Lu’u lu’u 1

Advertisement

*1*

 

*K’ASAR TEXANDA*

*09/07/2000*

 

Shekara ta 2000 (dubu biyu) ita ce shekarar da wasu suka dinga farfagandan cewa za’a tashi duniya, sai dai lamarin Ubangiji ya fi da haka, dan a lokacin da ake taradaddin za’a bar duniyar, a lokacin ne kuma wasu ke zuwa duniyar, wasu kuma a lokacin suke bayyanuwa a duniyar ma, daga ciki kuwa akwai bayyanar cikin *haske marar iyaka* ga Juman.

*MASARAUTAR KHAZIRA*

 

A hankali ta bud’e idonta akan rufin d’akin mai kalar sararin samaniya, lumshe su ta sake yi sannan ta sake bud’ewa dai a kan rufin, cikin nauyin jiki ta juyar da kan ta b’angaren da take da tabbacin nan sarkin na ta ke kwantawa, kasancewar ta mace ta farko a gareshi saidai akwai k’wark’warori da yake zuwa garesu duk sanda ya so. Wayam ta ga inda yake kwancin wanda hakan ya tabbatar mata da lallai ya kai wa wata baiwar ziyara.

A sanyaye ta mik’e zaune akan gadon tana mayar da dogon gashinta baya, dafe goshinta tayi a hankali ta shiga tariyar mafarkinta, ko kuma tace mafarkanta dan yanzu kam abun har ya fara zama mata jiki, wata hud’u kenan da take yawaita wad’anan mafarkan, indai har zata rintse idonta da sunan bacci, to tabbas zatai mafarkin wannan yarinyar mai abun al’ajabi.

Advertisements

D’aga kan ta tayi tana huro iska tare da mik’ewa tsaye, wasu sauk’akk’in takalmi ta saka dake gefen gadon, hannu ta zura ta d’auki doguwar rigar baccinta fara tas mai zubi da alkyabba ta saka ta nufi hanyar fita, a falo na farko babu kowa babu komai sai kayan d’akin da suka k’awatashi, tana bud’e d’aya k’ofar dogarin dake tsaye yayi saurin sunkuyar da kan shi k’asa, ba yabo ba fallasa ta kalleshi tace “Ka je b’angaren hadimai ka kira min *Habbee*.”

Sake sunkuyawa yayi yace “Angama sarauniya ta.”

Falon na farko ta dawo ta zauna k’afa d’aya kan d’aya tana jiran isowar Jakadiyar ta ta da tafi aminta da ita, bugu da k’ari suna sirri su kashe su binne a tare.

Jim kad’an sai ga dogarin ya k’wank’wasa k’ofar tare da bud’ewa a hankali, tsaye yayi gaban k’ofar ya rusuna yace “Sarauniya ta, Jakadiya Habbee ta amsa kiranki, tana neman izinin k’arasowa gareki?”

Da hannu ta masa alamar za ta iya shigowa batare data kalleshi ba, juyawa yayi rike da doguwar sandar shi, sakan (second) k’alilan dattijuwar ta shigo da girmamawa da kuma rusuna kan ta k’asa, saida ta zauna k’asa gabanta tace “Uwar-gijiyata, fatan tsawon rai da lafiya d’orarriya, na zo da hanzarina domin son sanin abinda ke damun sarauniyata da har ya hanata bacci a tsohon daren nan.”

Sauke k’afarta tayi daga kan d’ayar sannan ta d’ora gwiwar hannayenta a kan cinyoyinta ta tallabe hab’a, kallon Jakadiyar tayi cike da damuwa da alhini tace “Jakadiya.”

Da sauri ta amsa da “Na’am ranki shi dad’e.”

A sanyaye tace “Ina shiga damuwa sosai akan mafarkin nan nawa, gashi malaman gidan abun bauta ma sun kasa fassara min mafarki na, shi ne dalilin da yasa na kiraki dan ki bani shawara, me ye abun yi?”

Sunkuyar da kai ta sake yi ba tare da sun had’a ido ba tace “Uwar-gijiyata indai har yanzu kina mafarkin nan, to fa abun yi shi ne mu nemi sanin fassararsa, ina ga zaifi ki je ki ga babban malamin gurin bauta kai tsaye.”

Kallonta tayi ta sauke numfashi tace “Hakan zai fi ko?”

Jinjina kai tayi tace “Hakan shi ne mafita ranki shi dad’e.”

Yatsina fuska tayi tace “To amma fa Jakadiya kinsan babban malami yana da kusanci da sarkina, duk tattaunawar da zamuyi dole sarki zai san komai, ni kuma ina tsoron kar mafarkina ya zama na sharri.”

