Zee Baby Book 1 Page 1

Advertisement

*Free Page 1

Saudi ARabia cikin garin mekkah Misalin karfe ukku na dare ihu najiyo kida na tashi da gudu na nufi inda naji kidan ina cike da mamaki ah irin lokacinna lokacin da kowa ke bacci wasu kuma suna ibada domin nema kusanci da Allah sabahanu wata’alah to su awannan lokacin lokacin iya shegentane ko nace ita shegensu Dan duk mafi akasarin su Saudia yaran su da manyansu ba bacci sukeba sai anyi sallahr asubahi to Zee baby

haka take bata bacci cikin hadaddan parlon na shigo Wanda ya gaji da haduwa har na zarce zan nufi d’akin da kidan ke tashi naga wata kyakyawar balarabiya yar kmanin shekaru 35 year azaune da cazbi ahannuta tanaja ta hada kai da gwiwa tana magana muryata na Rawa tsayawa nayi domin naji me take cewa naji da harshen larabci tana cewa” Ya Rabbi ka dubeni ka yayemun damuwata Allah ka shiryamun Zaeenaba da wanne zanji da rashin mijina ko da rashin iyayena ko da rashin ‘ya’yana maza har biyu mahaifina ya nuna musu yada zasu tsaneni an rabani dasu nazabi Zaeenaba akan komai munbar musu komai namu munbaru Jeddah mun dawo mekkah amma babu sauyi bakin mahaifina ya bini nima yata ta bijiremun Ashe haka bijirewa iyaye yake Dole zan dauki mata karya saka akasheta dole zatab bar

Saudiya tunda ta kamala secondary school gashi yau tacika gida da raye raye bata fice yawo ba har aje akasheta idanu na zaro nabar gurin na nufi d’akin da kida ke tashi ikon Allah nace yarinya na gani yar kimanin 17 year sai tikar rawa take tana juyi tamkar tarwada wani shegen wando mitsitsi bakinsa mazauninta rigar kuwa bata da maraba da breziya yaran duk bakar fatane su biyune kade larabawa duk da itama farinta bai kai na Jannat ba sai tafawa suke RAF RAF RAF suna zugata ” Sai Zee,baby aikuwa ta Kara da gewa ta kwasar shoki idan ka kalleta balarabiya sak saide ta

dan sa dishi kadan Dole ma zakasan ruwa biyu ce saboda tsantsar kyauwon da Allah ya mata gashinta har gadon bayanta ta saka masa kalolin colour har kashi uku da ja da ruwan furfura da kuma bleu kunnenta dauko take da tila har biyar ajere tasa musa kananun barima na zinariya sun jeru Cas sunyi mata masifar kyawu hancinta ma atille yake tasaka yar karamar barima ta zinare kasan lebenta lebanta ma a tile yake shima yar barimar zinarece amanne agun Wanda hakan ya Kara kawata kyawon fuskarta duguwace masha Allahu kirjinta cike yake dam da albarkatun fulani akwaita cikar halitta duk da batada jiki ko kadan amma akwai mazauna kirata sak Coca-Cola sak

idanuta manya manya ne saide alumshe suke kana kallonta sai kazaci kaga kamar da gan take lumshesu amma ba haka abun yake ba halitta tace hakan kwayar idanunta tamkar iron ta turawa haka yake abinda ya Kara mata kyau kenan gashin idanunta gazar gazar ne tana da gashin gira mai kyau mutika tanada dogon hanci dan bakinta madedeci dan bai cika karamtaba ya dan bude kadan pink ne tamkar ta shafa Jan baki kalar pink zaka gani itako halitta tace haka wlh ajikinta babu makosa saide halayarta batajin magana ga rashin kunya da mugunta kamar me batada tsoro kuma bata barin ta kwana mutikar zaka Nuna mata rainin wayo to fah zata nuna maka ita tafika inko ka Nuna mata so to fah zata Nuna tafi kowa sonka kai ita duk da yada kazowa Zaeenaba to zata iya dakai wayarta da take hannu Jannat kawarta ta dauki ringing gunta ta zo ta janyeta tana mata magana da harshen larabci ” habibty zee

