TAKUN SAKA 26

Advertisement

 

*_Typing📲_*

*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

Advertisements

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

_________________________

*_Chapter Twenty Six_*

………..Kai tsaye gidan A.G Abba ya nufa. Dan yasan yau ranar hutu ce baya a Station. Kasancewar basu cika haɗuwa a gidajensu ba yasa da ƙyar maigadin gidan A.G ya yarda yay masa sallama da shi. Dan ya kira wayarsa yafi a ƙirga amma bata shiga.

Advertisements

      Cikin takaici A.G ya fito, dan yayi zaman yin breakfast ne maigadi ya sanar masa zuwan baƙo. Turus yayi na ganin Abba. Sai dai tunda ya gansa babu damar komawa. Dole ya karaso inda yake yana faɗin, “Alhaji Halilu wai dama kai ne?”.

        Kai kawai Abba ya iya kaɗa masa. Kafin ya ce, “A.G akwai babbar matsala fa”.

     Saurin dakatar da shi A.G yay yana ɗan waige-waige. “Alhaji Halilu kayi haƙuri maganar nan bata nan bace. Inaga shigo ciki har motarka”.

    Babu musu Abba ya koma mota. Maigadi ya wangale masa gate bisa umarnin uban gidansa. Koda yay fakin ciki suka shige babban falon baƙi na gidan. A.G na niyyar fita domin kawo masa wani abin taɓawa Abban ya dakatar da shi.

        “A.G ci ko sha duk bashi bane a gabana yanzu, zo muyi magana.”

        “Humm Alhaji Halilu kanada ruɗani kai dai. Dan ALLAH ka kwantar da hankalinka dan nasan tatsuniyar gizo bata wuce ƙoƙi dai”.

      “A.G bazaka gane ba. Kai dai zauna kaji mike tafe da ni kawai.”

     Babu musu A.G ya koma ya zauna. Abba da ke a firgice ya fara masa bayani muryarsa har rawa take. “Asiya da ƴaƴanta sunbar gidan a daren jiya. Zuwa yanzu kuma bamusan ina suke ba. Hakan ya sake tabbatarmin yaron nan Master ne ya taimaka musu…….”

        Katsesa A.G yay da faɗin, “Master kuma Alhaji Halilu? Wai nikam miyasa duk kake zargin Master ne? Tayaya zai taimakesu miye ribarsa? Bayan kasani na sani akwai jiƙaƙiyar TAKUN SAƘA tsakaninsa da ƴarsu ma. To kai miye ma na damuwa da tafiyar tasu ne? Ba dama ta samu ba na hawa kan dukiyar da kake dako tsahon shekaru kaci karenka babu babbaka”.

         “A tunaninka kenan. Amma da ga abinda ya faru zuwa yau ka auna da hankalinka da ka fahimci inda alkiblar yaron nan ta dosa mana. A wannan karon da alama burgar banza kakeyi baya tare da kai. Dukiyar nan kuma da kake ganin zan cita cikin sauƙi bazata ciyu ba, koka manta duk kaddarorinsa sunayen ƴaƴansa ya sa matsayin next of kings. Wasu kuma sunan Asiyar ne ma”.

      “Hhhh wannan ganganne Halilu. A yanda na raini Master ni da abokan aikina bai isa zillemana ba ya maidamu abokan TAKUN SAƘAr sa. ai kaima kasan ko a gidan giya akwai babba. Maganar dukiya kuwa shi da kansa ma zai mana aikin”.

       “Ni duk ban musa maka kun raini master da wani blaa blaa ɗin zancenka ba. Yanzu so nake ka kirasa ka bigi cikinsa ko zamu san inda su Asiya suke. Sannan duk yanda za’ai inason ka samamin ma’aikacin banki da zaimin aikin sirri kuɗaɗen dake a accaunt ɗin Aliyu su dawo accaunt ɗina baki ɗaya, ka kuma saka shi Master ɗin nemo mana lauyan Aliyu duk inda yake”.

