HALIN GIRMA 30

Advertisement

 Halin Girma

      30

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINKπŸ‘‡πŸΎ_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINKπŸ‘‡πŸΎ_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

Advertisements

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINKπŸ‘‡πŸΎ_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINKπŸ‘‡πŸΎ_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

******* β˜…

A durkushe ya ganta tana kuka ta rik’e kanta, saurin durkusawa yayi a gabanta yana janye hannun nata

“Menene?”

Advertisements

“Miciji!” 

Tayi maganar tana nuna masa wajen, saurin kalla yayi amma be ga komai ba, ya yunkura zai tashi ta kankame shi sosai tana fashewa da kuka. Hannun ta ya kama zuwa wajen switch din falon, ya kunna haske ya bayyana a ilahirin falon, wurwurga idonsa ya dinga yi a gaba dayan falon amma be ga komai ba, 

“Aina kika ganshi?”

“Adaidai nan zai shiga dakin chan!”

“Tsaya .” Ya tsaida ita yana sake dubawa amma babu komai. Riketa yayi ya kaita daki, tayi saurin rikeshi ganin zai fita

” Dan Allah karka fita ka barni.”

” Kinaji? Calm down babu abinda zai faru, yanzu zan dawo.”.

Sakin sa tayi, ya fita ya taso securities din a gaba, suka zo suka hau bincika falon da ko ina na part din,ciki ya koma ya sameta ta kudundune a saman gadon still jikinta be bar rawar da yake ba, tana addu’a kasa kasa, daga gani kasan ta tsorata sosai dan bata taba ganin shi haka a zahiri ba. Jawota yayi jikin sa, ya mannata da kirjinsa yana shafa mata baya kad’an kad’an.

” Babu abinda zai faru kinji? Ki kwantar da hankalin ki.”

Da kai ta amsa masa, zuwa lokacin ta fara dawowa nutsuwar ta, sai wani uban juyi da taji cikin ta nayi,ta dora hannun ta a saman cikin yana yatsine fuska, kallon hannun nata yayi, ya dauki nasa ya dora a saman nata yana tayata shafa cikin, 

“Ciwo?”

“Eh.”

“Sannu zai daina, bari na dubo ko sun gama dubawar.” 

Ya kwantar da ita ya fita, a tsaye ya same su rik’e da abu me kama da maciji, matsawa yayi yana dubawa cikin son karin bayani

“Macijin roba ne ranka ya dade!”

“Roba?” Yace cikin yanayin mamaki

“Me ya kawo shi nan? Me yasa bamu ganshi ba tun da rana sai yanzu…”

“Waye da waye suka shigo part din nan?” Ya fad’a yana daure fuskarsa tamau. Rantse rantse suka hau yi, kowa na son kare kansa, wata uwar tsawa ya daka musu, duk suka nutsu suka kame suna masu saukar da kansu k’asa 

“Kwana daya tal na baku, ku gano wanda ya shigo part din nan har ya ajiye wannan shirmen, koma waye sai ya fuskanci hukunci me tsanani!”

” Yes sir!”

Har ya juya sai kuma ya tsaya.

” Get ready, we are leaving tomorrow in the afternoon!”

” Yes sir!” 

Suka kara hada baki wajen fad’a sannan ya juya ya bar su a wajen da sassarfa. Dayan dakin ya shiga, ya hau bincike wasu kaya da sauri da sauri, ba zai yarda a taba masa ita ba, idan har ba zasu iya tsayawa iya kansa kawai ba, toh zai yi abinda zai girgiza su matuka. Ya dan dau lokaci a dakin, sai da ya tuna ya barta ita kadai ya kuma san tsoro take ji, sannan ya koma da sauri, ya tarar bacci ya dauke ta, ta takure waje daya tana fitar da numfashi kad’an kad’an. AC din dakin ya rage, zuwa low ya dawo ya gyara mata kwanciyar, ya kura mata ido yana jin son ta na kara ruruwa a zuciyar sa, ba zai bari banzar al’adar gidan su ta taba ta ba, zai yi duk abinda zai yaga ya kareta da dukkan karfin da yake dashi.

   Da asubah ya tashe ta, sukayi sallah a dakin, sannan ya fita ya shigo mata da micijin robar yana mata dariya

“Matsoraciya, nina fa na shigo dashi jiya by mistake, abun wasan yaran chan ne suka bani, ashe sai na yar dashi ban ma lura ba.”