majeed na kira fah daket ta cirota daga rawar da takeyi ta bata wayar tayi picking ta fito parlo Umminta na zaune jikinta ta kwanto tana wayar” hello Qalbi me ya hanaka zauwa haka mukayi da kai shiru yayi tsaki taja zata kashe kiran taji daga can yace ” Zee babyna yau inama su Abbu magana tunda kin kammala karatunki suzo ayi magana Dan wlh inajin tsoron yada ‘ya’yan hausawa ke kawo miki hari karki bijiremun tunda kince sunfi burgeki Akan mu kiss ta sakar masa ta wayar tana wani shegen murmishi ” Qalbi na kasan ina Sonka fah to ya kukayi. Da su fashe mata yayi da kuka idanu ta zaro gabanta na faduwa badai shima an Hana ya aure taba” Qalbi garkameman kato da kai kake kuka lfy ta fada dariya nason kufce mata Dan rashin jarumtarsa tasa Sam baishiga zuciyartaba Dan ita tanason jarumin namiji mai cikar zati jajir tacce Wanda abinda za saka sa kuka to fah ba karami bane ba amma shi wai ko fada sukayi ta kirta masa rashin mutumci ya fara mata kuka kenan tsoki taja ranta ya bacci sosai cikin zafi zafi tace Qalbi wlh zan kashe wayar baki daya ayi

namiji ba juriya da jarumta haba ina Dan dalili haka kakeso muyi aure ina juyaka sai yada nayi da kai ga shegen kukanka tsiya to ni idan namaka na shagwaba wa zai lallasheni tirr” Afuwan zee zeena Abbu ya hana yace kasheni zaiyi idan nasake maganarki wai ke yar macace wata uwar tsawa ta daka masa mai firgitarwa idanuta sun kada sunyi jajur kallo daya Raiyan ta mata ta dauke kai tanajin tsoron kar abunta ya motsa Dan bataji bata gani cikin bala’i tace masa ” so wait Dan sunki aikin banza aikin wofi kaine abun tausayi ba niba lusarin Namiji kawai Dan kai kake fama da dafin so kai majeed ba Zaeenaba ba kuma ba nibace yar mace Abbunka ne Dan mace Dan uwarshi da Sauri ummi ta rufe mata baki kashe wayar. tayi tana turo baki ta rungume Raiyan wato mahaifiyarta idanuta wasu irin ruwan hawaye ke fitowa jajaye tamkar jini uwar tagani amma Dan karta lallabata abun yafi karfi sai cewa tayi ” Zaeenaba abinda kikeyi ganinki yanada kyau Kenan duba kiga shigarki kuma dama nace kibar kula maza duk nawa

kikene gashi kinaja anawa mutane cin mutumci ? ” ummi me nayi Dan buro ubansan zaicemun yar mace asali suka fimune ko mai za’a cemun haka mutuwa kan waye bata zuwa shi majeed din ba yaga yan uwan mahaifina ba duka duka watansa nawa da komawarsa kasarsu da ya kammala karatunsa waya baiga tsantsar kamarmu da wannan banzan gayan ba baki ta buge mata” kiyimun shiru ina rabaki da kaya kina shirin lada ganmo ko ” to ummi majeed da kansa yake cewa ko makaho ya shafa yasan muna kama to mai nayi zaki dokeni? ” ni dai ina son ki nutsu ki kama kanki kibar yawo don Allah da raye raye da rashin kunya ni kam Allah yana gani na baki tarbiyya yada uwa tagari takeba d’anta amma ke Al’amarinki sai gyaran Allah fatana ya shiryaki kalli kanki wacce yar mutumci zata maida gashin kanta haka?

” ummina dadin murnar gama makaranta ne fah kuma Dan uwarsu karsu bari ya aureni shegu yan iska ni shiyasa duk cikinsu babu Dan buro uban da na taba so har can cikin raina ta fada tana goge hawayen fuskarta da ya fara rikidewa ya zama jini jini ” ummina kinsan Allah?

Advertisements

Baki ta rufo Mata “imun shiru Allah ya shiryeki Dole zan hadaki da mai gyara miki zama mik’ewa tayi tana zunbura baki tabar wajan duk da ranta abace bai hanaba ta koma gun su manal sukaci gaba da casu saida aka kira sallah asubahi suka kashe kidan Ana wasu suka zube Dan sunyi taune taunesu ko sallah

basuyiba sai bacci amma zee da Jannat saida sukayi sallah suka kwanta don duk iskancin to fah bata wasa da sallah tanajin majeed na kiranta taja tsaki tana harara wayar takin dauka har bacci ya kwashe da kudirin idan suntafi gidansu Jannat baza dawo gidaba sai tayi sati Raiyan tana gama sallah ta kwanta da kudirinta aranta na fitar da zee daga kasar baki daya ko Allah yasa ta shiryu acan Dan tasan anan Dole mahaifinta na farautar ran zee gwara tayi nesa da kasar tasan tabbas za’abata kulawa a can

