TAKUN SAKA 34

Advertisement

*_Typing📲

*_Zafafa biyar na kuɗi ne. Dan girman ALLAH ki saya kafin ki karanta. Muna haɗaki da ALLAH idan kin saya karki fitar mana saboda hakan cutarwa ne a garemu da ke kanki da kika saɓa mana alƙawari ta hanyar zalintarmu da son ruguza mana kasuwancinmu._

*_ZAFAFA BIYAR FACEBOOK LINK👇🏾_*

https://www.facebook.com/groups/494948898814888/?ref=share

*_ZAFAFA BIYAR INSTAGRAM LINK👇🏾_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=u8e91axrluzc&utm_content=nj79azb

Advertisements

______________________

*_Chapter Thirty Four_*

………..Harta yanke ba’a ɗaga ba, sai dai da ga ƙarshe ake sanar mata ta dakata ana amsa wasu kiraye-kirayen ne. Bakin gado taje ta zauna tana sauraren a ɗaga ɗin, dan an saka taken ƙasa ne domin kar a bar mai jira shiru. Kusan mintuna uku ba’a amsa mata ba taji haushi ta yanke. Tagumi ta rafka ranta zattakaici, taci alwashi duk ma yanda za’ai a yau ɗin nan sai tayi sanadin da za’a kama Master da su Halilu. Bazata yarda ta kira yaya Abubakar ba dan gudun kar’a sake irin na farkon kaita wajen ƴan sanda.

  

       ★★★★

     A ɓangaren su Master kuwa koda Musbahu ya fita sai ya koma can gefe. Da wayar gayen nan da Zaidu ya sano musu yay amfani, sai da ya tabbatar yayi duk wani abunda bazai saka rayuwar gayen a haɗari ba sannan ya ƙaddamar da shirinsu. Cikin ƙanƙanin lokaci shi da Master dake can ana cike masa form yana danna waya da subaɗi suka shiga wawasar kuɗaɗe. Yayinda acan kuma su Salis suma suke kaddamar da nasu shirin akan sauran asusan. Dan yau aikine ba’akan mutum ɗaya ba. Kusan asusu goma sha zasu yashe a ƙiyasi.

          Master na gab da tatse kuɗaɗen asusai uku daya haɗa gabansa yay wata irin faɗuwa. Addu’a yay saurin karantowa zuciyarsa na harbawa da sauri-sauri. Cikin sauri ya dubi Zaidu.

Advertisements

      “Ba’are anya kuwa baƙaƙen shanun gidan ɗan sandamu basu shirin kaima gonata ta yammaci hari? Inaji a jikina maƙwafcina ya samu damar yimin ƙafar angulu kuwa”.

        Kai tsaye Zaidu ya fahimci zaurencen, dan haka ya ɗan kallesa a ɗan firgice. “Alhaji Baba wanne maƙwafcin a ciki? Mati mai igiya ko sambo?”.

       “Bansan waye a cikiba ba’are, sai dai zuciyata na min zargin Mati mai igiya ne dan nayi kuskuren ajiye wayar lantarkin nan da za’aimin wayarin wuta a kogon ɓaure. A lokacin Kuma Mati na cikin gonata zai bani taimakon ruwa saboda zafin ranar da akai jiya. Inhar hasashena yayi dai-dai akan idonsa na ajiye wayar lantarkinnan. Ɗakko tarho ɗinka ka kira min ɗan ƙane ka shaida masa ya leƙa gonata ya bincikamin waya a cikin kogon ɓaure, sannan ya sanar maka Mati mai igiya yana kan tudune koya tashi?”.

       “An gama alhajin ALLAH”.

Zaidu da duk jikinsa ke tsuma ya faɗa yana nufar hanyar fita daga cikin bankin. Waya master ya ɗaga yay kira. Ana dagawa ya fara magana cikin wani zaurancen. “Sallau kun gama tattare harawar nan kuwa?”.

       Gaban Salis dake gab da kammala nasa aikin ya faɗi. Cikin ɗan waige-waige ya bashi amsa da faɗin, “Muna gab dai”.

