TAKUN SAKA 31

Advertisement

 

*_Typing📲_*

*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

Advertisements

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

_________________________

*_Chapter Thirty one_*

………..Tab ɗinsa data yasar a ƙasa ya ɗauka ya bar wajen batare da yako kalleta ba. Hakan yasa taɗan sauke ajiyar zuciya tana fitowa da ga bayan Baba Saude data ɓuya. Kallonta baba Saude da ke murmushi tayi. Cikin son tsokanarta tace, “Anya baza’ai ƴar gida ba anan ɗiyata?”.

     Cikin rashin fahimta Hibba tai ƴar dariya tana zama. “Baba Saude ina kwana”. “Lafiya lau”. Ta amsa mata da kulawa. Sai kuma ta ɗora da faɗin, “Ke da baki da isashen lafiya ya kamata kizo ki karya”.

      Kallon su Habib da suke tattare plates ɗin da suka gama tayi. “Baba nifa lafiyata lau ALLAH. Waya ce miki banda lafiya ne?”.

       Da sauri gudun karta ɓaro musu aiki Khalid ya ce, “Baba saude yau dama tuwon rana akai mana miyan ɗanyen kuɓewa”. Hankalinta ta maida garesa da faɗin, “To shikenan Khalid inhar suma duk suna so ai sai ayi.”

Advertisements

     A mamakin Hibbah da ke kallonsu sai gani tai sun hau murna harda rawa. Baki ta ɗan taɓe tana mikewa, a ranta ko tana ayyana taɓararsu.

       Duk yanda Hibba take dojema su Habib a wannan yini sai da ta saki jikinta da su ƙarfi da yaji, saboda yanda suke shiga lamarinta. Da ga ƙarshe sai gashi sun baje a falo suna hira tare cikin nutsuwa. Dan idan taso nutsuwar bazaka taɓa ɗauka ita bace. Ita kanta Baba Saude tayi mamaki. Takuma fahimci cewar gata ne kawai ke ɗawainiya da Hibbar.

      Tare suka shiga kitchen ita da baba Saude sukai girkin rana. Bayan sun kammala ta fito ta koma sama. Salla tayi tai kwanciyarta sai barci. Da ga haka babu wanda ya sake jin ɗuriyarta har bayan la’asar. Dan koda ta tashi tai salla sai tai zaman shan kukan kewar ahalinta. Sai kusan biyar ta fito falon.

     Kowa bata samu ba sai motsin baba saude a kitchen. Ta leƙa ta gaisheta tana tambayarta su Idris. Computers room ɗinsu baba sauden ta nuna mata. “Suna cikin can, suna dawowa da ga sallar la’asar babana ya kaɗasu can kinsan su ƙwararrune na na’ura mai ƙwaƙwalwa anan suke wasu ayyuka nasu da nima bansan kona minene ba”.

       “Na satar kuɗaɗen mutane mana”. Hibbah ta faɗa a hankali batare da baba Saude tajita ba. Ɗakin ta nufa, ganinsa a buɗe yasa ta danna kai da sallama. Shi kaɗai da ke tsaye a kansu ya ɗago ya kalleta. Su Salis kam duk sun duƙufa aikin gabansu. Haɗa idon da sukai yasata janye nata ta maida kansu Adam. Yanda suke sarrafa kwamfitocin sun matuƙar birgeta. Dan sai ka ɗauka bada hannu suke sarrafa keyboards ɗin ba tsabar ƙwarewa da yawan dannawar da suke a koda yaushe.

           “Guys are you ready?”.

Musbahu ya faɗa da ɗan ƙarfi. A tare suka haɗa baki wajen faɗin yes. Sosai Hibbah ta nutsu wajen kallonsu matuƙa, suko sunata aikinsu cikin maida hankali garesa har aka kira sallar magrib. Ganin ya kalli agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa da faɗin, “Lokacin salla yayi” ya sakata juyawa zata fita.

     “Hii Auntynmu”. 

Salis ya faɗa yana ɗaga mata hannu. Juyowa tai tai wani ɗan yaƙe tana ɗaga masa hannu sai kuma ta gimtse fuska da hararsa. Ya haɗe hannayensa alamar tuba fuskarsa ɗauke da murmushi kamar yanda suma sauran sukeyi mata. Sake tsuke fuska tai ta fice batare data sake tankawa ba.

