Zee Baby Book 1 Page 5

Advertisement

Page 5

 

*…..asalinsu* Alhaji Hasheem Almahadee magawata haifafan garin tahoua ne cikin Niger sun gaji sarauta GABA da baya mahaifinsa ne kan kujera mulki shidayane gun iyayansa rana tsaka aka riske gawar iyayansa lokacin yana kasar waje karatu labari na zuwar masa, ya dawo gida domin ahalin yanzu shine Wanda zai hau kan mulki anshirya komai aka hada yan mata biyu rana daya aka aura masa, amma sai me ana gobe nadin sarauta aka nemesa sama da kasa aka rasa, Abu kamar wasa, saida aka shafe shekaru biyu babu labarin Hasheem Almahadee Wanda suka kulla manakisar kuwa tuni sun hau kan sarautar suna zuba mulkinsu matan da aka aura mishi kuwa tuni an kashe auran shikuma baisan ya akayiba ya tsinci kansa a daura Nigeria yana yawo garari wani bawan Allah mai suna Alhaji Nuhu haifafan katsina ne amma mahaifiyarsa ce ta daura shi ya temakesa yana ganinsa yasan aikin jifane cikin ikon Allah ya dawo haiyacinsa yasha mamaki da ya gansa a Nigeria Katsina Nuhu ya tambayesa ko shi na wani garine dan ya ganshi jajur ga kyau tamkar balarabe bai boye komaiba ya labarta masa koshi waye Dan kasar niger ne buzune na Tahoua yagaji sarauta gaba da baya saboda itane aka fito dashi an kashe masa iyaye amma yace baya shawar komawa gida indai akan sarauta aka fito dashi yawon duniya ya hakura zai zauna ana Allah yasa haka yafi Alkhairi shikenan mafarin zaman sa tare suke hada hadar kasuwanci shida Nuhu tamkar uwa daya uba daya haka suke bayan shekaru kusan goma hasheem da nuhu sunyi aure sun zama wasu sunyi arziki shakaru na tafiya arzikinsu na bunkasa kuma har lokacin bai taba jin son komawa gidaba hasheem yanada yara hudu Abdulmutallab sai mai binsa Hauwa’u sai Faisal sai Salmanu daga kansu haihuwa ta

Tsaya sun taso cikin gata da kulawa Hasheem da zainab sunba ‘ya’yansu tarbiya sun sami karatun boko da na Addina Allah ya kara bunkasa dukiyar Hasheem dan haka yace yaran sa kowa ya zabi kasar da yakeso ya tafi ya biyawa kowa yaje karatu lokacin Faisal yanada shekaru sha bakwai yace saudia nuhu ya tsaya masa kan komai saboda Hasheem yafi sonsa a yaran Nuhu akwai yayarsa acan madina Faisal ya tafi yake karatunsa cikin kwanciyar hankali da nasarori gidansu na Katsina abin kallone dan babu abinda babu aciki Hasheem na kula da yaransa shida zainab Abdulmutallab ne ya matsa masa saida ya gayamusu garunsu ya nemi izininsa ya tafi Tahoua gun dangin mahaifinsa cikin ikon Allah yasami tarba maikyau amma banda mai martaba ana Allah ya hadasu da Khadija suka kulla soyayya kafin ya dawo yana dawowa magana tayi karfi Dole hasheem ya tafi shi da Nuhu aka sanya ranar aure khadija yarinyace kyakyawa itama buzuwace GABA da baya farace tas kama Abdulmutallab sunyi aure cikin so da kaunar juna da mutum ta juna bayan bikinsu da shekara biyu ta haifi danta namiji yaci sunan Nuhu bayan shakaru hudu ta haifi Mahabeer shima sai bayan sharu hudun ta haifi mace mai sunan maijidda ko yayeta batayiba cikin ikon Allah tasake samun cikin ta haifo zankadeden danta namiji kyakyawa ajin karshe jajir dashi yaron

