Zee Baby Book 1 Page 4

Advertisement

*Free Page*

page 4

…..sosai take kuka tana kiransa hankalinsa atashe yazo bakin kofar ya jingina yana sabke ajiyar zuciya yarasa ya zaiyi da zee baby gashi baya son kukanta hankalinsa tashi yake ahankali cikin sanyin murya ya kirayi sunanta ” Zee babyna yi shiru banason kukanki kinji kara sautin kukan tayi tana buga kanta da kofar tana kiransa arikice ya bude kofar ya sunkuyo gabanta ya dagota yana bata hakuri tayi shiru bazai karaba tunda bataso jikinsa ta shige tana sabke ajiyar ziciya bayanta yake bugawa alamar lallashi ransa duk babu dadi shi sam yanzu bayajin shawar kukanta yafi daga masa hankali hannuta yaja suka iso gun kujerun parlon suka zauna tana manne jikinsa har yanzu ajiyar zuciya take sabke dan taji haushin gudunta da yai ya rufo kofa fuskarta ya kamo yana goge mata hawaye ” zee babyna kiyi hakuri ki yafemin bazan sakeba kinji kanwata idanuta ta zuba masa tana taro baki alamar bata hakura ba murmushi ya sakar mata

yana hura mata idkar bakinsa a idanunta lumshe idanu tayi ta saki murmushi ta boye kanta akirjinsa gashinta yake shafa mata yana mata hira mai dadi aikuwa ta fara dariya saida yaga kamar dariyar tayi yawa ya bari kuma cikin ikon Allah duk yada, take manne jikinsa baiji komaiba game da shawarta sai tsantsar kaunarta da take ratsa jininsa da tsokarsa har kusan karfe biyu da rabi ya ga fah batada niyar bacci har gyangyadi ya fara fur ta hanashi idanu ya bude ya kalleta” kanwata kiyi hakuri ki barni na kwanta kinji zee na? ganin yada idanusa sukayi ya bata tausayi duk batason rabuwa dashi ta daurΓ© ta jinye jikinta anashi ” Ahukhuya muje ka kwanta mik’ewa tayi ta kama hannuwansa suka nufi d’akin ashe duk zaman da suke a parlo Jamal na labe yana kallonsu ajinsa ko wani abun zasu oho yanaga sun nufo d’akin ya koma da sauri ya kwanta har dakin suka shigo tana rike da hannusa kiss ta masa ” mu kwana lfy murmushi yayi ya daga mata kai ficewa tayi daga d’akin

ta rufo masa, kofar dakinta ta nufa naga ta daga hankadan pillow ta dauki wata yar kwallaba ta bude murfin ta kafa bakinta saida tasha rabi ta maida ta buye ta dauki wasu kwayoyi ta zuba bakinta tana taunawa ta kunna kida ta saki sauti wakar larabci ce sai tikar rawa take baji ba gani sai ihu take da tsalle da juyi kafin zuwa karfe biyar abubuwan da tasha sunyi mugun ratsata sai tangadi takeyi amma haka ta Mike taje tayi Alawlla tasaka Riga doguwa ta tayar da sallah amma ta kasa tsayuwa sai azaune tayi tana gamawa ta bungire saman daddumar sai bacci ya kwasheta,,

***************************************
Bayan kwana ukku zuwa wannan lokacin zee da Mahabeer sunyi muguwar shakuwa bata iya nisa ko nan da can tare sukaje sukayo sayaya tsaraba kaf yan gidansu yayo masu tsaraba tare sukaje kabah yayi umarah wacce da kashigo garin ake rakaka kayi yayima zee baby Addu’ar shiriya da shaye shayen da takeyi dan ya kamata tasha kuma ajikinsa mayen ya fara kamata har kuka yayi ummi Raiyan tace ai shine babban abinda yake daga mata hankali shiyasa ta matsu tabar Nigeria dan tasan acan ina zataga kayan maye shiyasa ya kara Sata jikinsa dan yasan saida lallaba sun gama shirya kominsu na tafiya yau suke tashi karfe ukun dare zee baby har cikin ranta batason tafiyar amma da ta tuna sati dayane zatayi taji tanaso taje kasar hausa ta ga ya take ya tsarinsu da Al’adunsu yake tasha kunshi kafa da hannu kitsone dai ba’ayimata saboda tausahin gashin da santsinsa ko anyi tsefewa yakeyi ga zafi da ciwon kai da yake Adabarta shiyasa bataso

