Lu’u Lu’u 10

Advertisement

*10*

 

Ko da ta saka wayar sai bata ga tayi alamar ta d’auka ba, ta jima zaune tana son ta ga wayar ta nuna mata tana d’aukar cajin, Deeyam da suke zaune kan gado suna jiran 12:00 ta yi ne tace mata “Dan Allah ki rabu da wayar nan ki zo, mu ji me kike shiryawa?”

Cike da damuwa tace “Wayar nan ce ta k’i d’auka fa.”

Sabrine ce tace “Ki kunnata mana ta yiwu ta d’auka.”

Jinjina kai tayi ta danna wayar dan kunnawa, Deeyam ce tace “E lallai, irin wannan damuwa haka, da alama fa akwai k’amshin wani abu tsakaninki da malam Umad.”

Ganin wayar ta kama kuma lallai ta fara d’aukar cajin yasa ta mik’ewa ta nufosu tana tab’e baki tace “Kinji wani banzan tunani kuma, malamin na wa?”

Tsaki tayi ta zauna tana fad’in “Ba zan iya had’a hanya da mai saka uniform ba, dama dai shi d’in joker ne ko kuma mai aikin gidan zoo, zai fi armashi.”

Bushewa sukayi da dariya sai Deeyam da tace “Ke kuma ki rasa wanda kike son yin rayuwa da shi sai wanda bai kai komai ba.”

Sabrine ce tace “Ba ma wannan ba, me yasa take son auren irin mutumin nan?”

Advertisements

Zuba mata ido sukayi, numfashi ta sauke sannan ta kalkesu dukansu tana murmushi tace “Saboda ina so na rayuwa kusa da dabbobi, ina son ganinsu a kewaye da ni.”

Gyara zama tayi tace “Ba wannan ba, yanzu me kuka shirya min ne na ga kuna ta b’oyo d’azu har da korata a d’akin nan.”

Da sauri dukansu suka ce “Ba komai.”

Da kallon tuhuma ta bisu tace “Kun tabbata?”

“E.” Suka fad’a a tare, tab’e baki tayi ta mik’e ta nufi gadonta ta kwanta tana fad’in “Da 12:00 tayi ku tasheni.”

“Ba ma sai kin fad’a ba.” Cewar Deeyam, dan suna son bata mamaki kamar yanda ita ma take basu idan irin wannan ranar ta zo musu, Ayam k’awa ce da kowa zai yi fatan samu, zata tsaya maka idan buk’atar hakan ta tashi, idan kana da kad’aicin yan uwa ita ta kan maye maka wannan gurbin, idan kuma maraici kake fama da shi zata mantar da kai shi, duk abinda take da tana baka ba tare d tunanin yawanshi ko darajarshi ba, haka kuma zata iya tare maka duk bala’in dake neman tunkaroka iya k’arfinta, kamar dai yanda tayi a kan Sabrine tsakaninta da Zafreen.

*12:57* ta d’an fara juya kan ta tana motsawa kamar zata farka, sam mafarkin da take yi bata jin dad’inshi, yatsina fuska take yi duk da a cikin bacci take, a can k’asan mak’oshi cikin bacci take fad’in “Ku daina, ku daina azabtar da ita, ku daina.”

12:00 a daidai kunnenta suka taru su uku suka d’aga murya wajen fad’in “Barka da zagayowar ranar haihuwa.”

A mugun zabure ta tashi zaune da k’arfi tana zazzaro ido a tsorace, Deeyam ce tace “Ke mu ne fa.”

Kallonta tayi kamar bak’uwar hallita a hankali ta fara saisaita nutsuwarta, shafa kan ta tayi ta sauke ajiyar zuciya tace “Oh, thanks.”

Wani k’aton cake suka aje mata gabanta suka fara tafawa suna mata wak’ar murnar k’ara shekara, bushe wutar tayi sannan ta yanka cake d’in, a bkin Deeyam ta fara sakawa sannan ta saka a bakin Sabrine da d’ai k’awar ta su, dukansu ma yankawa sukayi suka saka mata a baki sannan suka dangwala suka shafa mata a fuska, daga haka suka haukace inda suka dinga d’ibar cake din suna shafawa junansu suna ta dariya suna tsalle akan gadon cikin nishad’i, dan iya daren garesu kawai da zasu iya yin wannan farin cikin, idan ba haka ba babu lokaci zuwa wayewar garin.

Wata babbar kwalba Deeyam ta d’auko ta lemu mai tsadar gaske sai ka ce barasa, saida ta girgizashi sannan ta bud’e duk ya pallatsar musu a jiki, kowa kofin tangaran ya mik’a ta zuba mi shi, suna tsaka da sha suka ji vibration na waya, a tare suka juya hakan yasa Sabrine cewa “Tun d’azu fa ake kiran wayar nan.”

