Advertisement
*_Typing📲_*
*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*
______________________
💥🔥🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥
*HOHOHO WANI KAYA SAI AMALE, DON JAKI BAZAI ‘DAUKA BA, INA MATA MASU BUK’ATAR ‘DAGA DARAJARSU A WAJAN MAZAJENSU INA MATAN DAKE SHAN WULAK’ANCIN MIJI KO NA KISHIYA ,INA MATAN DAKESON ZAMOWA MOWA AGIDAJEN AURENSU TO ALBISHINRU MAMAN ZARAH YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GABATAR MAKU DA ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI WANDA BASUDA ALGUS ACIKI , AKWAI MAGANI DANAYI BINCIKE AKANSU DAN FARIN CIKIN MA’AURATA NAMU BA IRIN NASU BANE KAYAN MU NA DABAN NE NA ASALIN SAKKWATAWAN SHEHU MASU ABUN MAMAKI* 07034251528
🔥💥🔥💥🔥💥🔥🔥💥
Advertisements
kayanmu masu inganci ne masu ladaftar da kowane irin namiji💃🏻💃🏻💃🏻🔥
Kad’an daga cikin abubuwan da muke dasu 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Ingantaccen maganin nono , Wanda zai gyara maki nononki donmin dawo da martaban nononki acikin kankanin lokaci komai lalacewarshi kuwa sauran bayani sai mun had’u pc +234 703 425 1528
Maganin hips (hips up) Wanda zai ciko maki da hips dinki su cika suyi bul bul ga laushi dasu k’ara suyi dass abun sha’awar kowane namiji 🔥💥
Maganin infection Sha yanzu magani yanzu Yana fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci magani ne na maza da Mata insha Allah kowane irin sanyi gareki kikayi amfani dasu anwuce wajan💥🔥💃🏻
Ingantacce Kuma sahihin maganin k’iba Wanda Zaki ciko acik kankanin lokaci zakiyi kibar ki Yar dai dai misali ki huta Zama da Rama Baki rasa ci ba Baki rasa sha ba amma kullum Ana kallon cewa kinada matsala agidan aurenki saboda wannan ramar , Rama batayi ba Sam Yar uwa😉😉
Advertisements
Sabulun wanka
Kalolin sabulun tsarki
Turaren tsugunno
Turaren al’ajab
Hatsabibin turare
Da sauransu 07034251528
Kalolin gumba👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Gumbar Dabino
Gumbar gero
Gumbar madara
Gumbar matsi
Gumbar ukku bala’i
Gumbar tada zaune tsaye
Gumbar sabon budurci
Gumbar sa buzu kuwa
Gumbar aya da kwakwa
Gumbar ridi
Gumbar mazari
Sarauniyar gumba 3in1
Da sauran kalolin da bansamu fadi ba,
Kalolin gari
Garin mallaka
Garin hutar da malaminki
dakan jaraba
Dakan Amare
Dakan Ni’ima
Dakan kishiya in bakiyi bani waje
Garin sa buzu kuwa
Garin buje.sharkaf
Garin Dan la’asar
Yayan hadiya mai suna dan la’asar
Original Dan goshi
Original Dan goshi (sabon salo)
Original man damo
Original man ayu
Kitsen damo
Sirrin tafin kafa
Sirrin farinjini na uwargida da amarya harma da yan mata
Kwallin idonka idona
Muna hada set na sirrin mallaka hajiya ba boka ba Mallam sai tarin sirrika kema kizama kowa agidan surenki👍🏼💃🏻💃🏻
Akwai hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar d’a namiji da izinin Allah akayi maki wannan hadin to an wuce wajan sauaran bayani sai mun had’u pc 💥🔥
Kalolin tsumi👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Tsumin mallaka
Tsumin jaraba
Tsumin madarar ni’ima
Tsumin tabaje
Tsumin Amare
Tsumin sabon budurci
Tsumin nono raƙumi
Matan gaske
Ruwan jaraba,
Da sauran kalolin da ban fada ba