*Nigeria* da misalin karfe goma na safe azaune na hango wani hadadan gaye Dan kimanin 28 year cikin wani makeken Office Wanda ya gaji da haduwa waya ce manne

akunnesa yana magana cikin nutsuwa sai lumshe mayatattun idanuwansa yake lumshewa ya tura hannusa cikin kwantacciyar sumar kansa yana shafawa sai sheki take tamkar ta larabawa kana kallonsa kasan soyayya yake zubawa farine dogo ingarma namiji jajirtace yanada faffadan kirji fuskarshi ta kawatu da saje Wanda yayi masa masifar kyau yanada manyan idanu lumsassu tamkar yanajin bacci haka suke yanada dogon hanci dimple dinsa har har biyu sun loba sosai Wanda hakan ya Kara masa kyawu na musamman dugone mai sufar karfafa kai da ganin yanayinsa baya daukar wargi ko raini,

nocking kofar akayi ga wayoyi har biyu na ruri yaki ko kallonsu kiran ya tsinke ya bada izinin ashigowa kofar ta murda ta shigo da sallama fuskarsa babu wal wal ya

amsa ta risina cikin bashi girmansa Nurse din tace” Doctor an gama shirya komai kai ake jira ka Shiga tiyata? cikin dadadar muryasa tamkar baya son magana yace “OK ganinan ficewa tayi yai picking din wayar da an kira yafi so goma ya Kara akunnesa shiru ba ayi magana ba gani lokaci na kuremasa ya tsinke kiran ya kashe wayoyinsa ya ajiyesu ya core wani tsadadan agogo ya ajiye ya Mike cikin wani taku na isa da kasaita ya ke takunsa yana bude akofa yaci Karo da yayansa Mahabeer fuskarsa dauke da murmushi yace” haba Dr Sardauna tun yaushe ummi Raiyan ke kiranka baka dagawa wlh itace ta tasuni da kira ina aikina nazo Hospital naga ko lfy baka daukan kiranta kansa, ya dafe ” oh my God wlh my brother abubuwa sun Mun yawa yanzuma tiyata zan shiga ai mun kashe magana da ita ni ba nida dama kaine zaka tafi Dan ta gama shirya komai yada za’a fito da fitsararar yarinyar nan Dan wlh bazan jeba inada abun yi wannan aikin sai kai bantashi kamuwa da ciwon zuciyaba shine daddy yayi fushi wai ai nafi ka sanin garin nade

lallabashi nace ga babba murmushi mahabeer yayi Dan dama yafiso yaje ayi abin karamci” ai nasani tace wai akwai maganar da zakuyi ” OK kace zan kirata idan na fito da Sauri ya wuce cikin kuzarinsa yayi d’akin tiyatar mahabeer ya juya fuskarsa dauke da murmushi Dan yasan halin rikitattan kanan Nasa tunda yace bazai jeba to fah bazai jeba Dan baya ra’ayin zauwar yarinyar Sam yana fita ya shiga motar yaja ya nufi can gidansu yaji ya za’ayi don yasan Tabbas Dr Sardauna bazai jeba kai ya girgiza yana driving dinsa cikin nutsuwa kida na tashi kadan kadan cikin motar ya dauki hanyar gidansu yaji abinda Daddy da zai yanke gama da tafiyarsa saudiyar, kamar yada Dr Sardauna yace din…

 

Sai kunji next page insha Allah

*Karku manta kudin* *wannan book nera dari* *ukku ne kacal zakusha* *karatu maicike da* *abubuwa daban daban*
*na rayuwar duniya ga me bukata ya tuntubeni awannan number my kashe magana Yanda* *zaki sambadi karatunki* *akan dari ukku kacal*πŸ€ΈπŸ»β€β™€
πŸ‘‡πŸ»
*+22796515805*

Rahma ce ummu FareesaπŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€πŸ€ΈπŸ»β€β™€

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like

SALON SO 43-44

Advertisement  πŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎ             🌹 SALON SO 🌹 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾     BOOK ONE πŸ“–…

YAU DA GOBE 19&20

Advertisement  πŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎ   🌹YAU DA GOBE 🌹 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾 Story & writing by mmn fareesa πŸ…ΏοΈ19&20 ,,,,,,Tsaye tayi bakin…

SALON SO BOOK 1 PAGE 17-18

Advertisement  πŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎ             🌹 SALON SO 🌹 🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾     BOOK ONE πŸ“–…