Advertisements

Girgiza kai Jakadiya Habbee tayi tace “Babu abinda zai faru uwar-gijiyata, mafarkinki alkairi ne.”

Ajiyar zuciya ta sauke tace “Shikenan, da sassafe zamu je mu gan shi.”

Cikeda girmamawa ta amsa mata da “To ranki shi dad’e, ni zan koma, a kwana lafiya.”

Da ido kawai ta amsa mata kafin ita ma ta mik’e tana turo d’an k’aramin bakinta ta koma makwancinta, kuma har lokacin sarki Musail bai dawo ba.

Washe garin ranar litinin 10/07/2000 sarauniya Juman ta isa wurin bautar dake nesa da masarautar Khazira dan had’uwa da babban malamin fadar wato *Dhurani*, tsaye yake a gabanta hannayrnshi akan had’e kusa da cikinshi yana kallonta, yayin da take zaune akan kujerar katako doguwa kan ta k’asa, dan yana da matuk’ar girma a k’asar ta yanda wasu abubuwan shi ke ba wa sarki Musail shawararsu kafin ya gabatar, cikin kulawa a harshen slovaque yace “Sarauniya ta, me ye mafarkin na ki?”

Ba tare data d’ago kan ta ba ta shiga girgiza kai tana bud’a baki kamar za tayi magana kuma damuwa da tsoro na hanata, a sanyaye ta d’aga kai ta kalleshi tana yatsina fuska tace “Babban malami, mafarkin nan yana damuna, kuma kullum kusan kala d’aya ne, yarinya da bata fi shekara biyar ba a duniya, amma sai na ganta a kan kujerar mulki cikin shiga irin ta sarakai, abun al’ajabi shi ne, idonta da kuma haskenta mai matuk’ar d’aukar ido, wannan hasken ya isa ya haskaka garin nan da kewayensa, kayan jikinta ma ban tab’a ganin wani gawurtaccen sarkin daya tab’a saka ko da kwatankwacin irinsu ba, suna da d’aukar hankali da k’yalk’yali tamkar madubi.”

Sake kafeshi tayi da ido tace “Babban malami, wasu lokuta a saman ruwa nake ganinta tana tafiya, kuma kullum k’ok’arin bani hannu take tana fad’a min wai na kawo hannuna ta cece ni, na…na rasa gane… Wannan abun, na rok’eka kayi wani abu a kai ba tare da sarki ya ji.”

Tunda ta fara magana Dhurani ya tsura mata ido yana kallo, tabbas wani yanayi ya shiga da asalinsa b’acin rai ne musababbin sa da tashin hankali, da sauri ya juya ya shige wata k’ofa dake cikin wurin bautar ya rufo, gaban wani teburi ya k’arasa ya bud’a wani k’aton littafi dake gabanshi, dama yana ajiyar wurin saboda jiran wannan ranar, sake karanta wurin yayi a k’alla ya maimaita ya fi sau goma kafin ya rufe.

D’aga kan shi yayi ya kalli rufin d’akin goshinshi na tsatsafo gumi, lumshe ido yayi yana tunanin mafita akan bala’in dake shirin tunkarosu, da sauri ya bud’a ido skamakon jin wata shawara da zuciyarshi ta yanke mishi, sauke kan shi yayi k’asa ya sauke nannauyen numfashi ya juyo hannunsa rik’e da littafin yana murmushin mugunta ya fito.

Sarauniya Juman da tunda ta ga ya bar ta nan ta shiga tashin hankali da jin cewa lallai mafarkinta ba alkairi bane kamar yanda tayi zato, mik’ewa tayi ta juya a sanyaye zata bar wuri dan Habbee na bakin k’ofa tana jiranta, fitowarshi tasa ta juyawa sai kuma ta tsaya, sake nuna mata wuri yayi inda ta tashi yace “Zauna sarauniyata.”

Komawa tayi ta zauna tana kallon shi a raunane tace “Babban malami lafiya ko?”

Murmushi yayi yace “Lafiya lau, karki damu.”

Kujerar dake gefenta ya zauna yana kallonta yace “Ita wannan yarinya da kike gani a mafarkinki, *’yar da zaki haifa ce* wato *Zafeera*, ma’ana haske marar yankewa.”

Mamaki ne fal a kan fuskarta inda ta shiga jujjuya kan ta, da k’yar ta kalleshi tace “Zafeera? ‘Yar da zan haifa? To amma ai…”

Da saurita kalleshi kuma tace “Yaushe?”

