Advertisement
*_Chapter Forty Six_*
………..Duk da a yanayin da aka kawo su Hajiya mama ko’a jikin su A.G, sai ma wani kallonsu suke a wulaƙance. Hajiya mama dake kukan azabar da takeji a jikinta sai makyarkyata take dan kallon fuskokinsu kawai firgita rayuwarta yake.
Abba kam duk da a yanayin da yaga su Dr Sufi ɗin sai bai kawo komai a ransa ba. Ya duba A.G yana da ga zaune inda yaransu suka zubar da shi. “A.G ya halaka rayuwata, maimakon yaymin aiki sai yayi aiki akaina. Komai ya kwashe min, naira dubu 50 kawai ya barni da shi. Ya tafi da dukkan takardun dana bashi, na rantse bazan ƙyaleshi b……”
“Kai dalla yima mutane shiru”. Engineer ya katse Abba a harzuƙe. Ya nuna Abba da ke masa kallon mamaki. “Kai Halilu mu mun wuce kai mana wasan kwaikwayo anan. Yanzu kai ka rasa waɗanda zaka ruguza sai mu? Mune zaka cima dunduniya a garin nan bayan mune mukai maka sutura harka fito ake maka kallon mutum. Ka manta randa Balele ya kawoka nan tamkar ɗan dakon kashi. Amma bamu ƙyamaceka ba mukai maka buɗar kai da wanke duk wani datti naka da maƙudan kuɗaɗe. Shine a ƙarshe ka rasa waɗanda zaka halaka sai mu. mu zaka haɗa baki da matsiyacin yaron nan master kuci amanar mu……”
“Ni ɗin?!!”.
Abba ya faɗa a matuƙar razane har yana fama ciwonsa. Ya dafe ƙafar yana sakin marainiyar ƙara. Cikin rawar jiki ya shiga rantsuwa da ALLAH akan shi bai san wannan magana ta Engineer ba. Dan shi a gaba ɗaya rayuwarsa ma fa sau biyu ya taɓa ganin Master ɗin nan. Zaman farko da sukai ya bashi aiki kuma tare da A.G ne. Sai zama na biyu da sukai tare da su gaba ɗaya.
R.D ya sake katsesa da faɗin, “Kai maƙaryaci, idan har maganar daka faɗa gaskiyane yaya akai ya auri ƴar ɗan uwanka, sannan kuma matar da kake iƙirarin bakaso da manufa ka aureta ubanwaye ya sata barin gidanka ta koma wani daban? Mun kuma je can ɗaukarsu muka iske babu su a gidan”.
Abba da zuciyarsa ta fara hawa sama matuƙa yayma R.D ɗin wani shegen kallo, dama can yasan baya sonsa batun yanzu ba. “Amma yallaɓai ya kake magana haka kamar ba’a gabanku mukai komai da yaron nan ba a ranar. Miye haɗina da Asiya dazan ɓoyeta bayan nima nemanta nake ruwa a jallo. Ni kaga ma bansan ina suka koma ɗin ba har yanzu. Haka kazalika bansan an kamasu ɗin ba ma”.
Advertisements
“Ƙarya kake Halilu. Amma tunda bazaka faɗa ta arziƙi ba zaka faɗa ta yaren daya dace”. Cewar Alhaji Sallau a masife. Kafinma ya cema yaransu wani abu sun rufe Abban da duka shi da Hajiya mama. Cikin ƙanƙanin lokaci falon dama gidan baki ɗaya ya kaure da ihu da kururuwarsu. Abba da ya fahimci halakasu suke nemanyi a kiɗime ya nuna A.G. “Wlhy yasan komai, wlhy shi ya kamata ku tambaya inda master yake dan yafi kowa sanin sirrinsa anan wajen. Na tabbata da shi aka haɗa kai aka yashe mana kuɗaɗe dan nima shi naba takardun kaddarorina, kuma shine ya haɗani dashi, ta sanadinsa na sanshi”.
A razane A.G yake duban Abba, haka su Alhajin Mande ma a rikice suke kallon A.G ɗin. “Kai munafuki, ya kake neman ƙullamin sharri. Halilu anya ƙwalwar kanka kuwa bata samu matsala ba!!”.
“Na rantse da ALLAH kai ne”.
Abba ya sake faɗa cikin kuka wiwi. A.G da tuni zufa ta jiƙesa zaiyi magana Engineer ya katsesa cikin tafa hannu yana ƴar dariya. “Jama’a ga maganar Alhaji Sallau fa ta bayyana!”.
