Lu’u Lu’u 17

Advertisement

*17*

 

Kamar wasa sai kam Bukhatir ya shirya cikin shigar alfarma da take nuna ya fa yi niyyar zama mai mulkin k’asar Egypt na gaba, motoci aka shirya inda ya umarci Zafreen da ta shirya zasu tafi, ba kuma Zafreen kad’ai ba har da matarshi Zeyfi, ita kan ta tayi mamaki dan ba zata iya tuna lokacin da sukayi tafiya tare ba, duk da yanzu ma bai fad’a mata inda suka nufa ba, amma hakan ma ya mata dad’i tunda dai ga ta ga shi, dan kwana biyu kenan ko gidan da take bai kwana saboda zumud’in Zafeera wacce ta ke ganin ta shigar mata hanci a duk’unk’une, tana sunan matarshi ne kawai, amma gangar jikinsa da zuciyarsa sun haukace aka wata wacce bai ko tab’a ganinta ba bayan jiya.

Haka kam akayi inda suka d’auki hanya zuwa babban birnin Texanda, *awa takwas* suka d’auka a hanya kafin suka isa masarautar.

Sanda sukayi oda daga k’aramar tagar dake jikin k’ofar mai gadi lek’o, ganin bak’in motoci yasa shi bud’e k’aramar k’ofa ya fito, motar dake gaba ya lek’a ta madubi yace “Yallab’ai daga ina?”

Dreban dake tuk’a motar da Zafreen take ciki ne yace “Daga Egypt tare muke da gimbiyarku.”

Idonshi ya sauke a kujerun bayan motar, ganin Zafreen ta wurga masa wani kallo yasa shi saurin rusunawa yace “Ranki shi dad’e.”

Da sauri ya juya ya koma ciki ya rufe k’ofar k’arama sannan ya shiga fafutar bud’e k’atuwar k’ofar mai taya wacce turawa ne kawai yake, saida ya bud’esu gaba d’aya sannan hancin motocin suka durfafa ciki, duk tak’ama da ji da kan Bukhatir saida ya tabbatar lallai sarki Musail yana murza mulki a daular nan, irin dukiyar daya zuba wajen k’era gidan nan, shuke shuken dake wurin ka rantse lambuna ne ta ko ina, manya manyan b’angarori ne guda uku, na tsakiyar kuma shi ke shaidawa mai kallo a nan sarki Musail yake rayuwarsa.

Kamar yanda sauran motocin ke bin motar dake gaba har saida suka tsaya daf da b’angaren tsakiya, ganin fuskarta daga cikin farin gilashin motar yasa wasu masu tsoron k’ofar su biyu d’aya a cikinsu ya taho da sauri ya bud’e mata ta fito, juyawa tayi ta kalli Bukhatir da matarshi da suka fito su ma, kallon bafaden nan Zafreen tayi tace “Ina mahaifina yake?”

Da ladabi yace “Shugaba na yana fada.”

Advertisements

Juyawa tayi ta kalli Bukhatir tace “Pah yana fada, zaku same shi a can ne ko zaku jira?”

Wani kallo ya mata yace “Ai mu masaukin bak’i ne ya dace da mu, dan maganar data kawomu babba ce.”

Harara ta galla masa sama da k’asa ta kalli bafaden nan tace “Ka kaisu masaukin bak’i.”

Rusunawa yayi yace “Angama ranki shi dad’e.”

B’angaren dake hagun su ya nufa yana kallonsu alamar su tafi, da kallo Bukhatir ya bita sanda take shigewa ciki da mamakin yanda ta bayar da umarnin a rakasu masaukin bak’i.