Shiru tayi tana kokarin daidaita maganganun nasa da abinda ta gani, idan har ba gizo idon ta yayi mata ba, toh tabbas tafiya ta ganshi yana yi, har ya kai kofar dakin kafin ta daina ganin sa.

“Common!” Yace yana son dauke tunanin ta

“Babu komai fa I promise you.”

“Amma na ganshi fa yana motsi!”

“Imagination ne kawai nothing else, karki damu ki kwantar da hankalin ki.”

Shiru tayi tana kallon sa, yanayin sa yayi mata kama da na wanda yake so ya dauke hankalin ta, amma idan ba haka ba babu yadda za’a yi taga abu yana tafiya da idonta ya zama imagination kuma, hore mata idon yayi yana jawo ta jikinsa

“Karki yi ta tunani kinji? Anjima zamu wuce ma, Abuja zamu fara zuwa na gaida Mummy, daga nan muyi tafiyar mu gidan mu mu sha soyayyar mu.”

“Da gaske?”

“Da gaske mana, are you happy?”

“Naji dadi sosai, bari na fara hada kaya na, da wuri zamu tafi ko? Ko sai da yamma.”

“Yamma!”

Komawa tayi ta zauna tana jin kamar yamman ya mata tsayi

“Zanga Aji ne, sannan bana son kowa yasan mun tafi sai Ammi kawai, shiyasa ba zamu dauki yaran chan ba, i mean ma’aikatan gidan, akwai screening da za’a yi musu kafin su biyo mu.”

” Owk Allah ya kaimu.”

” Amin my beautiful wife.”

Murmushi tayi, ya dauko musu al’qurani me girma suka shiga karantawa, ya dinga admiring muryarta da yadda take bawa kowanne harafi hakkin sa, cikin nutsuwa da fitar da tajweed a duk in da ya dace. Sai da rana ta fito, sannan sukayi wanka, suka shirya a tare suka fita don karyawa, bud’e warmers din yayi, ya kakkala sannan ya saka aka kwashe masa su daga wajen, ya aika part din Ammi aka karbo musu breakfast din, taso ya barta tayi amma ya hanata, ya kuma ki gaya mata dalilin da ya saka shi sawa a kwashe abincin da aka girka a part din, bata ce komai ba, ta barshi a zuwan kawai zata ji koma menene daga baya, dan ta lura yadda ya boye masa kanta kafin aure akwai abubuwa da yawa da yake boyewa a yanzu ma, duk da haka ba zata zarge shi ba, zata bashi lokaci sosai ta kara fahimtar shi, jikinta na bata akwai wani abu da shi kadai ya sani, sai ko Aji da take ganin kusancin su yafi na kowa hatta mahaifiyar sa da mahaifin sa.

  Bayan sun gama breakfast din ne ya fita, cikin shigar kayan sojoji da suke masifar yi masa kyau, cikin rakiyar yaransa ya nufi part din Kilishi, wanda tun kafin ya karasa sakon zuwa nasa ya ishe mata, tana zaune ta gama karyawa, tashi tayi da sauri ranta na baci, tasan zuwan sa babu abinda yake jawo mata sai bacin rai. Daki ta shiga ta chanja kaya, ta zauna tana jiran sanarwar isowar sa. Tana jin sanda ya shigo, dan har falon ta na ciki ya shigo, ya zauna fuskar sa fes dauke da farin ciki, idonsa na kan kofar da zata fito, ya dan dauki lokaci a zaune har ya fara tunanin ko ba zata fito ba, agogon hannun sa ya kalla, ya daga kai ya kalli na jikin bangon dakin, a tare suke tafiya dakiya daya, sauke idon sa yayi yana murza agogon nasa, takun tafiya yaji, yaki d’agowa amma yasan itace,sai da ta zauna sannan ya dago yana dubanta, yayi murmushi cikin salon girmamawa yace

“Barka da gida ranki ya dade.”

“Barka dai, ya iyali?”

“Lafiya kalou kalou, kamar yadda kike fata a kowanne lokaci.”

Yak’e tayi, tasan magana ya fad’a mata, dan ya saba gasa mata ita dama, murmushi ya sake yi yana lankwasa hannayen sa baya

” Haka ake so ai, sai a sake kula sosai.”