su manal da jannat da Radia tun safe suke gidan suka gaji da raye rayansu kuma suka koma kukan rabuwa saida ummi Raiyan da Mahabeer suka lallashesu sukace ai sati daya zatayi ta dawo tukun hankalinsu ya kwanta suka saki jikinsu sukaci gaba da sabgar gabansu, sai bayan sallahr magrib sukayi shirin zuwa Jeddah gaba dayansu sukayi rakiya zuwa Jeddah, karfe tara suna Jeddah Airport zazaune sai lokacin ummi Raiyan takejin ciwon rabuwa da Zaeenaba amma ta daurΓ© dan tasan idan zee din ta gani zatace bazata ba yawonsu su zee suka tafi da su jannat sai sayaya take duk ba sanin mutanen tayi taji tana son kaimusu abubuwan nan k’asar sai wajan sha biyu suka dawo Mahabeer yacewa ummi Raiyan su tafi dan bayaso sai lokacin tafiya yayi ta kafa kuka rungume juna kuwa suka suna kuka su dukansu sai daket ya lallabasu sukayi shiru Jamal ma sallama sukayi Mahabeer yayi masa godiya sosai da karamcinsa Jamal yace saboda zee gashinan zuwa Nigeria Mahabeer ya amsa dan yasan karyace Raiyan ta kara rumgume zee tanata sumbatarta itama sumbatarta takeyi sun jima ta jata gefe tayi ta mata fada ta nutsu tako amsa ta da to suka rabu kowa na hawaye abinda yasa zee bata damuba saboda ance sati dayane zatayi shiyasa su manal da kuka suka shiga mota suka tafi ji sukeyi kamar su bita, kuka ta fara daket yasamu tayi shiru

Sai karfe biyu da rabi suka shiga cikin jirgi saboda shirin da Mahabeer yayi bazaka taba cewa ba balarabe bane ba zee ko baka ganin komi nata sai kwayar idanuta to dama Al’adar garince haka jirgin cairo ne suka shiga sai karfe ukku da yan mintuna sukaji alamar jirgin zai tashi zee ta fara rawar sanyi dama jikin Mahabeer ta jingina kallonta yayi yaga tana karkarwa jikinsa ya janyota ya rumgume ya ciro mayafi ya lullubeta kara shigewa jikinsa tayi” zee,na menene? jinkita ya taba yaji zafi gum hankalinsa ya tashi dan yaji zazzabine ya zubo mata hannuta ta sakalo wuyansa tana hucin zazzabi ga rawar sanyin da takeyi kiransa tayi”Ahukhuya? ” Na’am zeena yi hakuri kinji jirgin tashine zaiyi bari ya tashi na samo miki magani kara matseta yayi yana lallashinta yada ya shigar da ita jikinsa yasa ta rage jin sanyin cikin sa’a wani balarabe cikin ma’aikatan jirgin masu rabon abunci yazo wucewa Mahabeer ya tsayar dashi duk da yaga sauri yakeyi cikin sa’a ya tsaya ya tambayeshi da turanci maganin zazzabi yakeso matarsace babu lafiya yace” ok ya jira jirgin ya daga yanzu zai kawo masa, godiya yayi masa ya tafi yaji dadi sosai da za’a samu maganin tasha karfe uku da rabi dai dai jirginsu ya daga zee na manne da yayanta tana rawar sanyi hankalinsa ya kara tashi jirgin na tashi zee ta fara kwarara amai jikinsa ya rumgume tsam har ta gama yana bubbuga bayanta hankalinsa atashe ” my zeena sannu kinji kai ta daga masa dagata yayi ya mike ya janyo jakarsa ya ciro wata jallabiya baka mai shegen kyau ya ciro karamar Jakarta itama ya ciro mata abaya shi ya fara zuwa ya gyara kansa cikin toilet ya canza kaya tsaf sai yafi d’azu kyau ya dawo ya kama hannuta suka tafi akofar toilet ya tsaya ya bata kayan ta shiga ta canza ta wanke fuskarta da bakinta

ta fito ya kamo hannuta suka dawo ya feshesu da turare ya zauna ta kwanta jikinsa ya lullubeta bai jima da zamaba mutumin ya kawo masa maganin harda ruwa da dan abin masarufi cimarsu ta larabawa ya lallabata ta danci ya bata magani tasha dan batada matsala da magani saboda ta saba cin kwayoyi Allura ce ko zata mutu babu uban da ya isa ya mata ita tanasha ya rungumeta yana lallabata ba jimawa tayi bacci ajiyar zuciya ya sabke ya duko ya mata kiss saman goshinta ya kara shigar da ita jikinsa ya rufeta ruf, koda akazo rabon abunci bai amsaba dan shi bai fiye cin abunci ba idan yana tafiya kansa ya jingina da kujera ya lumshe idanusa dan bacci yakeji bai jimaba ko baccin ya daukeshi jirginsu na sharara gudu cikin hazo

