AZIZA DA AZIMA 21-30

Advertisement

 *بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

Advertisements

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*

1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._

2- _GUDU A JEJI._

3- _SHUHADA._

4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._

5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._

6- _COLONEL UBAIDULLAH._

Advertisements

7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._

8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._

9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._

10- _DA NA SANI NA._

  11- _BADAWIYYAH_

12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_

Now

13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_

   🍃🍃🍃🍃🍃

🙇🏻♀️🙇🏻♀️🙇🏻♀️🙇🏻♀️🙇🏻♀️

*WANNAN DUƘAWAR NAKI NE SISINA, DAN ALLAH KIYI HAKURI KI HUCE KINJI🙇🏻♀️😟 KAR AYI MANA DARIYA, ALLAH YA HUCI ZUCIYARKI🥰 AMEENATUNA SLIMZY BABY🥰 MATAR MIJINTA🥰*

Mom Ahlan, macijiya🐍😂

[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

    💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨

    (🐍 _Macizai ne_🐍)

    MALLAKAR.

*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din

0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.

Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*

1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._

2- _GUDU A JEJI._

3- _SHUHADA._

4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._

5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._

6- _COLONEL UBAIDULLAH._

7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._

8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._

9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._

10- _DA NA SANI NA._

  11- _BADAWIYYAH_

12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_

Now

13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_

_Follow me on wattpad,@Fateemah’0_

   🍃🍃🍃🍃🍃

*IDAN DAI BAKI BIYA KUDIN KARATUNKI YANZU BA LALLAI BANE IDAN NA GAMA KI SAMU CMPLT A #100NAIRA BA, ZA KI SAMU NE A #300 DAN HAKA YAR UWA WANNAN BONUS DIN KAR TA WUCE KI.*

*REMAIND 1 FREE..*

🅿️==2️⃣1️⃣↪️2️⃣2️⃣

“Garkuwa suna can, ya ƙi tahowa wai sai ya musu bayani, da wuya yanzu idan su Garkuwa su na numfashi” Liman ya karasa maganarsa yana zama sharaf a ƙasa yana fifita da hularsa irin na fulanin nan wanda ake saƙa shi, cirko-cirko suka tsaya, yayinda Mai Unguwa Ori ya ce

“Mu ba mu kashe Innu Maciji da gangan ba,akasari ba bamu ne muka kashesa ba! Me yasa zasu kashe mana garkuwa!?” cikin fusata wanda yake nuni da damuwa da ɗimauta Baffa ya ce

“Laifin su waye!? Na ce laifin su waye!? Ga irin abunda nake gaya muku amma kun kasa fahimta, ai shikenan sai mu jira har ta Allah ta kasance damu! Ga bala’in kisan macizai! Ga bala’in yaƙi dame zamu ji ne kam! Ya Rabbi gamu gareka! Babu yadda banyi daku karku aikawa da yankin ja’i wasika ba, yanzu mai hakan ta haifar!? Da ace kun saurareni duk ba za a kai ga haka ba, amma mu da shike fulani Allah ya yi mu da taurin kai bamu jin shawari, wlh da kun bi abunda zan shinfiɗa da mun magance matsalarmu da ikon Allah sabida ina da imanin za a…..”

      “Ka rufe mana baki Magaji!!Ya isheka haka!!” Jauro ya katse Baffa, Jauro shine mai magani na yankin kwana

“A kan me zamu bi abunda zaka gindaya!? Kana da halin da zaka taimakemu amma kayi hakan ne? Duk wani yaƙin da zai kunno kai kasa a ranka har da sa hannnunka a ciki! Da ace ka taimaki yankinka har za a yi aike a wani yanki mai suna yankin ja’i ne! Dan haka babu abunda zaka gayawa mutanen yankin nan! Sai ka bar mu mutu! Idan an kashe Garkuwa da yan faɗa biyu sai mu ma mu jira mu ga mai zai yi ajalinmu,Macizai ne ko kuma jama’ar ja’i!” 

      “Haba Jauro miye haka ne kake yi! Bai kamata ka faɗawa Magaji wannan maganar ba! Kwata-kwata ma yanzu ba lokacin musayar yawu bane!” cewar Arɗo, Jauro ya ce

“A kan me ba zan faɗa masa ba! Karya nayi ne! Na ce karya nayi ne!!?” sarki Chubaɗo ya ce

“A gaskiya ban san me zance a wannan lamari ba, amma zan iya bin maganar Jauro! Magana ta domin Allah wannan yanki ya kafu tun kakanni, wanda ya taimaka ya kara tsayawa ma wannan yanki kai ne Magaji! Tun ban san da cewa zan zo na zama sarkin fulanin kwana ba, ni dai roƙonka zanyi da girman Allah ka taimakemu Magaji! Muji da masifa ma daya ta ishemu ba sai an ɗaɗo mana da na yaƙi ba” Sarki Chubaɗo ya faɗa yana haɗa hannunsa alaman roƙo,Baffa ya jinjina kai tare da faɗin

“Naji! Kuma na yarda! Abunda aka binne shekaru ashirin shine zanje haƙosa yau! Shin zaku iya fama da masifu biyar!? E ko a’a? A da masifa daya ce, sannan ku ka kuma janyo mana wata da hannunku, yanzu kuma kun bada dama aje a kara haƙo wata shin zaku iya tayani tareta? Nayi imani a yanzu yankin kwana babu mai iya tayani yaƙi da aljanu babu shi!”

       ” *AZIZA!* Baffa ya ji an raɗa masa a kunne, da sauri ya dago yana waige amma bai ga kowa ba, “Aziza kuma?” Baffa ya tambayi kansa a zuciyarsa yana shirin faɗawa kogin tunani ya tsinkayo muryan Arɗo da Baffa Mandi suna fadin

“Gaskiya ba zamu yarda a haƙo ba,ta bakinka Magaji babu wanda zan iya wannan yaƙin kawai a bar maganar mu sake neman taimako ku kuma ka faɗa mana hanyar da zamu bi” Sarki Chubaɗo ya ce

“E hakane magaji, ka gaya mana wace hanya ce zamu bi?”

     “Inaaaaa! Sam-sam  ba zai yu ace Magaji bane zai bamu mafita sam ban lamunta ba! Ni fa wlh ina zargin Magaji, duk yadda aka yi yaransa ne *MACIZAI!*” Jauro ya faɗa yana huci, saurin dagowa Baffa ya yi yana kallon Jauro, dama ya jima da sanin jauro baya sonsa yana baƙin ciki da shi, ya jima yana masa ƙulli amma kawai bai san yadda zai yi da Baffa bane, shuru Baffa ya yi yana kallon Jauro, yayinda Arɗo ya katse Jauro da fadin

“Wai lafiyarka kuwa Jauro? Ko dai akwai wata a kasa ne tsakaninka da Magaji?” 

“Miye haɗi na da shi?” Jauro ya faɗa yana yiwa Baffa kallon ƙasƙanci,

“Kawai dai gaskiya abunda na sani ne,meyasa ya ƙi aurar dasu yara duk sun gandare a yanki babu mai rab’arsu, shekarunsu goma sha biyar oh Allah ni Jauro, yara na tafiya jiki na lankwasa ace mutane ne! Taya hakan zata kasance!? Kullum fuskarsu a rufe sabida babu ido mai kyau, sannan duk taron da za ayi na magani basu zuwa, dan Allah a cikinku nan ku gaya min suwaye suka yarda da yaran Magaji mutane ne?” nan wa inda Jauro ya haɗa baki dasu suka amsa da basu yarda da Azima da Aziza ba, sannan Jauro ya matso kusa da Baffa wanda ya koma tamƙar wanda aka dasa bishiya ya ce

“Zan fara sakawa yaranka ido fiye da yadda na saka musu a baya, idan har na gano cewa su ɗin ba mutane bane na maka alkawari da hannuna zan kashesu a gabanka!!” rass!rass!rasss! Gaban Baffa ya bada yana kallon Jauro, shi kuwa Jauro yana gama faɗi ya juya zai bar wajan ya tsinkayi muryar Baffa na faɗin

“Allah ya baka sa’a,ni nan zan baka takwabin da zaka kashe yarana a gabana!” ko uhum Jauro bai ce ba ya bar wajan, Baffa Mandi ya ce

“Wai miye haka ne kam?” murmushin takaici Baffa ya yi ya ce

“Ba komai! Ni na jawowa kaina ai!” shi ma ya juya zai bar wajan sai gasu Garkuwa a muraran! Da sauri aka tarbesu kowa yana furta kalman Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Da sauri aka sauko dasu daga dokin yayinda Garkuwa ana sauko da shi yana sumewa, ba shiri aka ce a kai sa wajan Jauro ya duba sa.

@@@@@@@

      A ranar yankin kwana babu wanda ya rintsa, Aziza kuwa ta yi neman Azima ta rasa hakika Aziza idan tace akwai natsuwa da sauran hankali a tare da ita ta yi karya.

       Da washe gari Aziza na idar da sallar asuba ta fice, jejin kwana ta nufa, tana zuwa ta kirawo Inno Fandi, Inno Fandi na zuwa Aziza tasa kuka, girgiza kai Inno Fandi ta yi ta ce

“Aziza ba kuka bane mafita, abu mai mahimmanci shine a yanzu ki maido da natsuwarki, rashin natsuwarki shi ya hanaki ganin Azima, zaki iya ganinta amma sai kin samu natsuwa, sannan zaki iya zuwa dan ki gayawa Baffanku gaskiyar su waye ku, dan ba zaku ci gaba da boyewa ba Azima na kashe mutane,idan ba haka ba a duban da nayi kowa na yankin nan ya kusan mutuwa! Abunda Magaji baya so dole karshe shi zai aikata, wato haƙo baiwarsa da ya binne shekaru ashirin, sannan duk yaƙin da zata kama da wuta kece garkuwar mahaifinki Aziza,ki koma gida Magaji ya ba ki asalin tahirin rayuwarsa na abunda ya faru shekara ashirin amma har sai kin gaya masa gaskiyar su waye ku!” Inno Fandi na gama faɗi ta b’ace, Aziza kuka takeyi kamar ranta zai fita,taya zata fara faɗawa Iyayenta su ba mutane bane Macizai ne? Taya!? Ya Hajja da Baffa zasuji? Idan suka gano cewa duk kisan da akayin nan Azima ta yi su?” kuka sosai ta yi ta godewa Allah fuskarta ya yi jajur idonta ya ƙara komawa fari sol, tashi tayi tana ajiyar zuciya tare da tattaro natsuwarta  kamar yadda Inno Fandi ta gaya mata sai ta samu natsuwa kafin ta iya sanin ina Azima in ba haka ba yau ma kisan da zatayi sai Allah ne yasan adadi, a hankali ta rintse ido tana karanto adduar samun natsuwa ta hanyar tasbihi ga Ubangijin talikai, sai da taji zuciyarta ya samu natsuwa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta rintse ido nan ta ganota kwance a jejin hayi, da sauri ta buɗe idon tana me daukar hanyar jejin hayi ba tare da bata lokaci ba gwanda taje suyi na yau.