” In Sha Allah, za’a kula kulawa me kyau, duk wani me sharri Allah zai maida masa kansa ma, saboda addu’a itace makamin mumini, kuma matakin duk wata nasara.”

” Haka ne!” Tace tana gid’a kanta. Mikewa yayi cikin salo na burgewa, ya dan rankwafa yace

” Na barki lafiya!”

” Nagode!” Tace tana danne zuciyar ta, bayan sa tabi da kallo har ya fice gaba daya, 

“Ahhhh!” Tayi kara tana jifa da trow pillow din dake kusa da ita,kamar ta shako shi haka taji, gashi kamar masifa yasan duk wani shirin ta, ta rasa yadda zatayi dashi ya zame mata tamkar kadangaren bakin tulu! Ya kuma zame mata ciwon ido, da za’a bata makami ace ta kashe mutum daya toh tabbas shi zata kashe, bata son ko ganin wulgawar sa.

   Laila ce ta shigo, ta tarar da ita cikin halin da take ciki na bacin rai, bin ta tayi da kallo har ta dauki jakar ta, ta bud’e ta dauki ATM cards din Kilishin, ta juya zata bar dakin.

“Laila!” Tsayawa tayi ta juyo

“Ina zaki? Me kuma zakiyi da Atm dina?”

“Haba Mah, tunda har na dauka ai amfani zan dashi.”

” Shine ba zaki iya fada min ba?”

” Da ma fa na saba dauka kuma bana fad’a miki, why now?” Sai ta juya ta cigaba da tafiyar ta

” Zan dawo dashi wani payment kawai zan.” Sai data kai karshen kofar sannan ta fad’a, ta saka kai tayi ficewar ta, kwafa Kilishin tayi ba tare da ta sake cewa komai ba.

****Bayan fitar sa ne tana zaune da waya a hannun ta suna chatting sama-sama da Ya Maryam,rabin hankalin ta na kan Tv sai tana duba sakon lokaci zuwa lokaci, ta kira Abba bata same shi ba, kila ko ya fita ko kuma baya kusa da wayar. Kara wayarta tayi a tunanin ta Abban ne, sai taga number Ya Maryam ce, dauka tayi tana tashi zaune

“Ina ta magana a whatspp kin sauka, yanzu aka kira ni a gida Aunty Bilki ta haihu!”

” Dan Allah!” 

” Wallahi yanzun nan kuwa ta haihu.”

” Masha ALLAH, me aka samu?”

” Ina ma na tsaya tambaya? Murna ta saka ni kiranki, kinga al’amarin Allah, bayan ta cire rai, dama ba’a cire rai da  rahmar Allah.”

” Wallahi, kai Masha ALLAH, nayi murna sosai Allah ya bata lafiyar shayarwa.”

” Amin ya Allah, zuwa kano ya kamaki.”

” Gaskiya, dama yau zamu bar nan din, amma Abuja zamu wuce daga nan zamu dawo Kanon.”

” Ah shikenan ma, ki kirata toh kafin nan, bari na kira Amira itama na fesa mata.”

” Owk ki tura min number ta, Inaga kamar bani da ita yanzu.”

” Ok tam, zan ajiye miki a WhatsApp.”

” Yawwa.” 

Ajiye wayar tayi farin ciki na kamata, after all a karshe dai itama ta samu nata babyn, shekara ashirin da aure amma bata taba ko batan wata ba, sai yanzu Allah yayi, dama dai sunji kishin kishin din ciki ne da ita musamamn da bata zo bikin da akayi ba, sai mutane suka kara tabbatar da zargin su, boye labarin sukayi sun fi so kawai aji haihuwa daga sama. Duk da bata da yawan magana amma tana masifar son kananan yara, musamman jarirai zuwa 4years haka, ko magana sukayi sai taji dadi, shiyasa take son kaninta Marwan ba kuma tajin komai idan Mama ta sakata aikin sa.

   Daukar number aunty bilkin tayi, ta kirata tayi mata murna sosai, suna wayar kiran Abba ya shigo, ta katse na Aunty Bilkin ta daga nasa suka gaisa, anan yake fad’a mata labarin haihuwar ta nuna kamar bata sani ba tayi farin ciki sosai, bayan sun gama wayar ne ta kira Mamma take fad’a mata zuwan su, amma bata san ko a yau din zasu iso ba ko sai gobe dai, murna tana jiyo su Amaan ta wayar kamar zasu shigo ciki saboda karadin su.

