TAKUN SAKA 32

Advertisement

 *_Typing📲_*

_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._*

*_ZAFAFA BIYAR WATTPAD LINK👇🏾_*

https://www.wattpad.com/1178725798?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ZAFAFABIYAR&wp_originator=Rf3bdM1DxoE6rtr%2FpmofDT2LwC%2FVfwSkcdyq99bn0JQs6Y4vrnr66bh9cxKlfOuPfF5VyLoSKGor57378NB4Zb%2FxLxcsULfA0VJvg4flaQvgAACdVin4LPGGN8XRDxBS

Advertisements

*_ZAFAFA BIYAR TELEGRAM LINK👇🏾_*

https://t.me/+SBu4brdnI29hSBfw

_________________________

*_Chapter Thirty Two_*

……….A ɗan firgice Hibba ta farka da ga gajeran barcin da Master ya sakata na dole. Waige-waige ta shigayi cikin ruɗanin ganinta a sabon waje. Yayinda wani irin tsoro da tsantsar firgici ke bayyana akan fuskarta. “Na shiga uku wa kuma ya kawoni nan?”.

      Ta faɗa muryarta na rawa alamar son yin kuka……..

      “Hi aunty queen!”.

Advertisements

Da sauri ta juyo tana kallon Habib mai maganar da maɗaukakin mamaki, sai kuma ta ɗan sauke ajiyar zuciya koba komai taga wanda ta sani, duk da suma ɗin ba wai abin yarda bane. 

       “Barka da yamma aunty queen”. Aka sake faɗa ta ɗayan gefenta. Khalid ne yay maganar dan haka ta ɗan hararesa. Ta buɗe baki zatai magana Master ya fito ta wata ƙofa waya manne a kunnensa. Ga kofin baƙin shayi a hannunsa. Baiko kalli kowa a cikinsu ba ya kai zaune bisa kujerar dake kallonsu yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya.

      Yayinda yake amsa wayar cikin rashin sakewa da ƙasaita. Hararar gefen ido Hibbah tai masa tana gulmarsa a cikin rai. Ta dubi su Habib da suka nutsu a tsaye. “Ni ku bani abinci yunwa nakeji aka satoni nan”.

      Cikin gumtse dariya Khalid yace, “Mi zaki ci to?”.

       “Komai ma”. 

   Barin wajen yayi. Babu jimawa sai gashi ya dawo da damammiyar madara da kwalin cornflakes. Yaja ƙaramin stool gabanta yana faɗin, “Gashi auntynmu”.

       Komai batace ba. Sai dai babu musu ta zuba cornflakes ɗin batare data kalli inda Master yake ba, har zata kai baki kuma sai ta dakata. Ta ɗan saci kallonsa tana faɗin, “Khalid inji dai ba’a saka ka barbaɗa wani abun mutuwa ba ko?”.

       Idanu ya ɗan waro waje. “Abin mutuwa kuma Aunty Queen? Wazai saka miki abin mutuwa?”.

       “To na sani, tunda agabana ranar akace a bani maganin feshin ƙwari nasha”.

         Habib da Khalid suka dubi juna suna satar kallon Master daya gama wayar yana daƙilarta ne kawai alamar akwai abinda yakeyi, duk da yana jinsu yayi kamar baisan dasu a wajen ba. Cikin danne abinda ke taso musu Khalid yace, “A’a babu abinda aka saka miki aunty. D……”

        “Zaku wuce abinda ke gabanku ne? Ko zaku zauna surutu?”.

     Ya faɗa batare da ya ɗago ya dubesu ba. Kafinma ya rufe baki sun bar wajen. Hibbah ta taɓe baki da cigaba da shan cornflakes nata dan yunwar takeji da gaske. Cigaba da abinda yakeyi yayi harta kammala bai dubeta ba. Sai da ta mike tana ɗan dafe kai ne ya bita da kallo.

      “Ina ne kitchen?”.

  Ta tambaya cikin kwantar da murya dan ita tayi alƙawarin daina tsiwa har sai ta gano wanene shi.

