TAKUN SAAKA 45

Advertisement

 *_Chapter Forty Five_*

  ………..Tunda suka fara tafiya duk sanda Hibbah zata ɗago sai taga idon Master a kanta. Dole ta tilastama kanta daina kallon nasa ta koma sauraren hirarsa shi da Abdull dan wata sabuwar kunya yake sake haddasa mata. Sai idan Abdull ɗin ya ɗan tsokaneta ne takanyi murmushi kawai. 

      Ba wata tafiya sukai mai nisa ba. Koda Abdull yay fakin bata fito ba sai da ta bari suka fara fita sannan ta fito a ƙarshe. Ɗan duban Master dake kallon agogon tsintsiyar hannunsa tayi, dan suna gab da shiga gidan ya saka mask a fuskarsa. Dai-dai ya ɗago shima suka haɗa ido. Saurin yin ƙasa tai da nata tana ɗan murza yatsun hannunta waje guda. 

      Abdull dake fiddo ledoji a booth yay ƴar dariya yana kallonsu. “Mutanen nan kuna lafiya kuwa? Sai wani abu kuke tamkar wasu budurwa da saurayi”. 

    Harararsa Master yayi da faɗin, “To kai banda sa ido miya kawo idanunka nan?”. 

         “Ikon ALLAH, sai na rufe idanu saboda karnaga masoya”. Abdull ɗin ya faɗa yana ɗan kallon Hibbah da tai kamar bata a gurin, sai dai sarai tana jinsu. Gaba ɗaya dai hankalinta na’a kallon gidan daya gama ƙyau da haɗuwa sashe-sashe kamar wani ƙaramin estate. A kallo guda zaka fahimci sabone ko tarewa cikinsa ba’ayiba, dan wasu wajejen ma ba’a kammala ginin ba. 

       Ƴan sandan dake a cikin gidan tako ina kusan su ashirin suka nufosu fuskokinsu da fara’a. Cike da girmamawa suka shiga ƙame jikinsu suna gaidasu. A yanda sukeyi ɗin zai baka tabbacin suɗin suna ƙasa da master ɗinne.  

Advertisements

     Ɗaya da ga cikinsu ne ya kwashi ledojin da sukazo da shi suka nufi sashen dake can  ƙarshe da alamu suka nuna an ɗan jima da kamalashi. Suna shiga cikin falon Hibbah da ke a bayan Master kirjinta yay wani irin bugawa saboda tozali da tai da Yaya Ammar ya fito da ga kitchen ɗauke da kofi yana faman danna waya dake a hannunsa. Jin takun mutane da yawa ya sashi ɗagowa duk da yasan zagaye suke da ƴan sanda a gidan tun randa aka kawosu. Shima ya wani waro idanunsa waje lokacin da idanunsa ke sauka akan Hibbahn da Master daya cire mask ya koma Isma’il ɗinsa bayan sun shigo cikin falon. Da wani uban gudu ta kwasa har tana ɗan ture Master ta nufi Ammar. Babu wani tunani a ranta ta daka tsalle ta ɗanesa da sakin wani kuka mai ban tausayi.

        Har cikin rai sai da Master yaji wani abu mai kama da kishi ya soki maƙoshinsa. Amma sai yay saurin kaudawa a ransa dan yasan dai Ammar ɗan uwanta ne uwa ɗaya uba ɗaya. Fitowar Ummi dake magana cikin ɗan faɗa akan kiran da Ammar  yake ƙwala mata yasaka Hibbah saurin sakin Ammar ta nufi Ummin. Itama ɗanetan tayi tamkar zata tsaga jikinta ta koma har Ummi na neman faɗuwa.

        Da masifar ƙarfi Ammar ya shiga ƙwalama su yaya Umar kira su da matansu. Suma sai gasu ko suna sakkowa da ɗaɗɗaya daga saman Upstairs. Cikin ƙanƙanin lokaci gidan ya harmutse. Har Hibbah tama rasa jikinwa zata kasance dan farin ciki. Sosai Master yaji tausayinta ya kamashi, dan shi kansa ya sake tabbatar da ɗunbin soyayyar dake tsakanin wannan ahali. Dan yanda Hibbah ke kuka haka su Yaya Muhammad ke faman sharar hawayen kewarta da ƙaunarta.

      Da ƙyar Ummi ta samu suka lafa dan lura da su master ɗin da tayi. wanda su kansu su Yaya Abubakar sai yanzu suka gansa. Sosai mamakin ganinsa ya kamasu, dan kewar Hibbah ya mantar da su mamakin ganinta anan ɗin duk da basusan wanene yasa aka kawosu nan ɗin ba tsahon kwanki huɗu kenan. 

         “Isma’il yaya akai kuka san nan?”.

Ummi ta tambaya cikin tsaresa da idanu. A karon farko ya saki murmushi kansa a ƙasa. 