Wani murmushi yayi yace “Ai fara mafarkinta da kikayi alamu ne na cikinta na jikinki.”

Dafe mararta tayi mamaki bai bar fuskarta ba ta sake fad’in “Amma kuma ban ga wani alamu na samun ciki ba, a k’alla wata hud’u dana fara mafarkin nan, idan har haka alamu ne na samun cikin ta, to fa ina ganin jini a kowane wata, ta ya haka zata kasance? Bayan cikina na farko ban ga haka ba.”

D’aga mata hannu yayi a hankali cike da izza ya mik’e tsaye ya fuskanceta yace “Sarauniya Juman, kakan kakana ya kasance zab’abb’e ne ga abun bauta *Ghira*, shi d’in ya kasance d’an baiwar da ba’a tab’a samun kamar sa ba bayan shud’add’un wasu shekaru, mu malam gurin bauta mun yi amanna cewa k’arni bayan k’arni lokaci bayan lokaci abun bauta Ghira yana bijiro da wani zab’abb’e a cikin bayinsa, kakana ya fad’a min sanda kakansa ke gargarar mutuwa ya ambaci wata zab’abb’iya da zata zo mana bayan wani k’arnin, kin ga nan?”

Ya fad’a yana mik’a mata k’aton littafin nan sannan ya ci gaba da fad’in “Ya suffanta mana alamun bayyanarta, zata kasance ‘yar baiwa da kowane motsinta zai ba wa mai hankali mamaki, idonta masu matuk’ar ban tsoro da birgewa ne ga ma’abota kallonsu, sannan ki sani wannan ‘ya da zaki haifa zata zama mafari ga sabon canjin k’asar Texanda baki d’ayanta. Dan haka ‘yar ki ta samu sunanta tun kafin ki haife ta, *Zafeera*, ko kuma ki kirata da *LU’U LU’U*.”

D’auke idonta tayi daga kan littafin ta kalleshi a matuk’ar tsorace tace “Amma babban malamin, me ye manufar ganinta cikin kaya kamar na sarauta?”

Juya mata baya yayi dan baya son fad’a mata gaskiya sannan yace “Alamu ne na ita ce abun bauta Ghira ya zab’a a cikin zab’abb’un sa, sannan zata zama mai daraja a cikin al’umma.”

Numfashi ta sauke ta ci gaba da kallonshi tace “To kuma me yasa take mik’o min hannu tana fad’a min zata taimake ni?”

Da sauri ya juyo a hassale yace “Sarauniyata ya isa haka, kada ki tsananta tambaya a cikin lamarin ubangiji, ki je gida sannan ki yi shagali tare da farin ciki na zab’arku a cikin masu daraja.”

Lumshe ido tayi a sanyaye ta mik’e tare da aje masa littafin akan kujerar ta juya tana mai d’an rik’e k’asan rigarta saboda jan k’asa da take yi, a sanyaye har saida ta kai bakin k’ofar ta saki ‘yar rariyar dake rufe mata fuska a matsayinta na matar sarki, Habbee da dogaran suna ganinta suka sunkuya suna mata barka da fitowa, a sanyaye ta k’arasa bakin dawakai guda biyun da aka k’awatasu da abun zama aka musu rumfa, shiga tayi ta zauna sai Habbee data zauna daga baya akan wani siddi dake bayan dawakan sannan suka bar wurin.

*MASARAUTAR GIOBARH*

Da sauri ya ja ya tsaya a in da yake sakamakon ganin sarkin da yayi tare da iyalinshi, sunkuyar da kai yayi sosai tare da had’e hannaye alamar girmamawa yace “A gafarce ni ranka shi dad’e.”

A mugun dak’ile cikin yatsina fuska ba tare da ya kalli dogarin ba ya ci gaba da ciyar da uwar gidan ta shi wacce ke kwance bata motsi. Matashiyar matar da ke gefenshi a tsaye rik’e da faranti ce ta kalli dogarin cikin harshen galloi tace” Lafiya? ”

Sunkuyar da kai yayi alamar risinawa sannan yace” Ranki shi dad’e, dama boka *Kasur* ne ya zo kuma ya tabbatar mana lallai sarkina ya ke son gani yanzu.”

A sanyaye matar ta kalli sarki *Wudar* saidai ba tace komai ba, d’an satar kallonta yayi kafin ya sauke numfashi ya sake maida hankalinshi kan uwar gidan shi ya sake mik’a mata lomar abinci, cikin rawar kai kamar wacce lantarki ya kama ta bud’a bakinta ta karb’a har rabi na zubewa, tissue ya d’auka ya goge mata baki sannan ya mik’awa matar nan farantin abinci.

