TAKUN SAKA 48

Advertisement

 *_Chapter Forty Eight_*

…………Duk wanda ya kwana ya tashi a wannan ƙasa yau an wayi garine da babban labarin kama master da iyayen gidansa. Duk da kasancewar akwai sauran duhun asubahi hakan bai hana anguwar cika da mutanen cikinta da jami’an tsaro ba. Hakama ƴan jarida da basu yarda a barsu a baya ba. I.G da C.P ma basu zauna ba nan suka nufo dan case ne babba da kowa ke buri akan ganin wannan rana da za’a kama master. Kowa

ba’a bari ya shiga gidan ba hatta sauran jami’an tsaro, dan Master da yaya Abubakar sai da suka gabatar da sallar asubahin su, sauran yaransu ma sukayi sannan suka yarda suka buɗema su I.G ƙofa. Duk da I.G ya jima da sanin su A.G a cikin tawagar ta bakin Master a yau daya gansu sai takaicinsa ya sake ninkuwa da tsanarsu. Ya kauda kansa hawaye na ciko masa idanu. (Wai fa manyan mutane daya kamata su bama ƙasa kariyane anan tare da ɗan ta’adda mai ruguza ƙasa. ALLAH kaɗai yasan irin ɓarnakun da sukayi a tsahon shekarun da suke tare da shi. Akwai irinsu da yawa kuma dake lulluɓe da rigar mutunci suna cin dunduniyar ƙasa. Ta yaya ƙasa zata gyaru bayan manyan cikinta sune masu bada gudunmawar gurɓatar yaran dake ta’addanci. Kullum aiki sukeyi ƴan ƙasa na ganin gazawarsu da tunanin yaudara a dalilin tufkar da suke wasu na warwarewa saboda makullan madafun iko dake cikin hannayensu ta ɓangarori da dama).

         Duk da agalabaice su A.G suke saboda harbin da Master yasa akai musu hakan bai hanasu jin kunyar idon su I.G ba, ga ƴan jarida da aka bama damar shigowa sai ɗaukarsu suke a hoto da video lokacin da ake fiddosu da ga gidan. Master ya bada damar saka hajiya mama a motar asibiti, su Abba kam da su A.G aka tarkatasu zuwa police station jami’an tsaro zagaye da su mota-mota.

_____________________________

         Hibbah da Ammar na zaune a falo tun bayan sallar asuba, Hibbah dake latsa wayar Ammar tana kallon hotunan biki tai wani irin zabura ganin news da ɗumi-ɗuminsa a facebook akan an kama Master. Gaba ɗaya ta rikice dan duk zatonta Master ɗinta ne. Cikin tashin hankali Ammar da yaga yanda ta gigice ya warce wayar ya duba shima, da sauri ya rarumi remote ya kunna ƙaramar television dake a falon, a dai-dai nan su Yaya Usman ke sakkowa da ga sama hakama Ummi. Gaba ɗaya wutar kan kowa ta ɗauke saboda ganin abinda ke faruwa. Hibbah ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya lokacin da ake nuna su A.G da master ɗan ta’adda a galabaice saboda harbin da suka sha. Sai su Yaya Abubakar da Master dake ƙoƙarin zillema ƴan jaridar dake neman titsiyesu nason jin yaya akai suka kama master.

Advertisements

       “Kambu! Da gaske fa Yaya Isma’il jami’in tsarone Ummi”.

     Ammar ya faɗa a zabure yana nuna television ɗin. Hannu Ummi ta ɗaga sama tana godema ALLAH, dan harga ALLAH taji daɗi har cikin ranta, ta share hawayen dake zubo mata na tsantsar farin ciki tana kamo hanun Hibbah ta rungumeta.  

