Advertisement
*_Chapter Thirty Three_*
………..Can cikin dare Hibbah tai ɗan juyi cikin barci, da sauri ta sake mirginowa baya jin zata faɗa ƙasa. Gaba ɗaya ta manta a inda take ma. Ƙara bajewa tai jinta yanda takeso. Hakan sai ya sake bata damar matsawa jikin Master da har yanzu baiyi barci ba saboda zazzaɓi da jikinsa ya ɗauka mai zafin gaske.
Jin yanda ta matsosa har tana janye masa bargo ne ya sakashi ɗan buɗe idanunsa, hannu ya kai zai gyara bargon sai yaji ta duƙunƙunesa a jikinta, ya cija lip ɗinsa kamar ya mangareta, dan wannan shine karonsa na farko a rayuwa da yake kwance tare da mace a gado ɗaya. Ya ɗanja bargon da ƙarfi, Hibbah da batasan mi ake ba ta biyo bargon gaba ɗayanta ta shige jikinsa. Zafin zazzaɓinsa ya sata sake matsawa sosai dan ɗumin ya mata daɗi kasancewar itama har yanzu tana ɗan jin sanyi.
Saurin jan numfashi da rumtse idonsa yayi da ƙarfi. Babu shiri yakai hannu zai janyeta ta sake dabaibayesa har dayin filo da damtsen hannunsa. Ta sakala hanunta ta gefen cikinsa. Wani irin harbawa da ƙirjinsa yayine ya sakashi matseta babu shiri yana datse leɓansa cikin haƙora kai kace zai hudasu ne.
Ƴar ƙara Hibbah ta saki tana ƙoƙarin janye jikinta cikin lalube. Ina ta rigada tazo hannu, dan wani ƙara matseta yayi da ƙyau. Cikin rawar sanyi dana harshe ya ce, “Please ”. A hankali cikin kunnenta.
Kanta ta shiga jujjuya masa duk da kuwa a cikin duhu suke. Jikinta sai tsuma yake najin sabon al’amari ga rayuwarta. Bata sake tsurewa ba sai da ya tattaro jallabiyarsa dake jikinta yay sama da ita alamar zai cire dan ta rage masa wasu kaso na ɗumin jikin nata da yafi buƙata a yanzu. Duk da kuwa shima jikin nasa tsumar yake na shiga sabon yanayi akaf tarihin rayuwarsa. Rashin ƙarfin jiki da ciyo ya haddasa masa baisa tafi ƙarfinsa ba. Dan cikin ƙanƙanin lokaci ya zare rigar ya barta yanda Ummi ta sulmiyita duniya. Kuka ta fashe masa da shi tana yunƙurin tashi. Yasa hannu ya kuma matseta, cikin muryar ciwo da rakinsa ya fara magana a cikin kunnenta.
“Baki da tausayi ko?, kina son kiga na mutu. Please Muhibbat 30minutes kawai…”
Sake firgicewa Hibbah tayi dan bata taɓa jin makamanciyar muryar daga garesa ba. Gaba ɗaya ya tashi mata da ga Master data sani mai mazurai da tsare gida ya koma mata wani daban. Harga ALLAH tanajin tausayinsa, sai dai ayanda suken akwai tashin hankali da tsoron kar wani abu ya faru, dan sarai tasan minene aure, tunda tanada iliminta dai-dai gwargwado. Ɗan karatun nan na littafi tana taɓawa a waya, ga kawaye a gefe…….
Advertisements
“Ina jin tsoro Yaya Master, dan ALLAH kar kaimin komai”. Ta faɗa cikin suɓutar baki.
Duk da halin ciwo da yake ciki maganarta sai da ta saka wani lallausan murmushi subuce masa. Ya tura yatsun hannunsa cikin sumar kanta tare dayo ƙasa da kansa yasa goshinsa akan nata. Hancinsu na gogar na juna. Cikin shaƙaƙƙiyar muryarsa yace, “Ashe Tanee ɗin Ummi tasan minene aure?”.
Kanta ta shiga ja baya tana faɗin, “Ni wlhy A’a, dan ALLAH ka bari”. Yanda ta ƙare maganar hawaye na rige-rigen sakko mata a kumatu ya sashi sake yin murmushi da har taji sautin fitarsa a maƙoshinsa. A gefen zuciyarsa kuma yana sake yarda da tarbiyyarta, dan yanda ta ruɗe zai tabbatar maka bata taɓa tsintar kanta a yanayinba. “Relax!, Yaya master ba ɗan iska bane bazaiyi komai ba ga ƙanwar nan tasa mai bakin akku himyim??”.