      Kafin ya samu damar cewa wani abu Yaya Abubakar daya kafesa da idanu ya kira sunansa cikin alamar kowanto. Guntun murmushi kawai master yayi yana ɗauke kansa. Ganin kallon da suke masa da fahimci sauran wasiwasi a ransu ya ɗan duba Hibbah da ke naniƙe da Ummi da alamar magana ce fal bakinta, hakan yayi dai-dai da satar kallonsa datai niyyar yi batasan shima ita yake kallo ba suka haɗa ido. gargaɗi yay mata da idanu alamar ta kiyayi bakinta. Baki taɗan tura gaba da ɗauke kanta tana sake nanuƙe Ummi da ɓata fuska.  

       Master ma ɗauke nasa idon yay ya maida ga duban Yaya Abubakar dake kallonsa har yanzu yana wani ƙayataccen murmushi dake tafe da ma’anoni da yawa. Murmushin shima Master yayi ya ɗauke kansa kawai. A karon farko yay ƙaramar dariya har haƙoransa na bayyana sosai. Ya kai hannu yana shafa fuskarsa da duban Ummi cikin haɗe hannayensa waje guda🙏🏻. 

        “A gafarceni Ummi, ni a haka labarin nawa yazone, nima bada son raina na ɓoye miki hakan ba. Dan kallo nake miki na uwa bayan mahaifiyata. Tun asali haka na tashi cikin ɓoyayyar rayuwa saboda samun cikar burina, sai kum yanayi ya sake ɓoyeni saboda neman martabata. Kuma Yaya Muhammad ku gafarceni yau ga auta nan na kawo muku, insha ALLAH kuma zuwa yanzu babu wani tasiri dake tare ga masu burin cutar da ita ko ku kanku. Nagode da halaccinku gareni. Nasan kunada tambayoyi fal bakinku akan kawoku da akai nan aka ajiye, karku damu insha ALLAH daga yau zuwa gobe zaku fahimci komai, dan haka a yanzu dan ALLAH kuyi haƙuri karku tambayeni komai”

     Ya riga ya gama ɗauresu tunma kafin suce komai, dan haka bakunansu suka gagara ce masa koman domin tuhuma. Sai ajiyar zuciya kawai da suke faman saukewa a jajjere. Master ya maida dubansa ga Yaya Abubakar. “Ayi haƙuri babban Yaya, inaga ya kamata ka bimu mu maidaka wajen aiki yanzun dan kafi kowa buƙatar komawar a wannan gaɓar. Yana gama faɗa ya miƙe da ɗan duban Hibbah ya ɗauke kansa yana kallon agogo. 

           Dole yaya Abubakar ya miƙe shima ya fita domin kimtsawa batare da ya iya cewa komai ba tunda Master yace karsu tambayesa komai dan ALLAH. Sai dai kuma a ransa ya gama yarda Isma’il jami’in tsarone tabbas.

Advertisements

       A nan suka bar Hibbah da hakan yay matuƙar sakawa cikin farin ciki, hakama sauran yayunta da su Zahidah. Sai dai duk bugun cikin da suke mata akan son jin wani abu game da Isma’il tayi mirsisi. Sai ma ita dataita musu ciwon baki akan dama sun san Isma’il ne ya saceta shiyyasa sukaƙi nemanta balle damuwa da rashin ganinta. Lallaahinta su Yaya Muhammad suka dingayi. Daga ƙarshe Ammar ya bata labarin komai daya shafi Master, wanda zuwa yanzu itama duk tasan wannan harma da abinda su basu sani ba na kasancewarsa jami’in tsaro. Tana da matuƙar wayo, dan haka taki yarda tayi maganar Abba Halilu a gaban su Zahidah da abinda taji har sai da suka shiga salla ɗakin Ummi su kuma suka tafi sashensu. Wayar Ummi ta ɗauka ta turama su Yaya Muhammad massege akan idan sun dawo salla zatai magana da su a sashen Ummi.

     Suna idarwa kuwa koda suka shigo gidan kai tsaye sashen Ummin suka nufa, inda suka isketa naniƙe da Ummi tanata bata labarin su Habib da baba Saude. Ummi sai dariya take da jin daɗin autarta batai rayuwar ƙunci da damuwa ba ashe. Sai take sake ganin girma da mutuncin master a cikin idanunta da jin kaunarsa a ranta fiye da da can. Zama sukai suma suna sauraren surutun na Hibbah suna dariya, idan Ammar ya musa mata magana idan tayi yace bai yardaba su hau faɗa yana dariya da daɗa tunzurata. Sai Yaya Muhammad ya hararesa sannan ya bata haƙuri.

       Yaya Umar yace, “Auta ajiye wannan labarin naki sai anjima faɗa mana mikike son gaya mana?”.

     Kanta ta jinjina masa tana gyara zama, “Wani abu zan sanar muku akan Abba wlhy kuma da gaske nake. Ummi kindai san bana ƙarya, bakuma nayima mutun sharri dan kince ɗan aikene idan ka aika zai dawo kanka komai tsahon shekaru”.

