TAKUN SAKA 29

Advertisement

 

*_Typing📲_*

Albishirinku mata💃.*

shin Ina ma’abota ado da kwalliya🗣️? Ina team no makeup🗣️? Mata gareku ina mai tabbatar muku dacewa duk wanda takeneman kayan gyaranjiki walau matsalan fata kike fama dashi kamarsu pimples, tabo, sunburn,nankarwa, knuckle ko Mai Kika shafa yabatamiki jiki Dama sauransu walau Kuma kawai kinasan kigyara fatarki kizamto tauraruwa abarso abar marari agurin kowa😍Mata inamai tabbatar muku

dacewa kujaraba kayan mg’s skincare Koda gudane dg cikin kayansu kuga abun mamaki🧚🏻‍♀️ domin kayansu kankat ne Koda iya sabulunsu Kika Dana saikinfita zarra cikin Mata domin ynd fatarki zaikoma Shar kamar Madara kidinga kyalli kina haskakawa duk inda kikayi se ankalleki😘Kuma wani abun jindadin ma shine duka kayansu organic ne  Babu na bleaching kawai zaigyaramiki jikine yafiddomiki d ainihin natural beauty dinki inma NASA haske kikasiya natural ne kawai bn bleaching b💁‍♀️mekike jira hjy maza garzayo kinemi naki acikin farashi merahusa kigyara jiki kiyi fes abinki baruwanki da sekinyi kwalliya inzaki fita😃kifita aganki da zallar kyawunki hjy😍kanawa mutanenmu ina godiya Kuna nunama mg’s one luv tnx for ur patronage dama Yan sauran state mg’s na godiya may your pocket never lck azo asiya Kaya hilis karnakoma kauyenmu🥺Yar shawarmannan karta gagareni🤧😂

Henajiku lvs🤭

Meso should chat

08062991549

07046881166

Call 08064532391

Advertisements

Soap:3k, beauty kit:11k,bridal kit 18k

Instagram:glow_with_mgs

Facebook:mg’s skincare

Team glow✅

 munayin makeup Yan kaduna gamai bukata ze iyazuwa nd munazuwa gida shima in anaso

08062991549

_________________________

Advertisements

*_Chapter Twenty Nine_*

…………..“Ina da son yara matuka, duk da ban son yawan hayaniya da yawan magana. Sannan kuwa nima yaro ne, hakan yasa a koda yaushe zaka ga yara zagaye da ni musamman saboda Habib da wasu jariran biyu da mama mai kula damu take raino tare da Habib. Wannan dalilin yasa suka taso tamkar ƙannena a gidan marayun, idan sukai laifi nike hukuntasu na musu faɗa, sannan nine ke kula da karatunsu dan mun cigaba da zuwa makaranta musamman ma ni dana fara secondary a wajen gidan marayun da baba ke kaini da kansa kullum bayan na ƙarasa shekara ɗaya a primary ɗin gidan marayun. Mama mai kula damu ce ta sakamin suna Master duk da bana so banƙin amsa mata. A hankali sai sunan ya bini a gidan kowa ya koma kirana da Master har su Habib”

          “Ina girma sunan Master daya kashe Abbana na ƙara zama a ƙwaƙwalwa ta fiye da karatu, a gefe kuma da an tashi a makaranta nake tafiya talla batare da sanin baba ba da hukumar gidan marayu. Kai wani lokacin ma bana zuwa makarantar gaba ɗaya. Da kuɗin sana’ar nake sayoma su Habib sweets, biscuits da kayan kwaɗayi na yara. Tun kowa bai farga ba har suka farga dani. Baba ya dinga min faɗa, sai dai da ga ƙarshe kuma da kansa ya bani kuɗaɗe da bawani yawane da su ba na cigaba da sana’ar dan ya fahimci inaso. Saboda tunda aka hanani saina ɗauka ƙunci da fushi na sakama kaina.”