       “To maza kuwa ku tattare dan Mati mai igiya ina tabbatar da ya turo baƙaƙen shanun ɗan sandamu cikin gonar yamma. Da alama kuma zasuyi ɓarna bawai a gonata kawai ba harda ta maƙota. Kuyi himmar tafiya gonar yamman harda su Kalla ku tasamin ƙeyar mati kafin shanunsa su iso ya koma gabashi. Ni kuma zan kira maigari na tabbatar masa tsiyar da matin ke shirin tafkawa”.

     Lokacin da Master ke wannan ƙoƙarin na fargar da yaransa halin da ake ciki a dai-dai lokacin Hibbah ta sake kiran wayar. Kuma cikin sa’a aka dauka mata. Jikinta har rawa yake jin an amsa. Daga can aka tabbatar mata ta kira wayar taimakon gaggawane daga police station mai lamba talatin da uku a anguwar andu dake jihar. Wane taimako take buƙata. 

       “Babu taimakon da nake bukata, ina dai tabbatar muku a yanzu haka gawurtaccen barawon nan da yaransa na kan hanyarsu ta wawasar kuɗaɗen wasu mutane ta banki. Nima satoni yayi yanzu haka sun barni anan gidanne sun wuce”.

      “What!?”.

Aka faɗa daga can ana mikewa. “Ƴammata minene sunan anguwar da kike yanzu haka?”.

       “Nima ban sani ba yallabai. sai dai ku bibiyi wannan kiran nasan zaku dace. Dan a yanzu haka suna gab da dawowa na tabbatar”.

      

★★★

      *_Bank_*

       Cikin jin haushi gaye yace, “Nikam Baba kodai baka shirya buɗe accaunt ɗin nan bane na kama gabana? Inada abunyi fa na zauna taimakonka amma sai wani kiran waya kake akan wata wayar lantarki ɗin banza ne ko harawa ma oho maka”.

         “Kai ja’iri waccan harawar tanada mahimmacin da tafi wannan buɗe akawun ɗin. Kaga nama fasa buɗewar sai wani satin zanzo da jikana muzo tare.”

     Master yay maganar yana mikewa. A take mutane suka shiga bashi haƙuri da wasu ma’aikatan bankin, amma fafir yaƙi dan gab aikinsa yake da kammala shiyyasama ya tsaya yana biye musu. Kuɗin daya wawasa na kammala shiga accaunt ɗinsa wani irin jiniya ya fara a cikin bankin. Yanda abin yazoma mutane a bazatane ya tsoratasu bankin ya hargitse aka fara fita a guje. Tuni master yabi rububi ya fice bayan ya cire babbar rigarsa da mask ɗin fuskarsa ya yarda, da sandarsa da carbi. Securitys da ma’aikatan bank ɗin da sukasan minene ma’anar jiniyar dan an sakatane saboda tsaro dama hankalinsu yay masifar tashi. dan fara ƙaɗawar jiniyar yayi dai-dai da fitar maƙudan kuɗaɗe a cikin wasu asusai biyar na manyan mutane dake bank ɗin. Ƙoƙarin hana mutane ake fita ta ƙarfin tsiya, yayinda daga cikin bank har sun kira jami’an tsaro.

     Master na fitowa ya sake cire dayar mask ɗin face ɗinsa ya yarda, dan zuwa yanzu zuciyarsa ta gama bashi Hibbah ta ɓallo musu ruwan da yafi na bankin tsauri. Sam baiyi tunanin taga sanda ya ajiye wayar nan ba. Babbar damuwar wayace da sam babu wani tsaro tare da ita sai idan tana a kashe. Dan yana amfani da itane wajen yin magana dasu A.G, ya tabbatar inhar ta kunnata ko tai kiran wani cikin sauƙi zasu gano inda take musamman da ya san saƙon da ya aika na wawashe musu kuɗaɗe zuwa yanzu ya isa garesu. Hankulansu yana a tashe ne, tare da tsintar kansu ckin ruɗanin yanda akai reshe ya juye da mujiya.

