Advertisement
*6*
Fitowarsa tayi daidai da k’arasowar su Zafreen zasu je b’angaren su Ayam dan ganawa da wata k’awarsu, zasu wuce shi ma zai wuce kawai Zafreen ta k’ura masa ido, baki da hanci ta saki tana binshi da kallo, cike da birgewa ta juya saboda har yayi gaba ba tare da sanin me take ba tace “Wow! Amma malamin nan ya had’u.”
Laika ce tayi saurin kallonta tace “Gimbiya Zafreen, kina nufin ya birgeki ne?”
Juyawa tayi ta kalli Laika tace “Sosai ma, idan har zan iya yin aure to shi ne mijina.”
Murmushi ta saki ta kalli k’wayar idon Laika tace “Ina zuwa.”
Kafin Laika tayi wata magana har Zafreen ta tafi da sauri tana fad’in “Malam, malam ji mana.”
Tabbatarwa da yayi da shi ake yasa shi dakatawa ya juya, a tsanake ya shiga k’are mata kallo, tabbas kyakyawa ce data amsa sunan kyakyawa, komai na ta yayi kuma y had’u, bata da makusar da duk namiji mai son more rayuwa ba zai so samunta ba.
Kayan jikinta sun nuna mishi a wani b’angaren take nata karatun, ga kuma wani yankakkan gashi dake kan ta mai kalar ruwan d’orowa wanda haka kalar idonta ma suke.
Iya fatar jikinta ta nuna masa ita ma yar hutu, ko ‘yar hamshak’in mai kud’i, ko ‘yar mai iko ko kuma sarauta, tana k’arasowa ya sake gyara tsayuwarsa.
Saida ta zo daf da shi sai kuma sai ta ji wani kwarjininshi ya kamata, kanta sadde a k’asa ta shiga doka murmushi, cikin sanyayyar murya tace “Malam barka.”
Advertisements
Fuskar nan a had’e ya amsa da “Uhum.”
Duburburcewa tayi ta shiga rausayawa kamar zata taka rawa, kame-kame ta fara tace “Am.. Dama dai… Ni sunana Zafreen Musail, gimbiya Zafreen Musail.”
Tsura mata ido, da fari dai ya d’auka mai hankali da ilimi ce, ashe ba haka bane. In banda abinda me ye abun birgewa a cikin nuna kai waye kai tsaye? Saidai yayi farin ciki da haka, dan tabbas idan bai samu ‘yar uwar ta Zafeera ba, to kan ta zai *d’auki fansa*, dama ya fi son d’aukar fansar ne ta hanyar Zafeera saboda ita yaga an fi cin buri a kan ta, amma wannan ma zai iya maleji da ita madadin yayi biyu-babu.
Wani d’an siririn murmushin mugunta ya sakar mata a dak’ile yace “Barka princezna, haka kuke fad’a a yarenku na slovaque ko?”
K’ara washe baki tayi kamar zata fad’a masa tace “E yallab’ai, ka iya yarenmu kenan?”
Shu’umin kallo ya mata yace “E, yanayi ne yasa na iya.”
Sake fad’ad’a murmushi tayi tace “Am…Yallab’ai, zan iya rok’on wata alfarma?”
Da ido ya mata alamar “Ina jinki.”
Mamaki ne ya kamata ganin wannan ma yana neman ya fi ta shan k’amshi, basarwa kawai tayi tace “Zamu iya zama abokai?”
Yatsina fuska yayi kamar ya ga abun k’yama yace “Hakan ai ya sab’awa dokar kowace makaranta.”
Tab’e baki tayi tace “Karka damu yallab’ai, indai ka amince wannan ba matsala bane, mahaifina shi ne sarkin Khazira, duk wata masarauta a k’asar nan a k’ark’ashin ta mu masarautar take, dan haka zan iya yin komai da nake so.”
Sake b’ata rai yayi yana mai jin wani takaici fiye ma da wanda ya ji yayin had’uwarshi da waccen tamatsirin, dan gaba d’aya wannan magana take ta alfahari da d’agawa wacce babu tunani a cikinta.
Advertisements
Girgiza kai yayi ya d’an juya zai bar mata gurin, da sauri tace “Yallab’ai ya haka kuma? Baka ban amsa ba.”
Juyowa yayi a kasalance ya kalleta, lumshe ido yayi yace mata “Kiyi hak’uri.”
