Advertisement
*_Chapter Thirty Nine_*
………..Duk da ba sanin mitake tattaunawa da zuciyarta yayi ba yaji a ransa yau ƙila har ALLAH ya isa sai tai masa. Tama nutsu ta tabbatar da shiɗin Isma’ill ɗinne ko wanine daban hakan ya gagara saboda rashin man kanta. Komai bai iya yace ba, yasa bargon kawai ya share mata hawayen da har yanzu sun kasa tsayawan. Wayarsa ya sake ɗauka dai-dai shigowar sabon saƙo. Yasan Abdull ne dan haka bai tsaya ɓata lokaci ba ya buɗe saƙon. Duk da dai sai da Abdull ɗin ya gama masa sheri irin nasa ya rubuto masa dukkan abinda ya buƙata baibi takansa ba. Kwantar da kanta yay bisa filo a ransa yanajin
haushin ya akaima baiyi tunanin yin duk hakan ba, duk da dai ba fitowa fili yay wajen gayama Abdull ɗin ba, shegen bin ƙwanƙoninsu ne kawai irin na likitoci zaisa ya fahimta. Toilet ɗin ya sake komawa yay duk yanda ya rubuto masa sannan ya dawo wajen Hibbah.
Da ƙyar ya samu ta tashi tana faman masa raki. Nokewar farko da tai saboda babu kaya a jikinta ya sashi ɗaukar rigarsa dake gefe ya saka mata. Koda ya mikar da ita azaba ta sata faɗa masa jiki ta fashe da kuka.
Kansa ya ɗan girgiza da ɗaukarta dukanta kawai dan shi kansa wajen hutawar yake bukata. Ga tausayinta fal ransa dan shi bayason ganin mutum a damuwa dalilin sa. A banɗakin ma ba tsira yayiba. dan harda cizo ya sake sha. Ummi da su Yaya Abubakar kam sunsha kira matuƙa. Da ƙyar ya samu ya taimaka mata tayi yanda Abdull ɗin ya rubuto masa. Koda ya tambayeta batun wanka bata tankaba. Dan dama tunda suka shigo bata yarda tako kalli yatsan hannunsa ba idonta a rufe suke. Sai da yaja mata gargaɗi a kausashe sannan tayi, shi ya sake taimaka mata suka fito. Ya zaunar da ita a gefen gadon yasa karamin towel ya rage mata ruwan kanta. Gudun kar lokacin salla ya cigaba da shigewa ya sashi ɗakko mata wata doguwar rigan a kanyan da batasan a ina ya samoba. Shiya taimaka mata ta saka nan ma. Ya saka mata hijjab ɗin da faɗin, “Tashi kiyi salla”.
Wani irin bugawa ƙirjinta yayi a karo na biyu, saboda jin da muryar da yay magana sak na yaya Isma’il. Sai dai ta dake matuƙa na hana kanta dubansa ta tada sallan cikin layin rashin ƙwarin jiki har yanzu tana hawayen. Sauƙinta ma ta ɗanji daɗin taimakon ruwan zafin da yay mata duk da sai da ya haɗa da mazurai.
Sallar ma dai haka tayita harta kammala tana kuka. Yayinda shi kuma yake kimtsa gadon cikin mamakin abinda ya ci karo da shi. Bai daice komai ba ya naɗe zanin gadon ya hau duba wani a ɗakin kozai samu. Sai dai babu. Dole ya fito zuwa ɗayan ɗakin dake a sashen. Zanin gadon dake ajiye na gadon ɗakin ya dauka ya koma. Da kansa ya shinfiɗa cike da karfin hali. Gamawar tasa tayi dai-dai da kammalawar Hibbah sai dai ta kasa tashi a wajen.
Duk da ya fahimci ta idar baiyi magana ba. sai ma zama da yay a bakin gadon ta gefen ta yana latsa waya. Massege ya turama Habib akan ya kawo masa abinci ya ajiye a falo. Wayar ya ajiye yana maida hankalinsa gareta. “Kin idar?”.