Kalolin matsi da basuda illa ajikin mace sai dai ma sukara maki lafiyar HQ💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Matsin Dan mannau
Matsin mallaka
Dan la’asar
Sabon budurci
Mak’alemata
Mashahurin matsi
Ukku bala’i
Matsin uban budurwa
Akwai gumba ta matsi wadda Shanta akeyi ga matan da basa son yin matsi
Muna hada set ga wadda Allah ya jaranfa da matsalar fyade har yarasa budurcinta , muna hada mata kaya ingantattun don dawo da martabar ta,
Hohohohoho in ana dara fidda uwa ake
*Kyallen al’ajabi* babban sirrin mallaka mai abun al’ajabi mallaki naki don samun damar shiga cikin jerin mata masu fada aji a gidan mazajensu ,
KARKU manta da sunan maman zarah sokoto sayen nagari maida kudi gida🥰🥰🥰🥰🥰👍🏼👍🏼👍🏼👍🏼
07034251528 ina maraba daku sayen daya ko sari ina Sokoto sannan ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah🤝🏼🤝🏼
Ga Wanda suke bukatar ganin kalolin kayana to suyi sarving number na suyimun magana nayi sarving number ku zaku dinga ganin kalolin kayana a status ngd sosai 07034251528
Maman zarah mabera sokoto state💥🔥💥🔥💃🏻
_________________________
*_Chapter Twenty Seven_*
………..Madam Hibbah na shiga ta danna ma ƙofar ɗakin key. Cike da jin daɗi ta daka uban tsalle ta dire da taka ƴar rawa. Kafin ta harari ƙofar ɗakin da yin gwalo. A fili ta ce, “Ɗan tara dangin su Halilu yau dai call zaku kwana. Dan yanzun nan zan dokama Yaya Abubakar kira”.
Ta ƙare maganar da ƙyalƙyale wa da dariya ta je gadon ta haye. Jinta take kamar an mata gafara. “Yaya Abubakar kai ya kamata na fara kira. Sai Ummi, sai Yaya Muhammad. Sai Yaya Umar da Yaya Usman. Yaya Ammar mai kan gwanda ne ƙarshe”. Ta sake ƙyalƙyalewa da dariya ita kaɗai kamar zararra. Dan kaf yayunta babu lambobin wanda bata riƙe akai ba tsaf.
Kamar yanda ta tsara lambar Yaya Abubakar ta fara lodawa. Tanayin dailing Habib na rufe network ɗin gidan. Ɗin! Ɗin! Ɗin!! Wayar ta bada sauti, alamar tambarin mtn ta kona Emergency.
Zumbur Hibbah ta miƙe da bubbuga wayar. Sai kuma ta ɓalle murfin ta cire batir ɗin. Zaman sim ɗin ta gyara a tunaninta gocewa yay. Sanann ta sake maida batir ɗin ta kunna. Still Emergency. Ta ɓata fuska kamar zata fasa kuka tare da sakkowa saman gadon tana bibbiga wayar da ɗagata sama. Sai dai sam babu alamar network ɗin. Wayarta ta ɗakko danta duba, sai taga nanma hakan take.
“Inaga network ne ya ɗauke duka”. Ta faɗa cikin gamsar da kai. Sai kuma ta koma ta zauna bakin gadon zaman jiran dawowar network.
Kamar wasa Hibbah na zaune zaman jiran dawowar network har la’asar. Ta tashi tai salla ta sake komawa ta zauna. Kaɗan-kaɗan saita ɗauka waya ta duba amma wayam. Ahaka ta sake shafe awa guda. Agogon ɗakin ya nuna 5pm. Mamaki ne ya kamata matuƙa, sai kuma tunanin fitowa ta bincika yazo mata a rai. Sai da ta fara leƙo kanta ta ga baya falon sannan ta fito, dan harma kayan abincin da yaci an tattare. Cikin sanɗa tazo har bakin karfen da aka ƙawata upstairs ɗin ta leƙa ƙasa. Babu kowa a falon sai ɗan motsi a kitchen, da alama baba saude ce.
Juyawa tai da nufin sauka ƙasan gab tai karo da abu. Cikin sauri da rawar jiki ta ɗago dan jin mayataccen ƙamshin turarensa ya daki hancinta. Baya taja da sauri ta manne da ƙarfen ta fara karanto addu’a.
