HALIN GIRMA 25

Advertisement

Halin Girma

      25

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

Advertisements

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

***Ta dade a kitchen din tana jujjuya yadda zata yi, gashi lokaci na tafiya dan har kusan bakwai ce zatayi, barin kitchen din tayi ta wuce ta fara gyara falon, duk da ba wani datti da yayi amma sai da ta sake share shi ta bubbuge kujerun ta tattare komai ta ajiye a gefe har da rigar baccin da ta gani a jikinta dazu. Daga nan ta sake komawa kitchen din kawai ta yanke shawarar tayi abinda zata iya, ta dauki indomie ta dafa da egg sannan ta dafa ruwan tea ta jera musu akan dinning din ta wuce dakin da yake a mazaunin nata da tunanin yadda zata samu waya ta kira gida, ko kuma ta samu hanyar da zata bar gidan dan bata ga alamar Bashir zai kyaleta ta sauki ba.

  Tana zaune tana sak’awa da warwarewa aka turo wata yarinya kiranta, kamar ba zata tashi ba, sai kuma ta mike tabi bayanta tana taraddadin abinda zata tarar. Matan jiya ne jere akan dinning din, sai uwar gayyar daga gefe ta hade rai sosai tana mata mugun kallo, tun kafin ta karaso ciki ta hau surfa mata ashar

“Saboda tsabar ke yar iska ce, abinda nace ki dafa daban abinda kika dafa daban ko? Zo nan.”

Advertisements

Kin zuwa tayi, ta k’ame a wajen tana kallon su

“Ji yadda ta tsare mu da ido Hajiya Lay, amma dai yarinyar nan bata da kunya.”

“Ku barta, bata san wacece Layuza ba, zan koya mata hankali.”

Bud’e baki Zeenat din tayi, tace.

“Ke nake aure ne wai ko shi?”

“Kutmelec! Ni kike wa wannan tambayar?”

“Toh ai naga dai iyaye na Bashir suka aura min ko? Me yasa kike nuna kamar ni din me aiki ce a gareki, ni bansan ki ba, bansan wacece ke ba kawai zaki dinga nuna iko akaina “

“Lallai yarinya, kinyi babban kuskure da har zan fad’a ki mayar, toh dake da Bashir din duk a karkashi na kuke, kuma baki isa ki hada miji dani ba wallahi, kinyi kad’an ace kece kishiyata, dan haka yanzu baki da maraba da me aiki a gidan na, kuma dan ubanki dole kiyi duk abinda nace, na samu labarin komai da yadda auren ya kasance, shegen kwadayi da son zuciyar uwarki dake ya jawo miki, dan haka ki wuce ki yi abinda na saki kafin na taso na yi miki mugun dukan da zaki kasa tashi wallahi.”

” Ai da kawai daidaita mata shegen bakin nan nata akayi gobe ba zata sake fad’a ki fad’a ba.”

” Barta, zata gane kurenta.”

Zumburo baki tayi, ta ki barin wajen ita a lallai basu isa ba, ganin haka ya saka Hajiya Layuza tasowa aikuwa tana ganin haka ta kwasa da gudu bata tsaya ba sai data kai dakin tayi saurin saka sakata tana maida numfashi. 

***Tagumi Mama ta rafka, duniyar gaba daya ta daina mata dadi tun bayan da ta tabbatar da babu wani abu da zata iya dan Abba sai da ya sake jaddada mata akan duk wani abu da ya samu auren Zeenat toh ta tabbatar da mutuwar nata auren, ada taso suyi duk wacce zasuyi amma daga baya sai tayi wa kanta fad’a ta hakura ta zuba wa sarautar Allah ido, gashi ta kikkira wayar Zeenat din amma ko da yaushe bata shiga, takanas ta tura Habib ya je har kofar gidan amma sai ya tarar a rufe, abinda ya kara daga mata hankali kenan, ta saka Abba a gaba tana kuka dole ya dauki waya ya kira Bashir din, ya kuma yi mata handsfree dan taji. Maganar an je an ga gidan a rufe Abban yayi masa nan ya shaida masa ai suna family house dinsu sai sun danyi kwanaki zasu dawo gida haka al’adar gidan su take, addua Abban yayi musu daga nan ya kashe yana kallon Maman da tayi tsuru tana ji har suka gama.

“Kin dai ji ko? Ko kuma address din gidan nasu zan baki?”

