Advertisement
*_Typing📲_
💥🔥🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥🔥💥
*HOHOHO WANI KAYA SAI AMALE, DON JAKI BAZAI ‘DAUKA BA, INA MATA MASU BUK’ATAR ‘DAGA DARAJARSU A WAJAN MAZAJENSU INA MATAN DAKE SHAN WULAK’ANCIN MIJI KO NA KISHIYA ,INA MATAN DAKESON ZAMOWA MOWA AGIDAJEN AURENSU TO ALBISHINRU MAMAN ZARAH YAR MUTAN SOKOTO TA SHIRYA TSAF DOMIN GABATAR MAKU DA ZAFAFAN KAYAN MATA MASU KYAU DA INGANCI WANDA BASUDA ALGUS ACIKI , AKWAI MAGANI DANAYI BINCIKE AKANSU DAN FARIN CIKIN MA’AURATA NAMU BA IRIN NASU BANE KAYAN MU NA DABAN NE NA ASALIN SAKKWATAWAN SHEHU MASU ABUN MA
🔥💥🔥💥🔥💥🔥🔥💥
kayanmu masu inganci ne masu ladaftar da kowane irin namiji💃🏻💃🏻💃🏻🔥
Kad’an daga cikin abubuwan da muke dasu 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Advertisements
Ingantaccen maganin nono , Wanda zai gyara maki nononki donmin dawo da martaban nononki acikin kankanin lokaci komai lalacewarshi kuwa sauran bayani sai mun had’u pc +234 703 425 1528
Maganin hips (hips up) Wanda zai ciko maki da hips dinki su cika suyi bul bul ga laushi dasu k’ara suyi dass abun sha’awar kowane namiji 🔥💥
Maganin infection Sha yanzu magani yanzu Yana fatattakar sanyi cikin kankanin lokaci magani ne na maza da Mata insha Allah kowane irin sanyi gareki kikayi amfani dasu anwuce wajan💥🔥💃🏻
Ingantacce Kuma sahihin maganin k’iba Wanda Zaki ciko acik kankanin lokaci zakiyi kibar ki Yar dai dai misali ki huta Zama da Rama Baki rasa ci ba Baki rasa sha ba amma kullum Ana kallon cewa kinada matsala agidan aurenki saboda wannan ramar , Rama batayi ba Sam Yar uwa😉😉
Sabulun wanka
Kalolin sabulun tsarki
Turaren tsugunno
Advertisements
Turaren al’ajab
Hatsabibin turare
Da sauransu 07034251528
Kalolin gumba👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Gumbar Dabino
Gumbar gero
Gumbar madara
Gumbar matsi
Gumbar ukku bala’i
Gumbar tada zaune tsaye
Gumbar sabon budurci
Gumbar sa buzu kuwa
Gumbar aya da kwakwa
Gumbar ridi
Gumbar mazari
Sarauniyar gumba 3in1
Da sauran kalolin da bansamu fadi ba,
Kalolin gari
Garin mallaka
Garin hutar da malaminki
dakan jaraba
Dakan Amare
Dakan Ni’ima
Dakan kishiya in bakiyi bani waje
Garin sa buzu kuwa
Garin buje.sharkaf
Garin Dan la’asar
Yayan hadiya mai suna dan la’asar
Original Dan goshi
Original Dan goshi (sabon salo)
Original man damo
Original man ayu
Kitsen damo
Sirrin tafin kafa
Sirrin farinjini na uwargida da amarya harma da yan mata
Kwallin idonka idona
Muna hada set na sirrin mallaka hajiya ba boka ba Mallam sai tarin sirrika kema kizama kowa agidan surenki👍🏼💃🏻💃🏻
Akwai hadin sabon budurci ga yarinyar data rasa budurcinta ta hanyar fyade ko yaudarar d’a namiji da izinin Allah akayi maki wannan hadin to an wuce wajan sauaran bayani sai mun had’u pc 💥🔥
Kalolin tsumi👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
Tsumin mallaka
Tsumin jaraba
Tsumin madarar ni’ima
Tsumin tabaje
Tsumin Amare
Tsumin sabon budurci
Tsumin nono raƙumi
Matan gaske