★★★★

              Kamar yanda Master yay hasashe hakance ta kasance. Dan kuwa aikinsu na cika dukkanin wayoyin su A.G saƙwanin alerts na fitar kuɗi suka fara shiga musu. Duk da a mabanbanta wajeje suke kusan a lokaci ɗaya duk suka miƙe zumbur a cikin matuƙar ruɗani da tashin hankali kowa na tambayar mike faruwa? Yaya haka?. Zukatansu na jera musu waɗan nan tambayoyin suna ƙoƙarin kiran juna. Cikin ƙanƙanin lokaci suka fahimci cewar ɗan zakin da suke tunanin sun raina ya girma. Dama a kwanakin nan babu abinda sukeyi sai zaman meeting akan Master. Dan zukatansu na raya musu lallai akwai abinda yake shiryawa shiyyasa yaƙi basu kuɗaɗen da ake tarawa tsahon shekaru biyu. Sun yankema kansu shawarar yana kammala musu aikin nan da suka bashi zasu ruftashi kawai. Sai gashi shi ya fara rufta rayuwarsu alamar shirinsa daɗaɗɗe ne a kansu.

     A.G ne ya saka bibiyar masa number master ɗin duk da basu da tabbacin samu, ana tsaka da bibiyarne batare da an samu ɗin ba Hibbah ta kunna wayar, cikin hanzari jami’in da ke zaune a computer room ɗin nasu yana aiki akan number ya sanarma A.G. shine ya bashi damar yin azamar saita layin akan duk kiran da za’ai ya shigo wayarsune, sannan ya bibiyi a inda lambar take. Shi kuma ya fita yana bada umarnin a haɗa runduna za’a fita operation na gaggawa. Yana dawowa computers room ɗin ya samu Hibbah na zuba bayani ta waya, kuma komai akan kunnensa shima ta zayyane.

       

         A ɓangaren Abba shi kuwa sai da aka fara lasa masa zumane, dukannin kuɗaɗen dake a asusun mahaifin su Hibbah sai da aka juyesu a asusun sa. Farin ciki ya sakashi kaiwa duƙe yay sujida (irin mufa mun fara tsoron ALLAH ɗin nan). A lokacin duk yaransa na zagaye da shi dan an sallamo Junaid ne yau da ga asibiti duk da bawai ya warke bane ba. Gaba ɗayansu galala sukai suna kallonsa. Ameera tace, “Abbah halan yau wani ya maka kyautane? Dan inba kuɗi ba banga abinda zai sakaka wannan rawar jikin ba harda su salla babu alwala babu kallon gabas?”.

      Farin cikin da yake a cikine ya hanashi tanka mata, sai baki da ya sake washewa yana nufar hanyar bedroom ɗinsa cikin ɗunbin farin ciki. Sai kuma ya dawo da baya domin ɗaukar babbar wayarsa da nufin turama Master kuɗin tukuyci kafin yaji farashin sauran na aiki. Dan ya saka a ransa ko nawane Master ya nema sai ya bashi harma da ƙari. Yana ƙoƙarin ma Master transfer ɗin dubu ɗari biyar na tukuyci wasu sabbin alerts ɗin suka fara rige-rigen shigowa. A zatonsa wasu kuɗinne suka shigo dan haka ya buɗe da zumuɗi.

      “Wayyyyiiiihuuuuuu!!!!! Ni Halilu na mutu!”.

     Ya faɗa a matsanancin firgici har sai da su hajiya mama suka toshe kunnuwa suna miƙewa tsaye a matuƙar firgice ganin Abba ya yanke jiki ya faɗi a wajen wayoyin duk sunyi gefe.

★★★★★

     Abinda ke a kunnensa ya danna lokacin da yake shiga motar da sukazo yabar wajen, dan tuni su Zaidu sun ware. “Habib ka ɗauki yarinyarnan yanzun nan kubar gidan nan, ka tabbatar kafin ku wuce ka kashe wayar hannunta ka cire sim card ɗin ciki kayi flushing ɗinsa. Ga su Zaidu nan isowa. Kubi ta cikin store ɗin kitchen akwai hanyar da zata fiddaku ta wancan layin.”