      Tunda Hibbah ta koma ɗakinta taketa faman kai kawo na mamaki. Gashi takadari shu’umi, amma a ɗan kwanan da tai a gidan biyu ta fahimci sam baya wasa da salla baya barin su suma suyi wasa da ita. Anya bazata amshi tayin yimasa aikin na wata guda ba kodan ta yo leƙen asirinsa. Dan bata da wani babban burin da ya wuce ganin ta damƙa su Abba da dukkan mabiyansu ga hukuma kodan kuɓutar da kanta da ahalinta garesu.

     Wannan shawarar da ta yankema zuciyarta ne ya sata fitowa bayan sallar isha’i. Cikin sa’a kuwa ta samesa a falon saman shi kaɗai zaune yana aiki a system. Gefe kuma yana shan baƙin shayin da keta tashin ƙamshi. Sarai ya ganta ta gefen ido, sai dai a ransa yana mamakin ganin yanda ta fito a nutse tamkar ba ita ba. Mamaki bai karasa kasheshi a zaune ba sai da ta zauna a ƙasa tana faɗin, “Yaya Master barka da aiki”.

    Duk yanda yaso shareta sai ya kasa. Batare da ya kalleta ba yace, “Kina buƙatar wani abu ne?”.

      Duk da ta ɗanji haushin yanda yay ɗin sai ta danne. Cikin sanyin murya da kwantar da kai tace, “Dama zance maka ne na amince zanyi maka aikin. Amma dan ALLAH nima ka cikamin alƙawarin barina naje ga ahalina bayan na kammala. Sai dai ina roƙonka abu biyu. Ka haɗani dasu ko waya muyi dan su sami nutsuwa nima na samu. Sannan dan ALLAH karka sakani aikata abinda ba dai-dai ba. Kaga ni ɗin marainiya ce, sannan kuma mace. Ɓacin sunana ko fitar tambarin fuskata da sunana ga al’umma tamkar daƙile wata ƙofar mutunta sunan gidanmu ne. Sannan zaiyi wuya ace na sami mijin aure bayan wannan shine fatan kowacce ɗiya. Abu na ƙarshe bana fatan a tada mahaifina a nuna masa ni matsayin ƴar ta’adda bayan ban nema masa mutunci da addu’a ba. Sai kuma dan ALLAH ka zamemin garkuwa na mutuncina a gidan nan duk da tunda na shigo babu wanda ya nufeni da ko maganar banza a cikin yaran ka da ya shafi iskanci. Kaima ka ɗan rage kusancin da kake son haifarwa a tsakaninmu kodan gujema sharrin shaiɗan”.

        Tunda ta fara magana ya gagara cigaba da danna system ɗin. Karo na farko a rayuwarsa da ya sakata a jerin masu hankali da nutsuwa. Ko sanda yake zuwa gidansu da farko kallon miskila yake mata sangartacciya. Sai daga baya ya fahimci kawai gatane data tashi a ciki ya sata zama kamar wata sakalya ga shegen baki……..

      “Dan ALLAH”.

Ta faɗa cikin katse masa tunani. Numfashi yaja ya fesar tare da janye idanunsa a kanta. Kujerar gefensa ya nuna mata alamar tazo ta zauna. Babu musu ta mike ta zauna kanta a ƙasa dan batason kallon idanunsa tsoro suke bata.

     “Muhibbat!”.

Ya kira sunanta a karo na farko tun shigowarta gidan.

      Ta amsa masa da “Na’am” a nutse kai kace ba ita ɗin bace ba.

      “Shekararki nawa ne?”.

“Sha tara”.

Ya gyara zamansa yana fuskantarta sosai. “A shekarun nan naki nasan dai kinsan minene aure tunda har kika ambacesa, sannan kina zuwa islamiyya kinsan minene addininki”.

    Kanta ta jinjina masa, tana wasa da yatsun hannunta. 

          “To Alhmdllh. Da farko dai naji duk bayaninki da amincewarki. Na biyu inason ki kauda duk wani tunani akan waɗan nan yaran da kike gani a gidan nan. Duk da nasan zuciya bata da ƙashi bana fatan wata rana da wani a cikinsu zai miki kallo irin wanda kike tsoro. Dan kasantuwar hakan na nufin tabbas zan iya halaka yaro kona nakasashi.” Ɗagowa tai ta ɗan kallesa saboda jin abinda ya ce. Sai dai ganin shima ita yake kallo ne yasata maida kanta ta duƙar.