Fuska ya sake tsukewa dan tsaf ya fahimci inda ta dosa. Irin dai taga aljanin nan. Sai da ya ɗan kai dubansa a downstairs ɗin ya tabbatar babu kowa sannan ya matsa jikinta sosai, hannayensa duka biyu ya ɗora saman ƙarfen, hakan yasata kasancewa a tsakiya, idan ma kana nesa da su ne sai ka ɗauka rungumarta yayi.
Ƙara manne jikinta tai da ƙarfen jikinta na ɗan rawa saboda yanda take iya jiyo fitar numfashinsa, “Dan ALLAH ka matsa wannan fa iskanci ne wlhy.”
Dara-daran idanunsa ya zuba a saman ƙyaƙyƙyawar fuskarta, tare da ɗago hannunsa na dama ya ɗaura saman cikinta. A bazata Hibbah taji wannan al’amari. Babu shiri ta zabura ƙafarta na gocewa tai baya. Cikin zafin nama ya taro ƙugunta ta dawo saman ƙirjinsa, sannan kuma ya tura hannunsa da ke kan cikinta ƙasan rigarta.
A matuƙar firgice Hibbah da taji saukar lallausan tafin hannunsa saman fatar cikinta daya tura cikin zaninta ta ce, “Na shiga uku Ummi”.
Shima da ƙarfi ya cije lip ɗinsa yana zaro wayar baba Saude da ta soke a zani da sakinta ya matsa saboda fitowar baba saude da ga kitchen tana faɗin, “Ƴar nan lafiya? Badai faɗuwa kikai ba?”.
Ina Hibbah bama taji baba Saude ba. Dan yana sakinta ta zame ƙasa saboda wani irin rawa da jikinta keyi. Shi ko tini ya fara taka steps ɗin tamkar bai aikata komai ba. Dan ko tanka maganar baba Sauden baiyiba harya ƙarasa sakkowa ƙasan.
“Babana kamarfa ihun yarinyar nan naji”. Baba Saude ta faɗa aɗan rikice.
Cike da basarwa ya ɗan dubi Baba Sauden ya janye idonsa. “Kunnenki ne kawai baba”. Yay maganar yana nufar hanyar fita abinsa.
Cikin shakku baba Saude ta bisa da kallo, sai kuma ta kaɗa kai kawai ta juya kitchen tunda taga da ga saman ya ke. Maybe kunnen nata ne kamar yanda ya faɗa.
kuka sosai Hibbah ta saki jikinta a ƙanƙame. Dan wannan sabon abune wanda a tsayin rayuwarta bata taɓa fuskanta ba ga wani ɗa namiji. Ga baƙin ciki da takaicin wayar da ya amsa. Sosai takejin kewa da tsoron kar wani abu ya sami ahalinta. Dan babu abinda ta gano a tsakkiyar idanun Master sai ɗunbin hatsabibanci da mugunta. Tabbas zai iya aikata duk abinda zuciyarta take tunani. Anya bazata janye kalamanta ba kodan ceton ahalinta?, Ummi tana da ciwon da bata buƙatar damuwa, rashinta a gida kuma babbar damuwace ga Ummin da yayyenta. A yanzu haka ALLAH kaɗai yasan halin da suke ciki na rashin ganinta.
Cikin Kuka ta ke faɗin,, “Wlhy Ummi zan iya sadaukar da komai domin ke, na haƙura da *takun saƙar* da shi zan roƙesa ya dawo dani wajenki”. Tana maganar tana miƙewa a wajen, ɗaki ta koma ta faɗa saman gadon da jan bargo ta ƙudindine har saman kanta. Dan harga ALLAH wani irin zazzaɓi-zazzaɓi ma takeji. Ummi tasha gargaɗinta da tsoratar da ita akan illar sakarma namiji jiki harya iya kai hannu wani sashe naka. Sai gashi tsohon najadun nan yau ya tura ƙazamin hanunsa har kan mararta.
