TAKUN SAAKA 38

Advertisement

 

*_Chapter Thirty Eight_*

……….Tsabar firgita batasan ta wantsalo da ga jikinsa zuwa ƙasan carpet ba. Ta kalla mask ɗin hannunta ta dubesa har kusan sau uku tamkar wadda kwalwar kanta ke neman juyewa. Kanta ta shiga ɗan girgizawa zuciyarta na sake tabbatar mata ba abinda take tunanin bane ba. Tabbas da wani salon yaudarar ya sake shirya zo mata kuma. Yayi amfanine da face ɗin Yaya Isma’il tamkar yanda yakeyi da wasu a baya.

       Cikin rawar murya da hawayen da ke sakko mata ta fara magana tana dubansa, duk da ya tsume fuska tamkar bai damu da a yanda ta gansan ba. Kamar zatai magana sai kuma ta miƙe tana jefar da mask ɗin da ja baya. “Amfani da fuskar Yaya Isma’il domin badda kama bashike  nufin zaka samu daraja irin tasa da ga gareni ba ko ga iyayena. Kabar yaudarar kanka Muhibbat Aliyu Gwarzo bazata taɓa amincewa rayuwar aure da kai ba koda mazan duniya sun ƙare. Idan kuma kai amfani da fuskarsa ka aikata wani laifin na rantse da ALLAH bazan yafe maka ba, koda zan rasa raina a wannan gaɓar bazan barkaba, bazan barkaba…….”

     Kuka ya sarƙeta ta kasa cigaba da maganar, da gudu tabar wajen dan ji take tamkar falon na juya mata ma. Master da gaba ɗaya bama ya fahimtar zancen nata saboda wani ruɗaɗɗen al’amari dake ratsa jinin jikinsa zuwa kwanya ya cije lip ɗinsa na sama da ƙarfi, dan wani irin mahaukacin murɗa masa mararsa tayi a yanayin da bai taɓa fuskanta ba a rayuwarsa. Tabbas yanajin sha’awa da buƙatar mace batun yanzu ba, amma na yau ko yace yanzun nan dabanne dana ko yaushe. Dan tunda ya kammala shan tea ɗin nan dama yakejin jikinsa tamkar yana canjawa. Bai kawo komai a ransa ba da farko sai tunanin murar dake nuƙurkusarsa ce kawai. Sake ƙullewa cikin yay har yana jan numfashi a fisge zuciyarsa na wani bugu da sauri-sauri. Duk yanda yaso nuna jarumta da juriya ko tunanin daga ina matsalar take hakan ya gagara. Babu shiri ya rarumi waya ya fara neman number Abdull kuma amininsa ɗaya tal a duniya….

       Hibbah kam koda ta afka bedroom saman gado ta faɗa tana fashewa da sabon kuka mai tsuma rai.

      “Nashiga uku ni Muhhibat wace irin *MAKAUNIYAR ƘADDARA* ce haka ta kutso rayuwata?. Wane irin mutumne wannan da sam baka gane gabansa balle baya. Ya ALLAH ka kubutar da ni daga mutumin nan kozan samu ƴancin rayuwa daga shu’umcinsa. Kai yau duk ma yanda za’ai dolene na bar gidan nan”.