Akwai farin jini tamkar ba’a taba haihuwa ba shine yaci sunan Almahadee wato Faisal tun yana karaminsa akwai son gaskia da son girma bayason raina ko kadan ga miskilanci da jiji da kai bai fiye fara’a ba idan ba yana tare da khadija ba wacce suke kira Ghaisha Kakansa hasheem ya saka masa Sardauna saboda yaron kana kallinsa kasan jinin sarautane ba karya sunan ya bishi tun yana karami yace karatun likita zaiyi ya temaki mutane to fah tun yana karami sukece masa Dr Sardauna kyawunsa ya fits daban agidan Dan sak kamar Hasheem ya fito yanada kanne hudu shima Najib ke bimasa sai Zainab sai hafeeza da auta Nawwara bangaran Mariya Amarya da Abdulmutallab ya aura saida ta kwashe shekaru biyar ta haifi yarta daya nana khadija sunan uwar gidansa sai mareniyar yarta da tazo da ita Khalisat idan ka ganta bazaka taba cewa ba yar gidan bace babu banbanci yarinyace kyakyawa amma ba canba batada laifi dai farace saidai batada hayaniya shiru shiruce suna zaune lafiya bazaka taba cewa ghaisha da Mariya kishiyoyineba sai Hauwa kanwar Abdulmutallab tana aure itama cikin Katsina da yaranta hudu sai salmanu shima yayi aure da yaransa biyu wannan zuri’ar Allah ya hada kansu suna kaunar junansu yaransu sun taso cikin hadinkai da kaunar junansu Faisal ne kawai da baya kasar rashin auransu ya damesu sunata Addu’ar Allah ya janyo hankalinsa gid

*********

Faisal bayan ya kwashe shekaru tawas saudia yana, karatu bai taba zauwaba gidaba kuma bashida kiyuwa duk da ana aiko masa, kudi daga gida hakan baisaba yazauna ranar da ba karatu fita ya keyi neman na kansa dan yanaso shekarun biyu da suka rage ya koma kasarsa yabasu mamaki dan yanzu haka ya tara uban dukiya taban mamaki amma babu wanda ya sani ranar ya fito zai tafi daidai wani super market wani shahararan mai kudi sun fito da iyalinsa daga, siyaya zai shiga mota yada takarda ta fado aljihunsa da sauri ya nufi wajan daide ya dauka motar ta tafi dan taxi ya gani ya shiga yace yabi waccen motar bayansu sukebi har kofar gidan ya biya dan taxi ya nufi gun mutumin amma har sun shige gida yayi sallama yajima kafin ya fito yake tambayarsa, lafiya ya bashi takardar da ya yada bai saniba ya amsa ya duba saida ya tsorata dan takardun kadarorinsane da ya mallakawa yarsa kwaya daya Raiyan godiya yayi ta masa ya jasa suka shiga ciki yayi masa alheri sosai amma yaki amsa yace yayine don Allah sosai tarbiyar Faisal ta burge Fahad Abbu Rahaman to daganane suka saba ya sama masa aiki a kamfaninsa kullum yana gidan kamar dan gida sai abunda Fahad Abu Rahaman bai saniba Raiyan tun ranar da taga Faisal ta mutu akan sonsa tun tana daurewa har ta baiyana masa kiyawa yayi saboda tsoron balaraban saudia bayaba hausa dansa duk shima ba hausarba ne idan ma ba ance maba ba barabe baneba to bazaka ganeba saidai su suna banbance jansin su Abu kamar wasa Raiyan ta kwanta jinya ciwo hankalin iyayanta yayi kololuwar tashi har aman jini takeyi likita yace sumata abunda takeso zuciyarta takai matakin karshe dab take da bugawa nanne suka tambayeta ta fadamusu damuwar sunyi rantsuwa da Allah zazu mata dan basu taba zaton harakar soyayya ce jin sun mata alkawali yasa, tace Faisal ne takeso ranar anyi tashin hankali sunce saidai ta mutu taya zazu aurar da ita da Wanda basusan asalinsa ba kuma ba hausarsu dayaba, da sukaga fadan bayayi suka dawo lallashi suna rokonta tace ta janyen tunda sun mata alkawali har kuka suka mata amma fur takiya karshema da, numfashinta ya dauke saida, tayi sati bata farfadoba ganin zazu rasata yasa sukace sun yada ta zureshi saboda alkawali amma ba ruwansu da ita kuma yada yasasu bakin ciki taki musu biyayya itama sai ta zubar da hawaye haka akayi bikin Hasheem da Abdulmutallab su ne sukazo akayi komai amma Faisal yace shi yananan bazai komaba saidai ya rika zuwa ziyara. bayan aurene Ashe mahaifin Raiyan kodiri dayawa aransa sosai Raiyan da Faisal soke zuba soyayya kamar ba gobe Ashe shima yana sonta ganin kamar abin bazai yubane yasa da farko yace bayason ta bayan auransu da shekara biyu ya kammala karatunsa

