Advertisement
HALIN GIRMA Hausa Novel
(1)
#team zafafa biyar
Advertisements
ร ร A tsaye take gaban sink din cikin toilet din tana wanke kananan kayan da ya kasance mallakin Maama da Zeenat, lokaci zuwa lokaci tana cire hannun ta tana yarfe shi saboda sanyin da ake zugawa kasancewar karshen December ne a lokacin da ake zuga sanyi. Dauraye kayan tayi ta yi saurin fitowa ganin haske ya hudo ta window din toilet din. Karfe shida da rabi agogon falon ya nuna, tayi saurin karasawa kitchen din domin dora abin karin kumallo kafin ahalin gidan su tashi.
ร Tun kafin asubah take fara ayyukan gidan wani lokacin har karfe tara na safe bata kamalla wa, duk kuwa da tana iyakar kokarin ganin bata wuce taran ba saboda karatun ta na islamiya da take zuwa duk weekend, tana ganin shine kadai gatan da zata yi wa rayuwar ta a halin da take ciki a gidan mahaifin ta. Bata fatan wani ya shiga irin rayuwar da take ta kunci da tsantsar makirci, babu wanda ya san halin da take ciki balle ya kawo mata dauki, bata isa ta bud’e baki ba saboda kowa ganin kirki da karamcin Maman yake, mace ce me masifar kirki, me haba haba da saka duk wani abu nata gaba da na duk sauran yayanta a idon ahalin gidan,a badini kuwa bata da maraba da bola.
ร ร Kowa kallon mara dadin zama yake mata ko kuma mara godiyar Allah saboda rashin walwalar da take fama da har ya shafi kaso mafi rinjaye na rayuwar ta, zaka dauka bata dariya ko doguwar magana sai dai bata da sukunin yin kamar sauran yan matan gidan nasu.
ร Kowa kallon wadda tayi sa’ar uwar riko yake mata, ayi ta sakawa Maman albarka da yabo a gabanta tana amshewa amma a bayan idon mutane! Bakar wahalar da take sha ba zata misaltu ba.
ร ร Da tunanin ta kammala aikin ta dauraye hannayen ta sannan ta fito ta jera musu a saman dining ta dauko nata a dan plate ta wuce zuwa dakin su.
ร ร Bude kofar da tayi ya farkar da Zeenat, a zafafe ta dago ta watsa mata kallon banza gami da jan d’an karamin tsaki tana sake rufe kanta da katon duvet din da take kanannade a cikin sa. Cikin nutsuwarta ta karasa shigowa d’akin tana dora plate din saman d’an madaidaicin mudubin dake cike da kayan shafe-shafe ta soma gyara wajen data tashi. Katifar ta fara daukewa ta kaita chan store sannan ta dawo ta share dakin a hankali gudun magana taci abincin a tsaitsaye ganin lokaci na neman kurewa tayi saurin watsa ruwa a gaggauce ta fito.
ร Dogon hijabin ta ash colour daya kasance a matsayin uniform din islamiyar tasu ta saka bayan ta gama shiryawa ta dau yar madaidaiciyar jakarta me dauke da Al-kurani me girma da sauran littafan addini ta fito.
ร ร Habib na zaune saman dining da alamun zaman sa kenan ta gaishe shi a nutse sannan tayi masa sallama ta wuce islamiyyar dake chan kasan layin su inda take zuwa duk asabar da lahadi da safe sai sauran ranakun da yamma amma banda juma’ah.
ร ร
ร ร
Advertisements
ร ร *Babban gida ne irin wanda zaka kirashi da Family house, bangarori ne da dama a ciki wanda yake dauke da gidaje guda shida dake kunshe da mutane cikin su suna rayuwa irin wadda suka zaba ma kansu. Duk da kowanne bangare na da tsarin da yake tafiyar da rayuwar sa akai amma kuma suna tafiya ne da ra’ayoyin juna, daya baya taba zartar da hukunci be sanar da daya ba, sannan duk abinda suka zartar din dole ne ya samu amincewar mahaifiyar su Hajiya Fatima wadda suke kira da Gaji.
ร ร Gidan ta ne a tsakiya in da sauran gidajen ke kewaye da ita, galibin yan matan family din suna tattare ne a shashen nata da ya zama tamkar matattarar su, yanayin haihuwa a family din na tafiya ne kusa da kusa, inda zaka samu yawanci sa’oin juna a kowanne gida.
ร Duk da basu da tarin dukiya irin me yawan nan amma suna da rufin asiri daidai gwargwado, sannan ana damawa dasu a duk bangarorin ilimi na Islama dana bokon hakan ma bangaren kasuwanci da siyasa duk babu wanda basa tabawa.
ร ร Zamu iya cewa kowanne a cikin yayan Gajin yayi sa’ar abokiyar zama ta kwarai dan babu wanda yake kuka da abokiyar zaman sa, daidai gwargwado suna zaman su lafiya suna kuma mutunta juna suna girmana Gaji da duk wata bukatar ta.
ร ร Muguwar mace me kinibibi da kissa zai yi wuya ka gane alkiblar ta farat daya, komai su kayi daidai ne suna kuma da kokarin kyautatawa kowa, suna kokarin boye aibun su suyi amfani da hakan wajen muzgunawa wanda basu so, idan yayi korafi a bashi rashin gaskiya saboda kirkin su.
ร ร Alhaji Muktar shine Babban dan Hajiya Gaji bayan Babbar Yayar su mace da suke kira da Hajiya Babba dake zaune a Sheffield dake birnin London tare da family dinta , sai me bi masa Dr Ibrahim, sai Abba Usman sai Abba Musa sai dan auta Abba Kabir.
ร ร Dr Ibrahim dan boko ne sosai dan har ya kai matakin associate professor in da yake lecturing a halin yanzu. Matar sa daya ta aure Maama wanda zamu iya cewa kaf family din babu wanda baya kaunar ta saboda kirkin ta. Yaranta uku da Dr, Habib ne Babba, sai Zeenat sai karamin kanin su Marwan. Sai dai shi yana da ya daya daban wadda suke haifa da matar da ya aura a lokacin da yaje karatun sa na Masters a University of Michigan, anan suka hadu har sukayi aure suka haifi ya daya me sunan Gaji (Fatima-Iman) a lokacin ne kuma suka rabu saboda wata babbar matsala da ta taso tsakanin shi da family dinta, dan dama basa son auren, yana ji yana gani ya rabu da ita, ya dawo gida. Fatima na yin wayo suka kawo masa ita inda ya dauki rikon ta ya damka a hannun Maama wanda a lokacin take goyon Zeenat itama. Bata taba nuna masa komai ba ko a fuska kuma be taba ganin wani banbanci tsakanin Fatima da Zeenat ba, shiyasa ya kara bata mazauni me girma a zuciyar sa.
***Daidai layin su ta hangi Zeenat tsaye da Bashir, dan dam taji a zuciyar ta kasancewar ba wannan ne karo na farko ba, duk wanda yace yana son ta in sha Allah ba za’a dau lokaci ba zata same shi tare da Zeenat shikenan kuma ta ta maganar ta sha ruwa. Zeenat yar uwarta ce amma duk da haka tana jin babu dadi, sai dai bata bar hakan yayi tasiri a zuciyar ta ba, ta dau hakan a matsayin wata jarrabawar rayuwar ta. Daidai in da suke tsaye tazo zata wuce Zeenat din ta kira sunan ta
“Iman!” Tsayawa tayi chak, ta kalle su kad’an sannan tace
“Sannun ku.”
Murmushi Bashir din yayi mata sannan yace
“Malamar islamiyya, sannu da zuwa.”
Bata amsa masa ba dan yadda yayi maganar taji akwai alamun rainin wayo
“Ya akayi?” Tace tana kallon Zeenat.
“Babu!” Ta dage kafadar ta.
“Ok!” Tace tana cigaba da tafiyar ta, tana jin sanda suka kwashe da dariya, ta dan ji babu dadi a ranta amma ta danne, ta karasa gidan duk ranta babu dadi. Da gaske ta ji zuciyar ta, ta amince da Bashir farkon magana da yayi mata har tana addu’ar Allah ya tabbatar mata dashi, sai gashi tun ba’a je ko ina ba, ya koma wajen Zeenat wadda ko da ace da wasa yaje wajen Zeenat din toh babu ita babu shi har abadah.
A gate taci karo da Maryam, a kalla ba kamar sauran ba, Maryam ta fuskance ta, shiyasa tasu tazo daya sosai, duk da ba wata doguwar hiraa ce ke hada su ba amma ta kan sake da ita fiye da kowa. Bikin su za’a yi su hudu a gidan. Maryam din sai Bilkisu, Aysha da Amina. Daga su sai ita da Zeenat da yar gidan Abba Musa Rabi’ah sune a layi, duk cikin su babu wanda bashi da me son shi amma banda ita da ta gagara samun wanda ma zai tsaya din.
Bangaren Gajin suka wuce tana mata hira akan shirye shiryen bikin, rabin hankalin ta baya kan Maryam din har suka karasa, suna shiga ana kiran sallar magriba sai kawai suka wuce sukayi alwala.