     Ta faɗa tana mikewa zumbur tamkar wadda aka tsikara. Ɗankwalin jallabiyarta da yay gefe ta ɗauka ta naɗa a kanta tana share hawayen da suke ziraro mata. Yau fa koma minene zai faru sai dai ya faru saita rabu da mutanen nan kafin su salwantar mata da rayuwar ahalinta da ita kanta. Wadrobe ta buɗe ta ɗaukko hijjab ɗin da ita kanta batasan ina ya samosa ba tana cije baki saboda wani irin kartawa da mararta tai mata a karon farko. A dai-dai nan ya shigo bedroom ɗin waya a kunnensa alamar magana yake da Abdull haryanzun cikin kamar fitar hayyaci, a kuma real Isma’il ɗin sa. Kasancewar yana gab da isowa gareta ita kuma ta juyo sukaci karo. Baya tai ƙoƙarin ja ya riƙo hijjabin hannunta. Koda taja taji bazata iya ba sai ta sakar masa kawai. Shima hijjab ɗin ya saki ya riƙota, nan ma turesa ta shigayi da iya ƙarfinta tana kuka, sai dai ko gezau baiyiba duk da tsuma da jikinsa keyi, sai ma mannata da yay da jikin nasa sosai yana cigaba da amsa wayarsa tamkar zai karya mata ƙasusuwa. Kuka mai cin rai ta sake sakar masa da kaima hannunsa cizo saboda jin azabar riƙon da yay mata.

        Duk da yaga abinda take da niyyar yi bai saketa ba, saukar hakwaranta kan fatar hannunsa ta sakashi rumtse idanun da ƙarfi har yana janye wayar da ga kunnensa ya katse kiran…..

Advertisements

         “Ouch!”. Ya faɗa da janye hannunsa a ɗan zafafe saboda yanda cizon yay masifar ratsa masa jiki ga azabar da ke neman kiɗima rayuwarsa. Sam baiyi tunanin zatai cizon da bakar mugunta bane irin haka shiyyasa ya barta. Barin jikin nasa tai da sauri ya sake fisgota cikin fara ficewar hayyaci. Shi kansa zuwa yanzu ya tabbatar akwai matsala, dan ji yake inhar bai kasance da mace ba zai iya rasa ransa ma.

          Ita kanta Hibbah baƙon al’amarin dake ratsa magudanar jininta ne ke neman saka hankalinta gushewa gaba ɗaya, tama rasa ina zata tsoma ranta taji sanyi da wannan yanayi mai rikita tunani. Wani irin mahaukacin cikuykuyesa tai tana fashewa da kuka, taringa jujjuya kanta bisa ƙirjinsa jikinta na wani irin kakkarwa sai cije baki take. Cikin sake ficewa da ga hayyacinsa saboda rungumar da tai masa, ga yanda take juya kanta a ƙirjinsa ya sashi faɗawa da ita saman gadon yana rufe mata bakin ruf da nasa, dan kukan nata wani irin tunzura fitinarsa take zuwa gareta..

         Da zafi-zafi yake cuɗata tako ina har shi kansa baisan mima yake ba. Dan ɗan haɗin kan da take bashi cikin gushewar nata hankalinne ke sake harmutsa tunaninsa da gigita dukkan jarumtarsa. Canjawar salon wasan ne ya saka Hibbah fara turesa ta fisge bakinta, tanada ilimin addini tasan minene ma’anar addu’ar da yake karantowa, cikin karkarwar jiki da jujjuya masa kanta tana sake sakin wahalallen kuka ta hau roƙonsa da magiya. 

       “Dan ALLAH kar kayi bana so. Na tuba Yayana, wlhy na haƙura bazan sake cewa zan tafi ba har sai ka yarda. kaimin rai, ka dubi maraicina karka ruguzamin rayuwa”.

     Kansa ya shiga juya mata shima yana sake riƙota. Yanda idanunsa ke sake canja kala sak na bahagon zaki ya sake sakata fashe masa da kuka, gashi ita tunaninta facemask yasa dan ya yaudareta da fuskar Isma’il. Sake turata yay cikin jikinsa, da wata irin muryar da batasan a wanne fanni ko rukini zata sakata ba ya fara mata magana cikin kunne. “Uhm-uhm Hibbaty, kiji tausayin Yaya Isma’il ɗinki karya m…u…tu”.