       Da yatsa ya nuna mata yana miƙewa. Ficewa yay da ga falon yana sake ɗaura wayar a kunnemsa alamar wani kiran yayi. Gaba Hibbah tai itama inda ya nuna mata. Bata wani jima ba ta fito tana gyara hijjab ɗin jikinta da batasan ta yanda akai ta sakashi ba, balle inda ta samoshi. Sake komawa tai kan doguwar kujerar ta kwanta ranta fal tunanin dalilin da yasa aka kawota nan ɗin kuma?. Harga ALLAH hatsabibancinsa na bata mamaki. Mutum ne da sam baka taɓa gane ina ya dosa balle manufarsa. A ɗan zaman da tai da su sosai ta fahimci wasu halaye na mutanen kirki tattare da shi. Sai hakan ke yawan raba mata hankali daga ɗabi’unsa na zahiri da kowa ya sani. (Zan dai sake nutsuwa na fahimci guy ɗin nan).

     Ta ayyana a zuciyarta cikin yarda da kai. Cigaba tai da tunane-tunanenta har ta fara jiyo hayaniyar su Adam da batasan ta ina suka fita ba. Jin hayaniyar tasu na cigaba da tashi sama-sama ya sata miƙewa dan zaman shirun baya mata daɗi, ga jikinta duk babu ƙarfi kanta kuma na mata ciwo kaɗan-kaɗan. Ta riga ta saba da baba Saude acan da Sharifat. Duk da ba sanin ko’ina tai ba haka ta fito compound inda take jiyosu. Girman gidan ya bata matuƙar mamaki, an wadatashi kuma da abubuwa kai kace ba a cikin gurguwar ƙasarnan tamu bane ba. 

       Tsaye tai tana kallon su Habib da ke faman buga basket ball. Haka kawai taji wani nishaɗi har fuskarta na bayyana murmushi. Ta shagala sosai a kallonsu ta hango wata ƙyaƙyƙyawar mage na fitowa da ga ɗakin maigadi. Tana son mage, tsoronta da yaya Usman keyi a gida ya saka Ummi ta hanata ajiyewa. Magen ta nufa tana faɗin, “Woow Cutie”. Tai maganar tana kaiwa duƙe ta ɗauka magen. 

       Master da ke kallonta da ga can inda yake ta gaban ruwan da aka ƙawata na swimming pool ya ɗan yamutse fuska ganin ta ɗaga magen ta rungume a jikinta tana murmushi tamkar ta samu ɗa. Sam shi bai wani damu da mage ba amma ba tsoronta yake ba, baya son dai sam ta taɓa masa jiki. Ɗauke kansa yay ya cigaba da  danna wayarsa.

      Hibbah ba lura da Master tayi ba, dan haka ta cigaba da hidimarta da mage cikin nishaɗi. Lokaci-lokaci takan ɗaga kai ta kalli su Salis. Wani ɗan zare ta ɗauka tana ɗagawa sama magen na tsalle zata kamo. Hakan yasaka Hibbah ƙyalƙyalewa da dariya tana tafiya da baya-baya magen na binta da son kama zaren.

     Tana gab da isa inda Master yake Idris ya farga. Zungurin Musbahu da ke kusa da shi yayi. Musbahu ya ɗan waro ido dan ganin abinda ke shirin faruwa. Yay saurin ɗaga hannu zai fargar da Hibbah da ke gab da zuwa inda Master yake Idris ya rufe masa baki.

        “Kai malam waye ya saka. Barta dan ALLAH, wlhy ni so nake babban yaya ya amsheta matsayin matar gaske bawai ta wucin gadi ba. Dan sun matuƙar dacewa.”

     Musbahu da ya gamsu da bayanin Idris ya jinjina kansa yana janye hannunsa. “Ashe bani kaɗai nake da fatan nan ba.”

    “Sosai kuwa”

Cewar Idris cikin bada tabbaci.