      A lokacin dana kammala secondary su Habib suka shiga na fara tunanin kutsa kaina cikin ƴan jagaliya, dan na gama nazarina kaf ta wannan hanyarne kawai zan iya nemo Master daya kashe mahaifina. Anan ɗin ma batare da sanin Baba ba na faɗa cikin ƴan daba tare da zama da kaina naima facemask ɗina wasu gyare-gyare saboda ni mutum ne mai fasaha matuƙa tun ina da ƙarancin shekaru, sai dai ALLAH ya tsareni bana shan komai na maye, duk sanda kuma zasu aikata tsiyatakunsu nasan ta yanda zan zille musu. Dan na shiga cikinsu ne kawai dan neman ilimi da kuma neman Master. A gefe kuma na takura baba akan mubar gidan marayu, dan na tabbatar zan iya rikemu mu duka da sana’ata da zuwa lokacin tayi ƙwari na daidai talaka mai neman cin yau da gobe. Da ƙyar baba ya yarda muka dawo cikin mutane da zama a gidansa ɗin nan da muka bari shekarun baya. Ni na cigaba da buga-bugar karatu akan su Habib duk da lokacin dai da ɗan saukin wahalhalu akan mai karatun secondary. Yayinda niko a dalilin ƙoƙarin da ALLAH ya bani wani bawan ALLAH ya ɗauki nauyin karatuna na jami’a a ranar taron tshoffin ɗalibai da akai na makarantarmu.”

        “Na cigaba da kutsa kai cikin ƴan daba ina neman Master a sirrance har ALLAH yasa na dace na kasance ɗaya da ga cikin yaransa, dan zuwa yanzu ya matuƙar gawurta. Cikin ƙanƙanin lokaci na zama amintacce a wajensa, dan ina bala’i-bala’in kwantar masa da kai har sauran yaransa najin haushi da takaici na. Ban damu ba, dan tunaninsu da nawa dabanne suke haukarsu. A zahiri ina cigaba da karatun jami’a. Baɗini ina karantar kowanne motsi na rayuwar Master, gefe kuma ina kasuwancina da ALLAH ya sakama albarka mukeci muke sha ni da waɗan da nakema kallon ƙanne kuma ahalina bayan Habib. Bayan kammala jami’ata na shirya takanas na kaima wanda ya ɗauki nauyin karatuna result ɗina dan ya gani, tare da sake masa godiya. Yaji daɗi, ya kumayi farin ciki a take anan ya bani jari mai kauri da zan iya riƙe kaina harma da ƙannena.”

          “Koda na dawo na nunama baba ya sanyamin albarka, ya kuma bani shawarar maida hankali akan kasuwa basai na jira aiki ba, na amince da shawararsa dan haka na ƙara jari akan kasuwancina, UBANGIJI mai rahama dan-danan harkoki suka buɗe na canja mana gidan zama, na kuma koma makaranta nima. Domin cigaba da karatuna akan computer a wajen ƙasarnan. Tunda na tafi ban dawo ƙasata ba sai da na kammala karatuna. Amma koda yushe ina sanin motsin su Habib. Tun kafin na dawo na gama tsara yanda an tunkari master, dan kuwa na samo horo na musmman akan abubuwa masuyawan gaske.”

             “Yarana sunyi farin ciki da dawowata nima kuma nayi farin ciki da ganin sun zama manya sun kuma sake hankali. Sai dai kuma na iske baba babu lafiya. Hankalina ya tashi matuƙa dan ina sonsa hakama su Habib, duk muna masa kallo ne na uba. Kwanana biyar ALLAH yay ma baba rasuwa. Tabbas munji wannan mutuwa dan su Habib kuka rurus suka dinga yi suna sake ɗaga hankalina. Sai da na dage matuƙa suka dawo hankalinsu. Da ga lokacinne na fara basu horaswa ta musamman da basu san manufarta ba. Na kuma sake komawa cikin su Master da zuwa yanzun dukkan sirrinsa a tafin hannuna yake, dan dukkan abokan mu’amularsa a cikin manya da ƴan ta’adda irinsa na sansu nasan inda suke, nasan makamar harkokinsu. Na iya maganarsa. Na iya salon tafiyarsa na iya abubuwa da dama irin nasa wanda inhar na juye maka shi baka isa cewa bashi ɗin bane, musamman idan na saka mask na fuskarsa. Indai taƙaice muku zance a wani dare batare da sanin kowaba a cikin yaran Master na ɗaukesa, zuwa safiya na maye gurbinsa, yaransa kuma duk nabi hanyoyi daban-daban aka kamasu ɗaya bayan ɗaya ta yanda babu yanda ubannin gidan Master zasu iyama ganosu balle cetonsu………”

       “Kenan yanzu duk kuɗin da ake sata a banki da sunan Master wancan ne ba kaiba Yaya Isma’il”.

    Ammar ya faɗa cikin katsesa da zaƙuwar son jin yaya take ne.