Baki ta tura gaba duk da a cikin duhu suke. Ta sake ƙoƙarin ja baya ya sake matseta a jikinsa da har yanzu yake tsumar sanyi. Duk yanda taso ya barta hakan ya gagara. Dole ta nutsu waje guda badan taso ba. Sai dai yanda zuciyarta keta faman harbawa da sauri-sauri zai baka tabbacin haƙurin na dole ne kawai, ta riga tazo hannu babu mafita. Itama a ɓangarenta tana jiyo sautin motsin da zuciyarsa keyi a cikin ƙirjinsa. Har abin na bata mamaki da tsoro. Dukansu sunyi shiru kowa na sauraren na ɗan uwansa. A hankali barci ya fara fisgar Hibbah, dan yanda yake ɗan motsa yatsun hannunsa da har yanzu suke a cikin gashinta tanaji kamar yana mata susa ne.
Cikin ƙanƙanin lokaci Master ya farajin numfashinta na sauka a hankali jikinta na saki alamar barcin yaci ƙarfinta. Bakinsa ya matsar bisa goshinta ya sumbata da sake turata a jikinsa sosai yana maijin nutsuwa da wani yanki na guntun damuwarsa na sauka. Yayinda wata sassanyar ajiyar zuciya ke sauka a hankali. Sai gashi barcin da ya kasa tun ɗazun na fisgarsa yayinda jikinsa ke ƙara ɗaukar zafi.
Barcin da basu sami yi da wuri ba ya sakasu makara da asuba. Dan sai wajen bakwai saura Master ya farka. Har yanzu jikinsa da zazzaɓi bai gama sauka gaba ɗaya ba. Ga idanunsa sun ƙara girma na alamar mura ta tabbata. A hankali ya buɗe idonsa saboda nauyin da kansa yay masa. Akan Hibbah dake lafe a jikinsa ya saukesu. Barcinta take hankali kwance, gashin kanta daya warware dukya baje akan filon da fuskarta. Bakin da baya barin saita kwana yake kallo, idanunsa ya sake lumshewa da buɗewa a kanta lokaci guda. kafin ya saka yatsunsa yana janye mata gashin daya sakko mata akan fuska. Taɓa rumfar idonta da yatsansa yayi a mistake ya sata farkawa. Idanunta ta buɗe itama a hankali dan tama manta a inda take. Akan fuskar boginsa ta sauke, wadda inba faɗa maka akaiba bazaka taɓa ɗauka ba tashin bace. Wani zabura tai babu shiri tai azamar juya baya zuciyarta kamar zata wantsalo ta fito. “Innalillahi….” ta faɗa tana rumtse idanunta da ƙanƙame bargo da ƙarfi.
Uffan baice mata ba, sai ma mikewa yay zaune yana dafe kansa da yay masa nauyi. Kafin ya miƙe gaba ɗayansa ya nufi toilet da alamun har yanzu jikinsa babu ƙarfi. Yana shigewa Hibbah ta miƙe zaune da nufin guduwa tabar ɗakin sai ta ganta salin alin. Bama tasan sanda ta daddage ta fasa ƙara ba da maida bargon ta rufe jikinta.
Cikin sauri Master ya fito a zatonsa wani abune ya sameta. Yay saurin yaye bargon data ƙudundune a ciki, wata sabuwar ƙarar ta sake fasa masa da saurin faɗawa jikinsa ta duƙunƙunesa ita a dole batason yaga jikinta. Babu shiri wata dariya ta nema kufce masa. Dan ya fahimci abinda takema wannan kwakwazon. Sai dai yay ƙoƙarin danne dariyar ya dafe kansa da hannu ɗaya. Sanin su Habib na a cikin gidan yasashi fara mata magana a Master ɗinsa babu wasa. “ALLAH idan baki rufemin bakin nan ba a safiyarnan zan canjaki”.
Duk da magana yay ta hikima kuka Hibbah ta fashe masa da shi. “Ni wlhy bazan yarda ba. ni ba ƴar iska bace ka maidani wajen Ummi na. Ummina tace karna sake namiji ya tabamin jiki, amma kai har ganina kayi, nashiga ukuna ni Muhibbat bazan yafe ba.”