     Sosai hankalin Habib ya tashi, dan yanzun nan dama ya kama Hibbah da waya. Yana tsaka da tambayarta ne kiran master ya shigo masa. Wayar ya fusge daga hanunta a fusace ya takata bayan ya fashe. murfin ya ɓalle da kyar, ɗan pin ɗin dake jikin blackboard ɗin inda computers ɗin suke ya ɗauka ya cire sim card ɗin ya karya. Yay azamar danna wani abu a jikin teble ɗin yay ƙasa. 

    Baki Hibbah ta taɓe dan a ganinta kafin ya gama duk wannan abun da master yace ta tabbatar ƴan sanda sunzo. Ranta fes yau ALLAH yayi dubun masu aikata saɓon ALLAH ya cika.

       Dawowar Habib yayi dai-dai da shigowar su Salis kusan a tare. Gaba ɗaya firgice suke. Jakunkunansu suka shiga ɗakin da suke kwana suka tattaro. Habib ya fisgi hanun Hibbah da duk abinda suke tana tsayene kamar dogariya tana kallonsu. Sai faman taɓe baki take irin ko’a jikinta ɗin nan. Hannun ta fige tana ture Habib, a dai-dai na Master ya shigo falon shima. 

      “Ku tafii!!!”.

Ya faɗa da ƙarfi jin jiniyar ƴan sanda na gabato anguwar. Yay maganar yana nuna musu hanyar kitchen, kallo ɗaya zakai masa kai kanka ka firgita dan gaba ɗaya ya rikiɗe tamkar wani bajimin zaki. Kobi takan Hibbah da tsawarsa ta firgita baibi ba. Ya nufi ɗakin da suka kwana cikin zafin nama. Mintun uku tsakani ya dawo falon, wanda yay dai-dai da ƙarasowar ƴan sandan ƙofar gidan. Ga kuma Hibbah data nufi hanyar waje da gudu. Baya ya take mata shima. Sabon tashin hankalin daya yunƙuro masa ne yasashi fisgo Hibbah cikin zafin nama ya yarfa mata wani shegen mari mai azabar zafi da saida jinta da ganinta suka gushe na wucin gadi. Ya kama kunnenta ya murɗe da shegen karfi yana magana cikin matuƙar hasala da hargowar da bata taɓa gani tare da shi ba. “Stupid girl!!, idan ni baki kasheni ba, ke da hannunki da wannan shegen taurin kan naki zaki kashe ahalinki”. Wani irin rawa jikinta ya fara hawaye na mata ambaliya akan fuska. Ya turata ta zube ƙasa dan ji yake kamar yay mata bugun mutuwa kozai huce daga abinda yakeji a halin yanzun. Sake miƙewa tai da gudu, Fitowarsu compound ɗin gidan yayi dai-dai da shigowar ƴan sandan cikin gidan. 

        “Ku buɗe musu wuta gaba daya!!!”.

     A.G ya faɗa da ƙarfi. 

        A razane wani a ciki ya bashi amsa da cewar, “Oga yarinyarfa data bamu information akai gata tare da shi”.

       “Har ita ku haɗa”.

A.G ya faɗa cikin karaji. Ba ƙaramin firgita Hibbah tayi ba. Ta waiga ta dubi Master take biyota ta kalli ƴan sandan da suka saita bindugu akansu da alamun cika umarnin ogansu zasuyi ta rumtse idanu da ƙarfi wasu zafafan hawayen nadama da dana sani na sakko mata. Ita data bada bayani akansa amma jami’in tsaron daya kamata ya bata kariya wajen kubutar da itane ke cewa a harbeta baida matsala. Wace irin ƙasa muke da ita kenan? Ahaka akeson wanda yaga mai laifi ya tona masa asiri…….