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Advertisements

Karfe takwas na safe jirginsu ya sabka Egypt sabka da jirgiya yayine ya tashi Mahabeer da ya kananade zee suna shakar barci manne da junansu idanu ya bude cike da mamakin irin baccin da yayi tashinta yayi taki tashi dan sam bacci bai ishetaba bakinsa ya kai kunneta ” my zee,na kitashi mun iso cairo juyan jirgi za’a mana zuwa Nigeria kinji my zeena? Shagwab’e masa tayi tanarke masa tana turo baki ashagwab’e tace” Ahukuhya? ” na’am my zeena ya akayi” shiru tayi tana kallonsa murmushi yai mata ” bacci ko kai ta daga masa, tana lumshe idanunta ganin mutane sun fara fita ya mikar da ita Dole ta tsaya mikewa yayo ya ciro karamar akwatunsu ya gyara mata mayafin abayar ya kama hannuta suma suka sabko dogayan motocinan sai kwasar yan k’asa k’asa takeyi suka shiga aka kaisu inda zasu zauna kafin jirgin da zashi Nigeria ya shirya suna zaune tana manne

Kusansa yayi ta lallabata taci wani Abu taki Dole ya hakura basu wani jimaba sosai ko awa daya basuba suka shiga jirgi yanzuma jirgin na shirin tashi yaga tanason yin amai rumgumota yayi yana bubbuga bayanta ya shiga mata rada akunne” my zeena please karkiyi amai ki daure wlh damuwa nake shiga yanda yake matan cikin ikon Allah taji batajin aman ta dago kanta ta zuba masa shanyayun idanunta tana murmushi tana shafar fuskarsa haka suka kure junansu da ido har jirgin ya nutsa sararin samaniya idanuta ta janye tana dariya ta dora kanta kafadarsa, ana raba abunci akazo kansu lemo kadai ya amsa adan cup yasha itako tace tea Mahabeer ya matsa ata amshi pizza ya bata abaki taci ta koshi ya bata magani saboda jikinta akwai zafi ya kwantar da ita jikinsa ya rufeta da mayafi ba jimawa tayi bacci dan dama ita wuni baccine tunda bata na dare bare yanzu safiyace shima baccin ya daikeshi ya jingina bayansa da kujera

🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

karfe shabiyu da rabi na rana jirginsu ya diro garin Kano Mahabeer idanusa biyu jirgi ya sabka ya tashi zee idanu ta bude ” munzu gida fah yanzu sai Katsina murmushi tayi ta shafi fuskarsa mikar da ita yai dan masu sabka har sun sabka yan Kano yan Abuja ne basu fitaba tashi yai ya d’aura mata Niqab dinta ya kama hannuta dayan hannusa, rike da jaka itama tana rike da jaka saida zasu fito wata latijuwa takira Mahabeer dan ita Abuja zata ya dawo ” d’ana gaskiya ka iya rikon mace rayuwar auranku ta burgeni kai da yar balarabiyarka gatadai yarinya karama amma akwai nutsuwa Allah ya sabketa lafiya Allah ya karamuku dankon soyayya Allah yasa mutu ka raba kai da ita yaji dadin Addu’arta cikin farin cikin ya amsa yana godiya, suka sabko kallon gurin take ya burgeta sosai suna