Ruwan jaraba,
Da sauran kalolin da ban fada ba
Kalolin matsi da basuda illa ajikin mace sai dai ma sukara maki lafiyar HQ💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Matsin Dan mannau
Matsin mallaka
Dan la’asar
Sabon budurci
Mak’alemata
Mashahurin matsi
Ukku bala’i
Matsin uban budurwa
Akwai gumba ta matsi wadda Shanta akeyi ga matan da basa son yin matsi
Muna hada set ga wadda Allah ya jaranfa da matsalar fyade har yarasa budurcinta , muna hada mata kaya ingantattun don dawo da martabar ta,
Hohohohoho in ana dara fidda uwa ake
*Kyallen al’ajabi* babban sirrin mallaka mai abun al’ajabi mallaki naki don samun damar shiga cikin jerin mata masu fada aji a gidan mazajensu ,
KARKU manta da sunan maman zarah sokoto sayen nagari maida kudi gida🥰🥰🥰🥰🥰👍🏼👍🏼👍🏼👍🏼
07034251528 ina maraba daku sayen daya ko sari ina Sokoto sannan ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah🤝🏼🤝🏼
Ga Wanda suke bukatar ganin kalolin kayana to suyi sarving number na suyimun magana nayi sarving number ku zaku dinga ganin kalolin kayana a status ngd sosai 07034251528
Maman zarah mabera sokoto state💥🔥💥🔥💃🏻
_____________________
*_Chapter Twenty Eight_*
………….“Shuraim!!”.
“Sunana ne”.
Ya faɗa cikin izza da garada yana gyara zaman bindigar akan Ammar da yay surrender suna cigaba da takowa tsakkiyar falon har gaban Ummi da gaba ɗaya jikinta tsuma yake da kyarma..
Cikin raunin murya da tashin hankali ta dubi Ammar tare da maida kallonta ga Shuraim ɗin. “Yaro dan ALLAH karka cutarmin da zuri’ata. Kar kai ƙoƙarin sakanka alkairi da sharri. Ka faɗa mana komi kake buƙata zamu maka, amma karka cutar da mu”. Ummi ta ƙare maganar jiri na neman kwasarta. Yaya Muhammad yay azamar tarota shima nasa jikin na tsumar ɓacin rai.
A kausashe yaya Abubakar da ke ta faman taunar lips ɗinsa ya ce, “Ummi barsa ya kawo kansa a dai-dai lokacin da ya da ce ai.”
“Dama sai da na auna lokaci sannan nazo”. Shuraim ɗin ya faɗa yana mai maida dubansa ga Yaya Abubakar. Sai kuma ya janye bindigar da ga kan Ammar. Nannauyan numfashi Ammar da ya gama sadaukar da rayuwarsa ya sauke a hankali.
Sai dai kuma ganin ya nufi Ummi gadan-gadan ya sakasu zabura kansa lokaci guda. Turus suka ja suka tsaya ganin yay ƙasa a hankali ya durkushe yay kneeling down gaban Ummi yana mai ajiye bindigar hannun nasa a ƙasa, ta re da haɗe hannayen nasa waje guda🙏🏻 yay ƙasa da kansa cike da nuna tsantsar nadama da girmamawa a gareta.
Ba Ummi kawai ba, hatta su Yaya Muhammad sagade sukai suna dubansa. Ummi da illahirin jikinta yay sanyi dan mace ce mai tsananin tausayi ta tsura masa idanu cikin wani irin kallon wasiwasi da shakku.
Kansa ya ɗago a hankali shima tare da ɗora hannunsa saman fuskarsa ya zare facemask ɗin fuskarsa ta ainahi ta bayyana.
Gaba ɗayansu zabura sukai baya a razane. “Yaya Isma’il?”. Ammar ya faɗa jikinsa na karkarwa da kaiwa durƙushe gabansa domin ƙafafunsa sun gaza ɗaukar nauyin jikinsa dan firgici.