           Master da gaba ɗaya kamaninsa sun canja duk da bindugun da aka saitasu da shi ya nufota a guje da alamar son kubutar da ita saboda harsasai guda uku da jami’an suka harbo gaba ɗaya kanta sukayi gadan-gadan, sai ɗaya ne ya nufosa shiko ya saka bullet proof jacket a jikinsa, yasan duk tsiya harbin bazai samu makasrsa ba sai dai idan kwanansa ne ya ƙare yau. Yana gab da isowa gareta bullet ɗin ya shiga cikin kafarsa. Ƙaramar ƙara ya saki yana kaiwa duƙe, hanunsa ɗaya na zaro karamar bindigar jikinsa shima ya fara maida murtani. Wani irin zabura Hibbah tai babu shiri ta nufosa, hakan ya bata damar gocema bullets ɗin da suka nufo kanta har guda biyu ɗaya ya sake samun master a hannu.

        Hankalinta ya ƙara matuƙar tashi ganin shi ƙoƙarinsa ya bata kariya, yayinda waɗanda ya kamata su bata kariyar su son kasheta sukeyi. Sam rikicewa ya hanats gane fuskar dattijo A.G. Shiko Master ya gansa ne duk da yana ƙoƙarin ɓoye fuskarsa garesa. Duk da tasan ya mata nauyi haka ta miƙa hannu ta kamo nasa tana kuka. Haɗin kai ya bata ya miƙe shima da ƙyar cikin dakiya da dauriyarsa duk da tuni jini ya ɓalle masa ta ƙafa da hannu. Kasancewar suna gab da ƙofar falon suka sami nasarar afkawa ciki, Master ya danna security jin A.G ya bama yaransa damar bin bayansu duk da dama ba daina harbin sukaiba ALLAH dai ne ya bama su Master kariya bayan biyun da suka sameshi wasu basu sake taɓasu ba. Jakkarsa daya yasar a falon ya ɗauka, da sauri Hibbah ta amsa ta goya a bayanta. Ya fisgi hannunta cikin bama kansa ƙwarin gwiwa suka afka cikin kitchen ɗin suma. Sai dai su a tsakiyar kicin ɗin ya tsaya ya haye saman table ɗin wajen duk da jini dake kwaranya masa. Hannu ya miƙa ta tsakkiyar p.o.p ɗin kicin ɗin ya burma sai ga ƙofa. Ya ɗan daka tsalle ya fisgo wani zare mai kama da tsani. Hannu ya miƙa mata ta ɗora nata sai faman wai-waige take jin ƴan sandan nata ƙoƙarin buɗe kofar falon. Ta tabbatar suka shigo kuwa sun gama yawone. Cak ya ɗagota duk da tanada nauyi.

        Da taimakonsa ta fara hawan zaren tsanin harta shige. Kafin shima ya fara hawa. Yana gab da shigewa suka sami nasarrar ɓalla ƙofar falon. Cikin sa’a ya ida shigewa da jan tsanin ya maido ƙofar ya rufo. Karan farko a tarihin rayuwa Hibbah a cikin zinc bisa gangancin da taso tafkama rayuwarsu. Wani ƙaton bututu kamar na ruwa suka samu cikin zinc ɗin, Master da ya fara ɗan galabaita saboda jinin dake fita a jikinsa dama ba isashen lafiyane da shi ba ya nuna mata cikin bututun da bata fitila ƴar karama mai shegen haske.

      Ɗan kwalin kanta ta cire tana kuka ta yagashi biyu, ƙafarsa ta ɗaure masa dai-dai wajen da bullet ɗin ya shiga. Sauran rabin ta ɗaure masa hannunsa. Cikin taune lips ya turata cikin bututun shima yabi bayanta dan yasan jinin da yake zubarwane zai nunama su A.G inda sukabi.