        Wani ƙasaitaccen murmushi Master ya saki. tare da kai hannu ya shafa kan Ammar. “Da ga shekara biyu zuwa yau duk nine”.

     Kai Ammar ya jinjina cike da gamsuwa. Sai faman murmushi yake dan shikam jin wata sabuwar ƙaunar shi yake har cikin jini da ɓargo duk da har yanzu bai faɗi dalilinsa na wawasar kuɗaɗen ba bayan dalilin kama Master daya kasance mai laifi a garesa.

       Master ya cigaba da faɗin, “Na shigo rayuwarku ne a dalilin Muhibbat, sai dai labarin ya sauya adalilin karamcin Ummi da ku kanku. Sai kuma randa na jima Halilu ciwo saboda ranar na fara ganinsa a gidanku, na kuma sansa a matsayin yaron su Alhajin Mande. Wannan dalilin ne ya sani yin bincike akanku sosai harna gano mummunar manufar da yake da ita a kanku. Cikin sa’a kuma abinda yake shiryawa a kankun sai aikinsa ya faɗo hannuna duk da dai nina saka A.G yay hakan batare da shima ya sani ba. Shiyyasa na koma ta bayan fage nazo ma Muhibbat matsayin Muhammad Shuraim. A lokacin da naita bibiyarta nine da kaina. Sai dai kuma ƙanina Musbahu shine yake zuwa gareku da fuskar Shuraim. Yayinda shima kansa baisan niɗin nine Isma’il ba, na kuma cigaba da ɓoye musu zahirina saboda wani dalili nawa daban. Dan basu taɓa sanin ainahin fuskata ba duk da kuwa tun suna ƙanana suke tare dani. Sannan basu taɓa sanin aikin dana tsundumasu a ciki munayi tare ni miye dalilinsa ba. Tsabar biyayya da soyayyar da sukemin ce kawai tasa basu taɓa min musu ba akan komai da nace suyi. Domin gaba ɗayansu na horar da su akan harkar Computer.”

      “Kune mutane na uku da kuka san ainahin fuskar Isma’il bayan iyayena da baba. Wanda da farko naje asibiti da wata fuska ne daban, a dalilin Ummi naji bazan iya zuwa mata a baɗinina ba shiyyasa na sake komawa na biya kaso ɗaya bisa ukun kuɗin aikinta bayan na biya duka a farko. A yau kuma na zaɓi bayyana muku zahirin gaskiya ne a dalilin Ummi. Banason ta shiga wani hali akan rashin Muhibbat, sannan ya kamata kusan wane ƙudirine a zuciyar Halilu kar yabi ta wata hanyar ya cutar da ku idan yaga ban masa aikinsa yanda yake so ba. Dan na tabbata zai binciko gidan nan yanzu hakama dan a rikice yake kuma shi mutum ne kamar sauna idan ya ƙwallafa rai akan abu.”

         “Na ɗauke Muhibbat ne saboda bin bayan Halilu da tai ranar ɗaurin aure batare da kun sani ba, yayinda ta jiyo sirrikansa masu yawa. A ranar ɗaurin aure yawan mutane yasa bazaku fahimci bana tare da ku ba. Amma kuma nazo, sai dai ganin fitowar Muhibbat da duk da ta saka hijjab da Niƙab na ganeta ya sani fasa bin ƴan ɗaurin aure nabi bayanta. Sai da na tabbatar da inda ta nufa sannan na  koma gida a hanzarce, amma tunkan na ƙarasa na kira Habib ya sameta a wajen, hakama maigadin gidan halilun, saboda duk gidajensu na sirri da suke aikata tsiyatakunsu akwai yarana a ciki, amma ba cikin su Habib ba. wasu masu gadi, wasu masu musu aikin gidan batare da sun sani ba. Aurenku kuwa da yaransa dama can na shirya wargazashi tsaf. Dama na tsara sai an kai Muhibbat gidana zaku san nine master, a gefe kuma na cigaba da kasancewa daku matsayin Isma’il. To sai akai rashin sa’a autar Ummi ta buɗemin aiki saboda rashin jinta”.

       Murmushi Ummi tayi da kai hannu ta share hawayenta. Suma su yaya Muhammad duk murmushin suke da sauke ajiyar zuciyoyi.

