TAKUN SAKA 40

Advertisement

 

*_Chapter Forty_

……….A kallo ɗaya da sukai masa suka fahimci lallai bashi da wadataccen lafiya, dauriya da jarumtace kawai irin tasa ya sashi amsa kiran nasu. I.G da gaba ɗaya dama burinsa yaga halin da Master ɗin ke ciki dan bashi da nutsuwar zuciya akan harbin da akai masa tun jiya ya mike da sauri ya nufesa. 

        Dai-dai master na karasowa garesa ya dan kame jikinsa alamar girmamawa. “Shuraim wannan gangancine ai. Shiyyasa nace maka basai kazo ba a wannan halin da kake ciki ka aiko Habib kawai”.

        Murmushi Master yay mai ciwo, cike da girmamawa a garesa ya ce. “Karka damu Uncle ina lafiya. Idan mun biyema ciwon da kawai mukeji a jiki su kuma masu ji a cikin zuciyoyinsu fa?. Tabbas inajin ciwo a jikina, dan shigar bullets a cikin jiki ba wasan yara bane, amma idan ina kwatantashi da ciwon da su waɗanda babu inda zasu kai kukansu sukeji sai naga ban cancanci raki ba”.

         I.G da ke murmushi mai ciwo ya ɗan bubbuga kafaɗar Master. Tabbas shima yanajin irin ciwon da Master ɗin keji a cikin ransa. Dan shine ma ya horesa akan wannan tsarin duk da dama shima yanada irin wannan zuciyar ta damuwa da halin da al’umma ke ciki fiye da kansa. Bin master ɗin dake ƙoƙarin isa gaban Efcc Chairman da General yay da kallo, yana jin ƙaunar yaron matuƙa a cikin ransa tun kafin randa ya gansa a wajen taron bikin gama secondary school. Kwazonsa ya sashi jin kwaɗayin biya masa kuɗin karatu. 

        Master da ya juya ga General da efcc chairman duk da kuwa haɗakace ta aiki ta haɗasu dalilin I.G duk yana basu girma suma, kodan shekarunsu da ƙyaƙyƙyawar zuciyarsu. Ƙame jikinsa ya sakeyi da risinar da kansa ya ce. “Good Everning Sirs”.

            Sosai ƙwazonsa da ƙoƙarin mutunta na gaba da shi ke sake saka musu ƙaunar yaron a zuciya. Efcc Chairman ya miƙa masa hannu alamar suyi musabaha. Babu musu Master ya bashi dan shima yafi bukatar hakan. Shima General musabahan sukai. 

           Cikin nuna kulawa suka tambayesa jikinsa? Akan harbin da ya sha. Ya tabbatar musu babu wani damuwa yaji sauƙi. Karkuma su damu tsautsayi ne kawai.

Advertisements

     Dukansu murmushi sukai, dan sun san dai Master ɗinsu ya faɗa soyayya da gaske. Dukansu sun san Hibbah, tun harin farko data kai masa batare da wani niyya ba I.G ya bashi shawaran aurenta, a cewarsa ba’a sakaci da irin waɗan nan yaran masu ƙwazo. Ko basu fito duniya ta sansu ba zasu taimakama mazajensu da ƙasa a gidajen aurensu. Da farko Master yaso zillewa. Sai dai kuma shiga cikin ahalinta da yay ya fahimci matsalar da suke ciki a hannun Halilu ya sashi amincewa. I.G ɗin ma da kansa suka nema masa auren nata.

        “Madam dai ta rantse sai da kasha bullets”.

        Efcc Chairman ne mai maganar cikin ƴar tsokana. Dariya sukayi gaba ɗaya, yayinda Master ya ɗan kai hannu ya shafi ƙeyarsa yana murmushi shima. A zuciyarsa kam aiyanawa yake (ai itama yau tasha nata bullets ɗin).

            Sai da suka ɗan gama barkwancinsu Master dai na tayasu da murmushi kafin su fara abinda ya tarasu. Cikin nutsuwarsa da bama aikinsa dukkan hankalinsa ya fara musu bayani akan abinda suka buƙata. Harma da wanda basu san da shi ba. 