“A ah.” Tace a sanyaye tana mikewa. Cigaba da aikin gabansa yayi dan be ga dalilin da zai saka ta tada hankalin ta ba, bayan sun riga sun aurawa Bashir din basu da ikon bibiyar in da duk zai kaita.

***Zuwa yamma masarautar ta cika sosai, duk wanda Ammi ta gayyato sun hallara, yan mata ne kyawawa masu aji suka fi yawa sai manya tsirari wanda Ammi ta barsu sai ranar nadin dan kar ya zama an takure mutum, Ba’a dau lokaci aka shiga gabatar abinda ya tara su, saboda a ranar su Mamma suke so su wuce. Tsarin daban ne da duk wani taro da akayi na bikin, Muhammad da be niyyar attending ba, amma ganin abinda ya faru ya sakashi shiryawa cikin shigar da yasan zai burge Iman dinshi, wanda be san iya adadin yan matan da suka sake faller masa ba a ranar. Yana zaune kusa da ita daf ya dan karkace yana fuskantar ta, yana mata magana k’asa-kasa, tana jin sa sarai amma ta fuske dan ta gama gane shi so yake suyi abin da zata sha kunya dan taga kamar shi be san kunya ba sam. Daga nesa ba zaka gane yanayin da suke ciki ba, zaka dauka yanayin zaman nasa na mulki ne, sai ka matso sosai zaka gane kan abun. Shigar da Laila tayi a wajen ta kusan fin ta Iman din, babu laifi Allah ya hore mata kyau ba kad’an ba, dan sanda ta shigo wajen sai da gaban Iman ya fadi ganin uwar kwalliyar da taci kamar wata dawisu, kai tsaye wajensu ta nufo tana tafiya tana karkada kowanne lungu da sako na jikin ta, kamar bishiyar da iskar rani ke kadawa haka ta dinga karkada jikin ta har ta karaso wajen fuskar ta a washe ta matsa daidai saitin Capt Muhammad ta rankwafo tana nunawa camera man sign din ya dauke su.

  Da ido Muhammad yayi masa alamar idan ya dauki hoton sai dai wani bashi ba, sum-sum ya bar wajen hakan ya bata wa Laila rai tace

“Capt wanne irin wulakanci ne wannan?”

“Baby kinga waccar da ta shigo yanzu?” Yayi kamar be ji ba, ya matsa jikin Iman din yana nuna mata wata,

“Kanwar Ammi ce, itace Aunty Fatima.”

“Ok wadda ka bani labarin ta ko!?”

“Yea ita.”

“Allah sarki, she’s nice.”

“Sosai.” Sai ya sake kai fuskar sa jikin ta sosai

“Baby perf din nan akwai kamshi, i just love it, yayi dadi.”

“Thanks dear.” Tace tana smiling

Bakin ciki ne ya tuke Laila, tayi saurin barin wajen kafin zuciyar ta, ta buga. Tana barin wajen sukayi wa juna murmushi.

A gajiye suka koma cikin gidan bayan an gama taron, su Mamma sun jima da tafiya dan haka part din Ammi aka maida ita, daga nan Ammi ta saka mutane da yawa suka yi mata rakiya zuwa nata part din da ta riga ta tare tun a jiya ba tare da Ammin ta sani ba, sai gobe za’a rakata wajen Bubu idan ta huta shi ma baya nan yau sai goben zai dawo.

   Masu kula da bangaren da duk wani abu da ya shafe ta Ammi ta nuna mata, suna isa kuwa suka shigar da kayan su dakunan su dake bayan part din suka shigo suka fara aikin gyara shashen, suka gama suka saka masa turaren wuta sannan aka jere musu abinciccika masu rai da lafiya. Sai da suka tabbatar babu wani abu da zata bukata sannan sukayi mata sallama suka tafi.

   A gajiye take sosai amma kuma dole tayi wanka dan sosai Mamma ta jaddada mata muhimmanci wanka da gyara jiki, cire kayan jikin ta tayi, ta zari towel daya ta daura ta nufi toilet din, wanka tayi ta hado da alwala ta fito tana sharce kanta. Wayarta ce tayi kara ta dauka tana dubawa, Mommy ce ke kiranta, tunda aka fara bikin basuyi magana ba, sai dai ta jisu da Mamma suna yi, zama tayi tana daga wayar dadi na cikata 

“Mummy barka da dare.”

“Iman… Kuna lafiya?”

“Lafiya lou mummy, dama yanzu nake so nazo na kira.”

“Ko? Toh gashi na kira ni ai, ya sabon waje?”

“Alhamdulillah.”