Juyawa ya sake yi yai tafiyarshi ya bar ta nan tsaye, haushi ne ya kamata ganin yanda ya cizgata a gaban mutane, fuska a kumbure ta juyo ita ma rai b’ace ta nufi wajen su Laika dake tsaye suna kallon komai daya faru.
Tana isowa ganin yanda take cika tana batsewa yasa a cikinsu babu wacce ta tambayeta lafiya? Dan zata iya juyewa a kan su, a tsiyace take tafiyar kamar zata tashi sama inda suma suke biyarta a haka.
Daf da bakin k’ofar shiga su Ayam su kuma zasu fita rakata kiran Momma, a rashin sani Sabrine da Zafreen suka bangaji juna, da k’arfi Sabrine tace “Aouch!”
Zafreen kuma a mugun tsawace tace “Ke!”
Kafin kuma kowa ya ankara Zafreen ta kwad’awa Sabrine wani wawan mari, ihun da tayi a firgice yasa Ayam waro ido ta sauke akan Zafreen d’in, a karo na biyu Zafreen ta sake d’aga hanu zata mari Sabine tana fad’in “Ke har wace…”
Cak maganar ta tsaya mata, dan bata san lokacin da Ayam ta rik’e hannun na ta ba kuma har da nasarar marinta a fuska.
Dafe kuncinta tayi tana kallon Ayam dake dafe da kafad’ar Sabrine tana fad’in “Kiyi hak’uri kinji, ke ma ai kina da gata.”
Kamata tayi zasu wuce ka rantse da Allah bata san me tayi ba, duk k’awayen kuma sun yi mutuwar tsaye saboda ganin girman lamarin, musamman ma Laika ta fi kowa tsorata, a sukwane Zafreen ta shak’i wuyan rigarta cike da masifa tana fad’in “Ke kin…”
Yanda Ayam d’in ta zuba mata ido ta kalleta sai abun ya gigita Zafreen, yanda idonta masu launin nan mai ban tsoro suka samu sirkin launin ja na b’acin rai, sai kawai ta ji gabanta yayi wata mummunar fad’uwa, kamar wacce mai fad’a a ji ya bata umarni sai ta shiga zame hannunta a jikin rigar Ayam d’in, hakan ya ba su Ayam d’in damar k’arasa ficewa a wurin.
Da kallo suka bisu har da ita Zafreen d’in data sake dafe kunci tana murzawa a hankali, ta ji zafi sosai na marin nan, yau ma sai suka fasa shiga kamar dai jiya suka juya da sauri suka bi bayan Zafreen dake tafiya har da gudu gudu.
*Shigarsa* ke da wuya d’akinshi ya bud’e taga kenan ya hangi Zafreen zata mari Sabine a karo na biyu Ayam ta rik’e hannun kuma ta mareta, duk da b’angaren malamai da b’angaren su Ayam d’in ba wai yana kallon juna bane, kamar kusan a jere ma suke saidai akwai ginin babban ofishi a tsakaninsu (zauran malamai).
Yanda ya ga wannan abu da tuna had’uwarshi da Zafreen d’in sai ya ji gabanshi ya fad’i, a yanayin da bai saba da shi ba ma’ana tsoro yace ” Wai *wacece ita*?”
D’ora hannunshi yyi a kai yace “Tsarki ya tabbata ga Allah.” Maganar gaskiya ko shi da ke namiji ba zai iya marin Zafreen ba, dan tana da kwarjini da izza wacce kana gani kasan ta samo asali ne daga gidan sarauta, musamman ma ita da mahaifiyarta Juman ‘ya ce ga sarkin Egypt (Ya akayi ka sani? 馃), sannan mahaifinta ma sarki d’an sarki kuma jikan sarki.
*Ayam* kam suna fita Deeyam a mugun tsorace ta rik’o hannun Ayam tace “Ayam kinsan me kika aikata kuwa? Ita ce fa naji ana rad’e-rad’in gimbiya ce.”
Saida ya zage hannunta daga na Deeyam tana karbar wayar da mai kula dasu ya mik’o mata ta d’ora a kunne tace “Then.”
Da mad’aukakin mamaki Deeyam tace “Ayam ba wasa nake ba fa, gaskiya nake fad’a miki.”
Cikin muryar kuka Sabrine da marin ya gama gigitata tace “Gaskiya Ayam da baki mareta a kai na ba, zaki iya shiga matsala.”
Ko kulasu ba tayi ba sai ma saka lambobi da tayi suka ji tace “Yes Momma na, barka.”