      @@@@

Maga Isar da Sakon yankin kwana ne yake karantawa fada sakon yankin ja’i kamar haka

” _DAMA MUNYI MAMAKI ACE KUNA DA MUTUM A YANKINKU KAMAR MAGAJI BAWA AMMA ACE KUN ZO YANKINMU NEMAN TAIMAKO DA INNU MACIJI! HAKIKA MUMA MUN ZAMA SHASHASHU DA MUKA YARDA DA KUDIRINKU! BAYAN MUN SAN DA CEWA KU ƊIN ABOKAN GABANMU NE NA TUN TULI-TULI! A KODAYAUSHE KU YANKIN KWANA KUNA SO KU DINGA NUNAWA KUN FI SAURAN YANKUNA! TO MUNA SO KU SANI KU KARA SANI, LOKACI YA YI DA ZAMU MAIDA YANKIN KWANA BABBAR MAƘABARTA! DAN KUWA MUNYI SAƘO YANKIN JIMO MUN ZUGASU NA JARMAN MACIZAI DA KU KA KASHE! TUN KAFIN KUYI AIKE YANKIN TUDU MUN RIGAKU DAN BA ZAMU YARDA DA KASHE MANA INNU MACIJI DA KU KA YI BA, MUN GAYAWA YANKIN TUDU KUN KASHE MANA INNU MACIJI SANNAN BA MAMAKI KU MUSU AIKE A BAKU IRO MAGANIN MACIZAI TO MUN TOSHE WANNAN HANYAR DAN MUN TONOWA SARKIN TUDU TSOHON RAUNIN DA YANKINKU SUKAYI MASA TA HANYAR KASHE MASA GUDAN JININSA, DAN HAKA KU FARA SHIRYAWA TARBAN YAƘI NA YANKUNA GUDA UKU, YANKIN JA’I: YANKIN JIMO: YANKIN TUDU: SAKO DAGA YANKIN FULANIN JA’I._”

     Maga Isar da sako yana gama karantawa aka hau kallon-kallo, Mai Unguwa Ori ya ce

“Yaƙi da yanki uku a kan yankin daya?”

“Kuma lokaci daya?” cewar Sarki Chubaɗo,Arɗo ya ce

“Mu dai mun san bamu aikata komai ba, mu sa a ranmu wannan wata jarabawa ce daga Allah, kuma yana sane damu, shi zai kawo mana dauki, kar mu ce zamu yi wani shirin yaƙi, mu zubawa sarautar Allah ido” kowa ya amsa da haka ne sannan kowa ya watse cike da alhini.

       🐍🐍🐍🐍🐍

Azima na kwance a kan bishiya rabinta mutum rabinta macijiya, jelarta na lilo a ta saman rashen bishiya fuskarta a haɗe har gefe da gefe ya yi jaa! Idonta kuwa ya kara rikiɗewa ya rine ya koma blue sosai harta fari babu, Aziza tana zuwa jejin hayi jelar Azima ta fara hangowa, saurin karasowa ta yi ta ce

“Azimaa!?” jin muryar Aziza yasa Azima sulalowa tare da komawa mutum, a fusace tayo kan Aziza tana isowa gabanta kafin ta yi mata magana Aziza ta yi saurin dafe goshin Azima nan take taji abu ya shige mata kai sai da ta girgiza.

     Ganin yadda Azima ta tsaya yasa Aziza faɗin

“Azima lokaci ya yi da zaki saduda! Ki dakata haka” murmushi Azima ta yi tana yiwa Aziza kallon baki da hankali

“Ni kike cewa na saduda? To naji zan saduda, amma bayan na kashe Baffa!” ta faɗa tana cije baki, Aziza ta ce

“Wai ke wace irin dabbace Azima?” murmushi Azima ta kuma yi ta ce

“MACIJIYA! ina kina tambaya ne wace irin dabba ce ni? To ni Macijiya ce kamar ke amma bambancin shine ni muguwa ce ke akasin haka! Har yanzu ban huce da abunda kika min ba, ki bar ganin kinsa jikina ya yi sanyi kin kafar min da dafina! Ba shi zai dakatar dani ba, na iya yau ne kawai, amma gobe zan haɗa da kisan da banyi yau ba!” Aziza ta jinjina kai ta ce

“Kin sha fadamin idan na isa na dakatar dake! Ni kuma na sha fada miki cewa bazan bar hakan ta faru ba, shine zan kara nanata miki, ba zan bar hakan ta faru ba! Dan haka muje gida, kafin Hajja ta titsiyemu da tambaya!” a hankali Azima ta juya tana dafe kirjinta dan abunda Aziza ta tura mata ya shigeta sosai, a hankali suka jera suna tafiya dan Azima na da bukatar ta kwanta dan jikinta da ya mutu, sabida abunda Aziza ta tura mata a hankali yake bin jikinta yana kashe mata shi, dan makarin dafi ta tura mata.

       Da haka suka iso kofar gida Aziza ce ta fara shigewa da sallama ta samu Baffa da Hajja suna zaune yana labarta mata wasikar yankin ja’i wanda kaff abunda Baffa ya faɗi a kunnen Azima, a tana rarrafawa da kyar amma wani dadi ne ya mamaye zuciyarta nan ta hau murmushi tare da fadin

“Yankuna uku zasu yaƙe yankin kwana? Wayyooo Dadi!bari na ɗan daga kafa dan ganin yadda za a shafe yankin kwana idan ya so na kashe Magaji Bawa daga baya!” ta faɗa gami da sallama ta shiga gidan, Hajja ta ce

“Azima ina kika je ne? Ni anya jiya na ganki kuwa? Yana ganki haka kamar wacce bata da lafiya?” 

“Kin ganni mana Hajja! Ko dai wannan bala’in ne yasa kanku ke da Baffa ya kama da wuta!? Sannan da kika ganni haka ba wata matsala bace babba kaina ke ciwo, da nayi bacci na farka zan dawo dai-dai” Azima ta fada tana kallon Baffa, da ido Baffa yake bin Azima yayinda take yi masa wani irin kallo, Hajja ta ce

“Allah ya kyauta, jeki kwanta” Hajja ta shige bukka, Azima ta juya kenan zata shiga bukka idon Baffa na kanta dan ya kasa kauda ido a kanta, wuyarta taji ya mata ƙaiƙaiyi tasa hannu ta sosa, tana sosawa sai ga sab’ar maciji ya fadi carab a idon Baffa, wani wawan firgita Baffa ya yi,ya tashi jikinsa na rawa ya karasa ya dauki sab’ar yana kalla,saurin girgiza kai ya yi yana fadin 

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!! Me hakan ke nufi?” jikin Baffa ya yi mugun sanyi dan ya tsorata ba kadan ba, bukkarsa ya shige yana jeka ka dawo dauke da fatar a hannunsa, cikin rawar murya ya ce

“me ya kamata nayi? Dole na haɗa maganin ganowa idanuna, amma kafin na samu furen surfa sai naje jejin gangare, kuma kafin na dawo sai na samu kwana biyu sabida dogon tafiya ne ban ci ta zama ba, In sha Allahu zan tafi gobe” yana gami fadi ya fito ya shiga bukkar Hajja ya gaya mata gobe da safe zai tafi jejin gangare Hajja ta ce

“Me zaka je yi?”

“Akwai maganin da nake son haɗawa ne, kuma furen da ganyen dole sai naje jejin gangare”

“To Baffa yan biyu Allah ya kaimu lafiya” Baffa ya amsa da amin ya fice, bai zarce ko ina ba sai wajan Ardo bai boye masa komai ba kasancewarsa mahaifinsa ya gaya masa komai, sosai hankalin Arɗo ya tashi ya kallesa ya ce

“Magaji bana so ka gaya ma kowa wannan batun ka ji ko? Har sai ka tabbatar” Baffa ya gya ɗa kai cike da damuwa, nan suka ci gaba da tattaunawa a kan lamarin.

    🐍🍃🐍🍃🐍🍃

COMMENTS AN SHARE

BY MOMYN AHLAN

[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

    💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨

    (🐍 _Macizai ne_🐍)

    MALLAKAR.

*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din

0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.

Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*

1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._

2- _GUDU A JEJI._

3- _SHUHADA._

4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._

5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._

6- _COLONEL UBAIDULLAH._

7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._

8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._

9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._

10- _DA NA SANI NA._

  11- _BADAWIYYAH_

12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_

Now

13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_

_Follow me on wattpad,@Fateemah’0_

   🍃🍃🍃🍃🍃

*YAR UWA ZO BIYA KUDIN KARATUNKI DAN JIN YADDA ZATA KAYA A CIKIN BOOK DIN AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE, BIYA DARINKI KACAL YANZU,IDAN KUMA NA KAMMALA CMPLT DARI UKU ZAKI SAMESA.*

*LAST FREE..*

🅿️==2️⃣3️⃣↪️2️⃣4️⃣

Da washe gari asubanci Baffa ya yi ya bar yankin kwana dan bai ga ta zama ba, ko da Aziza ta farka ita ce kawai ta tambayi ina Baffa yake nan Hajja ke gaya mata ya tafi jejin gangare dan samo wasu ganyen magani, Aziza ta ce

“Allah ya dawo min da Baffana lafiya” Hajja ta amsa da amin.

     Ita kuwa Azima tunda ta fara bacci ba ita da farkawa ba sai gefen sallar la’asar, ko da ta farka Aziza na shirin ɗora mata hannu a goshi ta yi saurin rike hannun Aziza ta ce

“Ba bukata Aziza, yau ina cikin farin ciki babu wanda zan kashe amma za a mutu dayawa gobe! A’a ba wai ina nufin ta hannuna ba fa,dan naga kina min wani kallo! Wallahi babu wanda zan kashe! Amma gobe akwai zubda jini a yankin kwana!” tana gama fadi ta tashi ta fito ta samu Hajja a tsakar gida, Hajja ta ce

“Azima wannan baccin naki ya yi yawa, haba dan Allah mutum ya ta faman bacci ba sallah ba salati ko kina fashin sallah ne?”

Yatsine fuska Azima ta yi kafin ta ce

“Ni fa Hajja wannan fashin sallan da kika fadi me ma yake da suna? Al’ada ko? To ni banayi! Kuma ban taba yi ba! Sallah gabadayanta ne bana yi,kuma ma Hajja sadda Aziza ke zuwa islamiyyar Malam Saini ni kin taba gani naje ne? Har Aziza ta yi sauko ni ban taba zuwa Islamiyyar Malam Saini ba,ko kuma kin taba gani da watan ramadan ina azumi? Ki kyaleni da maganar wani abu wai shi sallah!” tana gama fadi ta fice, Aziza na tsaye a bukka tana kallon Azima, bayan Azima ta fita Hajja ta kalli Aziza hankali tashe ta ce

“Aziza meke damun yar uwarki!?” murmushin tausayin Hajja Aziza ta yi ta matso kusa da Hajja ta kama hannunta ta ce

“Kun kusa ku sani Hajja nan ba da jimawa ba, dan bazan iya jure ganin hawayenki na zuba a kanmu ba, zan gaya miki gaskiya da zaran Baffa ya dawo ko da kuwa za a kashemu!” 

    Hajja ta bude baki za ta yi magana da sauri Aziza ta ce

“Dan Allah Hajja karki ce komai, Azima bata sallah bata salati bata Azumi duk wani aikin ibada bata yi,na gaji da miki karya Hajja, bazan iya jure miki karya ba!” tana gama fadi ta fice da gudu da kuka.

Aka bar Hajja da kakkarwar jiki.