     Ummi ta gyaɗa mata kai kawai. Hibba tace, “Yauwa Ummi ranar ɗaurin aure da yaya Muhammad ya sakani fita amsa waya…………”

            Wani irin zufa ke ketoma su Ummi a jiki da kiɗima tunda Hibbah ta fara basu labari. A fuskokinsu kawai ya isa ka irga yawan tashin hankalin abinda sukeji. Dan numfashin Ummi har fita yake a sarƙe kamar mai Asthma. Hibbah dake kuka rurus itama zuwa yanzun ta faɗa jikin Ummi tana faɗin, “Ummi na tsaneshi, bana son sa, bana son sake ganinsa a rayuwata har abada. Ummi dan ALLAH karki sake zaman aure da shi, yaya kuma ku daina cemasa Abba shi ba abbanmu bane fasiki ne azzalumi mai aikata saɓon ALLAH batare da yaji kunya ba”.

        Cikin rawar murya Ammar yace, “Hibbah kin tabbatar maganar nan taki da gaske kikeyinta?”.

       “Wlhy Yaya Ammar da gake nakeyi, kama tambayi Yaya Isma’il yasan komai shima. Nama san zai sanar daku idan ya kammala abinda yake sonyi”.

       Innalillahi wa-inna’ilaihirraji’un suketa faman maimaitawa zufa na sake gudu a jikunansu. Yaya Usman mai ragon zuciya kam harya fara kuka dan kallon abin yake tamkar a mafarki ƙanin mahaifinsu da aikata homo duk da kasantuwarsa dattijo a yanzun. Ummi kam a take zazzaɓi mai zafi ya lulluɓeta duk da kuwa akwai wani lokaci kafin rasuwar mahaifin su Hibbah data taɓa zargin Abban da wannan ƙazantar akan abokinsa Alhaji Balele. Sai dai gudun karta aikata zato akan abinda bata da tabbas yasata kauda al’amarin ta nema tsarin ALLAH daga sheɗan. Lallai dolene rashin imaninsa ya sake ƙarfi a zuciyarsa. Dubi da yanda yake mata fyaɗe cike da cin zarafi da tozarci a gareta. Su duka babu wanda baiyi hawaye ba hatta yaya Umar mai ƙarfin zuciya, sai suka godema ALLAH ma da yaya Abubakar baya nan baiji wannan kwamacala ba. A fusace Ammar yace, “Wlhy Ummi sai mun tona musu asiri, dan barin irin waɗan nan shaiɗanun a duniya haɗarine da barazana ga matasa, musamman waɗanda suke a halin rayuwa na rashin aikinyi. Dan da kuɗi ake jan ra’ayinsu a gurɓatasu kamar yanda nake hasashen shi kansa halilun baƙin matsiyaci ya shiga”.

     Kai Ummi dake sharar hawaye ta girgiza masa. “Ammar tona masa asirinsa tamkar tona namune. Zai ma iya musawa akan hakan. Idan muka zuba ido ma ALLAH da kansa zai tona asirinsu wa duniya insha ALLAH. Sai dai ban yarda Isma’il yana cikin masu aikata wannan kwamacalarba nima Tanee. Koke kin taɓa ganin wata alamar hakan tattare da shi?”.

         Kai Hibbah ta girgiza, dan batason faɗa musu komai da Master ya sanar mata tunda ya gargaɗeta. “Ummi bana tunanin hakan gaskiya, nafi zarigin akwai dalilin da yasa yake tare da su ɗin tamkar yanda ya faɗa…..”

       “Ko kuma wancan master ɗin daya ɓoye sukema tunanin shine Yaya Isma’il ba. Anya kuwa Yaya Isma’il ba jami’in tsaro bane ba?”.

    Ammar ya faɗa yana duban su Yaya Muhammad.

        Yaya Umar yace, “Nima na fara zargin hakan Ammar, tun ma a randa yayma Junaid dukan nan nakeji a jikina jami’in tsarone ɓadda kama kawai yakeyi a cikinsu kamar”.

     “Koma dai miye muɗan sauraresa muji daga bakinsa to”. Ummi tai maganar tana share hawayen dake sakko mata na baƙin cikin halin Abba halilu har yanzun. ALLAH sarki Hajiya mama, ta ƙyamaceta akan tazo cikin ƙaddara bada aure a tsakanin iyayenta ba. Yau ga ɗan data haifa nan yana aikata aiki mafi muni da yafi wanda mahaifinta ya aikata wajen samar da ita. Haka rayuwa take, shiyyasa karka ƙyamaci abinda UBANGIJI ya ajiye bisa ALƘALAMIN ƙaddarar faɗakarwa ga wasu mutane. Kai dai kazamto mai faɗar alkairi ko kawai kayi shiru.

         Haka suka cigaba da hira gwanin sha’awa. Duk yanda sukasha cikin Hibbah akan jin wani abun mara kyau daga Master taƙi yarda ta faɗa koda da suɓutar baki. Sosai kuma ta birgesu suka sake yarda autarsu ta daɗo hankali kenan.

       Addu’a Hibbah ta dingayi kar Master ya dawo yace su koma gida, cikin amincin ALLAH kuwa sai gashi har dare babu shi babu yaya Abubakar. Taji matuƙar daɗi dan yau koba komai a bayan Umminta zata kwana………..✍

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like