Ɗagota yay gaba ɗayanta ya maida ya zaunar, tai azamar lalubo bargo ta sake duƙunkunewa tana kuka wiwi. Harara ya zuba mata, cikin ɗan faɗa-faɗa yace, “Ohhh! To ni Mamyna tace na bari mace ta taɓamin jikine mai Ummi. Koni na gayyatoki bisa gadona? Idan wannan bakin baimin shiru ba anan na rantse sai na haɗiyesa”.
Ya ƙare maganar yana matsota da dungure mata kai. Babu shiri tasa bargon ta toshe bakinta hawaye na sakkowa. Sake zuba mata harar yayi da jan siririn tsaki yana miƙewa. “Sai shegen tsiwa ga tsoro”. Ya faɗa yana nufar toilet.
Advertisements
Sake fashewa da kuka Hibbah tai da komawa ta kwanta tana jan bargon har saman kanta. “Ni wlhy ban yafe ba kwarto kawai”.
Karaf a kunnen Master dake fitowa a bayi alamar alwalar daya fara ihunta ya fiddosa yaje ya sako. Kobi takanta baiyiba dan kansa ciwo yake ya kabbara salla. Harya idar bata tashi ba. “Zaki tashi kiyi salla ko saina hawo gadon?”.
Ya faɗa a yanda yasan dole zataji tsoro. aiko zumbur ta miƙe, ta ƙudundune bargon har kanta tana sauka a gadon da gudu tai toilet. Saurin riƙota yay, dan yasan tana shiga da bargon toilet ya gama yawo. “K miyasa sam mai bai wadaci kanki ba?”. Yay maganar fuska a tsuke. Jikinta taso fisgewa ya zuba mata ranƙwashi tare da fisgota ta dawo jikinsa. Zata fashe masa da kuka yace, “Karma ki soma”.
Dolenta ta haɗiyesa kuwa. Jallabiyar sa daya cire mata jiya da daddare ya ɗakko mata. Yana ajiyewa a kan gadon ya juya ya fice a ɗakin yana danne dariyar dake taso masa. Raka bayansa tai da harara kafin taja jallabiyar ta saka. Koda ta shiga toilet ɗin saita yanke shawarar yin wanka. A gurguje tai wankan tayo alwala ta fito.
Salla ta fara gabatarwa kafin ta kimtsa cikin kayan da aka kawo mata. Har lokacin master bai dawo ɗakin ba. Dan haka ta fara gyara ɗakin. Tana gab da kammalawa Habib yazo yay kiranta. Sai da ta saka Hijjab sannan ta fito tana ta faman ɓata fuska. Duk zaune ta samesu a dining har uban gayyar daya canja kaya alamar yay wanka a inda bata sani ba. A kallo ɗaya zaka fahimci baida lafiya. dan idanunsa jajur suke ga wata ƙatuwar rigar sanyi daya ɗora. Gaisuwar da su Musbahu sukai mata ta amsa cikin ƙara ɓata fuska tana hararsu. Su dai murmushi kawai sukai dan babu damar magana boss na a wajen. Habib yaja mata kujerar kusa da Master dake karyawa, koda suka fito baiko ɗago ya kallesu ba abincinsa yake tsakura fuska a ɗaure, dan sam baya masa daɗi saboda mura. Dan ma yasa sun masa mai ɗan yaji da kayan ƙamshi ne.
“Nifa na ƙoshi”.
Ta faɗa kanta a ƙasa dan gani take kamar duk suna kallon abinda ya faru jiya da daddare a fuskar tata. A karon farko ya ɗago ya kalleta da jajayen idanunsa. Babu shiri takai zaune dan kallo ne na gargaɗi da babu alamar wasa a cikinsa. Kofi ya ɗauka da kansa ya haɗa mata shayi tare da zuba mata soyayyan doyan ya tura gabanta. Kallon juna su Habib sukayi cike da iya shegensu. Adam ya dafe saitin zuciyarsa yana wani lumshe ido irin dai ƙauna takai ƙauna kenan.
Hibbah kam kamar zatai kuka murya ƙasa-ƙasa ta ce, “Dan ALLAH a rage yamin yawa”.
Bai ma nuna yajita ba, balle tasaka ran zai karɓi ƙorafinta. Sai ƙaramin bowl ɗin daya sha farfesun ya ture yana warwarar tissue ya goge bakinsa. Baya ya ɗanyi da kujerar yana ɗaukar wayarsa yabar dining ɗin. Su Idris na ganin haka sukai azamar cigaba da cin abincinsu dan sunsan yau akwai aiki tunda basu sami damar yi a daren jiyan ba saboda abinda ya faru. Ɓata lokaci kuma yana nufin amsar hukunci a wajen babban yaya.