Advertisements
Kanta kawai ta jinjina masa tana share hawayen da suka ziraro mata. Duk da ya fahimci kukan take baice komai ba ya miƙe ya fita a ɗakin. Yasha mamakin iske abincin da yasa Habib ɗin ya kawo harma da wanda baiceba. Dan harda magunguna a leda. Tambarin jikin ledar maganin ne ya sashi shan jinin jikinsa. A fili ya furta “Abdull”. Aljihun wandonsa ya ɗan laluba domin cirar wayar sai ya tuna ya barta a bedroom. Dan haka ya ɗauka abincin kawai ya koma. A inda ya barta anan ya sameta, sai dai yanzu ma ta sake haɗe kai da gwiwa.
Komai baice mata ba har sai da ya haɗa mata abincin, cikin dakewarsa, dan ya fahimci lallaɓawar bazatai masaba, Hibbah bahaguwar mutumce kuma zuma ce sai da wuta. yace, “Tashi kici abinci”.
Ɗagowa tai, dan muryarsa kawai razanata takeyi a halin yanzun. batare da ta yarda ta kallesa ba cikin rawar muryar kuka tace, “Na ƙoshi, dan ALLAH ka kaini wajen Ummi na, inason na ganta”.
Maimakon ya amsa mata sai ya miƙa mata kofin tea kawai. Ganin taƙi amsa, tamaƙi ɗagowa ta dubesa ya kamo hannunta ya ɗaura kan kofin. “Baki gaji ba kenan mu koma a ƙara”.
Da dauri ta amshi kifin jin abinda yace, yay gajeren murmushi yana ɗauke kansa daga kallonta. Uziri ke garesa na fita, gashi babu dama baima san yanda zaiyi da ita ba. Tsoro da yunwar da takeji ga zazzaɓi yasata shanye tea ɗin akan lokaci ta ajiye kofin, komai baiceba anan ma ya ɗauka ledar maganin ya duba. Ƴar takardar da yaci karo da ita a cikin maganin ya warware ya fara karantawa. Yanda duk za’a sha maganin ne a ciki, sai ƴar tsokanar da yay masa a ƙasa wadda ta sashi sake tabbatar da zarginsa akan Abdull ɗin yana kusa da shi. Ajiyewa yay ya ciri maganin ya bama Hibbah. Babu musu ta amsa ta sha.
“Wai nikam baza’a kalleni ba?”.
Yay maganar yana ƙoƙarin ɗago haɓarta ganin taƙi yarda koda kuskure ta dubesa. Idanunta ta rumtse hawaye suka ziraro. “Kuka dai, kuka dai babu hutu?. Bakisan yanzu ke kin girma ba ne? Kin tashi da ga autar Ummi, shalelen su yaya Muhammad. Nanda ƙanƙanin lokaci za’a fara kiranki Mamy insha ALLAH ”.
Sake fashewa tai da kukan tana ture masa hannu da juya kanta gefe, sai hakan ya bashi dariya. Amma yay ƙoƙarin gimtsewa da faɗin. “ALLAH ya baki haƙuri tashi muje ki kwanta”. Yay maganar Yana miƙar da ita. Koda ya kwantar da ita a saman gadon shima sai ya kwanta a gefenta tare da ɗan ranƙwafowa yay mata runfa da jikinsa. Hannu yasa yana share hawayen da take zirarwa har yanzun. “Bana son kukan nan Muhibbat, kinga yana ƙara miki zazzaɓi da ciwon kai, yaya Isma’il yayi laifi. amma a yafe masa shalelen Yaya Ammar….”
Cikin dasashshiyar muryarta ta katsesa da faɗin, “ALLAH ya kiyaye, kai ba Yaya Isma’il bane. Gara ma ka daina wannan ɓoye-ɓoyen fuskar da yaudarar mutane kana jefa rayuwarsu a haɗari kai kazo ka kwana lafiya”.
Murmushi kawai yayi batare da ya amsata ba da sumbatar laɓɓanta ya rungumeta a jikinsa dan kansa ciwo yake masa. Tun tana jan ajiyar zuciyar kukan da take har barci ɓarawo ya saceta. Shima dai barcin ke son ɗibarsa saboda maganin da yasha. Cikin ƙanƙanin lokaci duk suka tafi duniyar barcin.
Barci sukai sosai har magrib ma ta ɗan gota. kiran wayarsa da akai ne ya farkar da shi harda ma Hibbah, sai dai ita tayi luf bata nuna ta tashin ba harya janyeta a jikinsa ya ɗauka wayar. “Barka da yamma sir”.