Bayan sun idar ne Gaji ta kalle su tana kan abun sallah kamar zatayi magana sai kuma ta fasa. Sai da ta gama ta tashi sannan tace
“Maryama daga ina haka ke da alhuda-huda?”
“Daga islamiyya Iman take ni kuma na fito zan taho nan muka hadu.”
“Toh ku tashi ku dubo min ko an gama tuwo dan cikina ya soma kiran chiroma.”
“Wai Gaji wasa wasa fa kina da ci wallahi.”
“Saukin ta ba kowa ke siyan kayan abincin ba ‘yaya na ne, ko zaku hana su bani ne?”
Rik’e baki Iman tayi tana dariya Maryam tace
“Bamu isa ba ai Gaji, aci dadi lafiya lokacin ki ne.”
” Yafi muku sauki dai, kema alhuda-huda kin fara zama su balki ko? Kika biye musu baki da bakin da zaki iya karawa dani atau.”
Shiru tayi bata ce komai ba, suka zagaya kitchen din Gajin da ke baya suka hado mata abincin suka kawo mata sannan suka zauna suka ci tare, lokaci lokaci Maryam na tsokanar ta, ita dai Iman jin su kawai take har aka gama suka tattare kayan sannan Maryam ta tafi ta barta a nan, sai kawai ta zame tayi kwanciyar ta a saman doguwar kujerar ta fad’a kundin tunani kamar yadda ta saba.
“Yaya Iman kizo inji Maama, zamu ci abinci kar ya huce baki ci ba, kiyi sauri.”
Muryar Marwan ta iso daidai kunnenta, da sauri ta tashi zaune, sai kuma ta mike da sauri tana jin sanda Gaji tace
“Hajara ba dai kirki ba, yadda kike kula da yarinyar nan ubangiji Allah ya kula miki da naki yayan.”
Wasu guntayen hawaye ne taji suna neman zubo mata, tayi saurin maidasu ta kara sauri zuwa shashen nasu domin amsa kiran Maama.
_*KASHI NA BIYAR*_
_*KASHI NA BIYAR*_
_*KASHI NA BIYAR*_
_*KASHI NA BIYAR*_
*_KASHI NA BIYAR_*
_*SABUWAR SHEKARA, SABUWAR TAFIYA, SABON SALO*_
รฐลธโยฅรฐลธโยฅ. รฐลธโยฅรฐลธโยฅ. รฐลธโยฅรฐลธโยฅ.
_*ZAFAFA BIYAR!! KASHI NA BIYAR!! SINADARIN ZAFAFA5 (BEST TOP 5)*_
_*INA MASOYA KUMA MAKARANTA, MABIYA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR? KU MATSO DOMIN NESA TAZO KUSA, KU SHARE HAWAYEN KU, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE DANNOWA DA TURURUN SU, MASU ZAFAFAN FADAKARWA, NISHADANTARWA HADรขโฌโขI DA ZAFAFAN KAUNA MARAR GAURAYE.*_
_*YAN BIYAR DIN NAKU KAMAR KO DA YAUSHE SUNE:*_
_*SAFIYYAH HUGUMA*_
_DABI’AR ZUCIYA_
2-_*BILYN ABDULL*_
_TAKUN SAKรขโฌโขA_
_*3- MAMUH GEE*_
_DEEN MARSHALL_
_*4-HAFSAT RANO*_
_HALIN GIRMA_
_*5~NANA HAFSAT (MISS XOXO)*_
_SO DA ZUCIYAรขยยครฏยธย_
1
_DAGA TASKAR *SAFIYYAH HUGUMA* MARUBUCIYAR ZAFAFA DA TAYI; DAURIN BOYE, ALKAWARIN ALLAH, ALKIBLA, SIRADIN RAYUWA TA SAKE ZUWA DA WANI RANTSATTSE MAI SUNA:_ *_รล ABI’AR ZUCIYA_*รฐลธหย
2
_DAGA ALKALAMIN *HAFSAT RANO* , MARUBUCIYAR ZAFAFA DA TAZO MUKE A BAYA DA, DAURIN GORO, ABINDA KE CIKIN ZUCIYA, SAUYIN KADDARA, MABUDIN ZUCIYA. WANNAN KARON TAZO DA WANI SABON SALON MAI SUNA:_ *_HALIN GIRMA_*
3
_DAGA SALON TAFIYAR *MAMUH GEE* ,WADDA A LITTATTAFAN TA NA ZAFAFA TAYI; MIN QALB, BURI DAYA, KAUNAR MU, UBAYD MALEEK. WANNAN TAFIYAR TAZO DA WANI DADDAรขโฌโขDA MAI SUNA:_ *_DEEN MARSHALL_*รฐลธยฅยฐ
4
_DAGA TAFIYAR RUBUTUN *NANA HAFSAT (MISS XOXO)* WADDA A ZAFAFAN BAYA TAYI WASU KAMAR SU: KAI MIN HALACCI, KIBIYAR AJALI, DALAAL, IGIYAR ZATO. WANNAN NEXT LEVEL DIN TAZO DA WANI MAI TAKEN:_ _*SO DA ZUCIYA*รขยยครฏยธย_
5
_DAGA SALON RUBUTUN *BILYN ABDULL* MARUBUCIYAR ZAFAFA DA TAYI NA BAYA IRIN SU: WUTSIYAR RAKUMI, SARAN BOYE, MAKAUNIYAR KADDARA, GUDU DA WAIWAYE. WANNAN SABUWAR TAFIYAR TAZO DA WANI MAI SUNA:_ *_TAKUN SAKAรฐลธโยฅ_*
รขหโรฏยธยรฐลธโยซรฐลธโยฅรขลยจรฐลธโ?
_*KADA KU BARI AYI BABU KU, KUZO A DAMA DAKU A SABUWAR TAFIYA MAI TAKEN SABON SALO, SINADARIN ZAFAFA BEST TOP 5, MASU ZAFAFAN DARUSSA, NA RAYUWA, WANDA DUK WANI MAKARANCI BA ZAI RASA DARUSSAN DAUKA ACIKI BA.*_
_*GUDA DAYA: 300*_
_*BIYU 400*_
_*UKU 500*_
_*HUDU 700*_
*_BIYAR DUBU DAYA (1k)_*
*_YAN TALLAH SAMAN SHAFI NAIRA 300, รขโฌหKASAN SHAFI KUMA 200 NE_*
_*YADDA ZAKU BIYA*_
*_ZAKU TURA KUDINKU ACIKIN WANNAN ASUSUN NA BANKI_*รฐลธโโกรฐลธโโกรฐลธโโกรฐลธโโก
*6019473875*
*MUSAA ABDULLAHI SAFIYA*
*keystone bank*
*Sai katura shedar biyanka ta wannan number*รฐลธโโกรฐลธโโกรฐลธโโก
08184017082
_*IDAN KATIN MTN NE, KO VTU SAI ATURO ZUWA GA*_รฐลธโโกรฐลธโโกรฐลธโโกรฐลธโโก
09134848107
_#TEAM ZAFAFA BIYAR_รฐลธโยฅรฐลธโยฅ
ร ร
1/2/22, 22:47 – Buhainat: *HALIN GIRMA!*
รยฉรยฎHafsat Rano.
FREE PAGE
(2)
*****
Takalmin Abban su da ta gani a kofar shiga falon yasa ta sauke ajiyar zuciya, ta bud’e labulen hade da sallama, idonta ya sauka a cikin na Mama da take kallon kofar, tayi mata wani kallo me cike da ma’anoni da ba kowa ne zai gane ba sai ita kadai da ta san manufar sa.
“Abba barka da gida.” Tace tana zamewa k’asa
“Yawwa Uwata, kina ina haka mamanki na ta neman ki kinsan bata so kici abincin da ya huce ko? Ga yanayi na sanyin nan ba komai ne yake rik’e zafin sa ba.”
“Ina wajen Gaji ne.” Tace tana sake yin kasa da kanta.
“Toh dai a dinga kula ana abinda ya kamata kinji? Allah yayi muku albarka.”
“Amin.” Tace tana mikewa ta shige dakin su da dan sauri tana avoiding idon Maman da ta rakata dashi. D’are-d’are ta tarar da Zeenat a saman gadon tana waya, wuceta tayi ta bud’e jakar kayan ta, ta sauya kayan jikin ta da wasu ta ninke Hijab din sannan ta dawo ta saka abun sallah a k’asa ta zauna ta ciro littafin da akayi musu a islamiya ta soma karantawa a hankali.
“Malama kina distracting dina.”
Ta zare wayar daga kunnen ta tayi maganar a chunkushe. Banza tayi mata ta cigaba da karatun ta ba tare da ta daina ba.
“Mtsww!.” Ta ja dogon tsaki
“Baby bari zan kiraka ina zuwa.*
“Owk dear, ina jira.”
Katse kiran tayi ta zuro kafafunta daidai wajen da Iman din take zaune
“Malama duk karatun da kikayi a islamiya be ishe ki ba, sai kinzo kin cika mana kunne mu san kina zuwa makaranta, bayan kowa yasan dalilin da ya saka kika nace da zuwa ko kya samu ya sayyadi ya ce yana so.”
