Lu’u Lu’u 15

Advertisement

*15*

 

Murmushi ta sakar masa ta tafa hannayenta tace “Ni ce, ai guduwa na yi, na rok’eku ku tafi da ni, idan na bar nan daga can zan koma garina ni ma, kai tsaye ma gidanmu zan wuce dan mutanen can sun tsorata ni da haukansu.”

Da fara’a sarki Wudar ya amsa mata da “Haba ai ba sai kin rok’emu ba, mu da masarautarmu ai duk mallakinki ne.”

Nuna mata hanya yayi yace “Muje ko?”

Kallon wani bafaden shi yayi cikin rad’a yace “Ka tabbatar bata samu matsalar hawa jirgi ba.”

Jinjina kai yayi ya juya zuwa gurin masu ruwa da tsakin na kampanin, su kuma tuni suka shiga jirgin har da Ayam d’in wacce har zata zauna kusa da Umad sarki Wudar ya nuna mata kusanshi yace “Zauna nan.”

Cike da girmamawa ta zauna kamar yanda ya ce dan ita a uba take kallonshi tunda mahaifin malaminta ne, sun d’auki a k’alla minti sha biyar kafin jirginsu ya d’aga zuwa k’asar Giobarh.

Kamar wacce ke son fakar idon mutane tayi sata haka Ayam ke son fakar idon sarki ta ma Umad magana, bakinta cike yake da kalamai inda zuciyarta ke tumbatse da tambayoyi kala kala, shi kan shi Umad a k’alla zata jefa masa tambayar data bawa guda biyar baya, dan haka ta matsu, ta k’agu ko jirgin nan ya sauka su keb’e ta fara bayani.

Har ga Allah sai ta fara bashi dariya saboda yanda ta tsaresa da ido bakinta kam mm-mm-mm kawai yake, hnnayenta dake kan hannun kujerar sai bubbugasu take tana d’an jijjiga k’afafunta, daya kalleta yake d’auke kan shi dan ya sani ne da magana a bakin nan da take ta turo masa.

Advertisements

Adadin awoyin da suka d’auka gurin tafiya yanzu ma suka b’ata illa sab’anin sakanni kawai, Ayam ta ga ikon Allah ganin idonta sanda aka shiga yi musu tarba ta musamman ana murnar dawowarsu ka d’auka shekara sukayi basa nan.

Ita yanda ta ga ana t sunkuyawa Umad shi ya fi bata mamaki, suna shiga katafaren falon ta kuma bud’a idonta tana lumshe su a hankali, saida suka kai tsakiyarsa suka tsaya, a k’alla hadimai maza da mata sama da goma ne suka ding rusunawa suna gaishesu, babban abun mamakin yand sarki Wudar ke ta nunata yana fad’in Zafeera ce, kai ita wannan suna ma k’ona mata rai yake, wani wai Zafeera a ganinta fa.

Wani dattijuwa ya nuna mata yace “Wannan ce zata zama mai kula dake daga yanzu, duk abinda kike da buk’ata kai tsaye ki fad’a mata zata sanar min.”

Da mamaki Ayam ta d’aga labb’a tace “Amma kum…”

Nuna mata wata kyakyawar matashiya yayi wacce shigarta ta banbanta data sauran da alama itama babba ce a gidan yace “Wannan Joyran kenan, k’anwar matata ce, sakamakon rashin lafiyar dake damun uwar d’akina wacce muka rasa gabanta yasa yanzun alhakin kula da cikin gidan nan yake wuyanta.”

Kallon fuskarta Ayam ta sake yi, a kallon nan d’aya tak ta ji sam matar bata kwanta mata a rai ba, uwa uba kwalliyar dake fuskarta ta wayayyi, kayanta kua duk da na sarauta ne manya amma rigar ta fito da maman ta sosai.