Khalid ne da yaga Hibbah na tsakurar abincin yace, “Aunty Queen ALLAH ki maza dan yana kallonki”. Hararsa tai tana tusa doya cikin baki. “To shikenan ashe da rabon ai miki ɗura ko”.
Cokali ta ɗauka zata jefesa yay saurin mikewa yana dariya sauran ma na tayasa. Tashinsu a dining ɗin ya bata damar cigaba da cin abincin, sai dai kunnenta na jiyo mata bayanin da yake musu wanda bata fahimta ba cikin muryarsa da ke tabbatar da mura ta shakesa bana wasa ba. Har ya gama jawabinsa duk suka mike bata kammala ba. Sai da Habib ya fito yana sanar mata tayi maza ta kammala ita yake jira sannan ta mike. Ganin yana tattara kwanikan ta tayasa suka kai kitchen. Fitowarsu yayi dai-dai da fitowar su Salis cikin sabon shiri. Da kallon mamaki ta bisu ganin kowanne ya canja kamanni zuwa na daban. Zatai magana Master ya fito, dole ta haɗiye tata ta dauke kanta dan bata son koda wasa su haɗa ido.
Cikin dakewarsa da ƙasaita ya fara magana cike da gargaɗi. “Ku kula, komai kanƙantar matsala ku sanar dani. Khalid kai da Salis zaku tafi a napep. Idris da Musbahu ku hau mashina. Idan komai ya dai-daita ku sanar dani muma zamu taho. Musbahu ka tabbatar duk layin da zaka shiga ya zamto mai tsayi ne, kamar na masu amsar ATM ko Customers care ”.
“Insha ALLAH sir”.
Musbahu ya amsa cike da girmamawa. Kallonsu kawai Hibbah take tamkar ta samu television. Mamaki bai nema halakataba sai da taga sunkai zaune a falo sunyi addu’a nema nasara ga UBANGIJI kafin su Salis duk su fice a barta ita da sauran sai shi. Batare da ya kallesu ba yace. “Ku kuma ku biyo ni”
_______________________________
☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠☀️🔴☀️🟠
*_K’AMSHI,K’AMSHI RAHAMA NE MATAN DA SUKA AMSA SUNANSU MATA SU SUKA SAN MUHIMMANCIN DA K’AMSHI YAKE DASHI MUSAMMAN A WAJAN MAI GIDA ,_*💃🏻💃🏻
*_Zafafan turarruka masu zazzafan k’amshi hade da wasu irin manyan sirrika na mallaka cikin sauki ba boka ba malam hajiya , Zaki jefe tsuntsu biyu da dutse d’aya , domin zamowa star azuciyar mijinki_*🌟🌟🔥
*_nasan dai kunada labarin mashahuriyar Mai Saida kayan k’amshin Nan Wanda akafi sani da *HUMKAM GIDAN K’AMSHI* *_a wannan karon ma ta sake kawo maku da sabbin kayanta masu abun al’ajabi Wanda da kud’i k’alilan zaku more zafafan turarruka Kuma ki shiga jerin Mata masu aji_*
*IDAN SARI KIKE BUKATA INA BADAWA SANNAN INAGYARAN JIKI CIKI DA WAJE SHIN KINA FAMA DA INFECTION INA HADA MAGANIN SA DA IZININ ALLAH KISHA KI WARKE*
*Kadan daga cikin kayan da muke dasu*👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*BLACK KAJII*
shin kina bukatar turaren da Zaki turara gidanki ya dauke maki warin sanyi ya kwana biyu Yana k’amshi ,?ki saye black kajiji Zaki Gane banbancinsa da sauran wannan ba k’amshi kawai yake ba idan kina turara. Jiki dashi Yana maki maganin kala kala ciki kuwa har da na sanyi , nemi naki Kar ayi Babu ke☀️🟢☀️🟠🌟08132506044 HUMKAMINCENSE
*ANA WA HABIBY* Wannan harkan na oza room ne special turare Dan matan aure kadai yana dauke da abubuwa Wanda bazan fadesu anan ba sannan bashi kadai bane akwai Crazy powder da na ke hadawa dashi zakisha garin sannan kishafa turaren hmm
*SUDANESE HUMRA* Turare dake dauke da sirrika Mai DAUKAR hankali kamshin ya banbanta da sauran turare Hajiya babbar sirrine Wannan hadin manyan Mata 08132506044 HUMKAMINCENSE
*GLOWING OIL*
Wannan yasha bam bam da irin Wanda kuka Saba gani ,Yana kashe kuraje Yana cire tabo Yana maganin kezbi da duk wani matsalan fata ,stretch marks duk Yana ciresu ….