Advertisements

Deeyam yace tace “Watak’ila kiran ujila ne, ko wani abu mai mahimmanci.”

Lek’a wayar Ayam tayi ta ga lambar an rubuta sunan *Ffrind* (aboki) da yaren Gallois, d’auke kanta tayi tace “Ku manta kawai, abokinsa ne.”

Mantawar sukayi kamar yanda ta ce, saidai tuni aka sake kiran hakan ya katse musu shagalinsu, Deeyam ce tace “Ayam me zai hana ki kashe wayar nan, idan ba haka fa ba zamu huta ba.”

D’an k’aramin tsaki tayi tace “Haba, malam ka kira sau d’aya ka ji ba’a d’aga ba kayi na biyu har da na uku, me zai hana ka shafawa mutane lafiya?”

Sabrine ce tayi saurin fad’in “A’a fa Deeyam, ni ina ga da d’agawa mukayi ko kuma dai ta je ta kai masa wayar, ki tuna fa akwai ujila a rayuwa, muka sani matarshi ce ko kuma mahaifiya ko mahaifi.”

Cike da gatse Ayam tace “Ke ki je mana tunda ke ce matarsa d’in.”

Murmushi tayi tace “Babu inda zan je in fad’a miki, ke zaki je tunda ke ya bawa wayarsa.”

Deeyam ma cewa tayi “Gaskiya ne, ki je ki kai masa to.”

Tsaki tayi ta kalli jikinta sai kuma ta kallesu, sauka tayi daga kan gadon ta d’auki wayar ta nufi hanyar fita, Deeyam ce tace “Akwai sanyi fa a waje, ki saka rigar sanyi mana.”

“An k’i.”Ta fad’a kai tsaye tana ficewa a d’akin, da kallo suka bi d’an k’ugunta da baya juyawa saidai dake tana da k’ira ba zaka gane komai ba.

Likitar dake daf da k’ofar shigowa ma’ana sai ka bi ta kan ta zaka wuce tana ganin Ayam ta murje idonta daga baccin dake son d’aukarta daga zaune, ba alamar girmamawa tace “Ke ina zaki je yanzu a daren nan?”

Kallonta Ayam tayi tace “Zan je gurin yallab’ai ne.”

“Me zaki je yi?” Ta fad’a a gatsalce, gyara tsayuwa tayi tace “Dama kina zaune a nan ne dan tambayar abinda zai shigar da kowa nan?”

Mik’ewa tayi tsaye cikin hassala tace “Ke bana son shashanci banza, ya zama dole na san me zai shigar da ke ciki, idan ba haka ba kuma ki koma.”

Matsowa tayi ta tsaya gabanta cikin gadara ta rumgume hannayenta, zuba mata ido tayi kamar zata had’iyeta tace “Kika ce saidai na koma?”

Haka kawai tsigar jikinta ta tashi ta ji ta kasa jurar kallonta, samun kan ta tayi da rusuna kan ta tace “Kinyi sa’a yau bana jin bala’i, da…”

Kasa k’arasawa tayi sai kawai ta kalli k’irjin Ayam tace “Shiga kawai.”

Sama da k’asa Ayam ta galla mata harara ta wuce, tana shiga zaune ta sameshi yana kurb’an coffee a farin kofin tangaran.

Bud’a k’ofar da tayi ce ta ja hankalinshi zuwa kan ta, yanda ya so yi mata kallo d’aya sai abun ya ci tura ya kuma gagara, bai d’auke idonshi daga kan samb’ala samb’alan cinyoyinta ba wanda suke a cikin fari kuma gajeran wando iya cinyoyinta, haka ma rigarta fara ce mai siraran hannaye, kan ta kuma yanzu babu komai a kai face launin gashinta mai kalar maroon da d’an ratsin yellow yellow.

Gabanshi ta tsaya cike da shak’iyanci sakamakon lura da kallon da yake mata tace “Wato na maka kyau ko? Saboda ka ganni a hakane? Ai dama ni d’in kyakyawa ce.”

Cikin jin kunya da takaicin kan shi ya duk’ar da kai yana fad’in “Me ya kawoki kuma? Ko dai kin gagara bacci ne a dalili na?”

Yatsina fuska tayi tace “Tabb’! Akan me ni kuwa zaka dameni?”

Ziiii! D’in da wayarsa dake hannunta tayi yasa ta mik’o masa tace “Uhum ka gani, wannan abokin na ka ne ya addabi mutane, a gakiya mutumin nan da ina da wani iko a hannu na dana sa an d’aure min shi, haba mutum sai takurar tsiya.”