Joyran ma haka ta k’ura mata ido cike da zababbiyar tsana da kishi had’e da takaici da jin kamar ta shak’o wuyanta, tsabar ta rasa jurar halin da take ciki yasa ta gagara b’oyewa har saida tabi Ayam da mugun kallo sannan ta d’auke kan ta ta mayar kan sarki Wudar, wani fitinannen kallo ta masa ta shiga masa signa da ido alamar tana son magana da shi ya kuma biyota.

Da kai ya fara amsa mata ta hanyar gyad’ashi kad’an yanda babu wanda ya gane, sai kuma ya lumshe ido alamar tabbatarwa, tana samun amsarta ta juya a fusace ta bar falon zuwa b’angaren daya zama na ta yanzun.

Sarki Wudar ne ya kalli dattijuwar nan yace “Ki rakata d’akin kusa da na sarauniyata, ki mata duk abinda ta buk’ata.”

Sunkuyawa tayi tace “To shugabana.”

Matsawa tayi kusa da Ayam ta nuna lata hanyar da zasu bi tace “Muje ranki shi dad’e.”

Satar kallon Umad tayi da gaba d’aya yayi kamar baya wurin yake ta danna wayarshi, kallon sarki tayi a shagwab’e ta nuna Umad da yatsa tace “Yallab’ai, ka had’a ni da wannan mana ya rakani, na ga ya na jin yaren da na iya.”

Advertisements

Dakatawa yayi daga danna wayar amma bai kalleta ba, sarki Wudar kam jiki na b’ari na ta fad’i buk’atar ta ya nuna Umad yace “Yarima na, ka je sai ka rakata ka ji ko, idan da wani abu da take buk’ata sai ka fad’awa jakadiyarta.”

Kallon fuskar mahaifinshi yayi irin kallon me kake nufi kuma? Ni ma fa masu hidima ne da ni, ha kuma zan zauna yi ma wata rakiya.

Maida kallonshi yayi gareta, har yanzu dai abu d’aya yake gani tareda ita wato zance, sake kallon sarkin yayi ya jinjina kai alamar to, a wani gadarance cikin takon sanyi ya shiga takawa kamar wanda k’wai ya fashewa a ciki, haka suka shiga taka matakalar har suka haye sama yana gaba tana baya, d’aki na farko suka wuce haka ma na biyu inda mahaifiyarshi take, na uku ya bud’e ya kauce a hanya alamar ta shige.

Hannu biyu ta sa ta tura k’ugunshi zuwa cikin d’akin, kamar zai fad’i haka yayi yana kallonta da mamaki, shiga tayi ta ja k’ofar ta rufe da sauri ta k’arasa gabanshi, takalmin k’afarta ta cire da hannunta masu tsini sannan ta dafe k’ugu suna ci gaba da kallon juna tace “Uhum! Tel me, me yake faruwa?”

Wani shashantar da zancen yayi ya mayar da wayarshi aljihu, juyawa yayi ya k’arasa gaban gadon dake lafiye da shinfid’a ya zauna, kallonta yayi yace “Ban gane ba?”

Da sauri ta matsa gabanshi ta zauna k’asa ta tank’washe k’afafu ta rik’e k’afarshi d’aya tana ta mitsikawa tace “Ka ga na fa gane ka, tambayoyi na a kan ka masu yawa ne, yanzu ka fara amsa min wannan?”

Jinjina kai yayi yana siririn murmushi yace “Zana duka tambayoyin, zan amsa miki su d’aya bayan d’aya.”

Sakin k’afarshi tayi ta dinga nuni da yatsunta tana lissafi tace “Na d’aya… Ba kayi mamakin ganina a gidan nan ba, shiyasa ban ji ka tambaye ni me kike yi a nan ba ko me ya kawoki nan? Na biyu kai ma me ya kai ku can a wannan lokacin? Shi mutumin nan waye shi? Me yake nema a gareni daya saceni? Sannan me yasa ka ce kar na nuna musu na san ka.”

Gyara zamanshi yayi ya sauke numfashi yana kallon fuskarta yace” Me yasa kika tambaye ni duka wannan? Me yasa shi baki tambaye sa ?”