Cikin takaici Yaya Muhammad ya ce, “Isma’il wane kalar shashashan wasa ne haka zaka danganta kanka da wannan fuskar da zukatanmu ke mana zargin mai ita ɗan ta’adda ne?”.
Ƙasaitaccen murmushi ya saki yana mai ɗago dara-daran idanunsa tamkar na zaki masu cikar gashi ya duba Yaya Muhammad.
“Yaya Muhammad ba wasa bane, zahirin gaskiya ce a gabanku. *_Isma’il Aliyu Hikima_* ne a gabanku. *_(Muhammad Shuraim Aliyu)_* Sannan kuma *_Master!_*”.
“What?!”.
Ammar ya faɗa yana ja da baya cikin tsuma. Haka suma su Yaya Usman bayan sukayi idanu waje.
“K..k…kana nufin kai ne Master? Gawurtaccen ɗan ɓarawon nan da ake nema ruwa a jallo?”.
Murmushi Master ya saki yana mai maida dubansa ga yaya Muhammad da yay maganar cike da son tabbatarwa da ƙaulani.
Hannu ya kai saman kansa ya sauke hular jacket ɗin jikinsa da ya kai har saman kai. Kafin ya miƙe da ga kneeling ɗin da yay yana kallon Ummi da ko motsin kirki ta kasa. A take idanunsa sukai rauni har wasu ƴan ƙwalla na taruwa a cikinsu. “Ummi dan ALLAH ki saurareni”.
Ummi da gaba ɗaya zuciyarta ta gagara gaskata abinda Master ya faɗa ta gyaɗa masa kai cikin sanyi da rauninta. Sai kuma ta duba su Yaya Muhammad da ke ta ƙyalli cikin shaddoji na zuwa ga amarensu. Da idanu tai musu umarni.
Ita ba abar wasansu bace, dan haka babu wanda ya nuna alamar musawa suka ƙarasa ga kujerun falon duk suka zauna.
Master ya ɗan sauke ajiyar zuciya yana jingina bayansa da kujerar da ya zauna tare da lumshe idanunsa. Tsahon minti ɗaya da wasu sakanni ya buɗesu a hankali yana tasowa zaune sosai ya fuskanci Ummi.
“Da farko zan fara da neman gafararki Ummi, matsayinki na uwa da nake kallo da kima da daraja bayan mahaifiyata. Tabbas kin bama Isma’il gata da kulawa irin wanda a kowane dare yake kukan kishirwar rashin samu tun daga ƙuruciya. Na shigo jikinku a dalilin kutse da Muhibbat taima rayuwata. Kafin isowa ta gareku da nufin yaudararku na hukuntata nazo, sai dai labarin ya canja tun a ranar farko, awannin farko, mintunan farko, sakannin farko. Ummi kece kika canja komai, a lokacin da zuciya batai tunanin sauyawar ba. Dan da ga lokacin da wanann hannun naki mai albarka da daraja ya sauka saman tsakkiyar kaina yayin da kike a gadon asibiti, kika furta kalma mai matuƙar tsada da girma a gareni komai ya canja.”
(Na gode ɗana. ALLAH yay maka albarka. Ya tsare rayuwarka da imaninka). “Wannan addu’a ce da kika ambata a gareni wadda zuciya ta daɗe tana ƙishirwa da bege”. Yay murmushi mai ciwo tare da kai yatsa ya ɗauke wasu guntun hawaye da suka ciko idanunsa suka taru a gefe.
Gaba ɗaya jikin su Yaya Muhammad yay sanyi. Duk sun tsaresa da ido.
Ya cigaba da faɗin, “Naji matuƙar fargaba da tsoro a lokacin da su Yaya Muhammad sukace bazasu amshi kuɗin aikin nan ba, dan ina tare da su batare da sun san ni ɗin wanene ba. Tabbas da basu amsaba Ummi bazan yafema kaina ba. A yau a kuma yanzu zan sanar daku wanene *_Master_*. Na zaɓi wannan lokacinne domin samarwa ƴan uwana kwanciyar hankalin shiga sabuwar rayuwa. Amma kafin sannan zan sake tabbatar muku Muhibbat tana hannuna”.
