TAKUN SAKA 41

Advertisement

 *_Chapter Forty o

…………*_WASHE GARI_*

       Da asuba Hibbah ta rigashi tashi, dan cikin barci ya dinga jiyo motsinta a bayi. Tashi yay da ƙyar yana ambaton sunan ALLAH. Alhmdllhi jikin ya masa daɗi, dan magungunan da yake sha sun matuƙar taimaka masa. Koda ta fito kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta. Shima baice komai ba ya mike zuwa bayin yayo alwala. Koda ya fito shine yaja musu sallar, yana lure da

yanda Hibbah taƙi yarda ta kallesa bai nuna ya damu ba. Bayan sun idar tana ƙoƙarin miƙewa ya riƙota ya zaunar a jikinsa. Kanta ta kauda gefe tana ƙoƙarin haɗiye ƙwallar da suka ciko mata idanu.

       Hijjab ɗin jikinta ya cire, tare da riƙo fuskar tata cikin tafin hannunsa ya juyota garesa. “Nikam wai har yanzu ba’a huceba”. Yay maganar yana ɗaura kansa bisa goshinta”.

       Duk yanda taso ƙwace fuskar tata hakan ya gagara. Dole ta nutsu waje guda, gashi tanason yin magana amma babu dama. Ta tabbatar datayita kusancin laɓɓansu zai iya sawa ya haɗu da nasa.

       Fahimtar hakan da yayine ya sashi ɗaura laɓɓan nasa saman nata ya ɗan sumbata. Sai kuma ya janye goshinsa yana kallonta da ƙyau. Duk yanda yaso su haɗa ido ko tayi magana taƙi. Sarai ya fahimci borin kunyane kawai. Dan haka ya saketa yana murmushi. 

       Zumbur kuwa ta miƙe tabar wajen, har tana cin tuntuɓe da ƙafarsa. 

Advertisements

       “Ni dai kar amin asarar ɗan tayi na”.

      Ya faɗa cike da shaƙiyanci yana binta da kallo. Cikin tunzura baki gaba ta haye gadon taja bargo ta rufe har kanta tana ƙunƙunj. Duk da dariyar dake son kufce masa dai ya danne abinsa baiyi ba. Sai ma ya miƙe shima ya hau gadon dan barci yake son ƙarayi. Hibbah data ƙudundune waje guda tai saurin buɗe idanunta a tsorace. Zata miƙe ya riƙota yana daidaita fuskarsu waje guda. Yatsansa ya ɗaura saman laɓɓanta ya shiga zagayawa dashi a hankali. Tsigar jikintane ya fara tashi amma sai ta danne taƙi nunawa.

      Cikin ƙasa da murya sosai tamkar mai raɗa yace, “Mikike faɗa da banaji?”.

      Hannunsa ta ɗan ture daga bakinta tana kumbura bakin kamar zatai kuka, “Ai dai ALLAH ya sani bance komai ba”.

        Ganin zata juya masa baya tana maganar yay azamar tareta, laɓɓansa ya matsar gab da nata yana wani narke idanu, “Ni nasan kince ai”. 

       Kafin ta samu damar cewa wani abu ya rufe bakin nata, cikin shauƙin dake ɗibarsa ya shiga aika mata da sumbata a nutse data saka zuciyarta shiga tsoro harta fara tsuma. Duk da yaji a yanda jikin nata ke ɓari bai saketa ba ya cigaba da abinda yake har sai da ya tabbatar tayi laushi. Hagitsatstsun idanunsa da suka kaɗai sukai jajur ya ɗago yana kallon fuskarta, idanunta dake hawayen tsoron ya sumbata da jan nannauyar ajiyar zuciya.

         “Nasan ni mai laifine a gareki ta kowacce fuska Muhibbat, sai dai inason kisani kece kika faramin laifi.”

     A karon farko Hibbah ta buɗe idanunta ta kallesa, ga hawaye shaɓe-shaɓe. Sai kuma cikin sauri ta sake maidawa ta rufe, dan batason ganin idanun nan nasa da fuskar nan ta yaya Isama’il da ya saka, ga matsananciyar kunyarsa dake matuƙar cizon ranta da ɓargo. Batare da ya damu ba ya tura yatsun hanunsa cikin gashin kanta da sake matsota jikinsa. “Inason ki nutsu a yau kisan kowanene Muhammad Shuraim (Master). Asalin sunan shine Isma’il Aliyu Hikima”.

       Cikin sauri Hibbah ta sake buɗe ido har yawu na sarƙe ta. Ganin ta miƙe zaune shima ya miƙe, ruwan dake a bedside ya ɗakko ya ɗora mata a baki. Babu musu tasha tana kallonsa tamkar idanunta zasu zubo a karon farko wajen kallonsa. 

        “Tabbas Isma’il shine sunan, kuma shine a gabanki yanzu haka da fuskar zahiri bata bogi ba Muhibbat.”