        @@@@@

Da yamma sai ga wasika daga yankuna uku izuwa yankin kwana, zasu kawo musu farmaki gobe da safe, hakika wannan sako ya hautsine hankalin jama’ar kwana inda mata da dama har ma da mazan wasu suka fara kuka, sarki Chubaɗo da mai unguwa ori suka ce ga shi Magaji baya nan, kuma babu halin yi masa saƙo har sai ya dawo, saukinta ma Garkuwa ya ɗan samu lafiya, kafin kace me Sarki Chubaɗo ya bada umarnin ayi shela a yankin kwana gabadayanta za a kawo farmakin yaƙi gobe kuma yankuna uku,dan haka kowa ya kasance cikin shiri amma bana tarban yaƙi ba.

@@@@@@

       Hajja da Aziza sun kasa zaune sun kasa tsaye sabida tashin hankali sai jeka ka dawo suke yi a tsakar gida amma Azima na zaune hankali kwance tana fizgar dogon gashinta, Aziza ce ta kallenta ta ga babu alamun damuwa a tattare da ita,cikin haushi da tsanar Azima da ya fara ɗarsuwa a zuciyarta ta ce

“Wai ke Azima wace irin dabba ce ke ana maganar kawo farmakin yaƙi amma kina zaune kina tsifar kai?”

    “Macijiya!” Azima ta faɗa ba tare da ta ɗago ta kalli Aziza ba, Hajja ta juyo a firgice ta ce

“Ma mai kika ce Azima! ?” tana shirin kara nanatawa Aziza tayi saurin faɗin

“Mahaukaciya kawai!”

“Ga ki kuwa babbar mahaukaciya!” Azima ta faɗa tana dagowa a fusace.

    “Dan Allah fadan ya isa haka!” Hajja ta katsesu, 

“Kuyi ta addua kawai Allah ya bamu mafita yafi wannan fadar naku” ko uhum basu kuma cewa ba.

      🍃🍃🍃🍃

      

Da washe gari kamar yadda sako ya iskesu haka kuwa ta kasance inda yankin ja’i da yankin jimo da yankin tudu sukayi cincirindo sun zo yaƙar yankin kwana, amma abun mamaki babu wani daga yankin kwana da ya dauki makami, abun ya basu mamaki, Arɗo shine wanda ya fito ya fara magana kasancewarsa Babba, tsohon bafulatani mai dattako

“Mu ba zamuyi yaƙi daku ba, idan har kuna so duk ku sa takwabi ku kashemu! Har ga Allah munyi imani wannan ita ce kaddararmu! Bamu kashe Innu Maciji ba, a ranar da aka kashe Innu muma munyi rashin mutane a yankin nan har mutum sha huɗu, haka ma jarman macizai, sannan sarkin fulanin tudu bamu aikata muku komai ba kawai neman fitina kukeyi,idan kuma yaronka da aka kashe a yankin nan ne laifi ya aikata aka masa hukunci, na rantse da wanda ya busamin numfashi idan har aka samu ɗan wani yankin kwana da laifi makamanciyar wanda ɗanka yazo yankin nan ya aikata wlh mun yarje muku ku fille kansa ku kawo mana kamar yadda mukayi, ba a barin laifi a ɗoran kasa, dan ba a san mai zai kuma aikatawa a gaba ba, mu sabida muna bin al’ada da ibada shiyasa yankinmu ta yi baƙin jini a wajan sauran yankuna, idan har maganar da nayi baku gamsu ba kuna iya shafemu a doron kasa ko kwayi farin ciki” Arɗo na gama fadi jama’ar kwana suka miƙa wuya,ganin haka yasa yankin jimo jikinsu yayi sanyi suka ce ba zasuyi yaƙi da yankin kwana ba,nan take suka juya, yankin tudu da yankin ja’i kuwa sunce suna nan, sai sun shafe yankin kwana.

      @@@@

Gudu Baffa ke yi a dokinsa dan haka yake ji a jikinsa mahaifarsa babu lafiya.

      A kwana kuwa ganin yadda yankin ja’i suka fara zubar da yara da manya ta hanyar saresu da takwabi yasa garkuwan fulanin kwana cewa Sarki Chubado da Ardo

“Ranka ya dade, hakika ba zamu tsaya a shafemu ba tare da mun sa hannu ba dan bamu aikata laifi ba, burin yankin ja’i shine su ga sun shafe yankin kwana, dan haka kowa ya dibo makamai mu gwabza tunda haka suke so” mai Unguwa Ori ya ce

“Tabbas hakane” nan garkuwa ya bada umarnin a dauka takwabi a fara maidawa yanki biyu martani.

    Duk wannan tarzoma da akeyi Azima na saman bishiya tana kallo tana dariya, Aziza ganin kisan da ake yiwa mutanen yankinta ya yi yawa ne ya sa ta fadi a ranta “inaaa! Burin Baffa shine ya ga ya mutu ya bar yankinsa lafiya, dan haka dole ne na dakatar da yaƙin nan ta ko wani hanya in ba haka ba, tabbas yau babu sauro da zai rage a yankin nan” ta kalli Hajja dake tsaye tana kalman shahada dan yawancin mutane sun sadakar da zasu rayu ta ce

“Hajja ina jin fitsari zanje gida na dawo” ta karasa fadi tare da juyawa,saurin kamo hannunta Hajja ta yi ta ce

“Aziza bakki hankali ashe ban sani ba?kina ganin yadda ake zubar da jini tamƙar ana ɗibo ruwa a rafin jimulo ne ake watsawa kice zaki koma gida kiyi fitsari? Idan kika bincika wasu a nan har da kashi sukayi a jikinsu,dan haka Aziza yi fitsarinki kawai a jikinki, gwanda mu tsaya ta nan idan har Allah yasa aka gama da sauran kafin a iso kanmu,idan kuma Allah yasa Baffanku ya dawo a kan lokaci to, dan shiyasa nace miki mu tsaya a nan sabida ga hanyar da zai fito nan” Hajja ta faɗa tana kara riƙe hannun Aziza, girgiza kai Hajja ta yi ta ce

“Hajja to ni kin riƙeni babu fa Azima a nan” da sauri Hajja ta ce

“Na shiga uku! Azimaaaa!?”

“Kwantar da hankalinki Hajja bari na je nayi fitsari sai na dubota mu dawo tare”

“To dan Allah Aziza ki kula,ki min alkawari zaki dawo lafiya?”

“Na miki alkawari Hajjata zan dawo lafiya” sai da Aziza ta faɗi haka kafin Hajja ta saketa,da gudu Aziza tayi hanyar gida dan ta shirya ta dawo ta tare yaƙin.

          @@@@

       Haka Baffa ya shigo yankinsa ya samu gagarumin yaƙi, amma da shike baya da lokacin tsayawa  gida ya wuce kai tsaye ya haɗa maganin furen surfa, sannan yaje ya kirawo Hajja a inda ya ganta sadda ya shigo, amma ita bata gansa ba, yake tambayarta ina Aziza da Azima? Hajja ta ce

“Aziza tace min zata zo gida ba mamaki tana kewaye cikinta ya tsure sabida wannan tashin hankalin,Azima kuma ban ganta ba dan Aziza tace min idan zata dawo zata dubota su sameni a can”

Baffa ya ce 

“Boye a can,ni kuma zan boye a nan karki kuskura kiyi magana kinji ko?” Hajja tana shirin tambayar Baffa me yake son yi ya ce

“Jumala karki tambayeni komai! Zaki ganewa idanunki!ke dai kiyi abunda na sakaki! Yaƙi kuma inada yaƙini a kan garkuwa zai tarewa yankin kwana tunda yasa hannu kafin na gama wannan binciken da zanyi, dan haka karki tambayi komai kawai je ki boye,kuma karki kuskure ki fito” Hajja ta amsa da to, maganin da Baffa ya haɗa ya kewaye kofar shigowa gida da shi, sannan ya zuba wani ya koma ya maqale, Azima dake kwance a jikin bishiya haka kawai taji kamar an tsikareta saurin saukowa tayi a saman bishiyar idonta ya kara canza kala nan ta nufa hanyar gida ba tare da tasan dalilin hakan ba wanda take ji kamar an saka mata kuran karfe ne yake janta.

      @@@

     Aziza ce ta fito daga kewaye idonta jajur alama ce na taci kuka, tana fitowa ta shige bukkarsu, Baffa dake maqale ta zanar kofar waje ya hangi Azima na tahowa tana layi, tana zuwa zata shiga gidan da aka yi wani sama da ita aka bugata da kasa, yayinda taji ko wani fata ta jikinta na mata zafi, ihu ta saka tana rirriƙe jikinta, ta kafarta ta fara rikidewa, wani wawan zare ido Baffa ya yi,yayinda yayi sumar wucin gadi, wannan shi ake kira tashin hankalin da ba a sa masa rana.

     Aziza kuwa shiryawa tayi dan taimakawa yankinta ta zo fitowa kenan har ta sa kafa akayi sama da ita ma, ihu ta saka ta fadi kasa wanwar, girgiza kai ta hau yi jin yadda jikinta ya amsa tana shirin rikidewa ta koma macijiya,cikin dimauta take furta “furen surfa na macizai? Wa ya kawo ya zuba a kofar gida? Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! a’a a’a a’a!!”  bata bari hakan ya faru ba ta shige bukka da gudu, Hajja dake kallonta ta zaro ido waje,to meke faruwa da yarta ga Baffansu yace karta fito? Anya zata iya kuwa ba zata fita ta je ta duba me ya samu Aziza ba? Hakuri dai ta yi amma hankalinta na kan Aziza, Aziza kuwa tana shiga bukka ta hau kwalawa Inno Fandi kira yayinda fatar jikinta ya koma fari sol, daga kugunta abunda yayi ƙasa ta koma macijiya🐍, cikin matsanacin kuka Aziza ke kiran Inno Fandi har ta bayyana, ta ce

“Na shiga ukuna Inno Fandi furen surfa na macizai wa ya zuba?” 

     Inno fandi ta ce

“Yanzu za a fara Aziza! Ba kowa bane ya haɗa maganin furen surfa illa Magaji, wanda a halin yanzu Azima tana waje tana rikidewa,ke ma haka gaki nan, a yanzu *BAFFANKU YA GANE CEWA AZIMA MACIJIYA CE!* kece kawai bai gani ba, dan haka ki gaya masa gaskiya dan a san yadda za ayi a yi maganin abun”

“To wani irin maganin abun Inno Fandi? Karshe dai nasan kashemu Baffa zaiyi da hannunsa” Inno Fandi ta ce

“Bana da ikon gaya muku komai, idan har na gaya muku zan iya mutuwa, Magaji shine zai gaya muku, yanzu dai me kike da bukata na miki?”

“Ina so naje na tsaida yaƙin da akeyi ne kafin na dawo ayi ta gida, ki taimaka min na fita a gidan nan” Inno fandi ta ce

“An gama” sannan ta dauki Aziza suka b’ace dan zuwa tsaida yaƙi.

      A waje kuwa fadin halin da Baffa yake ciki bata lokaci ne bayan ya farfaɗo daga suman da yayi, a hankali yake tunkarar Azima dake birgima tana ihu jikinta na kan rikiɗewa, rasa abun yi Baffa yayi kawai yasa kuka ya duƙa a gaban Azima, ganin haka yasa Azima b’acewa b’att! A wajan Baffa ya yi zaman yan bori.