*MOWAR MACE*
turaren mowar mace turare ne da larabawa suke amfani dashi Wanda da yawa mutanenmu Basu San da wannan iccen ba Mai dauke da magani k’amshi da sauran abubuwan masu matukar amfani ga fata ba
Shi wannan iccen yanasa hasken fata yanasa fata tayi laushi da santsi sannan d’an alk’awari ne matuk’ar kina amfani dashi zai tsirga maki cikin fata ta yadda ko Bakiyi amfani dashi ba zakiji k’amshin shi na fita ta cikin fatar ki ,ke amfanin iccen mowar mace yanada yawa jaraba ko don gyaran fatarki , 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Muna gyaran jiki na amarya da uwargida zakizo har gida ayi maki gyaran jiki irin na Mata masu aji zakiyi kyau kiyi fresh ga kamshin da zai Kama jikinki💃🏻💃🏻💃🏻
Munada 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*JAS OUD* (hatsabibin turare kenan )
*AL’AJAB* ( Mai abun mamaki kenan )AL’AJAB Turaren tsuguno mai abubuwan Al’ajabi Yana maganin sanyi (infection) Yana matse HQ (Tightening)sosai 08132506044 yasa HQ dumi yasa jikinki da hq kamshi lokacin da kike AMFANI dashi idan Yana shiga gabanki zakiji wani Dadi na ratsaki Yana k’ara Dadi da Yana ciko gaba ya rikita oga🙈
*FIRST LADY* na Mata masu aji turaren Kaya Dana daki
HAWII
KAJIJI
HALUT
👸🏻 *_PRINCESS_*
_Sabon turare Dana hada na shafawa ajiki da gashi *PRINCESS* Yana da Dadi cool kamshi gare shi babu hayaniya na fad’a muku sabbin turaruka na Nan tafe princess na daya daga ciki kisayi *PRINCESS* kiji sabon Hadi me sanyin kamshi babu kosarwa da ace zan iya zabi tabbas zan zabi princess a matsayin turaren gashina zan dauki princess ya zama shi zan farawa shafawa jikina idan zan kwanta zan dauki *PRINCESS* sbd yara na Dan kamshi bamai hayaniya bane musamman zan rika yi musu amfani dashi *PRINCESS* salon na daban kamshin daban dadin na daban *PRINCESS* Zabin ku ne Zabin Humkam shine farin cikin ku Masoya *PRINCESS* gidan kowa_
Duk wad’an Nan turarruka ne hatsabibai masu rikita mazaje masu wani irin k’amshi Mai shiga zuciyar masoya 💃🏻💃🏻💃🏻
*SHU’UMAR HUMRA*
ke daga jin sunan kinsan ta dabance mashahuriyar humra ce ta tayi shuhura wajan birkita tunanin Yan maza , humra ce da indai namiji yajita a jikinki to komai muskilancinshi sai ya susuce maki tana tado da sha’awa shauk’i sirrin mallaka, cikin kankanin lokaci ki rikita maigidanki da daddadan k’amshin ki😍😍😍🥰
*HUMKAM GIDAN K’AMSHI INA NAN ZAUNE A KANO GA MASU BUK’ATAR ZAFAFAN KAYANA INA AIKAWA KOWANE GARI DAKE NIGERIA HAR MA DA K’ASASHEN K’ETARE , KARKU MANTA A DADE ANAYI SAI GASKIYA* 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
________________________________
Duk mikewa sukai sukabi bayansa. Ganin Hibbah batako motsaba Habib yay mata alamar ta taho. Da ga can table ɗin da aka ajiye computers suka nufa. Kowa ya zauna ɗaya Hibbah dai na tsaye. jerarrun atishawa ya saki a cikin tissue ɗin daya warwara kafin ya dubeta da idanunsa dake jazur. “K zauna nan”.