            A ɓangaren Hibbah kam gab take da kaiwa ga Master da gaba ɗaya hankalinsa nakan wayar dan abu mai muhimmanci yakeyi a ciki. Khalid da sai yanzu idanunsa ya kai shima ya ɗan zaro ido. Da sauri ya ɗaga mata hannu da faɗin, “Aunty Queen bayanki”.

       Tsorata Hibbah tayi, dan duk zatonta wani abun cutarwa ne, musamman ganin yanda Khalid ɗin yayi maganar. Tai ƙoƙarin juyawa da sauri sai dai ta rigada tazo gab da shi, ga magen ta ɗane ƙafarta saboda kama zaren da tasamu damar yi. Uban tsalle ta doka da ƴar ƙarar tsoratan data fargar da Master. Cikin zafin nama ya riƙo hannunta ganin tayi baya zata kai ƙasa, sai ko gata gaba ɗaya a kansa.

       Hawar masa ƙafa da magen tayi ne shima ya sakashi saurin ɗaga ƙafarsa, ga Hibbah ɗare-ɗare a cinyarsa. Yanda yayi ɗinne kuma ya sake firgitata ta duƙunƙunesa gaba ɗaya har yana sakin wayarsa a ƙasa babu shiri. Cikin sauri su Idris suka shiga jan hannun juna suna barin wajen ransu fari tas..

     Master ya sake rumtse idanunsa da ƙarfi jin yanda Hibbah keta sake cusa kanta a ƙirjinsa da dabaibayesa. Ga mage da kamar ance ta nane musu sai tsale-tsallenta take. Dole ya miƙe gaba ɗayansa dan bayason magen na taɓa masa jiki. Hibbah ta fasa ƙara da son sake ruƙosa jin zata faɗi ƙasa, sai dai abisa tsautsayi ta riga tayi baya da yawa, idan kuma takai ƙasa tabbas zata cutu. Magen ya yakice a jikinsa yana ƙoƙarin kai ɗayan hannunsa ya riƙo nata ganin gaba ɗayanta zata sulmiya cikin ruwan ne.

     Maimakon ta riƙe hannun sai ta damƙe rigarsa gaba ɗayansu suka antaya a cikin ruwan ji kake tanjamm😬😱.  

  

           Yanda ruwan ya bada ƙara yasa su Habib fitowa kusan duk a guje sukayo wajen pool ɗin har maigadi. Sam Master bai iya ruwa ba. Hasalima bai cika son ganin babban ruwa ba, kona swimming pool ɗin idan ya zauna wajen saboda son sanyi baya yarda yay masa kallon daya haura sakanni yake ɗauke ido. Idanko damina tazo duk wani rashin jinsa nutsuwa yake saboda rashin sakewa, ko yaya ruwa ya dakesa sai yaji a jikinsa dan sai yayi ciwo. 

      Hankalin su Habib ya tashi saboda sanin bai iya ruwaba. Gashi basu da damar cewa zasu shiga ruwan saboda Hibbah dake tare da shi. Cikin ƙanƙanin lokaci Master ya shaƙi ruwa, sai dai kuma ƙoƙarin son ceto Hibbah yake a zatonsa bata iya ruwanba itama. Duk yanda yaso hakan ta kasance ya gagara, dan harya fara galabaita. Hibbah kuwa tanata ƙoƙarin ganin taje gaɓa dan itama dai bawai ta iya swimming ɗin bane ba, amma ta fisa dan ta kuɓutar da kanta batare data fita hayyacinta ba. Ruɗewar data lura su Zaidu sunyi ne ya sata saurin waigawa bayanta tana ƙoƙarin sharce ruwan fuskarta. Idanu ta zaro matuƙa, dan Master harya fara yin ƙasa. 

       Da sauri ta koma bayan inda yake. Tasa hannu ta toshe hancinta tai ƙasa wai zata ɗagosa. Ina yafi ƙarfinta, amma tsabar ƙarfin hali tanata kici-kici cikin rawar jiki na tsoro, dan ta fahimci bai iya ruwa ba. Da ƙyar ta samu da taimakon su Habib data miƙoma hannunsa suka kama ta ɗagoshi, sai faman cije baki take dan ya mata nauyi a jiki, tana turawa suna ja har suka ɗagosa gaba ɗaya.

