Advertisement
*11*
Fuskarshi ba yabo ba fallasa yace “Mahma, na zo muyi magana da ke, zan iya shigowa ciki?”
Had’e fara’arta tayi tace “Magana da ni kuma? A kan me?”
D’an d’aga idonshi yayi zuwa saman kanta dake ya fita tsayi ya hangi d’akin, a take kuma ya kalleta yace “Mahma, mai gidan baya ciki ne?”
Murmushi tayi tace “Shi ka ke nema?”
D’aga kai yayi alamar e tare da fad’in “E mahma.”
Kaucewa tayi a hanyar tace “Shigo ciki, ya d’an fita zai siyo mana gasasshen bredi ne, yana shigowa yanzu.”
K’afafunshi ya shiga zurawa cikin d’akin yana bin bayanta, amma idonshi akan gaba d’aya d’akin yake, komai kallo yake yana so ya ga ko zai ga hoto kafin ma ya ga zahirin, saidai babu komai daya shafi mutum, muryar Habbee ce ta katse shi daga wulk’itawar da yake ta ma idon shi tace “Me zan kawo maka?”
Murmushi yayi yacce “Coffee.”
Advertisements
Jinjina kai tayi ta juya ciki, da kallo ya bita kafin ya sake maida idonshi kan komai dake d’akin, yana cikin kallon aka sake danna k’ararrawar k’ofa, da azama ya mik’e da tunanin Utais ne, Habbee kuma har ta fito dan ta bud’e k’ofar, juyawa yayi ya kalleta yace “Karki damu zan bud’e.”
Murmushi tayi tace “Nagode.”
K’arasawa yayi bakin k’ofar ya kama hannun zai murd’a sai kuma ya lek’a ta yar hudar da aka yi don tsaro ne dama, mutumin daya gani ne yasa shi zaro ido, duk da kayan jikinshi ba na masarauta bane amma ya san shi farin sani, da sauri ya shiga waigawa neman inda zai b’oye, a k’arshe wani labule ya d’aga ya shiga saboda jin an banko k’ofar da k’arfin da yasa Habbee daga madafa fad’in “Waye wai?”
Umad na kallo ta labulen nan har suka shigo tsakiyar d’akin, tunaninshi bai wuce son sanin abinda ya kawosu ba, tsakiyar falon suka shiga suna ta waige waige alamar su ma wani abun suke nema, d’aya daga cikinsu ne ya kalli Habbee dake ta tsatsaresu da ido yace “Ina mijinki yake?”
Cikin fad’a fad’a tace “Me zaku masa? Su waye ku? Me kuke nema a nan?”
K’akk’arfan ne ya d’aga hannunshi sosai ya d’auke fuskarta da mari, a gigice ta dafe kunci tana fashewa da k’ara har ta fad’i k’asa, a tsorace ta kalleshi sanda ya d’ora yatsarshi akan labb’anshi yace “Shiiiiii!”
Hannu yasa ya d’aga rigarshi ya ciro bindiga ya d’ora mata a kai yace “Ina yake?”
Daidai shigowar Utais kenan rik’e da takardar dake nad’e da bredi, sakin kayan yayi suka zube ya ruga a guje yana kiran “Kai! Su waye ku? Me ta muk…”
Bai gama fad’a ba d’ayan ya zuba masa k’ulli a ciki, duk’uwa yayi yana dafe cikinshi kamar zai mutu, tarin lafiyayyar gashin kan shi ya kaa da k’arfi ya jawoshi k’iii saida suka kawoshi daf da inda Habbee take zaune suka jefar, dukansu suka nunawa bindiga wanda yafi kaushin a cikinsu yace “Ina take?”
Kallonsu sukayi a tare Utais ne yace “Wacece?”
Wani wawan naushi ya zuba mishi a baki yace “Karo na k’arshe kenan da zaka nemi raina mana hankali, dan haka daga yanzu zuwa sanda zamu bar nan kasan me zaka fad’a mana.”
Habbee fashewa tayi da kuka tace “Na rok’eku ku rabu da shi, ku daina dukansa hakanan.”
Advertisements
A tsawace d’ayansu yace “Shiru.”
Sake nuna Utais yayi da bakin bindiga yace “Tana ina?”
Lumshe ido Utais yayi ya had’e wasu yawu masu d’aci, bud’e idon yayi ya kallesu yace “Saidai ku kashe ni, amma na yi alk’awarin ba zan fad’a ba, ba zan tab’a cin amanar sarauniyata ba.”
Jinjina kai d’ayan yayi ya d’an ja baya kad’an ya d’ana bindigar ya saita akan Habbee yana fad’in “Idan kai a shirye ka ke ka mutu, ban sani ba ko ka shirya rasa matarka ma? Zan k’idaya uku ka ceci matarka.”
Da sauri ya kallesu a rud’e yace “A’a na rok’eku, kar ku tab’a ni ku min ko ma menene, kar ku cutar da ita.”
Cikin kuka Habbee tace “A’a ka barsu, na yarda su kashe ni indai akan alk’awarin da muka d’aukawa sarauniya ne.”
A tsawace yace mata “Shiru, kina da buk’atar kasancewa a raye, ko kin manta kina da mahaifiyar da rayuwarta ta dogara a ta ki ne? Ita kan ta gimbiya ta fi buk’atarki fiye da ni.”
A hassale mutumin ya daka musu tsawa ya saka yatsarshi zai danna kunamar bindigar a kan Habbee yana fad’in” Ku mana shir…”
Bai gama fad’a ba alburushi ya tashi kan shi sai fad’uwarshi kawai suka gani da kua sautin alburushin, k’ara Habbee tayi a take Utais ya jawota jikinshi suka duk’e, d’ayan kam da wani irin sauri ya kalli inda harbin ya fito, saidai tuni Umad ya kawo daf da shi, bai ankara ba kawai ya buga mi shi hannun bindigar a hanci ya b’arke da jini, a take kuma ya rik’e hannunshi mai bindigar ya karya wuyan hannun hakan yasa shi sakin k’ara, su Habbee na kallon ikon Allah sai gani sukayi ya kama wuyansa gaba d’aya ya murd’e ba tare daya barsu sun shaida wanda yayi ajalinsu ba ya turasu kiyama.
A matuk’ar tsorace suka shiga kallonshi sai Utais da yayi k’arfin halin tashi tsaye yana kallonsa, nunashi yayi da yatsa jikinshi har b’ari b’ari yake yace “Kai ne? Me ka ke yi anan?”
Gyara tsayuwarshi yayi tare da soka bindigarshi a mazauninta ya kalli Habbee yace “Mahma, ki gafarce ni kar ki fahimce ni ba daidai ba.”
A tare kuma ya kallesu yace “Kun ga, ya zamar muku dole ku fad’i sirrin da kuke b’oyewa tsawon shekara ashirin, ko ku fad’a ko kar ku fad’a kun sani da dole zata zama shugaba, dan haka ban ga anfanin b’oyewar ba har yanzu.”
Jiki a d’arare Habbee tace “Waye kai? Ya akayi kasan da maganar nan? Ko dai kai ma kana cikin masu nemanta?”
Fuskarshi a d’aure yace “Sanin waye ni ba shi ne a yanzu ba, ina so na san wacece gimbiya Zafeera?”
Girgiza kai Habbee tayi sai Utais da yace “Kai kuma a cikin wace tawagar masarautar ka ke?”
Wani kallo ya musu ya zura hannu ya fito da bindigar yana sake saisaita ta, wani shak’iyin murmushi yayi yace “Kar ku d’auka na taimake ku daga hannunsu ne, gani na yi basa buk’atarta tunda har zasu juri jin jayayya a kan ta, shiyasa na k’ara musu gudu.”
Tsakiyar goshin Utais ua d’ora bindigar dan yasan mace ta fi rauni sannan ya kalli Habbee fuska a tamke ba alamar wasa yace” Zaki fad’a ko sai kin ga gawar mijinki?”
D’aga hannaye tayi tana girgiza kai tace” A’a, a’a na rok’eka kar ka kashe shi zan fad’a, zan fad’a maka.”
” A’a Habbee, kar ki…”
Dungura masa bindigar yayi yace” Zan fasa kanka na sake jin bakinka.”
Jiki na rawa Habbee ta nufi inda Umad ya b’uya d’azun a bayan labule, bud’a labulen tayi ta wareshi gaba d’aya, Umad na kallonta ya ga ta tura wurin ka rantse bango ne, amma sai gani yayi wurin yayi baya alamar dai mashiga ce, juyowa tayi ta kalleshi tace “Zo ta nan.”
Kallon Utais yayi ya sake kallonta, nuna Utais yayi alamar ya fara wucewa, gaba Utais yayi sannan ya bishi baya ba tare daya d’auke bindigar ba, saida suka shiga dakin Habbee ta kunna hasken daya gauraye wurin.
Dauuuu! Hotonta da hasken d’akin suka daki idonshi a tare, zazzago idonshi yayi kamar zasu fad’o k’asa yana sake k’urawa sosai, gab d’aya jikinshi ya ji ya d’auki wata irin tafiyar tsutsa yayam yayam, sauke bindigar yayi daga kan Utais ba tare daya sani ba, baki da hanci da ido duk bud’e yana kallonta.
Ganin kamar baya hayyacinshi yasa Utais kallonshi yace “E ita ce, nasan abinda kake tunani kenan, ni ma ko da na ganka jiya na ji ban yarda da kai ba, sannan ina ji kamar na san fuskarka, sai dai na rasa inda na sanka.”
A hankali Umad ya taka ya k’arasa gaban tabkeken hoton da aka manna a bango na takarda, rigar sanyi ne jikinta kalar bleue mai haske da dogon wando, gashinta mai yawan gaske da yasha gyara kalar maroon ya kwanta a gadon bayanta, d’aya hannunta a mik’e har yana gugar cinyarta d’ayan kuma ta rik’e damtsenta da shi ta kalli hoton.
Ba wai kyau ta yi a hoton ba da yasa ya k’ura mata ido, kawai mamaki da al’ajabin yanda dai ta kasance ita, *Ayam*, ita ce zab’abb’iyar nan? Ita ce lu’u lu’un da ake ta haurigiyar nema?
“Waye kai?” Habbee ta fad’a daga bayanshi, ajiyar zuciya ya sauke ba tare daya d’auke ido a kan ta ba yace “Tun ina shekara ashirin nake neman hanyar da zan bi na d’auki fansa a kan sarki Musail.”
Juyowa yayi ya kallesu yace “Yau kuma gashi Allah ya kawo ranar, burina a kan Ayam mai girma ne, da kua nasan ita ce na fara had’uwa da ita ranata ta farko dana fara zuwa makarantar nan da nayi awon gaba da ita, ina tabbatar muku da saidai ku samu labarin b’atanta a karo na biyu.”
Zaro ido sukayi da sauri Habbee ta durk’ushe k’asa tana kuka tace” Mun rok’eka dan soyayyarka da iyayenka kar ka kasheta, bata san komai ba ita bta da laifi, me yasa zaka d’auki fansa a kan ta madadin mahaifinta daya cutar da kai?”
Da sauri ya kalleta yace” Kasheta kuma? Na fad’a muku zan kasheta ne? Ai na nemeta ne dan na fi kowa bata kulawar data dace, rad’ad’in rashinta kawai nake so mahaifinta ya ji.”
Gyara tsayuwa yayi yace” Kunga babu lokacin b’atawa a nan, ko ba komai mak’otan nan sun ji hatsaniyar data faru, a kowane lokaci yan sanda zasu iya zuwa nan.”
Dafe k’ugu yayi da hannaye biyu yace” Aurenta zaku bani yanzu ni kuma na karb’a, idan kuma kun fi so mu bi ta d’aya hanyar shikenen, sai na koma makaranta na sameta.”
Kallon kallo suka shiga yi wa junansu, mamakin lamarin shi da kula abinda ya zo musu da shi yasa suka kasa aiwatar da komai, d’aga kafad’a yayi yace” Shikenan tunda baku son ceto rayuwarta, amma ku sani a halin da ake ciki yanzu mahaifinta ya rufe sarauniya Juman a kurkukun Sabah, sannan sarki Wudar na garin Giobarh ma ya baza dakarunsa dan nemo masa ita, wad’annan ma biyu ne daga cikin su, haka ma mai Bukhatir wanda yake kamar d’a ga sarkin Misra shi ma nemanta yake ido bud’e yana son aurenta, kuma wannan a shirye yake ya kashe iyayensa ma saboda ita.”
Rab’asu yayi zai wuce da sauri Utais ya rik’e hannunshi yace” Mun amince, amma a bisa sharad’i d’aya.”
Kallonshi yayi ya jefa masa tambayar me ye sharad’in? Cike da kalar tausayi yace” Ka bamu tabbacin ba cutar da ita zakayi ba, ka rantse da abinda kake bautawa babu abinda zaka mata.”