Advertisements
Ya faɗa cikin muryar barci lokacin da yake kai wayar saman kunnensa. Jin abinda wanda ya kira sir ɗin ya faɗa da ga can ya sashi miƙewa da sauri yana kallon agogon ɗakin. Kansa ya ɗan dafe ganin yanda lokacin yaja sosai harma anyi magrib. “I’m sorry sir kaina ke ciwo na ɗan kwanta ne bansan lokaci yaja ba haka”.
Amsar da aka sake bashi da ga can ta ɗan sakashi sakin ɓoyayyen murmushi da faɗin, “No sir insha ALLAH yanzun nan zan iso ɗin ka jirani, dan ina son baka gaba ɗaya bayanan kawai kafin na ida tattara sauran gobe idan ALLAH ya kaimu.”
Idanu Hibbah da maganganun nasa suka bama mamaki ta ɗan buɗe tana kallonsa. Gabanta ya sake faɗuwa dan still dai Yaya Isma’il take gani har yanzu, kamar yanda a murya ma dai ɗin shine. Duk da ta jima tana wasiwasi akan muryar master idan yayi magana dama batun yanzu ba. Sai dai tsakanin ɗazu zuwa yanzun muryar tasa tafi kamanceceniya data Yaya Isma’il ɗin fiye da ko yaushe. Ganin ya juyo ya dubeta bayan ya katse wayarne ya sata saurin maida idanunta ta lumshe zuciyarta na azabar bugu da sake shiga a ruɗani. Ya fahimci ta tashi. dan haka ya miƙe batare da yay magana ba ya shiga toilet a ɗan hanzarce.
A gaggauce yay alwalar ya fito yana duban gadon. “Tashi kiyi salla”. Ya faɗa yana shinfiɗa sallaya ya tada salla. Ganin ya fara sallarne ya sata yunƙurawa ta tashi da ƙyar. Alhmdllh taji matuƙar daɗin jikinta, da alama maganin daya bata na kashe raɗaɗi da zogi ne. Sai dai jitake bakinta babu daɗi. hakama jikinta fayau kamar isaka zata ɗauketa. Sai da ta ɗan samu ta sake shiga ruwan zafi ya ratsata fiyema da ɗazun da taita raki dan batajin dai-dai a wajen har yanzun sannan ta sake samun nutsuwa, tana fitowa ta samu ya idar da sallar, motsinta yasa shi juyowa suka haɗa ido.
Saurin maida kanta tai ƙasa hawaye na sakko mata. “Dan ALLAH ka cire fuskar nan, ni basai ka suffanta kanka da yaya Isma’il ba zanyi haƙuri har ALLAH ya kuɓutar dani da ga gareka”.
A yanda tai maganar saita bashi tausayi da dariya. komai baice mata ba ya miƙe, har inda take tsaye yazo ya kama hannunta. Ɗayan hannunsa kuma yasa ya ɗago fuskarta tare da ɗan matso tasa gab har sunajin saukar numfashin juna. “Karki tsananta tunani, duk abinda kike buƙatar fahimta zaki tabbatar da shi nan da kwanaki biyu kacal insha ALLAH. Kiyi sallan ki sake kwanciya ki huta zan fita bazan jimaba, kukan nan kuma ya isa haka ok”. Ya ƙare maganar da sumbatar laɓɓanta.
Komai ita dai batace ba, sai ma sake rikitata da yay. Shiko ganin yanda time ya ja ya sashi daukar wayarsa da jacket ya daura saman t-shirt ɗin jikinsa da sabon mask ya fita a ɗakin da ɗan hanzari. Takardun da ya bari a falon Habib ya tattare masa lokacin da ya kawo abinci ya ɗiba ya fito cikin zafin naman da ALLAH ya azurtashi da shi. Mota ya buɗe ya zuba kayan hannunsa sannan ya zagaya mazaunin driver. Su Habib da keta aikin da ya sakasu a sashensu sai jiyo fitarsa sukai. Basu damu ba. dan tunda safe suka fahimci jikinsa da sauƙi Alhmdllh. Sun kuma san a yanda komai ya rikice bazai zauna ya zuba ido ba. Dan tun ɗazun da yamma labari da ɗumi-ɗuminsa keta yawo a kafafen sada zumunta da gidan redio dana tv akan binciko wasu mafakar master ɗin da sirrikansa da jami’an tsaro sukayi. Harma suna iƙirarin cewar suna gab da kamashi harma da samo iyalan su A.G da ke a hannunsa.