Yatsina fuska tayi tace” To ai na tambaye shi amma shi da yarinyar nan suka dinga fad’a min wasu maganganu na daban.”

Kafeta yayi da ido yace” Me suka fad’a miki?”

Cikin turo baki tace” Wai ni yar uwarta wannan ita mai shegen girman kan ce, wai k’anwarta.”

Mik’ewa yayi tsaye ya d’an shiga takawa d’aya biyu sannan ya juyo ya kalleta ita ma ta juya ta kalleshi yace” Gaskiya suka fad’a miki, yayarki ce.”

Zunbur ta mik’e tsaye tace” Me? Kamar ya? Ka kuwa san me kake fad’a?”

Girgiza kai tayi tace” Ta ya ya?”

Kallonta yayi cike da tausayin yanayin da zata samu kan ta yace “Ki samu kiyi wanka ki ci wani abu sai ki huta, zuwa dare zamuyi magana.”

Matsawa tayi kusanshi ta girgiza kai tace “Ba zan iya ba yallab’ai, ka daure ka fad’a min ko na samu sassauci, ina so na san dalilin da yasa aka kawoni nan, kuma ina so na ga iyayena.”

Tsare fuskarta yayi da ido yace “Ayam.”

Zuba masa ido tayi ita ma tace “Na’am.”

A sanyaye yace “Kiyi abinda na ce, bana so idon mutane ya dawo kan mu yanzu.”

Dantse leb’enta tayi da hak’ora dan yanda ya mata magana yanzun ba zata iya musawa ba, sunkuyar da kai tayi dan gabanta fad’uwa yake, tunaninta bai wuce son sanin wane irin garari ne ke neman tunkaro rayuwarta haka? Me ye b’oye a cikin rayuwarta haka da ake neman bankad’o mata shi yanzu? Ko kuma dai sab’ani aka samu wata ake nema ba ita ba? Rashin sanin ko d’aya daga cikin amsoshin nan yasa ta jin k’walla taf a cikin idonta.

Lumshe ido Umad yayi ya sake bud’ewa a kan ta, dan ba komai ya zo masa ba sai tunanin ta yanda zai fara fad’a mata wacece ita, da kuma alak’arsu ta yanzun, a hankali ya tako gabanta ya saka yatsa d’aya ya tallabo hab’arta, suna had’a ido hawayen suka gangaro kan kumatunta har saida suka sauka kan yatsarshi.

Cike da rashin jin dad’i yace “Ohh! Haba dai zakanya, kuka kuma? Kiyi hak’uri kinji, na miki alk’awarin fad’a miki komai anjima, yanzu babu lokaci ne, ki daina kukan nan bana so.”

Kamar k’ara zugata ne yake sai kawai ta fashe da kukan da ita kan ta a rayuwarta bata tab’a irinsa ba idan ka cire na farin ciki da tayi sanda gwamnatin Khazira ta d’auki nauyin karatunta a sanda iyayenta suka nemi gazawa, ba tare da sanin me tayi ba, cike da son samun wanda zai rarrasheta, cike da kwad’ayin a lallab’ata ta fad’a k’irjinshi tana ci gaba da kukan.

Gam gam ya rintse idonshi sakamakon irin jijjigar da jikinshi ya d’auka, ya san ba da wata manufa ko niyya tayi ba face hakan su ba komai bane, saidai shi yanzu yana da ak’ida, yana da madogara da kuma k’akk’arfar shari’ar dake saitashi ga daidai da barin daidai, sa’a d’aya ita ce akwai igiyarshi a kan ta, amma dake abun sabo ne gareshi sai ya gagara komai, jinta yake har cikin b’argon jikinshi da jininshi, jin ta yake can k’asan k’asan zuciyarshi kamar tare aka haifesu, sai yake tuhumar ko dai jikinta ne ke da wannan tasirin.