Bata tanka mata ba, hakan ya sake kular da Zeenat din, ta saka hannu zata warce littafin tayi saurin janyewa ta mike tsaye,
“Wallahi sai dai ki hakura da karatun ko kije chan kiyi, naga ma aiki ne gaban ki kin sani tsabar kinibibi so kike sai ya jiyo ki kina karatu. “
” Kinga duk abinda kike yi bana taba tanka miki, ba wai don ina tsoron ki bane ko wani abu, kawai bana son tashin hankali ne da hayaniya. “
” Toh ki tanka min ma mana, wallahi yanzu zanje na hado ki da Mama.”
Bata sake magana ba ta fice daga dakin dan ba karamin aikin Maman bane ta hanata zuwa makarantar na wani lokaci, sai kawai ta zarce kitchen ta tarar da kayan wanke-wanke tuli guda, ta nannade hannun ta tasoma wankewa. Abincin da ta gani a tukunya ta san nata ne, yayi mugun sanyi ita kuma a ka’idar ta bata cin abinci me sanyi, ko ruwan sanyi bata sha a rayuwarta balle yanzu da ake zuga sanyi sosai., gudun ta barshi bata ci ba gobe a hanata yasa ta samu leda ta juye a ciki ta wanke tukunyar ta goge gas da k’asan kitchen din ta gyara komai tsaf sannan ta fito da ledar ta zagaya ta kofar baya ta fita zuwa part din Gaji, ta samu me aikinta ta bata sannan ta dawo ta dauko katifar ta a store ta wuce dakin.
ร ร Har lokacin Zeenat bata gama wayar ba, toilet ta wuce ta dauro alwala tazo tayi shafa’i da wutri sannan ta kwanta ta rufe kanta gaba daya da dan yalolon zanin gadon da duk ya yayyage ta gefe da gefe ta kudundune da haka bacci ya dauke ta.
ร ร Da safe ta tashi kamar kullum tayi ayyukan da suka zama wajibi akanta, kasancewar litinin ce sai ta yi wanka kawai ta wuce shashen Gaji bayan ta tabbatar da fitar Mama tun sassafe, a chan taci abincin ta sannan ta kwanta bacci. Sai da rana ta soma dagawa sannan ta koma ta daura girkin rana,ta gama kafin lokacin tafiya islamiya, ta dauki na Gaji ta kai mata ta sake zama tana jiran lokacin ya cika.
“Yaki takwara ta, zo nan.” Gajin tace tana daga zaune a in da take
“Me yake damun ki?”
“Na’am?”
“Fad’a min idan kina da wata matsala ne, na dade ina lura da yanayin rashin walwalar ki, sai dai na kan dauki hakan a matsayin halitta, amma kuma jiya sai abun yazo kaina, na dinga tunanin ko dai kina da wata damuwa ne? Da kika kasa sanar wa wani kika barta a ranki.”
“Babu komai Gaji, yanayi na ne a haka amma ni babu abinda yake damuna.”
“Kin tabbata.”
Daga mata kai tayi tana jin kamar ta saki kuka, ga dama ta samu amma bata da ikon furta wa, toh tace mene ma wai? Hakan ba shi zai hana Mama ta daina muzguna mata ba, Kai tsaye zata kare kanta da zarar Gajin ta tuhume ta karshe kuma abun ya koma kanta kowa ya cigaba da mata kallon marar kirki ko kuma wadda bata san halacci ba. Shiyasa ta zabi yin shiru kawai dan fadar ba zata sauya komai ba, su duka sun yarda da Maman yarda irin ta ban mamaki.
“Ai nasan bangaren Hajara baki da wata matsala dama, na dai zata ko damuwa ce dai irin ta rashin maman ki kusa dake, duk da bani da haufi akan kulawar da kika samu iyakar abinda zaki samu kenan ko da ita mahaifiyar taki ce.”
“Haka ne.” Tace a kasalance
“Yawwa ki dinga dan daurewa kina shiga cikin yan uwanki kinji? Zaman shirun da kike babu dadi.”
“In sha Allah zan gyara.”
“Yawwa… Haka nake son ji.”
“Ya batun yajin aikin nan kuwa? Kun dauko karatu tiryan tiryan yajin aiki ya tsaidaku da tuni wata maganar ake ba wannan ba.”
“Wallahi shiru ba labari, muna dai ta addu’a Allah ya sa a daidaita.”
“K’asar nan kenan ai, dan karatun ma yanzu nema ake a hana dan talaka yin sa.”
“Wallahi.”
” Allah yayi mana maganin abinda yafi karfin mu.”
” Amin ya Allah!”
” Shiyasa nace duk ku fidda mazaje kawai da zarar wadanchan sun tafi kuma azo ayi naku zaman haka nan ba zai yiwu ba.”
Shiru tayi gabanta ya fadi, bata son taji ana maganar auren su, gashi kuma taga alamar ba za’a dauki lokaci ba za’a ce su fidda mazaje, ya zatayi da ranta? Da ganin suna makaranta yasa maganar ta lafa amma yanzu yajin aikin da aka tafi da ba’a san ranar dawowa ba ya saka iyayen nasu yanke shawarar suma su aurar dasu kawai sai karasa karatun a dakin su.
ร ร Tashi tayi tayi ma Gajin sallama ganin lokaci yayi, taje tayi alwala ta saka Hijab dinta ta fito, a falo ta tarar da Mama tayi saurin tsugunnawa ta gaishe ta
” Mama barka da gida.”
” Saura idan an tashi ki tsaya shiririta a hanya ko ki tsaya gidan Gaji karki zo kiyi abinda ya dace, jiya kam kinci darajar babanku yana nan.”
“In sha Allah.” Tace sannan ta mike ta fice Maman ta rakata da harara.
****Sati biyu tsakani aka fara bikin gidan nasu, duk yadda taso gujewa wasu abubuwan amma Maryam bata barta ba, komai idan za’a yi sai ta sakata a ciki, haka kunshi da gyaran kai tare suka je da wata kawar Maryam din.
ร Alhamis suka fara bikin, a compound din gidan Anty Mabruka sukayi bridal shower iya su da kawayen su, juma’ah akayi kamu asabar aka daura aure hade da yini, lahadi aka kai kowacce gidan ta.
ร ร Ranar litinin suka tashi gidan da sauran bakin da basu riga sun tafi ba wanda yawanci dangin Gaji ne, a babban kitchen din gidan suka hadu aka hada breakfast Masa da miyar taushe, har rana tayi sosai basu kammala ba hakan ya sake haifar mata da wata irin gajiya bayan wadda take fama da ita, tasan halin Mama sarai idan ta makale taki fitowa ayi aikin da ita duk da akwai masu yi din amma dolen ta ne ta fito, duk da hakan ba karamin taimaka mata yayi ba wajen gogewa da kalolin girke-girke mabanbanta. Sannan uwa uba girkin mutane da yawa wanda ba kowa bane ya iya.
ร ร Da saurin ta, ta karasa dakin su, ta kwanta a gefen gadon saboda wani irin sanyi da take ji alamun zazzabi ne ke neman rafke ta, rawar sanyi ta fara hakoranta suka shiga haduwa waje daya, ta saka hannu da k’yar ta jawo bargon Zeenat din ta lulluba.
ร ร Shigowar ta kenan ta tsaya daga kofar
“Kut! Lallai ma.” Tace tana karasawa ciki, ta fuzge bargon da karfi
“Dan Allah zee ki kyale ni bani da lafiya.” Tace muryar ta chan ciki. Shiru Zeenat din tayi tana kallon ta, sai kuma ta sakar mata bargon ta juya ta fice daga dakin. Har dare zazzabin be sake ta ba, babu kuma wanda yazo neman ta. Tayi tunanin Zeenat din zata fad’a wa Maman ne duk da bata saka rai ba, amma jin shirun ya tabbatar mata da ta fad’a mata dan da ba haka ba da tuni Maman ta turo neman ta akan wani aikin.
ร ร Wajajen Tara Zeenat ta dawo dakin, ta kalle ta a zaune saman abun sallah ta kudundune, juyawa tayi ta fita ta dawo da paracetamol a hannun ta da ruwa ta mika mata. Karba tayi da sauri tayi mata godiya, bata amsa ba ta sake fita sai gata ta dawo da katifar Iman din, ta shinfid’a mata sannan ta dauko bargon ta, ta dora mata akai ta haye gadon ta kwanta ta rufe idon ta. Sosai Iman taji dadi a ranta, ko ba komai tayi mata abinda bata taba ba, tashi tayi da k’yar ta lallaba ta fita kitchen ta hado tea sannan ta dawo ta sha da k’yar ta sake komawa ta kwanta ta kudundune.
ร ร Kwanan ta uku a haka, har ta soma samun karfin jikinta, Mama ta shigo sau daya ta bata anti-malaria shima dan tasan Abban zai iya tambaya ne, shima da tasan zai shigo ya duba ta ne, tana jin sanda take ce masa sun je asibiti ma kuma jikin da sauki.
ร ร
***Karamin daki ne da yafi kama da shago, katifa ce karama irin ta yan boarding school sai jakar kayan sa a gefe, bayan haka babu komai a dakin sai wani dogon mudubi dake rataye jikin bangon dakin.