       @@@@

A wajan gari kuwa sadda Inno Fandi ta fice da Aziza nan Aziza ta b’ace tana kwasar mutanen yankin ja’i tana watsar dasu, mutum na tsaye sai dai yaji an dagasa an wurgasa, idan ta tashi kwasa kuwa sai ta kwasa kusan mutane goma da jelarta ta watsar dasu, mutanen yankin tudu jin sun daina yaƙi da mutane sun koma yi da aljanu ya sakasu fara arcewa suna fadin kaff! yankin kwana ba mutane bane, harkazalika yankin ja’i da suka fara jin jiki su da kansu suka tsare, su Garkuwa gani kawai suka kafin kiftawar ido da bismillah duk yawan rundunar da suka zo sun watse, hamdala suka fara yi suna godiya ga Allah, amma tabbas an kashe musu mutane.

     A hankali Aziza ta bayyana ta zama mutum tana ganin mutane kwance a cikin jini yara da manya mata da maza, hawaye ta share gami da kama hanyar gida,tana cikin tafiya Inno Fandi ta kira sunanta “AZIIIZAAA!” cak Aziza ta tsaya, sannan Inno Fandi ta ce

“Idan kinje gida ki tambayi Baffanku Magaji Bawa su waye *BANJU DA BAHULA!*” Inno Fandi tana faɗin haka bata kuma cewa komai ba, da gudu Aziza ta yi hanyar gida,ko da ta isa har yanzu Baffa na zube a kofar gida ya kasa tashi, da sauri Aziza ta dagasa tana kiran sunansa “Baffa! Baffa! Baffa!” a tsorace dan tayi zaton Azima ta yi masa wani abun ne dan zata aika, da kyar Aziza ta kama Baffa ta zo shiga gidan ta ga har yanzu da sauran furen surfa a kofar gidan, ga shi babu abunda zata iya yiwa furen surfan, abu daya zata iya yi shine ta nemi taimakon Inno Fandi, tun kafin ta kirata ma ta bayyana ta kwashe sauran na bakin kofar kafin Aziza ta ja Baffa suka shiga gida, suna shigowa Hajja wacce har yanzu tana maqale ta kasa fitowa bisa da cewa Baffan yan biyu bai ce ta fito ba shiyasa ta ci gaba da maqalewa, ganin Aziza ta shigo da Baffa a hannu yasa Hajja fitowa a kiɗime tana fadin “Subhnallahi! Aziza me ya faru da Baffanku?” 

Aziza bata tsaya ba wa Hajja  amsa ba illa randar kasa da ta nufa ta dibo ruwa mai sanyi ta watsawa Baffa nan ya sauke ajiyar zuciya yana ji kamar numfashinsa zai dauke, ruwan Aziza ta ba shi da kyar ya karba ya sha sannan ya dafe kansa, sannu suke jera masa ba tsayawa, sai zuwa can Hajja ta ce

“Wai ni kam Aziza kamar dazu na ga shigarki bukka,amma tayaya kika fita a gidan ban gani ba? Ko b’acewa kika yi?” Hajja ta tambayi Aziza ne kawai amma ga mamakinta sai ji ta yi Aziza ta ce “e Hajja b’acewa nayi, sabida bazan iya bi ta bakin kofa ba, Baffa ya zuba furen surfa!” zaro ido Hajja tayi bama Hajja ba harta Baffa da bai gama dawowa dai-dai ba ya ɗaga kai yana kallon Aziza wacce ta miƙe tsaye tana ja da baya tana girgiza kai tare da hawaye mai ban tausayi tana fadin

“Gwanda ayita ta kare, yau zaku san wani irin yara ku ka haifa, Hajja Baffa kuyi hakuri hakika baku haifi mutane ba, Baffa na san da hannunka zaka kashemu bayan kasan mu ɗin su waye! Na san ka gama gane Azima nice kawai baka gane ba,bazan iya munafurtanka ba Baffa!” da sauri Hajja ta miƙe tana fadin

“Me kika faɗi ne haka Aziza!”

    “KARKI MATSO INDA NAKE!!” Aziza ta fada da karfi, Hajja ta ce

“Sabida me Aziza? Nifa mahaifiyarki ce!” tana fada tana kara tunkaro Aziza dake matsawa baya, rintse ido Aziza ta yi ta buɗe ta haɗe rai cikin daga murya ta ce

” *SABIDA NI MACIJIYA CE! AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE!*” Aziza ta faɗi tare da komawa Macijiya! Wani mahaukacin kara Hajja ta saka tare da yin baya-baya ta faɗi timmm! A kasa, ganin haka yasa Aziza komawa mutum ta yi kan Hajja tana jijjigata tare da ambatar sunanta,amma ina Hajja bata motsi numfashi ya tsaya cak, cikin kuka Aziza ta ce

“Hajja ba dai hadiye zuciya kikayi ba!? Na shiga ukuna Baffa!!” Aziza ta fada tare da juyowa wajan Baffa nan ta ga ashe shima ya suma! Randar ruwan kasar gabadaya Aziza ta dauka ta juye a kan iyayenta, da kyar suka saki ajiyar zuciya, suna dawowa Aziza ta ce

“Baffa waye su *BANJU DA BAHULA!!!?*” wani zabura Baffa ya yi yana kallon Aziza, da sauri ya miƙe tsaye ya ce

“Dole kafin nasan abunda ke yawo a jikinku saina haƙo abunda bana son haƙowa, Aziza na fahimci ke ba kamar Azima ba ce, da ace ke kamar Azima ce yadda muka suma da kin kashemu! Na sha zargin Azima na son kasheni amma naki ba wa shaidan damar da zai saka min waswasi a zuciyata a kan ‘yar da na haifa ta cikina! Dan haka zan gaya miki waye Banju da Bahula da abunda ya shiga tsakanina dasu, amma kafin nan zo muje jejin firi”

Saurin riƙe hannun Aziza Hajja tayi idonta jajur ta ce

“Ya isa haka Baffan yan biyu! Ka sha saka rayuwarka a hatsari ga shi yanzu ta shafi yarana!” Hajja ta fashe da wani matsinacin kuka tana zuba guiwowinta a kasa, da sauri Aziza ta kama hannunta, ko kaɗan Hajja bata ji tsoron Aziza ba, cikin kuka ta ce

“Macizai! Macizai! Macizai! Ni Jamila na haifi Macizai! Inaaa ba zai yu ba ni kawai a dawo min da yarana!” Hajja ta kuma sa kuka bai tab’a zuciyar mai sauraro, rungumeta Aziza ta yi cikin tausayawa domin kuwa Hajja abun tausayi ce ita da Baffa, fita Baffa ya yi yaje ya kirawo Arɗo da Yawuro, da Inna Wuro, da kuma tsohon sarkin kwana wato Baffa Mandi, bai boye musu komai ba ya gaya musu komai, hakika hantar cikinsu ya kaɗa fiye da tsammani, Arɗo ya ce

“Lallai kuwa idan har Banju ne ya dawo daukar Fansa! Kisa bai ma yi komai ba kenan! Ashe kuwa idan ba a dakatar da Banju ba idan har shine sunanmu toka” Baffa ya ce

“Bazan bari hakan ta faru ba, yanzu daga nan jejin firi zamuje nida Aziza, zanje na haƙo kayana dan nasan taya zan taimaki yankina da kuma yarana” Baffa Mandi ya ce

“Magaji!? Hakowa fa kace? Aljanu da mayu ayi yaya dasu?” Arɗo yace

“Buhun bala’in Banju gwanda haƙo aljanu da mayun da Magaji ya kulle, dan ba karamin babban shaidani bane Banju! Ko ka manta b’arnan da Banju ya yi kafin Magaji ya kashesa?” 

“Taya kuwa zan manta Arɗo? Bayan dukka ahalina Banju ne ya kashesu!” 

Baffa wanda ke goge gumi ya ce

“Aziza tana tare dani, dan haka yanzu a gayawa su sarki Chubaɗo halin da ake ciki, sannan a cewa yara da manya kar wanda ya fito ko da kofar gida ne, domin kasan aljanun da aka ɗaure duk wanda ya samu damar guduwa zai fito ne da haushi da b’acin rai na dauresa da akayi na tsawon shekaru, dan haka duk wa inda suka samu zasu bugesu ne, Yawuro, Inna Wuro ku kula da Jumala, Aziza muje” Aziza ta amsa da to Baffa a sanyaye abun tausayi, zasu fita Hajja ta kuma sa kuka tana salati dan ita kadai tasan abunda yake damunta, su Yawuro da Inna Wuro suna dannarta, yayinda Arɗo yace bari yaje wajan Chubaɗo su zanta a kan lamarin.

       🐍🐍🐍🐍

B’acewar Azima jejin hayi ta nufa tana kan ihu fatar jikinta na mata zafi sosai,zubewa tayi a kasa tare da furta “KARYANKA! NACE KAYI KARYA MAGAJI! FANSA NE DAI SAI NA DAUKA! AMMA NA RASA MEYASA KAKE GALABA A KAINA TUN TSAWON SHEKARA ASHRIN! YANZU MA SO KAKEYI KA SAKE KASHENI! INA HAKAN BA ZAI YU BA, DOLE NA MAKA MUGUN TABO! TA HANYAR CI GABA DA RAYUWA A GANGAR JIKIN ‘YARKA AZIMAAA!!” 

       Wannan murya na gama fitowa ta b’alli gashin kanta tasa a baki nan taji sauƙin raɗaɗin, sannan ba tare da bata lokaci ko dogon tunani ba Azima ta dauki hanyar barin Al’karyan yankin kwana dan ta shiga cikin gari ta cika burinta na tarwatsa jama’a da hanasu kwanciyar hankali.

      🍃🍃🍃🍃

Baffa da Aziza suna isa jejin firi ba bata lokaci Baffa ya fara haƙo abunda ya binne, yana gaff da gama cirowa ya kalli Aziza ya ce

“Kin shirya?” Aziza ta gya ɗa kai gami da cewa “e Baffa a shirya nake”

“Fara” Baffa ya faɗa,yayinda Aziza ta daga hannu sama ta fara haɗa wani baƙin guguwa mai cike da rami dan tare mayu da aljanu ya kasance ko da zasu gudu kaɗan ne, da karfi Baffa ya fizgi wani abu kamar irin akwatin karfe na tun tsawon wasu shekaru, yana fizgowa take wani mahaukacin guɗa ya tashi, wanda ba iyakar jejin firi ba dukkan jeji sai da ya amsa tare da dukkan mutanen yankin kwana babu wanda bai ji wannan gudar ba, Aziza na tsaye sai haɗa zufa takeyi yayinda take riƙe da wannan baƙin guguwar wanda ta riƙe aljanu da mayu, ganin halin da take ciki da sauri Baffa ya buɗe akwatin wanda da ka gani kasan ya daɗe ya dauki guru da layarsa ya maida (Allahu Akbar Baffa an tuno baya) duk wani abu da Baffa ke amfani da shi sai da ya dauka,na ɗaurawa ya ɗaura na sakawa ya saka, na mannawa ya manna, ya fiddo wani tulu mai murfi, yana fiddowa ya sake kama wasu aljanu da mayun ya rufe yayinda wasu suka gudu, Aziza na sakewa ta zube sumammiya, Baffa bai damu da sumar da tayi ba dan na hucin gadi ne, ta ma yi namajin kokari, dan ko shi iyakar abunda zaiyi kenan,kuma dabadin ita ba da yana haƙo abun nan ba tare da an rikesu ba bala’in da zata kunno yankin kwana sai Allah.