         Ganin kamar bashi da rai yasa Hibbah fashe musu da kuka, dan gaba ɗaya kanta ta bama laifin. Ruɗewar da tai yasata fara danna ƙirjinsa kamar yanda taga Musbahu nayi. Amma babu alamar ruwan daya shaƙa zai fita.

      Adam yay saurin faɗin, “Aunty Queen taimakon gaggawa ta baki Please”.

           Ruɗewa ta sakata ranƙwafawa kansa ta ɗaura bakinta kan nasa, yayinda ta toshe masa hanci da yatsunta biyu, bada wani tunani ba ta shiga bashi taimakon gaggawa. Ganin taja numfashinsa na farko babu wani alama yasata jawowa a karo na biyu da iya ƙarfinta tana matse ido. 

          Gaba dayansa ya yunƙuro saboda tahowar numfashinsa mai haɗe da tari da ruwan daya shaƙa. Hannayensa duk biyu sukai sama, tana ƙoƙarin dagowa ya sake rungumota ta dawo kan ƙirjinsa. Tsam ya matseta yana cigaba da tarin ruwan daya shaƙa na fita. 

      Nannauyar ajiyar zuciya su Khalid duka shiga saukewa na godiya ga ALLAH. dan da gaske sun shiga tashin hankali. Sai mutsu-mutsu Hibbah take nason ƙwace jikinta amma ta kasa koda motsi. Sai da tarin ya lafa masa ne ya ɗan janye hanun daya dabaibayeta yana buɗe idanu da ƙyar. Cikin sauri ta miƙe a kansa duk kunya da takaici sun dabaibayeta. Ya ɗan kalleta ya maida idanunsa da sukai jaa ya lumshe.

        Ganin ya saki Hibbahr su Salis da duk sukai ƙasa da kai tunda ya kawo numfashi duk sukayo kansa. Sune suka taimaka masa ya tashi zaune. Zasu kamashi ya mike ya girgiza musu kai alamar zai iya. Baya duk sukaja. Shi kuma yabi Hibbah dake jike da ruwa ta nufi hanyar falo da sassarfa da kallo. Mikewa yay da ƙyar yana dafe kansa da ke juya masa. Shima ya nufi falon su Habib suka take masa baya sunata jera masa sannu. Har cikin ransu kuma ganin laifinsu suke dan sun bada gudunmawa a wannan accident ɗin.

       A falon suka iske Hibbah sai rawar sanyi take har haƙoranta na haɗuwa. Duk tausayi ta basu, tayi tsumu-tsumu tamkar an tsamo ɓera a ruwa😹👐🏻. Shi kansa ta bashi tausayi, duk da bayajin ƙarfin nasa jikin shima gabanta ya ƙarasa. Babu zato Hibbah da duk kunya ta dabaibaye saboda yanda kayan suka manne mata a jiki sai ji kawai tai anyi sama da ita.

          Da sauri ta harɗo hannayenta a wuyansa saboda wani Masifaffen  kunya daya rufeta tashi a karo na farko tun zuwanta gidansa. Ta tura kanta akan ƙirjinsa da riga ta manne shima yanata ɗigar da ruwa.

        Ƙin ɗagowa tai har sai da taji ya direta ta ɗan buɗe ido. Da sauri ta kalla inda ya kawotan shima ta kallesa. kafin ta ɗaga baki tai magana ya kammala dai-daita ruwan ɗumin ya saki ruwan shower ɗin ya sauka a kansu. Wani irin bahagon ajiyar zuciya Hibbah ta saki jin ruwan akansu. Ta rumtse idanunta da sauri tana juya masa baya ganin zai cire riga abinsa hankali kwance.