Duk tana maganar shi kuma yana kallon bakinta ne, saida ta dasa aya ya karb’i wayar ya duba sunan, kallonta yayi yace” Nagode to zaki iya tafiya, amma ki sani zan tuna miki wata rana.”

Da mamaki tace” Me zaka tuna min?”

Girgiza kai yayi alamar ba komai, sannan ya lumshe mata ido ya bud’e alamar tafi, baki ta bud’e da matsanancin mamaki tace” Kai! Ni zaka kora da ido? Na rantse babu inda zan je sai ka min magana da baki, kaji ka kamar wani sarkin gaba d’aya k’asar Texanda.”

Wani malalacin murmushi yayi yace” Kenan dole sai nayi magana da baki?”

D’aga kafad’a tayi tace” Haka kawai na ji bai min ba da ka min magana da ido.”

Girgiza kai yayi saboda fara hawa masa kai da tayi ya nuna mata k’ofa yace” To ta fi.”

Zura dogayen k’afafunta ta fara yi ta masa bye bye tace” Saida safe.”

Saida ta kai daf da k’ofa zata fita yana k’are mata kallo yace” Barka da zagayowar ranar haihuwarki.”

Juyowa tayi da fara’arta tace” Merci beaucoup.”

Juyawa tayi ta fita a d’akin saidai kafin ta rufe kofar ta sake kallon shi, murmushi ta sakar masa tace” Halinka ya had’u yallab’ai, kai mutumin kirki ne.”

Rufe k’ofar tayi ta fice shi kuma bai san sanda ya saki k’ayataccen murmushi ba har saida ya ji an sake kiran wayar, yana d’agawa cikin jin haushi Haman yace” Haba Umad, me ye haka dan Allah? Ya zanyi ta kiranka akan abu muhimmin amma baka d’aga min waya? Tun yamma fa nake kira.”

Cikin rashin jin dad’in rashin kyautawa yace” Kayi hak’uri Haman, wallahi na samu wani d’an had’ari ne sakamakon shigarmu jeji, amma da sauk’i yanzu.”

Cikin kulawa har ya manta da b’acin ranshi yace” Subhanallah, me ya sameka Umad? Kana ina yanzu?”

Girgiza kai yayi ya aje kofin hannunshi yace” Ba komai karka damu, na ji sauk’i yanzu ai, fad’a min ya ake ciki daga wajenka?”

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yace” Umad munyi nasara da yardar Allah, adreshin unguwa da lambar gidan da gimbiya Zafeera take duk yana k’wak’walwata.”

Da k’arfi ya sauka daga kan gadon yace” Da gaske Haman? Ka samu? Ina take?”

Cikin farin ciki yace” E na samu, kuma abun farin cikin tana cikin garin da kai ma yanzu kake kamar dai yanda kayi hasashe tun farko.”

Cike da k’aguwa da zumudi da farin ciki yace” Da gaske Haman? A ina take? Ban adreshin?”

Murmushi yayi yace” Na yi tunanin haka dama, na so zuwa garin yau amma na ga zanyi dare.”

A k’age yace” Haman ba wannan na tambayeka ba, ina ne adreshin da zan sameta? Zan yi sammako na je na had’u da su.”

Dariya Haman yayi yace “Bayan kassuwar Buffar, gida mai lamba 115, amma Umad…”

Bai barshi ya k’arasa ba yace “Nagode Haman, zan kiraka zuwa safe.”

K’it! Ya yanke kiran ya shiga tattara komai na shi dake wurin ya fita a d’akin, likitar na masa magana amma ko kulata bai yi ba saida ya bar asibitin kwana kwanan.

*01/01/2021*

Tun gari bai gama wayewa ba d’aliban suka duk’ufa wajen gudu a filin makarantar, sun yi har sun fara gajiya amma yallab’ai Umad babu shi babu dalilinshi, cikin hakane Zafreen da tawagarta suka biyo ta filin zasu wuce.

Da gangan Zafreen ta bi ta inda Ayam ke gudu, Ayam kam na ganinta a cikin gudunta ta nemi kauce mata, amma dake neman fitina take da d’aukar fansa sai kawai ta tareta gadan gadan ta bankad’eta.

Fad’uwa ta nemi yi hakan yasa tayi baya tana tangal tangal, amma ikon Allah sai Ayam ta jawo hannun Zafreen hakan yasa suka fad’i tare k’asa.

A tare suka saki k’ara inda Zafreen ke kan Ayam d’aro-d’aro, da sauri su Laika suka kamo Zafreen ta mik’e tsaye, Ayam ma mik’ewa tayi tana kallon Zafreen d’in, hannunta na dama ta d’ora kan sark’arta tana k’ok’arin mayar da ita cikin rigarta dake riga biyu ce jikinta, d’aya ta sanyi mai zip a gaba sai k’aramar daga ciki.