        “Maganar kiran Master ba damuwa bane, hakama zancen canja kuɗi zuwa accaunt ɗinka koshi zai iya mana wannan aikin.  Matsalar ɗaya ce ka yarda Master bazai zama shashasha akan mace ba. Macen ma ƙaramar yarinya kamar ɗiyar ɗan uwanka”.

         “To naji na yarda kirashi”. Abba ya faɗa badan ya yarda ɗin ba har cikin rai. Dan yanaji a jikinsa Hibbah tayi shu’umcin na mata akan Master. Sai dai shi A.G tsananin yardar da ya bama Master ɗinne yasa bai fahimtaba.

        “Kiran Master bazai yuwuba a yanzu. Amma zan tura masa saƙo da kansa zai biyo lokacin da yaga ya dace”.

     “To ashe kuwa yau a gidanka zan kwana”. Abba ya faɗa kansa tsaye.

     “Gidana kuma?”.

“Ƙwarai kuwa. Dan babu inda zanje saina tattauna da Master.

       “Humm Alhaji Halilu kai fa sam baka da haƙuri. Maganar zama anan bazai yuwuba. Kaje zan sameka gidan hutawarka. Kokuma mu haɗu wajen su Alhaji Alu”.

      “Kawai jeka shirya ina jiranka mu tafi tare”.

             Ɗan tsaki A.G yaja dan Abbah ya takura masa. sai dai babu yanda ya iya dole yace ya jirasan to.

        

★★★★★

            A ɓangaren Hibbah kam Shawarar data yankema zuciyarta ne ya sata sauka a gadon ta nufi toilet. Fuskarta ta wanko ta fito. ɗaukar tray ɗin kwanikan da tai breakfast tai ta fita da addu’ar ALLAH yasa yabar gidan. Babu inda ta sani amma tsabar ƙarfin hali yasata yarda zata gane. Taji matuƙar daɗin ganin baya falon, taɗan tsaya yima falon saman kallon tsaf. Sosai tsarinsa ya mata ƙyau. Ga wani ƙamshi mai daɗi da sanya zuciya nutsuwa na tashi duk da mayataccen ƙamshin turarensa na neman dannewa. Tunaninta ya bata baza’a samu kitchen anan ba, dan haka ta nufi downstairs ɗin kai tsaye.

        Tunda ta fara tako staps ɗin su Adam dake zaune a dining suna breakfast suka ɗago kusan a tare. Hibbah da ke sakkowa tayi ɗan turus ganin matasan samari kusan bakwai. (Su kuma waɗan nan fa?) tai tambayar a zuciyarta. Kai tsaye zuciyarta ta sake ayyana mata (Kin manta minene aikin mai gidan, ba dole kiga maza ba tare da shi). Tsaki taja a ƙasan maƙoshi tana ɓata fuska. Akan laɓɓanta tace, “Asararru”. Tana cigaba da sakkowa.

        Suko su Habib tuni sun maida kawunansu ƙasa tun kallo guda da sukai mata. Tana sakkowa step ɗin ƙarshe suka haɗa baki wajen faɗin, “Barka da safiya aunty”.

       “Aunty?!” ta faɗa tana kallonsu cikin ware idanu. Sai kuma ta turo baki, “Kujimin mutane dan ALLAH. Rusa-rusa daku zaku wani kirani aunty wannan ai zagi ne”.

        “Tofa ga mai gayya mai aiki, Kunga wata zuƙeƙiyar halitta. 

Cewar Salis a hankali.

    Zungurinsa Zaidu yayi cikin magana ƙasa-ƙasa yace, “Karkai maganar banza matar babban yaya ce, akwai tazarar taku”.

     “A gafarceni wlhy suɓutar baki ce”.

      Baba Saude da ke zaune da ga can falo tana murmushi ta ce, “Kinga manta da waɗan nan shaƙiyyan ɗiyata. Keda baki da lafiya ai da baki fitoba kinma barsu zanzo na ɗauka.