cike da nasarori ya sami aiki a Jeddah Dole sukabar madina koda sukaje sallama gidansu Raiyan ba Wanda ya kulasu haka suka tarkata suka tafi lokacin tana fama da laulayin ciki yana bata wuya saida ya warware sosai ta samu sauki, ranar haihuwa ta zagayo taci uwar azaba amma kasa haihuwa tayi da kanta sai tiyata akamata aka ciro yara ukku maza biyu mace daya kyawawa, masha Allah ranar Faisal ya nuna tsantsar farin cikinsa amma babu Wanda yazo daga gidansu Raiyan sai wata Faisal ya samo take kula dasu, ranar suna ya sakawa mazan Hassan da hussaini macan sunan mahaifiyarsa, Zainab ranar anyi bidira a Nigeria yan uwa sai jin dadi sukeyi suna jinjina al’amarin Ashe rabone tunda Fahad yaji labarin Raiyan maza ta haifa yaji dadi sosai yasan yanzu zai cika burinsa haka akayi ta tafiya rayuwa na gudu yaransu sun girma sosai saide sunfi shagwaba zee baby yarinyar akwai fitina sosai ga mugunta har uwayan bata bariba gashi muguntar ta tafi karfi suma mazan imusu takeyi makaranta mai tsada ubansu ya sakasu ko acan bata barin yaran mutane har malaman sun dukanta to ranar basu ba koyarwa idanu take likewa ta koma gefe tana dariya ahaka saida aka canza masu maranta ukku daide lokacine Faisal karami yazo karatunsa na likitanci Wanda zai dauki tsawon shekaru biyar amma yana madina sai karshan wata yake zauwa jeddah

sam jinunsu bai hadu da zainab idan tayi ba daidai ba dukanta yake ba da wasaba kuma hakan yanawa iyayanta dadi dan duk rashin tsoronta to tsoronsa takeyi ba da wasaba dan babu irin azabar da baya mata yan uwanta har kuka sukeyi tasha masa kunama amma duk yaji zafi zai dake sai bayan ya gusa yaje yayiwa kansa Allura ta rufe masa idanu yafi akirga amma dan taurin rai bai taba nunawa yaji zafin abun ba to wannan abubuwan yasa zee baby take tsananin tsoronsa tana tunanin to shi wani irin mutumne

dan taga yada mutane suke tsalle idan ta cutar dasu amma shi sam idanma tamasa guri yake nema ya zauna ko iyayanta sun roketa sai yacemusu kar ta kuskura ta bude masa idon yafi son zama dama baya gani kuma cizon kunama burgeshi yakeyi to ita ko ta tsani abunda yakeso shiyasa ta fasa masa saide duk ranar da muguntarta ta motsa sai tamasa, haka rayuwa tayi ta tafiya zainab ta gama primary school ta shiga secondary school loakacin kyawunta ya baiyyana kawayanta duk diyan hausawane jannat ce kadai balarabiya manal hausawane kuma dama tafi kulasu kaf cikin kawayanta jannat ta koya mata shaye shaye manal hausa dama kuma mahaifinta na koya mata, zee baby ta kware wanja shaye shaye da fitsara da rashin kunya gidan rawa ba inda bata zuwa gata da saka kananu kaya idan tayi shigar abaya ta fito to tana zuwa sai tacire ashiga, shaye shaye da raye raye idan kaga zee baby agida to Sardauna na garin to fah ko hauka take bazata fitaba saidai ta hanasu bacci dan kure kida take tana ihu da raye raye amma bata shan komai dan akwai lokacin da Faisal Sardauna ya yanka mata harshe kuma yace idan ta barsa ya kwana aduniya bata cika yar halak ba abun na damun Raiyan sai dai tayi ta Addu’a Faisal kuwa sai yace yarinta ce zata daina amma yanajin dadin yada Faisal karami yake hura masa ita haka sukaci GABA da rayuwa Hassan da hussaini iyanyansu sun kasa gane kansu duk sun canza musu ba kamar zee baby ba suma saida Sardauna yaci ubansu kafin su fara daidaituwa ana cikin haka Faisal wata Ranar. juma’a ya fito daga cikin gari yana waya yana driving kawai sai jiyayi babbar mota ta shigesa kafin yayi wani kokari mai afkuwa ta afku dan daket aka tataro na mominsa yayi raga raga abin babu dadin fadi ranar Raiyan ta shiga tashin hankali