A mugun razane kuma a kid’ime cikin tashin hankalin da Zafreen bata tab’a tsammanin fuskanta na ta ga wannan sark’a a wuyan Ayam wacce sark’a ce da ba ko ina ake samunta ba sai a wajen maccen data kasance mata a gurin sarkin Khazira, tabbas ana na bogi amma ta gasken kana ganinta zaka fahimceta, dan dutsen da aka k’era sark’ar da shi daga k’asan ruwa ake samunshi, had’akar lu’u lu’u da murjani ke samar da da dutsen sark’ar, hakan yasa Zafreen jin mugun jiri na neman kayar da ita ya tima a k’asa.

Kamar wacce aka tsoratar ko aka firgita ta juya tana fad’in “Ina! Hakan ba zai faru ba, ina!!!!”

Da gudu ta juya ta nufi hanyar da ake zuwa dan amsa kiran waya, su Laika ma da gudu suka bita suna kiranta, Ayam kam tab’e baki tayi ta gyara sark’arta ta juya a tsanake dan komawa b’angarensu dan ta gaji kam, tunda bai zo ba kuma shi ya sani.

Zafreen na zuwa a gigice ta shiga danna kiran lambar mahaifinta, tan fara kururuwa kam aka d’aga, a matuk’ar rud’e ta shiga fad’in “Pah, pah na ganta, na rantse da abun bauta Ghira na ganta, na ganta sanye da sark’ar Mah, na ganta da ido na.”

Cikin fitar hayyacin daya ninka na Zafreen sarki Musail ya amsa da “A ina? Ina kika ganta?”

Saida ta shiga yarfa hannaye tace “A makaranta ne, yanzu haka tana wajen motsa jiki, gudu take, Pah ita ce na rantse.”

Kamar zai fasa mata dodon kunne yace “Gamu nan zuwa, yanzu zamu zo Larhjadin d’in, waziri da Adah tun jiya suna nan dama, sun samu wasu bayanai akan ta.”

Da sauri tace “Pah indai suna nan su ma ai sun isa, ba sai ka zo ba Pah zamu kawo maka ita.”

Jim ya d’anyi sannan yace “Shikenan ‘yata, na yarda dake.”

Aje wayar ta yi ta juya ta kalli su Laika tace “Ina so na had’u da ita yanzu.”

Jinjina kai sukayi suka nufi inda suka barta, amma da basu sameta nan ba sai kawai Laika ta ce su tafi dan su ma lokacin na su darasin yayi, idan sun fito sun had’u da ita.

*A k’ofar* gidansu Ayam gari ya k’arasa wayewa Umad, safiya na yi ya danna k’ararrawar sanarwar dake jikin k’ofar, daga ciki ya ji an ce “Ana zuwa.”

Gyara tsayuwa yayi ya k’urawa k’ofar ido yana tunanin fuskar mahaifiyar ce ko ta ‘yar zai fara arba da ita dan mace ce tayi magana.

Gaba d’aya k’ofar Habbee ta wangale ta sauke idonta cikin na Umad da shi ma ya saka na shi a cikin na ta, ganin bak’uwar fuska ce sai ta saki murmushi tace “Yaro da me zan taimaka maka?”

Fuskarshi ba yabo ba fallasa yace “…

*Yar uwa kin biya na ki ne? To ki hanzarta dan jin me zai faru, ga Umad k’ofar gidansu Ayam yana neman Zafeera dan d’aukar fansa, ga sarki da mutanenshi ma daf da ita, shin wanene ma Umad d’in nan wai? Sai kin biya na ki zaki san haka.*

 

*Alhamdulillah*

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

KIBIYAR AJALI 5

Advertisement  *KIBIYAR AJALI…..!!!!* _(Sulke baya tsare ta sai ta wuce)_           ๐Ÿน๐Ÿ‘‘๐Ÿ‘ฉโ€โค๏ธโ€๐Ÿ‘จ๐Ÿ’ MALLAKAR:- NANA…

SALON SO BOOK 1 PAGE 23-24

Advertisement   ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ             ๐ŸŒน SALON SO ๐ŸŒน ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ     BOOK ONE…

SIRADIN RAYUWA 2

Advertisement  ๐Ÿ‘‘ *SIRAD’IN RAYUWATA* ๐Ÿ‘‘ *_Wannan littafin na kudine,amana ce a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar…

DIYAM 54 & 55

Advertisement โค๏ธ DIYAM โค๏ธByMaman MaamaEpisode Fifty Four & Five : The Games We Play“Check up” na maimaita a…