    Ya kai karshen maganar da ƙyar yana kamo hannunta ya ɗaura a jikinsa da yakejin tamkar an ɗaura dutsi mai zafi dan azaba. Gaba ɗaya sai ta sake ruɗewa. Tai azamar jan hannunta baya ya sake damƙewa. Duk yanda yaso magana bakinsa ta cigaba da fita hakan ya gagara. Itama ya hanata cigaba da roƙonsa dan yasan bazai iya mata alfarmar da take buƙatar ba a wannan halin. 

        Tun Hibbah na tunanin samun alfarma da ga garesa harta fidda rai, ta fara kwala kiran sunan Ummi da su Yaya Muhammad suzo su taimaketa, daga ƙarshe ma sai kukan ya gagareta balle neman samun ceto, tun tana fahimtar mi duniyar ke a ciki har komai ya koma ɗiff a cikin kunnuwanta da idanunta…

            __★★★__    

       A yayinda Master ke can yana angwancewa da gwangwaje sadakinsa da ranar ALLAH anan hukumomin jami’an tsaron jihar ne gaba ɗaya sukai zaman meeting akansa da yanda zasu ɓulloma al’amarinsa. Dan video ɗin daya saki a safiyar ta yau ba karamin tsaya musu yay a rai da zuciya ba. Tsare-tsare suke na tashin hankali da taimakon su A.G da suke iƙirarin sanin sirrinsa a baɗini, a zahiri kuwa suna nuna cewar ƙwazon aiki ne ya sakasu jajircewa da son ganin iyalansu sun dawo hannunsu. Dan a cikinsu iyalan Abba ne kawai ba’a ɗiba ba. Sai dai yanda Abban keta surutai tamkar zararre yana neman buɗe musu sirrika yasa A.G aika amintattun yaransa wai su bama su Abban tsaro saboda kar Master ya bibiyesu. Da wannan damar sukai amfani wajan sakawa a ɗirka masa allurar barci danya samu hutu. acewarsu jininsa yayi sama. 

       Abbah dake a birkice ya sake rikice musu akan shi baya buƙatar kowa tare da shi, kuma lafiyarsa lau doctor bai isa yay masa allura ba shi kawai su kira masa Master ya bashi kuɗinsa. Su Hajiya mama da basu fahimci ainahin alaƙar Abban da Master ɗin ba tuni suka sake aminta Abban ya zare da gaske. Dan haka suka bada goyon bayan ai masa allurar musamman ma da ƙafarsa mai karaya ta sake gocewa.

Advertisements

       A ɓangaren su Alhajin Mande kuwa duk da ƴan jaridu sun ishesu da yawan tambayoyi musamman akan sakin videon Master harma da jami’an tsaro yasasu killace kansu waje na musamman sunata tattaunawa akan al’amarin na master mai matuƙar ban mamaki da firgici. Duk abinda A.G keyi kuwa da yawunsu. Sun bada ɓoyayyun sirrika na inda Master ke zama wa jami’an tsaro cikin ɓaddabamin cewar binciken su A.G ne ya gano hakan.

        Bayan kammala meeting jami’an suka rarraba kawunansu a hanyoyin da duk ake tunanin za’a iya kama master, tare da bin diddigin abubuwansa da dama da su A.G ɗin suke tunanin sun sani…..