Advertisements

Sardauna lokacin karatu ya tisasa gaba ya nemi ma alfarama yazo sun hanashi Dole ya hakura zee baby mutuwar mahaifinta ta girgizata mutika komai ajiyeshi tayi agefe ta nutsu ummi Raiyan haukane batayi ba yan Nigeria da sukazo saida akayi sadakar arba’in suka koma cike da jimamin mutuwar dan uwansu Wanda sukafi so saboda kirkinsa yana saudia ma babu abinda ya rage na zumunci bayan Arba’in Hassan da hussaini suka bijirewa ummi Raiyan fur basu ragamata ga wata irin tsana suka mata tun zee baby bata luraba har ta lura tako ci ubansu mafarin da mahaifin Raiyan yazo ya dauke yaran babu yanda baiba yaja hankalin zee ta gujema Raiyan takiya shiko yace yayi alkawali sai yaga bayan duk mai kaunar Raiyan to daga shine zee ma ake farautar rayuwarta gashi rashin jinta yayi tsauri yanzu idan ta fita bata dawowa gida sai tayi kwana biyu ana haka watarana Sardauna yazo ummi Raiyan take fada masa yada zee ta kara lalacewa ransa yayi mutikar baci cikin sa’a kuwa tsakiyar dare ta dawo wlh ranar saida ya sumar da ita saboda launikan azabar da ya gana mata ya kuma yankarmata aharshe saboda tayi shaye shayen to tundaga lokacin Dole ta tsayar da yawon saidai ta tara kawayanta agida ana haka har Sardauna ya ka kanmala karatunsa shekara biyar yazama babban doctor wanda kafin yaje an gama Gina masa makekiyar asibiti mai zaman kansa wacce akasawa sunan *Almhadee Sardauna clinic hospital* asibitin da ta tsaru garin katsina iya tsaruwa nan unguwar malali cike da kewar juna suka rabu da ummi Raiyan tana kuka zee kuwa d’aki ta shiga ta rufo ta saki sauti tana mai farin ciki masifa da

jaraba tabar su har abadan yanaji bai dai biyataba idan kaga Sardauna bazaka taba cewa ba balarabe baneba saboda tsantsar kyawunsa kamarsu daya da zee dan ita Faisal ta fito sak sabanin mazan da suka fito Raiyan ya jadada, mata mutikar halinta da ta canza ya dawo ta kirasa shi zaizo ya kaita Nigeria ko dan kwasar shara su aura mata ummi harda dariyata haka ya tafi da haushin zee baby da yan uwanta da suka tsani ummi Raiyan bayan ya komane aka bude hospital din wada ake tururuwar zuwa dan Faisal Sardauna Allah yayi masa, baiwa kan aikinsa kaf katsina shine akeji dan ya karanci fanni ko wane ciwo a tsawon shekaru biyar da ya kwashe a saudia amma yafi aiki fannin zuciya da kwakwalowa da kuma binciken lafiyar mata amma duk da haka yana kula da, kowa shiyasa yayi suna a Nigeria ko wani gari kiransa akeyi indai ba mutum na matsa bane to bai fiye zuwaba yazo da wata dayane suka hadu da mashakurah an kawota batada lafiya Dan tana fama da ciwon ciki shine ya dubata lokaci daya sonta ya kamashi amma bai fada mata ya dai saka akabisu har gida aka ga gidan bayan kwana biyu yaje baisha wuyaba ta yarda amma tace tana karatune a London yanzu haka saura wata biyar ta gama tazo hutun karshan shekarane nan tabashi tarihinta tace subiyune gun iyayansu Alhaji Ma’aruf shine mahaifinta dan siyasa ne yanada kudi sosai duk da baikai su Sardauna ba sai yayarta Amina tana aure Abuja mashakurah kyakywace baka tanada jiki akwaita nutsuwa ga tarbiyya bata fiye surutuba haka suka kulla soyayyarsu har takoma taci GABA da karatunta kullum suna mnnne da waya sunajin lafiyar junansu,

