Lu’u Lu’u 12

Advertisement

*12*

 

*Ayam* na komawa b’angarensu d’akin baccinsu ta shiga, kayanta ya cire tz d’aura towel ta shiga wanka, sa’ilin da ruwan ke sauka kan ta ta samu damar rufe ido, a lokacin tunanin mafarkinta ya dawo mata wanda su Deeyam su ka katse mata shi a daren jiya, haka kuma ta had’e abun ta ba tare data yarda kowa ya ji ba, d’an gashinta daya had’e da juna ta shiga murzawa tana mayar da shi bayanta tana gumtsar ruwa a bakinta tana tofowa, idonta a rufe suke k’am ta shiga fad’a a ran ta “Me mafarkin ke nufi? Ko dai mafarki ne kamar kowane? To amma me yasa matar ba tayi kama da wanda na tab’a sani ba?”

Da sauri ta bud’a idonta sakamakon jin motsi a d’akin, amma sai ta share ta ci gaba da wankanta kawai, dan tunaninta su Deeyam ne.

A tsanake ta k’arasa wankanta ta d’auro towel, hannun k’ofar ban d’akin ta kama dan bud’ewa, tana zuro k’afa d’aya ta fito ta k’arasa fito da k’afar d’aya tana fad’in “Ke! Me ya kawoki n…”

Wani duka aka mata a kai ba tare da imani ko tausayawa ba, ko shurawa ba tayi ba ta fad’i gure a sume inda kan ta ya b’alle da jini a k’eyarta, cike da jin dad’i da farin cikin zata cika burinta a kan ga Zafreen ta kece da dariya ta mik’e tsaye tana kallon k’akk’arfan matashin da suka saka ya musu wannan aikin, wanda saida suka jadadda mishi ya mata dukan da zata suma.

Tafa mi shi tayi da murna tace “Aikinka na kyau, nagode sosai.”

Laika dake gefenta ne tace “Gaskiya ne, ni ma ki min godiya.”

A wulak’ance ta kalleta tace “A kan wane dalili?”

Shiru Laika tayi saida Zafreen ta juya bayanta ta maida hankali ga Ayam dake yashe kwance, bata ankara ba Laika ta d’auki hoton dake aje gefen gadon Sabrine na ita da danginta, sai kuwa ta fasawa Zafreen shi a kai har saida madubin ya mutu a kan ta, take ita ma ta zube bayan ta dafe kanta tana k’ok’arin juyawa ta kalli Laika.

Advertisements

Kallon juna sukayi Laika ta ciro wata k’aramar waya a cikin rigar mamanta ta danna wasu lambobi ta d’ora a kunne, a tak’aice tace “Angama.”

Tana aje wayar sai kuwa wata irin kara ta gauraye makarantar an danna na’urar dake nuni da idan wani had’ari ya samu musamman ma gobara, ai kuwa tuni hatsaniya ta kaure a makarantar dan kuwa sauran munafukan da ke tare da su Laika ne sukayi nasarar tashin zanga zanga a ciki, sai gashi sun fara farfasa abubuwa har da motocin malamai da ofisoshinsu.

Makaranta ta hautsine, duk jami’an sun yi iya k’ok’arinsu amma abun da gaske fin k’arfinsu aka yi, ana cikin hatsaniyar nan aka fitar da Ay da Zafreen ta bayan makaranta inda jirgi ya d’aukesu, Laika ma da tawagarta sulalewa sukayi suka bar makarantar, inda suka bar wanda basu ji basu gani ba a hannun jami’an makarantar suna son hukuntasu da laifin tayar da tarzoma.

Tunda ya doso ya ga wannan hayaniya da tashin hankali jikinshi ya bashi babu lafiya, yana fitowa daga dalleliyar ferrarin nan da gudu ya nufi inda yake tunanin samunta, bai damu da kowa ba da kuma abinda kowa zai fad’a.

Yana zuwa b’angarensu yayi sa’ar kicib’is da su Sabrine sun fito da gudu zasu fita, hannun Deeyam ya rik’o da sauri yace “Tana ina?”

Girgiza kai tayi tace “Mu ma ita muke nema, mun shiga d’aki amma bamu sameta ba.”

“Shiiit!” Ya fad’a yana sake zubawa a guje ya juyo ya sake tambayar “Ina d’akin?”

Nuna masa tayi da hannu, bai jira komai ba ya bangaji k’ofar ta bud’e ya shige, turus ya tsaya kallon d’akin, da gudu ya k’arasa gaban tagar daya gani bud’e ya lek’a, tabbas ko ma su wanene ta nan suka fita da ita, ga alamu nan ya nuna har da sawayen takalmi.

