsowa suka taya Momy ɗaukar Junaid da zuwa yanzu ya sume sabida azabar murzar da wuyansa yasha da haƙarƙarinsa.

        Da gudu Ammar ya taho ya rungume Isma’il ta baya yana dariya da hawaye a lokaci ɗaya. Hakan yasa Ummi ma da tai mutuwar zaune tana kallon Isma’il ɗin ta miƙe zuwa garesu. Hannun Isma’il ta riƙo cikin nata hawaye na sakko mata saman kumatu. Jawo hannun nasa tai ta zaunar da shi akan kujera tare da ɗaukar goran ruwa da ke a saman centre table da aka ajiyema baƙi ta ɓalle murfin ta ɗora masa a baki tana shafa kansa.

      Babu musu ya hau sha yana jan ajiyar zuciya. Sai da ya shanye shi tas ta janye goran tana cigaba da shafa kan nasa.

Advertisements

     A hankali ya lumshe idanunsa da komawa baya ya jingina jikinsa da kujerar, numfashinsa tun yana sauka da zafi-zafi har ya koma sauka a hankali alamar zuciyarsa nayin sanyi.

     Ummi ta share hawayen fuskarta tanayin murmushi da duban su Yaya Usman da har yanzu ruɗani da al’ajabin mamakin Isma’il ɗin ya gaza barinsu. Matsowa sukai gareta. Yaya Umar da yaya Usman suka rungume Isma’il ɗin. Yayinda Ammar yazo ya zauna gabansa ya ɗaura kansa a saman cinyarsa fuskarsa washe da dariya tamkar gonar audiga.

    Hannu ya kai a hankali bisa kan Ammar yana shafawa. A karon farko ya saki murmushi da ɗago kansa ya na kallon Ummi da su Yaya Muhammad.

       “Kiyu haƙuri Ummi, lamarin mutanen nan sai da over acting. Na fahimci wannan ce kawai mafita a garemu. Inba haka ba sai wata fitinar ta kaure har akai ga jima wani ciwo”.

     Yanda yay maganar cikin sanyin murya tamkar yanda suka sanshi ne ya saka su Yaya Usman sakin ajiyar zuciyoyi. 

        “Amma Isma’il ka bani tsoro matuƙa wlhy, har mun fara tunanin ko baka da lafiya ne”. Cewar Yaya Muhammad yana murmushi. 

     Ɗagowa Isma’il yayi zaune sosai yana saki ƴar dariya. “Yayanmu lamarin tsohuwar nan ne sai da haka. Sai dai fa nasan wlhy ba haƙura sukai ba, dan da alama na jima wancan wawan yaron Junaid ciwo a haƙarƙari. Ummi inhar shirinku na barin gidan nan na nan to lallai dole ne ki tafi kema a yau ɗin nan. Kamata yay ma ace yanzu kawai. Kinga sai ki tarbi amare da kanki”.

       Yaya Abubakar da har yanzu shi dai yake kallon Isma’il ɗin cike da nazari da wasiwasi ya gyaɗa kansa cikin gamsuwa. “Wannan mafita ce mai ƙyau. Dan Abba kam ba kanwar da za’a lasa bace aji kaifi kawai. Ummi kamar yanda Isma’il ɗin ya faɗa barin gidan nan yanzu shine mafita kawai”.

       Sosai itama Ummi ta gamsu da zancen. Dan duk abinda zai ɓata mata taron auren yaranta bata fatansa. Sarai kuma ta fahimci abinda su Hajiya mama ke burin yi kenan. Sai dai kuma cikin damuwa da rauni ta ce, “Tanee ɗin fa an ganta?”.

         Da sauri Yaya Umar ya gyaɗa mata kai. “Eh karki damu tana tare da ƙawayenta ashe. Zuwa anjima nasan zatabi masu kai su can kawai”.

        Duk da zuciyarta a raunane take hakan bai hanata gamsuwa ba. Ta mike tana warware mayafinta da dama tana tare da shi tun ɗazun ta sake yafawa. Dama ba wani muaten bane sosai a sashen. Makwafta da suka shishshigo sukai mata ALLAH sanya alkairi duk sun fita saboda yamma tayi sosai. Sai ƙawayenta na kusa sosai irinsu Hajiya Mardiyya. Suko sunsan da shirin barin gidan. Dan dama sune zasuje amsar amare acan. Jin hukuncin da su Yaya Muhammad ɗin suka yanke ne ya sakasu mimmiƙewa suma suka hau kimtsawa. 