ร ร Tsaye yake a gaban mudubin yana duba fuskar sa dake cike da kasumba ko ina har baka iya ganin komai na fuskar tasa sosai, kansa rufe yake da katuwar hular sanyi, ya nannade wuyan sa da abu, kafar sa da hannun sa duk rufe suke cikin hular sanyi, idan ka cire fuskar sa da itama kasumbar bata wani bari a ganta sosai, babu wani abu na jikin sa dake a bud’e. Kayan jikin sa a wanke suke tsaf, sai dai sun tsufa sosai, har da wata yar bula a jikin hannun rigar.
ร ร A ko da yaushe yakan tsaya ne a daidai hanyar da take hucewa idan ta dawo daga islamiyya, amma kuma kwana biyu ya rabu da ganin ta, shiyasa ya yanke shawarar zuwa gida duk da yasan ba tsarar sa bace amma zai gwada sa’ar sa.
ร ร
*_WAIWAYE……ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR รฐลธโยฅรฐลธโยฅรฐลธโยฅรฐลธโยฅsune suka sake dawo muku da wasu nau’in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI…..yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA รหWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALLรฐลธโโฐรฐลธยยพMamuhghee_*
*_HALIN GIRMAรฐลธโโฐรฐลธยยพhafsat rano_*
*_TAKUN SAรหAรฐลธโโฐรฐลธยยพbillyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYAรฐลธโโฐรฐลธยยพmiss xoxo_*
*_รล ABI’AR ZUCIYAรฐลธโโฐรฐลธยยพhuguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN รล AI รล AI HAR BIYAR…ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2รฐลธโโฐรฐลธยยพ400
3รฐลธโโฐรฐลธยยพ500
4รฐลธโโฐรฐลธยยพ700
5รฐลธโโฐรฐลธยยพ1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*รฐลธยคยรฐลธยยฝรฐลธยคยรฐลธยยฝรฐลธยคยรฐลธยยฝรฐลธยคยรฐลธยยฝรฐลธยคยรฐลธยยฝ
#team zafafa biyar
1/2/22, 22:47 – Buhainat: *HALIN GIRMA*
Hafsat Rano
3
****
Tsaye yayi jikin gate din gidan yana kare masa kallo, tunanin ta yadda zai fara shiga yake musamman da ba sanin sunan ta yayi ba, ya dai saka mata suna da zuciyar sa kuma be taba yunkurin tsaidata balle yaji sunan ta ba.
ร Lekowa maigadin gidan yayi, ganin mutum a tsaye yasa shi fitowa gaba daya
“Sannu.” Yace masa yana kokarin daidaita muryar sa
“Yawwa sannu, wa kake nema?” Maigadin ya tambaye shi yana kare masa kallon cikin rashin sani.
Nan fa ake yinta, shiru yayi kamar me nazari shi kuma maigadin ya kafe shi da ido yana son jin abinda ya kawo shi.
“Am… Amm nazo wajen…”
“Malam Iliya.” Zeenat dake fitowa ta kirashi tana leko wa.
“Na’am ranki ya dade!”
“Siyo min kati na 500 kayi sauri dan Allah.”
“Yanzu kuwa, ga wani bako nan bansan wajen wa yazo ba dai kin tambaye shi.”
Yayi gaba, kallon sa tayi tun daga sama har kasa a wulakanci ta yatsine baki tace
“Wa kake nema kai kuma Malam?”
“Yar uwarki nake nema dan Allah, wata me zuwa islamiya kasan layin nan doguwa haka fara.”
“Waye kai a wajen ta?”
Kallon cikin ido yayi mata, ta ja tsaki tana juya fuskar ta
“Ban fiye son kallo ba Malam, ka shigo ciki bari na tura maka ita dama ai sai dai ita din…”
Gaba tayi tana cigaba da sababi
“A kaf gidan nan wa zai kwaso mutum irin wannman dan Allah! Ji shi kamar wani mahaukaci.”
Sai ta kwashe da dariya tana sake daga kafa.
A kwance ta tarar da Iman tana danna wayar ta da ba kasafai ta cika wani amfani da ita ba, yanzun ma wani labari ne yaja hankalin ta a Facebook take karantawa.
” Kina da babban bako a waje da galleliyar ranar nan.”
” Waye?”
” Idan kika je idon ki zai gane miki shi.”
” Owk.”
ร ร Tace tana tashi zaune, har yanzu bata gama dawowa daidai ba amma haka ta karfafa jikinta tayi ayyukan ta. Hijab ta saka madaidaici akan doguwar rigar jikinta ta fito. Daga chan hanyar gate ta hange shi a tsaye ya rataye hannayen sa a bayan sa, kansa a kasa yana wasa da kafar sa.
ร ร Dogo ne na ajin farko, jikin sa ko ina a murje babu alamun rama ko kad’an, yanayin shigar sa bata dace da tsarin zubin halittar sa ba, kafin ta karasa ta gama ayyana shi a ranta. Da sallama ta isa, ya dago da sauri a lokaci daya kwayar idon sa ta sauka a cikin ta ta, gabanta ne yayi masifar faduwa, tayi saurin janye idon ta, ta russuna kad’an tace
“Ina wuni?” Lumshe idon sa yayi ya bud’e, fuskar sa dake cike da kasumba ta dan yi fadi alamun farin ciki, ya tattaro dukkan nutsuwa da jaruntar sa yayi gyaran murya yace
“Kina lafiya?”
“Alhamdulillah.” Tace a gajarce ta matsa wajen wasu kujerun roba guda biyu ta dauko daya ta kawo masa.
“Bismillah zauna kana ta tsaiwa.”
Hannun sa ya dora a saman kujerar ta kalli hannun yayi saurin janye shi ya zauna sannan yace
“Kefa?”
Wani dan tudu a wajen ta nuna masa da hannu, ta zauna akai tana jin duk ta takura ganin yadda yake bin ta da kallo da wasu irin idanun sa da suka sake shiga ciki sosai.
“Na same ki lafiya? Ya gida yasu Mama da yan uwa?”
“Lafiya lou Alhamdulillah.”
“Ban gane waye ba amma?”
“Me sonki ne, me kaunar ki da son duk wani farin cikin ki, yan kwanakin nan da na dauka banga wucewar ki ba, sun zame min kwanaki mafiya muni a rayuwa ta. Na kan zauna a duk yini ina dakon wucewarki, ban taba yunkurin yi miki magana ba, sai dai zuciya ta, ta gaza dauka har sai dana biyo bayanki, ina fatan ban takura miki ba?”
Girgiza kai tayi tana jin wani bawai, wai ita ake karantawa wannan kalaman, idan har taji daidai wato ya dade yana bibiyar ta, bata ma sani ba.
” Kinyi shiru!” Yace yana gyara zaman sa
Shirun ta sake yi dan bata san me zata ce masa ba.
” Nasan dama karambani ne irin nawa, ban kai ajin ko da me wanke miki takalmi bane, kiyi hakuri idan nayi miki shishigi a rayuwar ki.”
” A ah wallahi, ba haka bane ba, a kalla mutumin da yace yana son ka ai yafi makiyinka, nagode sosai da soyayyar ka gareni.”ร Tace da sauri sannan tayi murmushi, ji yayi kamar zuciyar sa zata fito daga kirjin sa, ya danne sosai ya maida mata murnushin
“Nagode Nuryyy… Nagode sosai.”
Shiru ya biyo baya, ta dinga wasa da gefen Hijab dinta shi kuma yana satar kallon ta. Nutsuwarta tafi komai tafiya dashi.
“Bari na wuce.”
Da sauri ta mike kamar me jiran kad’an,
“Ka gaida gida.” Tace tana saurin yin gaba
“Ko zan samu number waya dan Allah?”
Tsayawa tayi ta mika masa hannu, ya shafa aljihun sa dukka
“Kinga garin sauri na manta wayar a daki, amma zan rik’e fad’a min.”
“Ok .” Tace ta karanto masa,
” Nagode sunana Muhammad.”
” Fatima, ka gaida gida.”
Ta juya ta barshi a tsaye a wajen. Sake maimaita sunan Fatiman yayi, ya saki murmushi a hankali sannan ya juya ya fice daga gidan.
***A zaune a falo ta tarar da Mama na waya, zata wuce ta tsaida ta da hannu ta cigaba da wayar ta
” Ba za dai ka bar maganar nan ba ko Khalil? Toh shikenan sai kazo din dai ma sake tattaunata, idan yaso ko a dangi ne sai ka duba sosai ba za’a rasa ba ai.”
Amsa ya bata daga bangaren sa, ta ja tsaki tace
” Matsalata da kai kafiya wallahi toh sai anjima, sai kazo din.”
Ta kashe wayar ta dangwarar da ita a gefen ta
” Na rasa shegen taurin kai irin na Khalil wallahi, sam baya kaunar ya ganni cikin farin ciki, mtsw.”
Ta sake jan tsaki a karo na ba adadi.
” Daga ina kike?”ta jeho mata tambayar bayan ta riga ta san inda take.
” Wani ne yazo dama.”
” Waye shi?”
” Bansan shi ba nima, wai a bayan layi yake.”