★★★★★
A ɓangaren Abba suna fita daga gidan A.G gidan shakatawar Alhaji Sallau suka nufa. Sun samesu kusan su biyar da alama zaman jiransu suke suma. Da ido R.D yay ma A.G alamar miya kawo Abba cikinsu?, dan gaba dayansu manyan masu faɗa aji ne a ƙasa da mukamai ke hannunsu. Sannan a shekaru duk sun girmi Abban, hasalima sune suka ɓata rayuwar Abban dan lokacin da Alhaji Balele ya sakoshi a harkar wajensu yake kawosa kasancewar su ubannin gida a garesa. kai A.G ya gyaɗa masa da masa alamar cool down.
Cikin kaɗa kai R.D ya janye idanunsa yana gyara zamansa cike da isa. Kasancewar duk ubannin gida suke a wajen su Abban cikin girmamawa ya gaidasu. Kafin ya kai zaune inda A.G ya nuna masa.
Alhajin Mande ya dubi Abban da faɗin, “Lallai Halilu idonka kenan?”.
Ƙasa Abba yayi da kai a girmamame. “Ayi hakuri ranka ya daɗe na samu raunine a ƙafa, amma Alhmdllh zuwa yanzun na fara fita kaɗan-kaɗan”.
Alhajin Mande ya gyaɗa kansa da faɗin, “Eh A.G ya sanar mana ai randa ya kawo mana invitation ɗin auren yaran wajenka. Sai dai kuma muna baka haƙuri bamu samu zuwa ba bisa wasu dalilai”.
“Babu komai ranka ya daɗe dan auren ma ba’a ɗaura ba”.
“Tofa miya faru aka fasa?”.
Cewar Engineer Zailani Ginger.
“Engineer matsala aka samu, wadda a dalilintane ma muka zo nan ni da A.G”.
Gaba ɗaya dattijan ala kwankwan ɗin suka maida dubansu ga A.G.
A.G ya gyara zamansa yana dubansu shima. “Hatsabibin yaron nanne ya ɓata masa aiki”.
Kai tsaye R.D yace, “Kana nufin Master?”.
“Shi kuwa”.
Kusan a tare suka haɗa baki wajen faɗin, “Ya akai yasan Master shi?”.
A.G yay ɗan tiri-tiri da faɗin, “E..e eh ya sanshi ne sakamakon yarinyar nan data hari Master ɗin kwanaki ƴar yayansa ce. To da mukai bincike ta office akan yarinyar ne na fahimci haka. Shine na nemesa danjin wani abu akanta. Daga nanne ya roƙeni muyi masa wani aiki akan yayun yarinyar da uwarta shima zai taimakemu ta yanda zamu amfani da basirar yarinyar. Shine fa na saka Master akan aikin dan nasan zai iya, gashi kuma yarinyar dama ta shiga gonarsa. Hakan yasa muka yanke shawarar ya aureta………..”
“Aure fa kace?”.
Dr Sufi ya faɗa da mamaki.
“Eh Doctor, dan aurenne kawai zai iya bashi damar ɗaukar yarinyar cikin sauƙi saboda ƙanwar shegen jami’in nanne Abubakar Aliyu Hamza Gwarzo. Kasan kuma shima hatsabibin kansa ne mai faɗa aji wajen I.G”.
Lokaci ɗaya ruɗani ya bayyana a kan fuskarsu. Engineer Zailani yay saurin tare numfashin A.G da faɗin, “To yanzu dai yaya akai?”.
Carab Abba ya karɓe zancen. “Ya auri shegiyar yarinyar, sai dai ni ya wargazamin nawa aikin na hana yayun yarinyar auren nawa ƴaƴan. Yanzu hakama ya ɓoyesu inda ban sani ba”.
“Alhaji Halilu kabi a hankali, na tabbata master bazai aikata hakanba sai da manufa”. A.G ya faɗa cikin jin haushi. Kafin Abbah ya ce wani Abu Alhajin Mande ya karbe da faɗin, “Master kam banajin zai ɓata lokacinsa akan wanann shiriritar, amma ku jira na san yana gab da zuwa nan”.
Cike da zalama Abbah yace, “Yauwa Alhmdllhi. Gara yazo naji yaya aka faɗi a ragaya ranka ya daɗe”.
