Lu’u Lu’u 14

Advertisement

*14*

 

Akan babban teburin cin abincin mai d’aukar mutane goma sha biyu, Bukhatir ne zaune akan kujerar tsakiya dake iya fuskantar kowa, a tunaninshi sarki Wudar zai zauna a nan, amma sai gani yayi ya ja kujerar kusa da shi ya zauna, Umad kuma ya zauna kan kujerar da ke fuskantar Bukhatir d’in.

Haka kawai had’uwarsu ta farko ya ji ya tsani matashin, wani cin magani da yake da wani jiji da kai shi dole ga d’an sarki, hakan sam bai masa ba.

Mutane shida ne a wurin gaba har da mataimakin sarki da kuma na hannun daman shi, inda fadawanshi masu tsaronsa suke bayanshi d’an nesa kad’an tsaye, shi ma Bukhatir dattijon nan ne a bayanshi tsaye.

Mata biyu ne ke zuba musu had’add’e kuma lafiyayyen abincin da aka girka dan su, sarki Wudar ne ya kalli Bukhatir cikin rad’a dan dama a kusa suke yace “Me zai hana ka gabatar mana da ita?”

Wani shak’iyin murmushi Bukhatir yayi yace “Yallab’ai ina fata dai ba ka zo da tunanin zaka tafi da ita bane ko?”

Da sauri Wudar ya kalleshi sai kuma ya sunkuyar da kanshi, numfashi ya sauke yana tunanin me Bukhatir ke nufi kuma? Ko ya manta da yarjejeniyarsu ne? D’aga kan shi yayi ya kalleshi cikin sassauta murya yace” Ka fad’a min adadin farashinka? Zan biya ko nawa ne.”

Wata dariya Bukhatir ya tintsere da ita ba tare da sanin yayi ba, ganin kowa ya maida hankali a kan shi har da Umad daya kalleshi cikin jin haushi yasa ya tsagaita, kallon sarkin yayi a cikin rad’a shi ma yace” Yallab’ai, me yasa kayi tunanin tana da farashi a gurina? Ai ni ma na karb’i gayyatarka ne dan na tambayeka farashinka, dan bana so ka d’auka ni ma ci amana ne, ka taimaka min wajen samota kuma na juya maka baya.”

Irin kallon nan mai saka fad’uwar gaba sarki Wudar ya masa, fuskarsa a tamke yace” Bukhatir kasane zaka dinga fad’a min, idan ba haka ba yayan mahaifinka zai san duk abinda kake shiryawa a kan shi, haka zalika zai samu labarin bayyanar jikarshi a k’asarsa.”

Advertisements

Wata harara harara Bukhatir ya wurga masa sai kuma ya shiga rarraba ido yana tunanin lallai fa komai nasa zai lalace idan har Emir ya san da batutuwan nan.

Iska ya huro tare da jan plate d’in abincin gabanshi ya kalli sarki Wudar yace” Na yarda zaku gana, amma ba zaka tafi da ita ba, daga baya zamuyi magana akan wanda ya dace ta zauna tare da shi.”

Kafin sarki Wudar yace wani abu Bukhatir ya kalli dattijon dake bayanshi, da ido kawai ya masa alama, amsawa yayi da girmamawa ya nufi wani sashe na daban.

Umad dai na zaune yana kallon komai a tsanake yana kuma d’ora komai a kan ma’auni, yasan mahaifinshi na neman Zafeera, amma yasan dan ya d’auki fansa ne a kanta kamar dai shi, amma bai san dalilin da yasa yake zafafawa ba sosai haka, duk da dai yanzun ba wai ya fahimci akan me suke magana ba, amma yana ji a jikinshi batun ba zai wuce na son had’uwarshi da Zafeera ba, tunda har a bincikenshi sunan Bukhatir ma ya fito a cikin masu son samunta kuma su mallaketa, to baya raba d’ayan biyun cewa zasu had’a k’arfi da k’arfe ne dan ganin sun samota sannan su muzgunawa mahaifinta, dalilin da yasa Bukhatir kuma yake son kassara sarki Musail d’in wannan ne kam bai sani ba sai nan gaba.

K’wasss! Sautin takalmin k’afarta ya isar musu da sak’on zuwanta farfajiyar, wanda dama yake a k’age da son ganin zab’abb’iya, da ma wanda sam bai da niyyar kallon b’angaren kamar Umad saida suka samu kan su da juya kusan a tare.