Fitowa ta cire niqab ta tatare abayar ta daurΓ© Mahabeer ya fara mata fada ta rufe jikinta surata duk awaje kar wasu yan iska su kalle masa ita shagwabe masa tayi yayi hakuri zafi takeji yanda ta shagwabe yasa yaji tausayinta maybe ko zafin takeji amma ransa bayason wani yaga kyawunta ya yaba ta lokacin su Daddy sun jima da isowa tarbarsu bayan sunje sun gama sa hannu anga posport dinsu sukaje gun kayansu Mahabeer ya jido ya zubaso cikin abun tura kayan bayan angama aunasu suka fito inda jama’arka ke tsayuwa domin tarbar baki Daddy ne ya fara hangosu ya kirasu Mahabeer yaga yan gidansu su shida ne sukazo sai Nawwara ita karamace Dr Sardauna na hango cikin wani danyan boyal baki mai masifar tsada da kyau ya manna bakin gilashi kan fuskarsa wlh fadin kyawun da Sardauna ya zuba bata lokacine saide fuskarsa ba walwala harda mashakurah nagani taci uban kwalliya ta kece raini agaskiya tayi mutokar yin kyawu tana kusa da masoyinta sai wasu mace da namiji sukam ban sansuba sai ghiasha fuskarta dauke da farin ciki Mahabeer ya nunawa zee baby yan gidansu idanun da zata dago idanusu ya sark’e da juna amma ita bata ganin kwayar idanusa saboda gilashi ranta amutikar bace amma zahiri wani makirin murmushi dauke kan fuskarta ta kauda kanta tace” Auzubillahi minal Shaidanir Rajim Mahabeer ya kalleta yana nuna mata Daddy tana hangosa saboda ta sansa sosai ta pic ta yada Jakarta ta saki hannu Mahabeer ta ruga da gudu tana dariya shima dariya yakeyi Sardauna tsaki yaja ya kauda kansa aransa yace ” Allah rabamu da jaraba gudu take amma gani take kamar an kara mata nisan gurin dariya suke ta mata yada ta zage tana gudu ko ina na jikinta motsi yakeyi masha Allah sai kallonta jama’a suke dan zee ba kyau Bade da sura tana dabda isa gurin Daddy sai kawai ta yanke jiki ta fadi da gudu sukayo kanta Mahabeer ya kira sunanta da karfin gaske “Zainab…. arikice yayi kanta da gudu kafin yazo Daddy har ya dagota amma abin mamaki bata mutsi babu alamar rai jikinta Mahabeer ya karasu ya amsheta yana kirkiza agigice amma bata motsa hankalin Daddy yayi mutikar tashi ya kalli Sardauna da yakema mashakurah masifa akanme zata to indai tana tare dashi karta kuskura taje kwalla tausayin zee ta goge ta sada kanta kasa Daddy haushine ya cikashi yace “dan ubanka zo maza dauki yarinyar muje asibiti mafi kusa ka dubamun lafiyarta idanu Dr Sardauna ya zaro bakinsa na rawa yace” Daddy ni kuma zan dauketa saboda Allah ga Wanda ya kawota nan Daddy bai sake maganaba yaje gun Mahabeer yace ya ajiye Zainab ya tashi baiyi musuba ya ajiyeta yace duk su tafi har mashakurah yace ta biyosu ya kalli Dr Sardauna yace” idan ka cika dan halak karka tabata kabarta ta mutum ka kaimun gawarta Katsina komin dare mu muntafi sai ka kawo mana gawarta yaja tawagarsa ghasha tazo ta dafa Sardauna cikin lallaba kome tacemasa oho kai ya kada yana kallon masoyiyarsa da aka hana tabishi saboda wannan banzar lips dinsa ya ciza da karfi yana kallonsu Mahabeer sai kukan zuci yakeyi kayansu yaje ya turo suka fice mashakurah harda kukanta an rabata da masoyinta bazata amotarsa ba sororo yayi yana gani har suka fice ransa yayi mugun baci ya nufi gunta yana yamutsa fuska ya kalli hannuwansa yaja tsaki sunkuyowa yai ya yaja mata rigarta ya ciccibeta ransa amutikar bace amma sai yaji sakwat kamar ya dauki yar karamar yarinya batada nauyi ko kadan miyau ya zubar ya kara hade face yayi waje da ita shikadai yasan yada yatsara cin uwarta da zai mata da zaran ta farfado….

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

SIRADIN RAYUWA 6

Advertisement  πŸ‘‘ *SIRADIN RAYUWATA*  _wannan littafin na kudine,kuma AMANA ce a hannun duk wanda yasiya,idan kina da buqatar…

SALON SO 49-50

Advertisement   🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾             🌹 SALON SO 🌹 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾     BOOK ONE…

KWARATA 24

Advertisement πŸ…Ώ —— 24          Muna fita gidan biki Baba Ζ™arami ya Ι—auki wayarshi ya…

SIRADIN RAYUWA 7

Advertisement  πŸ‘‘ *SIRAƊIN RAYUWATA*πŸ‘‘ *_wannan littafin na kudine,kuma amanace a hannun duk wanda yasiya,idan kina buqatar siya ki…

SALON SO 43-44

Advertisement  πŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎ             🌹 SALON SO 🌹 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾     BOOK ONE πŸ“–…