“Ban gane ta bayyana ba! Mi kake nufi?”. Cewar A.G yana kallonsa hankali tashe.
“Abinda kowa yaji a kunnensa mana A.G”. A matuƙar hargitse A.G ya miƙe ido rufe ya yarfama Engineer wani gigitaccen mari da sai da wutar kansa ta ɗauke. Abinka da jami’in tsaro yasan sirrin cin uban mutum. A razane duk suka miƙe baki buɗe. Har suna haɗa baki wajen ambatar sunan A.G ɗin.
A.G da gaba ɗaya ya birkice yace, “Sunana ne. Tayaya wannan mara mutuncin zai duba tsabar idona ya alaƙantani da cin amanarku. Duk iya ƙoƙarin da nake muku akan ɗan iskan yaron nan baƙwa gani har takai yau za’a kalleni da wannan suffar. In ban kashe Engineer ba kuce bani bane A.G”.
Da sauri Alhajin Mande ya riƙosa. “Haba A.G yada harzuƙa haka daga magana. A gabanka fa Halilu yace kaine minene laifin Engineer?”.
“Okay bakagama laifinsa ba! To yayi. Kai kuyita dukan Halilu da uwarsa har sai ya faɗi gaskiya”.
Tamkar ƙyaftawar ido zaratan samarin suka shiga lugudar su Abba har sai da suka suma aka zuba musu ruwa suka farfaɗo. Sake cigaba da dukansu sukai kuma babu ko tausayi balle duban tsufan Hajiya mama. Ganin zasu iya mutuwa Dr Sufi yace, “Nifa ina ganin duka bashi magani, idan kuma kun kashe Halilu ta ina zamu samu wani information kenan”.
Maganarsa ce ta saka Alhajin Mande dakatar dasu. Da ga Hajiya mama har Abba nishin azabar fitar rai kawai sukeyi. Dan tabbas sun sadaƙar yau kam zasu iya barin duniyar nan ma baki ɗaya.
Faɗa ya cigaba a tsakaninsu dan sufa sunƙi yarda da rantsuwar da A.G ke kwarara musu akan ƙarya Abba ke masa. Shi kuma ganin sunƙi fahimtarsa ya sake birkice musu kawai har takaisa ga fara dambatawa shi da Engineer da yafi kowa zaƙewa duk da tsufansu….
Advertisements
_________________________
A ɓangaren Master kam koda suka baro wajen su Ummi kai tsaye station suka nufa dan I.G ya shigo gari suna tare da C.P ma. Yaya Abubakar yayi matuƙar mamakin ganin inda sukazo, musamman daya san ana neman Isma’ill ɗinne ruwa a jallo. Sai dai kuma zargin daya jima a ransa ya sakashi yin shiru domin ganin ƙarshen wasan. Kasancewar Master bada fuskar Muhammad Shuraim yazo musu ba babu wanda yace da shi uffan. Sai dai saboda Abdull da wasu tsiraru ke gaishesu kasancewar sunsan yaron I.G ne. Sai ko shi yaya Abubakar daya haɗu da mutane biyu da ya sani.
Dama I.G ya shigo ne saboda case ɗin dake a hannun Master ɗin, dan haka sunayin knocking aka basu iznin shiga. Yaya Abubakar da Master suka ƙame kusan a tare domin girmamawa ga I.G da C.P.
Yaya Abubakar yay saurin juyowa ya duba Master, shima da yake shiɗin yake kallo sai ya sakar masa murmushi kawai ya ɗauke kansa ya maida ga I.G dake magana.
“C.P wannan shine A.S.P Muhammad Shuraim Aliyu, jami’i ne mai ƙwazo, dan haka na ɗorasa akan case ɗin nan na yaron nan master a sirrance. Bakuma hakan na nufin su waɗancan da suke aiki akan hakan bazasu cigaba ba”.
“Okay sir”.
Cewar C.P a girmame yana duban Master da ya ɗan sake ƙame jikinsa domin girmamawa ga C.P.
“A.S.P!”.
“Yes sir”.
Master ya amsama C.P ɗin.