        Mamakin yanda Master ke tafida aikin da har wanda bai shafesaba ya basu. Shi dai ɗan sanda ne, ɗan sandan ma normal ɗan sanda. Sai dai a dalilin faruwar wani abu da ya shafi I.G yake ɗaurasa akan wasu ayyuka na sirri da yake yi domin hidimtama ƙasa batare da wani mahaluki ya sani ba. General abokinsa ne, hakama Efcc Chairman. Kamanceceniyar halinsu na kirki yasa akoda yaushe suke zaman tattaunawa akan abinda ya shafi yankinsu dama ƙasar baki ɗaya. Wanda suna iya bakin ƙoƙarinsu sai dai sukan rasa a ina matsalar take akoda yaushe suna tufƙawa ana warwarewa?. 

      Akoda yaushe sai dai suyi zaman kawai su tashi, dan duk da kasancewarsu manya masu faɗa aji a hukumomin tsaro basu iya yin komai dake dai-dai da burikansu. Aikin da I.G ya fara ɗaura master a sirance yayi nasarane yaja ra’ayinsu gareshi har sukai kwaɗayin dinga sakashi ayyuka na musamman, duk da kuwa shi baida alaƙar aiki da su ta wani fanin. Ba yau kawai bane Master ya fara musu aiki. Yasha zaƙulo musu bara gurbi a cikin jami’ansu da manyan mutanen dake akan karagun mulki, kuma idan sukabi diddiginsu sukan samu abinda suke buƙatar.

    Bai wani jimaba tare da su saboda halin da yake ciki, sun tabbatar ƙarfin haline kawai yakeyi badan lafiya ta ishesa ba. Sallama yay musu akan zai ƙarasa sauran ayyukan da suka rage masa na tattare dukkanin bayanai na kowanne fanni nan da kwanaki biyu insha ALLAH da zasu kasa komai a fai-fai dangane dasu A.G da ire-irensa. Daga haka yay musu sallama ya fito cike da dakewa kamar yanda ya shigo. dan baya buƙatar wani ya fahimci halin da yake ciki musamman akan ciwukan harbin dake tare da shi.

★★★★

        Gudu yayi sosai akan titin, hakan yasashi isowa gidan cikin ƙanƙanin lokaci duk da kuwa ya ɗan tsaya a wani waje. Ledojin dake bayan motarsa na tsarabar su Habib ya ɗiba zuwa sashensu. Koda ya shigo suna baje a falo suna aikin da ya sasu, sai dai hakan bai hanasu shan shaftarsu ta hira ba kamar ko yaushe. Ko sallamarsa basuji ba sai da Sharifat ta nufosa da gudu tana kiran “Uncle oyoyo”.

      Tattausan murmushi ya saki a karon farko yana ajiye ledojin hanun nasa ya kai duƙe dai-dai da tsahonta yana buɗe mata hannayensa. Jikinsa ta haye tana dariya, ya lakaci hancinta shima yana murmushi da faɗin, “Beauty ɗin gidanmu batai barci ba”.

Advertisements

         Sharifat data makale masa kafaɗa tai yar dariyarta da kwantar da kanta kan kafaɗarsa. “Uncle ina game ne a wayan Yaya Idris”.

        “Lallai ƴar gatan Yaya Idris”.

Ya faɗa yana kaiwa zaune batare da ya kula su Habib da sukai tsitt ba tun kiran da Sharifat tai masa. Ledojin daya ajiye ma Adam ne ya miƙe ya kwasosu. Leda ɗaya ya amsa a ciki ya bama Sharifat. “Tom ga wannan maza ki cinyesa duka ki kara ƙatuwa. Kina gamawa kuma ayi brush da alwalan barci ai addu’a. Ki gaidamin baba sai da safe”.

      Cike da ɗoki ta amsa sheƙa da gudu tana faɗin, “Yeee thanks you Uncle ”.

          Hannayensa ya harɗe akan ƙirjinsa yana binta da kallo da murmushi harta shige. Yana son yara matuƙa tun shima yana yaron, shiyyasa a yanzu bashi da babban burin daya wuce yaga jininsa a rayuwa. Numfashi ya ɗan ja da gyara fuskarsa ya gimtse yana maido dubansa gasu Habib. A kusan tare suka haɗa baki wajen gaishesa da tambayarsa jikinsa. Cike da nazartar yanayinsu ya amsa musu dai-dai idonsa na sauka kan Habib da yaƙi yarda ya kallesa.