Jinjina kai yayi ya kalli Zeyfi ya rik’o hannunta, da sauri Zeyfi ta kalleshi tana sakin murmushi dan hakan ya mata dad’i sosai, gana son mijinta so mai tsanani kuma tana kishinsa, saidai tana tsoronsa da kuma shakkun halayensa, dan tun ranar daya wanka mata mari a kan Zafeera bai sake ko kallon fuskarta ba, ita kamba tasan ya zatayi da Bukhatir ba, wasu lokuta har mamakin irin biyayyar da take masa take, gashi dai tana so ta haihu da shi, amma gaba da gaba ya fad’a mata bata isa ta fara haihuwa ba har sai Zafeera ta zo ta fara haihuwa sannan ita ta biyo baya, tabbas ta ga illar auren tushe, watak’ila da mai son ta ta aura da bata ganin wannan k’ask’ancin, amma dake mahaifinta kwad’ayi yasa shi aura masa ita wulak’anci kawai take gani ta ko ina.

Zafreen na shiga duk hadimai suka kama jikinsu, d’akinta ta shiga da sauri sauri ta shiga cire kayanta inda hadimar ta shiga ban d’aki dan had’a mata ruwan wanka, tana kammalawa ta fito ita kuma ta shiga d’aure da k’aramin towel tace “Ki kawo min madara mai sanyi.”

“To shugaba ta.” Ta fad’a tana ficewa a d’akin, bata wani jima a wurin wankan ba ta fito dan dama ta shirya a can, madarar data samu ajiye ta d’auka tana kurb’awa tana kallon kan ta a madubi, dafe k’ugu tayi tana shan madarar tana ayyana _”Ashe dama ita ce Zafeera? Tana da abun al’ajabi yarinyar? Shi yasa ta iya d’aga hannu ta mare ni a fuska? Ai kam zatayi nadama, zan samota sannan na hukunta ta, zata san ni ce gaba da ita ko a haihuwa ma.”_

K’wafa tayi mai k’arfin gaske tare da aje madarar ta shiga shiryawa a tsanake, cikin shigarta ta alfarma na kayan sarauta ta shirya inda ta fito fes da ita ta gama kyau, fitowa tayi daga d’akin tana ta k’amshi abun ta, jakadiyar da suka had’e da ita yasa ta tambayar “Ke ina Mah?”

Da sauri ta d’aga kai ta kalleta tana rarraba ido da tunanin ta inda zata fara fad’a mata, sunkuyar da kai tayi tace “Ranki shi dad’e sarauniyata bata nan.”

Yatsina fuska tayi tace “Ina kuma ta tafi?”

Kad’an ta ja baya dan tsoron mari take idan ta bata amsar, girgiza kai tayi dan kare lafiyarta tace “Ni ma ban sani ba gimbiya.”

Advertisements

Tsawa ta daka mata tace “Kamar ya baki sani ba? A gidan nan fitar Mah tana b’oyuwa ne ko dan yan rakiyar da Pah yake had’ata da su, zaki fad’a min ko sai na wulak’antaki?”

Jiki na b’ari ta durk’ushe k’asa tace “Ranki shi dad’e ai sarauniya ta kwana biyu a gidan kurkuku na sabah.”

Da k’arfi tace “Me? Kurkuku?”

Da sauri ta taka zata bar wurin sai kuma ta juyo ta kalleta tace “Akan me wai?”

Shiru tayi hakan yasa Zafreen fita da sauri kamar zata tashi sama, b’angaren damansu ta shiga inda anan fadar take, sosai ke da banbanci tsakanin babban b’angaren da kuma nan d’in, inda kujerarshi take cikin sauk’i Zafreen ta hangeshi, fadawan kuma duk suna zazzaune suma a kan kujeru cikin shigarsu ta alfarma.

Tunda suka ji an bud’e an shigo babu neman izini suka maida hankulansu kan k’ofar, ganinta yasa kowa mamaki har sarki Musail da waziri Khatar suka mik’e dan suna tsaka da maganar inda ta shiga ne ita ma, da sassarfa sarki Musail ya sauko a matakalar ta fari da ta biyu har zuwa ta uku wacce ita ce ta k’arshen dake sadashi da kujerar mulkinshi, bud’a hannayenshi yayi da farin cikin ganinta yace “Gimbiya Zafreen, yaushe kika shigo? Ina kika shigo haka?”