______★

     Cikin ƙanƙanin lokaci duniya ta ɗauka. Hotunan su R.D da Master suka fara yawo a social media ta kowanne ɓangare. Tuni kowa ya fara tofa albarkacin bakinsa akan wannan al’amari mai ban mamaki, musamman ma da manyan ɓarnakun da su A.G suke aikatawa suka fara fitowa a bakunan wasu mutane da suka san sirrinsu. Waɗanda ada tsoro ya hanasu fitowa su faɗa. Musamman ma’aikatan gidajensu na shakatawa. Sai kuma wasu boyayyun mutane da harkalla ta haɗasu da su A.G ɗin suka cutar dasu ko makamancin hakan. Wannan fa shine allura ta tone garma. Dan kuwa har abinda ma ba’ai zato ba sai gashi yana fitowa. Cikin ƙanƙanin lokaci ƴan bani na iya musamman matasa suka fara yo gangami zuwa police station akan a basu su A.G su halaka. Hankalin su Master ya tashi, dan an rasa wanda ya fara fasa zancen su A.G ɗin na Homo. Sai da suka zurfafa binciken gaggawa aka gano a wani shafi na manhajar facebook maganar ta fito, sun bibiyi shafin kuma sunga an buɗesane a safiyar yau dai-dai lokacin da zancen kamasu A.G ɗin ya fito. Babu wani kuma damar da za’a iya bibiyar mai shafin da ita kai tsaye, dan komai bai saka ba. Email ɗin da akai amfani da shi ma babu wani information tattare da shi. Ana cikin haka sai ga wasu hotuna kuma sun fara yawo nasu Halilu da su A.G ɗin tsirara haihuwar uwayensu suna aikata baɗala fami muni da cizon zukatan masu imani.

     Tuni komai ya sake birkicewa, matasa da dama ƙiris suke jira sun sake harzuƙa akan infa ba’a basu su Abba ba to lallai zasu ƙona ofishin ƴan sandan. Duk yanda su Master sukaso controling mutane cikin sauƙi hakan ya gagara, dole aka haɗa da barkonon tsohuwa mai saka hawaye sannan suka tarwatse, jami’an tsaro ta kowanne fanni suka maye gurbin harabar station ɗin dama titin baki ɗaya. Amma duk da haka fama aketayi da matasa.

         I.G da yaga abin na neman zama babban al’amari dole ya fito yay magana ga ƴan jarida cikin lallashi, ya tabbatar ma da jama’ar gari basuyi ƙasa a gwiwa ba wajen miƙa su A.G gaban alƙali, dan haka su kwantar da hankalinsu gaba ɗaya suspects ɗin zasu sami hukunci dai-dai da ɓarnar da suka aikata. Zakuma a zurfafa bincike domin cigaba da zaƙulo duk waɗandama suke tare da su da ba’a kamaba a yanzu haka.

       Bayanin I.G ɗin ya ɗan kawo lafawar tarzomar, sai dai fama matasa nata kaikawo a media cewar inhar ƴan sandan basuyi wani abu da wuri ba to lallai su zasu ɗauka hukunci a hannunsu, kuma zasu tabbatar da shi.

        Da ga Master har yaya Abubakar a jigace suke, tun daren jiya suke abu guda babu hutu, ga Master dama ba isashen lafiya ne da shi ba. Dauriyace kawai da jarumta da son sauke aikin nan ya hutama ransa. Idanunsa kawai ka kalla dake cikin mask zaka tabbatar da yana buƙatar hutu, sai dai kuma babu damar hakan. Sai da I.G ya fahimci kamar jiri na neman ɗibar Master ɗinne sannan ya kamosa ya zaunar yana masa faɗa.

        Koda yasa aka samo masa abinci tea kawai ya iya sha, ya samu yasha maganin da Habib ya kawo masa da ga gida da ƙyar bisa taimakon Abdull. dan su tun jiya da suka kammala aikinsu suka koma gida suka koma kallo da jiran news. Sai da suka fahimci Master bashi da niyyar fasa ƙwai akan ƙazantar su A.G ne yasasu buɗe shafi suka saki hotunan su A.G ɗin da suka taɓa samu a camara ɗin Master batare daya sani ba tsahon lokaci. Sai dai kuma kafin su saki nasu sai ga wani shafin ya saki zancen su A.G ƴan homo ne. Hakan ya musu daɗi dan sun samu abokin ritatawa. Yanda garin ya hargitse da yunƙurin mutane na abasu su A.G su halaka ba ƙaramin daɗi yay musu ba a rai da zuciya.

Advertisements

  

            ★★★

    A nan wajen su Ummi ma Ammar da Hibbah suna a cikin kwatankwacin farin cikin da su Habib ke ciki, dan kuwa ita da Ammar ɗinne suka buɗe shafin farko wajen bayyanama duniya su Halilu ƴan homo ne. Kasancewar Hibbah kwararriya ce mai ƙwazo ta tabbatar za’a iya bibiyan shafin koda badaga jami’an tsaro ba tabi matakai na ɓoye kai da bin hanyoyin da labarin zai saurin yaɗuwa ga al’umma. Sai ko gashi bukatarsu ta biya. Dan ko mintuna ashirin cikakku basuyi ba zancen ya fita. Har manya-manyan shafukan sada zumunta na yaɗa labarai irin su bbc suka ara suka yafa suma.

