Advertisement
*4*
Bayan fitar Umad aka kira wayarshi, ganin mai kiran yasa hankalinshi ya tashi da sauri ya d’aga kiran yana fad’in “Hello yallab’ai.”
Daga can b’angaren wazirin sarki Musail yace “Yallab’ai Jacob, ya aiki?”
“Lafiya lau yallab’ai.”
Wazirin ne yace “Kaga na kiraka ko?”
Amsawa yayi da fad’in “E yallab’ai, fatan dai lafiya?”
Wani d’an murmushi yayi yace “Lafiya lau, gimbiya ce ta kirani yanzu take fad’a min sun samu matsala da wata ‘yar talakawa, ta fad’a min yarinyar ta ci mutumcinta sosai.”
Mik’ewa yayi tsaye yace “A nan makarantar? Wacece wannan?”
A gadarance yace “Sunanta Ayam.”
Advertisements
Zaro ido yayi dan har jikinshi saida ya amsa sunan, ba kasancewarta wacce gwamnati ta tsaya ma ba, shi kawai yarinyar tsoro take bashi, shiyasa ko kallon fuskarta baya son yi, yarinyar da zata maka yare kuma ta nuna bata son wane yare tayi ba. A ladabce yace “Yallab’ai ya kake so a yi yanzu?”
Kai tsaye ya furta “A koreta ko da kuwa k’arshen shekararta ce wannan, hakan zai zama izina ga yan baya.”
Da sauri ya cire hular kansa yace “Me?”
Da mamaki waziri yace “E, ko da matsala ne?”
A gigice yace “Yallab’ai *Khatar* akwai babbar matsala ma, dan yarinyar nan da kuke gani gwamnati ce ke d’aukar nauyin karatunta, yallab’ai Ayam bana jin ko a k’asar England za’a iya korarta a makaranta bare 脿 nan k’asar.”
Cike da tsiwa waziri Khatar yace “To shine me? Waye ubanta a k’asar nan?”
Girgiza kai yayi cike da tausayin kanshi dan har wata zufa ke tsatsafo masa yace “Yallab’ai Khatar ba ‘yar kowa bace, hasalima mahaifinta ba wani hamshak’i bane, amma kuma tasirin yarinyar yafi na democrad’iya.”
Wawan tsaki ya ja tare da fad’in “Kenan yanzu babu abinda zaka iya yi?”
A sanyaye yace “Gaskiya yallab’ai akan yarinyar nan zan iya rasa aikina had’e da tukuicin shiga babbar matsala, dan kad’an daga cikin ikon da gwamnati ta ba wa yarinyar nan, akwai lamunce mata ta ziyarci iyayenta duk sanda ta so, dan ma yarinyar na da lissafi ne take daidaita kanta da sauran d’aliban.”
A tsawace Khatar yace” Shiru malam, ni ba wannan na tambayeka ba.”
Cikin rarrashi yace” Kayi hak’uri yallab’ai, na maka alk’awarin zan ja mata kunne ta fita harkar gimbiya Zafreen.”
K’it! Ya kashe wayar hakan ya ba colonel d’in damar sauke numfashi mai nauyin gaske shi ma ya aje wayar.
Advertisements
K’aramin Sajan (sergent) d’inshi ya kira yace” Kira min Ayam *Utais*, izuwa yanzu suna aji tare da malam *Pedro*.”
Sara masa yayi ya amsa da” To yallab’ai.” Sannan ya fice.
Mintuna k’alilan suka shigo tare da ita, fita yayi bayan ya mata iso ta samu wuri ta zauna tana kallon major d’in, saida ya rufe musu k’ofar kafin ya kalli fuskarta saidai ba cikin idonta ba yana wani inda-inda yace “Am… Ayam Utais, dama nasa…a kirani ne naji dalilin samun sab’aninki da gimbiya Zafreen?”
K’uri ta masa da idonta hakan yasa shi mik’ewa tsaye yana dariyar rashin gaskiya kamar wacce tace kwab’e kayanka na zaneka, cikin duburburcewa ya ke fad’in “A’a, kin gane ko? Ba komai ma ba sa茂 kin fad’a ba, abinda nake so dake kawai ki rabu da ita, karki sake shiga sabgarta dan ke karatu ne ya kawoki nan, kin kusa kammala zangonki dan haka ki maida hankali kinji.”