        Dukansu tarbiyarsa ce, dan haka ko laifi sukai masa a ƙanƙanin lokaci yake gano wanda ya aikata ɗin. Komai baice ba game da abinda ke a bakinsa ya miƙe, kai tsaye ƙofar fita ya nufa, sai da yaje gab fitar batare da ya juyo ba yace, “Habib ka sameni”. Daga haka yay ficewarsa.

         Dama tun kallon da yake binsu da shi suka sha jinin jikinsu akan an masa laifi, kowa fatansa kar yazam shine ya aikata. Jin ya ambaci Habib ya sasu maida kallonsu kansa. “Yaron nan wane ruwa ka ɓallo mana ne?”.

   Cewar Musbahu cikin ɗan tsoro. Harararsa Habib ɗin yayi yana miƙewa yabi bayan Master ɗin dan gudun sake wani laifin. Yana fita Adam yace, “Ni wlhy tun shigi da ficin danaga yanayi jiya akan waya nai tunanin hegen mai jajayen kunne wata tsiyar yake shiryawa. Sai dai banyi tunanin bahagon zaki zai ɓallo ba”.

          Salis yace, “Ni nasan laifin daya aikata, amma ku jira dai ya dawo muji a bakinsa”.

        Kansu duk suka jinjina alamar gamsuwa. Kafin su ajiye aikin gaban nasu a koma buɗe ledojin tsaraba cike da jin daɗi da farin ciki.

     Habib kam koda ya fito can ya hango master ya ɗebo sauran ledan daya bari a motan. Nufarsa yay ya amsa suka sufi sashen nasa tare. Kamar yanda yabar falon a haka ya samesa. Ya kai zaune bisa kujerar 1seater yana ɗan dafe kansa da ke masa ciwo har yanzun. Yasan akwai issue ɗin jini tattare da shi, shiyyasa ciwon kan yaƙi barinsa sam. Bayansa ya kwantar jikin kujerar da zare mask ɗin fuskarsa ya ajiye, yana daura ƙafarsa ɗaya kan ɗaya, razanannun idanunsa ya zuba akan Habib dake tsaye kai a ƙasa.

          “Miyasa ka aikata?”.

  Yay maganar yana dauke idonsa a kansa ya maida ga takardun dake a saman centre table ya ɗebo su yana dubawa. 

          Habib da kansa ke ƙasa saboda girman laifin da ya aikata. Sanin halin yayan nasa akan buƙatar yin magana kai tsaye koda ta laifi ce, yace, “Itama taji irin raɗaɗin da kaji”.

       Master da bai ɗago ba ya sake tamke fuska da cizar lip yana cigaba da aykin gabansa 

         “Yaushe na fara wasan banzan nan da kai?”.

        Shiru Habib yay yana faman haɗiyar zuciya.

  Master da yaji shiru ya ɗago ido ya dubesa fuska a tamke. “Ince da kai nake magana ko?”.

      Yanda yay maganar aɗan zafafe yasa Habib ɗin girgiza masa kai. “Yaya hakan dazan mata ne kawai zaisa na huce da ga abinda ya faru, itama kuma zata kiyaye sake yin wani yunƙuri makamancin hakan.”

        Idanu kawai Master ya zuba masa saboda mamakin Habib ɗin matuƙa. Shiko yaki yarda ya kallesa dan yasan yayi ba dai-dai ba.

        Kansa ya sake maidawa ga takardun, “Hum aure kake buƙata kenan? Ko ka fara neman mata ne?”.

        Da sauri Habib ɗin ya ɗago ya dubesa yana girgiza masa kai. “Wlhy Yaya ni ko ɗaya babu a raina. Kawai dai…..” sai kuma yay shiru bai ƙarasa ba

        Takardun hannunsa ya ajiye ya maida hankalinsa gaba ɗaya garesa yana sake tsuke fuska irin yanda bai taɓa gani ba. “Ƙawai dai me?. ƙarya kakeyi, idan har baka neman mata taya kasan ka sakamin pills nasha dan naje ga mace koda babu niyyar haka a gareni.”

       Habib da idanunsa suka kaɗa sukai jajur ya kai tsugunne gabansa. “Wlhy yaya ban taɓa aikata zina ba ka yarda dani, kamar yanda na faɗa maka kawai nayine dan karta sake tunanin kwatanta abinda ta aikata, sannan inason ku rayu har abada”.