___________________

         Kwatanta muku irin baƙin tashin hankalin da iyalan Halilu da nasu A.G dake hannun Master suka shiga ma ɓata lokaci ne, tsabar firgita na shigar al’amarin cikin kunnuwansu wasu har yanke jiki suke suna faɗuwa musamman akan zancen Homo ɗin nan. Dan masu guntayen hawan jini dana suga tuni sun haura dubu bisa dubu ma ba ɗari biyu ba. 

      Dole cikin tashin hankali masu tsaronsu suka kira Master suka sanar masa halin da ake ciki. Yay ƙoƙarin nufar gidan I.G ya dakatar da shi danshi tausayi Master ke bashi matuƙa saboda sanin shima likitan yake buƙatar gani. Wasu jami’an aka tura da motar Ambulance domin kwaso waɗanda ke a halin ciwon. lafiyayyun kuma za’a kawosu station ɗin.   

_________________

         A ɓangaren su A.G ɗin suma an cire musu bullets ɗin dake a jikkunansu tun bayan isarsu station ɗin, sannan aka garƙamesu cikin cells ɗaya na musamman na masu aikata manyan laifuka. Da wannan damar sukai amfani wajen titsiye master cikin bahagon yanayi, zayyane musu komai na yanda akai Isma’il (Master) ya dunƙule rayuwarsa ya maye gurbinsa ya basu. tare da azabobi kala-kala daya dinga gana masa ta hanyoyi da dama da bazai iya tuna wasuba a tsahon shekara biyun nan ma. 

      Tabbas sun harzuƙa ƙwarai da gaske, sai dai babu damar ɗaukar mataki, yayinda mamaki, al’ajabi na hatsabibancin Master ya sake kashesu matuƙa. Sosai zukatansu ke zafi da ɗaci, musamman idan suka tuna ɓarna da tabargazar da suka dinga zubawa a gaban Master ɗin da a yanzu sunsan bakin alƙalami ya rigada ya butse. Basu da wani sauran tasiri akan kansu ma balle akan wani. Daga ƙarshe takaicinsu da haushinsu suka shiga saukewa akan Halilu daya gallabi rayuwarsu da kukan azabar da yakesha a jikinsa na dukan da suka saka akai masa da karayarsa data koma sabuwa dan shi Master bai sa an harbesa ba saboda ganin halin da yake ciki.

       Marayan kukan azabar da Halilun keyine da ihu ya saka jami’an dake zagaye da su saurin sanarma C.P da keta kai kawo. Dole yasa aka ciro Halilun daga cikinsu dan gaba ɗaya ya galabaita har numfashinsa na fusga na alamar mutuwa. Cikin hanzari C.P ya bada umarnin a miƙasa asibiti.

_____________________________

       A gaba ɗaya yinin yau ma dai su Master basu samu kansu ba har dare, dan shi zazzaɓi ma ya masa rijif koda yasha magani bai samu ya kwantan ba yanda ya kamata. Sai kusan ƙarfe ɗaya da wani abu na dare bayan sun gama meeting ya samu da ƙyar ya rarrafa gida bisa taimakon Abdull.

      Hakama Yaya Abubakar sai dare ya shiga gida, inda su Hibbah da barci ya gagari idanunsu suka zagayesa suna masa sannu dan kallo ɗaya zai baka tausayi shima tsabar zirga-zirgan da sukasha yau. A bakinsa suka sake jin abinda ya faru da Halilu a hannun su A.G harda Hajiya mama da baisan miya kaita hannun su A.G ɗin ba. Mamaki sukai suma matuƙa sai dai ko kaɗan basu wani ji tausayin Halilun ba balle Hajiya mama. Garama Ummi ta ɗan nuna tausayawarta ga Hajiya maman. Sai ko Master da takejin kamar tai tsuntsuwa taje taga halin da yake ciki dan Yaya Abubakar ya sanar musu shima bayajin daɗi.