Take yanayin fuskarshi ya canza daga had’ewar nan zuwa wani sassauk’an murmushin da baisan sanda ya kubto ya taho masa ba, inda zuciyarsa ta shiga masa wani irin sanyayyan duka tana sanar da shi ta iso, jikinsa kuma gaba d’aya wani karsashi had’e da kasala ya ji suna saukar masa, a tausashe ya juyo da kanshi yanda babu wanda ya fahimta, murmushi ya sake yi bayananne tare da shafa sumar kan shi, a hankali a kan labb’anshi ya furta ” *Zakanya*.”

Tun daga k’asa har sama sarki Wudar yake k’are mata kallo, bakinshi bud’e kamar zaka fad’a a guje, kallo d’aya zaka masa kasan tabbas yana cike da farin cikin daya shekara da shekaru bai samu kan sa a ciki ba, wani b’oyayyan murmushi ne ke fita a fuskarshi mai kama da lallausan dariya.

Ta b’angaren Bukhatir ma haka yake, duk da shi d’in ya ganta ba kamar sarki da sauran jama’ar ba, amma dai haka ya kafeta da ido har saida ta k’araso dattijon nan ya ja mata kujera ta zauna.

Tsarguwa ta fara yi dan kallon da mutanen wurin ke mata tana ji kam a shari’ance ma ya wuce k’a’ida duk da bata da madogara mai kyau, saidai bata nuna hakan ba sakamakon ganin yallab’ai Umad, tsura masa ido tayi tana kallo amma shi kan shi a k’asa, kamar ta k’wala masa kira tace “Yallab’ai.”

Sai kuma muryar Bukhatir ta katseta sanda yake nunawa sarki Wudar ita yace “Yallab’ai ga Zafeera.”

Wani mahaukaciya kuma siririyar dariya sarki Wudar ya dinga yi yana kallonta kamar marar gaskiya yana fad’in “Ehehehehe… Hahahahaha… Ehemmm, na gan ta, na gan ta Bukhatir, fiye ma da yanda ake fad’a.”

Kallon Zafeera Bukhatir yayi ya nuna mata sarki yace “Ma pr茅cieux, ga yallab’ai sarki Wudar, ga kuma d’an sa, wad’annan mak’arrabansa ne sun zo ganinki.”

Advertisements

Wanda ya nuna yace mata d’an sarkin ta bi da kallo galala, amma har yanzu idon shi na kallon farantin gabanshi, cikin larabcin parsi tace “Dama d’an sarki ne?”

Baki wangale sarki yace “E, d’ana ne.”

D’agowa yayi ya kalli mahaifin na shi, d’an tsakin jin haushi yayi a ranshi yana ayyana kar mahaifinshi la ya zama sakarai a gabanta fa, dan ya ga yanda suke k’arewa da canal Jacob.

Juyawa tayi ta kalleshi cikin hatsari suka had’a ido, k’yabta ido tayi sau d’aya sau biyu sau uku, shi kam dan ya fahimci me take fad’a sai ya shiga yin zooming fuskarta yana kallon idon na ta da gashinsu yayi mata wani zar-zar-zar, ganin bai fahimci komai ba sai kawai ya d’auke idonshi ya d’auki cokalin gabanshi.

Cikin jin haushi Ayam ma ta d’auki cokalin gabanta duk da babu komai a cikin farantin ta, turo baki tayi a dole ita ta ji haushin ya k’i kulata ta shiga caccakar farantin na ta, kamar sub’utar baki a harshen italien tace “Wai me ya kawoku nan?”

Dukansu zuba mata ido sukayi, saidai babu wanda ya fahimci me ta fad’a sai Umad, shi ma yana kallonta da ya ga kowa ita yake kallo sai kawai ya d’auke kan shi, kamar wanda baya son yin maganar a harshen data masa magana shi ma yace “Kar ki nuna musu kin sanni, kiyi harkan gabanki kawai.”

Wani irin kallo ta masa irin mamakin nan a zuciyarta tace “Kutttt!”

A zahiri kuma farantin ta ta dinga kallo da ake zuba mata abinci amma cokalin a hannunta tana t daddaga shi a teburin wanda hakan yasa duk mutanen suke kallonta, ita ma mayar mi shi tayi da fad’in “Ashe kai d’an sarki ne, shi ne ka je makarantarmu a matsayin malami.”