      Cikin halin ko in kula da yanayin nata ya cigaba da faɗin, “Bazance miki na amince da kowa a cikinsu ɗari bisa ɗari ba, sai dai ina musu ƙyaƙyƙyawan zato kasancewar su ɗin tarbiyyata ne. Nasan su ba muharramanki bane ba, hasalima bai dace na kawoki cikinsu ki zauna ba. Sai dai nayi hakanne bisa ga lalura da kuma sanin nan ɗin shine kawai yafi tsaro a gareki. Abu na ƙarshe inason ki sani ni ɗin mijinki ne”.

       “Miji?”.

Hibbah ta faɗa a kiɗime.

     Kansa ya jinjina mata yana tamke fuska fiye da da saboda sanin halinta. “Kamar yanda naje neman aurenki gidanku ban ɗakkoki nan ba sai da na biya sadaki aka ɗaura da shaidu”. Ya ƙare maganar da ɗakko lap-top ɗinsa dake gefe ya danno mata video. Tabbas taron ɗaurin auren yayinta ne. Dan yana saka play da fuskar Yaya Umar ta fara cin karo, wanda yake sanye cikin kayan da suka saka ranar ɗaurin auren. Yanata waya alamar baima san ana ɗauka ba. Cikin tsumar da jikinta ke mata ta cigaba da kallo har aka gama ɗaura auren duka yayunta dasu Zahidah aka ɗaura nata a ƙarshe ita da ango mai suna Muhammad Shuraim Aliyu. Kuma hakan na nufin shine kenan. Tunda Baba Saude ta tabbatar mata sunansa ne.

     Kanta ta shiga girgizawa hawaye na kwaranyo mata. Ta buɗe baki kamar zatai magana sai kuma ta kasa kuka ya kufce mata. Tashi tai da gudu tabar falon zuwa ɗakinta. Ya bita da kallo harta shige. Baki yaɗan taɓe da ɗauke kansa irin ko’a jikinsa ɗin nan.

★★★★★★★★

          A gidan Ummi kam yau anguna sun gwangwaje daren alkairinsu ga matansu. Inda suka samu ƙyaƙyƙyawan sakamako daga tsare kai ga zina. Basu ɓata rayuwar ƴar kowa ba suma ALLAH ya kare matayensu ya basu cikakku nagartattu.

      Kowanne ka kalla a wannan safiyar zaka fahimci ransa fes yake da shiga sabuwar rayuwa. Ita kanta Ummi farin cikin nasu data gani ya sakata a farin ciki itama. Tasan ko basu faɗaba sunga wani abu na daga sakamakon haƙuri.

        Sun so zama da ita su tattauna akan Isma’il tace karsu damu tana kan nazarine game da shi. Suma ta basu dama kowa yaje yay nazari yazo mata da sakamako. Amma kar suyi gaggawar yanke hukunci akan ƙaddara balle fara TAKUN SAƘA da shi game da sirrin da UBANGIJI ne kawai yaso basu haske shiyyasa ya aiko Isma’il ɗin a cikinsu.

     Badan sun so ba sukai shiru. Dan ita ɗin ba abar rainawa bace a garesu.

★★★★★

       Da ga ɓangaren haji Halilu ma dai sai a hankali. Gaba ɗaya ya maida kansa kiɗimammen ƙarfi da yaji. Ga momy na addabar rayuwarsa akan ciwon Junaid. Ta dage sai an kamo Isma’il an miƙa ga hukuma. Hakama su Ummi.

      Ya yarda da nemo Isma’il dan haka ya bama jami’an tsaro dama. Sai dai damuwar itace babu ko hoton Isma’il bakuma su san ɗan inane ba shi ɗin. Gashi su Ummi da za’a iya samun bayanai da ga garesu an memsu an rasa. Dan haka suka saka aka kama baban hafsat da baban Zahidah da Sheikh Aliy akan sunsan ina su Ummi suke tunda ƴaƴansu aka aurama yaƴan Ummin.

       Su kuma an kaɗa dambu da taliya sunce sam basusan ina Ummi take ba. Batun tarewar yara kuwa wani gida suka nuna akan nan aka kai amaren. Sheikh Aliy dai uffan baima ce musu ba. Kwarjininsa kuma da sanin shi ɗin wanene ya hanasu kausasa harshe garesa. Koda akaje gidajen aka duba sai aka samu gidajen da Abban ya kama musu hayane su zauna da ƴaƴansa.

      A take ƴan sanda suka fahimci wani abu su ummin suka ƙulla shiyyasa sukai ɓaddabami. Sai kawai suka duƙufa neman su ummin suma bayan Isma’il.