★★★★★★★

       Ba ƙaramin azaba Hibbah taci a hannun master ba, tayi kuka har muryarta ya dishe, tun tana gane da yaren da yake tare da ita harta bar fahimtarsa komai ta koma a halin gushewar ji da gani harma da ɗaukewar numfashi. bama ita ba shi kansa ya jigatu dan sam hankalinsa baya tare da shi, baima san a yanda ya wajiga rayuwar Hibbah ɗin ba sai da ya cimma burin abinda bai taɓa tunanin amsa ba a yanzu, kodan halin mutuniyar tasa. Babu abinda yake sai sauke ajiyar zuciya a jajjere, a karon farko na rayuwarsa ya mallaki abu mai daraja da ada sam baya sakashi a lissafinsa. Bai taɓa tunanin zaiyi aure nan kusa a rayuwarsa ba, sai gashi Hibbah ta canja dukkan lissafinsa. Ita ɗin ta zama ta musamman, a lokaci na musamman, ga ahali na musamman da suka kutso cikin ƙaddararsa ta dalilinta. Sake rungumota yay jikinsa da kyau ganin yanda jikinta ke karkarwa haƙoranta na haɗuwa waje guda tamkar maijin sanyi, ji yake tamkar ya tsaga fatarsa ya tura ciki. Cikin dasashshiyar muryarsa mai gauraye da mura da azabar wahalar da yasha kafin mallakarta yake magana a kunnenta hawayenta masu ɗumi na sauka bisa ƙirjinsa, “I’m sorry autan Ummi, ki yafema yaya isma’il ɗinki uhyim”. 

         Duk da halin da take a ciki na azabar raɗaɗi da jigata ga tashin hankali da tsananin damuwar rabata da budurcinta da yay sai da taji zuciyarta ta tsarga jin ya ambaci kansa da Isma’il. Tana son ɗagowa ta sake kallonsa dan tabbatarwa tsananin kunya da jigata ta hanata hakan. Sai wasu hawaye ne masu ɗumi da suka sake ziraromata suna sauka a kan jikinsa. Idanunsa dake a rufe ya buɗe a hankali jin sabbin ɗumin hawayen nata. Yay ƙoƙarin ɗago kanta dake a jikinsa amma taƙi yarda. Rashin ƙarfin dake tattare da jikinta ya bashi damar ɗagotan duk da shima jikin nasa babu ƙarfi ga shi da ciwuka ga mura. Fuskarta kawai ya tsurama idanunsa yana kallon yanda take shaƙar zuciya tamkar zata suƙe. Ga idanunta da ke rufe duk sun kumbura. Hannunta ya kamo ya ɗaura akan fuskarsa ya danne da nasa batare da yace komai ba. Sai dai har ƙarƙashin zuciyarsa yanajin kukanta na sukarsa. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali tare da sumbatar goshinta da hancinta ya dire laɓɓansa saman nata da sukaci matuƙar wahala a hannunsa sai zogi suke mata. 

       Sabuwar rawa jikinta ya ɗauka. Ta fashe masa da kuka tana mutsu-mutsun son matsawa da ga jikinsa. Dan duk zatonta zai sake ne kuma. Tausayinta da dariya suka riskesa a lokaci guda. Amma sai yadake baiyiba ya cigaba da abinda yakeyi dan kawai yaga yazatayi.

          Ganin yanda take juya kai da son ja baya ne ya sashi sakin bakin nata. Tanaji an saketa ta saki kukan da take riƙewa mai sauti. Cikin wahalalliyar murya ta fara roƙonsa. “Dan ALLAH, dan ALLAH kayi haƙuri wlhy zan mutu, ka kaini wajen Ummina”.

     Cikin ɗan murmushin daya kufce masa babu shiri, da disashshiyar muryarsa ya ce, “Sai naga kin daina rashin ji”. Yay maganar yana son tashi ya ɗan ranƙwafo kanta yanda yake iya ganin fuskarta data juyar da kyau.  Ganin yanda taja bargo ta rufe har fuskartane ya sashi sake sakin murmushin. Sauka yay a gadon cikin dauriyar rashin ƙarfin jiki dan har lokacin sallar azhar ya gota sosai. Toilet ya nufa kai tsaye, ya gyara jikinsa a gurguje ya fito. Shashashar kukan Hibbah da ke tashi a hankali a ɗakin ya bashi tabbacin kuka take har yanzun. Yafasan yau ya taɓoma kansa jangwam, dama yaya lafiyar giwa.