Mik’ewa yayi tsaye ya juya ya kalli dogarin yace “Yana ina?”

A ladabce yace “Yana masaukin bak’i shugaaba na.”

Numfashi ya kuma saukewa sannan ya juya ya kalli matar nan yace “Ki kula da ‘yar uwarki *Joyran*, ina dawowa.”

Da wani kallo mai wuyar fassara ta raka bayanshi tare da sakin murmushi, saida ta ga fitarsu ่„ฟ d’akin ta kalli matar da ke kwance.

Babban farantin ta ajiye a kan wani dogon desk kafin ta zauna kan gadon gefen matar, fuskar alhini ta nuna sosai idonta tap da k’walla ta rik’o hannunta da ko motsashi ba tayi, cikin muryar jimami tana kallon k’wayar idonta tace “Sarauniyata, kuma ‘yar uwata *Kossam*, hak’ik’a ina matuk’ar jin rad’ad’in wannan ciwon naki, ina ma a ce ina da maganin cutarki? Tabbas da na sadaukar da duk abinda na mallaka dan samun lafiyarki,’ yar uwata ki ci gaba da hak’uri kin ji, wannan ciwon jarabawa ce a gareki, ki tuna wani abu d’aya yayata, da a ce yau wanda ya zama sanadiyar shigarki halin nan yana duniya, na tabbata da zai fi kowa shiga damuwa na halin da kike ciki.”

Nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da k’ara jimk’e hannunta tace” Kossam, hakan da nake ba dan bana k’aunarki bane, saboda ceton rayuwata nake haka, amma ina baki tabbacin komai ya kusa zuwa k’arshe.”

Muskutawa tayi kafin ta mik’e tsaye tana goge ‘yar k’wallar da suka tarar mata, kallon Kossam tayi tana fad’ad’a murmushi tare da fad’in” Yar uwata, ni zan koma b’angare na, sai na dawo baki abincin ranarki.”

Tana fad’a ta juya da saurinta ta bar d’akin inda doguwar rigarta ke jan k’asa sosai. Hadimar da ta gani ่„ฟ k’ofar d’akin ya saka ta k’are mata kallo, cikin wurga mata harara tace” Kossam ta ci abinci yanzu, idan za ta ci anjima ่„ฟ kirani na bata.”

Da girmamawa ta amsa mata da” Angma ranki shi dad’e.”

Cikin sauri ta k’arasa fita tayi b’angarenta, hadimar kuma da kallo ta bita sannan ta murgud’a baki ta bud’a d’akin ta shiga tana fad’in” Sarauta, kamar mu d’in musakai ne da ba zamu iya bata abincin ba dole sai ita.”

*Masaukin bak’i*

Bayan sarki Wudar ya zauna akan babban kujera ne ya tambayi bokan na shi me ke tafe da shi? Da sauri ya mik’e tsaye cike da zumud’in son sanar da shi abinda ke tafe da shi ya fara da fad’in” Shugaba na, labari nake tafe da shi wanda zai sa ka farin ciki, labari ne da nake da tabbacin zaka min kyautar da baka tab’a kwatanta yi ma wani ita ba.”

Cike da k’asaita da izza irin ta mulki sarki Wudar ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya yana k’arewa boka Kusar kallo, kamar mai ciwon baki ya d’aga labb’an shi yace” Ina jinka.”

Wangale baki yayi yana dariya yace” Sarki na, ka tuna zab’abb’iyar da mu ka maka bayani zata zo a zamanin mulkinka?”

A zabure sarki wudar ya sauke k’afa d’aya yana zaro ido yace” Taya kake tsammanin daidai da sakan d’aya zan iya mantawa da lamarin yarinyar da ku kuka bani tabbacin ita ce ci gabana ? Kai fa ka fad’a min inhar na sameta to ni zan dama mulkin da ya fi na *Alexandre* ma, kana ganin akwai wani mutum da baya son ci gaban rayuwarsa ne ? Ko kuma zan zauna na zama shashashan sarkin da ba zai so dawwama a mulki ba ?”

Sunkuyar da kai yayi yace” Ran sarkina ya dad’e, ba haka nake nufi ba, ina son maka tuni ne saboda abinda na zo da shi.”

Gyara zamanshi yayi yana hura hanci tare da fad’in” Je ga gundarin magana.”