“Tunda boss ya tabbatar da ƙwarewarka hundred percent muma mun yarda. Ina fatan kasan wannan aikine na gaggawa kuma mai buƙatar jajircewa. Duniya gaba ɗaya ta ɗauka burinta kawai taga Master a hannunmu, kowace hukuma ta tsaro farautarsa take domin ta kasance mai nasara. Kamar yanda wasu daga cikin jami’an mu suka tabbatar da harbinsa har sau biyu bazai kasance yayi nisa ba. Lallai-lallai yana cikin garin nan baije ko’ina ba, dan babu wata hanya da ba’a saka jami’an tsaro ba tun bayan mintuna goma sha bakwai da harbin nasa. Waɗannan mintunan kuma sunyi kaɗan ace ya fita a garin nan. Dan haka munada tabbacin yana cikin garin nan. Akwai teams da yawa dake zagaye da case ɗin nan, dan haka kaima zaka haɗa naka team ɗinne dan bama buƙatar duk waɗan can a naka operation ɗin”.
“Yes sir!”.
Master ya sake faɗa.
Sosai yaya Abubakar ya narke a tsaye, dan shikam yau Isma’il ya matuƙar jefa tunaninsa a garari da ruɗani. C.P ya katse masa tunani ta hanyar kiran sunansa.
Maida hankalinsa yay ga C.P ɗin yana ƙoƙarin dai-daita yanayinsa. Shima yace, “Yes sir”.
“Zaka taimaka masa a wannan aikin saboda na yarda da ƙwazonka matuƙa, shiyyasa mukasa ya ɗakko mana kai, dan mune muka saka aka ɓoyeku saboda information da muka samu cewar jami’an farin kaya zasuyi amfani da ku saboda ƙanwarka dake a hannun master. Kaga wannan shine amfanin sanar da abu da wuri, da baka sanar min ba da nima zan shiga tawagar masu zargin kasan master kai da ahalinka”.
Yaya Abubakar da duk suka rikitasa ya ce, “Thanks you sir” kawai, dan yafi buƙatar jin komai da ga bakin Isma’il, zuciyarsa ta fara raya masa Isma’il rainama su C.P hankali yake kenan suma? Kokuwa wani abu ne daban……
I.G dake rubuce-rubece jikin takarda ya miƙama Master. “A.S.P a yau zaka dawo filin daga, sai kayi ƙoƙarin haɗa sabon team. Ga wannan file ɗin zaka samu dukan bayanan da zaka buƙata a ciki insha ALLAH”.
Takardan da file ɗin master ya amsa da faɗin, “Thanks you sir”.
Daga haka suka fito, Master ya sake salute ɗin I.G cike da wani salo. A waje suka bar Abdull, dan haka ya miƙe suka fice a tare magana fal bakin yaya Abubakar.
Sai da suka fito da ga katafaren gate ɗin Yaya Abubakar da abu keta masa kaikawo a cikin rai ya duba Master.
“Anya kuwa Isma’il baka ɓoye mana wani abu? Zuciyata ta kasa riƙe zargin da take maka a wannan gaɓar gaskiya. Dama kai jami’in tsaro ne?”.
“Jajirtacce ma kuwa! Gwarzo abin kwatance da alfahari ga al’ummar wannan ƙasa.”
Abdull ya bama Yaya Abubakar amsa kai tsaye yana murmushi da juya sitiyari.
“Karka yarda da shi”.
Master ya faɗa yana duban Yaya Abubakar dake kallonsa ta mirror yana wani ƙayataccen murmushi dake tafe da ma’anoni da yawa. Murmushin shima Yaya Abubakar yayi a karon farko ya ɗauke kansa yana jinjinawa. “Dama na jima ina wannan zarigin a raina, a randa aka kaimu gidan can kuma na sake tabbatarwa. Jira da sauraren zuwanka kawai nake dama ai. Amma abinda ban fahimtaba anan shine, suma su I.G basusan kaike basaja matsayin master ba kenan?”.
Shiru Master yay tamkar bazai amsa ba. Sai kuma yay murmushi da kai hannu ya zare mask ɗin fuskarsa. Yaja tissue ya goge real face ɗinsa yana furzar da huci. “Ɗan uwana nake kallonka, dan tunda har kasan wanene Isma’il wannan ma zan iya sanar maka saboda a ƙarshen tattare aikin nan nake bana son abinda zai maidani baya kodan Muhibbat.” ya ƙare maganar da ɗaga idanunsa suka kalli juna da Yaya Abubakar. Murmushi sukayi a tare, master ya sake ɗauke idanunsa. “I.G yasan komai, C.P ne bai saniba.”