       Sai da Hibbah ta ɗan harari su Musbahu da murguɗa baki duk da bawai jin mi suke faɗa tayi ba sannan ta maida dubanta ga baba Saude tana sakin murmushi. “A’a babu komai mama. Ai naji sauƙi Alhmdllhi. Inane kitchen ɗin?”

       Cikin jin daɗin wayewar kan yarinyar da ko alamar baƙunta babu tattare da ita ta nuna mata hanyar kitchen. Kan Hibbah tsaye ta nufi kitchen ɗin kuwa. Komai ƙal fes tamkar ba girki aka kammala a cikinsa ba. Ganin hakan yasa Hibbah ajiye kwanikan a wajen wanke-wanke ta fara yunƙurin wankewa. 

      Motsin wanke-wanken natane ya saka Baba Saude shigowa. “Ya ALLAHU ƴar nan inake ina wanke-wanke kina fama da kanki. Ki barsa su Habibu zasuzo su wanke idan sun gama shiritar cin abin nasu”.

        (Uhm ai da yake ƴan daudu ne) Hibbah ta ayyana a ranta. A fili kuma sai tai ɗan murmushi. Karki damu mama zan wanke kawai. Ina maza ina wanke-wanke banda dai gidan naku a haguggunce yake”.

      Baba saude da ba fahimtar ina Hibban ta dosa tai ba tai ƴar dariya da faɗin, “Taɓ. Ai indai waɗan canne komai yi suke har girki. Babana ya musu horon tarbiya mai ƙyau ai. Sai dai ALLAH ya saka masa da alkairi”.

        Ɗan kallonta Hibbah tayi danjin abinda ta faɗa. Sai kuma ta saki guntun murmushi. “Mama iyayensu dai, shi da ya samesu da ga sama ai ba’ace tarbiyyarsa ba”.

       “To ƴar nan ai shine iyayen nasu. Dan dukansu da kike gani nan shi yay wahala da su tun daga gidan marayu, yawancinsu ma tun suna jarirai. Tarbiyarsa ce, horansa ne. Shine uwa a garesu shine kuma uba. Shine dangi. Ai samun mutum irin babana a wannan zamanin abune mai matuƙar wahalar gaske. ALLAH dai ya saka masa da alkairi ya cigaba da dafama rayuwarsa.”

        Karon farko da Hibbah tai sagade tana kallon Mama Sauden. Dan ba karamin dukan zuciyarta zancen yayi ba. Sai kuma tunawa da fasikancin da su Abba ke aikatawa da shi da tai yasata juyawa tana taɓe baki. A ranta tace (dan ya taimakesu shine kuma ya ajiyesu yana ɓata musu rayuwa kenan. ALLAH ya saka musu).

        Baba Saude da bata fahimci abinda Hibbah tai ba ta cigaba da bata labarin ƙoƙarin Master da jarumtarsa akan su Khalid na tsayama rayuwarsu har suka sami ingantaccen karatu a fanin islama da boko. Hibbah dai gyaɗa kai kawai take, dan zancen wani na shiga wani na fitane kawai. Ita duk wannan tarin alkairin nasa bawai gani take ba sam. Tsiyar da suke aikatawa da su Abba ta goge mata duk wannan farin nasa baƙi ya maye gurbinsa. 

      Sai dai cikin son bugar cikin Baba Sauden sai catai “Uhm lallai yaci sunan nasa Muhammad Shuraim”.

         Baba Saude tai ƴar dariya da faɗin, “Wai ƴar nan kinko iya faɗar sunan. Ni wlhy wahala yake min sunan nan nasa na larabawa. Shiyyasa nafi ganema kiransa da baba na saboda asalin sunan sa”.

      Gaban Hibbah ne ya faɗi. Kenan sunansa ne Muhammad Shuraim ɗin? Da sauri ta juyo tana duban baba Saude. “Oh mama bayan Muhammad Shuraim ɗin yana da wani sunan yanka ashe?”.