Dafe gaban goshinshi yayi yace “Ya Allah! Su waye kuma yanzu?”

Wayarshi ya ciro da sauri ya shiga daddanawa ya d’ora a kunne, jim kad’an Haman ya d’aga, cikin tashin hankali ya nufi hanyar fita a d’akin yana fad’in “Haman kana ina? Akwai matsala fa.”

Shi ma hankali tashe yace “Matsala kuma? Me ya faru?”

Da azama yace “Kai dai ka fad’a min inda ka ke zan zo na sameka.”

Advertisements

Da sauri shi ma yace “Ina nan masauki na dana fad’a maka.”

K’itt! Ya yanke kiran ya shiga takawa da sauri har ya k’arasa ga motarshi ya shiga ya sake barin harabar makarantar.

*Egypt*

Babban masaukin daya tanada dan wannan ranar yasa aka sauke mishi su, ya kashe kud’i masu azababben yawa dan kawai ya k’awata mata wannan gida, Zafreen ce ta fara bud’a idonta a hankali da suka mata nauyi har suka d’an fara kumbura, a hankali ta zura hannunta ta dafe k’eyarta saboda tuna abinda ya faru, a sanyaye ta furta “Wash!”

Muskutawa tayi ta tashi zaune sai kuma ta zabura da k’arfi saboda ganin Ayam kusanta kwance ita ma, juyawa tayi dan son ganin ko akwai wani kusansu, sai kawai ta ga kan ta a madubin drower da Bukhatir ya shak’ewa Ayam kaya da ita, saboda a bazata ta ga kanta sai ta saki yar k’arar data saka Ayam motsawa ita ma, tana bud’a ido ta sauke akan kwalliyar rufin d’akin wacce aka yi kamar da gwal aka yi ta.

Ganin Zafreen yasa ta yunk’ura da sauri ta tashi zaune, za ta yi magana sai kuma ta dafe kan ta da ta ji yana mata ciwo sosai, d’an kallon kanta tayi sai ta ga daga ita har Zafreen an nad’e musu kai da bandeji fari, kallon Zafreen tayi tace “Ina ne kika kawo ni nan? Ke ba fa na son iskanci kin ji ko, ki fita a harkata kafin na sake b’ata miki rai.”

K’wafa tayi ta mik’e tsaye tana k’arewa kanta kallo ta madubin, towel d’in jikinta shi ne dai har yanzu, Zafreen ma mik’ewa tayi tace “Ke kinsan wacece ni? To ni ma ina son sanin inda nake.”

Tsaki Ayam tayi ta nufi inda ta ga k’ofa da niyyar fita, kafin ta isa bakin k’ofar aka bud’o aka shigo, kallon kallo suka shiga yi da k’ akk’arfan matashin dake cikin shiga ta alfarma, had’e fuska Ayam tayi ta dafe k’ugu tace” Wannan wane irin rashin mutumci ne? Ina ne nan kuka kawomu?”

Wani sanyayyar murmushi ya saki ya bud’e hannayenshi zai
rumgume ta, da sauri ta ja baya tace” A’a, kai mahaukaci ina ne? Waye kai?”

Ba tare daya d’auke murmushin dake kan fuskarshi ba yace” *Pr茅cieux*, embrasse moi, tu sais combien da temps je passe a attendre ce jour (mai daraja, rumgume ni mana, kinsan lokacin dana d’auka ina jiran wannan ranar)?”

Nunashi tayi da yatsa tace” Zan wanka maka mari idan ka kuskura ka tab’a ni.”

Murmushi ya kuma saki ya juya ya kalli wasu matasa guda biyu dake gefenshi ya nuna musu Zafreen yace” Ku d’auke wannan daga nan ku kai ta b’angaren bak’i, wannan b’angaren na gimbiya ta Zafeera ne.”

A wani yatsine ta kalleshi inda Zafreen tace” Ni kuma me yasa kuka kawoni nan? Waye kai ma?”

Gyara tsayuwarshi yayi yace” Sunana Bukhatir, mai jiran gado a Egypt.”

Zafreen ce ta d’ora da” To ni kuma me na ke a nan? Ku maida ni makaranta mana, kasan ka mu su waye?”

A wulak’ance ya kalli Zafreen yace” Na sani, kuma a dalilin yawan fad’a da kike yi ne ya kawoki nan?”