” Toh kina jina? Idan zaki yiwa kanki kiyamullaili ki rik’e shi hannu bibiyu toh, idan kuma kika yi wasarairai da shi shima ya gudu kamar sauran, sai ki zauna muyi ta jerawa a gidan nan,tunda dai bakin hali ya hana samarin zama kowa yazo sai ya tafi.”
Bata dago ba, bata kuma ce kala ba, tana jin Maman tana kuma ajiye kowacce magana a mazaunin da ya dace, sai da ta gama yi mata cin fuskar sanann tace
” Khalil zai zo gobe, babu ruwanki dashi da shiga harkar sa, ko falo bana so naga kina kaiwa da komowa har ya tafi, zan fi so ki tattara ki koma wajen Gaji da zama aikin ma na yafe miki, idan ya gama kwanakin ya tafi shikenan, bana son daukar magana dan shi ba kunya magana yake ji ba, kinji dai na gaya miki.”
” In sha Allah.”
” Jeki.”
Tashi tayi ta bita da kallo ranta na tafasa, da gaske take kishi da ita dukda bata zauna da mahaifiyar ta ba, amma duk sanda ta kalle ta sai ta tuno abinda ya faru.
****A guje suka taso ganin ya fito, ya nufi wajen da jerin motocin ke fake suna jiran sa, ransa a bace yake da kiran amma bashi da ikon kin amsawa, dole ya ajiye shirin sa a gefe ya kirawo su domin ba zai taba yarda da shigar masa shirin sa ba. Shiyasa su kansu basu da yakini ko masaniyar komai, dan ya tabbatar da zasu taimaka wajen lalata masa shirin sa. Dan su din basu da ikon kansu sai abinda aka gindaya musu.
Bud’e masa bayan motar daya daga ciki yayi, ya russuna kad’an sannan yace
“We are very sorry sir!”
Be tanka masa ba, ya shige cikin motar ya jingina bayan sa da kujerar ya lumshe idon sa.
“Oga Main house zamu?” Yayi tambayar yana tada motar
“Lamido Crescent!” Yace yana sake rufe idon sa.
Chan suka wuce direct, suna isa ya fito ya shige ciki, tun daga falo ya fara wurgi da kayan jikin sa, ya rage daga shi sai boxer da farar singlet, kallon kansa yayi a jikin tangamemen mudubin dake tsaye kikam a falon, ya juya ya sake juyawa sannan ya wuce zuwa cikin bedroom din sa.
Wanka ya fara yi a gurguje sannan ya fito ya shirya cikin shigar babbar riga da jamfa da wando farare kal, sau cikin sa ya jawo ya ajiye a gefe ya fara saka farar socks a ciki sannan ya saka ya fito rik’e da babbar rigar a hannu.
Zama yayi sannan ya danna remote din kofar, da sauri suka shigo su biyu, ya mik’a wa daya babbar rigar, karba yayi ya taimaka masa ya saka sannan ya dauki abubuwan da yasan zai bukata ya fita dasu.
“Ka zauna anan zan kiraka da zarar na sauka.”
Yace da dayan sannan ya tashi ya fice cikin takun da yafi kama dana jinin sarauta.
Motoci biyu ne suka fita daga gidan, shi yana cikin daya su kuma suna bin sa a daya har zuwa airport.
*Muhammad Ahmad Santuraki*
*(*Captain Moh*)*
*_WAIWAYE……ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR รฐลธโยฅรฐลธโยฅรฐลธโยฅรฐลธโยฅsune suka sake dawo muku da wasu nau’in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI…..yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA รหWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALLรฐลธโโฐรฐลธยยพMamuhghee_*
*_HALIN GIRMAรฐลธโโฐรฐลธยยพhafsat rano_*
*_TAKUN SAรหAรฐลธโโฐรฐลธยยพbillyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYAรฐลธโโฐรฐลธยยพmiss xoxo_*
*_รล ABI’AR ZUCIYAรฐลธโโฐรฐลธยยพhuguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN รล AI รล AI HAR BIYAR…ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2รฐลธโโฐรฐลธยยพ400
3รฐลธโโฐรฐลธยยพ500
4รฐลธโโฐรฐลธยยพ700
5รฐลธโโฐรฐลธยยพ1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*รฐลธยคยรฐลธยยฝรฐลธยคยรฐลธยยฝรฐลธยคยรฐลธยยฝรฐลธยคยรฐลธยยฝรฐลธยคยรฐลธยยฝ
#team zafafa biyar
1/2/22, 22:47 – Buhainat: *HALIN GIRMA*
*_Hafsat Rano_*
4
****
*Adamawa-Yola*
Tun daga yanayin manyan motocin da suka cika harabar ya tabbatar da bakin dake cike da fadar, yana da yakini dalilin kiran Bubun kenan a kalla zasu ganshi sannan ayi masa maganar da tafi komai kona masa rai, maganar mulki da yake dukkan kokarin sa wajen guje mata.
Be jira an bud’e masa ba, ya balle murfin motar ya fito bayan hango Aji da yayi yana nufar ciki tare da tawagar sa, da saurin sa ya cimmusu,domin ya samu su shiga a tare, ko ya gujewa idanun Bubun daga zuwan nasa. Yasan a cike yake taf dashi
“Aji!” Ya kira shi da sunan da yake kiran sa
“Hoo d’an nema, na dauka ba zaka zo ba ai.”
” Na isa naki amsa kiran ka ko na Bubu? Ai ban isa ba.”
” Dadin baki, idan har da gaske ne ai sai ka amsa kiran da muka jima munayi maka ko?”
Sosa keya yayi ba tare da yace komai ba, suka karasa ciki. Da ido Bubu ya kafe shi tun shigowar sa, tabbas ya rame fiye da ganin da yayi masa kwanaki da suka wuce, sannan akwai wani yanayi a tattare dashi da be gamsu ba, a gabansa ya tare, ya kwashi gaisuwa ya cigaba da bin sa da idon ba tare da shi ya yarda sun hada ido ba, gefen Ajin ya samu ya rabe yana sake hade fuskar sa tamau, murmushi kawai Bubu yayi ganin da gaske Muhammad yake har yau yana nan akan bakan sa, ya rasa dalilin da ya saka shi baya son mulki ko kad’an, tamkar ba dan naga da ba, kamar wanda aka juyawa tunani kwata kwata akai, gashi da gaske yake jin ya kamata ace ya huta, yakamata ya karbe shi kamar yadda ya karbi Aji a lokutan baya. Sai dai d’an nasa sam be shirya hakan ba, abinda yasa yake dada jan lokacin sosai, burin sa kawai yasa a gaba tun bayan shigar sa jami’ah, in da ya kwallafa rai akan aikin tsaro, ya kuma samu cikar burin sa duk da ba hakan ne ya kasanci burin sa ba shi.
Kamal ne ya shigo wajen, ya gaida kowa cike da girmawawa sannan ya samu gefe ya zauna yana fuskantar Muhammad din, kallon juna suka yi ba tare da wata magana ba, murmushi kawai Kamal din ya sakar masa wanda ya kasa maida masa domin ya san ma’anar sa, be damu ba ko kad’an, da ace Bubu zai ji shawarar sa da ya jima da yiwa Kamal din abinda yake muradi, amma shima kemaimai yaki, ya kwallafa rai akan Muhammad din, ko me yasa? Oho. Ya dage kafadarsa alamun baya da bukatar ya sani ma dai.
Duk batutuwan da aka tattauna a wajen be tsinci komai ba, zuciyar sa ta lula chan zuwa in da ya baro, tunanin halin da take ciki ko abinda take aikatawa kawai yake har kusan kowa ya gama ficewa ya zama na daga shi sai Aji, da Bubu.
“Muhammadu.” Yayi firgigit sai kuma ya hau sosai kai yana murmushi
“Barka da rana Bubu.”
“Kalli shigar ka fa Muhammad, kalle ka? Hakan ya dace a matsayin ka da gidan nan? Haka kaga dan uwanka Kamal yayi shiga irin ta masarauta?”
“Wallahi Bubu garin sauri ne, kuma gashi ba wani iya nada rawanin nan nayi ba wallahi, infact ciwon kai wallahi yake sani, amma za’a gyara ba za’a sake ba.”
Murmushi Aji yayi me dan sauti, ya kalle shi yana sake fadada fara’ar fuskar sa.
“Ayi hakuri ranka ya dade munyi kuskure ba zamu sake ba.” A duk sanda irin hakan ta faru Ajin ne ke yin uwa yayi makarbiya ya hana ayi masa fad’a, hakan yasa ba kasafai Bubun ke korafi gaban Ajin ba, sai ya tsuke bakin sa kawai be sake cewa komai ba.
Tashi yayi, ya dan russuna a gaban mahaifin nasa
“Zan shiga ciki Bubu!”
“Ka same ni a shashe na bayan sallar magriba.”
” In sha Allah. A tashi lafiya.”
” Aji sai na shigo wajen yar tsohuwa ta.”
” Tana nan tana jiran ka da manshanun ta da yajin daddawa.”
Murmushi yayi, ya fice suka raka shi da ido. Yana fita Bubu yaja tsaki
” Na rasa me yake damun yaron nan wallahi, ace yaro ya taso a cikin abu amma sam ya tsane shi? Wannan wanne irin abu ne?”