       Baffa na ciro kayansa ya haɗa wasu taurari guda biyu wanda suke kamar dutse mulmulen laka, sunan Azima da Aziza ya rubuta a kai, nan wani haske ya bayyana, na Azima ya fara gani, nan ya hangi Banju a gangar jikinta, Azima a sume take, wasu hawaye masu zafi ne suka wanke wa Baffa fuska, sannan ya duba taurarin jikin Aziza, nan ya ga Bahula ce ke rayuwa a jikinta, sannan ita an maidata Macijiya ba wani ke rayuwa a jikinta kamar Azima ba, cikin ruɗu da tashin hankali Baffa ya watsawa Aziza wani farin kasa nan take ta sauke ajiyar zuciya ta farka, ya ce

“Aziza muje gida” girgiza kai Aziza ta yi ta ce

“Baffa ba zan je gida ba har sai ka gaya min waye Banju da Bahula” Baffa ya ce

“Yanzu kuwa zan gaya miki Aziza, yau zan baki labari”

      🍃🍃🐍🍃🐍

*Tabb cakwakiya! Shin ya zata kaya ne? Idan Baffa ya ba wa Aziza labari taya za a rabasu da wannan bala’in? Ga shi Azima ta bar yankin kwana ta do shi hanyar shiga gari,Dukkan wasu manya tambayoyi yana sauran shafuka da suka rage a gaba, naira darinki ya isheki! Idan kuma kika jira cmplt dari uku.

Karku bari ayi babu ku.*

  COMMENTS AND SHARE

BY MOMYN AHLAN

[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

    💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨

    (🐍 _Macizai ne_🐍)

    MALLAKAR.

*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din

0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.

Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*

1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._

2- _GUDU A JEJI._

3- _SHUHADA._

4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._

5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._

6- _COLONEL UBAIDULLAH._

7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._

8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._

9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._

10- _DA NA SANI NA._

  11- _BADAWIYYAH_

12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_

Now

13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_

_Follow me on wattpad,@Fateemah’0_

   🍃🍃🍃🍃🍃

GODIYA TA MUSAMMAN GA DAUKACIN YAN PAID GRP DIN AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE, HAKIKA SHARHINKU YANA KARA MIN ƘARSASHI, KAUNA CE TASA KUKA KASANCE A PAID GRP DINA, DAN HAKA NIMA INA KAUNARKU🥰, KU MORE KUJI DADINKU.

*PAID.*

🅿️==2️⃣5️⃣↪️2️⃣6️⃣

Gyara zama Aziza ta yi ta naɗe kafarta sannan ta ce

“Ina sauraronka Baffana!” miƙewa tsaye Baffa ya yi ya juya baya gami da maida hannunwansa baya ya yi tsayuwar da jaruman maza ke yi wanda suka yarda da kansu ya koma ainahin asalin MAGAJI BAWANSA sannan ya ce

“Aziza! a da an yi wani mutum jarumi! sadauki! jajircacce! tsayayye! marar tsoro da fargaba!, da tare dukkan wani faɗa! kin san ana cewa ba a faɗa da aljani ko? to wannan mutumin yana yi! wanda a yanzu shike tsaye a gabanki! Wanda wannan mutumin mahaifi ne gareki da kuma ‘yar uwarki Azima, kamar yadda kika sani Ardo mahaifina ne wato kakanku! Inna wuro mahaifiyata ce! wasu daga mutanen yankuna suna fadin cewa nayo gadon Arɗo a lokacin yana saurayi, amma kin san me Arɗo ya ce?” Aziza da ta ƙurawa Baffanta ido tana yi masa kallo kamar bata taba ganinsa ba dan gani ta yi gabadaya ya canza mata ya tashi daga Baffanta da ta sani ya koma wani mutum daban ta girgiza kai alamun a’a, Baffa ya ɗora da cewa

“Arɗo cewa ya yi ni daya ne tak a wannan yankin dama sauran yankuna babu na biyuna! domin kuwa baiwata daga Allah ne, tun ina yaro nake mu’alama da aljanu sannan nake taimako! a taimakon da nakeyi ba iyakar mutane ba har ma da aljanun,a lokacin na shiga yankuna da dama dan kai wa wasu dauki! Yankin kwana ta shahara ta yi suna ta sanadina, tun a lokacin nake cin karo da abokan gaba da maƙiya wa inda basu sona sabida farin jinin da nayi a wajan yan mata a lokacin babu wani kyakkyawan jarumi ka ma na, shiyasa na kara yin baƙin jini, mahaifiyarku kamar yadda ku ka sani ‘ya ce ga Ƙanwar Arɗo wanda suke uwa daya uba daya, Jumala yarinya ce mai kunya da natsuwa da hankali da sanin ya kamata, tun ranar da naje gidan Inna Kab’o na ganta naji na kamu da sonta amma ban san taya zan bayyana mata ba, Jumala ta ta so ne a babban gida wanda suke da tarin iyalai masu yawa, wanda a yanzu Jumala ita daya ce tal ta rage a danginta duk Banju ya kashesu!”

     Kasa hakuri Aziza ta yi ta ce

“Baffa miye dalilin Banju na kashe mutane? Sannan naji Baffa Mandi ma ya ce shi ya kashe   masa ahalinsa! Sannan wanene shi Bahula din?”

“Bahula mace ce ba namiji bane Aziza! Saurin me kikayi Aziza? Zaki san komai a yau! duk wani jeji babu wanda bana shigansa da ikon Allah sannan na fito lafiya ba tare da wani abu ya sameni ba, domin nayi imani da Allah da ANNABI MANZON ALLAH S,A,W, nayi karatuna a wajan wani Babban malami a nan yankin kwana mai suna MALAM SHAINI wanda shima ahalin yanzu baya raye Banju ya kashesa! shi da iyalansa!”

      “Kenan Baffa yawancin mutane Banju ya kashesu?”

     Juyowa Baffa ya yi ya kalli Aziza sannan ya yi wani murmushi ya ce

“Kisan da Banju ya yi ba zai kirgu ba, dan zan iya ce miki a cikin kashi dari na mutanen yankin kwana Banju ya kashe kashi arba’in! Banju mugu ne, na kasance ina shiga jeji dan nemo ganyayyaki na haɗa magani, akwai wani jeji mai sunan jejin ‘Bingel, hakika har kwanan gobe ban kara shiga jejin ‘bingel ba”

     “Kenan Baffa akwai jeji mai suna jejin ‘bingel?”

    Baffa ya gyaɗa kai

“E Aziza, akwai a wannan jejin ne na tafka babban kuskuren da ban taba yi ba a rayuwata, ko kuma nace ya haɗu min har da tsautsayi! dan a wannan jejin ne tsautsayi ta haɗani da Banju, a da ban san wani abu mai suna tsoro ba a rayuwata! Banju shine mutum na farko da ya fara shuka min tsoro a zuciyata, ba dan komai ba sai dan ikirarin da ya yi a kaina da mutanen yankina a sadda zan kashesa! ba dan komai na tsorata da Banju ba illa ta’adi da b’arnan da ya yi a yankin nan”

        “Ranar wata laraba ba zan taba mantawa ba naje jejin ‘bingel dan nemo wani ganyen magani da zan haɗawa Inna Kab’o mahaifiya ga Jumala Hajjarku ciwon kafa ya sakata a gaba, a lokacin kuma an gano cewa ina son Jumala ita ma kuma tana sona har an fara maganar haɗamu aure, na shiga jejin ‘bingel har na tsinƙe ganyayyakina zan fita, da shike duk inda zanje ina tare da addana kin san fulani da takwabinsu suke yawo ni kuwa harda kifiya nake yawo, kifiyata kuma tana da guba a jiki, sabida shige-shigen da nake yi na saka rayuwata a hatsari dole na dinga tafiya da kariya duk da nasan ni Allah shike kareni, kifiyata ba mutum ba duk wani abu da zan harba da shi sai ya mutu walau na harbi aljanu ko mayu ko wani dabba ko ma me da kika sani, na juyo zan bar jejin bingel ban ankara ba na hangi wani zureren 🐍 jelar maciji mai cike da ban tsoro, dama kafin nan a kwanaki muna samun koke-koke daga maƙotan yankuna a kan saren maciji wanda nike zuwa dubawa,saren macijin kuma ya fita daban da saren macizan da na sani, to ganin wannan macijin ke da zuwa ban tsaya dogon tunani ba sabida na ɗan firgita na ciro kifiyata har uku na saita macijin na harba, kin san wane harba?” da sauri Aziza ta girgiza kai

” *BAHULA* wanda ƘANWA take a wajan Banju, wanda yake haukan sonta yake ji da ita, ban taba sanin suna rayuwa a wannan jejin ba, sannan ban san da cewa aljanun macizai bane,ni dai na ga Babban maciji kuma na harba, ina harbinta nan naga abunda ban taba gani ba, wato nan ta rikiɗe ta zama mutum kifiyar da ma harbeta da shi daya a kirji daya a juya daya a baya, kafin na farga da abunda na aikata nan naji ihun Banju yana furta “BAHULAAAAA!!” wanda sai da jejin bingel ya girgiza, a lokacin da Banju ya zo ga Kanwarsa Bahula ina tsaye ina kallon Ikon Allah, yayinda lokaci daya naji jikina na rawa, ko a lokacin da Bahula zata mutu sai da ta cewa Banju Dan Allah ya gyara halinsa na mugunta bata so a sake koransa a wannan jejin kamar yadda ya buwayi asalin garin da suke a jejin aka koresu ta hanyar yi musu turaren barkono dan tun asalin Banju mugu ne fiye da misali, a lokacin da na ga haka na matso kusa ina bai wa Bahula hakuri, murmushi ta min bakinta na fitar da baƙin jini ta ce min ba komai tasan ba da gangan nayi ba, sannan ta roƙi alfarma a kan cewa na bar ɗan uwanta Banju yayi rayuwarsa a jejin bingel, sun taso tare kamar yadda aka haifesu tare dan su ma yan biyu ne, a hannun Banju Bahula ta cika, Bahula tana mutuwa Banju ya hau kuka ina basa hakuri dan babu taimakon da zan iya yiwa Bahula dan guba ya shigeta,hakika nima nayi kukan kuskuren da na aikata, nan na dinga ba wa Banju hakuri, amma abunda ya ce min shine, shi *BAYA MANTUWA,KUMA BAYA YAFIYA* a lokacin Banju ya yi yunkurin kasheni amma ya kasa, yayinda ni kuma na gudu,ina zuwa gida banyi nauyin baki wajan faɗawa mutane abunda ya faru ba,tabbas a lokacin mutanen kwana sun tsorata matuka,inda aka yi cincirindo aka je aka ba wa Banju hakuri amma ya nuna sam ba zai hakura ba, bayan kwana biyu da faruwan haka nan yankin kwana ta koma mace-mace na hanyar kisan maciji ko kuma kisan gilla ta sanadin wani gurb’ataccen guba wanda Banju ne ke yi, a kwana biyu Banju ya kashe mutane sama da dari a yankin kwana, nan fa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya kare mana, ba mu sake yin kasa a guiwa ba muka sake zuwa wajan Banju basa hakuri amma kamar mun sake zugasa ne muna tunzura shi, ba zan iya ƙayyace miki mutanen da Banju ya kashe ba Aziza, haka ya bi dangin Jumala mahaifiyarku ya kashesu ita daya kawai ta tsira, a lokacin Arɗo ya dauketa ya kaita gidansa sannan ya daura mana aure da ita, a lokacin Baffa Mandi shi ne sarkin fulanin kwana, haka shima iyayensa matansa yaransa da duk wani danginsa sai da Banju ya kashesu! a lokacin ko yaro aka haifa yau Banju ya samu zai kashe, babu kalar farmakin da Banju bai kawo min, akwai sadda yankin kwana ya koma zallar ƙura ne ke tashi tare da jinin mutanen da basuji ba basu gani ba,nan nayi tattaki naje na samu Banju nace masa daukar Fansansa a kaina ne meyasa yake so ya shafe yankina, ina nine na masa laifi to ya kasheni ya kyale jama’a amma nan yace min ko da ya kasheni ya min alkawari babu wanda zai rage a raye a mutanen yankin kwana sai ya kashe kowa! ko da kuwa ɗan da yake ciki ne sai ya kashesa! a lokacin nayi niyyar na miƙa wuyata ga Banju amma na fahimcesa kamar yadda ya faɗi ba zai kyale kowa ba, nan jama’ar kwana aka hadu aka yi tattaunawa inda kowa ya kawo shawara a kan na kashe Banju dan abun nasa yayi yawa,da fari naqi amincewa sai daga baya na amince, a lokacin da zamu gwabza na fahimci ba zan iya kashe Banju kai tsaye ba,kamar yadda shima ba zai iya kasheni kai tsaye ba, a lokacin ne na tafi jejin lore aka bani zare mafi hatsarin gaske, wato zaren saƙar dana, a wajan yanki muka gwabza da Banju gaban dukkan  mutanen yankin kwana, kin ga wannan takwabi da shi na kashe Banju bayan na saƙa zaren saƙar dana na naɗe a jiki na sokesa da takwabin a ciki, nan ya fadi yana aman jini amma jinin ba ja bane kore ne, kafin ya fadi kasa shine ya mana alkawarin cewa zai dawo daukar fansa a kaina ta ko wace hanya dani da mutanen yankin nan, to kinji abunda ya shiga tsakanina da Banju!”