   

***Tana idar da sallar la’asar sai gashi ya shigo, ba kayan da ya fita dasu bane a jikin sa, wasu ne daban da sukayi mata kama da sababbin da ba’a taba sakasu ba, gaishe shi tayi a ladabce tana daga kan sallayar, ya amsa yana zama, yanayin sa ya nuna a gajiye yake, sai ta tashi ta ninke sallayar ta ajiye ta nufi kitchen ta dauko masa ruwa da soft drink, akan tray ta doro ta dawo falon ta ajiye masa tana rissinawa, saurin tayata yayi yana hadawa da hannun ta da tray din, sukayi dariya a tare ta zauna a gefen sa tana zuba masa ruwan. Karba yayi yasha, sosai saboda tunda ya fita be saka komai a cikin sa ba, gashi sam baya jin yunwa so yake kawai su tafi.

“Ga abinci akan dinning ko na kawo maka nan?”

“Waye yayi?”

“Nice.” 

“Owk zanci, amma ki zubo min a plate ba da yawa ba, sai ki taimaka min da fruit please,.”

“Ok.” Ta mike bayan ta karbi cup din ruwan ta ajiye, taje ta zubo masa abincin ta kawo ta koma ta yanko fruits din ta kawo, yana kwance ya mike kafafunsa, har sai data zauna a gaban abincin sannan ya sakko yana saka spoon din a gaban sa ya soma cin abincin hankalin sa a kwance, sosai yaci dan beyi tunanin zai ci kamar haka ba, sannan ya sha fruits din kadan, bayan ya gama yace

“Thank you…Abincin yayi dadi.”

Blushing tayi cikin jin dadin yabon da yayi mata, ta hau tattare kayan zata kwashe ya rik’e mata hannu

“Ki barshi yaran chan zasu gyara idan mun tafi.”

“Ai ba wahala, bari na kwashe kawai.”

Sakin hannun nata yayi, ta dauki tray daya, cikin takun da bata san tana dashi ba, ta shiga takawa zuwa kitchen din, kallon ta yake har ta kule kafin ya dawo hayyacin sa, yana kallo ya sake dawowa ta kwashe sauran ya sake bin steps din nata da kalllo, ba zai iya hakura ba, musamamn idan ciki ya dauka, ga kuma abunka da sabon angon da be san ya isa ba, tashi yayi har da dan saurin sa, ya sameta a kitchen din tana tattare dattin plates din, sam bata ji shigowar sa ba, sai ji tayi an rungume ta, ta baya. Ta juyo a dan tsorace kafin kamshin turaren sa ya mamaye ilahirin kitchen din.

   Manne bayan su yayi waje daya, ya dora kansa saman gadon bayanta, ya shiga goga mata bayanta da kan nasa.

“Ba… Bari… Na karasa gyara kayan.”

“Barshi, ai dama ba aikinnki bane, ga aikin lada me yawa.”

Ya sake chusa kansa sosai, tsam ta dauke hannun ta, sanda taji hannun sa na yawo a daidai tsakiyar cikin ta, yana shafawa har zuwa kasan rigar ta, rik’e jikin kitchen cabinet din tayi dan ji tayi kamar zata fadi, Allah yaso ta dafe wajen. Daga ta yayi sama chak, ya wuce falon zuwa bedroom dinsu, ya dire ta yana mata murmushin mugunta,  a matukar tsorace take dashi amma kuma ba zata hanashi ba, dan ba zai taba bata damar da zata hanashin, yabi ya kanainayeta da salon kaunar shi me tsayawa a makoshi!

   Sai da suka bata lokaci sosai, dan har wani dan guntun bacci yayi bayan nan, da k’yar ta tashe shi yayi wanka ya shirya, suka fita a mota zuwa wajen Ammi, daga nan suka fice daga masarautar da magribar fari!

***

Tun bayan fitar sa bata tashi daga wajen da take ba, sai da taji yunwa na neman kai ta k’asa, ta tashi ta jawo ledar da ya bari ta cinye ragowar,tasha ruwa ta kwanta a wajen. 