“Mamma ta sanar dani duk yadda abubuwan suka kasance, nasan kuma duk abinda ya kamata ki sani ta sanar dake, dan haka ita rayuwar aure yar hakuri ce, sannan duba da irin gidan da kika samu kanki, sai kinyi hakuri kin kuma zama me lura sosai.”

“In Sha Allah mummy.”

“Yawwa, ki kula sosai da mijinki da duk abinda kika san yana so, karki ga tarin ma’aikata ki sakar musu kula da mijinki, duk wani abu da ya danganci mijinki ki taske kiyi shine hanyar samun ladan ki, kuma hanyar aljannar ki.”

” In Sha Allah Mummy, nagode sosai.”

“Ki ajiye kunya ki kula da mijinki sosai, banda sanyin jiki da lalaci.”

A kunyace tace

“Toh mummy.”

Turo kofar akayi, yana sanye da 3quarter wando babu riga a jikin sa, saurin dauke kanta tayi tana amsawa mummy bayanin da tayi mata akan wasu magunguna da ta saka mata a bag dinta. Gabanta yazo ya tsaya k’yam yana karewa cinyoyin ta dake bayyane saboda kankantar towel din. Tsugunawa yayi a gabanta ya saka hannu ya shafa saman cinyar ta ta, tayi saurin janye su tana jan numfashi, 

“Kina ji na Iman?” Mummy tace jin kamar attention dinta ya tafi wani wajen.

“Am.. am ina ji Mummy.” 

Ta amsa a firgice ganin ya kai hannu jikin towel din ya janye, da sauri ta saki wayar bayan ta danne power button din, ta mike tana rik’e towel din. Idonsa a shanye yake kallon ta

“Zanyi wanka.” 

Yace yana shigar da idonsa cikin nata, kasa matsawa tayi daga wajen, sai jan towel din take a dole sai ya sauka ya rufe bayanta. Bata taba jawowa zai shigo a lokacin ba, ta yi tunanin ma ya tafi, sai ganin shi tayi. Dariya ta bashi,yadda ta hakikance a dole sai ta saukar da towel din.

“Zanyi wanka.” Ya sake maimaitawa yana folding hannun sa, kamar ta dora hannu a ka tayi ta kurma ihu ta shiga takawa zuwa toilet din tana cigaba da jan towel din. Ji tayi an rungume ta, ta baya ya dora kansa a saman kafadarta.

“Me kunya, kunyar me kike ji?”

“Ba komai.”

“Shine kike ta jan towel din bayan halal dina ne, sai a barni na more kallon kayana ko?”

“Uhum”.

” Emana. ” Ya sake tura kansa wuyan nata sosai,yana jujjuya kan, hakan ya haifar mata da kasala, ta dinga kokarin zamewa amma ya hanata, a dole ta kyaleshi yayi budurin sa. Sai da ya tabbatar da tayi laushi sosai sannan ya jata zuwa toilet din. Mamakin rashin kunyar sa take, shi ko a jikin sa babu abinda ya dame shi, ita kuwa kamar ta shide idan ta kalleshi a hakan sa, da k’yar ta samu ya barta bayan ya kara tattabe ta, ta samu ta fito ta barshi a ciki, a gurguje ta shirya ta saka kaya ta tada sallah ko da ya fito tana sallah sai kawai ya shirya shima ya fita falo dan cikin sa ya fara kiran yunwa. Zaman jiranta ya dinga yi jin shiru bata fito ba ya leko ya kirata, dan baya so a kara kwana be bata labarin komai ba, a kalla hakan zai saka ta sake yarda dashi ta kuma taimaka masa dan ita kadai ce ta fara ganin Laila sanda ta shigo part din. Tsattsakurar abincin tayi tace ta goshi dan da gaske tsoro take ji, tsoron kar yace zai sake yi mata irin abinda yayi mata jiya, ba zata iya dauka ba, shiyasa tana gama ci ta sulale ta gudu ta kwanta ta kudundune a dole tayi bacci. Sai da ya gama komai sannan ya biyo ta dakin ya yaye abinda ta rufan yana shigewa jikinta. 

*_ZAFAFA BIYAR 2022🔥_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO)  s_*

_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*👇👇

D’aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*👇👇👇

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*👇👇

09134848107

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

HALIN GIRMA 22

Advertisement  Halin Girma       22 *_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_* https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share *_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb Advertisements…

HALIN GIRMA 19

Advertisement   Halin Girma       19 *_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_* https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share *_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb…