SULTAN 15-16

Advertisement

 

👑 *S U L T A A N

Mss Flower

*FITATTU HUƊU🔥_RESEMBLANCE OR SIMILARITIES OF STORY/LIFESTYLE SHOULD BE CONSIDERED AS TOTAL COINCIDENCE_

*FIRST CLASS WRITERS ASSO…*

Advertisements

           *15-16*

Ƙoƙarin tura min ƙarfen, rintse idona na yi ina jin wani irin ƙuna a zuciyata, na yi kaico da rashin jin maganar Amma da Abbu, da ban rasa gatana ba, da ban rasa su ba, ni da nake rayuwa kamar Princess sai ga shi ana treating ɗina as if I’m an animal.

“Hindu!” Muryar Kala ta karaɗe ɗakin cikin karaji, buɗe idona na yi. A zabure Hindu ta miƙe bayan ta saka rigarta tana zare idanu

Advertisements

Cikin fushi Kala ta ƙaraso tare da wanke fuskarta da mari ta ce “kina hauka ne?, She is someone’s personal maid ba taki ba, ba kuma home servant ba, how cud you treat her this way?”

Dafe wajen ta yi ƙwalla ta ɗigo mata ta ce “Kala kika mareni akan baiwa?” 

“She isn’t a slave, and bari na tabbatar miki duk ranar da kika kuskura kika kuma neman wannan yarinyar sai na faɗawa mahaifinki irin iskancin da kike yi”

“Then i will make her life a living hell!” Ta ce tana hissing. 

“Loose her!” Kala ta ba da umarni, take ƴammatan suka kwanceni, wani irin masifaffen daɗi na ji har raina, amma bn san dalili ba zahiri sai na fashe da kuka. Kala ta kama hannuna tare da cewa “ya isa haka, saka kayanki mu je” 

Wani mugun kallo Hindu ke bi na da shi irin na za ki ci ubanki, hakan ya sa na sadda kaina ƙasa na shirya sannan na bi bayan Kala. Sashenta muka wuce, inda ta bani haƙuri kan abin da Hindu ta min sannan ta kuma jadadda min kula da Prince ɗin da nake jinya, maganarta da ta ɗauren kai ta ce “ban lamunci ki sanar da kowa sirrinsa ba, walau na cuta ko lafiyarsa, daga shi sai wanda y haliccesa, ba shi da masoya, shi ɗin tamkar ɗanyen nama ne ja a tsakiyar namun daji, kowa farautarsa yake, ki tayani kula da shi har lokacin da zai samu lafiya” 

Jikina duk ya yi sanyi amma na gyaɗa kai tare da cewa “zan ba shi kariya da dukkan iyawa ta” 

“Ya yi!, Akwai taron cin abinci da dukkan ahalin za su yi a yau, ga kayanku can da za ku saka, in lokaci ya yi za a zo ɗaukarku” ta ce 

“To!” Na ce a taƙaice sannan na tattara kayan na nufi sashenmu. 

Misalin bakwai da rabi mun gama shiryawa, sosai ya yi wani mugun kyau sai fitinannen ƙamshin turare yake, sumar kan shi ta yi lufff wadda ta sha gyara, fararen kaya ne a jikinsa wani tsadadden silk yadi mai adon silver touches, ya yi masifar kyau tamkar wani zane, yana zaune kan wooden stool da ke harabar gidan idanunsa na kallon tsuntsaye da ke ta shawagi a bishiyun da suka wa wajen ƙawanya, murmushi na saki tare da ƙarasawa inda yake don ni ma na shirya cikin wata silk white gown da ta tsaya min iya cinya, na kuma gyara baƙin gashina da ya sauka har kan mazaunai na, na yi kyau matuƙa ni kaina na sani, zama na yi a gefensa tare da riƙe hannunsa na ce ” Kala ta ce in ka je ka tabbatar ka gaida mahaifinka” 

Ɗago kai ya yi ya ƙura min ido, sai kuma ya ɗauke kansa. Muna nan zaune sai ga Prince Wahid cikin shiga shi ma ta fararen kaya tas, da murmushi na miƙe. Shi ma murmushin yake har ya ƙaraso inda muke. Bayan mun gaisa ya ware tafin hannunsa wata white stone necklace ta bayyana

“Wow!” Na furta tsananin kyawunta

“Do you like it?” Ya tambaya da slight smile da bai yankewa a fuskarsa

“Sure! It’s beautiful” na ce cike da jindaɗi, turning ɗina ya yi tare da placing sarƙar a wuyana, sannan ya juyo da ni idanunmu cikin na juna ya ce “you look gorgeous!”, I couldn’t help but blush sannan na yi mumbling “thanks!” 

Bai ce komai ba sai ya matso kusa da ni sosai tare da pecking goshina cikin raɗa da wata iriyar murya ya ce “see you later!” 

Bin sa nake da kallo ina jin wani irin yanayi na sauko min, daidai nan carriage ɗin da za ta kai mu ta iso, juyawa na yi tare da nufarsa ina cewa “taho mu tafi” 

Kansa sauke a ƙasa duk maganar da na yi bai tankani ba, hakan ya sa na ɗan kama sa ina ƙoƙarin tada shi, janye hannunsa ya yi sannan ya ɗago ya min wani irin mugun kallo, gabana ne ya faɗi don ban taɓa ganin hakan daga garesa ba, sai na yi tsaye duk na kasa kataɓus, ganin mun jima kuma alamu mai carriage ɗin ya matsu na ce cikin sanyi “don Allah ka tashi mu je” 

Miƙewa ya yi ya nufi carriage ɗin tare da shiga, bai ko kalleni ba, wani irin kwarjini da zatinsa suka cikani, ban san dalilinsa na aikata hakan ba amma duk sai na rasa sukuni, mutumin da yake tamkar jariri a wajena, yau sai ya koma min zaki. Har muka ƙarasa na kasa gane yanayinsa, kana ganinsa ka san babu walwala a tare da shi haka ba za ka ce yana cikin ɓacin rai ba. Ko da muka shiga ƙaton teburin ya cika da jama’a, wasu na sansu wasu ban sansu ba, yayin da kowanne maid ɗinsa na tsaye a kansa yana serving ɗinsa, da hanzari na ja mai kujera ina sunkuyar da kaina alamun gaisuwa, ya samu waje ya zauna batare da ya tanka kowa a cikinsu ba. 

“Ko mahaifinka ba za ka gaida ba?” Cewar wata dattijuwar mata. 

Bai ko ɗaga kai ya kalleta ba, hakan ya sa Kala da sauri ta ce “ai bai da lafiya, watarana har hira zai yi da shi da yardar Allah” 

Mahaifinsa mai matuƙar kama da shi ya yi murmushi ya ce “in sha Allah!, Ina tunanin shelantasa a matsayin magajina tun da Wahid shi ya gaji kasuwancina, shi kuma Aswad bature ne”

“Ba zai yiwu ba, ya za ka ɗau sarauta ka ce ka ba wa wannan mahaukacin, duk faɗin alƙaryar nan wane bai aminta da Wahid a matsayin magajinka ba, sai yanzu out of nowhere daga bayyanar wannan ka ce magajinka, sam ba zai yiwu ba!” Cewar wannan dattijuwar wadda nake tunani maman Wahid ce 

“Tabbas! Ka dai duba wannan maganar Yaya” cewar wata mata da itama nake tunanin Aunt ɗin su ce 

“Ke ce mahaukaciya, ke ba ki da lalura ba, ko yau Allah na iya ba shi lafiya kuma rass zai yi mulki cikin aminci don ko ba komai bai tsotsi baƙin nononki mai tsatsa ba” cewar Kala a fusace 

” In har kuwa ina da rai wannan tsintaccen mahaukacin ba zai yi mulki ba, wa ya sani ma ko ba ɗa ba ne a masarautar nan, kawai ki kawo mana gansamemen ƙato daga sama ki ce shi zai yi sarauta, na san ra’ayinki ne wannan ba na mai martaba ba don na san bai da magajin da ya wuce Wahid a ransa!” 

“Ke!” Cewar Kala a fusace 

“E! Na faɗa” ta ce tana miƙewa cike da ɓacin rai 

Da hanzari ya dafe kansa yana jujjuya kan alamun ya gaji da hayaniyar ko kansa na ciwo, hakan ya sa na ɗan matsa tare da cewa “me ya sameka?” 

“Kaina!” Ya furta a karo na farko can ƙasan murya cikin wani irin yanayi. 

Wani masifaffen daɗi ya kamani na shiga wage baki har na manta da complain ɗin da ya yi na ce “me ka ce?” Ina son ƙara tabbatarwa. 

“Kaina!” Ya ce cikin wani irin sanyi, Kala da ke gefensa tana ruwan masifa ta waiwayo ta kallesa, sai kuma ta dubeni ta ce “je ki da shi, kar mugayen nan da ke mai fatan mutuwa su tarwatsa mai kai yana jinya, ku je!” 

Hannu na sa na kama shi ina ƙoƙarin ɗagasa ya yakice hannunsa daga nawa ya yi gaba. Yanda muka zo haka muka koma babu fuska a wajensa ko kaɗan, muna isa na ɗora mai ruwan wanka, ɗakinsa na koma na zauna sai dai fuskar da ya min mugun kwarjini ya yi min na kasa zuwa wajensa sai na koma can nesa na zauna ina satar kallonsa, can na ce “kan naka ya yi sauƙi?” 

Ya ɗago fararen idanunsa ya sauke a kaina sai ya watsar ya maida dubansa ƙasa, jikina ya yi mugun sanyi, duk rashin jin daɗi sai ya kamani, haka na tashi na je na kawo mai ruwan wankan, bai nemi taimakona ba ya cire kayansa ya nufi bathroom ɗin, haka da ya fito a karon farko ya buɗe ma’ajiyar kayansa ya ɗauko ya saka. 

Ina nan zaune kamar gunki mamakin mugun sauyinsa duk ya cikani ya haye gado ya kwanta, sai nai kamar an dasani zuciyata duk babu daɗi, jiki a mace na tashi na koma nawa ɗakin, duk yadda na so na rintsa abun gagara ya yi, duk tunanin me na aikata masa da zafi haka ya hana min sukuni. Washegari ko da na tashi da wuri na kammala girki na kai mai ruwan wanka, zaune na tadda shi jikin gado idanunsa a lumshe

“Ga ruwan wanka” na ce ina kallonsa, tashi ya yi ya shiga bathroom ɗin ba tare da ya tankani ba, ko kafin ya fito na shirya masa abinci, shiryawa ya yi cikin wani coffee and black soft clothes wanda suka yi mai matuƙar kyau, ina ta satar kallonsa don gani nake kamar an canza min shi, zama ya yi hakan ya sa na zauna a gefensa na zuba mai abinci, bai yi alamun ci ba hakan ya sa na ɗebo na kai bakinsa, mugun kallon da ya yi min ne ya sa na sauke jikina ya ɗauki rawa, a hankali na ce ” me na yi maka ne?” 

Ɗago dara-daran idanunsa ya yi ya sauke a kaina sai ya taɓe baki tare da ƙoƙarin miƙewa, duk yadda na so na jure sai na kasa kawai na fashe da kuka, a hankali ya dawo tare da tsugunnawa ya ɗago haɓata ya tsurawa fuskata ido da hawaye ke ta faman bi, ido cikin ido muke kallon juna yayin da hawayena ke ta zaryarsu, hannunsa ya sa ya shiga share min. A hankali na ce “me na yi maka?” 

Lumshe idanunsa ya yi tare da waresu a kaina sai ya ɗan langaɓar da kansa tare da kama hannuna ya shiga musu wani irin murzawa, sosai na fara fita daga hayyacina don ji nake wani masifaffen yanayi na saukar min, cikin kasala na kallesa na ce “me ya sa kake fushi?” 

Bakina ya tsurawa ido tamkar yana kallon majigi, ban yi aune ba na ji saukar tattausan lips ɗinsa saman nawa, a hankali ya shiga tsotsa tamkar ya samu sweet kafin ya janye don kansa, idanunsa sun ɗan canza yanayi sun cika da sha’awa ya kalleni, sai kuma ya ɗauke kai gami da tashi, wani irin shock da ya kamani har ya koma gado bai sakeni ba, na yi kiss har ban san adadinsu ba, but na shi is so special duk jikina ya mutu and I’m hoping for more, sosai kiss ɗin nasa ya shigeni ya karya duk wani kuzari na jikina, zuciyata ce ta shiga ingizani na…

*INA GAF DA RUFE FREE PAGE, LET’S WALK THROUGH THIS JOURNEY TOGETHER, DON ALLAH KAR KU BARI WANNAN LAGWADAR LABARIN MAI CIKE DA ZAZZAFAR SOYAYYA MAI TSUMA ZUKATA DA SANYA NISHAƊI HAKA DA ZALLAR… YA WUCE KU, KI YI SUBSCRIBING DAIDAI ƘARFINKI*

*🔥FITATTU HUƊU🔥*

      

*👑SULTAAN* # Nml grp ~N~ 300 vip ~N~ 500 via 1401611541 Access bank, shaidar biyanki ta wannan numbern 08167888934

*Mss Flower🌸*

TSINTACCIYA

Nimcyluv

Baƙar fata

Autar manya

DATTIJON ARZIƘI

Real ladingo

Gaba ɗaya 800

Via 6850917335 Na’ima Shu’aibu Sulaiman Fidelity Bank, masu tura kati 08167888934 ga ƴan uwa na Niger +22796515805 za ku tuntuɓa. To show evidence of payment 08142105218

*Mss Flower🌸 08167888934* For more information😇

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

YAU DA GOBE 27&28

Advertisement   🅿️27&28 …..wani irin zabura tayi had’e da k’ok’arin turesa….amma takasa k’arfi ba d’aya ba. Gogan kuwa baya…