     Baffa na gama ba wa Aziza labari tasa kuka tana fadin

“Kenan yanzu Baffa Fansar da Banju yake dauka a kanmu ne? Innalillahi wa inna ilahirrajiun! Yanzu Baffa kashemu zaka yi?” Baffa ya girgiza kai yana fadin

“A’a Aziza! Kin taba ganin Uban da ya kashe yaransa ne? Amma idan ta kama zan iya Kashe Azima dan tsaida wannan bala’in,idan ba haka ba tabbas ba a fara mutuwa ba, ke rabaki da Bahula ba zai yi wuya ba, amma ko da an rabaki da ita ke Banju ya maidaki Macijiya sabida bai samu yadda yake so a jikinki ba sai ta jikin Azima, kuma ni bana da masaniyar makarin abunda Banju ya miki, amma akwai wani Babban Malami mai suna Malam Shadi a can yankin ja’o zamu je wajansa dan ya mana bayani,ki kwantar da hankalinki, amma kafin nan muna da bukatar tsaida Azima mu ɗaureta, ki daina kuka kinji? Tashi mu tafi gida” Aziza ta miƙe tana share hawayenta suka nufi gida, a hanya kafin su karasa Baffa ya haɗu da Salti ɗan gidan Jauro mai maganin kwana aljanu sun bugesa, da sauri Baffa ya yi kansa yana dubasa,girgiza kai ya yi yana fadin

“Sai da nace kar wanda ya fito ai ga irinta nan, taurin kan Salti iri daya ne da na Ubansa Jauro” Baffa ya faɗa yana daukar Salti, gida suka nufa suna isa Baffa bai yi nauyin baki ba ya gaya musu ai Banju ne a jikin Azima, Bahula kuma tana jikin Aziza, sannan ko an raba Aziza da Bahula Banju ya maidata Macijiya, wani kuka mai rikita zuciya Hajja ta kuma sakawa, yayinda Aziza ta faɗa jikinta suka hau yi tare, Baffa Mandi ya ce

“Abun da za ayi yanzu shine, ya kamata muje wajan wannan Malamin wato Malam Shadi na can yankin Ja’o mu je zuwa gobe kawai dan bamu ga ta zama ba, amma kafin nan dan Allah kar a fadawa jama’ar gari dan ba a san me hakan zai haifar ba har sai munje an dawo, mu da muka sani ya tsaya a iya mu kawai” aka amsa da hakane, nan Arɗo ya ce

“Magaji? Ana ta wannan maganar ina Azima?”

     🐍🐍🐍🐍🐍

COMMENTS BUT PLSS DON’T SHARE BA DAN NI BA DAN ALLAH DA MANZON ALLAH 🥺👏🏻[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃

    💥✨ *AZIMA DA AZIZA*💥✨

    (🐍 _Macizai ne_🐍)

    MALLAKAR.

*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din

0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.

Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*

1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._

2- _GUDU A JEJI._

3- _SHUHADA._

4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._

5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._

6- _COLONEL UBAIDULLAH._

7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._

8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._

9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._

10- _DA NA SANI NA._

  11- _BADAWIYYAH_

12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_

Now

13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE🐍)_

_Follow me on wattpad,@Fateemah’0_

   🍃🍃🍃🍃🍃

 

*PAID.*

🅿️==2️⃣7️⃣↪️2️⃣8️⃣

“Azima?” Baffa ya nanata sannan ya kuma cewa

“Tun sadda ta b’ace ban ganta ba” Aziza dake kuka a jikin Hajja ta miƙe tana goge hawaye ta ce

“Baffa bari na dubota na gani tana ina” Baffa ya ce

“To dubota Aziza” rufe ido Aziza ta yi ta shafa hannun damanta da hannun hagunta,amma abun mamaki bata ga Azima ba, saurin bude ido tayi tana fadin “taya hakan zai faru?” 

“Menene Aziza?” Arɗo ya tambayeta

“Arɗo bana ganin komai,bana iya ganin Azima amma taya hakan zai kasance?” 

“Ki sake dubawa Aziza” Baffa ya faɗa Aziza ta gya ɗa kai tana fadin to Baffa, ta sake rintae ido amma wayam, sake buɗe ido ta yi ta ce

“Wlh bana ganinta, Baffa ya ce zan duba da kaina amma sai bayan munyi sallar magriba fatana dai daya kar ace Azima taje ta yi wani ɗanyen aiki”

“In sha Allahu ma ba zata yi ba” cewar Baffa Mandi,      kamar yadda Baffa ya faɗa bayan sallar magriba ya hau duba inda Azima take amma abunda bincikensa ya nuna masa shine kwata-kwata Azima bata yankin kwana ta fice gabadaya daga wannan sassanin, a firgice Baffa ke furta kalman “INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN! ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATIHI WA AKHLIFNI KAIRAN MINHA!” da gudu Hajja da Aziza suka shigo suna tambayar Baffa menene? “Azima bata yankin nan kwata-kwata,bata wannan al’ƙaryan! ta bar wannan sassanin, Banju ya ja min ‘ya sun bar wannan yankin!” cewar Baffa hankalinsa a matuƙar tashe, Aziza ta ɗora hannu a kai tana fadin

“Wlh Baffa ta sha fadin tana son shiga cikin inda yake da mutane da yawa ta tarwatsasu,kenan ina Azima ta nufa!? Duk inda zata je dai ba alkhairi zata shuka ba,dan nasha gaya mata shiganta mutane ba alkairi bane, yanzu miye abun yi Baffa?” girgiza kai Baffa ya yi ya ce

“Ban sani ba Aziza! Allah ya kaimu gobe asubanci zamuyi mu tafi yankin ja’o dan zuwa wajan Malam Shadi” Aziza ta juya tana kallon Hajja wacce ta kasa tsayar da hawayen da ke zuba a idonta, a hankali Aziza ta fice a bukkar tana sharan hawayen tausayin iyayenta, Aziza na fita Baffa ya matso kusa da Hajja dake hawaye tun tana kuka mai sauti har ta koma kukan baya fita sai ambaliyar hawaye, cikin sigar rarrashi Baffa ya ce

“Jumala kiyi hakuri! Ki dage da addua muna kai wa Allah kukanmu! Dan Allah ki daina wannan kukan kar ya jawo miki ciwo, kinji!?” dago jajayen idonta Hajja ta yi ta watsasu a cikin na Baffa wanda tun tahirin aurensu bata taba kallon tsakiyar idonsa ba sai yau, muryarta a dashe ta ce

“Ciwo? Ciwo fa ka ce Baffan yan biyu? Wani irin ciwo ne ya fi na zuciya? Shin kasan ya nake ji a raina?”

“Ko ma ya kike ji ki yawaita nanata kalman Innalillahi wa inna ilahirrjiun! ya zaki dinga jin sassauci a ranki, sannan…..”

“Don Allah Baffan ‘yan biyu!” Hajja ta kasa Baffa ba tare da ya idasa maganarsa ba, cikin zafafan hawaye ta dago ta ce

“Ni dai kawai abunda nake bukata a wajanka shine ka dawo min da yarana! Ka dawo  mini da Azima da Azizana, ni dai ban haifi macizai ba! mutane na haifa,idan wani abu ya samu Azima da Aziza hakika zan iya mutuwa kawai ka dawo min da yarana!” ta tashi ta fice da gudu a bukkan, Aziza dake maqale a jikin bukkan tana sauraronsu ta riƙe bakinta gam tana kuka itama da gudu ta fice a gida ta yi rafin jimulo, taje ta ci kukanta har ta godewa Allah kafin ta dawo gida, bukkar Hajja ta shige ta sameta zaune ta zauna kusa da ita ta ɗora kanta a kan cinyar Hajja ta ce

“Hajjana! Inaji a jikina kamar na kusan barinki! Ba wai ina gaya miki dan na tashi hankalinki bane, duk duniya babu abunda na tsana kamar na ganki ke da Baffa cikin tashin hankali,abunda yasa nake gaya miki Hajja dan na nemi yafiyarki ne! Hajja ki yafe min idan har nayi miki wani abu a zaman da muka yi dake! Kowa da kalar kaddararsa amma mu wannan shi ne namu kaddara! Ba mu kasance cikin mutane da zamu yi rayuwa dake ba Hajja,dan Allah ki yafeni! Ki yafemini!!” Aziza ta karasa da sakin kuka mai ban tausayi da karya zuciya,tana sa kukan Hajja ta rungumeta tana bubbuga bayanta dan tama kasa magana ko tace zatayi maganar ma muryarta ba zai fito ba dan ya dashe!” su na nan suna kuka har dare ya tsaga kafin Baffa ya shigo ya musu umarni da suyi alwala suyi sallah, hakan kuwa ta kasance, Baffa ne yaja su sallah suna gayawa Ubangiji, da haka har asuba ta yi basu rintsa ba.