     Da rarrafe suka dinga kutsa kai cikin bututun batare da Hibbah tasan ƙarshemsa ba, balle inda suka dosa. Sunyi tafiyar da har sai da ta fara galabaita saboda ƙura sannan ta fara hango haske alamar karshensa kenan. Koda suka fito batasan inane nan ɗin ba. Amma dai gidane a wajen shima mai kyawun gaske. Ya fisgi hannunta ya danna cikin motar dake fake a wajen bayan ya yaye tanfol ɗin da aka rufeta da shi. Shima shiga yay yana jan numfashi da ƙyar dan idanunsa sun fara ganin jigari-jigari. A mamakinta sai gani tai ya danna wani abu gate ɗin ya buɗe kansa. Ya fita da motar da gudu daga gidan. Har daga nan tana iya jiyo jiniyar motocin yan sanda da karar harbe-harbe alamar gidan da suka baro kusa yake da wannan. Gudu yake tsulawa na fitar hankali wanda dole motoci da napep ke basa hanya. Masu zagi nayi masu kiransa ɗan giya nayi. Baimasan sunai ba. Dan bai tsaya ba sai a wata anguwa. Motar taga ya faka a wani dan lungu ya fita. Batare da yayi magana ba itama ya zagayo ya fisgota. Key wani mai shushaina dake a lungun zaune shi kaɗai yana gugar takalma ya jeho masa. Ya cafe dajan hannunta suka sake shiga wata motar, yayinda tunkan su fice a lungun ta hango mai shushaina ɗin nan na rufe waccan motar da tamfol.

         Wani irin tsoransa ne ya tsargama Hibbah. Ta kafesa da ido cike da alamar tambayoyi sai dai babu damar yinsu. Yanzu kam ta cikin anguwanni ya dinga bi da su har suka sake zuwa wani layi sukai canjin mota, anan ko motar kawai suka samu sai mai tallan rake a gefe can shi kaɗai. Sai da ya shiga motar ne ya yafito mai tallan raken yana cizar leɓe. da gudu mai rake ya turo Wheelbarrow ɗinsa zuwa inda suke. “Rake na ɗari uku”.

    Master ya faɗa da ƙyar yana lumshe ido. 

      Raken mai rake ya ɗebo ya zuba a leda. Ya turo kansa ta Window ɗin motar yana ajiye keys a cinyar master. “Gida mai lamba takwas, anguwar bauranya”.

     Komai masbaiceba yaja motar suka bar wajen. Gaba ɗaya hibbah ta mutu a zaune a karo na biyu, kallonsa kawai take kamar gunkiya har suka iso anguwar da mai raken taji ya faɗa. horn yayi maigadi yay saurin wangale masa gate ya danna hancin motar. Gaba ɗaya su Salis dake tsaye sunata faman kaikawo a compound gidan mai sashe biyu sukayo inda yay fakin. Hakama baba saude dake can zaune goye da Sharifat ta mike da sauri duk da batasan ainahin abinda ke faruwa ba. Kawai dai su Habib sunje sun taho da itane acan L.E street batare da sun mata bayanin komai ba.

     Kusan gaba dayansu suka rufu akansa. Yayinda wasu a cikinsu harsun fara kuka ganin yanda ya samu harbi. Ga jikinsa harya fara saki saboda jinin da ya zubar. Da taimakonsu suka nufi sashen da ke a hannun dama suna shartar hawaye. Yayinda Hibbah wani irin nadama ke sake shiga bargonta, dan itama kukan da taga su Habib nayine ya sake tayar mata da hankali.

     Kanta baba saude tayo ta kamata itama tana tambayarta miya faru?  Jikin baba saude ta faɗa tana girgiza kanta hawaye na kwarara mata. Sai kuma tai saurin barin jikin baba sauden tabi bayan su Adam. Itama Baba sauden bayansu tabi jikinta sai rawa yake ganin jikin Master duk jini.