Yay maganar yana nuna mata kujerar dake kusa da inda yake tsaye. Idanu taɗan waro waje zatai magana ya tsatstsareta da nashi cikin gargaɗi. Tarasa miyasa take jin yau gaba ɗaya bazata iya masa tsiwa ba. Haka kawai wani irin shegen kwarjini yay mata ga kunyarsa da takeji matuƙa. Zuwa tai ta zauna a kujerar da ya ɗan ja mata baya.
“Zaidu! Ka tabbatar ka dakatar da number Alhajin Mande daga shigar kira ko fita na tsahon awa guda shi da A.G. Adam! Accaunt na Engineer da Dr Sufi ka karasa aikinka na jiya a kansu, duk sauran kuɗaɗen dake a sauran bankunansu ka maida kuɗin a accaunt ɗinsa da na baka. Zakuyi da sauri. dan su Salis na gab da kaiwa, a yanzu haka suna cikin holdup ne”. Ya ƙare maganar idonsa akan agogon dake a tsintsiyar hannunsa alamar tanan yake bibiyarsu.
Gaba ɗaya Hibbah tama rasa kalar tunanin da zatai, dan duk sun wani daburta mata ƙwaƙwalwa. Taja numfashi da sauri jin ya ranƙwafo ta bayansa, tare da ziro duka hannayensa biyu ta gefe da gefenta ya dafe table ɗin. A sarƙe taja numfashi tsigar jikinta na tashi, “Zaki fara aikinki da ga yanzun madam”.
Yanda yay maganar a hankali saitin kunenta ne ya sata ɗan janye kanta, sai hakan ya bata damar jingina da kafaɗarsa ta gefen haggu, da sauri ta sake gyara zamanta a yanda take tana cigaba da shaƙar mayen turarensa dajin hucin zazzaɓinsa. Master da ke daƙilar keyboard ɗin Computern gabanta ya cigaba da mata bayanin abinda zatayi da nuna mata.
“Shi aikin akan minene?”.
Ta faɗa cikin rawar murya.
“Babu ruwanki da ko na minene. Ke dai kiyi kawai”. Yay maganar yana ɗaukar hannunta ya ɗaura bisa mouse ɗin. Yatsansa manuniya ya ɗaura akan nata dake dai-dai kan ƴar tayar tsakkiyar mouse ɗin. Tai ƙoƙarin janyewa ya matse hannun. “Ki nutsu bana son shirme fa ok!”.
“Amma ai ya kamata a sanarmin aikin kafin nayi”.
“Ashe baki son komawa wajen Ummi kuwa”.
Amsar tasace ta sata sake ƙwaɓe fuska tamkar zata fasa ihu. Ga a yanda suke duk kunya ya dabaibayeta. Badan kujera data shiga tsakanin bayanta da ƙirjinsa ba a yanda suken tamkar ya rungumeta ne. Sai da ya gama nuna mata duk yanda yake bukatar tayi kafin ya janye jikinsa da ga nata. Wani wawuyan ajiyar zuciya ta saki lokacin da yake mikewa. Har sai da su Habib suka ɗan kalleta. Dan tunda ya duƙo kanta basu sake yarda sun kalli sashen da suke ba. Wata ajiyar zuciyar ta sake saki ganin ya nufi hanyar bedroom ɗin da suka kwana. Badan yace idan ta ƙiyi bazai kaita wajen Ummi ba da tabbas bazatayi ɗin ba, amma tana buƙatar ganin ahalinta zata iya komai dominsu. Kusan mintuna goma sha uku da shigarsa sai gashi ya fito. Badan ta tabbatar da bayan shi ɗin babu wanda ya shiga ɗakin ba da babu yanda za’ai ta yarda shine. Ya canja kayansa zuwa manyan kaya irin na tsoffin dattijan Alhazan kauyen nan harda rawani, ga uban farin sajen da ke akan sabuwar fuskar daya canzo sak wani dattijon ƙwarai irin wanda basuko damu da duniya ba. Sai sanda a hannunsa da dogon carbi. Hannunsa kansa sun canja da ga nasa zuwa kalar fuskar zam. Ya zaro ƴar karamar wayar nokia ɗin data sha wani shegen farin salatap da har ya fara komawa brown dan tsufa. Kunnensa ya kai alamar kira ya amsa. Yana sauke wayar a kunne yana duban su Adam da suka mike.
“Done”.
Suka faɗa a tare shi da Zaidu. Kai ya jinjina musu yana maida dubansa ga Habib. “Ka kula da komai, abinda bata gane ba ka nuna mata, aikinta ne na tsakkiya samun matsala daga gareta yana nufin komai zai ɓaci”.