Komai babu wanda ya sake ce masa. Dan ama kusan dai-dai rufe bakinsa maigadi ya shigo yana sanar dasu isowar Master ɗin.
Da hanzari R.D ya bada damar shigo da shi, dan sun rasa miyasa baya yarda ya shigo musu kai tsaye a duk sanda suka buƙaci ganinsa. Koda waya ya gama da su sai ya nema iso yake shigowa.
Cikin izzarsa da ƙasaita ya shigo falon da sallama ciki-ciki. A kusan tare suka amsa suna zuba masa ido tamkar tsoffin mayu. Yana matuƙar birgesu da tafiya da imaninsu. Sai dai sam sun kasa samun kansa domin biyan bukatar zukatansu. Ya dai amince yay musu sauran ayyuka, hatta kisan kai idan sukace sunaso ayima wani yakan amshi aikin, amma sanin yaya yake aikin har yanzu basu da tabbas. Kuma bai basu wata ƙofar masa tambaya ba, dan duk da karancin shekarunsa a cikinsu baya ɗaukar raini koda na kallon bamza ne.
Zaune ya kai bisa kujera yana mai ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya cike da ƙasaita. Kafin ya kai hannu bisa glass ɗin fuskarsa ya gyara masa zama da ƙyau yana kare musu kallo ta ciki. “Barkan ku”.
Ya fada a taƙaice yana zuƙar iska da fesarwa. Sosai sukejin takaici na salon iskancinsa da izza. Sai dai basu da damar tankawa dan duk sun kasance a tafin hannunsa, saboda sirrikansu da yawan gaske ya gama sani.
Bakuna suka shiga washewa. Kowanne na ƙoƙarin tambayarsa yaya yake. Nanma a takaice ya amsa musu da cewar,
“Normal”.
Ya tsuke bakinsa.
A.G ya nuna masa Abba. “Ina fatan ka gane wannan ko Master?”.
Cikin ɗan yamuste fuskar boginsa ya ce, “Kamar..”
Haushi ya kama Abba. Ya zuba masa harara da faɗin, “Kai saurayi miye kuma Kamar? Ni nasan ka ganeni kodan maƙudan kuɗaɗen dana sauke maka kafin karɓar aiki na”.
Mai makon ya amsa Abbah sai ya duba A.G da faɗin, “Wanann shine dalilin kiran?”.
“A’a ina” R.D yay azamar faɗa saboda sanin wulaƙancin Mastern. Kaɗan da ga aikinsa ya karta musu rashin m ya tashi yay tafiyarsa.
Abba da ya fahimci gadara bazatai ba sai ya kwantar da murya. “Kai ko saurayi dan ALLAH ka saurareni. Wlhy ina cikin matsala fiye da zatonka. Kuma ba kowa bane ya sani wabilahillazi sai kai. Miyasa munyi maganar ka auri yarinya kawai sai ka wargaza auren nawa ƴaƴan kuma? Bayan kuma duk na sanar maka ƙudirina akansu”.
Nan ma banza yay masa bai tanka ba, sai ma agogon hanunsa da ya kalla. Da sauri A.G da ya fahimci ma’anar kallon agogon ya ce, “Ayi haƙuri a sauraresa Master. Rashin tabbatar wannan aikin zai iya saka masa ciwon zuciya wlhy. Nasanka kuma baka karya alƙawari, ga shi bamu san dalilinka na hana auren yaran nasa ba”.
Kamar bazai tanka ba kuma sai ya dubi Abban. “Mi kake buƙata yanzun?”.
Baki Abba ya washe yana gyara zama. “Yauwa ɗan albarka. Su yaran da ka wargaza auren yaran nawa da su nakeson sanin inda suke su da uwarsu. Idan da hali kuma a karminsu ɗaya bayan ɗaya dan ALLAH kamar yanda mukai da kai a farko, ni yanzu ma basai sun auri yaran nawa su wani sami ciki ba. Sanann akwai dukiyarsu da ke a hannuna da kaddarori duk sunayensu ubansu ya saka matsayin masu gadarsa, dole sai sun saka hannu su da lauyan baban koda zan iya amfana da su. To shi kuma lauyan ya ɓata ɓat tsahon shekaru shegen shine nakeson a kwashe kuɗaɗen a maidosu accaunt ɗina. Takardun kaddarorin kuma a maida sunana. Amma inason a fara kashemin ita yarinyar da aka ɗaura aurenku da itan sannan, dan wlhy da baka ɗauketa ba a jiya ni da kaina da zan kasheta”.