Shiru yayi kamar ba zai amsa ba sai kuma ya kalli fuskar Bukhatir kamar irin da shi yake magana yace “Kasancewata d’an sarki matsayi ne da Allah yake son gani na a haka, zamana malami kuma aiki na ne da nake so.”

Kallonshi tayi tare da dakatar da bubbuga cokalin cikin masifa tace “Ama kuma shi ne baka tab’a fad’a mana ba, kenan zuba ido ne kayi kana jira mu maka rashin kunya ka hukunta mu?”

Kallonta yayi saidai kafin yace wani abu tayi saurin fad’in “Ni ba wannan ba, wannan k’aton garjejen basamuden daya kawoni nan ya aje, bana son ganinshi kuma bana son zama a nan, ka yi wani abu a kai yallab’ai Umad, sato ni sukayi.”

D’an satar kallon Bukhatir yayi da a daidai lokacin ya tsura masa ido, ido cikin ido suka dinga kallon juna da shi kafin Umad yace mata” Ki zama cikin shiri, zan bar nan tare dake.”

Murmushi tayi ta fara tsakurar abincin, zata kai lomar farko suka had’a ido da Wudar banda murmushi da kallonta ba abinda yake, murmushin yak’e ta masa ta kai lomar bakinta tana taunawa, sautin wasu takalmin suka ji daga bayansu da kuma alamar mai tafiyar ranshi a b’ace yake, dan yanda k’arar ke fita da k’arfi da kuma sauri zai tabbatar maka da haka, Bukhatir da kujerarshi ke fuskantar k’ofar da kuma sauran mutanen Wudar kawai suka kalleta, cike da gatsali da raini ta tsaya tsakanin kujerar Bukhatir da sarki Wudar hannunta d’aya rik’e da rigarshi data sauka k’asa sosai, cikin d’aga murya tace “Wai ni ka fad’a min zaman me na ke a nan? Na je na fita banzayen masu gadin can sun hanani, me kake nufi da ni?”

Fadawan dake bayan sarki Wudar ne suka zaburo sukayi kanta d’ayan na fad’in “Murya k’asa yarinya a gaban sarki kike.”

Juyawa tayi ta wani kalkesu a wulak’ance kuma a gatsine, sake juyawa tayi ta k’arewa mutanen kan teburin kallo, sake juyawa tayi ta kalli fadawan tace “To ai ni nan ban ga wanda ya d’auki kalar kama da bawan gidan mu ba ma bare kuma sarki.”

A tsawace Bukhatir ya buga tebur d’in ya nuna mata k’ofa yace “Bar nan kafin na lalata miki fuska.”

Tsaki ta masa ta harareshi sama da k’asa kafin ta juya da k’arfi zata koma, saidai had’ewar da idonta sukayi dana Umad yasa ta tsaya cak da mamaki ta kalleshi, a hankali ta k’arasa gabanshi tana k’ak’aro murmushi a fuska tace” Yallab’ai, kai ne?”

Da sauri ta k’arasa ta ja kujerar kusa da shi ga zuba tagumi tana kallonshi bakinta har kunne tace” Amma ya akayi ka zo nan? Kai ma kasan wannan mutumin ne?”

Kallonta kawai ya tsaya yi da mamaki bai ce komai ba, murmushi ta kuma saki ta kalli Ayam tace” Yasan dalilin zuwan mu nan ne?”

Sai kuma ta kalleshi tace” Yallab’ai, kayi wani abu kai, mutanen nan sato mu sukayi bamu san su ba, ina tsoron kar su siyar da mu fa.”

Sarki Wudar da baya jin yarensu ne ya kalli Zafreen fuska a murtuke yace” Idan ma kina son d’ana ne to ya fi k’arfinki.”

Kallonshi Ayam tayi ta tab’e baki ta ture plate d’inta ta juya dan barin wurin, sarki Wudar ma ture plate d’inshi yayi yace” Cin abinci ya k’are.”

Kallonshi Umad yayi yace” Hakan na nufin zamu tafi kenan?”

Sauran ma duk mik’ewa sukayi sai Bukhatir da yace” Ina ganin hakane, na ji dad’in ziyararku.”

Sarki Wudar ne ya kalli Bukhatir yace” Mu yi magana ko?”