        Baki Baba Saude ta buɗe zata bama Hibbah amsa Habib ya shigo kitchen ɗin wuff tamkar an jehoshi. Waya ya mikama Baba Sauden. “Baba Master na magana”.

         Cike da farin ciki Baba Saude ta amsa wayar takai kunnenta da faɗin, “Alo babana”.

     Batare da Hibbah tasan mi ake faɗa da ga can ba taga Baba Saude na gyaɗa kai da faɗin, “To to babu matsala babana sai a dafa maka. ALLAH ya dawo dakai lafiya”. Da ga haka ta mikama Habib wayar. A dai-dai nan kuma su Salis suka shigo ɗauke da kwanikan da sukaci abinci.

    Ganin Hibbah ke wanke-wanke suka zaro idanu waje. “Aunty da kanki? Rufa asirinmu kar boss yay mana walmakalufatu”.

     Cikin bata fuskar haushi biyu Hibbah ta juyo tana dubansu. “Malami kubar wani kirana da Aunty niba auntynku bace.”

         Dariya kawai sukayi batare da sunce mata komai ba. Sai ma Habib da ya sake faɗin, “Aunty kibar wanke-wanken zamuyi Please”.

     Harara ta dallara masa. Yay saurin ɗora hanunsa saman baki yana faɗin, “Na tuba”. 

     Dauke kanta tai batare data tanka ba. Idris ya matsa tacan gefe yana tattare hanun rigarsa. Bara to na miki ɗauraya kawai. Banza tai masa ta cigaba da wanke kwanikan a cikin kumfar data ƙara ganin sun ƙaro kwanikan. Wannan taruwar tasu a kitchen ɗin ya hanata jin ɗayan sunan na Master. Hakan kuma ba karamin takaici ya sakata ba shiyyasa ta haɗe fuska har suka kammala wanke-wanken bata sake kulasu ba. Sai sauraren hirarsu da Baba Saude da takeyi. A ranta kuwa sai gulmarsu take wai sun cika surutu.

         Suna kammala wanke-wanken Baba Saude tace taje ta huta zata ɗaura girkin rana. Cike da jin daɗin hakan Hibbah tace zata tayata. Duk yanda Baba Saude ta lallaɓata akan tabari sai ta ƙara jin sauƙi ta dage zatayi. Fahimtar yarinyar babu ruwanta akwai sauƙin kai yasa baba Saude barinta sukai girkin tare. Kusanma Hibbahr ce tayi komai kaɗan baba sauden ta tayata. 

      Har sukai girkin suka ƙare tas Habib na nane dasu a kitchen ɗin yaƙi fita. Hakan ya ƙarama Hibbah takaici matuƙa dan bata samu yanda take so ba. 

        Sai dai cikin sa’a Baba Sauden ta fita jera abinci dining dai-dai Habib ɗin yana fita a kitchen ɗin saboda lokacin salla yayi zasuje massallaci.

         Harara ta raka bayansa da shi tana sauke numfashi, dan duk surutunta da rawar kai ta kula waɗan nan samarin sun damata sun shanye. Sauran kayan da suka rage ta ɗakko ta fito zuwa dining ɗin itama. Tana tsaka da taya baba Saude shirya kwanikan taji ƙarar waya nokia. Da sauri baba Saude ta nufi falon tana faɗin, “Tofa wake kirana ni Saudatu?”.

        Wani ɗan tsalle Hibbah tayi dadi kamar zai karta. Sai kuma tai saurin kama kanta ganin baba saudan ta dawo dining ɗin tana faɗin, “To nidai Bara’u banajinka sam. Nasan dai so kake kayi magana da Zaituna gashi kuma bana gida ina wajen aiki. Ka kira wayar Habu mai shago sai ya bata dan nasan yanzu ta dawo gida”. Da ga haka ta cire wayar a kunnenta tana mita.