     Bayan Baffa ya dawo daga masallaci tare suka shigo da Ardo da Baffa Mandi, a lokacin Aziza da hajja suna zaune sunyi jingum-jingum, Baffa ya ce

“Aziza ta shi mu tafi, Jumala ke kuma ki tafi gidan Arɗo” ko uhum Hajja bata ce ba tana riƙe da hannun Aziza,fuskokinsu a kumbure,shima Baffa ɗaurewa kawai yake yi baya so ya kara karya musu guiwa amma da zai samu dama da shima ya sha kukan nan ko zai samu mai rarrashinsa, da kyar Aziza ta zare hannunta daga na Hajja ta fice da sauri jin wani kukan na shirin cewa a ba shi hanya, Hajja kuwa tuni ta sake saka wani kuka tasa hannuwanta a fuska, saurin ficewa Baffa ya yi jin hawaye ya fara bin fuskarsa, yana fita babu b’ata lokaci suka hau doki, da Baffa da Baffa Mandi da Arɗo sai Aziza, suna hawa doki suka dauki hanyar yankin ja’o ba tare da bata lokaci ba.

        🐍🐍🐍🐍🐍

Tun bayan da Azima ta bar yankin kwana take aikin tafiya ba tare da ta gaji ba dan bata jin gajiya a tattare da ita, hakika tana shan tafiya, dan kuwa ace mutum wanda yake ba aljani ba idan zai fita daga yankin kwana zuwa cikin garin kafin ya iske titi a kan doki sai ya shafe sati biyu, shiyasa su haka suke ba a shigo musu su ma kuma basu shiga gari dan nan ne rayuwarsu a kauyensu mai cike da abun burgewa da albarkatun korayen shuke-shuke, a kwana daya Azima ta yi rabin tafiya abunka da ba tafiyar mutane ba.

        🍃🍃🍃🍃

Sai kusan gaff azahar su Baffa suka isa yankin ja’o ba tare da bata lokaci ba aka musu iso izuwa ganawa da Malam Shadi, suna shiga bukkarsa Malam Shadi na haɗa ido da Aziza ya hau salati yana sanar da Ubangiji nan gaban Baffa ya bada dammm! amma ya daure suka zauna ana gaisawa cikin mutunci da mutuntawa, Malam Shadi ya kalli Baffa ya ce

“Ohh Allah Magaji Mazan fama kana raye? Yaushe rabonka da yankin nan? Inaji fa tun sadda wan can muguwar mayyar ta sakamu a gaba kazo ka rabamu da ita ban sake ganinka ba sai dai kayi aike” Baffa ya yi murmushin boye damuwa ya ce

“Wlh  kuwa Malam Shadi,tun sadda na daina shige-shige naji komai ya fita a raina”

“Allahu Akbar” cewar Malam Shadi yana kallon Aziza da ta dukar da kai gabanta na faduwa, ya kalli Baffa cike da al’ajabi ya ce

“Magaji Bawa ina ka samo *MACIJIYA!?*” juyawa Baffa ya yi ya kalli Aziza da ta rakube ta dukar da kai kasa kamar ma kuka take yi,sannan ya maida kallonsa ga Malam ya ce

” ‘yata ce Malam, na kawota ne wajanka dan ka duba min ita, Banju da na kashe yace zai dawo shine ya dawo daukar Fansa a kan yarana, yanzu haka dayar ta bar yankin kwana kwata-kwata, ita kuma wannan ka ganta nan, shine nace bari na kawosu wajanka dan a san ta yadda za a rabasu da su,bana so gwagwarmayan da nayi ya shafe yarana”

“Shafa kuma ta nawa magaji? Ai shafa kam an gama shafansu tunda gasu nan a macizai” cewar Arɗo, Malam Shadi ya gya ɗa kai yana fadin

“Ya Hayyu Ya Qayyum Ya Zuljalalu wal’ikram, hakika Banju mugun aljani ne, Banju mugu ne fiye da tunanin me tunani, amma Magaji kai ma zaka iya yiwa yaranka magani ai”

Girgiza kai Baffa ya yi ya ce

“Zan iya sake kashe Banju, amma abunda nake tsoro shine Banju na rayuwa ne a cikin Azima yana tafiya ne da kafafunta, yana aiki ne da hannuwanta,yana gani ne da idanunta,yana motsi ne da motsinta, sannan a binciken da nayi Azima a sume take a jikin Banju, idan har na kashe Banju to tabbas Azima ma ta tafi, na duba na ga ita Aziza rabata da Bahula ba wata damuwa ba ce, amma kuma tashin hankalin a nan shine,ko Bahula ta bar jikin Aziza, Aziza ba zata samu lafiya ba dan Banju ya maidata Macijiya sabida bai samu yadda yake so a jikinta ba” jinjina kai Malam Shadi yayi bayan Baffa ya gama yi masa bayani, Baffa ya kuma cewa

“Ina da bukatar taimako dan bana so na salwantar da rayuwar yarana! Jumala ba zata yafemini ba,sannan nima bazan yafewa kaina ba Malam Shadi”

       “Matso nan kusa dani Aziza karki ji tsoro” Malam Shadi ya fada yana kallon Aziza, a hankali ta taso ta matso kusa da shi ta duka, wani magani ya ɗiba a kasko ya watsa mata a fuska,ihu Aziza ta saka tana furta “Ya Allah! Ya Allah! Ya Allah! Baffana zafii!!” abun tausayi, hawaye ne ya cika a idon Baffa yana ji kamar ya tashi ya fita amma ina ba hali, Malam Shadi yasa hannu ya damƙi goshin Aziza da karfi, murkususu ta hauyi tana son kwacewa amma ta kasa,rintse idonsa ya yi yana gane-gane da hange-hange, ya dau lokaci yana riƙe da goshin Aziza wacce ke murkususun azaba har sai da ta suma kafin Malam Shadi ya saketa, Baffa ya yi saurin taro ‘yarsa ta fada jikinsa,jikinsa na rawa hawaye na zuba a idonsa ya d’ago ya kalli Malam Shadi yana fadin

“Malam me ya sameta?”

“Haba Magaji! Sai kace baka san yanayin aiki ba,ka kwantar da hankalinka zata farfado, amma gaskiya akwai babbar matsala wanda ba zan iya ce muku komai a kai ba, akwai aikin da nake so nayi cikin dare ina so na bincika na ga taya za a rabasu da mugun nan Banju, sannan Babban tashin hankalin shine ‘yar uwarta Banju ya jata sun bar al’ƙaryan nan,ina take? Ina za a ganta? Duk babu wanda ya sani” Arɗo da Baffa Mandi suka sharo zufar tashin hankali, Malam Shadi ya ɗora da cewa

“Babban damuwar shine abunda Banju zai ja Azima ta aikata,amma zanyi bincike a kai yau In sha Allah,ina dai a nan zaku kwana?” Baffa suka amsa da eh, sannan Malam Shadi ya kira wani almajirinsa yace ya kawo masa tarbama wanda yake na kara ne, bayan an kawo ya ce a shinfiɗe Aziza a kai, bayan Baffa ya kwantar da Aziza Malam Shadi ya kunna mata hayaki, sannan suka fita waje suka zauna suna tattauna yadda zasu yi a kan lamarin.

       🍃🍃🍃🍃

Sarki Chubado ne da mai unguwan kwana ori suke tattaunawa a kan batun Azima da Aziza Macizai ne,suna ta alhinin lamarin, su biyu suke magana a kan cewa suna tausayawa Baffa, a garin yaya sai ga Salti ɗan gidan Jauro mai maganin yankin kwana yazo wucewa caraf a kunnensa, dan Salti ba dai gulma ba,nan yaji duk wani tattaunawa da Sarki Chubado da Ori ke yi a kan lamarin har da tafiyar da su Baffa suka yi yankin ja’o, da gudu Salti ya kwasa yana fadin zai je ya gayawa Baffansa dan yasan zai yi farin ciki da wannan labarin da zai kai ma sa.