          Juyawar tatace ta bashi damar cire duka kayan jikinsa ya bar boxer kawai ruwan na ratsa masa jiki kozai samu nutsuwar abinda yakeji na ƙutsa masa cikin ƙashi. Sai da yaji ya ɗan fara samun nutsuwa ne ya kashe gaba ɗaya, batare da yace komaiba yaja bathrobe ya saka. Tun kafin ya fita a toilet ɗin ya fara sakin atishawa a jajjere.

      Ajiyar zuciya Hibbah ta kuma saki jin ya rufe mata ƙofar hawaye na gangaro mata. Gaba ɗaya kallon komai take tamkar a mafarki yau itace a banɗaki daya da namiji.

       Jin sanyin na neman dawo mata a jikine ya sata zuwa ta sama ƙofar key ta fara zame nata kayan. Dan dole ne idan tana bukatar zaman lafiya tayi yanda ruwan zai ratsata ta kuma rabu da kayan gaba ɗaya. Hatta da gashin kanta ji take kamar ta kwashe ta yar.

         Sai da taji tamkar fatarta zata ɗaye dan saukar ruwan dumin nan sannan ta kashe tana sauke numfashi da atishawa itama. Towel ya rage a toilet ɗin gashi guntu, bata da zaɓin daya wuce ɗauka ta sakama jikinta, ta sake jan karami ta naɗe kanta tana sakin atishawa da kallon facemask ɗin daya cire a fuskarsa. mask ɗin ta ɗauka tana jin takaicin kanta na juyawar da tai da tabbas saita ga face nashi yau. Jin atishawa zata halakata ya sata ajiyewa ta matse kayan data cire da nasa. Gefe kuma tana tunanin yanda za’ai ta fita a toilet ɗin da guntun towel ɗin?.

       A ɓangaren Master kam rawar sanyi sosai yakeyi, da kyar ya iya daukar wani mask ɗin ya saka a face nashi. Gadon ɗakin dake a gyare ya haye yaja bargo ya rufa yana sakin atishawa da rawar ɗari.

         Hibbah da taji kamar babu motsinsa ta ɗan leƙo kanta. Babu kowa a ɗakin dan haka tai tunanin ya fita dan bata farga da gadon ba. Sai da ta fito tsakkiyar ɗakin ya saki wasu tagwayen atishawa. Da sauri ta duba kan gadon saita ga a lulluɓe yake. Ajiyar zuciya ta sauke da saurin nufar Wadrobe ɗin ɗakin duk da bata tunanin samun kaya. Cikin sa’a taci karo da kayansa. Cikin sauri taja jallabiyar data fara gani ta zura  a jikinta duk da ta mata yawa sosai. Tanayi tana juyawa ta dubesa wai ko zai kalleta.

★★

     Da ga can falo su Habib nata kai kawon dafa masa ruwan zafi mai kayan kamshi, dan sun tabbatar a yanzu shine yafi bukata bisa taimakon farko. Su duka bakwai sun haɗu a kitchen ɗin abin tausayi da dariya. A haka dai suka haɗa Habib ya ɗakko ya nufo ɗakin nasa. Sai da yay sallama da knocking Hibbah ta amsa sannan ya shigo. Ganin yanda har yanzu a ruɗe yake ya bama Hibbah mamaki. Ta bisa da kallo lokacin da yake kaiwa durƙushe a gaban gadon saitin kan Master. A marairaice yake kiransa kamar zai saki kuka. 

     Master dake jinsa ya buɗe ido da ƙyar tare da kai hannu ya ɗan ja bargon daga saman kansa. Sosai idanunsa sukai wani irin kaɗawa jazur, jijiyoyin kansa sunyi ruɗu-ruɗu dan ma mask ya tare abin tausayi da tsoro. Sosai gaban Hibbah ya faɗi ganin cikin kanƙanin lokaci ya fita hayyacinsa. Batare da Hibbah ta sani ba tuni ta karaso gabansu itama har rigar na neman harɗeta zata faɗi ta dai dafe gado.