Turo baki tayi gaba kawai ta jinjina kai alamar gamsuwa tare da mik’ewa zata fita, da sauri yace” Kina ji Ayam.”
Tsayawa tayi ta juyo tana saurarenshi, d’orawa yayi da fad’in” Gobe mai horar daku malam Pedro zai koma k’asarshi, dan haka gobe da safe zaku ci gaba daga inda kuka tsaya tare da sabon mai horarswa.”
A sanyaye ta maimaita” Sabon mai horaswa?”
“E.” Ya fad’a yana komawa ya zauna, jinjina kai tayi ta fita a ofishin tana tab’e baki da maimaita sabon mai horaswa? Waye shi? Kuma da wane salo zai zo shi kuma? Ko shi ma irinsu malam *Elinio* ne da ya gama latse ‘yan mata kafin ya koma k’asarsa Brazil?
*Suna* zazzaune wajen cin abinci da dare Ayam ta kalli k’awayen na ta su uku tace “Kunsan me? D’azu colonel yake fad’a min wai gobe za’a kawo mana sabon mai horaswa.”
Duk k’ura mata ido sukayi sai Deeyam da tace “Sabon mai horaswa kuma? Gobe gobe kuma? To me ya samu Pedro d’in?”
Saida ta zura cokalin robar a bakinta tace “Yana nan, babu abinda ya sameshi, da alama wani aiki ya samu daya fi wannan.”
Jinjina kai sukayi kafin Ayam ta sake fad’in “Kunsan ni me nake so, ina tsoron kar a kawo mana irin malam Elinio, yana mana darasi yana tsaremu da ido yana kallar mana d’uwawu.”
Dariya Deeyam tayi tace “To ya zamuyi idan ma irinsa ne? Mu dai na mu bijire masa ne kawai.”
Kallon Deeyam d’in tayi tace “Ni kuma ba haka nake so ba, kunsan me zamuyi?”
Girgiza kai sukayi inda d’aya a cikinsu tace “Sai kin fad’a.”
Cikin rad’a tace “Mu kai ziyara b’angaren malaman, ta haka zamu san wane iri ne shi dan mu d’auki matakin kare kanmu.”
Zaro ido sukayi sai Deeyam da tace “Ta ya ya haka zai faru? Ko kin manta ba’a barin d’alibai zuwa b’angaren da malamai suke, haka su ma malaman basa zuwa inda d’alibai suke?”
Waina idonta tayi sannan ta k’urawa Deeyam su tana kallonta, kawar da kanta tayi murya k’asa k’asa tace “Ki daina kallona haka Ayam, na rantse miki saida gabana ya fad’i.”
Tab’e baki Ayam tayi ta d’auke idonta tace “To na d’auke, ni dai yanzu ku bar min komai a hannuna kawai, ku dai ku shirya zan tasheku a tsakiyar dare.”
Tana gama fad’a ta mik’e tare da juyawa ta bar wurin, da kallo suka bita da fari kafin d’aya 脿 cikinsu tace “Kamar kullum, yau ma mu zamu d’auke mata farantin abincinta.”
Deeyam dake cin abinci ce tace “Tunda kinsan da haka, me ye na bitar shi kuma?”
Wata a ciki ma murmushi tayi tace “Lokuta da dama Ayam tayi abu sai ka d’auka wata sarauniya ce.”
Dariya suka yi gaba d’ayansu haka har suka kammala suka mik’e suma da farantan a hannayensu suna ajewa wurin da aka keb’e dan ajesu kamar sauran d’alibai.
*01:43*
Tana daddab’a Deeyam ta bud’a ido tace mata “Tashi mu tafi.”
Tashi tayi zaune tana murza ido tace “Ayam, ina kuma zamu je?”
Cikin rad’a tace “Tashi mu tafi kedai.”
Sake bud’a idonta tayi ta kalli saura k’awayen dake bayan Ayam dukansu cikin kayan baccinsu, a hankali ta sulala ta sauka akan gadon.