★★★★

          Suma su A.G tunda suka mikama Master sunaye da accaunt Numbers nasu suka koma gefe suna jiran sakamakon aikin da suka bashi. Yayinda a zahiri suke tsakkiyar manyan mutane masu kishin ƙasa ana ta tattauna ta ina za’a nemo master da tawagarsa. Ɗari bisa ɗari an yarda da su. Saboda yanda suke nuna kishi da taɓarɓarewan tsaron ƙasar da son ganin an hukunta masu irin halin master. Ta ko ina sun kafa tsun tsare sune dai😏😥.

★★★★★★★★

       Tun daga wannan ranar Hibbah ta shiga wasan ɓuya da kowa na gidan. Idan ka cire baba Saude da kan ɗan ganta lokaci-lokaci. Master ya share kamar ma ya manta da lamarinta. Dan gaba ɗaya hankalinsa ya tattarune yanzu akan aikin da yasa gaba. Su kansu su Habib abinda ya janye hankalinau kenan ko zaman gidan basayi yanzun. Dan lokuta da dama ma da ga ita sai baba Saude suke yini a gidan. Sai weekend ne Hibbah tahaɗu da yarinyar da baba Saude ke riƙo wadda tsintarta tai ta rena tun tana jinjira gashi har tana da shekaru biyar yanzun. Sosai Hibbah taji daɗin ganin yarinyar, dan gata ƙyaƙyƙyawa da ita ga wayo. cikin ƙanƙanin lokaci shaƙuwa ta shiga tsakaninsu harta manta da wasu ababen halitta su Master a gidan. Sai dai kuma a duk minti cikin bin kwaƙwƙwafin komai take na gidan batare da ko baba saude ta farga ba.

     A kwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI sai ga Hibbah da sati biyu a gidan Master. Yau tsahon kwanaki goma sha biyu kenan bata sakashi a idonta ba. Ba kuma ta haɗu da su Zaidu ba, dan suma basa ma kwana a gidan, daga baya ne kuma ta fahimci shima uban gayyar baya kwana a gidan kusan sati guda kenan.

        Yau ma kusan la’asar bayan ta gama sharɓar kukanta ta tashi ta gyara fuskarta ta fito wajen Baba Saude. Zamanta baifi da mintuna goma ba ya shigo falon da sallama ciki-ciki. Sam Hibbah bata wani jisa ba saboda ta maida hankalinta gaba ɗaya wa tv ne. Sai da taji baba Saude ta ce, “A’a babaa barka da dawowa”.

      Saurin juyowa tai jin abinda baba Saude ta faɗa. Dai-dai ya ɗago idanu yana gaishe da baba Saude. Haɗuwar idanun nasu waje guda ya saka Hibbah saurin janye nata ta maida ƙasa. Dan gaba ɗaya ta koma cikin yanayin rashin walwala a ƴan kwanakin nan, shiyyasa duk wani rawan kan nan nata da tsiwa kamar an mata ruquyya a kansu. 

     “Ina yini”.

Ta faɗa acan ƙasan maƙoshi batare da tayi tunanin zaima jita ba. Duk da yaji ɗin bai amsa ba. Yana dai cigaba da kallonta dan a kallo guda ya fahimci bata a cikin walwalarta. Cigaba da takowa yay inda suke. Batare da ya janye idanun nasa ba ya ajiye ledar hannunsa a saman centre table tare da janye idanunsa da ga kan ta ya maida ga baba Saude.

       “Baba kuyi haƙuri mun barku gidan shiru”.

     “A’a babu damuwa wlhy babana. Ai da yake inada abokiyar hira dan ma dai kwanakin nan nakega kamar tana da damuwa ne. Ban dai tambayeta ba dan kar na ƙara ɗaga mata hankali”.

      “Karki damu baba baƙunta ke damunta kawai”.

        “Ai yaci ace baƙuntar nan ta tafi babana. Amma zan ƙara dagewa wajen ganin na gusar da ita.”

       Hibbahr ya sake ɗan kalla da janye idanunsa. Batare da yace komai ba ya nufi sama. Sai da ya hau kusan steps biyar sannan ya tanka. “Ki sameni anan”.

    Ya faɗa batare da ya juyo ba.

Ganin bata motsa ba harya gama hayewa ne yasa Baba Saude kallonta. “Muhhibatu tashi kije babana na kira kinji”. Dan ita duk zaton ta ƴana da alaƙa da Hibbahr ne. Tunda ita shaidace a kansu bata taɓa ganinsu da matan banza ba har ƙannen nasa. Dan haka take kyautata masa zato.