        “Kai samarin zamani dai babu kunya. Kigafa wanann ja’irin ɗan makwafcinane. Akwai ƴar maƙwaftanmu da yake so bata da waya kullum sai ya kira a wayata sunyi wayar dare. Yau kuma bansan wace fitina tasashi kira da ranar ALLAH ba”.

      Hibbah da ke cikin jin daɗi tai ƴar dariya kawai.

        Baba sauden ma sai bata sake cewa komai ba ta ajiye wayar a dining ɗin ta cigaba da aikinta. Aiko wani sanyi ya sake sauka a zuciyar Hibbah. Cikin dabara da wayon da ALLAH ya bata ta shiga gyara zaman kayan dining ɗin harta iso ga wayar. Cikin dabara ta ɗauka tai ƙasa da ita tasa a silent. Kafin ta faki idon Baba Saude ta tura a cikin zani.

       A dai-dai wanann lokacin Master ya turo ƙofar falon ya shigo da sallama ciki-ciki. Cike da mutuntawa a garesa baba Saude ta washe baki tana faɗin, “Babana sannu da dawowa”

        Saurin juyowa Hibbah da sam ba jin sallamarsa tai ba tayi, idonta ya sauka akansa dai-dai yana gyaɗa ma Baba Saude kansa. “Baba ya gidan?”. Ya faɗa a taƙaice yana ƙoƙarin wuce Hibbah da ya nuna tamkar ma bai ganta a falon ba.

      “Gida Alhmdllh babana. Dan yau na ƙara samun ƴar tayen hira”.

    Sarai ya fahimci Hibbah take nufi, dan haka ya fara hawa steps ɗin kawai batare da ya sake cewa komai ba. 

      Harara Hibbah ta raka bayansa da ita. Wani sashe na zuciyarta najin tsananin takaicinsa da kallonsa mutum mai tsananin girman kai da wulaƙanci. Sai da ya ɓacema ganinta ta ɗauke kanta da duban Baba Saude, “Uhm Mama tunda mun gama nima bara naje nai salla”. 

     Juyowa baba saude da ke nufar kitchen tai ta dubeta. “Eh ɗiyata kin fini gaskiya kam. jeki kiyi nima bara na haɗa ma Babana abinci da Habibu sun dawo sai ya kai masa saman”.

        “To mama”. Hibbah ta faɗa tana nufar upstairs. Harta hau step na biyu baba Saude ta dakatar da ita. “Kinga yi haƙuri ko zaki dawo ki tafi masa ma da abincin ma kawai, a saman nan ake shirya masa shi. Dan tunda kikaga ya dawo to yunwa yake ji”.

     Hibbah dai da yake neman hanyar kuɓuta take kafin baba Saude ta farga da rashin wayarta da sauri tace, “To baba ki bari kawai su dawo sai sukai masa kamar yanda kuka saba. Kar kuma kaiwar tawa yasa hakan bai masa ba”.

       Gamsuwa da zancen nata da kuma sanin halinsa yasa baba Saude faɗin, “Eh gaskiyarki kuma, dan dama inba Habibu ba babu ma mai yawan hawan saman kai tsaye sai inshi ya bukaci ganin wani a cikinsu. Jeki kawai”.

       

         Hibbah da batai tsammanin samunsa  zaune a falon ba tai ɗan diri-diri. Ƙoƙarin haɗiye abinda ya tsarga matan a maƙoshi tai tana cigaba da takowa ganin baiko nuna alamar yasan da shigowarta ba, kamar barci yake ma a hakan.

     Ta ɗan taɓe baki saboda ganin wani zaman ƙasaita da yay a cikin kujera. Hanyar ɗakin data tsinci kanta a ciki ta nufa zuciyarta na tsitstsinkewa saboda shegen sanyin da falon ya ɗauka. Amma shi ko a jikinsa, da alama ma matsanancin daɗi yake masa.

         “Kin koma satan waya ne?”.