Hanya ya nuna mata hanya yayi ba yanda ta iya dole ta shige gaba suka bi bayanta, kallon Ayam yayi yace” Ma pr茅cieux, zan turo hadiman da zasu kula min da ke yanzu, wannan shigar bata dace ki ba.”

Juyawa yayi zai fita Ayam tayi kukan kura ta shak’o rigarshi dam a hannayenta tana kallon fuskarshi tace” Babu inda zaka je sai ka mayar dani inda ka d’auke ni.”

Cikin matsanancin shauk’inta ya lumshe ido ya fara zura hannunshi akan cinyarta yana neman zurawa a cikin towel d’in, ido lumshe yace” Gashi kin kawo min kan ki, Zaf… Eera.”

Da sauri ta ske shi ta ja baya tana hararenshi, wani shakiyin murmushi yayi ya juya ya fita, da sauri ta kama k’ofar zata bud’e sai ta ji a rufe take gam, tsaki tayi ta shiga zagaya d’akin tana sln sanin a ina take? Me ta zo yi a nan? Su waye kuma take tare da su?

Bud’e k’ofar da aka yi yasa ta saurin juyawa, matasan mata ne su biyu da kayansu iri d’aya a jiki, da girmamawa suka rusuna suna gaisheta, cikin fad’a ta nufesu tana musu yarensu tace “Wai ku su waye? A ina nake nan ne?”

Nuna musu k’ofa tayi tace “Maza ku bud’e min k’ofar nan.”

Rusunawa sukayi a ladabce cike da tsoron kar su mata ba daidai ba ransu ne zai b’ace daga gurin mai gidan na su, d’aya daga ciki ce jikinta na rawa tace “Ranki shi dad’e yallab’ai ne ya umarcemu da mu tayaki shirya kan ki.”

A tsawace Ayam tace “Ranki shi dad’en banza, wane banzan shiri ne zaku tayani? Mu saka ce ni aka fad’a muku? Ko dama can fil azal ku kuke min wanka ne? Mtsssss!”

Rikicewa sukayi suka rasa yanda zasuyi, cikin hushi ta nufi k’ofar ta sake kamawa zata bud’e, amma sai ta ji ta gam ta k’i bud’ewa, a tsawace ta kallesu tace” Zaku bud’e min ne wai ko sai na bajeku a nan?”

Da sauri suka fara riga rigan bud’e mata k’ofar, d’aya a ciki ce ta d’ora hannu a k’ofar tare da danne wani mab’alli dake k’asan hannun k’ofar, bud’ewa tayi ta kauce mata a hanyar, ai kam ficewa tayi da sauri tana k’arewa tabkeken falon kallo, tsaye tayi ta shiga bin ko ina da kallo dan gaskiya d’akin ya birgeta sosai, tab’e baki tayi ta ci gaba da tafiyarta ta nufi inda take ganin nan ne mafitar.

Zata bud’e k’ofar kenan aka bud’e daga waje, cak ta tsaya ta zubawa mai shigowa ido, saidai sab’anin d’azu da fuskarshi ke d’auke da fara’a da annashuwa, yanzu kam fuskar a had’e take tam, yanda ta lura yana ta kallon bayanta ne yasa ta d’an juyawa, matasan matan nan ta gani duk sun zube k’asa kawunansu sadde jikinsu sai b’ari yake.

Juyawa tayi ta kalleshi sai kawai ta ja tsaki ta kula juyawa ta kallesu tace “Ku mik’e tsaye kunji, me ye na wani rusunawa har k’asa gaban mutum d’an uwanku.”

D’aya a ciki ce tayi k’arfin halin d’aga kan ta ta kalketa sai kula ta sunkuyar, muryar Bukhatir ce ta sa ta juyo sanda yake fad’in “Me na fad’a muku a kan ta?”

Jiki na kyarma d’ayar tace “Yallab’ai mun yi iya k’ok’arinmu amma ta k’i…”

Kashe fuskarta yayi da marin daya sakaya girgiza kamar zata fad’i kwance, a mugun hassale ya nunasu da yatsa yace “Ba k’ok’ari ba, abinda yasa na d’auko ku shi ne dan…”

Gauuuu! Ayam ma ta d’auke fuskar Bukhatir da mari, a wani irin razane matan da kuma dattijon ne dake bayansu suka kalleta, dan su kam yanda suke girmama Bukhatir ko sarkin Egypt basa girmamawa haka, idonshi da suka kad’a sukayi jajajir ya d’aga ya kalleta, ido cikin ido suka kalli juna babu mai alamar rusunawa.

Tunanin hanyar da zai fara hukunta ta yake, tunanin kalar muguntar da zai mata yake, hasaso hukuncin da zai mata yake wanda zaiyi sanadiyar ta fara kakkarwa sanda ta ji sautin muryarshi, amma ikon Allah sai ya ji ya kasa aiwatar da komai, sai ya ji wani tausayinta a zuciyarshi ya malayeshi sanda suka had’a ido, sai kawai ya d’auke hannunshi daga kuncin yana murmushin takaici, dan ko iyayenshi ba zai tuna ranar da suka tab’a marinshi ba, ba dan kar ya zama mak’aryaci ba sai yace tun na k’uruciya wanda bai san anyi ba ma.

Sake kallon fuskarta yayi yana lashe leb’enshi kafin yace “Idan har kina son barin nan sai ki fara bin duk wani umarnin da zan gindaya miki.”

A zabure tace “Kai a wa da zan bi umarnin ka?”

Sunkuyar da kai yayi k’asa yana murmushi kafin ya kalleta yace “Mijin da zai aureki.”

Da wani mamaki tace “What!”

Ba tare daya daina murmushin ba yace “Ba zaki gane komai ba a yanzu, ki fara shiga ciki ki shirya dan ki samu ki suturta min jikinki, idan kin fito zamuyi magana dake.”

Rumgume hannaye tayi tace “Kafin nan ka fara amsa min wad’annan tambayoyin nawa.”

Girgiza kai yayi yace “Zafeera mahimmanci gareki a wajena, idan na mayar dake sarauniyata ko fuskarki bana so kowa ya gani, ta ya zan yarda ki tsaya a haka wasu na kalleki? Kin san wacece ke kuwa? Kin san girma da matsayin darajar da kike da shi? Allah ya karramaki dan haka zan tayaki karrama kan ki.”

Cikin jin haushi tace” Tukuna ma wane banzan suna kake kirana da shi ne?”

Murmushi yayi mai kama da dariya ya juya zai fita yana fadin” Ki fara shiryawa sannan, zan amsa duk wata tambayarki.”

Da wata matsiyaciyar harara ta bi bayanshi har ya b’acewa ganinta, juyawa tayi a masifance tace wa matan” Sai ku tashi mu tafi ko? Zaku tsaya k’aton gardi na dukanku kamar ubanku, wahe shi ma tukuna?”

Yanda tayi tambayar tana rik’e k’ugu yasa d’aya a ciki tace” Kamar d’a yake ga sarkin k’asar nan.”

Yamutsa fuska tayi tace” Kama ne ma yake ba d’an sarkin bane, to wace k’asar ce wannan?”

D’ayar ce ta amsa da” Egypt.”

Da mamaki ta kallesu tace” Egypt? Kuna nufin nan a Egypt nake?”

Jinjina kai sukayi hakan yasa ta ita ma ta jinjina kai ta k’arasa bakin kofar d’akin, bud’e mata sukayi ta shige suka bi bayanta.

*Khazira*

A kausashe ya buga teburin yana kallon Adah da kan shi ke k’asa kamar zai fasa d’akin yace “Ta ya ya haka zai faru? Sai da na ce zan je da kai na kuka tabbatar min da zaku iya, yanzu me kuka aikata kenan?”

Cikin girmamawa Adah yace “Ka gafarce ni sarki, mun tarar da hatsaniya ne a makarantar, ga dukkan alama wasu abokan gabar ne suka fara ganota shiyasa suka tayar da zanga zangar, da haka kuma sukayi nasarar d’auke mana gimbiyoyinmu.”

Da wani sabon mamakin yace “Me? Gimbiyoyi kuma?”

Cike da d’ar d’ar yace “E shugabana, gimbiya Zafreen da gimbiya Zafeera sun b’ata a cikin tarzomar nan.”

Da bala’in k’arfi sarki Musail ya cire kambun dake kan shi na tsantsar gwal daya sa aka k’era masa dan alfahari ya jefar a k’asa, a fusace ya juya b’angaren da Dhurani yake ya kalleshi, sai kuma ya tattare rigarshi dake jan k’asa ya tunkari hanyar fita, rufa masa baya sukayi inda waziri Khatar ke fadin “Sarki na, ka nutsu mu bi komai a hankali, na tabbata sarki Wudar ne ya d’aukesu, dan shi ke da burin son d’aukar fansa a kanmu.”