Jinjina kai yayi ya nuna masa wata hanyar yace” Muje ta nan.”

Su biyu suka nufi hanyar duk sauran na kallonsu, saida suka shige ciki su kuma suka nufi hanyar fita, Zafreen da haushi ya gama kamata ganin bai kulata yasa ta mik’ewa tsaye tace” Yallab’ai.”

Kallonta yayi a wulak’ance cikin jin haushin abinda ta fad’a gaba d’aya a kan su har da mahaifinshi, yanda ya zuba mata ido yasa ta fad’in” Wai me yasa kake shareni haka? Na rok’eka kayi wani abu da zan bar nan.”

Cikin abokan tafiyarsu ne ya nunawa Umad hanya yace” Yarima mu je.”

Zaro ido tayi ta kalli Umad da kyau tace” Yallab’ai, dama kai d’an sarki ne?”

Girgiza kan shi yayi ya rab’ata ya wuce suka fita, amma abun mamaki sai ta bishi a baya tana fad’in” Yallab’ai kar ka barmu a nan, ban yarda da mutumin nan ba, kar ya cutar da mu.” Bakin motocinsu suka tsaya Umad hannunshi rik’e da waya yana dannawa.

Yanda ta tsaya masa k’ik’am yasa ya d’ago kai ya kalketa, gyara tsayuwarshi yayi ya soka wayar aljihu, nuna mata hanyar da suka fito yayi yace “Muje muyi magana.”

“Tom.” Ta fad’a da fara’a a fuskarta, har zasu shiga falon da suka fito sai kuma ya kalleta yace “Ina ne suka ajiye ku?”

Turo baki tayi tace “Ni ga b’angaren da yasa aka aje ni can.” Ta nuna b’angaren dake fuskantar wannan d’in, sai kuma ta nuna b’angaren dake manne da wannan wanda yafi kowane girma tace “Amma ita anan suka ajeta.”

Gyara tsayuwarshi yayi ya shiga kallon ko ina na gidan, mai gadi a bakin k’ofa, wani dattijo dake bawa flowers ruwa saboda yamma tayi sosai, sai masu tsaron k’ofar b’angaren da Ayam d’in take su biyu, sai kuwa mutanen da suka zo tare da su, kallon Zafreen yayi yace “Ki je ki canza shigarki, zan d’aukeki a nan.”

Da sauri ta jinjina kai cikin farin ciki ta nufi hanyar b’angaren da take, tun kafin ta shige ya k’araso kusan abokan tafiyarsu ya mik’awa d’aya a cikin dreban hannu yace “Makullin mota.”

Mik’a masa yayi ya karb’a sannan ya kalli dreban yace “Shiga ciki.”

Kamar yanda ya ce haka yayi ya shiga bayan motar ya zauna, shi ma shiga yayi bayan ya zauna ya kalli dreban, fuska a had’z alamar bayar da umarni yace “Ban rigarka.”

Da mamaki ya kalleshi har saida yayi sub’utar baki yace “Rigata kuma yallab’ai?”

“E, ko ba zaka bayar ba?” Da sauri ya girgiza kai ya shiga b’alle rigar dake nuna aikinsa ya mik’a masa, karb’a yayi ya sakata a cikin rigarshi ya daidaita mata zama, fita yayi a motar sai kuma ya zura hannu ya ciro hular dreban dake kan shi.

Da sauri ya koma falon da suka fito, saida ya waiwaya inda ya ga mahaifinshi sun nufa, ganin babu kowa yasa shi yin sassarfa ya bud’e k’ofar da aka shigo da ita d’azu, ya d’auka ko wani d’aki ne amma sai ya ga corridor ne, babu kowa a k’ofar shiga dan haka ya shige ciki, ya d’auka yanda babu kowa a k’ofar haka ma a ciki, amma sai ya samu d’aya daga cikin matan nan zaune tana kallo, a zahiri kallon ba wai wani dad’i yake mata ba, dan da alamar gyangyad’i ma take, amma kuma aikin da aka sata na kula da Ayam yasa dole ta kasance a ankare.

Da sauri ta mik’e tsaye tace “Yallab’ai ya dai? Kana buk’atar wani abu ne?”

Dakewa yayi ba alamar rashin gaskiya tare da shi yace “E, ban d’aki.”