Duk da dama shi suke zargi maganar ta dake su matuƙa. Musamman da labarin ya canja salo zuwa Isma’il da Shuraim da Master duk abu guda ne.
“Kuyi haƙuri, badan na ƙuntataku na ɗauketa ba. Nayi hakane domin kuɓutar da ita”.
Wata nannauyar ajiyar zukata suka sauke kusan a tare. Ummi ta kai hannu ta share hawayen da suka ziraro mata har cikin ranta tanajin nutsuwa da ƙaguwar son jin wanene shi?.
“Aliyu Ibrahim Hikima shine sunan mahaifina. Shahararren ɗan kasuwa da sunansa yay shura matuƙa a wasu shekaru da suka shuɗa. Sunan mahaifiyata Maryam. Auren soyayya sukai da mahaifina duk da dangin mahaifiyata basa so sam. Ba komai yasa basa son auren ba sai dan mahaifina bashi da komai a lokacin. Su kuma mutanene masu dukiya. Dagewar da mahaifiyata tayi akan sai shi ne yasa babanta yarda ya bashi aurenta. sai dai ya tabbatar masa babu shi babu ita.”
Ya saki ɗan murmushi da cigaba da faɗin, “Ko’a jikinta ta amince da sharaɗin, saboda son da takema mahaifina bashi da iyaka. Anyi aurensu babu wani shagali aka mikama mahaifina. Dukansu basu damuba, dan su dai burinsu ya cika kawai. A farkon zama sun fara rayuwa mai cike da ƙuncin talauci da fatara, amma sai soyayyar da sukema juna tai matuƙar tasiri wajen mantar da su hakan. Shekararsu biyu a wannan hali na matsi da kakana ya sakasu batare da sun sani ba. Dan kuwa duk wata hanya da mahaifina zai samu kakana ke tosheta wai duk dan mahaifiyata ta magantu. Amma sai akai rashin sa’a ko’a jikinta. Sai ma shi Abbana ne kan damu musamman idan yay dubi da ga gidan data fito. Dan ƴar gata ce sosai Mamy na a gidansu, sannan ita kaɗai iyayenta suka haifa. Rayuwa ta musu tsanani sosai, gashi babu ciki babu alamar samuwarsa. Fahimtar komai zai iya lalacewa yasa mahaifina ɗauke Mamy na suka bar garin. Wannan tafiya itace sanadin canjawar komai.”
“A yayin tafiyarsu sukai gamo da wani dattijo wanda alamu suka tabbatar da ba ɗan ƙasar nan bane. Dattijon nan shine ya fahimci akwai damuwa da talauci tare da su, dan ko kuɗin mota ma basu da isashe. Shine ya biya musu kuɗin mota na inda zaije, dan ya fahimci su kansu basu san ina suka dosa ba. Tafiya mai nisan zango ta kaisu wani gari dake akan gaɓar barin ƙasa. A garin suka kwana wajen dattijon nan daya hanasu matsawa ko nan da can, washe gari da safe ya sake basu umarnin su bishi. Mahaifina bashi da wata mafita banda ya bisan, da yake lokacin duniya na bacci azzaluman basuyi yawaitar yanzun ba. Sun sake yada zango a ƙasar Niger. Inda sukai kwanaki biyu anan dattijo ya kammala harkokinsa. Koda ya sake tabbatar musu gaba zasuyi basu damu ba, suka nuna masa amincewarsu. Yaji matuƙar daɗin yanda suka aminta da shi babu bincike ko nuna shakku”.