        Mikewa Hibbah tai a hankali ta nufi saman hawaye na ciko mata idanu. Babu wanda take muradi da ƙulafucin gani kamar Ummi da su Yaya Muhammad. Tsaye ta samesa a tsakkiyar falon da alama ita yake jira. Ta samu damar ƙarema bayansa kallo tunkan ta ƙaraso saboda da ya juya mata baya. Kaya na masa ƙyau, musamman ƙananun kaya da take ganinsa da su kawai dan bata taɓa ganin yasa manyan kaya irin na hausawa ba. Kullum cikin shigar kananun kaya yake tamkar dangin masu jajayen kunnuwa. 

      Jin idanu a kansa ne ya sashi juyowa. Saurin duƙar da kai Hibbah tayi ƙasa. Cikin dakewarsa yace, “Baki iya gaisuwa bane?”.

      “Ina yini?”.

Ta faɗa da sauri kafinma ya rufe baki. Juyawa yay ya karasa ga kujera batare da ya amsa ba. Sai da ya zauna sannan ya ɗago ya dubeta. “Mike damunki?”.

    Yay maganar cikin nuna kulawa duk da fuskarsa a tsuke take babu walwala. 

       “Ba komai”.

Ta bashi amsa hawayen da take maƙalewa suna rige-rigen sakkowa a kumatunta. Idanunsa ya janye a kanta yana ɗan furzar na numfashi. “Ummi ko?”.

     Saurin ɗagowa tai ta dubesa. Sai kuma ta fashe masa da kuka tare da durkushewa a inda take. Lip ɗinsa ya ɗan taune da lumshe idanunsa. Sai kuma ya buɗe yana miƙewa. Fridge dake a falon ya nufa. Ya ɗakko gorar ruwa ya dawo inda take durƙushe tana kuka. Mika mata yayi batare da yayi magana ba. Ganin taƙi karɓa ya sashi yin wani ɗan dirƙuso a gabanta. Yatsunsa biyu yasa a kan haɓarta ya ɗago fuskar tata. Babban yatsansa kuma na goge mata hawayen gefe guda yana cigaba da kallon fuskar tata. Ɗayan hannun kuma ya karasa fincike murfin goran ruwan ya kai bakinta. Abinda ya tokare maƙoshinta ne ya sata fara shan ruwan ko zai wuce. Tasha kusan kaso ɗaya bisa uku kafin ta janye kanta. Komai baice mataba ya janye shima tare da mikewa. Ya kai hannu ya kamo nata hanun. Dole ta miƙe tsaye dan kulawar daya batan kawai yasa zuciyarta ɗan yin sanyi taji kamar daya da ga cikin su Yaya Abubakar ne. 

     A doguwar kujera ya kaita ya zaunar. Hannun nata ya saki ya nufi hanyar bedroom ɗinsa. Hibbah ta bisa da kallo zuciyarta na ayyano mata wata kamanceceniya data rasa a ina take son gano ta. Ta yi zurfi a tunani barci ya fara fisgar jijiyoyin idonta. Duk yanda taso hana kanta hakan ya gagara. Cikin kanƙanin lokaci jikinta duk ya saki, dole ta zame ta kwanta a kujerar batare data shiryama hakan ba.

      Duk abinda take yana kallonta ta cikin ƙofa. Yana ganin ta zube kwance ya fito. Wata Wadrobe dake a gefe an shirya littatafai a ciki ya nufa. Key ya ɗauka a kasan wani littafi ya saka jikin kwabar sai ga shi ya buɗe alamar ƙofa. Yasa hannu ya juya katakon ƙofa ta bayyana. Dawowa yay ya leƙa kasa. Ya tabbatar baba saude hankalinta baya a wajen sanann ya ɗauka Hibbah gaba dayanta yabi ta ƙofar da tai ƙasa yabi ta barauniyar hanyar data fiddashi ta backyard ɗin gidan. Da sauri Habib da ke tsaye cikin parking space ya buɗe masa ƙofar motar. A bayan ya sata, shima ya shiga. Habib ya zauna a mazaunin driver suka fice a gidan bayan maigadi ya wangale musu gate………….✍

*_Kuyi haƙuri, yau gaba ɗaya na ɗauka Sunday ce ashe monday muke🥲🙏🏻🙌🏻_*

     TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

 

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like