Ko tari kasayi yaya Abubakar yay. dan kuwa a yau ɗinnan ya sake tabbatar da zancen nan na mutane dake kiran Master ɗin Hatsabibi duk da su ɗin bama su gama sanin wanene shi ba. Abdull dake saurarensu yay ƙaramar dariya yana ɗan duban Yaya Abubakar ɗin ta mirror shima. “Yayanmu ai mana afuwa. Wannan surikin naka baida maraba da aljanin kan kuka mai leƙa gidan kowa. Sai kun haɗa da addu’a gaskiya”.
Mangare masa ƙeya Master yayi, hakan yasasu kwashewa da dariya su duka dan Abdull sitiyarin ya saki sai da Master ya riƙe da sauri. Har yana magana cikin suɓutar baki.
“Kai ɗan iska karka zubar damu wlhy ban gama angwanci ba, Baby luv na buƙatata a kusa da ita”.
Abdull ya tsaida motar yana kwasar dariya. Yaya Abubakar ma dai dariyar yakeyi, ransa fal farin ciki duk da sun jima da fahimtar irin son da Isma’il ɗin kema autarsu.. Master ya harari Abdull yana ƙumshe tasa dariyar dan harga ALLAH suɓutar bakice. Cikin borin kunya yace, “Ɗan haɗa gurmi in bazaka tada motarba zamu fita mu barka dan munada abunyi”.
“A’a miyay zafi na Baby luv. Bara na kaiku nikam kafin ka ƙonemu a titi. Shiru Master yay bai sake tanka masa ba. Yaya Abubakar ma dai sai ya saki zancen ya cigaba da duba file ɗin da I.G ya bama Master ɗin har suka kaisa station ɗin da yake aiki suka ajiyesa bayan Master yay masa bayanin shine zai haɗa musu team ɗin, shi kuma zaije ya ƙarasa tattare abinda ya rage daga nan zuwa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu zasu fita operation ɗin. Cike da gamsuwa Yaya Abubakar ya basu hannu sukai musabaha sannan ya fita.
Daga nan gida suka wuce suma. Inda su Habib suke jiran dawowar master ɗin dan tun a jiya ya sanar musu yau ɗin ranar aiki ce da ga nan har zuwa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu…………✍
TATATTUN FITATTUN LABARAN ZAFAFA BIYAR NA 2022*🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*ALSHIRINKU MASU KARATU!!!*
*_NAJI DADI SHINE GARI……_*
*KINA DA BUQATAR TSAFTATATTUN LABARAI DAKE CIKE DA*
_ILIMI_
_NISHADI_
_TSUMAMMIYAR SOYAYYA KUMA MAI TSAFTA DA ZATA SAKI SHIGA SHAUQIN SOYAYYA DA DUKAR DARUSSA KALA KALA A FANNIN ITA SOYAYYAR DA RAYUWA?_
*MAZA GARZAYO KI NEMI LITATTAFAN ZAFAFAN MARUBUTA GUDA BIYAR*
*NA SABUWAR SHEKARAR 2022*
*WADANDA SUKA ZAUNA,SUKA TACE LABARANSU,SUKA MUSU ADO DA SABUWAR FASAHA!!!*
*SABBIN LABARAI*
*SABUWAR SHEKARA*
*SABON NISHADI*
*_FARINCIKIN KASANCEWA DA MARUBUTAN CIKIN SASHEN DA AKE GWABZA RUWAN SHARHI DA MUSAYAR RA’AYI NA DABANNE_*
*MAZA ‘YAR UWA SIYA NAKI KI SHIGA SAHUN WANNAN TAFIYAR,TARE DA SAMUN DAMAR SHIGA SASHEN COMMENTS NA MUSAMMAN MALLAKIN MARUBUTAN*
*_TAKUN SAAƘA!!_* _Bilyn Abdull_.
*_SO DA ZUCIYA_* _Hafsat (miss xoxo)_
*_DEEN MANSHAL_* _Mamu gee_
*_ƊABI’AR ZUCIYA_* _Safiyya huguma_
*_HALIN GIRMA_* _Hafsat Rano_
*ta hanyar tura kudin littafinki zuwa ga wadan nan lambobi dake qasa*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATI NE KUMA KO VTU,SAI KU TURA ZUWA GA*
09134848107
Littafi daya
1____300
2____400
3____500
4____700
5____1,000 (1k).
*INGANCI DA NAGARTAR RUBUTU,BABU NADAMA KO DANA SANI*🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽🤞🏽
#team ZAFAFA BIYAR🔥🔥🔥🔥🔥
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
GIPHY App Key not set. Please check settings