” Mu cigaba da hakuri kawai Ahmadu, komai zai wuce ne.”
” Allah yasa, kowa jira na yake, mutanen gari da manyan mutane kowa ya zuba ido yaga me zanyi akai, ga Kamal da gaske yake son mulkin nan, gashi sam be chanchanta ba, na rasa yadda zan.”
“Shima ka barni dashi kawai, ayi masa abinda yake so din, yanzu dai a zaman da zakuyi sai kayi masa maganar auren muji, a kalla auren zai taimaka masa ya zauna a cikin mu, kaga dole ya koyi komai.”
” In sha Allah, idan ma bashi da yarinyar da tayi masa ni zan nemo masa.”
” Kul, Muhammad ba irin yaran da za’a yi musu haka bane, mu da muke son amfani da soyayyar shi ga yarinyar, abi dai komai a sannu.”
” Shikenan in sha Allah, Allah yasa mu dace.”
” Amin ya Allah.”
***Bangaren Ammin sa ya wuce, yana tafe yana amsa gaisuwar da ya tsana, ayi ta gaida mutum kamar wata tsiya, hakan na daya daga cikin abinda yake hada shi da gidan su, ya gwammace yayi guduwar sa waje daya kawai ba tare da hayaniyar mutane ba.
Tana zaune ta dora kafarta a saman dan tumtum din dake falon, kafar na damun ta sosai shiyasa ko yaushe zaka ganta a mike ana dan mammatsa ta. Yana tura kofar duk suka mike, har rige rigen gaishe shi suke kowa yasan yadda Ammin ke masifar ji da tilon dan nata, mace me kirki da sanin yakamata, shiyasa ta karbe kowa a gidan daga ma’aikata har dangi kowa nata ne, wajen Bubu ma Itace star,itace kuma uwar gidan sa dan dai Allah be bata yawan haihuwa bane.
“Barka da zuwa yarima, sarki me jiran gado, uban mara uba me uban ma kaine gatan sa, shalelen Gimbiya da maimartaba, ka tsare gaba ka tsare baya, Allah ya kara maka daukaka da girma, Allah ya ida nufi.. sai…”
Da sauri ya dakatar da ita, sai ta juya sum-sum-sum ta fice, ya kalli Ammi yayi mata murmushi kafin ya zauna a daidai saitun kafafun nata ya tankwashe kafafun sa
“Ashe zaka zo.” Tace masa tana murmushi itama
” Na isa naki zuwa Ammi? Barka da gida mun same ku lafiya?”
” Lafiya lau Alhamdulillah , shiru daga cewa zaka je wani aiki Kano shikenan kamar an aiki bawa garin su, su ba labarin su da suka bika kaima ba labari, gidanka da kake sauka ma an ce min ba chan ka sauka ba.”
” Wani babban aiki ne ai Ammi, ki tayani da addu’a kawai in sha Allah zakuji labari me dadi.”
” Allah yasa toh, ya aikin naku?”
” Alhamdulillah wallahi, muna ta fama, ba dadi amma haka dai za’a cigaba da lallabawa.”
” Tunda kana so ba.” Tace.
Dariya ya saka kawai be ce komai ba. Ya dan jima a tare da Ammin tasa kafin ya tashi ya yi mata sallama zuwa shashen shi, da yake kusa da na Bubu.
Yana shiga ya tarar da kayan abinci a jere a falon nasa, sai kamshin turaren wuta dake fita ta cikin yar karamar burner din dake makale a jikin wani dan karfe.
Wuce komai yayi zuwa bedroom dinsa, ya kwanta rigingine a saman gadon ya jawo woyoyin sa, ya shiga cikin contact dinsa, number farko da yayi saving dinta da emoji din heart da padlock ya danna kira ya kwanta sosai yana lumshe idanun sa lokacin da ta soma ringing…
****Da safe ta tashi kamar kullum tayi duk abinda tasan wajibin ta ne, har zuwa sanda rana ta fito sosai, kayan ta na wanki dana Marwan ta hada ta zagaya baya ta hau wanke su, daga gefe ta ajiye wayarta tana jin karatun alkur’ani me girma, tana wankin tana bi har ta gama tsaf, ta tattare su ta shanya sannan ta dawo ciki ta chanja kayan ta, ta fice zuwa shashen Gaji.
Fitar ta kenan Khalil ya shigo, maigadi na bin sa janye da katotuwar trolly din sa a baya. Da Habib suka ci karo yana kokarin fita, ya bashi hannu suka chapke cike da murnar ganin juna
“Welcome welcome.” Yace masa yana juyawa suka shiga ciki. Da sauri Mama ta fito jin hayaniyar su..
“Wa nake ji kamar Khalil, inyee lallai yaron nan Ashe dai da gaske kake.”
“Gani dai, ai dama na gama shirin zuwa kawai ban sanar dake bane sai jiyan.”
“Maraba lalle da manyan yan jarida.”
Zama yayi a cikin kujerun falon, itama maman ta zauna tana gyara dan kwalin kanta.
“Wai dama kinsan zaizo Mah?”
“Nima sai jiya na sani, na zata kuma halin nasa ne Ashe da gaske yake shiyasa ma ban fad’a ma kowa ba.”
“Ina wuni Anty?”
” Lafiya lou Khalil, yaso Hajiya da kowa da kowa?”
” Duk suna nan lafiya, itama tayi mamaki da nace zanzo, gashi kuma zan dade sosai dan aiki ne ya kawo ni.”
” Ahaap ko da naji, Ashe zuwan dai da dalili, jairi dama nasan akwai abinda ya kawo ka.”
” Abubuwa dai Anty, karki manta da wannan maganar tamu hadda ita ma.”
Tsaki taja ta harare shi
” Zaka fara ko?”
” Nayi shiru.” Yace yana dora hannun sa baki
” Yafi maka dai.”
” Ina su Zeenat ne? Banji duriyar su ba.”
” Zaka ji su ne ai ba dai kananan ba, ka tashi ku shiga ciki ka huta kaci abinci, sannu da zuwa.”
Tashi yayi, yabi bayan Habeeb suka wuce dakin sa suna hirar yaushe gamo, idanun sa da kunnuwan sa na jiran yaji ta inda zasu bullo, he can’t wait to see her beautiful face, ko me Anty zatayi masa kuwa ba zai fasa bawa zuciyar sa abinda ta dade tana so ba. Kishin ta daban soyayyar sa daban. Period!
****Zaman ta a bangaren Gajin yafi komai yi mata dadi, abu daya ne kawai yake dan takura ta yawan maganar Gajin, duk da haka take daurewa tana amsa mata, gashi ta manta wayar ta a kitchen bayan ta gama wankin nan, gashi taji alamar Khalil din yazo ta tabbata idan taje dauka zasu iya haduwa, ta kuma san me hakan ke nufi a wajen Mama.
Zaman ta ta cigaba kawai har sanda taji ana kiran sallar, alwala tayi ta zauna ta jira a tayar, tana jin sanda za’a tada sallar ta fita zuwa bangaren nasu, lokacin tasan sun tafi sallah Maman ma kuma ta shiga ciki tayi sallar itama, ta baya ta bi, ta shiga kitchen din a daidai lokacin da ya saka wayar a kunnen sa
“Waye?”
Yace yana gyara rikon da yayi wa kofin hannun sa, tashi zaune Moha yayi da sauri, ya kalli screen din wayar ko be kira number daidai ba? Kai Anya? Daidai yadda ta fad’a masa ne
“Fatima nake nema, ko tana kusa?” Yace jin me maganar ya sake tambayar waye a karo na biyu.
“Fatima? Malam Waye kai din da kake neman ta?”
“Sanin waye ni ba zai taba maka dadi ba, idan tana kusa ka bata zanyi magana da ita.”
” Ba zan bata ba, abun yar karfi ne kazo ka karba idan kana dashi, mtsw.”.
Yaja dogon tsaki hade da kashe wayar, kafar ta ta sako a kitchen din zata shigo domin ta karbi wayar ta da ya daga mata ba tare da izinin ta ba, muryar Mama ta dakatar da ita, ta juya da sauri ta bar kitchen din.
” Kai kuma me kake anan kana jin an tada sallah?”
“Ruwa nazo sha.”
Yace yana juyawa ya bar kitchen din, kofar bayan ta leka ta tabbatar babu komai a wajen, tayi kwafa ta juya bayan ta jawo kofar ta ciki.
Wani irin tashin hankali ne ya ziyarce shi, ya tashi da sauri yana jawo dayar wayar tasa, cikin kankanin lokaci ya birkice ya koma Captain Moh din sa na ainihi, a yau ba sai gobe ba zai juya, dan ba zai taba daukar rainin hankali ba, ba dan ganin da zai wa Bubu ba, da babu abinda zai hanashi daukar hanya a yanzu, amma dole ya hakura zuwa lokacin da ya dauka masa duk da yana ganin yayi masa masifar nisa.
Kaiwa da komowa ya dinga yi a tsakanin dakin, zuciyar sa tamkar zata hudo daga kirjin sa saboda tsabar kishi.