Jim tayi alamar tana saurare daga gurinta kafin tace “Momma ina Pah?”
Kyab’e fiska tayi tace “To gaskiya ni dai ki fad’a masa ba zan hak’ura sai ya zo gobe ya kawo min kyautar k’ara shekarata.”
Yanda Momma ta amsa mata yasa Ayam yin jim, sau da dama tana mamakin wasu abubuwa da iyayen na ta ke yi mata, da zaran zata fara tunanin haka kuma sai suyi gaggawar katseta, yanzun ma dai yanda ta bata amsa da dole ma ya amsa kiran sarauniyarshi ba shi ya d’auki hankalinta ba kamar yanda ta ji k’amshin gaskiya da kuma b’ari na tsoro a muryarta.
A daddafe ba tare da karsashin da suka fara magana ba ta yanke kiran ta aje wayar, dafe gaban goshinta tayi zata tsunduma tunanin me hakan ke nufi ? Kawai Deeyam data damu sosai cikin d’aga murya tace “Ayam, hanklinmu a tashe amma ke waya ma kik…”
Wani bahagon kallo Ayam ta mata tare da nunata da yatsa manuniya, cikin sanyayyar murya kuma a tausashe tace “Karki sake d’aga min murya, ni ba ‘yarki bace.”
Jakarta ta d’auka wacce ta aje akan tebur d’in da wayar tangarahon ke kai, ko rataya ta batayi a bayanta ba ta juya a sukwane ita ma ta bar wurin a dole suka bi bayanta cike da zulumi da jinjina isa irin ta Ayam.
*Egypt*
Cikin girmamawa yaron na shi ya kalleshi cikin d’ard’ar d’in ta yanda zai karb’i abinda ya zo masa da shi yace “Shugaba na, sak’o ne daga Giobarh daga sarki Wudar, ka min izinin karanta maka abinda takardar ta k’unsa?”
Duk da ya ji shi sarai amma ka rantse bai ji me yace ba, ci gaba yayi da wasarshi da wani k’aramin k’wallo na kwalba mai kamar *Dutsen Diamond*, matar dake zaune gefenshi cikin fararen kaya na yadi da kambunta a kai mai kalar gwal ce ta kalleshi a tausashe tace ” *Bukhatir*, ka saurari abinda ya zo maka dashi mana, ka lamunce masa ya karanta maka me takardar tak’unsa, daga sarkin Giobarh fa sak’on ya zo.”
Ita ma banza ya mata sai ma ‘yar wak’ar daya shiga rerawa yana fad’in “Lu’u lu’u ki dawo gareni, lu’u lu’u ki dawo gareni, idan babu ke a rayuwata, ji nake kamar ma na mutu.”
A mugum hassale matar ta mik’e tana daka tsawa da fad’in “Ina! Ba zai yiwu ba, Bukhatir ka fara wuce gona da iri fa, wannan wace irin rayuwa ce ? Me kake neman ka mayar da kan ka ne ? Lu’u lu’un banza da…”
Tassssss! Ya d’auke fuskarta da mari, tuni bafaden dake tsaye ya rintse ido dan yasan dama haka zai faru, shi yasan yanda Bukhatir ke masifar son wannan lu’u lu’u, dan haka shi ma yake kaffa-kaffa indai abinda ya shafeta ne.
Tunda ta sunkuya ta dafe kunci kasa d’agowa tayi, a nutse kuma a ikonce tsabar yana ji da kansa da burin mallakar masarautar Egypt ya nunata da yatsa ya mata alamar ta fita a nan, d’auke hannunta tayi daga kunci ta kalleshi da ido sun mata jajir, cikin shashek’a tace “Ni ka mara saboda na zagi wata ban…”
Tauuuuu! Ya sake d’auketa da wani marin kuma, yanzu kam a hassale kuma a gigice cikin d’aga murya yace “Ki b’ace min da gani *Zeyfi*, kuma kar ki sake gigin tab’a kimar lu’u lu’uta, idan kuma kika sake to a bakin aurenki.”