Ja baya tayi cikin d’aga murya tace “Pah, me Mah tayi haka da zafi daka zab’i kulleta a kurkukun sabah? Kurkukun da kake rufe manyan masu laifin daka kama ko kuma kake son horar da mutum dan nuna masa ikonka.”

Sauke hannayenshi yayi ya dogara sandar shi a k’asa ya k’ura mata ido, shiru yayi bai da niyyar amsata, cikin jin haushi ta sake maimaita” Pah, mahaifiyata fa ka rufe a kurkuku, ina so nasan me tayi haka? Ka daina son ta ne?”

D’auke idonshi yayi a kanta yace” Zafreen, shin ba ke kika bamu bayani akan sark’ar nan ba?”

Gyara tsayuwa tayi tace” E.”

D’orawa yayi da” Me yasa bakiyi tunanin hanyar da suka samu sark’ar ba? Kin tab’a jin mahaifiyarki tayi k’orafi akan b’atan sark’arta ne?”

Tsareshi tayi da ido tace” A’a, hasalima bamu san da b’atan sark’ar ba, daren da zan bar nan na fahimci bata tare da sark’ar.”

Buga sandarshi yayi k’asa sosai tare da d’aga sauti yace” To wannan dalilin ne yasa na rufeta, Juman ta ha’inceni ta yaudare ni, shiyasa na kawar da duk son da nake mata na hukunta ta.”

Da mamaki tace” Kana nufin Mah da hannunta a b’atan Zafeera kenan?”

Shiru ya mata ya juya ya shiga takawa a tsanake har ya koma kan kujerarshi ya zauna, waziri Khatar daya kalla yasa shi gyara tsayuwarshi ya kalleta yace” Gimbiyata, an samu sarauniya Juman da laifi dumu dumu na b’atan Zafeera, dan da bakinta ta fad’i hakan saboda ta kub’utar da ita.”

Dafe k’ugunta d’aya tayi ta cije leb’enta na k’asa tana girgiza kai, ta d’auki sakanni a haka kafin ta kalli sarki tace” Mahaifi na, yanzu haka tare muke da wanda ya sace ni ya kuma sace maka Zafeera.”

Da k’arfi ya mik’e akan kujerar yace” Me? Wanene shi? Yana ina? Me ya kawosa nan?”

Lumshe ido tayi ta motsa baki alamar tambayoyin sun hau mata kai ba kuma zata iya amsawa ba, a hankalce tace” Yana masaukin bak’i.”

Cikin zumud’i yace” Kenan suna can tare da Zafeera?”

” A’a.” Tana fad’a ta juya tana fad’in” Zan je na ga Mah, Adah ka rakani.”

Da kallo Adah dake kusa da sarki ya rakata yana jin takaicin iya shegen yarinyar nan, amma sarki Musail na kallonshi bai da zab’in daya wuce bin bayanta da sauri suka fita.

Suna fita sarki Musail ma ya kalli waziri yace” Wanene wannan? Me yasa ya zo nan bayan yasan zan iya halaka shi?”

Dhurani dake kan kujera kusa da waziri ne yace” Ka gafarce ni sarki na, ina ga ka fara had’uwa da shi, watak’ila akwai dalilinshi na zuwa nan.”

Da kallon tuhuma ya bishi yace” Kana nufin ko da magana ya zo na zauna na saurare shi? Bayan kuma ina zarginsa da nesanta ni da Zafeera.”

Waziri ma cewa yayi” Hakane sarki na, mu fara sauraranshi mu ji, ta haka zamu san inda Zafeera take.”

Jinjina kai yayi ya kalli Dhurani yace” Muje tare.”