      Hibbah dai batace komaiba, sai da tazo kwanciya kuma abun yayta damunta arai. A sace ta ɗauka wayar Ummi datai barci tai kiran layinsa. Sai dai harya tsinke ba’a ɗaga ba. Massege ta tura masa ta kashe wayar ta koma ta kwanta zuciyarta tab bege da ƙishirwar son ganin halin da yake ciki.

*_WASHE GARI_*.

            A yau ɗin ma bada daɗin rai aka tashi ba. Dan dandazon jama’ar gari bisa jagorancin matasa tun farar safiya suka zagaye station ɗin. Su kansu su Master da ƙyar suka iya samun hanyar shiga Station ɗin suka fito dasu A.G da za’a miƙa kotu bisa shawarwarin masana da dattijan ƙasa. Dan kowa ya fahimci jinkirin miƙa su kotu zai iya kawo babbar tarzoma da matasan ke son tadawa tun a jiya. 

         Tsabar yanda mutane suka fusata wasu da ƙafa suka ringabin motocin su Master ɗin da wadda aka ɗakko su A.G a ciki dake tafiya a hankali kasancewar titin ma babu sauƙi. Haka suka tafi cikin wannan gangamin jama’a har zuwa kotu. 

         Su A.G laifi garesu har a wajen manyan ƙasar ma. Dan shi kansa shugaban alƙalan alƙalai da aka gayyato domin yin shari’ar tasu sun saka Master ya taɓa guma masa uban yasa a accaunt ɗinsa tun a farko-farkon shiga jikinsu da yayi. Rashin sanin Master ne yay waɗan nan yashe-yashen kuɗaɗen har yanzu yasa su gaba ɗaya zarginsu akan master ɗan ta’adda yake. Dan haka aƙali dake cike fam da mikin tabon da aka bar masa ya shirya musu tsaf shima domin acewarsa *RAMUWAR GAYYA TAFI GAYYA ZAFI.*

     

           Duk da shari’arsu shari’a ce buɗaɗɗiya hakan bai hana a bama lauyoyinsu damar fafatawa ba da lauyoyin gwamnati. Sai dai manya-manyan hujjojin da lauyoyin gwamnati ke riƙe da su yasa suka kada nasu A.G tun ma kafin shari’ar tai nisa. Dan dole aka matsi bakunan su Alhajin Mande suka zayyane kaso mafi yawa na daga tsiyatakun da suka aikata da rigunan mutunci da wanda master ɗan ta’adda ya aikata bisa umarninsu. Koda suka kawo maganar yashe asusan mutane ba master ɗinsu bane sam alƙali baima sauraresu ba. Dan ihu da boren dake faruwa ta waje daga jama’ar gari da kuɗin da alƙali yaci na manyan mutane irinsu matar gwamna yasa shi yanke musu hukuncin zaman gidan kaso na tsahon shekaru ɗari da hamsin-hamsin. A takaice dai kowa yasan ɗaurine na rai da rai wannan kawai.

       Sosai wannan hukunci yayma kowa daɗi a cikin manyan, nan take aka cikuykuyi su A.G da aka hana sake cewa komai akayo waje da su domin miƙasu magarƙama (prison). Duk da wannan hukunci da aka yanke musu hakan bai hana jama’ar gari da sukai ready ɗin fitowar tasu ba fara jifansu da gasu har jami’an da suka fiddosu. Dansu burinsu kawai a basu su A.G su kashe kawai yafi hukuncin zaman gidan yarin a wajensu. Sosai ruwan dutsuna ke sauka a kansu har takai da ƙyar aka turasu mota. Nanma basu tsiraba dan motar mutane suka dinga jifa tako ina suna fasa glasses ɗin. Dole jami’an tsaro suka koma kare kawunansu kawai basu A.G ba. Kafin a bar harabar kotun da anguwarma baki ɗaya dasu an musu mugayen raunuka sunata ihu da kururuwa. 