Sun san wanene Master ɗinsu sarai akan iya taku, duk da kuwa akwai ƙaddarar ɓacin rana da kan iya gittawa tamkar ta jiya da har yakai sun harbesa. amma basa tunanin wannan binciken da suke iƙirarin yi yana akan layin dai-dai. Dan a duk gidan da ya fahimci za’a iya ganesu cikin sauƙi idan sukai aiki sau ɗaya basa sake maimaita ko bin layinsa ma balle shigarsa. So duk inda zasu binciko sai dai ya sake sakasu a ruɗani badai a hanyar kama master ɗinsu ba.
A ɓangaren Hibbah kam tana idar da sallar ta miƙe. So take tayi wani abu amma tasan duk hanyar da zatayin bazai bari ba sai ya toshe ta kafin ya fita. Tunda ta sha shi sau ɗaya bazaiyi sakaci na biyu ba koda da kuskure. Gadon ta sake hayewa ta kwanta da cigaba da cuɗawa da kwancewa akan wannan sabon salon da ya dauka na zuwa mata da fuskar yaya Isma’il dan yaji ta ambaci nagartarsa ga reta ga ahalinta kuma. Tun tana lissafin dai-dai har idanunta suka fara lumshewa, dan dama barcin ma ba sakinta yay ba.
★★★★
A ɓangaren Master kuwa tafiyar da bata gaza mintuna goma sha bakwai bace ta kaisa babbar headquarter ta ƴan sandan jihar. Tunda yay horn securitys da ke a wajen suka leƙo suka gansa sai suka wangale masa ƙofar cike da girmamawa da ɗokin ganinsasuna sara masa. Ɗan salute ɗinsu yay shima yana tura hancin motar tasa ciki.
Cike da ɗoki wasu jami’an samari biyu suma suka iso garesa dai-dai yana buɗe motar ya fito. Wellcome sir!”. Suka haɗa baki wajen faɗa. Murmushi yay musu tare da miƙa masu hannu alamar suyi musabaha. Ɗabi’arsa ce hakan tunkan yay balaguron da babu wanda yasan ina yaje, sudai sun bar ganinsa ne kawai. Hannun suka bashi suma suka gaisa. Kafinyay musu nuni da Kayayyakinsa da ke cikin motar alamar su ɗebo.
Yayinda shi kuma yake bin ko’ina na station ɗin da kallo cike da kewa, duk da dai yakan shigo dama a sace cikin ɓadda kama.
Duk da dare ne akwai jami’ai sosai a ciki ta kowanne department, kuma mafi yawancinsu sun duƙufa ne akan batun Master ɗin, dan shine aikin da gaba daya ya birkita kowacce hukuma daga jiya zuwa yau.
Duk ta inda ya gitta sannu da zuwa ake masa bisa balaguron da yay na kusan shekaru biyu da rabi da girmamasa tamkar yanda shima yake bama kowa girma a rayuwarsa. A gefe kuma abokansa da manyansa na nuna jin daɗin dawowar tasa a dai-dai gaɓar daya dace. Masu kuma jin haushinsa najin takaicinsa dan mutum ne jajirtacce akan duk abinda yasa gaba tun ma yana ƙaramin ɗan sanda.
Katafaren office ɗin da yafi kowanne girma da alfarma a headquarter ɗin ya nufa kai tsaye su Rayyan biye da shi. Tun kan ma suyi knocking aka buɗe musu ƙofar alamar ansan da zuwansa. I.G da ke zaune shi da wasu manyan ginshiƙai na hukumar ƴan sandan EFCC da General na sojoji suka maida hankalinsu ga ƙofar fuskokinsu cike da fara’ar tarbar gwarzonsu, wanda ya yarda zai sadaukar domin ƙasarsa da yankinsa bisa aikin sirri na haɗin kai da suka shirya a tsakaninsu kawai saboda tashin hankali da rikicin da kowa ya kasa gane bakin zarensa a yankunansu……….✍
_________________________
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI……_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*
*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽
#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
GIPHY App Key not set. Please check settings