Dakatawa yayi ya juya ya kalli Khatar da yayi maganar, jinjina kai yayi yace “In kuwa hakane sarki Wudar ya jaza ma k’asar sa yak’in duniya na uku, dan babu abinda zai hanani shiga masarautarsa sannan nayi fata-fata da su.”

Dhurani ne yace “A’a sarkina, ba da haka zamu fara ba, kafin mu farmake su buna buk’atar samun tabbaci suna hannunshi, daga bisani koma menene sai ya biyo baya.”

Adah ne yace “Hakane shugabana, dan na tabbata kamar yanda muke tsananin buk’atar gimbiya Zafeera, haka shi ma sarki Wudar, ba kuma zai kamata bane dan ya kasheta.”

Cikin hassala yace “To yanzu ya zamuyi? Me ye mafita? A yanzu na fi buk’atar Zafeera a kan Zafreen d’in.”

Adah ne yace “Wannan mai sauk’i ne shugaba na, zanyi magana da d’aya daga cikin masu lek’en asirinmu dake sintiri a cikin fadarsa.”

Nunashi yayi da yatsa yace “Ka tabbatar nan da zuwa yammacin yau ka samo min masaniyar komai.”

“Angama yallab’ai.” Ya fad’a yana rusuna masa, saida suka ga ficewarsa kafin su ma duk suka bar wurin babu wani mai farin ciki da yanayin da yake ciki, dan su kansu sun fi buk’atar a samu Zafeera a kuma k’ara mata gudu zuwa lahira, dan su canjin da aka ce zata kawo shi ne yafi tsaya musu a rai, a ganinsu zata rabasu da addinansu ne, muk’amarsu da martabarsu, hakan kuma ba zasu bari ya faru ba mundun ran su.

Bai zame ko ina ba sai kurkukun sabah, tsabar a rikice yake bafade d’aya ne ya take masa baya zuwa can, hannunshi rik’e da doguwar rigarshi cikin sauri har suka isa can, mai tsaron d’akin da take ne yayi saurin bud’ewa sarki Musail ya shige.

Tana zaune rakub’e a jikin bangon ta had’a kai da gwiwa, idonta a rufe suke ruf dan ko ta bud’e babu abinda take gani face dishi-dishi da jiri, har saida ya isa gabanta ya durk’usa irin tsugunnon maza ya finciki gashin ta sakamakon gyalenta daya sauka a kan kafad’unta, da k’arfi ya d’ago kan ta har saida ta saki yar k’ara saboda zafin da ta ji, da k’yar ta d’aga idonta ta kalleshi.

Cikin gadara da cika baki ya mata murmushi yace “To ya kike sarauniyata?”

Kamar wacce ke cikin maye tayi luuu da idonta ta saki wani murmushi ita ma tace “Yan…da kake, haka na ke.”

Tura kanta yayi da k’arfi har saida ta bugu ga bango ya fashe da dariya yace “K’arya kike sarauniyata, ni ina lafiya kuma ina cikin farin ciki.”

Cikin layi tace “Kai ma ba gaskiya ka fad’a ba sarkina, hankalinka a tashe yake kamar yanda muryarka ke b’arin tsoro saboda ka fara jiyo k’amshin mutuwarka.”

Da sauri ya mik’e tsaye yana lumshe idonshi dan gaskiya ta fad’a kam hankalinshi a tashe yake, cike da k’arfin hali ya kalleta yana nunata da yatsa yace” Ki zuba ido ki gani Juman, gobe warhaka ke da ‘yarki duk zaku mutu, wannan alk’awari na ne.”

Malalacin murmushi tayi ba tace komai ba har saida ya fita a wurin, a zahirinta kam bata nuna damuwa ko tsoron abinda ya fad’a ba, amma k’asan zuciyarta cike take da tsoro da alhini da zulumin abinda zai iya aikatawa.

*Larhjadin*

Ko da Umad ya isa ya samu Haman a masaukinshi fad’a masa abinda ya faru a makaranta yayi, saidai haka kawai ha k’i yarda ya fad’a masa batun auren nan, dan dama yayi ne saboda yasa hankalinsu Habbee ya kwanta su ji nutsuwar zuci su tabbatar tana hannu na gari, duk da dai yasan ba lallai sun yarda da shi ba musamman da suka san waye, amma dai yanzu a tunaninsu tana tare da shi kuma ba zai bari a cutar da ita ba kamar yanda ya fad’a musu, dan haka a sanin da yake da shi yasan aurenshi da Ayam zai cika k’aida ne idan da amincewar iyayenta mahaifa tunda suna raye, shaidu da kuma sadaki.

