Advertisement
๐๐๐๐๐๐๐๐
*TAYI MIN ฦANฦANTA*
๐๐๐๐๐๐๐๐
*Zahra Surbajo*
*KIN SIYA KO KINA JIRAN A SATO MIKI KI KARANTA KYAUTA๐*
Advertisements
*SHIMFIฦAR AURENA na kuษi ne duk meso ze iya turo kuษinsa tun yanzu naira 500 kacal,update biyu arana,safe da dare,insha Allahu, ku biya ku karanta daga jin sunan kunsan zaa ษata hankalin dare,ga wanda yasan hannun surbajo yasan bazata bashi kunya ba karku bari abaku labari,SHIMFIฦAR
AURENA,littafine daze kerewa kowanne,novel nawa,akwai tarin sirrika da magunguna acikinsa,dazasu fito da kimarki ta mace,sannan ga sirrin riฦe miji da ฦดan uwansa,an baje kolin basira acikinsa,kisiya ki biya ki karanta,wannan soyayyar da akewa surbajo to afito a nuna ta akan SHIMFIฦAR AURENA,500 ne kacal*
*Zahra muhammed Nasir 2084024749 UBA*
*Whatsapp 07044600044 aturo shaidar biyan ta nan*
*A nunamin soyayyar ta hanyar siyan littafina,shine magana,*
*Allah gatan bawa*
*Surbajo*
Advertisements
*ฦณar bautar ฦasa*
*Cin Amana ko fansa*
*Sanadin kidnapping*
*Karen bana*
*ฦan karuwa*
*Aure da Haihuwa*
*Ummu Aymana*
*Kano to Jidda*
*Tayi min ฦanฦanta*
*Illar zawarci*
*Body guard*
*Amana ta barmin*
Da sauransu.
*Duka ฦyauta na baku su,dan soyayyata gareku๐*
*yanzu nima inaso anunamin kwatankwacin soyayyar asayi SHIMFIฦAR AURENA 500 kacal muci gaba da son juna๐*
*37*
“ke har yanzu baki girma da haye min cinya bane?”mummy ta faษi tana shafa kan zahra.
Dariya tayi sannan ta ฦara gyara kwanciyar tata,tace cikin shagwaษa”kai mummy,nawa nike gaba ษaya na,naga har yaya ma hawa yake wani lokacin”
“ay duk kun dena hawamin,ku kawomin jikokina su hau”mummy ta faษi cikin nishaษi.
Shuru zahra tayi,batace komai ba se murmushi.dan batun ya bata kunya.
Suna nan zaune a falon daddy ya shigo falon se ฦamshin turare yake irin nasu na manya,yana ganin zahra yace cikim fara’a “yau ,zahran tawace agidan nan ah lalle mina da babbar baฦuwa”
Zahra wacce tun shigowarshi data shaฦi ฦamshin turarenshi zuciyarta ta fara tashi daurewa kawai takeyi,
Guri daddy ya samu ya zauna,sakkowa zahra tayi domin gaisheshi,amma ina aman daya yunฦuro mata be bata damar yin hakan ba.
Tuni ta gama ษata gurin da aman,hankalin mummy da daddy ne yayi mugun tashi,mummy riฦe take da ita,daddy na jero mata tambaya”zahra me ya sameki dama baki da lafiya ne?”zahra ba baka se ido,ga wani sabon yunฦurin aman tanayi,
Kamata mummy tayi ta kaita ษakinta,kai tsaye ruwan wanka ta haษa mata,ta rakata har toilet ษin ta rufo mata ฦofar.
Masu ayki mummy tasa suka gyara gurin,daddy kuma ษakinshi ya wuce yayo wanka,yasako jallabiya sannan yadawo ษakin mummyn.
Ay yana shigowa zahra taji ฦamshin turaren da gudu ta kuma komawa banษakin,ta fara kyalaya amai,bin ta mummy tayi da sauri,ta riฦeta har ta gama,ta wanke mata baki da fuska,sannan ta kamota da nufin su fito.
Cogewa tayi a toilet ษin ta marairaice fuska tace “mummy ki barni anan turaren daddy ne bana son ฦamshin shi,shine yake sani aman nan”
Wani farinciki ne ya ziyarci zuciyar mummy wanda rabonta da jinshi tun lokacin data samu cikin surayya,wanda har a fuskarta seda ya bayyana.
Sakinta tayi ta fito bakinta a washe,daddy dake zaune zaman jiran fitowarsu kallon rashin fahimta yake mata, yace”hajiya ina ษiyar tawa kika barota kikazo nan kina min dariya?”daddy yayi tambayar cikin ษaurin kai.
Dariya mummy tayi sannan tace”Alhaji to ay kai jikan naka kaine baya yi dakai,dan turarenka ne ke sawa yake wahalar maka da ฦดar taka”
Janyota yayi jikinshi,yana murmushi yace cike da faraa”kina nufin zahra ta cikine da ita?”gyaษa mishi kai tayi tana dariya.
Rungume mummy yayi cike da faraa,yana sumbatarta a goshi yace”tukuicin wannan albishir hajiya,zan sauya miki mota”
Sosai mummy ke godiya,daga haka sakin ta yayi yabar ษakin,fanka mummy ta kunna,ta buษe windows,turaren yagama fita,sannan ta kashe fankar ta kullo windunan,ta koma toilet ษin ta kamota suka fito,ta kwantar da ita akan gado.
Abinci mummy tasa aka kawo mata taci,tasha ruwa,sannan mummy ta ษibi jininta sannan ta bata ฦดat kwalba tayi fitsari aciki .
ษakin data ware a mazaunin asibitin tafi da gidanka ta nufa,taje ta gwada komai dan ta tabbatar da hasashenta,ayko sakamako na fitowa cikinne.
Sosai mummy ke godiya ga Allah daya ara mata tsawon rai na ganin wannan lokaci.
Hammad ko nacan cikin abokai anata chapter,jikinshi ne yaji be masa daษi kewar matarshi duk ta dameshi,hakanne yasa yayi musu sallama gefin magriba,ya tuฦo motarshi zuwa gidan iyayen nasa.
Muje zuwa
Surbajo for life.
GIPHY App Key not set. Please check settings