   Har wajen takwas na dare Hajiyan bata dawo ba, turo dakin akayi, ta dago tana kallon sa, tashi tayi zaune da sauri tana kare jikin ta, murmushi yayi ya zauna a kusa da ita, ya ciro wayar sa a aljihu ya rik’e a hannun sa yace

“Zan kira miki Mama,dan ta kira tana son magana dake nace mata wayarki ce ta lalace, idan kika kuskura kika fad’a mata wani abu sai ranki ya baci.”

Banzan kallo tayi masa, ta warci wayar lokacin da taji tana ringing, bata jira Maman tayi magana ba ai tana jin ta daga ta rushe da kuka, 

“Lafiya Zeenat, wannan kukan fa?” Tace a kidime tana saka handsfree dan Habib yaji shima

“Mama dan Allah kice wa Abba yayi hakuri na tuba, dan Allah!”

” Ki nutsu ki fad’a min abinda yake faruwa, menene?”

” Bana son auren nan Mama, dan Allah kizo ki tafi dani wallahi zan mutu!”

” Mutuwa? Me yayi miki Bashir din?”

Shiru tayi ta rasa me zata ce, dan bata isa ta fadi abinda ya faru tsakanin ta da Bashir din ba, a sanyaye tace

” Mama yana da Mata, kullum sai ta sakani aikin wahala babu dare babu rana, ga tsangwama, karshe ma Mama a BQ nake wallahi.” Sai ta sake fashewa da wani kukan,salati Mama ta saka, ta kama zagaye a dakin tana jin bayanin Zeenat din

” Yana ina, bashi wayar.”

Tun kafin ta bashi ya karba yana mata murmushi,

” Hello Mama.”

” Kana ji? Wallahi tun muna shaida juna da kai ka dawo min da ‘yata, wannan ai wulakanci ne, wallahi ka dawo min da ita kafin kasha mamaki na.”

” Kiyi hakuri Mama, amma Zeenat matata ce,a yanzu nine nake da iko da ita,dan haka kiyi hakuri dai.”

” Kan bala’i, ni kake fadawa haka Bashir?”

” Ayi hakuri Mama, gaskiya ce, sai mun sake kira mu gaishe ki.”

Kafin ta sake magana ya kashe kiran, ya kuma kashe wayar gaba daya ya jefa ta aljihun sa, yayi gaba zai bar dakin ta chakumo shi ta baya

” Na rantse da Allah sai ka rabu dani,sai ka sake ni wallahi ba zan zauna ba, na tsane ka bana son ganin ka.”

Maganganun ta sun masa zafi kwarai, amma sai ya danne ya jawota ya hadata da bangon dakin, ya dalle mata baki sannan ya bi ta da kiss me zafi.

“Idan kika sake yi min ihu wallahi sai nayi fata-fata dake, aure na dake babu saki ko yaji, auren mutukaraba kenan, ko nace miki auren zobe, idan bakiyi wasa ba sai na tabbatar miki da haka a yau din nan, ta hanyar zuba miki ajiyar da baki isa ki guje min ba.”

Tofar da yawu tayi ta durkushe a wajen tana sakin kuka gwanin tausayi. Tsallake ta yayi, yayi ficewar sa yana dariyar mugunta, yana son Zeenat din da gaske, amma kuma ba zai dauki rashin kunyar ta ba, ko kuma ya kyale iyayenta su taka shi ba, sai abinda yaga dama zai yi da ita tun da dai shine me iko da ita a yanzu.

_ZAFAFA BIYAR 2022πŸ”₯_*

*_NANA HAFSAT(MISS XOXO) s_*

_SO DA ZUCIYA_

*_SAFIYYA HUGUMA_*

_DABI’AR ZUCIYA_

*_MAMUH GEE_*

_DEEN MARSHALL_

*_HAFSAT RANO_*

_HALIN GIRMA_

*_BILLYN ABDULL_*

_TAKUN SAKA_

*_Zaku biya kudin wainnan daddadan labaran Kamar haka_*πŸ‘‡πŸ‘‡

D’aya 300

Biyu 400

Uku 500

Hudu 700

Biyar 1k

*_Zaku tura kudin a_*

6019473875

*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*

*keystone bank*

*Sai shedar payment dinki a*πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

08184017082

*Kokuma katin waya na MTN anan*πŸ‘‡πŸ‘‡

09134848107

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like