_WAIWAYE……ADON TAFIYA inji masu salon iya magana_*
*ZAFAFANKU BIYAR รฐลธโยฅรฐลธโยฅรฐลธโยฅรฐลธโยฅsune suka sake dawo muku da wasu nau’in QAWATATTU kuma TSARARRUN LABARAN,masu dauke da SABBIN JIGO na MABANBANTAN LABARAI masu tsuma ZUCIYA*
*_SANIN HALI…..yafi sanin kama,indai kasan TAFIYAR ZAFAFA babu dana sani ko nadama cikin zuba kudi wajen siyan litattafansu,koda jin sunan ma kasan cewa tafiyar ta dabance_*
*GWADA IDAN BAKI TABA BA!!!,HAUSAWA SUKACE SAI AN GWADA AKAN SAN NA รหWARAI,burinmu kowa ya shigo cikin tafiyar a dama dashi*
*JERIN SABABBIN LITATTAFAN NASU NA WANNAN KARON SUNE*
*_DEEN MARSHALLรฐลธโโฐรฐลธยยพMamuhghee_*
*_HALIN GIRMAรฐลธโโฐรฐลธยยพhafsat rano_*
*_TAKUN SAรหAรฐลธโโฐรฐลธยยพbillyn abdul_*
*_SO DA ZUCIYAรฐลธโโฐรฐลธยยพmiss xoxo_*
*_รล ABI’AR ZUCIYAรฐลธโโฐรฐลธยยพhuguma_*
*DUKKAN WADAN NAN LITATTAFAN รล AI รล AI HAR BIYAR…ZAKU SAMESU AKAN KUDI NAIRA 1K KACAL*
2รฐลธโโฐรฐลธยยพ400
3รฐลธโโฐรฐลธยยพ500
4รฐลธโโฐรฐลธยยพ700
5รฐลธโโฐรฐลธยยพ1000
*Zaku saka kudinku ta wannan asusun bankin*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
keystone bank
Saiku tura shaidar biyanku zuwa ga wannan number
08184017082
*IDAN KATIN WAYA NE KO VTU,SAIKU TURA ZUWA GA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYANKU*
09134848107
*_HAR KULLUM MUNA MARABA DA ALFAHARI DA MASOYANMU_*รฐลธยคยรฐลธยยฝรฐลธยคยรฐลธยยฝรฐลธยคยรฐลธยยฝรฐลธยคยรฐลธยยฝรฐลธยคยรฐลธยยฝ
#team zafafa biyar
****
1/2/22, 22:47 – Buhainat: *HALIN GIRMA*
*_Hafsat Rano_*
ร ร ร *5*
*_Last free page!_*
****
Tana zaune ta idar da sallah, bata tashi daga kan abun sallar ba taji shigowar sa shashen Gajin, gabanta taji ya fadi, tayi kamar bata ji sallamar da yayi ba, tayi tsam a kan sallayar tana kallon gabanta. Da kallo ya bi bayan ta ya samu waje ya zauna a cikin kujerun falon yana kokarin daidaita yanayin da yake ciki. Gajin ce ta fito,
“Wa nake gani kamar Ibrahim?”
“Nine nan wallahi Hajiya.”
“Lale marhabin, barka da zuwa. Saukar yaushe?”
“Dazu na shigo, mun same ku lafiya?”
“Lafiya lou wallahi, yasu Hajiyan da yan uwanka?”
“Kowa lafiya suna gaida ku.”
“Muna amsawa, sannu da zuwa.”
” Yawwa.” Yace yana yawo da idon sa akan ta,
” Iman ba magana?” Yace yana son Gajin ta tanka
“Kaji sokonci, wai bata gaishe ka ba?” Tayi maganar da sauri
“Ina wuni?” Tace a gajarce
” Lafiya lou, kina lafiya?”
Shiru tayi bata amsa ba, Gaji ta hau sababi tana mata fad’a, tashi yayi hannun sa cikin aljihu ya zaro wayar ta
“Gashi na tsince ta a kitchen.”
Ya mik’a mata sannan yayi wa Gajin sallama ya fice yana raya ta yadda zai bulowa Iman din, ya gama gane yanayin ta ba irin nasa bane, shirun ta yayi yawa amma duk da haka shi ba damuwar sa bace, yadda ya shiga zuciyar kowa a gidan nan da hakan zaiyi amfani ya kafa kansa, ba zai wani ja lokaci ba zai gabatarwa Gaji da kansa, baya jin ma zai wuce gobe, zai sai fara tuntubar Yaya Hajara idan yaga ba ta goyi bayansa ba zai yi gaban kansa, iya ka tayi masa fad’a shikenan ya wuce.ร Be koma shashen ba, sai ya fice daga gidan a kafa yana adana number da ya dauka a wayar ta ta, so yake ya saka number a truecaller yaga ko zai samu wani information akai.
ร ร
Cikin call log dinta ta shiga ta duba amma bata ga number da aka kirata ba, taji babu dadi dan bata so yaga kamar tana sane ta bayar aka daga wayar tasa. Ko da tafiyar su ba zatayi daya ba, ba zata so yaji a ransa dan yana lacking wani abu bane shiyasa hakan ta faru. Kwantar da kanta tayi a saman hannun kujerar ta rufe idon ta tana tariyo zuwan da yayi wajenta, akwai wani abu me girma a muryar sa sai kuma abu daya da ya tsaya mata shine kamshin turaren da taji yana yi, wanda yayi kama da me tsada ne irin ajin farko, domin Allah ya hore mata kaunar kamshi, shiyasa ta kan yi saurin ganewa. Sai dai akwai irin tuurare yan durin nan da suke da kamshi me dadi har ka kasa tantance su, kila irin su ne, abunda ya kara burgeta dashi kenan, duk da yana cikin yanayin da zaka ce kai tsaye babu, amma be bar kansa a wulakance ba. Juya kanta tayi daya gefen ta dora wayar a saman cinyarta ta cigaba da tunani.
***Kiran sallar magriba ya sashi fita daga sashen nasa zuwa masallaci, achan yayi alwala ya shiga sahun farko sukayi sallar. Bubu na ganin shi yaji dadi sosai. Bayan an idar ya wuce bangaren nasa domin ya jira shi, yana zaune sai gashi ko ya shigo, ya tashi tsaye har sai da ya zauna sannan ya zauna shima a k’asa cikin girmamawa ya sake gaishe shi, ya amsa masa sake yana nazarin sa.
“Muhammadu!” Ya kira sunan sa, gyara zaman sa yayi ya tattara hankalin sa waje daya cikin son ganin be yi wani abu a gaban Bubun ba
“Kana ji na Muhammad?”
“Inaji Bubu.”
“Madallah, Muhammad ka san dai a tsarin gidan nan kana cikin lokacin da ya kamata ace ka ajiye iyalin ka kaima, ka nutsu waje daya a kalla hakan zai taimaka maka wajen cikar kamalarka.”
Kansa a kasa yana jin Bubun yayi ta bayani yana gida kansa cike da gamsuwa,
**A kofar ta tsaya tana kallon takalmin Muhammad din dake zube a wajen, ta samu labarin zuwan sa a wajen Kamal amma bata tsammaci irin wannan ganawar da Maimartaba ba, shiyasa ta kasa hakuri tazo ta nemi iso wajen Maimartaba din wajen sarkin kofa amma sai ya nuna mata ba zai yiwu ba, domin an gargade shi akan barin kowa ya shiga shashen maimartaba din har sai ya kammala ganawar sa da Muhammad din, ranta a matukar bace ta koma sashen ta tana jin wani irin tashin hankali, tana tsoron kar Muhammad din ya amsa tayin mahaifin nasa a wannan zaman da zasuyi.
Safa da Marwa tayi tayi, har wajen sallar isha basu fito ba, tana hangen bangaren ta cikin nata shashen, ta kasa zama tana da yakinin ko menene suke tattaunawa haka me muhimmanci ne sosai.
Tana tsaye jikin window taga fitowar su, fuskar Muhammad din a sake yana takewa mahaifin nasa baya. Tsaki taja ta saki labulen tana juyawa zuwa gefen gadon ta, ta zauna tana sake jan wani tsakin, tsakin haushin Muhammad din da ya zame mata ciwon ido shi da mahaifiyar sa.
“Ranki ya dade, Maimartaba ya aiko yana da bukatar ganin ki bayan ya dawo sallar isha’i.”
Bata amsa ba, sai ma juya fuskar ta da tayi wani sashen tana sake sakin siririn tsaki.
***Bangaren sa ya koma, ya tattaro abunda ya san zai bukata ya fito, sai kuma ya tuna da maganar Maimartaba ta karshe da suka tattauna, yana son ganin sa da safe kafin ya fito fad’a, komawa yayi ba dan yaso ba, ya ajiye komai ya zauna yana kirga lokacin zuwa wayewar gari. Nisan yayi yawan da yake jin kamar yayi loosing idan har ya kyale shi tsawon wannan lokacin.
Wayar sa dake ajiye a gefen sa ta dauki sowwa, ya daga ganin kiran da yake ta jira ne tun dazu,
“Oga na duba maka number din, akwai bayanan sa da komai har da wajen aikin sa, hoton sa da kuma location dinsa a yanxu, na tura maka ta mail sai ka duba.”