Bangaran zee tunda Sardauna ya tafi ta maido iya shege so biyu tana samari kuma tana son su amma daga baya dai suce iyayansu sunce bazasu auretaba duk tana yarinya bawani girmaba tayi ba tunda secondary take amma tanajin ciwo ana hakan suka hadu da majeed shima haka ta faru to da zaran sun mata haka ta haramtasu dama ita tafison gwarzon namiji tsayaiye Wanda zai juyata mutikar ba hakaba to tasan mijinta zaici bakar wuya agunta gashi har yanzu bata samu ba shiyasa take soyayya sama sama ana cikin haka su biyu ana harin zee za’a kasheta Allah yake gyarawa ta sha amma hakan bai hanata

Yawoba to hankalin ummi Raiyan yayi mutikar tashi ga yaranta sun tu SATA GABA tabasu gadon ubansu Dole ta basu duk wata kadara abuye dan sunyi mata kashan kar zee baby ta sani bayan nan taji ta tsani zaman jeddah Dole ta tatara abinda yake hannuta ta siyar da gidan da suke ciki suka koma cikin garin mekkah ta nemi unguwar hausawa khaleedia tasayi wani rantsatsan gida zee tayi ta rigima ita babu kawayanta su manal da jannat Ashe suma can sun tayarwa uwayansu hankali Dole sukace zazu kaisu mekkah su kammala karatunsu tunda duk suna da yan uwa acan hakan yamusu dadi dan makaranta daya suke kullum suna tare da juna amma iyayansu sun sa ansaka musu idanu dan duk shaye shayen da suke aboyé sukeyi su basa fito da iskancinsu kamar zee haka sukaci gaba da karatunsu har ranar gamawa tazo kuma mahaifin Raiyan har yau baisan ta kauro mekkah sunyi nema har sun gaji yanada kodirin kashe zee baby duk inda take ranar da suka gama secondary school da kwana ukku suka hada gagarumin party majeed tundaga shine bai koma jeddah ba yake zaune a mekkah gidan kawunsa ranar zee ta zuba hau maza da mata suncika gidan anci ansha ranar kwayoyin da tasha basu faduwa to daga shine ummi Raiyan ta yanke shawara Dole tabar saudia washe garine sukayi wannan raye rayen wanda majeed yace mahaifinsa yace ita yar macace shiyasa ta tsaneshi ta fasa sauraransa da taso suyi aure da Maharaz amma yaso mata Fade shima shiyasa ta rufe babinsa dan ta tsani mazinaci arayuwarta ana hakane Mahabeer yazo kaita suka lula Nigeria wasu samarin basu ko sani ba suma su jannat suna shirin komawa jeddah tunda karatu ya kare ga kawarsu batanan
Wannan shine asalinsu

*Mun dawo cikin labari*

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Taku yake cike da izza tamkar ba mutum ya rumgumo a hannusa ba fuskarnan tam ahade mutane cikin Airport din sai kallonsu suke cike da shawa parking spece ya nufa tun daga nesa naga ya danna rimote wata wulwuleliyar motar baka sudik k’irar land range Rover évoque 2020 ta bude bayan motar ya cillata ya rufo ya shiga mazaunin direba yai mata key yaja da karfin gaske ya fice yana hawa kan titi ya kunna sigari yana busa baki da hanci hospital Nasarawa ya nufa ya dauki wayarsa ya danna wata number bugo biyu aka daga saita nutsuwarsa, yayi ” Asallama Dr Yakub ykk” gud kana hospital ne ganinan saman hanya zan duba wata koran makkah ok bey sai nazo kitt ya tsinke Kiran ya maida hankalinsa kan driving har ya isa asibiti parking spèce ya shiga da motar fitowa yayi ya bude bayan motar ya ciccibeta ya rufe motarsa anutse yayi ciki da ita a respections ya hadu da Dr na jiransa ya taresa suka nufi emergancy Dr Sardauna yace” ai ba sai muje canba ba wani matsuwa tayi ba bani room inda ba kowa zan dan duba zata farfado? ” ok Dr muje wani room suka nufa ba kowa tsaf dashi komai na gwaje gwaje akwai ya fita ya bashi guri wurgata yayi saman gadon ya cire gilashin fuskarsa ya shiga aikinsa yada ya dace saida yayi awa, daya cur akanta atsaye yana famar ceton ranta ya samu numfashinta ya dawo amma bacci take tsaki yaja” ai wlh dama kwayoyin sun kasheki shegiya mai ruwa da tsuntsuwa yarinya karama sai masifar shaye shaye toilet ya nufa bai jimaba ya fito ficewa yayi daga d’akin, yafi awa daya kafin ya dawo saida yayi sallah azuhur sosai Dr yakub ya karamashi yako ji dadi hakan tare suka dawo d’akin har yanzu bata tashi ba sun jima suna hira da yakub ya fita zauna bakin gadon yai da niyar kiran mashakura yaji sun isa lafiya Dan yayi niyar yana gama wayar zai tasheta yaci ubanta Kafin su tafi wayarsa ta dau ruri ganin Mahabeer ne yasa ya dauka ya kara akunne” my brother saboda Allah kana ganinta ta ci kwaya har tamata yawa ga yunwa kuma kazo ka banka mata kwayoyin zazzabi suka hadu sukayi mata yawa shegiya tantiriya wlh dama mutuwa tayi masifa Mahabeer ya fara masa karya kuma zaginta murmushin gefen baki yayi baice komai ba ya shiga ciza lips d’insa Mahabeer