Cikin tashin hankali Haman yace “Me? Yanzu kana nufin ta sake b’ata kenan?”

Jinjina kai yayi ya kalleshi yace “Hakan alamu suke nunawa, amma a yanzu zamu iya cewa mun san inda take.”

Cike da k’aguwa yace “A ina kenan?”

Wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yace “Zan koma gida yanzun nan, ta hakane zan san inda take.”

Da mamaki Haman yace “Kana nufin zaka koma masarauta kenan?”

Jinjina masa kai yayi alamar e, cikin d’ar d’ar yace “Bana tunanin sarkinmu ya sameta, me zai hana ka fara saka ido akan Bukhatir?”

Da wani mamaki Umad ya kalleshi ya d’aga labb’enshi da k’yar yace “Bamu tab’a maganar Bukhatir da kai ba, ya akayi ka san shi?”

Zaro ido yayi alamar firgici, a take kuma ya had’e komai ya saki murmushi yace “Haba dai, ka manta ka min maganar sa? Daga gareka na ji batunsa ai.”

Cike da son waskewa ya d’an zagaya ya matsa daf da shi ya dafa kafad’arshi ganin kamar bai yarda da abinda ya fad’a ba yace “Ka gane ko, ina ga zai fi ka fara ta can d’in, zuwa gobe sai mu koma tare.”

Wani arnan kallo Umad ya masa sai kawai ya jinjina kai alamar to sannan yace “Shikenan.”

Sallama sukayi inda Umad na d’aukar hanya masaukin daya fara sauka ya k’arasa ya had’a kayanshi, dan yayi niyya yau ba sai gobe ba zai d’ora da neman Ayam, dan sai yake gani kamar Haman ya manta shi ne wajen rashin yarda da kafuwa, duk aminci da yardar dake tsakaninku ba zai saka shi d’auke ido a kan ka ba, bare al’amari na wacce yake da tabbacin za’a iya sadaukar da bilyoyin kud’i don samunta. Yana gama shiryawa saida ya fito ya d’auki hanyar zuwa filin jirgi sannan ya kira canal Jacob dan sanar da shi aikinshi ya k’are, dama hanya aka masa a gwamnatacce dan cika aikinshi, to tunda ya tabbatar da wacce yake nema ai shikenan.

*Bayan awa shida (Giobarh*: yana sauka a k’aton jirgin emirates d’in motoci guda hud’u ne suka zo dan d’aukarsa, sanda suka shiga rusuna masa d’aya daga ciki ya karb’i jakarsa mamaki ya shiga yi na samun tabbacin abinda yake zargi, dan ko mahaifinshi sarki bai fad’a ma zai zo ba, amma ga tarba ta musamman daga masarautarshi.

Limozine d’in da aka bud’e mishi ya shiga ya zauna suka mayar da k’ofar aka rufe suka d’auki hanya, gudu ake sosai dan tafiya ce mai nisan gaske daga filin jirgin zuwa fadar ta su, a d’an lokacin nan kuma tangale hab’arshi yayi yana kallon titi a zahiri a bad’ini kuma tunanin komai daya faru kuma yake faruwa yake, da wannan suka share awa d’aya a hanya kafin motocin su tsaya a k’ofar gidan suna oda.

Masu gadi biyu ne suka shiga jan k’ofar suna bud’eta tsabar girmanta da kuma nauyin da take da shi, danna hancin motocin sukayi a cikin farfajiyar wanda shi kan shi filin gidan wata k’asar ce daban data gaji da kyau da had’uwa.

 

*K’arshen free page, idan kina da buk’ata garzaya ki biya naki, sai kun zo masoyan asali.*

*Masoya na da suka biya kud’insu dan wannan littafi ina son sanar da ku zaku min alfarma d’aya, zan dinga sakar muku sabon shafi ne sau biyar a rana, saidai bai tsayar da ranakun ba gaskiya, kamar yanda a kowace rana ogana zai iya shigowa gari, hakan kuma na raunana rubutu na na kasa samun kai na, fatan zaku fahimce ni.*

 

*Alhamdulillah*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

YAU DA GOBE 43&44

Advertisement  🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾   🌹YAU DA GOBE 🌹 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Story & writing by mmn farees 🅿️43&44 Kuyi hakuri inda…

GOBE NA 64

Advertisement *GOBE NA…* By Khadeeja Candy  6️⃣4️⃣ Iyakar kokarin da nai na danne dariya ta ne domin har…