         Jallabiya ya zura a jikinsa kawai ya ɗan saka turare ya tada salla yana kauda tunanin dake ta masa kai kawo a rai tun bayan samun kansa da ga shan shayi. Lallai yau sai yaci ƙaniyar su Habib gwargwadon iko dan baya raba ɗayan biyu wani abu suka zuba a shayin daya kawo masa. Shidai lafiyar ALLAH ya tashi duk da kuwa a shekarunsa ya jima yana bukatar abokiyar halittarsa. Sai dai shi mutum ne da hidimomin kansa kansa ya kasance busy har damuwar bata tasiri mai nisa a garesa. Yana kuma ƙoƙarin ganin ya kiyaye idanunsa da kunnuwansa da ga dukkan abinda zai iya motsa masa sha’awa. Idan kuma yaji ya takura sosai ko baida aikinyi sai ya ƙirkirarma kansa dan gudun faɗawa tarkon saɓon ALLAH. 

     Sallarsa ya gabatar a nutse bayan ya tattara tunanin ya tureshi gefe. Koda ya idar zaune yay a wajen yana addu’a da jiran lokacin sallar la’asar ya ƙarasa dan yaji Hibbah shiru da alama barcin wahala ya ɗauketa. Kansa na masa ciwo sosai, harma yanajin wani zazzaɓi tare da shi, ga jikinsa sam babu wani ƙarfi zuwa yanzun, har ɗan jiri-jiri yakeji cikin idanunsa amma duk ya dake ya shanye dan yasan Hibbah duk ta ninka wannan wahalar tasa. Duk da rakin da taketa masa yaga dauriyarta, a yanda ya rutsatan ba cikin hayyacin nan nasa ba. 

        Koda lokacin sallar la’asar ɗin ma ya karasa a ɗakin yayita. Dan baya buƙatar su Habib su gansa a haka. Tunanin ta yanda zai bama Hibbah taimako ne ya sashi ture hukuncin da yake shiryama su Habib ɗin a ransa. Ganin ya rasa mizai hasaso ya sakashi tashi cikin dauriya ya koma bakin gadon ya zauna. Wayarsa da baisan a ina take ba ya shiga duddubawa a gadon. Da ƙyar ya samota ta shige tsakanin jikin gado da katifa. Sai da yay ɗan shiru alamar tunanin ta ina zai fara saboda sanin halin iya shegen aminin nasa. Bazai sake kirasa ba. dan yasan a muryarsa kaɗai zai iya gano halin da yake ciki tunda shiɗin ba kanwar lasa bane, ɗazun ma ba karamin sheri yay masa ba, dan shi ya fargar da shi cewar kodai wani abu yasha ma. Sanin iya shegen Abdull ɗin ne ya sashi yanke hukuncin tura masa massege kawai.

       Yana tura saƙon ya matsa kusa da fuskar Hibbah ya janye bargon. Sosai jikinta yay masifar ɗaukar zafi har numfashinta kansa ya canja alamar akwai damuwa. Duk da shima jikin nasa akwai zazzaɓi sai ya samu nata ya shanye nasan dan zafi sosai. Shigowar saƙo ya sashi janye hannunsa dake a saman goshinta ya ɗauka ya duba. Abdull ɗinne kuwa tamkar yanda yay hasashe sai dai tambayar daya turo masa ta shaƙiyanci maimakon amsar daya nema ta sakashi jan tsaki yana harar wayar tamkar Abdull ɗinne a gabansa.

          “Kaifa shashasha ne ka bani amsa kawai ina bukata da gaggawa”.

      Yana turawa ya sake ajiye wayar ya ɗago Hibbah da barcin wahala ya ɗauka. A firgice ta farka saboda barcin ya dauketa ne dama a tsorace. Taɗan zabura zata ƙwace jikinta ga azaba na cinta. “Dan ALLAH…..”