Cikin sand’a suka dinga fita a d’akin har sukayi sa’ar haurawa ta wani corridor ba tare da tsoron su fad’i ba, ai kuwa a sauk’ake sai gasu a b’angaren malam kamar wasu b’arayi, jerawa sukayi suka dinga hawa matakalar har suka iso wajen d’akunan, kallon juna sukayi Deeyam tace “Ina d’akin?”
Nuna musu Ayam tayi tace “Wannan d’akin ne ai babu kowa.”
K’arasawa sukayi suka sake tsayawa cirko cirko, kallon su Ayam tayi tace “Yanzu Sabrine ke ki fara shiga.”
Waro ido tayi tace “Me yasa ni zan shiga.”
Cikin rad’a Ayam tace “To ai kin fi mu kyau da dirin halitta mai kyau.”
Harara ta wurga mata tace “Na k’i to, babu ruwana ni.”
Juyawa Ayam tayi ta kalli Deeyam tace “To ke ki shiga, tunda kina da abubuwan d’aukar hankali.”
Cikin fad’a Deeyam tace “To wai ke da kika jagorancemu me zai hana ki shiga?”
Wata dariya tayi ta kalli kanta tace “Haba dai, dubeni fa, aini bana da fasalin d’aukar hankalin namiji, ba kowane namiji nake birgewa ba saboda nayi rama dayawa.”
Tab’e baki Sabrine tayi tace “To saidai mu koma kam, amma babu inda zanje.”
Deeyam ma had’e hannaye tayi tace “Ni ma haka.”
D’ayar ce ta kallesu tace “To mu koma kunji, bana son wani ya ganmu za’a hukuntamu.”
Cikin rad’a Ayam tace “Yanzu ku d’an aikin nan ne zai gagaremu? Kun manta irin tijarar da muka zuba a baya ne?”
Deeyam ce tace “Bamu manta ba, amma dai yau kam ni dai babu ruwana, inda matsalar take shine rashin sanin waye malamin, ni bansan me yasa kika damu da son sanin wane iri ne shi.”
Gyara tsayuwa Ayam tayi da kyau ta kallesu tace “Ku fad’a min zaku shiga ko a’a?”
“A’a.” Sabrine ta fad’a tana juya baya, jinjina kai tayi tace “Shikenan, ni zan shiga ciki, amma ku jirani a nan.”
Murmushi Deeyam tayi tace “Fatan nasara.”
Harara Ayam ta jefa mata tana gyara hularta tace “Matsalarku ce.”
Kallon k’ofar d’akin tayi tana sauke numfashi, wani yanayi na tsoro da fad’uwar gaba take ji wanda bata tab’a ji ba, hatta da jinin jikinta ji take ya k’ara gudun tafiyarshi.
Cije leb’enta tayi na k’asa sannan ta kai hannu ta k’wank’wasa k’ofar d’akin, amma sai ta ji shiru babu ko alamar motsi, sake kwank’wasawa tayi nan ma shiru, a karo na uku ta sake kwank’wasawa tana jan gajeran tsaki.
Deeyam ce tace “Ayam, tunda kika ji shiru ki zo mu je kawai, watak’ila baya nan.”
Sabrine ce ta karb’e da fad’in “Ko kuma ma bai zo ba.”
Juyowa tayi ta kalli Sabrine da tayi maganar tace “Hakane?”
D’aga mata gira tayi alamar e, jinjina kai tayi tace “Bari mu gani to.”
Cikin sand’a ta kama hannun k’ofar ta murd’a a hankali, jin ta bud’e yasa suka kalli juna, maida kallonta tayi ga k’ofar ta tura a hankali tana shiga cikin d’akin.
Tattausan k’amshin turaren 112 ne ya fara mata maraba, sai kuma siririn hasken daya gauraye d’akin, komai na d’akin a gyare kuma a killace yake sannan a tsaftace, babu alamun da suka nuna akwai mutum a d’akin, hakan yasa ta bayan k’arewa d’akin kallo ta jawo k’ofar da niyyar rufewa.
Cak! Ta dakata sakamakon tsikayar wani k’aramin hoto a gefen gadon ajiye, sakin hannun k’ofar tayi ta k’arasa da sauri ta d’auki hoton, k’urawa dattijuwar matar ido tayi mai cikar kamala da haiba, tana cikin shiga ta alfarma kamar wata sarauniya. Samun kanta tayi da sakin murmushi sanadiyar k’aunar matar data ji, a hankali a asalin harshenta na slovaque tace “Watak’ila ya manta da hoton ne?”