      “Kuyi haƙuri da fuskokin yaudara dana zo muku daban-daban. Ni kaina inaji haushin yaudarar Ummi, shiyyasa na zaɓi zuwa na bayyana muku kaina dan ku kanku ku sami nutsuwar shiga sabuwar rayuwa a yau. Hakama Ummi hankalinta ya kwanta kar garin neman gira a rasa ido dan bazan yafema kaina ba idan wani abu ya sameta adalilina. Auta na tare dani tana zubamin tsiwa da tsaurin ido Ummi, sai dai banason ta san niɗin wanene yanzu har sai nan gaba. Aiki akan Halilu kuwa ita daya raina itace zatayi komai da kanta insha ALLAH”.

         Dariya duk sukayi, Yaya Abubakar da gaba ɗaya ya tsunduma tunani da nazartar labarin Isma’il Master yay ɗan murmushi, “Ai ni auta kamar ba’a gasa mata baki wajen wankan jego ba. Dan wannan bakin natane ya jefata a tarkon jami’an tsaro su A.G sukaso yin amfani da ita. To ashe wanda suke bulayin neman shi tuni ya gama neme su”.

        Nanma dariyar suka sanya. Yaya Umar ya karɓe da faɗin, “Ai bakin auta ya mana rana. Tunda gashi ya jawo mana Master har cikin gida batare da mun saniba. Sai dai muna son sanin ƙyaƙyƙyawar manufarsa kodan mu cirema ranmu zarginsa a jerin na ɗan ta’adda ɓarawo da kowa ke kallonsa da shi.”

      “Wannan gaskiya ne yaya Umar. ALLAH ya jikan su Mamy yay musu rahama ya saka musu, amma ya kamata musani kam”.

        Cewar Yaya Usman da hawaye suka ziraro masa na tausayin Master ɗin. Gaba ɗaya suka amsa da amin, sannan suka shiga ƙara jero sabuwar addu’a ga mahaifansa. Ummi kam tama gaza cewa komai. Dan zuciyarta a matuƙar raunane take da tausayinsa. Yayinda a gefe takejin matuƙar nutsuwa da kasancewar sa miji ga ɗiyarta ɗaya mace tilo marainiya duk da yaƙi faɗar dalilin nasa na shiga wannan harkar, sai dai tana masa ƙyaƙyƙyawan zato. Sai ɗunbin al’ajab na son zuciya da shahara a zalunci na Halilu wanda suma su Yaya Muhammad ɗin duk yake cin zukatansu……

     Master ya katse tunanin Ummi da faɗin, “Ƴan uwana kuyi haƙuri wannan sirri ne mai matuƙar daraja a gareni, badan ban yarda daku ba kuma na ɓoyesa. Insha ALLAH zaku san dalilina wataran. Na yarda ku san niɗin wanene saboda kuma kun sanar dani sirrinku a lokacin da baku gama sanin niɗin wanene ba. Kun kuma yarda dani duk banzo muku a yanda kukai tsammanina ba. Dan ALLAH ina roƙonku ku bizne wannan sirrin a wannan falon har sai ranar da ya kamata gaskiya ta bayyana kanta ga kowa”.

         “Tabbas ita amana abuce mai nauyi Isma’il. Kuma ka cancanci muriƙe maka ita dan kaima ka riƙe tamu, yayinda kaketa hidima da gwagwarmaya a kanmu batare da mun sani ba. ALLAH ya saka maka da alkairi, ya cigaba da baka kariya akan ayyukanka. Ya kuma baka ikon sanar mana dalilin naka wataran. Bani da haufi game da sauran ƴan uwana akan riƙe maka wannan sirrin, dan nasan mahaifiyarmu ta mana horo akan hakan tunba yanzuba. Ballema wannan sirin riƙesa a garemu tamkar rike namu sirrine. Fita da shi kuwa tamkar tozarta kammune.”

       Yaya Abubakar ya amshe da faɗin, “Wannan gaskiyane Yaya Muhammad. Insha ALLAHU bazakai baƙin ciki akanmu ba Isma’il. A matsayina na jimi’in tsaro kuma zan cigaba da baka gudunmawa insha ALLAH a duk sanda kake buƙata, sai dai ina roƙonka ka tabbatar duk abinda kake aikatawar nan kanada hujja ta gaskiya aranar kare kai, dan idan naci karo da saɓanin hakan komai zai iya faruwa”.

        Murmushi yayi na ƙasaita yana jinjina kansa, “Nagode matuka yan uwana da Ummin mu. Abubakar karka damu kaima insha ALLAH, dan na jima da saninka da kuma gaskiyarka da ƙwazon aiki.