Rusunawa yayi alamar girmamawa da kuma amsa buk’atar sarkin, d’aga kanshi yayi ya kalli fuskar sarki Wudar saidai bai had’a ido da shi ba saboda kwarjini, cikin nutsuwa ya fara fad’in” Sarkina, yarinyar da muka tabbata zata zo ่„ฟ tarihi, kuma muka samu yak’ini ita ce silar duk wani ci gaba na ka da na ‘yan k’asar nan, yarinyar da kyawunta zai wadaci masarautarka da kewayenta, yarinyar da haskenta zai mamaye gaba d’aya k’asar Texanda, yarinyar da shek’inta tamkar na *Lu’u lu’u*, tana kusantoka, dan bincikenmu ya nuna mana da taimakawar abun bauta cewa ba shakka cikinta ya bayyana, za’a haifeta yayin da zamuyi murnar cika shekara ta dubu biyu, sannan mu fara lissafin lokacin da tarihin garinmu ya fara canzawa izuwa shekara ta dubu biyu da d’aya.”

Da sauri sarki Wudar ya tashi tsaye yace” A wacce k’asa za’a haifeta? Wacece mahaifiyar *’ yar baiwata*?”

Rarraba ido ya fara yi tare da fad’in” E to, sarkina saidai akwai wasu yan matsaloli da muka gano a game da hakan.”

A tsawace rai b’ace yace” Ban damu ba, ban damu da kowace irin matsala ba, abinda na sani kawai shi ne zan kashe duk wanda yayi k’ok’arin shiga tsakanina da cikar burina, dan haka ina jinka?”

Jiki a sanyaye yace” Shugabana, yarinyar za’a haifeta a masarautar sarki *Musail*, sarauniya *Zeyfi* ita ce mahaifiyar yar baiwarka.”

Wata arniyar dariya sarki Wudar ya bushe da ita tare da fad’in” Lallai boka Kusar baka da hankali, shin ka manta tsakani na da sarki Musail ne? Gaba ce marar iyaka, kuma a yanzu na samu damar da zan d’auki fansa a kan shi, duk da na sani hakan ba k’aramin jan aiki bane, amma akan cikar burina babu abinda zan yarda ya gagareni, zan auri ‘yarsa a gaban idonsa idan bai kawo min tangard’a ba, idan kuma yayi taurin kai to zanyi shirin yak’i da shi, zan kashe shi da hannuna sannan na mayar da matarshi baiwata ma’ana surukata,’ yarsa kuma zata zama matata a zahirance, a bad’ini kuma ita d’in *nasara* ce ga k’asata. ”

Tsawon lokaci sarki Wudar da boka Kusar suka d’auka suna tattauna kafin daga bisani su rabu zuciyar sarki Wudar na sake narkewa da mutuwar son zab’abb’iyarshi.

*31/12/2000*

*12:01* Yayin da milyoyin duniyoyi suke murnar tsallake shekarar fargaban za’a tashi duniya, a kowace k’asa an kacame da murnar shiga sabuwar shekara, a daidai lokacin Zafeera ta kutso duniyar ba tare da sanin wacece ita ba bare tasan manyan k’alubalen dake jiranta, a zahirance kam soyayya tsagwaronta ake nuna mata, saidai hatta mahaifiyarta da mahaifinta suna da na su nufin dake k’unshe ่„ฟ cikin zuk’atansu ่„ฟ game da ita, haka ma yayarta wacce aka haifa kafin ita mai sunan *Zafreen*, kama daga fadawan dake cikin gidan zuwa masarautun dake kewayensu babu wanda baisan da labarinta ba, saidai kad’an ne ke da kyakyawan k’udiri ่„ฟ kan ta.

*Babban* tashin hankalin da aka fuskanta a lokacin bai wuce b’atan yarinyar da aka haifa ba awa d’aya data wuce ba, an nemi Zafeera an rasata k’asa ko sama, hankalin kowa a masarautar ya tashi musamman ma na sarki Musail wanda babu wanda yasan asalin sahihiyar nuna damuwarshi akan yarinyar sai jakadiyarshi da kuma malamin fada Dhurani.

A wannan rana a masarautar Khazira kowa baccin tsaye yayi, dan kuwa gida gida sarki yasa ana duba masa yarinyar shi tare da hadimansa guda biyu da aka nema a lokacin aka rasa, wannan yasa ya ta’allak’a b’atan yarsa da su, kuma yayi alk’awarin kashesu idan ya samesu.

*Alhamdulillah*

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

YAU DA GOBE 5 & 6

Advertisement  ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ   ๐ŸŒนYAU DA GOBE ๐ŸŒน ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐ŸพStory & writing by mmn fareesa ๐Ÿ…ฟ๏ธ5&6 Wannan shafin na y’an…