“Bara dai karna jaku da nisa. Daga ƙarshe Iyayena sun tsinci kansu ne a ƙasar haihuwa ta wannan dattijon. Tun a tarbar da akai musu suka fahimci dattijon nan da ko sunansa bai sanar musu ba ƙasurgumin mai arziƙi ne. Yayinda suka isa katafariyar daular sa kuwa sai mamaki ya kamasu na dalilin zuwansa ƙasarsu, dan kuwa dai ya fito ne da ga gidan sarauta mai faɗa a ji da tarihi. Dattijo yasa an karrama rayuwarsu da basu muhallin zama mai tsafta. Bayan kwana biyu sun huta ya nema jin labarinsu. Mamana taso a ɓoye. amma sai babana yace su faɗa masa gaskiya kodan karamcin da yay garesu. Wannan dalilinne ya sakasu fayyace masa komai na rayuwarsu har barowarsu gida. Ya nuna tausayawa a garesu da ga ƙarshe ya ɗauka mahaifina ya ɗaura akan dukiyarsa. Amana da jarumtar da Abbana ya nuna wajen tsare dukiyar da nuna gaskiya yasa Dattijo yarda da shi, harya maidashi babban yaronsa makusanci, komai ya koma hannunsa. Wannan abu ya baƙanta ran ƴan masarautarsu ƙwarai da gaske. Harma da sauran yaransa da ke hidima ma dukiyar kafin zuwan su Abbana. Ƙiri-ƙiri suka ɗauka karan tsana suka ɗorama Abbana, kullum cikin masa gorin shi din baƙon haurene suke.”
Rayuwa ta sauyama iyayena. Dan cikin ƙanƙanin lokaci dukiya ta bunƙasa garesu. Basu da wata matsala sai ta rashin haihuwa da tsangwamar mutane. Haka suka cigaba da haƙuri da juriya na tsahon shekaru har ALLAH ya azurtasu da samun cikina. Sunyi matuƙar farin ciki, irin wanda baki bazai misalta ba. Hakama Dattijo Isma’il yayi farin ciki tamkar shi za’aima haihuwar, dan shima bai taɓa haihuwa ba. Bayan cikina ya cika watanni tara aka haifoni, inda naci sunan dattijon nan wato Isma’il. Sai dai kallon mahaifi da babana ke masa yasa sukemin alkunya da suna Muhammad Shuraim.”
Na tashi ɗan gata a wajen dattijo Isma’il da mahaifana. Yayinda tsiraru a cikin jama’ar masaruta ke sona. Wasu ko yanda suka tsani mahaifana haka suka tsaneni duk da ƙanƙantar shekaru na. Shekarata uku a duniya Abbana ya maido mamana ƙasarmu ta haihuwa saboda bazai juri tsangwamar da ake musu nima aimin ba. Dangi sunyi murna, sun kuma sha mamakin ganin ya kuɗance lokaci ƙanƙani. Dan yama take kakana ya shanye dukiyar da suke ƙinsa a dalilinta. Koda ya ajiyemu komawa yay ya cigaba da lura da dukiyar dattijo. Daga ni iyayena basu sake samun wani cikin ba har na kai tsahon shekaru takwas, kafin mamana ta wayi gari da ciki. Nanma sunyi murna, hakama ƴan uwa, musamman ma ni. Cikin mamana na watanni uku ciwo ya kai dattijo Isma’il ƙasa, wanda ake zargin sammu akai masa. Mahaifina shine ya koma jinyarsa, dan ƴan uwansa kowa ya noƙe, burinsu kawai ya bar duniya suhau kan dukiyarsa har matansa.”
“Dattijo Isma’il ya riga yasan da wannan tun ba yanzu ba, dan haka a wani dare ya zaunar da mahaifina cikin dauriya ya sanar masa ɗunbin dukiyarsa daya tattare ya killace batare da sanin masu jiran ya wuce su hau kai ba. Gaba ɗaya ya mallakama mahaifina wanann dukiya, sannan yay masa umarni da ya bar ƙasar bayan ya damƙa masa fuskokin jabu (Facemask) guda uku yace koda ya dawo ƙasar haihuwarsa ya cigaba da amfani dasu shi da mamy na da ni dan yasa ƴan uwansa zasu bibiyesa bazasu barsa ba. Mahaifina yayi kuka sosai a wanann dare, kuka irin wanda ɗa ke yi yayin rasa mahaifa ko yin nesa da su. Shidai dattijo Isma’il nasiha yayta masa da addu’oin fatan alkairi da gamawa da rayuwa lafiya. ALLAH sarki rayuwa ashe nasihar ƙarshe ce, dan kuwa a safiyar wannan ranar aka wayi gari da rashin dattijo Isma’il. Abbana ya shiga ɗimuwa matuƙa harma ya rasa ina zai saka kansa. Yayinda tsoro ya kamashi ganin yanda matan dattijo da danginsa tun kan akai gawarsa harsun fara rigima akan dukiyar da suke tsammanin ya bari. Ana kai gawar dattijo Abbana ya silale ya baro ƙasar da dukiyar daya mallaka masa bisa umarninsa. Inda yabar baya da ƙura. Dan kuwa dattijo kashi uku ya raba dukiya yabar musu kashi guda kawai. Wannan dalilin yasasu farga da rashin Abbana da wuri saboda sunce a nemosa yay musu bayanin ina sauran dukiyar take.”