       Dan dole aka canja akalar miƙasu prison aka nufi asibiti dasu domin fara treating nasu. Da wannan damar Master yay amfani wajen yima master ɗan ta’adda allurar guba batare da kowa ya farga ba, yayi kuma hakanne domin ɗaukar fansar iyayensa tamkar yanda yay ƙudiri a ransa tun farko. Bayan anyi treating ɗinsu dole nan ma aka bar asibitin dasu zuwa asibitin cikin prison ɗin saboda tsaro ba tsoro ba. Dan duk da boren nan na jama’a akwai magoya bayan su A.G a gefe musamman ƙasashen ƙetare da suke kallon ƙazantar da su A.G ɗin ke aikatawa wadda jama’a ke tada jijiyoyin wuya a kanta ba komaiba. Za’a kuma iya yin amfani da wannan damar a kuɓutar dasu, duk da kuwa a prison ɗin ma dai bawai sakaran tsaro aka barsu da shiba. An sakasune cikin tsatstsauran tsaro da horo mai tsananin gaske da sai sun gwammaci mutuwa da da rayuwa. A yanda mutane ma suka jigatasu da raunikan ruwan duwatsu da wahala wasu a cikinsu sukai labari. 

             Abubuwan sun ɗan lafa kaɗan, sai dai an cigaba da cecekuce a kafafen sada zumunta dana yaɗa labarai musam akan abubuwan da suka biyo baya daga bakunan ahalin su A.G, tun daga kan matansu, ƴaƴansu, zuwa danginsu daketa fitaowa suna nuna ƙyama da nisanta kawunansu da su. Yayinda wasu keshan tsinuwa a wajen tsoffinsu da basu riga sun mutu ba irinsu Hajiya mama dake kwance a asibiti rai hannun ALLAH. Dan da ƙyar take iya gane wanda ke kanta. Sai dai bakinta bai gajiyaba wajen jan tsinuwa da ALLAH ya isa ga Halilu.

     Koda su Ummi ma sukaje dubata bisa tursasawar Ummi ɗin da ƙyar ta ganesu tana darzar kuka da roƙon su yafe mata musamman ma Ummi. Ummi tasha kuka dan duk mai imani yaga yanda ƙafar Hajiya mama zuwa rabin jikinta sukai wani masifar kumbura dole ne ya tausaya mata. Ahakanma wai an samu anyi mata gyaran karayar datai a ƙugun a daren jiya a asibitin. Ba itaba. hatta su likitocin kamsu basu san adadin sumar da Hajiya mama tayi ba saboda azabar wahala. Fitsari kam ai ba’a magana ko fanfon birtzatse ya shafa mata lafiya.

     Ko’a jikin su Hibbah, dan ita hankalintama nakan mijinta da sam bataji ɗuriyarsaba yau ma. sai ganin data ɗan masa a tv sanda ake kotu da su A.G. Bisa jagiorancin Yaya Abubakar shima Abba aka kaisu suka dubashi. dan shima dai prison ɗin za’a miƙasa bisa hukuncin alƙali zaiyi shekaru ashirin a gidan yarin. Anan ko Ummi komai batajiba sai ma kallon kaɗan ka gani dataima Halilun. Hakama su Yaya Usman ko’a kwalar rigarsu tamkarma ba dubiyarsa sukazo ba. Basu wani jimaba suka koma gida abinsu.

___________________________________

       Tun Hibbah nasan ran Master harta cire rai, dan tsahon kwanaki biyar kenan babu shi babu alamarsa. Harma sun bar wannan gidan sun koma gidansu da yau Hibbah ta fara shiga. Duk da damuwar rashin ganin mijinta dake cin ranta haka ta danne ta nuna farin cikinta akan cigaban da yayunta suka samu. Dan ko gida sai sam barka komai yaji gishiri da magi. Sai fatan ALLAH ya sauki su Hafsat lafiya kuma.

        Sarai Ummi na lure da halin da Hibbah ke ciki na kewar mijinta amma ta fuske. Kowa yaƙi mata maganar Master ɗin ma a gidan dan ba’ason sanar mata baida lafiya kamar yanda ya roƙa a ɓoye mata har sai ya warke kan hankalinta ya tashi. Ba kuma dan ciwon ma kaɗai ya nisanceta ba. Harda shirye-shiryen ƙarin girma da zai samu shi da wasu tawagar jami’ai irinsu yaya Abubakar. Dan haka yay tunanin haɗewa da ɗan walimar cin abinci na ƙara’in bikinsu da ba’ayiba dana komawa sabon gidansu da yake fatan suyi rayuwa ta din-din-din shi da sauran ƴan uwansa.