         Shayin Habib ya miƙa masa kamar zaiyi kuka. Da ƙyar Master ya mike ya jingina da fuskar gadon sai atishawa yake akai-akai. Habib ya zuba shayin a muq ya mika masa. Amsa yay babu musu yana matse idanu dan yasan shine kawai abinda zai taimakeshi a halin yanzun. Sai dai maimakon ya kai baki sai ya miƙawa Hibbah yana mata nuni data zaune a gefen gadon.

        A yanayin da yake ne yasata kasa musa masa, dan ita sam bawai ta shiga wani hali bane, shi kansa ta fahimci kamar dai yanada wani ciwone da baya buƙatar shiga ruwa, musamman wannan da yay sanyi sosai, ko kuma halittarsace hakan. Gashi shi kuma ya shagesa da yawa. (Dama akwai mazan da basu iya ruwa ba?). Ta faɗa a zuciyarta tana satar kallonsa ta gefen ido.

      Wani shayin Habib ya sake zubawa ya miƙa masa, amsa yay. Habib dake kallonsa cikin damuwa yace, “Salis yaje gida ya ɗakko maka kaya masu kauri. Akwai abinda kake buƙata bayan shayin?”.

        Ƙasa yay da idanunsa ya ɗan kalli shayin ya ɗago ya duba agogon dake ɗakin. Ganin lokacin sallar magrib ma yayi sai ya girgiza masa kai kawai. 

      “Kuje kuyi salla”. 

Yay maganar a hankali miryarsa harta canja launi tamkar ba shi ba.

            Sannu Habib ya sake masa yana mikewa. ya dubi Hibbah da yake fatan ita babu komai da ga gareta. “Aunty ke bakijin komai ko?”.

      Batare da Hibbah ta kallesa ba ta girgiza masa kai. “Alhmdllhi” Habib ɗin ya faɗa da nufar ƙofar fita. Shuru ɗakin ya ɗauka kamar babu kowa, ita dai Hibbah kanta a ƙasa zuciyarta na wasuwasi da saƙe-saƙen mike damunsa haka daga shiga ruwan da kwata-kwata basu gaza 30minutes ba a ciki? Dan gaba ɗaya yanda ya birkice ɗin zaka fahimci akwai damuwa da yake fuskanta game da hakan. To amma kuma a koda yaushe ai cikin warware ac yake kamar goyon larabawa shi baya masa illa kamar haka kenan? Kuma yana wanka, Kenan shima duk basa masa illah?. 

      Oho shi dai Master baima san tanayi ba. Dan shayin yake sha cike da dauriya, amma lokaci-lokaci yakan ɗan kalleta ya janye idonsa. Duk da alamu ya nuna yanajin sanyi sosai haka ya miƙe dan shan shayin ma ya ɗan bashi nutsuwa. Bayan ya buɗe wadrobe ya ɗauka kaya toilet ya nufa yayo alwala da ruwan zafi sosai ya canjo kaya. Gaba ɗaya yanda yake jinsa bazai iya fita massallaci ba, dan haka yay ma Hibbah nuni alamar taje tayo alwala. 

       Haka kawai ta tsinta kanta dajin nauyinsa. Dan haka babu musu ta mike tana faman naɗe rigarsa. Batai tunanin jiranta zaiyi zaman yi ba sai da ta fito ta gansa a zaune ya rufa da bargo idonsa a rumtse. Sai atishawa da yake cigaba da jerawa. Motsinta ya sakashi buɗe idon, ya miƙe batare da yayi magana ba yana tunanin abinda zata rufa tai sallar…..

     Sallamar Salis ce ta sakashi sauke ajiyar zuciya. Hibbah ta amsa ganin shi muryar tasa tayi ƙasa. Itace ta bama Salis ɗin damar shigowa. Sai ko gashi da sabuwar sallama ɗauke da leda babba. Ya ajiye yanama Master daya koma bakin gadon ya zauna sannu. Kai ya jinjina masa kawai tare da miƙa hannu ya amshi ledar da faɗin, “Kaje kai salla”. 