        A falon suka zaunar da shi bisa wata kujera mara tudu mai laushin tsiya. Cikin sauri Musbahu ya dakko First aid box ɗin daya hango can gefe. Cikin sauri Khalid ya kai tsugunne ya fara warware dan kwalin hibbah data daura masa. Yayinda Idris ke kwance na hannun shi kuma. Cikin rumtse ido Khalid ya zuba masa ruwan magani akan wajen. Wata wahalalliyar ƙara Master ya saki yana sake damƙe hannun Zaidu dake gefensa. Khalid na kuka yasa wani ƙarfe cikin ramin ya fisgo bullet ɗin. Baki kawai Master ya datse da azabar ƙarfi. Tashi Khalid yay ya koma wajen hanun, yayinda Habib ya duka gaban kafar ya cigaba da treating ɗinta. Acan ma Khalid ya cire bullet ɗin hannun, ganin Habib bai gama treating ƙafar ba sai shi ya cigaba dana hannun.

         Tunda aka cire bullets ɗin wani irin zufa ke ketoma Master akowacce hudar gashinsa. Yayinda yaketa faman sauke ajiyar zuciya a jajjere. Sai da suka kammala tsaf suka goge jinin da duk ya bata ko’ina sannan ya buɗe idanunsa da sauri saboda abinda yazo masa a rai yanzun nan.

          “Ya ALLAH! Akwai matsala, akwai matsala!!”.

     Ya shiga faɗa yana jujjuya kansa. Hankali tashe su Salis ke tambayarsa wace irin matsala kuma?.    

        Bai iya basu amsa ba, sai wayar da ke a jikinsa ya laluba da sauri yana duban su Adam. Cikin wani yare da ko Baba saude bata taɓa ji Mastern yayi ba yayma su Adam magana. Cikin sauri suka nufi hanyar fita a falon suna amsa masa da girmamawa. Su biyar suka fice aka bar Idris da Khalid kawai.

         Da ido yayma Idris maganar da su kaɗai suke fahimtar yarensa ta hakan. Idris ya jinjina masa kai da duban baba Saude da har yanzu take sharar hawaye. 

         “Baba muje na kaiki ki huta ko? Karki damu komai yayi dai-dai insha ALLAHU ”.

     Badan baba Saude taso ba tabisa ɗauke da Sharifat dake barci a bayanta. Dan tunda ta fasa kuka sanda su Habib ke shiga gida suna ce mata tafito saita lallaɓata tai barci lokacin da suka shigo mota, koda suka iso gidan kuma saita goyata da gyalenta.

        Kuka sosai Hibbah keyi wanda ke sake hasala zuciyar Master. Sai dai da yake yanzu hankalinsa nakan wani abu daban yasa ya shareta. Sai da yaji ta cigaba da cika masa kunne ne ya daka matsawar da ba ita kadai ba hatta da Khalid sai da ya zabura.

      Idan baki bar min wannan garshekan kukan ba saina daddage kanki da bullets a gidan nan!!. Kuma ki tashi min anan kafin na hambaraki a ƙasa kanki ya bugi tiles ɗin nan!!”.

        Da gudu ta miƙe tabi bayan su baba saude. Dan yanzu kam ta tabbatar ada ba Master ta sani ba yanzu ne taga ainahin Master ganin idonta ba labari ba. Gaba ɗaya idanunsa sun koma na ainahin tsohon bahagon zaki da babu abinda ya sani sai farauta. Idanunsa kai kace aman wuta zasuyi saboda tsabar jan da suka koma.

             Kansa ya dafe da faɗin, “Ina ji kamar na kashe yarinyar nan a yau na manta da shafin rayuwarta a tarihina.”

        Sosai tausayinsa ya sake ɗarsuwa a zuciyar Khalid. Ya tabbatar yau Hibbah ta ballo ruwa na gaske wanda batasan harda aikin taimakon ahalinta suka fita ba. Mastern su baya kuka sai domin tausayin al’umma. duk haɗarin da zakaga ya jefa kansa a cikin domin taimakon wanine. Kullum wahala yake da mutane batare da sun san manufarsa ba. Kowa kallon ɗan ta’adda takadari yake masa. Hatsabibi shu’umi ɓarawo. Amma hakan bayasa ya sare daga aikinsa duk da waɗanda yake dan su ɗin ko 1% basu fahimcesa ba………….✍

*_Asirin da xoxo taimin yau ya warware🙄😏🚶🏻😖_*

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

 

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like