          Sai da Ummi taga damuwar Hibbah na fitowa ƙarara akan fuskartane ta zaunar da ita tai mata nasiha da kwantar mata da hankali akan wani babban uzirine yasa Master ɓuya amma yana nan dawowa daga tafiyar da yayi nan kusa. Ta ɗanji sanyi, amma taji ciwon rashin sanar mata da yayi bai kuma nemeta koda a waya ba balle ta san tanada kima a garesa.

          Da wannan damar Ummi da Mama Jiddah amaryar Sheikh Aliyu Maina da Uwargida ran gida Maimunatu sukai amfani wajen gyare Muhibbat ɗin ciki da bai da kayan gyaran jiki dana fata gangariya da ƙamshi. Tare da zaunar da ita suka fara ɗora mata karatu na musamman akan aure da zamantakewar cikinsa. Haƙoƙin miji akan mace da na macen ma akan mijinta. 

       A gefe kuma kayan auren Hibbah da aka shirya tun lokacin auren a gidan da Master ya bada matsayin Muhammad Shuraim tuni an kwashesu an maida inda zasu koma ɗin an jere mata su tsaf.

★★

       A ɓangaren Master ma cike yake da tsanin kewa da buƙatar matarsa. Sai dai yayi ƙoƙari matuƙa ya danne wajen ganin yama Ummi kawaici dan itace da kanta ta buƙaci yabar Hibbah a kaita kamar kowacce mace gidansa ita da su Yaya Muhammad. Bazai iya musa musu ba, dan sunyi matuƙar ƙoƙarin a garesa. Hakan yasashi yin amfani da wannan damar shima yay nasa shirye-shiryen da ƴan ƙannensa bayan jiyyar daya sha ta gajiya da sauran raunin jikinsa.

        Abinda kuma bai sani ba su Habib gagarumin biki suke shiryawa tare da Abdull da su I.G dayay burin hakan akan auren Master sai dai ALLAH bai nufa ba. Dan haka yay ƙudiri da aniyar biyan bashi a yanzu bayan yayi tattaki har gidan Sheikh Aliy Maina sun bada haƙuri akan yanda abubuwa suka faru, kasancewar su Yaya Muhammad suma suna tare da Sheikh Aliy ɗinne akan zaman dama duk sai suka nuna babu komai ƙaddarace ai wadda ta riga fata. Fatansu dai ALLAH yasa hakan shine alkairi ga Master ɗin da Muhhibat a yanzun.

      Al’amarin kamar wasa sai ga Muhibbat ta cika watanni biyu a gida tana jiran tsammani. Tayi wani irin masifar ƙyau da haske dake bama kowa mamaki, su Zahidah na tsokanarta akan cikine. Ita dai bata tanka musu duk da tanajin fargaba har cikin ranta. Dan da gaske watanni biyun nan datai a gida bataga al’adarta ba sam. Sai dai kuma ita sam batajin ciwon komai a jikinta dan haka take fatali da batun nasu.

      Ummi kam a yawan barcin da Hibbahn keyi a kwanakin nan yasata zargin ko cikinne da ita. Sai dai rashin ganin sauran alamomi yasata ajiye zargin nata itama dai. 

           A randa Hibban ke cika wata biyu da sati guda a gida aka sallamo Hajiya Mama. Ƙin amsarta su Momy sukayi acan gidan dan haka yaya Abubakar ya kawota nan wajen Ummi. Ummi bata musa ba ta amsheta kodan yaranta da darajar Aliyun ta da bazata taɓa iya manta hallacinsa ba shi da Malam. Ɗaki guda aka warema Hajiya maman ta cigaba da jiyya. Su Yaya Muhammad suka ɗakko mai kula da ita acan ƙauye cikin ƴan uwanta da ƙyar. Ko sau ɗaya Hibbah bata taɓa leƙa ɗakin hajiya mama ba domin dubata. Hakama Ammar da Yaya Umar da sukafi kowa tsanarta. Ummi tayi nasihar harta gaji ta sanya musu ido kawai.

         Shirye-shiryen tarewar Hibbah ake sosai a gidan, dan kwanaki biyu kacal suka rage amarya harta sha lalli ƙafa da hannu, tare da kitso na musamman irinn ƴan maidugiri da wata ƴar da Jiddahn ya Sheikh ke riƙo ta fanin Umminsu tai mata. Gyara kam ta shasa harta gaji, dan bayan gyaran dasu Maimoon uwar gidan yah Sheikh ke mata a ɓangaren mamansu Zahidah ma sun gayyato shahararriyar mai haɗaɗun kayan gyaran jikin nan mai kamfanin *mg’s skin care*, tun daga kan mayuka, sabulai kala-kala na maida tsohuwa yarinya. *(08062991549)* akan farashi mai sauƙi da rahusa ta haɗa mata kayyaki na musamman da dorata akan kayan shafa dana gyara na mata masu aji ta kowanne fanni itama tana katalleta.