Sai kuma ta tambayi kan ta “To amma wa ya zauna a d’akin?”
Rashin sanin amsar yasa kawai ta d’aga kafad’a alamar ko oho, juyawa tayi ta fara tafiya hannunta rik’e da hoton.
Tana daf da hita aka bud’e k’ofar k’aramar ban d’akin dake cikin d’akin, da sauri kuma a mugun tsorace ta kalli inda ta ji k’arar, a wani bala’in tsoracen wanda bata san sanda ya ziyarceta ba ta saki hoton wanda ke lullub’e da kwalba ya fad’i k’asa.
K’arar glass d’in da kuma ihunta a tare suka gudana, sai kuma tayi saurin yin gum da bakinta kamar wacce aka tusawa k’wallon goriba a bakin.
Idonta masu abun al’ajabi ta zuba masa tana kallo ba tare da rusunawa ko jin d’ar a yanda ta ganshi ba, a hankali take yi tana k’yabta idonta tana kuma sauke numfashi kamar wacce aka b’atawa rai, a zahirinta kamar jira take yace kul tace cas, amma a bad’ini kuma gabanta ci gaba yake da fad’uwa, ganinshi d’aure da towel d’in nan kalar shud’i ba k’aramin gigita mata lissafi yayi ba, dogo ne sosai mai k’ira da zubin jarumai, duk da ba wata murd’add’iyar sura ce da shi mai jan hankali ba, amma dai yana da fasali mai kyau wanda zai iya juyar da k’irarshi a duk ta yanda ya so.
Duk da bak’i ne amma kuma bak’inshi mai kyau ne da k’yalli kamar na macen dake samun gyara a kai a kai.
A hankali cikin b’acin rai da mamakin abinda ya kawota d’akinshi ya tsura mata ido, yana d’ora ido 脿 kan ta saida launin idonshi suka canza tsabar haushi da takaici, sai yake bala’in jin kamar ya k’urma ihu dan ya samu sassaucin abinda ya tokare masa zuciya.
Ba ma wannan ba, wai a kan wane dalili ne shi kam yake had’uwa da wannan mai zubin aljanun ruwan, ga ta dai 脿 cikin kayan bacci wando iya gwiwa da riga mai k’ananan hannu, gaba d’ayanta fa ba zata gagareshi ya dunk’uleta a hannu d’aya ya jefata a hudar hancinshi sannan ya fyatota.
Kallon hoton dake k’asa yayi, da sauri ya tako ya tsaya gabanta tare da durk’usawa yana kallon hoton, a mugun fusace ganin yanda hton ya fashe ya sa ya d’ago ya k’ura mata ido.
Ayam da tunda ya fara takowar nan da sauri gabanta ya shiga dakan uku, kasa motsawa tayi sai bakinta data warwareshi daga kumburewar da ta mishi, hannayenta ta d’ora kan mararta ta dafe tana fatan kar fitsari ya taho mata.
Umad kam cikin fitar hayyaci ya d’aga hannunshi ya wanketa da mari, a k’ufule ba tare daya bata damar gama fahimtar rad’ad’in ba ya nuna mata k’ofa da yatsa cikin hard’add’iya kuma nagartacciyar muryarshi da harshenshi da ya fi k’warewa a yaren Gallois yace “Fita a nan, kuma karki bari mu sake had’uwa, *b’arauniya* kawai.”
Da sauri ta d’aga idonta dake kallon k’asa ta kalleshi jin sunan daya bata. Shi ma sai lokacin ya fahimci wani abu a tare da ita, ya mareta marin da yake da tabbacin ya ratsata sosai, to amma” Me yasa bata yi ihu ba? Kuma bata fad’i ba duk da rashin nauyinta.” Abinda ya tambayi kanshi kenan, sam kamar ma ba ita ya mara ba a fuska.
A gaggauce ya kawar da tunanin ya maida hankalinshi ga Ayam data rumgume hannaye a k’irji cike da izza, salo da kuma gadara tana kallon k’wayar idonshi ita ma cikin harshen Gallois da bata tab’a sanin ta iya ba tace “…
*Alhamdulillah*
GIPHY App Key not set. Please check settings