A ladabce tace “Yallab’ai ban d’akik bak’i ta can wajen ne.” Ta fad’a tana nuna masa k’ofa alamar sai ya fita, fuska a gimtse yace “Ban da lokacin da zan koma baya, ke baki san ujila bane.”

“To to shikenan, ga hanyar can yallab’ai.” Ta nuna masa d’akin tsakiya, hanya ya kama zai shiga sai kuma cikin ladabi tace “Yallab’ai.”

A gadarance ya juyo gareta, sake tausasa murya tayi tace “Ka bi sannu, domin madame na ciki, tana da masifa sosai, ka taimake ni kar kayi abinda zata hassala ta ja min uk’uba.”

Da ido ya mata alaar ba komai sannan ya sa kai d’akin, kan shi tsaye ya tura k’ofar, amma d’akin duhu kuma babu motsi, gefenshi ya kalla sai kuma yayi sa’a da makunnin, kunnawa yayi amma bai ga kowa ba a iya dubawarshi, k’arasawa yayi gaban ban d’akin ya d’an k’wank’wasa saboda jin k’arar ruwa, babu wanda ya amsa shi sai ya gyara tsayuwa ya d’an jira, ganin fa bai da lokacin jira yasa shi sake k’wank’wasa murya a tausashe yace “Jiranki fa na ke.”

Shiru ya ji babu wanda ya amsa mi shi, haushi ne yasa shi jan tsaki ya tura k’ofar yana zuba idonshi ta ko ina, sam babu alamar mutum a ciki, dafe goshi yayi ya furta “Ina kuma take?”

Rufe ban d’akin yayi ya juyo ya fito matar nan na mi shi barka da fitowa, bai kulata ba dan hankalinshi ba kan ta yake ba ya fice, wajen motocinsu ha nufa yana zuwa kuma sarki Wudar sun fito shi da Bukhatir daidai kuma da dawowar Zafreen ta saka kayanta wanda ta zo da su.

Fuska a had’e Umad ya bud’a motar ya shiga tare da mik’awa dreban daya kasa fita saboda singlet ce ta rage mi shi makulli, turus Zafreen ta tsaya tana kallonsu dan gaba d’aya kuzari ta rasa ta tunkararshi bare tasan a wacce a ke ciki.

Tana tsaye tana kallo suka gama sallamarsu duk suka shiga motocin suka d’auki hanyar barin gidan, Umad da ranshi ya gama b’aci tuni ya yanke shawarar zai raka mahaifinshi zuwa filin jirgi, daga nan zai san yanda zaiyi ya sulale musu ya dawo, dan yayi alk’awarin sai ya koma tare da ita, ba zai barta nan ba ko da zai shekara d’ari ne ko kuma hakan na nufin rasa rayuwarsa.

Sarki Wudar ma ya tafi amma fa yayi niyyar sai ya had’awa Bukhatir wata mak’ark’ashiyar da zata dawo da Ayam hannunshi, dan ba zai yarda ya rasata ba bayan shekarun daya kwashe na jiranta.

Suna isa filin jirgin dama an basu izinin tashi saboda an san da zuwansu, har farfajiyar jiragen aka bawa motocin izinin k’arasawa saboda sarki Wudar, duk firfita sukayi suka rufe motocin, sun fara takawa kenan sun bada baya suka ji an d’an bubbuga boot, Umad da dreba da sarki ne suka juyo, ganin ba komai sai suka juya suka ci gaba da tafiya, bubbugawa suka sake ji da k’arfi har da tagomashin ihu ana kiran “Kaiiiii! Taimako?”

Umad na d’aukar muryar ya dawo da gudu yayi azamar d’aga boot d’in, da wani irin k’arfi Ayam ta tashi zaune ta sauke kakk’arfan numfashi, kallonshi tayi idonta duk sun rikid’a tace “Da na mutu fa, kai akwai takura a cikin nan.”

Tattare rigar tayi ta zuro k’afafunta ta diro daga motar, Umad kam a bad’ini farin ciki ne ya kama shi, to amma mamakin yanda akayi ta shigo nan sai ya hana shi shak’at, da sauri sarki da sauran mutane suka k’araso, sarki Wudar da farin ciki a fuskarshi yace “Zafeera, ke ce dama? Ya akayi kika zo nan?”

Murmushi ta sakar masa ta tafa hannayenta tace “…

 

*Alhamdulillah*

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like