      Wani irin bugawa ƙirjin Hibbah ya sakeyi. Cikin rawar jiki da son ƙin gaskatawa takai hannunta saman fuskarsa tana rumtse ido. Sake buɗe idon tai da sauri taja baya jikinta na sake ƙarfin karkarwa. “M….master kana nufin kaine Yaya Isma’il?”.

        Kansa ya jinjina mata yana lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta. 

Advertisements

        “Na shiga uku ni Muhibbat wane irin rikitaccen mafarkine wannan nake a ciki?. Impossible hakan ta kasance”. 

     Tai maganar tana ƙoƙarin sauka a gadon. Saurin riƙota yay ta dawo jikinsa. “Shiyyasa nace ki nutsu ki saurareni”. Ya faɗa a cikin kunnenta da wata murya mai taushi tamkar bashi ba. Batare da ya bata damar sake cewa komai ba ya cigaba da maganarsa. “Sunan mahaifina Aliyu……….” tiryan-tiryan ya cigaba da bata labarinsa tamkar yanda ya bama su Ummi. Sai kuma ya ɗora da “A farkon shigata tawagar su Master an taɓa kamamu, lokacin ina farkon shiga aji shida na sakandiri. Tunda aka kawomu police station wani babban jami’i keta kallona har kallon ya gundireni naji haushi. Fahimtar hakan da yay yasashi ɗauke kai yana murmushi. Bansan yaya akai ba bayan kamar awa guda aka fiddani ni kaɗai kuma babu wani bayani. Hakan ya tsayamin a rai, daga baya kuma saina watsar na cigaba da harkar gabana.”

        “Bayan na kammala jami’a na kaima wanda ya ɗauki nauyin karatuna result ɗina dan ya gani, tare da sake masa godiya, sai naci karo da jami’in nan da yayta kallona a station, abin ya ɗauremin kai, na kuma sha mamaki amma sai na danne. Yaji daɗi ya kumayi farin ciki a take anan kuma yaymin tayin aiki saboda ganin yanda nake da matuƙar ƙwazo da kaifin basira akan harkar kimiya da fasaha. Babu musu na amsa cikin farin ciki da murna dan kuwa aiki ne na jami’an tsaro. Na miƙe cikin farin ciki zan tafi ya dakatar da ni ta hanyar faɗin, (dakata yarona ai bamu gama magana ba). Komawa nai na zauna ina basa dukkan hankalina.”

        “Yarona zaka zama jami’in ɗan sanda amma na sirri, dan haka zakai aiki kafaɗa da kafaɗa ne da mu ƴansanda amma a sirrance batare da kowa yasan wannan ba sai ni. Inada abubuwa masu yawa dake cimin rai da zuciya, sai dai ina matuƙar jin tsoro da shakku akan wanda zan ɗora yaymin. Wannan yasa a randa na fara ganinka a station naji a raina zaka iya. Hakan yasani komawa na biya maka kuɗin karatu dan a cikin idanunka na fahimci da gasken zaka iya. A yau zan sanar da kai wani abu, duk tsahon shekarun nan daka ɗauka kana karatu ina biye da kai, hatta shiga cikin ƴan daba da kakeyi wanda na fahimci kanada wani dalili duk ina sane da kai).”

       “Nayi matuƙar razana dajin zancensa. Dan haka na miƙe ina girgiza masa kai. Saurin riƙoni yayi shima yana girgizamin nasa. cikin taushin murya kuma ya shiga lallashina. (Yarona zaka iya, ni na tabbatar zaka iya insha ALLAH. Wannan Master da kake ƙarƙashinsa ko kasan gawurtaccen ɗan ta’addane da muke fako tsahon shekaru. Sai dai a bincikenmu ya nuna yana tare da manya-manyan masu faɗa ajin da ko kamashi mukai munyi a banza zai fito kamar ko yaushe. Daga ƙarshe ma wanda ya kamasan shine zai rasa aikinsa ko rayuwarsa. Jami’anmu sun halaka da yawan gaske a dalilinsa. Sai dai a yanzu haka akwai yarona a cikin yaransa shine duk ke bani bayani game da kai, dan shima ya shiga jikinsa ne domin mana cid. Inason dan ALLAH ka sanarmin miyasa ka raɓu da shi kai?).”

         “Ina ganin kima da mutuncinsa. Dan ya ƙyautata rayuwata na samu ilimi a gaɓar dana yanke ƙauna da samun hakan. Dan haka babu musu na zauna na zayyane masa koma na rasa iyayena a dalilin Master da dangin Dattijo Isma’il suka saka. Na kuma tabbatar masa da fansa zan ɗauka dan bazan bar Master ba. Har hawaye sai da yayi domin tausayina. Ya kuma tabbatarmin burina zai cika cikin sauƙi amma saina zama jami’in sirrin da yaymin tayi. Na amince a lokacin. tare da bayyana masa ainahin fuskata ta Isma’il Aliyu Hikima. Yasha amamaki kwarai da gaske, musamman da yaji cewar tun ina yaro nake ɓoye fuskata ta zahiri, bayan iyayena shine na biyu daya ganni a hakan. Hakama da yaji nike haɗa dukkan Mask ɗin wa kaina yaji daɗi ya kuma yabama fasaha ta. Domin abune daba kasafai ake samunsa anan yankunanmu ba.”