Zaro ido tayi baki bud’e, ai da gudu ta fita a d’akin rigarta na jan k’asa, saida ya ga ficewarta yaja wawan tsaki, kallon bafaden yayi yace” Me ye? Me yace? ”
Jiki na kakkarwa ya shiga warware takardar, saida ya bud’e ya fara karantawa kamar haka _” Mai girma Bukhatir, wannan takardar d’amba ce ta neman sulhu tsakanina da kai, bisa tabbatarwa da mukayi mu da kai abu d’aya muke nema, zai fi idan muka had’a k’arfi da k’arfe wajen cimma burinmu, dukanmu manufa d’aya garemu a kanta, manufar kuwa ita ce *d’aukar fansa* ga sarki Musail, zanyi farin ciki idan ka had’a hannu da ni, hakan kuma zai zama k’aruwarka, idan ka amince da buk’atata ka turo min da sak’on gayyata zuwa fadarka, sak’o daga sarki Wudar.”_
Zaune yayi ya tsunduma tunani, ya d’an jima haka kafin ya kalli bafaden yace “Me kake tunani game da hakan?”
Cikin ladabi yace “Shugaba, a gani na wannan wata dama ce ta cimma abinda muka jima muna nema, duk da abu d’aya muke nema da su, amma ba kamar yanda sarki Wudar yake tunanin manufar d’aya bace.”
Jinjina kai Bukhatir yayi yace “Gaskiya ne, idan har muka had’a hannu da shi muka sameta, a dalilinta zan hau k’aragar mulkin kakan Zafeera ma’ana mahaifin mahaifiyarta Juman, idan haka ta kasance kuwa zan zama mai sa’a a doron duniya.”
Jinjina kai bafaden yayi tare da fd’in “Hakane shugaba na.”
Wani k’ataccen murmushi ya saki ya gyara zamanshi k’afa d’aya kan d’aya yana wasa da yatsunshi yace “Tun ina k’arami nake son hawa kujerar mulkin nan, saidai sarautar a hannun yayan mahaifina take, hakan yasa shi ke mulkar gaba d’aya k’asar nan, hatta da mahaifina da suka fito ciki d’aya shi ma duk’ar da kai yake a gabansa, sannu sannu sai na fara karkata hankali na kan ‘yarsa k’waya d’aya tak, murmushin da take min na d’auka na so, ashe ita tana can tana soyayyarta da wani ba ni ba, hummmm! To me ya kamata na yi? Sai na zauna na zama d’an kallo kenan?”
Wani malalacin murmushi yayi tare da girgiza kan shi sannan ya mik’e ha shige uwar d’aka yana fad’in” Ka tura masa da takardar gayyata.”
Sunkuyawa yayi alamar amsawa sannan ya fice zuciyarshi cike da farin ciki dan bai yi tsammanin zai amince ba.
*Masarautar Khazira*
Zaune suke akan babban teburin cin abinci kamar na bak’i, suna had’a ido ya sakar mata murmushi yace” Sarauniyata.”
Had’e fuska tayi ta kawar da kan ta, murmushin gefen labb’a yayi yana kallon farantin gabanshi da babu komai a ciki yace” Kina hushi dani saboda na fad’a miki ni na kashe mijin da da zai aureki, to me yasa kike tunanin zan k’yaleshi? Ba rabonsa bace ke, ki manta kawai.”
Girgiza kai tayi cike da takaici tace” Baka da tausayi Musail, bayan shi mutane nawa ka kashe? Yanzu ma gashi saboda son zuciyarka ‘yata data rage min ina kallo ina jin dad’i, ka turata neman wata wacce ba zata tab’a samunta ba har abada.”
Cikin d’aga murya tace” Idan ta mutu ita ma sai na yi me kenan?”
D’aga kai yayi ya kalleta a sanyaye yace” To sai me? Ni ba mijinki bane? Ai zan iya sake baki wasu ‘ya’yan idan kina so.”
A hassale ta mik’e tsaye tace” Tirrr! Har abada ba zan bari ka sake rab’ar jikina ba, kuma ka sani burinka akan y’ata ba zai tab’a cika ba.”
Da mamaki ya kalleta yace” Me kike nufi Juman?”
Cike da gadara tace” Ina nufin yata da kuka yi yunk’urin kashewa kai da Dhurani, na san komai da kuka shirya a kan ta, ba zaku tab’a nasara ba ka ji da kyau.”
Tsaye ya mik’e yana mata wani kallo yace” Juman, ko dai ke kika tseratar da yarki?”
Ba tare da tsoro ba tace” K’warai, ni na kub’utar da ita, ka samota mana idan ka isa.”
Juyawa tayi zata bar gurin ya daka mata wata irin tsawa yace” Jumaaaaaaann.”