        Haka kawai yau Hafsat ta tashi da ƙwazabar son yin gasashen kifi saboda ƙwazaba irin tamai ciki. Kasancewar matar Yaya Muhammad ita kuma sam bata shiri da kifin yasa Hafsat tahowa sashen Ummi tayi dan maƙwafta sashen Hafsat da Maimunatu (Kausar) suke. Koda ta gayyaci Hibbah ta tayata ƙin zuwa tai, kamar wasa ƙamshi ya fara sirɗaɗowa falon Hibbah na kwance tana kallo. Da farko dai ta ɗan fara yamutse fuska har Ammar na tsokanarta da cewar gulma. Ƙin kulashi tai dan ita kaɗai tasan mi takeji a tsakkiyar kanta game da ƙamshin kifin nan. Ammar da bai fahimci halin da take a ciki ba ya miƙe yana mata gwalo ya shiga kitchen wajen Hafsat ɗin. Ko mintuna uku baiyi cikakku da shiga ba suka jiyo tamkar gudu a falon. Cikin hanzari suka leƙo dan Hibbah suke zargi dama.

        Hibbah da aman daya yunƙuro mata yaci ƙarfinta dole ta durƙushe tan gab da isa ɗakinta ta sakesa a matuƙar wahale. Kanta suka nufo da gudu cikin tashin hankali da tambayarta lafiya?. Ina bama tasan sunai ba. Dan da alama dai aman baizo da wasaba. Hatta Ummi dake ɗaki tana azkar na yamma da sauri tayo waje. Haka ma mai kulla da Hajiya mama babu shiri ta fito duk suka rufu akan Hibbahr datai matuƙar jigata. Dan ko aman yayi kamar zai tsaya da ƙamshin kifin ya sake shiga hancinta saita sake sabon yun ƙuri.

          Fashewa tai da kuka jikin ta na rawa ta sake mamuƙe hanun Ammar dake riƙe da ita. “Y…ya…ya Ammar banaso ku fita da ki.f.in”. Ta faɗa da ƙyar tana sake sakin sabon kuka. Cikin sauri Hafsat ta nufi kitchen domin fita da kifin, yayinda Ammar ya ɗauka Hibbah ɗin gaba ɗaya sukai ɗakin Ummi dan a samu tabar jin ƙamshin kifin.

        Yanda ta galabaitan dole ne ta baka tausayi, da taimakon Ummi ta gyara mata jikinta a toilet ɗinta da Ammar ya kaita can direct. Kuka take wiwi jikinta duk ya saki harda su ɗan zazzaɓi. Har yanzu kuma jin kamshin kifin take har tsakkiyar ƙwalwar kanta saboda tsaya mata da yay a rai. Ummi data gama gaskata cikine da Hibban ta kamota suka fito a toilet ɗin. Zaunar da ita tai a gado ta fita zuwa ɗakinta ta ɗakko mata wasu kayan. A falo ta wuce Ammar da Hafsat na gyara wajen da Hibbah ta ɓata.

           Ummi na dawowa da kayan ta iske Hibbah harta kwanta. Ɗagota tai ta taimaka mata ta saka kayan tana jera mata sannu tausayin autar tata na ratsata. 

        “Ummi ki bani wani abun na shinshina ko zan daina jin ƙamshin banaso zan sakeyin amai”.

     Cikin lallashi Ummi dake murmushi ta shiga shafa kanta bayan ta kwantar da ita a jikinta. “Tanee ki ciresa a ranki kawai shine zaisa kibar jin ƙamshin a hancinki, dan tuni Hafsat ɗin ma ta fitar da shi a sashen nan. Amma faɗamin mikike son ci?”.

        “Ummi banajin yunwa, sai dai kozan samu tumatur masu ƙyau da suka nuna sosai zansha”.

      “Abu mai sauƙi”.