      🍃🍃🍃🍃🍃

Comments

🅿️==2️⃣9️⃣↪️0️⃣3️⃣0️⃣
Ko da Salti ya isa gida ya kwashe kaff yadda yaji su Sarki Chubaɗo da mai Unguwa Ori suka tattauna ya gayawa Baffansa, a hankali Jauro ya mike yana murmushi ya ce
“Salti,tun da kake kwaso gulma baka taba kwaso mai amfani ba sai yau, jeka dole nayi maka kyautar shanuwa daya” da sauri Salti ya miƙe yana murna ya fice,Jauro ya dungule hannu yana dukar iska ya ce
“Lokaci ya yi da zan fatattaki Magaji Bawa, ka fi ni a komai kyau,martaba,baiwa,kyakkyawar mata Jumala,ga kuma yara kyawawa! kai kana gani ka fi kowa ne! zargin da nake yiwa yaranka ya tabbata, wato ma har b’oye-b’oye ake yiwa mutane ana munafurtarsu kar a gaya musu gaskiya, to ni nan zan bayyanawa jama’a su waye Azima da Aziza!” ya faɗa yana murmushin mugunta.
       🍃🍃🍃🍃
Kamar yadda Malam Shadi ya faɗa da daddare ne ya yi bincike mai zurfi dangane da matsalar su Azima da Aziza,inda ya hangi gagaramin matsala mai rikitarwa inda tausayin yaran ya kamasa dan kuwa da wuya a samu maganin warakarsu.
       Da washe gari bayan sun idar da sallar asuba ana gaggaisawa bayan sun gama gaisawa Malam Shadi ya kalli Baffa sai kuma ya duƙar da kai, Baffa ya yi murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo ya ce
“Malam Shadi karkiji komai gaya min ko ma miye ne,ni musulmi ne kuma nayi imani da kaddara mai kyau da marar kyau, ka gaya min kawai”
      Jinjina kai Malam Shadi ya yi ya ce
“Tabbas ni shaidan hakane Magaji, wato a gaskiya ba zan boye maka ba, samun lafiyar Aziza yana tattare ne da Azima, domin kuwa wanda yake da alhakin abun ya ja Azima basu yankin kwana balle a musu magani, kai ko da Azima bata bar yankin kwana ba da wuya a samu wanda zai yi jahadin taimaka musu” goge gumi Baffa ya yi ya ce
“Malam Shadi ka gaya min kai tsaye kawai zan fi ganewa,dan a yanzu ji nake kamar kirjina zai tsage zuciyata ta faɗo kasa”
      Malam Shadi ya gyara zama ya ce
“Dole sai sunyi aure kafin Banju ya rabu dasu, barin ma Azima ita ce wacce take bukatar taimakon gaggawa, sannan wannan miji da zai auresu sai ya sadu da Azima kafin Banju ya fita a jikin Azima, idan Banju ya bar jikin Azima a cikin kaso dari mun yaƙesa kaso sittin, idan aka yi sa’a idan Banju ya fita a jikin Azima, Aziza zata iya samun lafiya,idan kuma bata samu ba ita ma dole sai wanda ya aureta ya kusanceta kafin makarin sihirin da Banju ya mata na siddabarun maidata macijiya ya karya”
       “Ma’asabamun musibatin Qalu Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Innallahi wa inna ilaihirrajiun! Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!” shine abunda Baffa da Baffa Mandi da Arɗo suke iya nanatawa suna fifita da hannunsu,Arɗo ya girgiza kai ya ce
“Tabdijam kawai Allah ya jikan Azima da Aziza, dan kuwa na tabbata babu namijin da zaiji cewa su macizai ne ya taimaka ya auresu har mu sa ran zasu samu lafiya”
      “Kuma dole wanda zai aure su zai fuskanci ƙalubale kafin ya kusancesu,sannan bayan ya kusancesu zai iya kamuwa da mugun ciwo amma ba ina nufin ba zai warke ba amma tabbas zaiji a jikinsa,idan an samu damar hakan zaka iya kara kashe Banju a karo na biyu” hawaye ne Baffa ya hau yi yana kan tasbihi ga Ubangijin talikai, Baffa ya ce
“Tabbas da ace na dinga ganin tashin hankalin nan na b’arna da ta’adin da Azima ke yi da ni da kaina zan kasheta! to amma yanzu tana ina? Me take yi? Su wa da wa zata kashe!? Akwai tambayoyi dayawa a raina wanda babu wanda zai amsamin” Baffa ya hau kuka Arɗo da Baffa Mandi suna rarrashinsa, Baffa Mandi ya kalli Malam Shadi ya ce
“Malam Shadi, yanzu ya maganar raba Aziza da Bahula?” 
      “A gaskiya Mandi ni a ganina a shawarce, kar a raba Aziza da Bahula, tinda bata cutar da ita, sannan ko an raba Aziza da Bahula Aziza fa ba zata taba komawa mutum ba, ni a ganina tunda Banju yana son kanwarsa Bahula sannan yasan cewa tana rayuwa a jikin Aziza dole wata rana zai dawo, karku manta kamar yadda Azima da Aziza suke ‘yan biyu haka ma Banju da Bahula suke ‘yan biyu, zamu iya samun dawowa da Azima gida ta hanyar Bahula dake jikin Aziza,ni a ganina kar a raba Aziza da Bahula a barsu tare idan ya so aka samu wanda zai yi jahadin aurensu bayan an raba Azima da Banju sai a raba Aziza da Bahula”
      “Tashin hankali wanda ba a sa masa rana” cewar Arɗo yana kan rarrashin Baffa dake kuka wi-wi, da kyar suka rarrashi Baffa ya samu ya tsaida hawayen idonsa sannan ya miƙe yana yiwa Malam Shadi godiya ya ce masa zasu wuce yau, Malam Shadi ya ce
“Ba damuwa Magaji,karka damu Allah zai shiga cikin lamarin” Baffa bai iya ya kara cewa kala ba, Malam Shadi ya miƙa masa wani ganyen magani ya ce
“Wannan idan ka je ka haɗawa Aziza,ita kuma Azima Allah ya dawo da ita cikin gaggawa, bari nasa a kira muku Azizan sai ku wuce” su Baffa Mandi da Arɗo suka yiwa Malam Shadi Godiya sannan suka fito a tare,bayan an kira Aziza ta fito Baffa ya kama hannunta idonsa jajur ya ɗorata a kan doki, Aziza tunda ta ga yanayin Baffanta tasan cewa kwai gagarumin matsala, haka sukayi sallama da Malam shadi cikin amince suka kama hanyar yankin kwana.
       🍃🍃🍃🍃🍃
Sai da lokacin sallar azahar ya gauta kafin suka iso yankin kwana kai tsaye gidan Arɗo suka nufa, Hajja na zaune tayi zugum Yawuro ta ajiye mata kwaryan nono a gabanta amma haka nonon ke kallonta, Yawuro ke fadin
“Haba Jumala! Dan Allah ki sa wani abu a cikinki mana, ga jikinki da zafi, kiyi hakuri mana haba dan Allah” hawaye Hajja ta goge ba tare da ta cewa Yawuro Uffan ba, sallamarsu Baffa ne yasa Hajja ta dago da sauri ta sauke idonta a kan Aziza da ta shigo kanta a sunkuye, duk irin kunya na Hajja amma da sauri ta tashi ta rungume Aziza wacce itama ta saki kuka take ji a ranta da ace kisan kai ba haramun bane babu abinda zai hanata bata sha guba ta kashe kanta ba, kuka sukeyi sosai sai da Inna wuro ta dakatar dasu, sannan Inna wuro ta hau tambayarsu ya suka yi a can yankin ja’o ɗin, Baffa Mandi ya ce “babu amfanin a boye muku, gwara a gaya muku gaskiya” Ardo ya ce “tabbas dan wannan ba abun boyewa bane” nan Arɗo ya kwashe yadda suka yi da Malam Shadi ya gaya musu, wani mahaukacin zare ido Aziza ta yi jin bala’in da suke ciki wai sai sunyi aure an sadu dasu kafin su warke! Wa ma zai auri macizai!? Barin ma wanda zai auri Azima ya ji labarin kisan da Banju ya yi tayi a jikinta ai ma babu mai aurensu,in kuwa dole sai hakane sun zama annoba a cikin jama’a barin ma yanzu da Azima bata nan.
       Sallallami su Inna wuro da Yawuro suke yi suna tafa hannuwa yayinda Hajja ke girgiza kai tana fadin ita a maido mata da yaranta tana wani irin kuka, Arɗo da Baffa Mandi suka ce Baffa yazo su je wajan Sarki Chubado da mai Unguwa Ori su gaya musu halin da ake ciki,    a tare suka fita aka bar Hajja da kuka ita da Aziza, su Inna Wuro suna rarrashinsu.
@@@@@@
        Bayani dalla-dalla suka yiwa su Sarki Chubaɗo da mai unguwa Ori yadda Malam Shadi ya shaida musu, Sarki Chubado ya ce
“Tashin hankali, gaskiya Banju ya mana illa dayawa, amma ina da shawara mai zai hana a gayawa mutanen gari halin da ake ciki, idan ya so sai a nemi wanda zai auresu ko da ba zai zauna dasu ba dai da sun samu lafiya sai ya sake su!”
      “Nima na fara wannan tunanin a raina ranka ya dade,amma abun dubawan a nan shine wa zai auresu?” cewar mai unguwa Ori, tattaunawa suke yi sosai ta yadda za a shawo kan matsalar amma duk inda aka dafa babu mafita, su na nan suna kan shawara sai ga Sanda da mugun gudu kamar wanda yake gudu a iska yana zuwa gabansu sarki Chubaɗo ya zube yana haki, Sanda jika ne ga Yawuro, Arɗo ya ce
“Sanda mahaukacin ina ne kai? Wannan gudu da ka zo a haka sai kace an kawo mana farmakin yaƙi miye haka? Meke faruwa?” kasa magana Sanda ya yi illa hanyar gida da yake nunawa da kyar ya furta “ADDA AZIZAAA!!” da sauri Baffa ya ce
“Me ya samu Azizan?” ya fada yana miƙewa tsaye, Sanda ya ce
“Baffa Jauro ne ya gayyo duka mutanen yankin nan wai zasu kashe Adda Azima da Adda Aziza wai macizai ne sune suka dinga kashe-kashe sune suka kashe su Ilu mai maganin Maciji dasu Jarman Macizai da Innu Maciji, yanzu haka ma sun saka wuta a gidan Arɗo ƙarami” da sauri su Chubado suka miƙe suna salati tare da al’ajabin ina Jauro yaji wannan maganar? Baffa Mandi ya ce
“Kafff yankin kwana da kewayenta babu munafuki sarkin gulma sama da ɗan Jauro Salti, to amma taya akayi ya ji wannan maganar?” Sarki Chubaɗo ya ce
“Yanzu babu lokaci maida magana muje kar su kashe Aziza” da gudu Baffa ya yi gaba idonsa har yana rufewa, ya rasa matsalar dake tsakaninsa da Jauro,bai san me ya tarewa Jauro ba a rayuwa da baya sonsa baya kaunarsa sam.
        Ko da su Baffa suka isa, sun samu gidan Arɗo karami na ci da wuta, ga Hajja a sheme a kasa an fasa mata kai, Aziza kuwa sun ɗaureta a jikin bishiya sai dukanta suke yi duk sun fasa mata jiki, a ranta take kalman shahada dama su kasheta kawai ta huta da wannan rayuwar, ihuuu Baffa ya yi ganin matarsa kwance a sheme a kasa an fasa mata kai ga ‘yarsa da aka yi mata daurin mayu ana dukanta, ihun da Baffa ya yi yasa hankalin jama’a dawowa kansa, Jauro ya yi murmushin gefen baki kafin ya matso kusa da Baffa yana magana yana daga murya
“Hakika bai kamata ace daku za a haɗa baki a munafurci mutanen yankin nan ba, (yana yi da sarki chubaɗo da mai unguwa ori) sannan kai kuma Magaji idan ka manta na tuna maka,kaine kace min duk ranar da na gano *AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE* kaine wanda zaka bani takwabin da zan kashesu! Dan haka yau sunan Aziza gawa,ita ma Azimar da ta bar yankin nan da ace tana nan da yau gunduwa-gunduwa zamuyi musu” murmushi Baffa ke yi hawaye na zuba a idonsa yana yiwa Jauro wani irin kallo wanda ko idonsa baya kiftawa, Jauro ya kuma cewa
“Shin zaku yarda ku rayu da macijiya mai kisa a cikinku?” jama’a suka amsa da a’a, Jauro ya kuma cewa
“Idan kuwa hakane ku ci gaba da dukanta har sai ta mutu!!” Sarki Chubaɗo da mai unguwa Ori suna dakatar da jama’a amma ina kamar kara ingizasu akeyi, wani ne da ya daga wani babbar sanda ya roɗawa Aziza a kai jikake kwasss!! Wani ihuuu Baffa ya kuma yi ganin yadda sandar ta shigi Aziza dan har sai da ta girgiza, Baffa ya kalli Jauro cikin jan ido ya ce
“Karka bari na nuna maka waye asalin Magaji!!”
“Zan so hakan” Jauro ya fadi yana dariya, ci gaba da dukan Aziza mutane suka yi, wani gurnani Baffa ya yi mai taken muryan zakin dawa, sannan ya rintse ido ya haɗa wani guguwa mai cike da barkono ya kwashi jama’ar da suke dukan Aziza ya watsar dasu, a take ya yi tsalle daya yaje gabanta yasa hannu ya shafe igiyar da suka daureta igiyar ta tsinke, sannan Baffa yasa hannu ya shafe mata inda suka ji mata ciwo ya kamo kafadunta cikin daga murya ya ce
“AZIZAAA!! NA YARDA DA KEEE!! INA SO NE KI BAR YANKIN NAN!! BANA SO SU KASHEKI ALHALI ‘YAR UWARKI TA BAZAMA GARI! INASO KIJE KI NEMOTA SANNAN KI DAKATAR DA ITA,IDAN HAR KU KA HADU KIKA GA B’ARNARTA YA YI YAWA NA MIKI IZINI KI KASHETA ITA DA BANJU!! IDAN KUMA KE MA TAKI TA ZO KARSHE DAMA BA ZAMA MUKA ZO YI BA,IDAN KUMA KIN SAMETA KU DAWO! NINA SAN TA INDA ZANYI MAGANIN BANJU!! AZIZA TAFIIIII!!” girgiza kai Aziza tayi tana wani irin kuka alaman ba zata iya tafi ta bar Hajja da Baffa ba, rai b’ace Baffa ya kara cewa bar yankin nan na ce Azizaaaa!! da gudu Aziza ta yankin jeji dan barin yankin kwana,   Jauro ya yi yunkurin binta Baffa ya ce
“Kana bin bayanta zan mata umarni ta kasheka! Ka godewa Allah Aziza ce ba Azima ba ce! Da sunanku gawa gaba daya!! Ni zaku yiwa haka! Sabida su waye yanzu nake fuskartar wannan bala’in!!?”

Leave your vote

-7 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like