         “Shiyyasa kazo kaketa min ƙafar angulu akan auta ko?”. Yaya Abubakar ya faɗa cikin barkwanci.

    Dariya suka sanya baki ɗaya. Banda Master da murmushi ne kawai nasa dan dama can yawan fara’a ba ɗabi’arsa bace. Sunema yake sakewa da su matuƙa fiye da zato da hasashe. Duk da dai lokacin baya yana zuwa musu ne da fuskar mutane masu sanyin hali saboda salon acting daya ƙware akai like wani ɗan film. Miƙewa yay yana duban agogo ganin dare yaja. “Kai kai bara na barku kuje ga amare fa Yaya Muhammad kar mu take shari’a. Ummi samin albarka na gudu nima”.

         Kansa Ummi ta dafa tana murmushi dan ita kallon ɗa take masa bawai suruki ba. Tai masa addu’a da sanya albarka saboda har yanzu zuciyarta bata gama dai-daita da sheɗancin da Halilu ke shiri akansu ba. Dan ma bataji yana aikata ƙazantar luwaɗi ba kenan. Sallama yay musu ya fita akan zai dawo zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu dan zai zama busy a satin nan.

     Har ƙofar gida su Yaya Umar suka rakoshi zukatansu sakayau bakamar yini da kwanan jiya ba da suka kasance a damuwar rasa Hibbah. Yana tafiya suka rufe gidan suka dawo ciki, zukatansu kuma fal tunanin miyasa yake aikata yahoo? Dan suna buƙatar sanin hakan kodan ƙanwarsu da ke a hannunsa matsayin mata. Bazasu so ta kasance a gararin rayuwa ba, ba kuma zasu so ta kasance da mijin da zai ciyar da ita ta hanyar haram ba.

       Sun so zama su tattauna maganar Ummi ta korasu suje ga matansu da safe zatai magana da su. 

      

★★★★

     Tunda yabar gidan su Ummi ajiyar zuciya yaketa faman saukewa da dafe kai saboda ciwon da yake masa na rashin sabon dogon surutun daya zuba a yau. Sai dai kuma yanajin zuciyarsa sakayau tamkar ya sauke wasu kaya masu azabar nauyi dake a kansa ne. Sai da ya biya ta gidan A.G ya amshi takardun aikin Abba sannan ya wuce gida.

       Koda ya isa gidan a falo ya samu su Habib sun baje kowa da hidimar da yakeyi, ga kayan ciye-ciye sun baje tamkar wata sabuwar bola. Shigowar tasa ce ta saka falon ɗaukar shiru kowa ya nutsu. Cike da girmamawa a garesa tamkar yanda suka saba suka shiga masa barka da zuwa. Hannu ya ɗan ɗaga musu yana bin falon da kallo fuska a tamke da binsu da harara. Sun san laifinsu dan haka suka shiga sosa ƙeya kowa na kai hannu a sace yana ɗauke ledar gabansa da su gwangwanaye.

    Komai baice musu ba ya nufi upstairs ɗin yana hawa steps ɗin a kasalance da izzar data zamewa gaɓansa jiki. A dai-dai nan Hibbah da yunwa da damuwa ke neman halakawa ta fito daga cikin ɗaki itama cikin ɗan layin barcin data fara tun bayan idar da salar isha’i. Abincin data hanga a shirye a dining ɗin falon saman ya sata nufar can duk da ta fahimci mai faɗa ajin gidan aka shirya mawa. Kujera taja ta zauna a fili take faɗin, “Daga gani shegen ci ne da wannan mutumin, tunda kuwa ya sakani kuka ɗazun na rantse da yunwa zai kwana shima mugu dangin su Halilu mtsoww ”.

       Karaf kuwa wannan zance a kunnen Master da ke hauro step ɗin ƙarshe. Cije lip ɗinsa na ƙasa yayi tare da kai dubansa gareta da lumsassun idanunsa da tsantsar gajiya da ciwon kai ya kanainaye. Ya ɗan sake tsuke fuska da nufar inda take batare da ita kuma tasan da shigowar tasa ba. Hidimar ma zuba lafiyayyen abincinsa da baba saude ta haɗa masa na musamman takeyi cike da mugunta. Ta ɗiba gasashen hantar da yaji kayan haɗin salad zata kai baki ya riƙe hannun…………..✍

*_Gashi nan harda na gobe idan ALLAH ya kaimu😌🚶🏻_*

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like