      “Kai da wa kukai shawarar aikata hakan a cikinsu?”.

        “Ni kaɗai ne, dukansu babu wanda yasan abinda ya faru sai Yaya Abdull da ya bani”.

      Idanu kawai master ya zubama Habib ɗin batare da ya sake cewa komai ba. Dama ya zargi babu wanda zaiyi wannan aikin garesa sai Abdull ɗin. Tunda aka ɗaura aurensa da Hibbah kullum cikin masa tsegumi yake su baby suke so da wuri. Habib da yaji yay shiru ya ɗago ya dubesa, shi kaɗai ne ya san ainahin fuskarnan a cikinsu, dan haka bai wani damu da ganinta a yanzu ba. “Yaya dan ALLAH kayi haƙuri. Nasan nayi kuskure tunma kan na aikata hakan. Inason naga kunyi zama irin na kowaɗanne ma’aurata da ita. Bana son ka rabu da ita saboda ƙyawawan halayyarta. Duk da ƙarancin shekarunta tasan kanta matuƙa kuma tanada tarbiyyar da kowanne irin nagartaccen namiji zaiso ta kasance uwar ƴaƴansa. Mu ɗin nan marayune, daga mace tagari kawai muke saran samun zuri’a mai albarka da zamu sake ginawa. Wadda zaka fara ginawa kuma itace ginshiƙin da zata riƙe tamu mu duka bakwai ɗin”.

        Harararsa Master yay, da alamar dai ya huce ya ɗauke kansa. Matsowa Habib yay jikinsa ya ɗaura kansa bisa ƙafafunsa. “Please yaya karka rabu da ita dan ALLAH, inaji a raina idan tasan kai ɗin ko wanene zata sakko ta fahimceka ku rayu tare”.

       Lumshe idanu yay bai tankaba nan ma. Shima kuma Habib bai janye kansa ba. Kusan mintuna biyu yaja ajiyar zuciya da furzar da numfashi, a hankali ya kai hannunsa bisa kan Habib ɗin ya shafa. Habib da wani farin ciki ya mamayesa ya miƙe da sauri ya rungumesa yana dariya. “Thanks you Mastern mu. I love you so much”.

        Karan farko Master ya rankwashi kan Habib ɗin yana murmushi. “Mara kunya tashi mun a jiki tunda ka sadaukar dani ai.”

     Cikin shagwaɓa Habib yace, “A’a Yaya ba duka na bataba fa. Ita rabi mu rabi.”

    Nan ma murmushi kawai yayi baice komai ba. Sai da ya miƙe batare da ya dubesa ba ya nufi hanyar bedroom ɗin da Hibbah ke ciki yana faɗin, “Kaje ka sanar musu kowa ya nemo matar aure nan da wata biyu”.

       Idanu Habib ya zaro, kafin yace wani abu Master ya shige. Wata shaƙiyyar dariya ya saki yana haɗiye sauran maganar a ransa ya juya ya fita da gudu dan kai rahoto.

      Master da ke jiyo dariyar Habib ɗin baima san murmushi ya kufce masa ba shima. Ya ɗan girgiza kai yana ƙarasawa cikin ɗakin da sallama a bakinsa. Shiru babu motsin komai alamar barci Hibbah keyi har yanzun. Ya zare jacket ɗin jikinsa yana ƙarasawa gaban gadon ya zauna ta gefenta. Babu abinda yafi buƙata a yanzu kamar kwanciya. Sam bayajin ƙarfi da daɗin jikinsa dauriyace kawai. Dan bashi da burin daya wuce ya tattare aikin nan ya ɗauki matarsa suje su huta. Bargon da take ciki ya ɗan janye da kai hannunsa saman goshinta. Zazzaɓin ya sauka, a yanda numfashinta ma ke fita kawai ya isa tabbatar da hakan. Yaji daɗi har cikin ransa, fasa tashinta yayi dan karya takaloma kansa wata rigimar, ya ɗauka ledar daya shigo da ita ya sake fita. Babu jimawa ya dawo ɗauke tea. Zama yay yasha tare da maganinsa. Shima yay shirin barci ya haye gadon yana sauke ajiyar zuciya…………✍🏻

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

 

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like