     Cikin girmamawa Salis ya amsa. shi kuma ya buɗe ledar sai ga Hijjab da kayan Hibbah a sama. Hijjab ɗin ya miƙa mata yana mikewa. Amsa tayi ta saka. A karan farko ya ja musu sallar magrib, koda suka idar ran Hibbah fal mamakin jin yanda yake karatun sallar cikin nutsuwa da tabbatar da ashi ɗin yanada ilimin addini.

    Bai wani samu nutsuwar addu’a ba ya miƙe dan jikinsa sai rawar sanyi yake. Ledan da Salis ya kawo ya buɗe, ya fiddo safa ya saka a ƙafarsa ya sake hayewa gadon yaja bargo. Sai dai kafin yakai kwance Habib yay sallama ɗauke da ruwan ɗumi. Yanzunma Hibbah ta amsa masa, ya shigo idonsa akan Yayansa da ya tabbatar yana cikin wani hali, sai dai shi mutumne mai juriya shiyyasa ba’a cika ganowa ba,  amma yasan yana da raki idan yana ciwo kuma. Dan in yana ciwo koma musu yake kamar shine karamin sune manyan tsabar rakinsa, kai kace ba Master bane maiba su A.G ciwon kai da jami’an tsaro da manyan ƙasa😂.

       Ita dai Hibbah tana gama shan maganin da Habib ɗin ya bata ta mike tana faɗin, “Habib wane ɗaki zan zauna?”.

      Habib da yasan gidan bawasu ɗakuna bane kuma ga halin da Master ke ciki na bukatar wani a kusa, dama idan yana ciwo shine ke zama tare da shi, tunda kuma gata yana ganin ai an wuce wajen. Mastern da yay kamar baisan sunai ba ya kalla. Ganin yanzun ma bashi da alamar cewa komai yasa Habib cewa, “Anan zaki zauna gidan babu ɗakuna sosai, sannan yana bukatar wani a kusa da shi, kiyi haƙuri ki zauna anan doctor na zuwa dubashi”.

       Ta buɗe baki zatai magana. Yay ma Habib alamar yaje. Babu musu ya juya ya fita. Fuska ta ɓata sai dai babu damar yin magana. Komai baice mata ba shima yaja bargo ya sake rufe har saman kansa. Tamkar Hibbah zata fasa kuka ta cigaba da zama a saman abin sallar har lokacin isha’i, a ranta tana tunanin ita tayaya ma zata iya zama da shi a ɗaki guda. Batai zaton zai tashi sallar ba sai gashi ya miƙe da alama ma ba barcin yakeba daman. Yanzun ma shine ya ja musu sallar isha’i kowa yay shafa’i da wutirinsa. Gadon ya sake komawa ya kwanta, baifi mintuna biyarba Habib yazo da doctor. Wani farin dattijone mai cike da kamala. Gaishesa tai ta cigaba da kallon yanda taga yana tarairayar master ɗin. Sai faɗa yake masa a tausashe akan shiga ruwa da yay bayan yasan minene matsalar jikinsa da ruwan sanyi da kuma rashin iya ruwa. 

        Shi dai Master komai baice ba sai wani langabewa yake. Doctor yay masa allura yana faɗin, “Kaga yanzu babu abinda kafi buƙata daga dakatawar wannan rawar sanyi kamar ɗumin jikin mutum. Gashi kaƙi aure Shuraim. Last daka samu irin wannan matsalar Habib ne ya baka ɗumin jikinsa lokacin bai kai haka girma ba. Amma ni yanzu bansan yanda za’ai ba”.

         “Doctor Ibrahim mutumin kirkine kuma ɗan amanarsu. Wanda suke kallo tamkar uba a yanzu, duk da ya musu nisa saboda bai cika zama ba. Shiɗin ɗan uwa ne ga baba wanda ya taimaki mamynsu kuma ya riƙesu. tunda Mastar na yaro shine yake kula da issue ɗin ciwon nasa na rashin son ruwan sanyi da likitoci da yawa suka tabbatar masa yanada alaƙa da jininsa ne. Sam jikinsa baya son ruwan sanyi, shiyyasa ya kasance ko alwala zaiyi sai da ruwan ɗumi, amma kuma yana son sanyin ac duk da shima yakan bashi wahala wasu lokutan.