Kai Habib ya jinjina masa da faɗin, “Insha ALLAH mune da nasara. ALLAH ya dawo daku lafiya”.
Amin ya faɗa yana duban ɗakin da su Zaidu suka nufa, sai kuma ya kalli agogon hanunsa irin na sarƙa ɗin nan da yaci duniya ya koɗe matuƙa duk da Silver ne dama. Dai-dai nan su Zaidu suka fito da sauri cikin sabuwar shiga suma. Daka kalli Adam bashi da maraba da driver. Zaidu kam tamkar irin yaran alhazan kauyen nan da bakinsu bai rabo da tsugudidi. Ga jikka ya riƙe wadda ko ba’a faɗaba kasan ta alaramma Muhammad Shuraim Master ce dai.
“Ga kuɗin an shirya Master”.
Zaidu ya faɗa yana buɗe jakkar hannun nasa mai kama da karamin akwatin maza na tafiya. Shiryayyun kuɗi ne a ciki ƴan ɗari biyar-biyar da ɗari bibbiyu. Kai ya jinjina masa kawai alamar komai yayi.
Inhar ana mutuwa a zaune to yau dai da alama Hibbah ta mutu. Dan harsu Master suka fice a falon bata gama dawowa hayyacinta ba sai da Habib ya fargar da ita. Cikin alamar ruɗani tace, “Ina zasuje wai?”.
Murmushi Habib yayi yana ɗan matso da kujerarsa kusa da tata kaɗan. “Aiki zasuje mana.”
“Aiki?”.
Hibbah ta faɗa cikin sigar tambaya. “Babu lokacin tambaya aunty Queen mu cigaba da namu aikin dan mune tamkar ƴan jagorarsu. “Gaskiya indai satar kudaɗen mutanene bazanyi ba”.
Tai maganar tana ƙoƙarin mikewa. Kamar daga sama taji muryarsa yana faɗin, “Ashe kuwa ke da Ummi har abada. Na kuma gama aiki nace yayunki sukayisa”.
Waige-waige ta shigayi cikin falon sai dai babu alamarsa. Sautin muryar tasane kawai data kasa fahimtar da ga ina yake fitowa. Kuka ta fashe dashi tana komawa ta zauna a kujerar. Lallai ta tabbatar yau tana a tsaka mai wuya. Abinda takeji a labari yau shi hannunta zai aikata.
“Kuka bazaiyi magani ba aunty Queen, duk wani motsinki dake anan tamkar akan idonsa ne garama kiyi kawai”.
Habib yay maganar cike da lallashi. Kamar ta makesa shima takeji, shiyyasa taki tanka masa ta cigaba da abinda takeyi zuciyarta na kawo mata wani shawara acan gefe. Yarda da shawaran yasata share hawayenta ta maida hankalinta ga aiki kamar yanda Habib ke nuna mata shima yanayi.
A ɓangaren Master kuwa sun isa banki a tsohuwar motar da Adam ya tuƙasu. Adam ne ya taimaka masa ya fito a motar shi a dole ga dattijon da yaci duniya jiki yay laushi. Yana gaba Zaidu na biye da shi yana zuga surutu da kyalƙyala dariya irin dai garorin nan yan bani na iya na gefen alhaji. Shiko Master sai wani gaftarar goro yake yana ƴar dariya da bama Zaidun amsar wasu zantukan nasa.
Gaba ɗaya kallon garori securitys ɗin bank ɗin sukai musu. Bayan an dubasu babu alamar wani abun ashha tare da su aka basu damar shiga. Yanda Zaidu ke zabga surutu Master na dariya yasa mafi yawan mutanen dake akan layin tura kuɗi da amsa kallonsu, wasu na musu dariya wasu na musu kallon ƙauyawa ne. Master dake lure da motsin kowa ya yafito wani gaye da ya tsuƙe cikin shigar manyan yara yanata bada iska. “Yaro yaka nan ka taimakeni, dan wannan mai bakin kamar bututun mai yanda bansan a ba shima ba bihim ya sani ba. Garama ni nayi yaki da jahilci lokacin da nake zuwa sarin atamfofi na manta wasu abubuwanne kawai.