“Ok! Thank you, zan neme ka. “
Ya katse kiran ya shiga mail dinsa, ya hau kan message din ya bud’e. Hoton sa ya bud’e yayi zooming sosai, sai kuma ya fita ya karanta information din. Karamin tsaki yaja ya ajiye wayar yana jin a ransa wannan din karamin kwaro ne be kamata ya hana shi walwalar sa ba, abu daya zai masa ya kama shi a hannun sa, sai dai ba zai hakan ba har sai ya je ya tabbatar da zargin sa.
***Anan sashen Gajin ta shirya, ta wuce islamiyya tana tafe tana satar kallon hanyar ko zata ganshi tunda yace mata yana zama ne domin yaga wucewar ta, har ta isa makarantar bata ga ko me kama dashi ba, sai kawai ta share tayi abinda ya kaita. A dawowa ma haka ta sake yi shima bata ga kowa ba, ta dawo gida ta chanja kayan ta kenan aka shigo aka ce tazo inji Muhammad, Hijab ta dora a saman kayan jikinta ta fito. A tsaye yau ma ta hange shi wajen kujerar, ya rataye hannayen sa a bayan sa yana tsaye kyam akan kafafun sa.
“Assalamu alaikum.” Tayi masa sallama tana jan kujerar.
“Sannu da zuwa, nan akwai rana bari na saka maka a chan.” Taja kujerar zuwa k’asan wata yar bishiya ta ajiye,
” Bismillah.” Tace masa tana nuna masa kujerar, be zauna ba, ya zaro hannun sa daga bayan sa, ya dawo dasu gaba ya rungume su a kirjin sa,
” Bismillah.” Ya nuna mata kujerar da baki
” Zauna babu matsala.” Yace mata
” A ah dan Allah ka zauna, be kamata na zauna kana tsaye ba, ance bakon ka…”
” Kyale fadar hausawan nan, zauna dan Allah.”
Allah da taji ya ambata yasa ta zauna a kunyace, ya zura mata ido har sai da ta dan ji wani iri.
” Na cika kallo ko? Kiyi hakuri.” Yace mata yana murmushi,kallon ta kadai yayi jin sa yake kamar yafi kowa sa’a a duniya
” Ba komai.” Tace tana gyara wayar hannun ta
” Ina wuni?” Ta gaishe shi yana dan zamowa
” Lafiya lou, sai kika jini shiru, tafiya nayi zuwa kauye Baba ya kira ni, naso ma na zo kafin na wuce toh tafiyar ce tazo a gaggauce, sauka ta kenan ma.”
” Allah sarki… Allah yasa lafiya.”
” Lafiya lou, sai godiya. “
” Ka baro su lafiya?”
” Alhamdulillah. Nagode da kulawa.”
” Ba komai.” Tace tana wasa da hannun ta.
Turo gate din akayi, Habeeb na gaba yana bin sa a baya, wani irin daukewa yaji ganin sa na neman yi. Iman zaune tare da wani suna hira, a cikin gidan kuma? Be san sanda ya isa wajen ba, sai ganin mutum sukayi a gaban su.
Wani kallo Moh yayi masa, yayi murmushi yana taune gefen lips dinsa na kasa
“Yaya sannu da zuwa.” Yace yana mika masa hannu, kin bashi hannu Khalil yayi, sai Habeeb ne suka gaisa, ya daki kafadar Khalil din
” Muje ko?”
” Yi gaba ina zuwa.” Yace masa,
“Ok.” Ya wuce ya bar Khalil din a tsaye
” Iman shiga gida.” Yace a gadarance, ta dago ta kalle shi da sauri, ya hade girar sama data k’asa tamau irin ba wasa din nan.
“My heart, ki shiga gida ki huta dama naji ba zan iya zuwa gida ban zo na ganki ba, shiyasa na taho nan kai tsaye, zan kira ki anjima ki ajiye waya a kusa dake kinji?”
Kunya ce ta kamata ta noke, ta mike da k’yar tace
“Ka gaida gida.” Sannan ta wuce ciki, tana barin wajen ya hade fuskar sa sosai.
” Da tsakar ranar nan ka taso yarinya, kazo zaka ishe ta da uban surutu, ku dama talakawa haka kuke, da kunga yar hanya sai kuzo kuce kuna so, kai kanka kasan ba sa’ar ka bace, ba sa’ar auren ka bace shishigi dai, toh ita din matata ce, ni zan aureta an gama magana, sai kaja tsumman kafafunka a koma in da aka fito, ka samu daidai da kai.”
” Zaka ga tasirin talaka da talauci kuwa, baka da ikon tsarawa kowa rayuwa, haka arziki ba wani abu bane face fitina, wadatar zuciya itace mutum…” Ya dan matso gaban sa
” Mark my word, a gaban idon ka, right under your noses, talaka zai baka mamaki, mamakiin da har ka kare rayuwar ka zaka fita daga cikin sa ba, count down dinka ya fara daga yanzu.”
” 1,2,3!” Sai na jika.
Ya juya ya fice daga gidan cikin takun da ya tsayawa Khalil a rai, cikin wani irin yanayi yayi cikin gidan yana jin yanzu ba sai anjima ba, zai yi abinda ya dace, gida be koshi ba, babu yadda za’a yi a bawa dawa.
**A tsaye ya tarar da Habib yana ganin shi yace
“Kaiko me ka tsaya yi ina ta jiran ka.”
“Abinda ka kasa yi, kana ganin kanwar ka da mutum a tsaye, kana ganin sa kaga mara gaskiya, wa ya sani ma ko dan boko haram ne da wannan uban kasumbar, amma baka damu ba kayi tafiyar ka, hakan ba daidai bane.”
Kallon sa Habib yayi, mamaki na kamashi,
” Yaushe hakan ya zama ba daidai ba khalil?”
” Habib, maganar gaskiya ina son Iman, son da ni kaina bansan adadin sa ba, zan iya komai akan na sameta, dan haka ba zan iya jure ganin ta da kowa ba, musamman mutum irin wannan da ya nuna alamun rashin gaskiya, gashi fakiri jibi shigar jikin sa, no ba zan iya ba, rakani wajen Gaji ayita ta kare.”
” Idan har kai din jinina ne, idan har na isa da kai babu kai babu Iman Khalil, na rasa kafiya irin taka, na rasa dagiya irin taka, bayan maganar nan mun dade da gama ta, na gaya maka ba zai taba yiwuwa ba.”
” Akan me? Dan Allah Anty ki gaya min hujja me karfi a musulunci da ya haramta min auren ta, na daya ni ba muharraminta bane tunda ita din ba ke kika haife ta ba, toh sai menene? Akan dalili mara tushe?”
” Akan duk abinda zaka kira shi Khalil ka kirashi, amma idan har ina numfashi ba zamu hada jini ba wallahi, ga mata nan bila adadin, me yasa sai ita, wannan da yazo shi ya dace da ita, shine daidai da matsayin ta, inaso auren da zatayi ya zama sakayyar aure min miji da uwarta tayi, ta saka yayana samun yan Uba!.”
” Ohh shit! Kin kasa fuskanta ta Anty, kiyi hakuri wannan karon zabin raina zan bi, zanje na samu Gaji na sanar da ita, gwara kowa ya sani a san me yakamata ayi.”
” Khalil!”
Ta k’wala masa kira, ya juya da sauri yayi hanyar fita, wayar sa tayi kara, ya tsaya chak jin layin da yake ajiye numbers din manyan mutanen sa ne, ciro wayar yayi sunan Sir ya bayyana a wayar, ya daga da sauri yana daidaita numfashin sa
” Kana ji Ibrahim? Sako ne daga sama ba daga ni bane, an dakatar da kai aiki zuwa wani lokaci, za’a neme ka idan bukatar hakan ta taso.” Be jira yace komai ba , ya katse kiran. Da sauri ya dafe bangon da yake kusa dan ji yayi jiri na neman kadashi, gaba daya rayuwar sa akan aikin ta dogara, yana da passion sosai a Kai sannan yana iyakar kokarin sa wajen aikin sa, maganar promotion dinsa ma ake idan har ya kammala wannan assignment din da ya kawo shi Kano, shikenan sai dakatarwa haka nan ba wani dalili?
” Ya akayi?! Habib ya matso ya taba shi ganin kamar ya shiga coma
รฐลธโยฅรฐลธโยฅรฐลธโยฅรฐลธโยฅรฐลธโยฅ
*_LAST BONANZA_*
*_farincinku shine namu,ZAFAFAN DAI,sun sake amsa kokenku,sun sake rage muku kaso 20 cikin 100_*
*_Daga yau 29 ga wata,har zuwa 31 ga watan nan,xaku iya biyan 800 a amadadin 1000 na kudin litattafai biyar_*
*_za’a fara posting in sha Allah 1st January da yardar Allah_*
*HANZARTA KI BIYA NAKI KAFIN RANAKUN SU QARE*
*XAKI BIYA TA WANNAN ACCOUNT NUMBER DIN*
6019473875
MUSAA ABDULLAHI SAFIYA
SAIKU TURA SHAIDAR BIYA
08184017082
GA MASU TURA KATIN WAYA KO KUMA VTU,SAIKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYANKU
GIPHY App Key not set. Please check settings