   Ƙasaitacciyar muryarsa mai amo da kamewa ta daki dodon kunnenta. Cak ta tsaya da rumtse idanunta da ƙarfi,  dan duk tsiwarta tana shakkar wanda baizo mata da wasa ba. Ko yau da safe takaicin tuno maganarsu Abbah yasata iya maida masa murtani badan bata ganin girmansa a idanunta ba. Ko bai tanka maka ba kwarjininsa da kame kai yasa ma’abocin mu’amulantarsa jin shakkarsa.

        Juyowa tai a hankali tana ɓata fuska ranta fal mamakinsa. Ta ɗan saci kallonsa amma sai taga yana a yanda ta shigo ta samesa ido lumshe bai motsa ba. Duk yanda taso yin tsiwar ta gagara koda motsa laɓɓanta tsabar yanda ya cika mata idanu har bata ganin wani fili a falon, dan fuskarsa tamau take babu alamar yasan minene fara’a.

       Cikin pretending da shagwaɓar da takema su Yaya Muhammad ta ce, “Ni wlhy ba ɓarauniya bace. Tunda dai ba’a taɓa cewa na ƙwamushe kuɗaɗen bankin mutane b?”. Tai maganar da ɗan murguɗa baki duk da zuciyarta kuwa babu abinda take sai lugude.

          Lumsassun idanunsa da suka kaɗa jajur kamar wanda yake cikin ɓacin rai ya buɗe akanta. Sallama Habib ɗauke da tray babba ya hanashi yin maganar da yay niyya.. 

     Itama sai ta juya tana amsa masa sallamar da yay ranta fal murnar samun hanyar kuɓuta. Habib ɗin ya ɗan risinar da kansa cike da girmamawa ya ce, “Sannu Aunty”.

    Harara Hibbah ta zuba masa tana sake ɓata fuska. Shi dai yay gaba abinsa yana murmushi. A tunaninta zuwan Habib ɗin zai kuɓutar da ita. Sai taga saɓanin haka dan ko motsi baiyiba, baima amsa gaisuwar Habib ɗin ba, sai mayatattun idanunsa da har yanzu ke a kanta. 

       Ƙasa tai da kai, ta kasan ido ta gama auna tafiyar da zata kaita ɗakinta. Ta ɗan dago ta sake dubansa. Ganin har yanzu ita ɗin dai yake kallo sai ta ɗan fara taku kamar zata koma wajensa. Hakan da tai ne shi kuma ya sashi ɗauke idanunsa ya maida kan Habib da ke zuba masa abinci. 

       Tana ganin haka ta zambaɗa da gudu. Sai ƙarar takun gudunta kawai suka jiyo.

        Habib yay saurin saka hannu ya danne bakinsa jin dariya zata kufce masa. Shiko gogan wani irin fici-ficin fitina yayi da idanunsa yana sake tsuƙe fuska. Cikin muryar da babu wasa ya dubi Habib.

      “A rufemin network ɗin gidan nan na tsahon awa biyu”.

           Tamkar Habib zai fasa kuka ya dubesa. “Master awa biyu?”.

     Harara ya zuba masa. Habib yay saurin gyaɗa kansa da amsawa da to. Kasancewar ya kammala zuba masa abincin ya nufi hanyar downstairs dan babu damar ƙara yin musu.

     Shi ko lip ɗinsa na ƙasa ya dan ciza da jawo abincin gabansa ya fara ci a nutse. Sai dai kuma tun a laumar farko yaji banbancin girkin dana baba Saude. Idanu ya lumshe ya sake buɗewa akan abincin, dan ɗanɗanon sak na wadda a yanzu yakema kallo irin na uwa mai saka zuciyarsa farin ciki da yin rauni. 

       A hankali saman laɓɓansa ya furta “ALLAH ya ƙara miki lafiya da nisan kwana mai albarka Ummi”…………✍

Ni dai na ce “Hummm Master wace Ummi?”🚶🏻😹   

 

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like