Gayen da gaba ɗaya ya gama ƙiyastama ransa tsuntsu da ga sama gasashshe ya karaso yana wani taɓe baki. Wata cimirmiɗaɗɗiyar takarda Master ya fiddo a aljihu ya mikama gayen. “Yarona duba mini nan, ƴan kuɗaɗena na kayan amfanin gona dana noma na sayar zan buɗe akawun na zuba. Nima jikana dake can kudu ya bani shawara amma yace na nema wannan daya rubuta min anan zai taimaka mini aimin komai na buɗe akawun din na zuba kuɗaɗena a ciki naje gida nai barci babu ruwana da takadarai”.
A karon farko gayen ya dashare baki da faɗin, “Ai babu damuwa baba koni ma na maka. Kaga zomuje can sama acan ake buɗewa.”
Babu musu Master ya amince. Suka nufi saman bene Zaidu na biye da su. Gaye da gaba ɗaya hankalinsa nakan jakar hannun Zaidu ya sami ma’aikaci guda sukayi magana. Form aka basu da zasu cike suka koma can gefe inda babu yawan mutane.
A ɓangaren master tun shigowarsu wajen yaga Musbahu, shima kuma ya gansa dan cike da ƙwarewa sukaima juna alama da ido. Kafin Master ya ɗauka ƴar nokia ɗinsa ya fara magana da ƙarfi har hankalin mutane na dawowa kansa. Wasu na dariya wasu na tsaki wasu taɓe baki. Dan kuwa dai garanci zam Master ke zubawa abinsa Zaidu na tayasa cikin kwakwazo shima.
Da wannan damar gaye yay amfani wajen saƙala hannunsa a hankali ta ƙasan teble ya zuge jakkar hannun Zaidu. Rafar yan dari biyar ya jawo har sau uku ya tura aljihu, yayinda a gefe tuni Zaidu ya sane wayar gaye daya ajiye akan table shi kuma. A dai-dai nan Musbahu yazo a ɗan fusace yana faɗin, “Haba baba dan ALLAH kake magana a hankali mana. Nan fa ba ƙauye bane ko gida cikin banki ne”.
Cire wayar Master yay a kunne yana zabgama Musbahu dakuwa. “Kaci gidanku dan bantan ubanka. Anki ayi a hankalin idan lahirace nan ɗin jefani a wuta. Mara mutunci takadarin banza.”
Yanda Master ke masifar yasa mutane fara bashi hakuri da nunama Musbahu kuskurensa na kodan furfurar Master ɗin ya kamata ai ya tauna harshensa yay masa magana ta hankali. Yayinda wasu kejin daɗin abinda Musbahun yayi. Ga Zaidu da tuni ya zurama Musbahu wayar gayen nan a aljihu yana nunashi da dan yatsa alamar bama ogansa kariya. Yanda suke abun baka isa tunanin suna da wata alaƙa ba. Musbahu ya fice a wajen a fusace saboda securitys da sukazo suka tasashi gaba. Yayinda suke bama Master dake matsar kwalla haƙuri.
Sai da wajen ya samu nutsuwa Gayen nan ya cigaba da cikema Master form yana tambayarsa. Yayinda Master ke amsa masa cikin raba hankalinsa. Dan nokia ɗinsa yake ta dannawa wai yana neman lambar jikansa daya sakashi zuwa ya buɗe akawun……….
Anan bangaren Hibbah kam aiki take yanda Habib ya nuna mata hankalinta na ga ɗakin da suka kwana. Habib na cewa su ɗan dakata ta miƙe wai zatayo fitsari. Ɗakin ta shiga ta maida key ta kulle ranta fal farin ciki, dan tayi alƙawarin saita buɗema su Master aikin da suka tafi yi. Wadrobe ta nufa ta fiddo wayar da taga ya ajiye a ciki yau da safe, cikin sa’a kuwa ta ganta. Koda ta ɗakko a kashe take, cikin rawar jiki ta kunnata sai ko gata ta kawo. Wani ɗan tsalle ta buga zuciyarta na mata canki in canka akan wayarwa zata fara kira ne. (Ta yan sanda) zuciyarta ta bata tabbaci. lambobi da yaya Abubakar ya taɓa sanar mata cewar na taimakon gaggawane da ga hukumarsu ta loda a wayar, cikin sa’a tanayin dialing kuwa ta shiga😱…………..✍
(Hibbah😬😬😬🙆🏻🤦🏻).
*_Kuyi haƙuri na zama sai a hankali sa kun haɗa da addu”a_*
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI……_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*
*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽
#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
GIPHY App Key not set. Please check settings