Ummi ta faɗa tana miƙewa bayan ta kwantar da Hibbah. Cikin lokaci ƙanƙanin sai ga Ammar da duk yay kalar tausayi kamar shine mara lafiyan da manya-manyan tumatur masu ƙyau a ƙaramin bowl har kusan goma ya kawo mata. Dan anyi sa’a an kawo musu cefanen dama babu jimawa. 

      Sagade yayi yana kallon Hibbah nashan tumatur ɗin cikin rawar jiki tamkar wadda ta samu wani apple ko inibi. A wannan halin su Yaya Umar da suka shigo gidan matansu suka sanar musu suka shigo suka sami Hibban. Su kansu mamakin shan tumatur ɗin suka tsayayi har Yaya Umar na yima Ammar faɗa.

        Amarairaice Hibbah ta ce, “Yaya inasone akwai daɗi”.

       Yaya Umar zaiyi magana Ummi ta ɗan girgiza masa kai. “Karka damu Umar barta tasha. Tunda shi zuciyarta keso shi kaɗai zatasha a zauna lafiya inhar ya zauna.”

        Shiru kawai sukai badan hakan ya musu ba. Hibbah na kammala shan tumatur ɗinta kuwa ta zame ta kwanta dajan bargo tana sauke tagwayen ajiyar zuciya, nutsuwa na ratsata. Wahalar data sha yasa barci saceta cikin ƙanƙanin lokaci batare data shirya hakan ba.

       Koda ta farka kusan bayan magrib garau ta tashi tamkar ba’ita ba. Sai dai ɗan rashin ƙarfin jiki da takeji shima bamai cutarwa ba. Salloli tayi ta fito falo inda take jiyo hayaniyar yayunta da matansu suna hira. Duk sunyi farin cikin ganinta garas. Suka shiga tambayarta jikinta tana amsa musu cikin shagwabar tata saba musu. Suko da kulawa suketa sake sonjin ko tana son wani abu da zataci. Kanta ta girgiza musu tana kaiwa zaune da faɗin, “A’a yaya ku kwantar da hankalinku zanci duk abinda aka dafa indai babu wancan abun na ɗazu (ko sunansa batason faɗa dan ma karta tuno). Sunji daɗin hakan suka sake mata addu’ar sauƙi mai ɗorewa. Daga haka suka cigaba da hirarsu tana lafe a jikin Umminta da tun ɗazun take cikin tsantsar farin ciki akan baiwar da ALLAH yay mata na albarkar auren ƴaƴan nata biyar reras kusan lokaci guda. Bata yarda tayi zancen cikin dasu ba dan batason ma zancen ya fita har sai Hibbah ta tare gidan mijinta. Shiyyasa tunkan aje ko’ina ta cewa Hafsat ma tai shiru da bakinta ko mijinta karya sani tunda ta lura Ammar shi dama bai fahimci komai ba garan😂………….✍

*_MATAYEN ƘWARAI KUNA INA NE?._*

_Maza ku garzayo da gudunku ga ƴar zuru mamar zee-zee mai kayan mata na maida tsohuwa yarinya💃🏻._

*Kayan matan ƴar zuru zasu maidaki shalele ƴar gaban goshin maigida koda kina da kishiya ƴar birnin shehu😂💃🏻*.

_Kayan ƴar zuru nada matuƙar sirrika da inganci irin wanda sai an gwada akansan na ƙwarai. Idan da ƙyautar gida akemiki a master room kikai amfani da kayan ƴar zuru Nigeria za’a baki harda jirigin sama na yawata ƙasashen duniya😉💃🏻_.

*MUNADA KAYAYYAKI KAMAR HAKA*👌🏻

Kaza akwai 10k

15k

5k

Tsimi 5k 10k

Matsi 5k

Gumba uku 2k 

Zumar gorun tula syrup3k

Garuka 3k

Cicccibi 5k

Zakara 20k

Zabo20k

Humra 

Turaren tsugunni 

Butar tsarki

Maganin infection

Tsimin tabaje 

Turaren al,ajab 

*Muna maraba da maisayen ɗaya ko sari, kayanmu garantee ne in har basuyimaba zan maidama kudinka*.

 

_Address maberar jariri bayan FGC sokoto_ 

08068526455

*Zaku iya saving number ta domin ganin hajata*

Zaku iya samun mu amanhajar

Facebook

Istagram

Yar_zuru_mamar_zeezee- kyn_mata.

Sai kunzo🥰🥰🥰🥰💃🏻👌🏻.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like