     Su Ummi basu da matsala da komai na sashen dan sun tsince masu muhimmancin sun killace sauran. Su hajiya mama nacan akan Junaid cike da ruɗani suka samu suka fice dan dama gari ya fara duhun magrib da ake ta faman kira a masallatan anguwar. Mutanen da ke a tsakar gida kuwa gulma da tsugudidin da suka haɗa kai sunayi group-group yasa basu hankaltu da su Ummin ba. A tunaninsu kawai ƴan biki ne zasu wuce gida.

          

★★★★★

         

           A can L.E street kuwa cike da farin ciki da ƙaunar yaran har cikin rai baba Saude ta mike domin gabatar da sallar la’asar ɗin itama. Tana idarwa ta fito ta hau shirya musu abincinsu na rana da basu ci ba. 

           Kasancewar yunwar kuwa na ƙwaƙular cikinsu ana idar da sallar la’asar ɗin suka dawo gidan. Sai dai su kaɗai suka shigo falon banda Master da yay zamansa a ƴar runfar bunun da ke a gefen swimming pool ɗin gidan. Dan yasan tunda suka dawo gidan shegen surutinsu ba zai barshi ya huta yanda yake bukata ba.

        Suko da ga can cikin zalamar kayan daɗin da baba Sauden ta baje musu a babban dining ɗin suka baje da fara ɗurama cikinsu. Yayinda kowa ya fara kai lauma sai sabon surutu ya ɓalle, baba Saude na gefe na musu dariya kamar yanda ta saba har suka kammala. Sune suka zaɓar mata ɗakin da zata zauna anan downstairs ɗin. Hundred percent kuwa ta gamsu da ɗakin, dan yana ɗan nesa da ɗakunansu ga shi kuma gab da kitchen. 

      Sune suka shiga gyara mata komai duk da bama wani datti bane da ɗakin. Bayan sun kammala Salis yay list ɗin abubuwan da yasan Baba Sauden zata buƙata na amfani musamman a toilet. Da ga haka suka dawo falo kowa ya kama hidimar gabansa. Lokaci-lokaci suka sakko zancen Zaidu da ke can gidan su Hibbah yana gano duk cakwakiyar da ke faruwa batare da kowa ya fahimci shi ɗin wanene ba.

*_8:16pm_* ya shigo gidan. Lokacin su Idris da dawowarsu da ga sallar isha’i babu jimawa na baje a falo suna kallon ƙwallo. Duk sun cika falon da hayaniyar gaddamarsu. 

      Khalid da ya fito da ga kitchen riƙe da drik ne ya fara farga da Master da ko sallamarsa basu ji ba. Cikin ɗan daga murya yanda zasu fahimta ya ce, “Barka da dawowa Master”.

      A take falon kuwa yay tsit duk suka juyo ga ƙofa. Cikin ɗan hararsu ya ajiye ledojin da ya shigo musu da shi ya haura sama da ɗaya batare da ya amsa sannu da zuwan da suka haɗa baki wajen masa ba. Suna ganin ya gama hayewa har rige-rige tasowa Zaidu da bai jima da dawowa gidan ba suke shi da Salis wajen zuwa su ɗauka ledojin da ya jiye. Suma sauran tasowa sukai akan ledojin cike da farin ciki da ƙaunar Mastern nasu.

       “Dalla malamai karkuyi mana hayaniya anan kuja a samu barcin dole”. Cewar Adam yana harar su Zaidu da suka ƙanƙame ledojin. 

      Cikin ƴar dariyar shaƙiyanci Musbahu yace, “Wanann kaɗan da ga aikin Master. Balle fa yau ango yake a gidan nan kuna ganin harda kazar tarbar amarya”.

        A tare suka wage bakuna zasu ƙyalƙyale da dariya Idris yay musu nuni da sama. Saurin saka hannayensu sukai suka dafe bakunan kowa na ƙoƙarin danne ta shi. Da ga haka suka koma tsakkiyar falon zaune  Salis na ƙoƙarin buɗe ledojin dake ɗauke da kwalayen pizza da shawarma.

       Sosai suka shiga farin ciki kowa yaja shawarma ɗaya dan dama a lissafe suke. Pizza kuwa kwali huɗu ce itama.

       Da ga ɓangaren oga Master kuwa koda ya haura sama a falo ya ajiye ledar ya nufi bedroom ɗinsa. Kusan mintuna goma sha biyar sai gashi ya fito. Ya sake ɗaukar ledar ya nufi ɗakin da ya kai Hibbah ɗazun. A yanda suka barta a haka ya isketa. Ya ajiye ledan a saman mirror fuskarsa na sake tsuƙewa. Ledar da Habib ya ajiye ɗazun ya ɗauka. Ya zaro handkerchief ɗin cikinta yana nufar gadon. Wata ƴar ƙwafa yayi dai-dai yana ranƙwafowa akan Hibbah da batasanma ya nai ba. Kansa tsaye ya ɗora handky ɗin saman hancinta. Tsahon minti ɗaya taja wani irin dogon numfashin da zai iya razanar da mai tsoro. Bai ɗaga handkerchief ɗin ba sai ma sake danna mata shi da yay akan hanci.