“Abbana ya dawo ƙasarsa ta haihuwa cikin zuri’arsa, sai dai kuma anyi rashin sa’a dangin dattijo nacan na bincike a kansa har suka gano inda yake. A nan kuma ɓangaren Abbana koda ya dawo ni kaɗai suke sakama Facemask idan za’a kaini makaranta ko zan fita waje. Su mutane a tunaninsu baƙon yaro mukai, shiyyasa basu taɓa kawo hankalinsu a kaina ba. komai ya sake canjawa. hankalin iyayena ya kwanta, sunan mahaifina ya sake yin shura musamman akan harkar kasuwanci. A ƙanƙanin lokaci ya zama bashi da abokan mu’amula sai manyan mutane, a ƴan uwa kuwa dama zuwa yanzun iyayensu duk sun rasu, babu wasu shaƙiƙai na jini dan shima tamkar Mamyna shi ɗaya aka haifa a gidansu, baima san mamansa ba.”
“Lokacin da cikin Mamy na ya shiga watan haihuwa a lokacin komai ya sake canjawa, dan kuwa dai dangin dattijo sun ƙaraso ƙasar nan batare da sanin Abbana ba. Hasalima har sun kammala bincike akansa da inda yake.”. Hannu ya kai ya ɗauke ƙwallar da suka cika masa ido, kafin ya cigaba da faɗin, “Ranar da bazan taɓa mantawa ba. Rana mafi ciwo da zafi, ranar da duk nisan tarihi bazai gogeta ba a gareni itace ranar juma’ar dana rasa iyayena duka. Dan kuwa dangin dattijo da taimakon wasu hatsabibai sukaima gidanmu dirar mikiya. Hankalin mahaifina ya tashi, dan ya tabbatar tamu ta ƙare, amma sai cikin jarumta ya faɗama mahaifiyata duk tsanani karta buɗe ƙofa shi zai fita shi kaɗai, idan kuma zamanta da nawa bazai yuwu ba ta tabbatar ta fita zai janye hankalinsu, ta kuma sakamin facemask ɗin wajen dattijo itama ta saka nata. Mahaifiyata na kuka ta shiga roƙonsa kar yaje amma sai ya lallasheta da bata ƙwarin gwiwa. Ya fita garesu, inda suka zagayesa da mahaukatan makamai tare da basa umarnin fiddo musu dukan dukiyarsa. Gane dangin dattijo da yay ya sakashi yarda zai basu, tare da roƙonsu idan ya basu su barsa da ransa cikin iyalansa. Sun nuna sun amince, dan haka Abbana ya tattara kuɗaɗen ya basu harma da dukkan takardun kaddarori suna kammala amsa ɗaya da ga cikin dangin dattijo cikin bada umarni yace (Master kashe shi). Shigar wannan furuci a cikin kunnena ya sani fashewa da kuka a cikin dakin da muke maƙure ni da Mamy. Na mike a razane da nufin fita Mamy ta hanani. Kuka nake ina fisgewa har na samu damar guduwa na leƙa ta jikin window. A dai-dai wanann lokacin wanda aka kira da Master yasa yaransa suka kama Abbana suka danne yay masa yankan rago cikin rashin tausayi da rashin imani duk da kwata-kwata shekarunsa bazasu gaza ashirin ba a duniya”.