      “Shiiii!!” yau saurin katseta yana ɗaura yatsansa akan laɓɓanta. Badan ta gamsu ba tai shirun amma taƙi yarda ta buɗe idanunta sam. Dan ko kallon fuskarsa bata bukatar yi. Bakinta ya mutune gaba ɗaya dan anfi ƙarfinta. Dan tunda take da shi bata taɓa jin tsananin tsoronsa da shayinsa a cikin ranta ba kamar yau. Ko tashin hankalin jiya gani take ya ninka na yau jefata a matsanancin tsoron san. Babban burinta kawai taga Ummi, dan bata raba ɗayan biyu mutuwa zatai kawai. Ko a mafarki bata taɓa cin karo da kalar azabar da bawan ALLAHn nan ya shayar da ita ba a yau. Ya gama dasa mata ciwo da takaici da tsanarsa a ranta fiye da farko. Yayi amfani da face ɗin Yaya Isma’il domin yaudararta. Ya kuma jigata rayuwarta ta hanyar da bata taɓa kawowa a ranta ba. Ya rabata da mutuncinta (Ya ALLAH ka sakamin, idan ni yafi ƙarfina kai nasan bazaifi ƙarfinka ba)…………✍

       

*_Saura inji wani yace banyi posting ba jiya😖😖😏🚶🏻_*

_______________________

Hi team no makeup

Ina kanawa mutanena🗣️

Shin Ina masoyan mg’s ina ma’abota ado da kwalliya kusaurara kuji dame nazomuku 💃

Nasan dayawa kunsiya kayanmu Kuma kunshaida yadda suke gyaranjiki cikin lokaci kalilan Koda iyasabulun kikayi anfani dashi sekinyaba balle kankat wato beauty kit dinmu toh inamaitabbatar muku cewa ynx kayanmu ankaramasu kayayyaki Wanda zasu Kara gyara fata fiye da tsammanin Mai tunani within 2weeks zakicanza kiga duk inda kikayi se anbiki d👀 domin ynd fatanki zaikoma Shar kamar madara bawanda zemiki kallo daya yadauke idanunshi😃😍

Hajiyata shin menene matsalanki, pimples ne?

Spot? sunburn,acne, stretch marks, knuckle, wrinkles, Black head,ko kinshafa Maine yabatamiki jiki

Inamai shaidamiki cewa ynx ne lokacin dayakamata kiyake dukkan wadannan kema kidinga fita sakayau abunki baruwanki da kunshe fuska ko kice sekinyi makeup hjy fita zar abunki kinuna ainihin natural beauty dinki😍domin kayanmu gbdynsu organic ne babuna bleaching zssu sa ki haskaka fatarki tayi ta kyalli kamar madubi ze fiddomiki d ainihin natural beauty dinki ne😘kunaji barin fadamuku wani Abu billah wannan prdcts damuke dashi ynx Koda kudinki seda rabanki domin duk sunzarce nabaya ankaramasu abubuwa dayawa masu matukar anfani agyaran fata🤗Ina Wanda basasan shafa Mai koda sabulun kawai kike anfani dashi inamai tabbatar Miki zkg ynd jikinki zekoma luwai luwai😘

Soap:3k

Beauty kit:12k

Chat:08062991549

07066210195

Call :07046881166

08064532391

Instagram:glow_with_mgs

Facebook:mg’s skincare

amare inakara shaidamuku duk wacce tayi anfani d kayanmu Bata bukatar gyaranjiki sedai ra’ayi🥰

Masoya kunanan kauna yanda nakwashe aljihu domin nafarantamuku kuyi achieving goal dinku pls Nima kunanan kauna kufarantamin😪🤠aljihuna yafarfado hilis karnakoma kauyenmu🥲 

Yar shawarmannan duk nasaba😤 hilis kugarzayo arabani da kaya🤝

Nd guest what🤩

Duk Wanda yy siya 10k zuwa sama zesamu Karin gift😃

Pamper your skin🧖‍♀️

Shine like a bride👰🏻

Glow🧚🏻‍♀️.

_________________________

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

 

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like