Yayi magana cikin lallaba ” Dr Sardauna namu Dan Allah gayamun zee babyna ta farka idan ta farka bani ita na kwantar mata da hankali Dan nasan rigimar nemana zata maka banaso tayi kuka kuma kayi tuki ahankali bata saba da wahalaba ran Dr Sardauna yayi mugun baci amma ya nutsu yana sauraron yada Mahabeer yake kafa masa sharuda a kan banzar yarinyar nan yar kwaya itako lokacin ta farka tana manta da ba Saudia take ba ganin bakaken kayan jikinsa da yanayin sa na Mahabeer duk da taga yau kamar ya Kara girma tunda Sardauna yafi mahabeer girma da cikar halitar Namiji mikewa tayi zaune ta rungumeshi ta baya ta sakalo hannuwanta ta wuyansa ta kwantar da kanta saman wuyansa ashagwabe ta kirashi tana shafa fuskarsa ” ya Ahukhuya me yasameni ta fadi tana Kara rumgumarsa shiru taji kukan shagwaba ta saka masa ” wlh Ahukhuya yunwa nakeji ta fadi tana goga fuskarta kagon bayansa tana kuka k’asa k’asa iya karshan Bacin rai yau Sardauna yaje idanusa sunyi bakikirin ya janyota ya birkitota ta dawo gabansa jikinsa har tsuma yakeyi ya yarfa mata maruka har hudu ajere ya bankare mata hannuwa ta baya saida sukayi Kara bashiri ta Saki ihu ” Dan Allah Ahukhuya yi hakuri me namaka cilata yayi ta hadu da bango saida goshinta ya fashe tunda take bata taba jin azabar da takeji yanzuba ga yunwar da takeji ga cikinta na mata ciwo kafin ta Mike taji ya harbata ” yar iska yar kwaya wlh sai kin gwammaci mutuwa da rayuwa take mata kafafu yayi sai yanzu tasan da wa take idanu ta dago ta kalleshi ido hudu sukayi kauda kansa yayi duk da taji mugun tsoronsa ga wata irin walkiya da take fitowa daga idanusa da yanyin yada taganshin hadiye tsoronsa tayi ranta idan yayi dubu ya baci yinkurawa tayi ta Mike tsaye ta rike kugunta tana girgiza cikin dauriya dan taji azaba ga cikinta na ciwo tace” kutumar babbar buro ubancan kai idan na yafema dukan da kamun ayau Wollah Ba Faisal Hasheem Almahadee bane ubana ta fadi tana tunkarosa shikuma tsaye yake yana wani miskilin murmushi ya tura hannusa cikin kwantacciyar sumar kansa yana shafawa yana ciza lips dinsa Dan ransa yakai kololuwar baci jiranta kawai yakeyi yaga mai zata iya dashi idan ta iso gareshi….

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Advertisement KANDALA  CHAPTER 12 Tana k’wance A jik’in sa yana shan lemon ya kusa k’aiwa rabi sai tare…

YAU DA GOBE 19&20

Advertisement  🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾   🌹YAU DA GOBE 🌹 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Story & writing by mmn fareesa 🅿️19&20 ,,,,,,Tsaye tayi bakin…