Jin bata samu abinda take nema ba sai kawai ta jaye jikinta daga na shi cike da kunya kanta sadde ta juya mas baya, bakin gadon ta zauna tana share fuskarta ta k’i d’aga kai bare ta kalleshi.

Shi kan shi sai yaji wata kunya ta kama shi daya kasa d’an daddab’a bayanta ko ya ya dan ta ji sanyi, a kunyace ya juya shi ma ya fice a d’akin.

Tana ganin ya fita ta fad’a kan gadon ta sake rushewa da wani kukan tana sake fad’in “Wai me yake shirin faruwa ne da ni?”

Umad na fita kai tsaye b’angaren Joyran ya nufa inda ya ga mahaifinsa yayi, bai samu kowa a b’angaren ba haka ma a falon, tsaye yayi a tsakiyar falon yana dubawa, a ranshi ya tambayi kan shi “Ina kuma suka nufa?”

Hannu d’aya yasa ya shafi sumarshi ya d’aga kafad’a alamar ohon nan sannan ya juya zai fita, ya fara takawa kenan ya ji sautin Joyran ta kwamtsa k’ara da “Ahhhhh.”

Dakatawa yayi ya juya ya kalli k’ofar da ya ji sautin, da d’an sauri ya fara takawa dan ya ga ko lafiya, sai kuma ganin mahaifinshi yayi ya fito daga d’akin Joyran a bayanshi ta rik’e babbar rigarshi tana share hawaye.

Wani irin mummunan bak’on yanayi ne ya ziyarceshi sanadiyar abinda zuciyarsa ta hasko masa lokaci d’aya, gagara komai yayi sai zuba musu ido suna ta kame-kame, daga bisani kuma sai mahaifinshi ya juya gareta a hassale ya fincike rigarshi ya nunata da yatsa yace “Na gama magana Joy, ko kina so ko ba kya so yanda na fad’a haka za’a yi, dan ba zan yarda ki zubar min mutumci ba, kowa laifina zai gani a ce da saka hannu na a faruwar komai.”

Juyowa yayi dan fita har ya zo daf da Umad zai rab’ashi ya wuce, da kallo Umad ya bishi yace” Sarki na, meyake faruwa ne?”

Wani huci ya dinga saukewa yana hararen Joyran data k’araso garesu, cikin shashek’ar kuka tace” Umad, mahai…”

Da sauri ya katseta da fad’in” Ciki ne da ita, ni kuma ba zan yarda wannan labarin ya fito ba.”

Da matsanancin mamaki ya kalli sarki yace” Ciki?”

Kallon Joyran yayi data shiga k’yabta ido, a razane yace” Ta ya ya? Goggo wa ye ya miki ciki kuma ba…”

Da sauri sarki Wudar yace” Waziri ne, dama soyayya suke amma rashin lafiyar mahaifiyarka ta sa ta k’i aminta da maganar auren.”

Wani iska Umad ya huro daga bakinshi ya dafe goshi, shiru kamar ba zai ce komai ba, ya d’an jima haka suma kuma jiran abinda zai fad’a suke, can ya d’ago ya kalleta yace” Amma gwoggo m yasa zaki yarda da haka kamar wata k’aramar yarinya, yanzu gashi ya kike so muyi?”

Sarki Wudar ne yace” Abinda nake fad’a mata kenan, na ce a zubar ta dage ita ba za’a zubar ba.”

Zaro ido yayi ya kalli mahaifinshi yace” Sarkina zubarwa kuma? Gaskiya ni ma ban goyi da bayan haka ba, kar a zubar mahaifina.”

A d’an hassale yace” To yanzu ya kuke so a yi? Ba fa zan yarda a haifa min shegen nan ba.”

Da wani kallo Joyran ta d’aga kai ta kalleshi, da k’yar ta had’iye abinda ya tokare mata ta sunkuyar da kai, a nutse Umad ya kalli mahaifin na sa yace” Abba na ka je kawai, zamuyi magana da ita, kar ka damu da abinda mutane zasu fad’a, zan ji da komai.”