       Numfashin ta kuma ja da ƙarfi tare da sakin tari lokaci guda. Ya janye hannunsa da jikinsa yana mikewa da ƙyau. Ganin yanda take jujjuya kanta da cigaba da tarin ya sashi ɗaukar goran ruwan da ya ajiye a bedsite tare da ɗora kafarsa ɗaya akan gadon ya sake ranƙwafowa kanta. Murfin gorar ruwan mai ɗan sanyi ya ɓalle ya shiga tsiyaya mata a saitin wuyanta duk da akwai hijjab a jikinta har yanzu dan basu cire mata ba. Yanda yake kwarara ruwanne ya sashi tsalle har saman fuskarta zuwa ƙirjinta da kan gadon.

       Tai wata irin zabura da jawo numfashinta da ƙarfi ya iso har cikin hancinta. Duk da wani irin nauyi da jikinta yay mata hakan bai hanata ɗago hannunta ba ta shiga ƙoƙarin sharce ruwan da har yanzu yake kwarara matan. 

       Ɗayan hannunta ta kai cikin lalube da rashin ƙarfin jikinta da nufin ture ruwan da ke sakko matan. Sai dai hannun nata bai kai ba, sai kafarsa data ɗan shafo kaɗan ta ajiyesa yaraf tana ƙoƙarin son buɗe idanunta da sukai matuƙar nauyi.

        Dakatawa yay da tsiyaya mata ruwan jin ta fara magana a fisge. “Y… y… ya… ya… Mu…. ham…. mad… kar… Kar…ku ɗaura zasu kashe ku”. Ta shiga faɗa a rarrabe cikin ƙoƙarin fisgar numfashi da yunƙurin son tashi. Sai dai kuma luuu ta koma yaraf bisa gadon dan sam babu wani ƙarfi tare da ita. Hasalima abin bai gama sakinta ba baki ɗaya.

        Fahimtar hakan da yayi ne ya sakashi jan tsaki da cillar da goran ruwan yana sauke kafarsa ya miƙe tsaye sosai. Kallonsa ya kai ga agogon hannunsa yana sake tsuƙe fuska. 

        Tunanin mi yayi oho masa, sai kawai ya ja bargo aɗan fusace ya lullu ɓa mata, tare da sake ranƙwafowa ya kama hijjab ɗin jikinta yaja da ƙarfi ya farkesa. jansa yay baya ya fita da ga wuyanta. Da ga haka ya ɗauka ledan da ya shigo da ita ya fice ransa fal takaici.

   Bedroom ɗinsa ya wuce, duk da yana jiyo hayaniyar yaran nasa da ke cigaba da kallon ball da ciye-ciyen abinda ya kawo musun suna zabga gardamar da sukafi ƙwarewa akai.

★★★★

        Su Ummi sun isa katafaren sabon gidan da su Yaya Muhammad sukai matukar ƙoƙari wajen ginasa. Dan babu abinda su Hajiya Mardiyya ke ambato sai masha ALLAH. Ƙwarai da gaske matasan samarin na Ummi sun nuna ƙwazon da za’a yaba musu ƙwarai da gaske. Dan komai yayi cif a talauce ba’a sarauce ba. Sashen Ammar ne kawai ba’a karasa ba daga linta aka barsa.

       Kai tsaye sashen Ummi da ke a farko suka shiga. Inda nanma dai su Hajiya Nafisa keta sakama yaran albarka dan komai yayi a asashen tamkar bana dattijuwa Ummi ba. Akwai ɗakin Ammar da na Hibbah a sashen Ummin. Sai bedroom ɗinta dana baƙi guda biyu. Ga babban falukanta biyu da kitchen da dining babba da ke ɗauke da dogon dining table na family baki ɗaya. A kallo ma zaka san sashen Ummin yafi kowanne sashe girma a gidan, sai dai nasu kawai upstairs ne su kuma. Itama kuma catai bataso shiyyasa akai mata nata flat da ya kayatu da zamani.

        Suna shirin fara gabatar da salloli dan mazan sun fice sai ga kuloli ana shigowa da su. Cikin mamaki Ummi ke tambayar da ga ina?. Matasan samari biyu da ke shigo da kulolin suka bata amsa kai tsaye da faɗin. Isma’il ne ya turosu.

      Rasama mi Ummi zatace akan wannan yaro ɗan albarka tayi, sai kawai ta saki murmushi zuciyarta na ƙara jin matukar ƙaunarsa har cikin jini…………✍

       

*_Amin afuwa da jina shiru. Ciwo me ya kadani a bazata._*

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like