“Zamu sake sabon ciniki. Dan baka sanarmin gaskiya ba a wancan aikin shiyyasa na wargaza auren ƴaƴanka. Ni idan za’a bani aiki bana son ƙarya bana son munafinci. Yanzu ma idan ka ƙara zakaga ba dai-dai ba. Ka tattara dukan bayanai da accaunt no. Ɗin da kuɗin suke da takardun kaddarorin ka bama A.G tare da kuɗin aikina”.
Yawu Abba ya haɗiye da ƙyar, dan awancan aikin fa 5mil ya bashi. Amma dan tsabar wulaƙanci ace wai sun ciwu batare da an masa aikin ba. Shikam ya fahimci yaron nan zigidir yake son masa. To amma ai yanzu kuɗaɗene masu nauyi zai samu. Dan haka ya sake gyara zama. “Na yarda zan sake biya. Amma nawane to? Dan ALLAH amin ragi”.
Cike da shan ƙamshi Master ya ɗan dubesa ta cikin glass ɗin idonsa ya ɗauke kai. “Zaka fara bada 10mil yanzun nan, bayan naga takardu da nauyin kuɗaɗen asusun zan faɗi farashi”.
“Bantan uba kana nufin 10mil ɗin ma ba farashi bane?”.
“Kuɗin saka data and transport ne”. Master ya faɗa a gadarance.
Abbah zai kara magana A.G ya zunguresa. Kallonsa yay a marairaice tamkar zaiyi kuka. Amma sai ya girgiza masa kai alamar karya sake cewa komai. Dole Abbah yay ƙasa da kansa. A zuciyarsa kuwa sai jama Master kwando-kwandon tsinuwa yakeyi.
Da ido Alhajin Mande yay ma A.G alamar ya sallami Abba. Kansa ya gyaɗa yana duban Abban. “Alhaji Halilu kaje ka tattara abinda ya ce idan na fito zan biyo ta gidanka na amsa”.
Miƙewa Abba yay yana faɗin, “To. To bara naje ɗin, amma dan ALLAH ka ɗan sake nemamin ragi kuɗin yayi yawa wlhy, dan ya zabtare kaso biyu bisa ukun abinda na mallaka idan aka haɗa da biyan farko. Gashi nayi hidimar kamawa shegun yaran can gidajen haya babu gaira babu sabar”.
“Babu damuwa kaje. Zamuyi magana da shi”. A.G ya faɗa cikin ƙosawa.
Sai da sukaji fitar motar Abba a gidan suka maida hankalinsu ga Master da ya lafe cikin kujera idanunsa da ke cikin glass a lumshe. Dr Sufi ya fara magana yana ɓalle murfin robar ruwa. “Master taruwarmu anan tana da nasaba da wani babban aiki da ya sake taso mana. Amma kafin mukai maganarsa nakega ya kamata ace kuɗaɗen hannunka daketa taruwa kusan shekara biyu mizai hana a ɗan raba wasu a ciki kar asusun ya cika da yawa har wani yay mana ƙafar angulu. Kaga tunda aka fara aikin nan biyanka kawai muke kuɗin aiki amma kuɗaɗen ko nera bata shiga aljihun ɗaya da ga cikinmu ba, sabanin da da kayi aikin kake bamu abunmu”.
Miƙewa yay zaune sosai tare da zare glass ɗin idonsa. Ya zubamasa razanannun idanunsa masu kama dana Zaki. “Likita kasan bana magana biyu, shiyyasa tun farko na sanar muku sai na kammala muku wannan aiki zan baku sakamako. Ko kana tunanin da kuɗaɗen nan nake harkar rayuwata ne?”.