Dakatawa tayi ta juyo tana kallonshi, a sukwane ya nufota da babbar rigarshi, kallonshi ta dinga yi har saida ya zo kan ta, bai tsaya komai ba ya gaura mata mari, kafin ta ankara ya shak’i wuyanta da hannu d’aya, duk da shi ya shak’eta amma kuma idonshi sun bala’in yin jajir dasu duk sun fito tsabar takaici da b’acin rai, cikin fitar hayyaci ba tare da duba yanda take d’aukar numfashi ba kamar zata mutu yace “Sai na kasheki, sai na kashe ki Juman, ba zaki tab’a zama silar gurguncewar rayuwata ba kuma na k’yaleki.”
Hadimai biyun da suka taho da kwanukan abinci ne suka tsorata ganin wannan lamari, juyawa sukayi zasu fita inda babban bafaden sarki Musail *Adah* yayo kansu da gudu, hannayen sarkin ya rik’e yana bashi baki da yayi hak’uri ya sakeg’ta zata mutu.
Hadiman da suka fita ne suka had’e da waziri Khatar zai shigo ciki shi ma, ai a tare suka sake dawowa da hanzari bayan sun fad’a masa, yana zuwa shi ma kamawa yayi suka shiga k’ok’arin b’amb’areta, da k’yar sukayi nasarar k’watarta a hannunshi duk ta galabaita dan k’iris ya rage ta suma, cikin hargagi sarki Musail yake nunata da hannu yana fad’in “Ba soyayyar da kika tabbatar ina miki fiye da komai bace ta sa kika min haka ? Ai dai tak’amarki ina sonki dan haka babu abinda zai faru ko? To ki ji da kyau Juman sai na hukuntaki, ke baki san waye ni ba shiyasa, amma da sannu zaki sani tunda kika tab’oni, kuma bak’ar ‘yarki zan kamota abisa taimakawar bayina, a gaban idonki zan yanka wuyanta, dan ba zan bari yar dana haifa ba ta kasheni sannan ta rabani da mulkina ba.”
Adah ya kalla yace” Kai Adah, ka mata jagora zuwa kurkukun k’asa na *Sabah*.”
Maida kallonshi yayi gareta har yanzu da numfashinta take fafutuka yace” Zaki d’and’ani uk’ubata Juman.”
Gefenta sarkin yak’i Adah ya tsaya hakan yasa ta kallonshi sannan ta kalli sarki Musail tayi dariyar mugunta tace” Uk’ubarka wacce ce ban sha ba ? Kai dabba ne ba d’an adam ba, kuma ‘yata tafi k’arfinka banza kawai.”
Kan ta ya sake yi da azama waziri dake ta rarraba ido tsakaninsu yana son fahimtar inda suka dosa ya shiga tsakaninsu, cikin d’aga murya sarki Musail yace” Ka fitar min da ita a nan, kuma na tsawon kwana uku ban yarda a d’iga mata ko da tafi d’aya na ruwa ba bare abinci, wannan umarni na ne.”
Fashewa tayi da dariya tace” K’arshenka ya zo Musail, na ga hakan nan ba da jimawa ba, ka tabbatar min da mafarkina zai zama gaskiya dalilin uk’ubar nan da kake neman sakani a ciki, tabbas ‘yata zata zo a dalilin haka, wannan shi ne ma’anar hannun da take mik’a min a cikin kowane mafarkina.”
Cikin ladabi Adah ya mata nuni da k’ofa, juyawa tayi da sauri ta shiga takawa tana fad’in” Ku zuba ido ku gani, da sannu sabon tsari zai zo a k’asar Khazira, ‘yata zata canza komai ko da hakan na nufin ta cire kawunanku ne, mak’ask’anta kawai.”
A dakonce waziri ya kalli sarki Musail da mamaki yace” Sarki na ka tabbata hukuncin nan ne ya kamaceta?”
A hassale yace” To da me ya kamata nayi?”
Dogon tsaki yayi ya nufi hanyar fita yana fad’in” Ka nemo min babban malami a duk inda yake.”
Sunkuyawa yayi yace” Angama shugaba na.”
Saida ya shige sannan ya d’aga kan shi, jiki a mace yana ta tunanin abinda ya faru yanzun ya fita isar da sak’on sarkin.
*Wannan littafi na kud’i ne, ku garzayo ku biya na ku dan jin yanda zata kaya, dan an kusa rufe free page, dan neman k’arin bayani tuntub’i lambar dake sama, zan ga masoyan k’warai da masoyan baka馃槀.*
*Alhamdulillah*
GIPHY App Key not set. Please check settings