Murmushin gefen labb’a yayi yace” Na fad’a muku ba zan bari wani ba ma ya cutar da ita bare kuma ni, kawai ina so ne ta wa sarki Musail nisa yana ji yana gani har k’addarar mutuwarsa ta gilma ta hannunta kamar yanda ake farfagandan fad’a.”
Jinjina kai Utais yayi yace” Shikenan mun amince, yanzu ya za’ayi ta zo nan dan mu shawo kan ta?”
Yar dariya yayi yace” Ni musulmi ne, kula zan aureta ne kamar yanda addini ne ya shar’anta min, zaka zama waliyinta yayin da zan wakilci kai na.”
Kallon juna suka yi da Habbee sannan suka jinjina kai, zaune yayi akan shafafffen tiles d’in dake d’akin da babu komai ya nuna musu su zauna su ma, laluba aljijunsa yayi sai kuma ya kallesu yace” Kuyi hak’uri fa babu kud’i hannu na, makullin motar da ya zo asalin masaukinshi ya d’auka ya aje gabansu yace “Wannan makullin motata ce Ferrari, na bata ita a matsayin sadaki.”
D’aukar makullin Utais yayi yana tsura masa ido, da sauri Umad yace “Karka damu fa, da zaran na d’auketa daga nan zan bata har da takardun motar, yanzu ka damk’a min amanarta ni kua na karb’a.”
Kamar wasa Utais ya mik’awa Umad auren Ayam daga nan wurin da taimakawarshi, suna gamawa Umad ya kalleshi yace “Cin ta, shan ta, suturarta, kula da lafiyarta, addininta, zamar mata abokin hira, iliminta, duk nayi alk’awarin kiyayewa iya k’arfina, haka ma sauke nauyin saduwa.”
Mik’ewa yayi yana fad’in “Insha’Allah ni zan zama uban jikan sarki Musail.”
Mik’ewa sukayi su ma Habbee ta sake fad’in “Wai waye kai?”
Wani siririn murmushi ya saki ya juya ya kallesu yace “Umad, d’a ga sarki *Wudar*, *yariman Giobarh*.”
Gaba d’aya cikinsu ya yamutsa suka shiga k’arewa kansu kallo, ganin babu wanda ya ce wani abu ciki alamar girgizar daya basu yasa shi cewa “Hankalinku ba zai d’auka ba dama, gaskiya ne mahaifina ma nemanta yake, amma manufar shi daban a kan ta, tawa ma manufar daban a kan ta, mace mai daraja Musail ya d’auke mana bayan ya rabani da d’an uwana da na fi so a duniya, shiyasa ni ma na d’auke masa ‘yarsa mai daraja, abun farin ciki kuma shi ne daya yarda ita ce zata zama silar mutuwarshi, hakan zai bani damar jijjiga rayuwarshi na yi wasa da ita kamar biri da mai wasa da shi.”
D’aga musu hannu yayi har ya kai k’ofa zai fita sai kuma ya juyo ya tarawa Utais hannu yace” Ara min makullin nan na mayar da kai na makaranta wajen amaryata.”
Baki wangale jiki a sake Utais ya mik’a masa makullin sun rasa ta cewa, fita yayi daga d’akin yana fad’in” Ku gaggauta barin nan garin kafin yan sand su nemeku da tuhumar kashe mutanen nan biyu.”
Daga haka ya fice a gidan mutane kam har sun fara taruwa a na hangen benen na su, suna dawowa daga doguwar sumar nan suka zabura suna kallon junansu, a gigice Habbee ta shiga fad’in” Me ka aikata haka? Me yasa ka amince masa? Yanzu idan fa ya kasheta?”
Rik’ota yayi yace” Kinga ki nutsu, da fari mu bar nan kamar yanda ya fad’a, idan ba haka ba kuma za’a kama mu.”
Da sauri suka fita a d’akin suka nufi d’akin baccinsu dan d’aukar abubuwansu masu mahimmanci.
*To yar uwa kin dai gani, ga Umad zai koma makaranta da auren Ayam a kan shi, shin zai sameta a makarantar kuwa? Ya akayi ma mutanen nan suka zo daidai da zuwan Umad? Wa ya sanar da su har suka yi kok’arin riganshi zuwa? Ya Ayam zata yi idan ta ji wai Umad ya aureta? Ya ma zasu rayu tukuna a cikin abokan gaban nan? Idan kika biya na ki ne kawai zaki samu damar sanin wad’annan abubuwan, ki hanzarta ki biya na ki.*
*Alhamdulillah*
GIPHY App Key not set. Please check settings