Da sauri Alhajin Mande ya ce, “Haba karma ka kawo hakan a ranka Master. Mu da kake gani anan mun matuƙar yarda da kai shiyyasa muke iya fasa maka sirrin cikinmu, karka manta tun kana ƙaramin ɗan jagaliya kake tare damu. Sam ba haka Dr Sufi ke nufi ba. Amma nima sai nake ganin ko kaso ɗaya bisa uku ne na kuɗin aɗan raba mu farfaɗo koda bayan ka gama wannan aikinne na yanzu da zamuyi magana. Dan shima asusun manyan gwasake ne”
Komawa yay jikin kujerar ya kwanta yana maida glasess ɗinsa cike da salonsa na izza. “Zaku bani accaunt numbers naku na sirri. Bayan aikin nan ya kammala zakuji billions ɗari-ɗari”.
Wani irin kallon zazzaro idanun mamakin jin nauyi kuɗaɗen da kawai tsakurowa zaiyi ga abinda ya tara musu sukai. Atake bakunansu duk suka washe. Alhaji Sallau yace, “Kace abin na gaske ne Master mu ƙara ƙaimi”.
Wani ɗan salo kawai yay masa da yatsunsa🤙🏻 ba tare da ya bashi amsa ba.
Wani irin shegen daɗi ya baibayesu. R.D ya jawo takardun gefensa yana faɗin, “Waɗan nan sune jadawalin sunayen waɗanda za’a wawashe ma asusu. Uku da ga ciki munason a fallasasu wa duniya bisa handamar da suka shuka akan kuɗaɗe. Na farko I.G na ƴan sanda. Sai ministern man fetur. Da shegen can Barau na ALLAH shaharren ɗan kasuwa a zahiri a baɗini kuwa kuɗin kwangilar gwamnati ne yake handama da ga aminansa da suka ɗaure masa ƙugu a gwamnatin. Sai gwamnan jihar gabas damu.”
Wani shegen murmushi Master ya saki yana miƙewa. ga accaunt no ɗina nan naji alert. Da ga safiyar jibi idan ALLAH ya kaimu zakuji sakamakon aiki.”
Dariya suka shiga ƙyalƙyalewa da shi suna tafawa. R.D ya miƙa masa takardun sunayen duk waɗanda suka lissafo da bayanai akansu yana faɗin, “Master muna son rayuwar shegen I.G ɗin can ta salwanta fiye data kowa. Kaima dai kasan yanda yake tsaye kullum akan son damƙoka da gurfanar da kai harma da alwashin da yake ɗauka na tabbatar da hakan. Ko nera kartai saura a asusunsa. Akwai bayanai shiryayyu akansa da fitarsu sai ta saka zuciyarsa bugawa kafin ma hukumar daƙile ta’annati da kayan gwamnati ta fara bincike a kansa. Kaga sai muga da wane taurin kan nasa zai cigaba da bibiyarka balle ya gano sunanmu da ke manne da naka a baɗini”.
Komai Master bai ce ba. Sai amsar takardun da yay ya nufi hanyar fita yana ɗaga musu hannu alamar bye.
Yana gama ficewa kusan dukansu sukaja tsaki. Dr Sufi yace, “Shegen yaro mun ɗorasa akan samu amma yana neman fin ƙarfin yanzu ɗan banza hatsabibin aljani”.
Cikin takaici Engineer ya karɓe, “Nifa wlhy namafi tsanarsa sama da maƙiyan namu a yanzu. Nakanji kamar na kar shege a wuce wajen tun yanzu”.
“Kulll” Alhajin Mande ya faɗa yana gyara zama. “Kudai mu cigaba da lallaɓashi da haƙuri kuɗaɗen nan da aka tara su dawo hannunmu. Cikin sauƙi zamu sakashi a tarko mu da kammu musa a kamashi, sai mun ƙasƙantar da shi a gaban duniya da kullum burin kowane jami’i ya ga gwiwarsa a ƙasa kafin mu ɗurama shege allurar guba namansa ya zaganye kowa ya huta. Dan ba karamar fitina uwar wannan ta haifama duniya ba”.
“Mu kuma ta haifa mana abinda ya amfanemu ai”. Cewar A.G.
Dariya suka sheƙe da ita baki ɗaya suna tafawa.