Kallon Joyran sarki yayi irin kallon garhad’i kafin ya juya a hassale ya fita, ajiyar zuciya Umad ya sauke ya kalli agogon hannunshi, kallonta yayi da sauri yace” Goggo zan je amma zan dawo, ki kwantar da hankalinki kinji.”

Jinjina kai tayi alamar to, da sauri ya juya ya fita dan sallolin dake kan shi yae san saukewa wanda suka riskeshi a hanya.

*12:36* daga d’akin mahaifiyarshi cikin sand’a ya shigo nan ba tare da ya bari kowa ya gan shi ba, a hankali ya bud’a k’ofar ya shiga ya mayar ya rufe, yana juyawa das ya sameta zaune tsakiyar gadon, fad’uwa gabanshi yayi dan yanda ta zubawa k’ofar ido da kuma yanda take zaune ya nuna fa tun da ya fita ya barta haka take, a hankali ya k’araso yana kallon fuskarta da idonta da sukayi jajir suka d’an kumbura, jiki a mace ya zaune gefenta yana ci gaba da kallonta ita ma kuma haka.

Cikin tattausan murya yace “Me yasa da aka kawo miki abinci kika kori mai aikin?”

“Saboda ba shi nake da buk’ata ba.” Kallonta yayi yace “Me kike da buk’ata yanzu?”

D’auke kai tayi daga gareshi tace “Iyaye na, ina so na gansu, ka mayar dani wajensu ni har karatun ma na fasa.”

Girgiza kai yayi yana murmushi ya jawo wayarsa a gaban aljijunshi, tana kallo ya dinga danna wasu lambaobi, ko da ya danna ok ya mik’o mata wayar yace “Kiyi magana da su, hakan zai sa hankalinki ya kwanta.”

Da sauri ta karb’i wayar ta d’ora a kunne jin tana k’ara, ana d’auka cikin muryar kuka da sangarta tace “Hello!”

Cikin zumud’i da karsashi Habbee ta amsa da “Gimbiyata, gimbiya kina lafiya?”

Mik’ewa tayi tsaye tace “Mah ban da lafiya, gaba d’aya bana jin dad’i, so nake na ganku.”

Cikin ladabi Habbeetace “Kiyi hak’uri kinji gimbiya, zamu had’u nan kusa, ki kwantar da hankali ki saki jikinki da mutumin nan, mutumin kirki ne, na tabbata zai kula dake yanda ya kamata.”

Juyowa tayi ta kalli Umad sannan tace “Mah, ni ban yarda da kowa ba, maganar gaskiya ma a tsorace nake, wasu abubuwa ke ta faruwa a nan kuma babu wanda yake min bayanin komai.”

Daga b’angaren Habbee ta numfasa tace “…

*Kuyi hak’uri da wannan yan uwa, akwai gobe Insha’Allah*

 

*Alhamdulillah*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

SALON SO BOOK 1 PAGE5-6

Advertisement  ðŸ¾ðŸ¾ðŸ¾ðŸ¾ðŸ¾ðŸ¾ðŸ¾ðŸ¾ðŸ¾ðŸ¾             🌹 SALON SO 🌹 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾     BOOK ONE 📖…

SIRADIN RAYUWA 8

Advertisement  ðŸ‘‘ *SIRAƊIN RAYUWATA*👑 *wannan littafin na siyarwa ne,kuma amanace a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar…

SIRADIN RAYUWA 6

Advertisement  ðŸ‘‘ *SIRADIN RAYUWATA*  _wannan littafin na kudine,kuma AMANA ce a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar…

YAU DA GOBE 13&14

Advertisement  ðŸ¾ðŸ¾ðŸ¾ðŸ¾ðŸ¾ðŸ¾ðŸ¾ðŸ¾ðŸ¾   🌹YAU DA GOBE 🌹 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Story & writing by mmn farees 🅿️13&14 …..Wata irin zabura…