      A dalilin ganin zan iya ɓoye fuskata yace babu damuwa ma zan iya aiki kafaɗa da kafaɗa da su kamr kowane ɗan sanda a zahiri, a baɗini kuma aikin sirrinmu, sai dai zan cigaba da ɓaddabamin ɓoye ainahin fuskar Isma’il zuwa wani lokaci. Na amince da hakan. Na kuma shiga cikin tawagar horaswa da fuskar Muhammad Shuraim, cikin amincin ALLAH na fito a jerin jami’ai masu matuƙar ƙwazo. Sai dai ana kammalawa na sake ɓacewa ɓat bisa umarnin I.G. Na sake komawa cikin su Master da zuwa yanzun dukkan sirrinsa a tafin hannuna yake, dan dukkan abokan mu’amularsa a cikin manya da ƴan ta’adda irinsa na sansu nasan inda suke, nasan makamar harkokinsu. Na iya maganarsa. Na iya salon tafiyarsa na iya abubuwa da dama irin nasa wanda inhar na juye maka shi baka isa cewa bashi ɗin bane musamman idan na saka mask na fuskarsa. Indai taƙaice miki zance a wani dare batare da sanin kowaba a cikin yaran Master na ɗaukesa, zuwa safiya na maye gurbinsa, yaransa kuma duk nabi hanyoyi daban-daban aka kamasu ɗaya bayan ɗaya ta yanda babu yanda ubannin gidansu zasu iyama ganosu balle cetonsu. A gefe kuma ina aikina a zahiri tuƙuru game da dukkan abinda ya dace”.

         “Duk da kasancewana normal ɗan sanda, nayi ayyukan sirri da yawa bisa umarnin I.G ni da ɗansa Abdull da ya zama aminina tun a jami’a. Efcc Chairman da General abokaine na I.G tun ƙuruciya, hakanne yasasu sanin ayyukana a wajen I.G har suma suka fara jana jikinsu dan halayyarsu ɗaya da I.G akan ganin ƙasarmu ta dawo hayyacinta. Sai dai rashin mabiya na ƙwarai yasa basa iya tufƙa sai an warware musu. Nasha kawo musu information da yawa daya shafi ayyukansu a dalilin bincike na. Hakanne yasa a wasu lokutan nakanyi aiki kafaɗa da kafaɗa dasu tamkar yanda akasan jami’an tsaro da yawa sunkanyi hakan a sirrance a tsakaninsu. Kin shigo rayuwata a dai-dai gaɓar da nake gab da kammala tattara bayanai akan duk wasu masu hannu bisa ta’addancin Master. Naso hukuntaki, dan kin kusa ruguzamin aiki, amma sai labarin ya canja salo a dalilin I.G, shine yasa akai masa bincike akanki da ahalinki harya gano bakida wani dalili na harata tsiwace kawai da rawan kanki. Babu wani kwanakana ya bani shawarar aurenki. Ban iya cemasa komai ba dan yanada mutunci da girma a idanuna. Sai dai na dauka ɗammarar shiga jikinki nima dan tabbatarda ƙwazonki da yaketa yabawa harda kwaɗayin na aureki. Dukkan abinda su A.G sukai miki mun sani, musamman daya kasance ni suke ɗauka Master ɗinsu a halin yanzun. Muhibbat a yau na gama aikina daya shafi wancan Master ɗin, zan kuma damƙashi ga hukuma shi da su A.G, zan kuma bayyana fuskar Isma’il ma duniya, shiyyasa na fara nunata gareki bayan iyayena, baba, Habib, I.G, da kuma su Ummi. Sai dai kafin hakan inason ki sani tun randa na fara ganinki a asibiti kikaima zuciyata shigar sauri. Kece kika ruguza dukan yaƙinina akan ƙin yarda da mace, kece kika ɓata duk wani alwashina akan soyayya. Da gaske nake ina sonki”.

          Hibbah da gaba ɗaya hawaye suka gama wanke fuskarta tun fara bata tarihinsa ta matsa jikinsa da sauri ta rungumesa tare da fashewa da sabon kuka, sai kuma ta ɗago tana kai masa kananun duka a ƙirji kukan na sake kufce mata……….✍

      

TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*

*_NAJI DADI SHINE GARI……_*

*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*

_ILIMI_

_NISHADI_

_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_

*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*

     *NA SABUWAR SHEKARAR 2022*

*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*

*SABBIN LABARAI*

*SABUWAR SHEKARA*

*SABON NISHADI*

*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*

*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*

*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.

*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_

*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_

*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_

*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_

*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*

6019473875

MUSAA ABDULLAHI SAFIYA

keystone bank

Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number 

08184017082

*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*

09134848107

Littafi daya

1____300

2____400

3____500

4____700

5____1,000 (1k).

*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽

#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

 

Leave your vote

-5 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like