★★★★★★
A gidan Ummi kuwa zuwa magrib duk wasu baƙi sun kama gabansu. An kimtsama kowacce amarya sashenta an barta ta jira shigar ango. Sashen Ummi ma dai babu kowa sai ita da samarin ƴaƴanta. Suma ɗin sun fita sallar isha’i basu kai da dawowa ba.
Da Ummi taji motsi sai ta kalla ƙofa da tunanin ganin Hibbah ta shigo. Sai dai shiru kakeji. Harga ALLAH zuwa yanzun zuciyarta a matuƙar raunane take. ji take kamar numfashin Hibbah baya tare da nasu a cikin gidan. Dan babu yanda za’ai Tanee ɗinta ta kwana ta yini batare data sakata a ido ba. Musamman idan ta tuna miya faru akan aurenta.
Kai anya kuwa bata yaudarrar kanta ma. Tayama akai ta amince cewar Hibbah na tare da su Zahidah bayan abin daya faru, dan babu kuma yanda za’ai ace Hibbah bata sani ba. Zaram ta miƙe da ga zaune da take a saman sallaya dan idar da sallarta kenan ta isha’i.
A yanayin kiɗima ta fito falon ƙirjinta da zuciyarta na wani tsitstsinkewa. Gaskiya haƙurinta ya ƙare da kanta zataje sashen su Zahidah ta bincika.
Yanke wannan hukuncin a rantane ya sakata nufar ƙofar falon. A dai-dai nan suma su Yaya Muhammad suka kawo jiki zasu shigo. Baya Ummin tai tana dubansu cikin rauni.
A take suma kuma yanayin nata ya saka gabansu faɗuwa. “Ummi lafiya? Kuwa”.
Yaya Muhammad ya faɗa yana matsowa kusa da ita sosai.
A raunane ta ce, “Muhammad Tanee. Dan ALLAH ku faɗa min gaskiya ina yarinyata take ne? Zuciyata na tabbatar min kuna ɓoyemin wani abu”.
Cikin son kauda mata hankali yaya Umar ya kama hannunta yana faɗin, “Ummi zauna kiji, kwantar da hankalinki indai auta ce tana cikin ƙoshin lafiya.”
“Ban yarda ba Umar, dan zuciyata tana bani numfashin Tanee yana nesa da nawa”.
Cikin in ina Yaya Abubakar ya buɗe baki zai yi magana akai knocking ƙofar.
“Tanee!”
Ummi ta ambata da sauri tana duban ƙofar. Gaba ɗayansu suma ƙofar suka duba, sai dai sanin Hibbah bata tare da su yasa su basuyi wannan zaton ba. Mikewa Ammar da illahirin jikinsa ke tsuma yay ya nufi ƙofar. Batare da tunanin tambayar wanene ba ya buɗe ƙofar da janta baya yana kai kansa zai leƙa aka ɗaura masa bindiga.
“Innalillahi wa-inna’ilaihirraji’un”. Ya ambata yana jan jikinsa baya.
Hakkane kuma ya bama wanda ya ɗaura masa bindigar akai damar sakko ƙafarsa cikin falon. A zabure su Ummi duk suka miƙe saboda jin sallallamin Ammar ɗin. Yayinda idanunsu ya sauka akan bindiga da mai shigowar duk suma sai suka ɗauki ambaton ALLAH.
Mutumin da dukkan illahirin jikinsa ke a rufe ya cigaba da takawa Ammar naja da baya cikin rawar jiki har suka iso tsakkiyar falon. Wani irin kyarma jikin Yaya Abubakar ya shigayi na tsantsar ɓacin rai, ya yunƙura zai nufesu Ummi da jikinta ke karkarwa itama tai saurin damƙe hannunsa tana girgiza kanta.
Idanunsa ya rumtse da ƙarfi cikin tsumar jiki da riƙon da Ummi tai masa a kausashe ya ce, “Who are you?!”.
Shiru bai amsa ma yaya Abubakar ɗin ba, sai hannu da ya kai saman fuskarsa ya janye hiramin da ya naɗe fuskarsa da shi.
Lokaci ɗaya suka zabura a tare, har suna haɗa baki wajen faɗin…………✍
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI……_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*
*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽
#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
GIPHY App Key not set. Please check settings