“Kuka na fasa wanda ya jawo hankalinsu ɗakin da muke. Cikin bada umarnin ɗan uwan dattijo ya ce muma a kashe mu. Hankalin Mamy da ya fara gushewane ya dawo jikinta saboda tuna wasiyyar Abba. Cikin rawar jiki ta kama hannuna muka fita ta ƙofar baya su kuma suna ƙoƙarin buɗe ƙofar. Kasancewar a cikin falo komai ke faruwa muka fice a gidan ina kuka mahaifiyata na kuka jini na zuba a jikinta ga tsohon ciki. Tafiya muke ta ceton rai dan kuwa suna buɗe ƙofa sukaga alamar mun fita ta ɓarauniyar hanya sai suka take mana baya. Fahimtar ana binmu yasa Ummi cikin galabaita ta ce naje kawai. Kaina nake girgiza mata ina kukan ni bazanje ko ina na barta ba. Sanin taurin kaina yasata juriyar cigaba da tafiya batare da mun fahimci inda muke jefa ƙafa ba dan gari yayi shiru kasancewar dare ya tsala. Sosai Mamyna ta sake galabaita, saboda alamar haihuwa data zo mata gadan-gadan, ga jini na zuba mata. Yanke jiki tai ta faɗi, na durƙusa a gabanta ina kuka da kiran sunanta ta tashi, amma ina bazata iya ba. Cikin amincin ALLAH mutumin da muke a ƙofar gidansa yaji kukana ya fito. (Sun kashemin Abbana da Ummina baba sun kashesu) na faɗa cikin kukan daya saka Hankalinsa tashi ya kamani ya muƙar tare da ɗaukar Mamy gaba ɗaya ya shige damu cikin gidan. A daidai lokacin su dangin dattijo da ke binmu suka iso ta ƙofar gidan tare da ƴanta’addan hayarsu. Sai dai rashin tabbatar da muna anan ɗinne ya sasu wucewa dan baban nan daya taimakemu ƙarar tahowarsu ta sakashi sa hannu ya toshen baki. Wucewarsu da kamar mintuna biyar naƙudan mamana ya tsananta. Baba ya rasa yanda zaiyi dan bashi da mata. Haka yanaji yana gani ya sama Mamyna ido harta haihu. A galabaice ta damka amanarmu a hannunsa tare da roƙonsa da cewar ya kaimu gidan marayu dan zama anan gidan bazai bamu tsaro ba tunda ta tabbatar dangin dattijo Isma’il sun gama sanin komai a kammu da kamanina na gaskiya tun kan suzo garemu. Tana gama faɗar haka ta bar duniya.”
“Na ɗanɗana raɗaɗi biyu na zafin rashi a dare ɗaya a kusan lokaci ɗaya. Ga kuma ƙani Ummi ta haifamin. A taƙaice dai a ɓoye dattijo ya samo maƙwafta sukai jana’izar mamyna a washe gari da safe, bayan wata tsohuwa ta suturtata. Bani da wayo sosai dan shekarata tara kacal. Amma na shiga damuwa sosai. Dan ma kallon jaririn Mamy na ɗan ragen jin zafi. Wasiyyar Mamyna tasa baba ɗaukarmu a washe garin da Mamy ta cika kwana uku mu da shi duka muka koma gidan marayu gudun kar makasan su gano inda muke. Ashe shima bai taɓa haihuwa bane shiyyasa matansa duk suka gujesa.”
“Mun koma gidan marayu da zama inda baba ya tambayeni sunan da zai sama jaririn Mamy na ce Habib. Babu musu baba yay masa huɗuba da suna Habib. Nine na cigaba da rainon Habib a gidan marayu, tare da matar da ke kula da mu da baba wanda a yanzu shine tamkar mahaifina. Karku manta inada facemask ɗin da dattijo Isma’il ya bama Abbana. Kuma ni kaɗai nake sakawa su basa amfani da ita. A kuma lokacin da zamu fito Mamyna ta ɗauka ta sakamin ita. Kuma koda muka zo gidan marayu ban cire ba na cigaba da amfani da kayana batare da kowa yasan ainahin fuskata ba”……………✍
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI……_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*
*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽
#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
GIPHY App Key not set. Please check settings