        “Uncle ai yayi aure fa”.

Habib ya faɗa a hankali yana satar kallon Master. Cike da mamaki Doctor ya kalli Master ɗin dake kallon Habib cikin alamar waya tambayeka”.

      “Shuraim da gaake ne?”.

Doctor yay tambayar yana raba hankalinsa biyu na kallon Master da Hibbah. Kai kawai Master ya ɗaga masa, sai kuma ya motsa baki a hankali yace, “Haka abin yazo babu shirine Uncle”.

      Daɗi ne ya kama doctor Ibrahim. Ya shiga sakama Master albarka da Hibbah, dan shi da da farko harya fara zargin ko master ya fara neman mata ne duk da yaga Hibbah ƙaramar yarinyace. To amma yanda zamani ya sauya komaima zai iya faruwa. Ya nuna farin cikinsa sosai, tare da yi musu addu’ar zaman lafiya da zuri’a mai albarka. Da ga ƙarshe yay ma Hibbah bayanin yanda zata kula da shan maganin master ɗin tare da bashi ɗumin jikinta.

     Ita gaba ɗaya ma tabar fahimtar yaren da yake magana. Saurarensa kawai takeyi da kunne. A ganinta tayaya zata bashi ɗumin jikinta tunda ba jini bane balle a ɗiba?. Harya gama ya miƙe zai wuce bata dawo hayyacinta ba. Sai da Habib ya kirata da ɗan ƙarfi sannan ta ɗago ta kallesa. “Uncle ne ke miki sallama”.

         Cikin sanyin murya taima Uncle Ibrahim ɗin godiya dan itama sanyin ruwan zuwa yanzu ya fara tasiri a jikinta na alamar saukar mura. Shi dai ficewa yay yana murmushi. Master da tuni ya koma cikin bargo ya kwanta dai yana saurarensu sama-sama. Koda suka fice kuma baicema Hibban komai ba har Habib ya dawo.

     Tattare syringe ɗin da akai masa allurar yayi yana faɗin. “Aunty Queen mizaki ci ne?”.

     Kanta ta girgiza masa alamar babu. Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Yay mata sai da safe yana ficewa abinsa. Idanu Hibbah ta rumtse da ƙarfi dan itafa babu yanda za’ai ta kwana ɗaki guda da namiji. Dan haka ta cigaba da zama a wajen tana yan tunane-tunanenta. Sai atishawa da Master keta faman yi akai-akai batare da tasan idonsa biyu ba ko barci yakeyi.

      Ta jima a wajen zaune har batasan adadin awannin data ɗauka ba. Sai gyangyaɗi take dan barci takeji ga sanyi itama tanaji dan ma tasha maganin da Habib ya bata na mura itama. Tashi tai cikin sanɗa ta buɗe ƙofar ta fito, babu shiri tai saurin komawa ciki ganin falon dunɗum da duhu, ga ko’ina tsitt alamar su Adam sun kwanta suma. Ta jingina da ƙofar zuciyarta na wani dif-dif. Ganin tsaiwar bazata mataba yasa ta dawo saman abin salla ta kwanta. Wani mugun sanyi taji yana kaɗata. Ta sake mikewa kamar zata fasa kuka tana harar gadon. Bazata iya kwanciya a saman tiles ɗin nan ba gaskiya, kuma harga ALLAH barci takeson yi dan maganin murar ya fara aiki. Zuwa tai ta kashe fitilar ɗakin, cikin sanɗa tazo ta hau gadon a ɗosane taɗan ɗaga bargon ta shiga zuciyarta na addu’ar ALLAH yasa karya farka har sai ta fara tashi. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa barci yay awon gaba da ita.

       Master da barcin ya kasa ɗaukarsa sai rawar ɗari yake duk yana jinta…………✍

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

 

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like