Mik’ewa Dhurani yayi ya bi shi suka fita inda waziri ya ji haushin hakan, ya so aje da shi ya ji me ya kawosu me kuma za’a tattauna, hakan yasa shi jan tsaki ya fara safa da marwa dan ba zai iya zama ba har sai ya jie aka tattauna.

*Giobarh*

 

Duk da ta jima bata kwanta ba amma sai ga shi k’arfe 07:00 tana bugawa ta farka saboda sabon tashi, saida ta bud’a idon ta ne ta fahimci inda ta kwana, a gajiye kuma a kasalance ta yaye rufar ta sauka a gadon, gaban madubi ta k’arasa tayi tsaye tana kallon kanta da tunanin me zatayi ? Gudu zata fara da shi? Ko kuma gyaran makwancin data tashi? A sanyaye ta fad’a ban d’aki ta fara da wanke bakinta da fitsari sannan ta fito, gurin kaya ta fara dubawa dan ta ga ko zata samu k’ananan kaya na motsa jiki, saidai duka kaya ne manya a ciki irin wanda ta gani jikin matar nan ta jiya (Joyran).

Rufewa tayi ta koma kusa da tagar gurin, bud’ewa labulen tayi hakan yasa hasken safiyar shigowa d’akin, ta madubin ta dinga kallon tarin shukokin wanda suka mata kyau take kuma ayyana lallai zasuyi k’amshi gurin kuma zai yi sanyi.

Da sauri ta saki labulen ta nufi k’ofa dan fita ta shak’i wannan daddad’an oxygen d’in, tana bud’e k’ofar ta fara takawa, fitowarta tayi daidai da bud’a d’akin sarauniya Kossam da wata hadimar tayi d’auke da farantin abincinta, a ladabce ta gaishe da Ayam d’in ta amsa, fuskarta a sake tace “Dama da mutum ne a nan?”

Da girmamawa tace “E ranki shi dad’e, ai d’akin sarauniya ne.”

D’aga girarta tayi sama tace “Oh ! Zan iya shiga ciki?”

A ldabce tace “E to ranki shi dad’e zaki iya.”

Hannu ta kai ta bud’e k’ofar ita ce a gaba hadimar na bayanta, ganin matar kwance yasa Ayam kallon hadimar tace “Bata da lafiya ne?”

“E, ai ta jima kwance a haka.” Ta fad’a sanda take aje farantin hannunta, da tausayi Ayam ta kalli Kossam da idonta ke rufe tace “Me yake damunta ne?”

Girgiza kai tayi tace “A gaskiya ban sani ba, shekara uku da fara aikina a nan, nima a haka na sameta.”

Da mamaki ta waro ido tace “Shekara uku? To ita shekara nawa ta d’auka a haka?”

Cike da jimami tace “A yanda na ji suna fad’a shekara ashirin kenan.”

Da k’arfi tace “What? Oh my God.”

Ta fad’a tana k’arasawa ga Kossam, zaune tayi bakin gadon ta rik’o hannunta, kamar ta tsikareta da allura sai kawai ta tsam ta bud’a idonta ta zuba akan Ayam d’in, wani tattausan murmushi Ayam ta sauke ta kalli hadimar tace “Ta farka, tana magana ne?”

Girgiza kai tayi tace “A’a ranki shi dad’e.”

Kallon Kossam ta sake yi, sanyayyan murmushi ta sakar mata a karo na biyu ta sake jimk’e hannunta, cikin taushin murya tace “Kina ji a ranki kamar ki ce wacece ni ko?”

K’urawa fuskarta ido tayi tana son ta ga ko zata amsa lata da ido, sai kawai ta ji ta d’an jimk’i hannunta, kallon hannayen na su tayi sai kula ta sake kallonta tace “Kin gaji da kwanciyar nan haka ko?”

Sake jimk’e hannunta tayi, da sauri ta sake kallon hannayen na su, k’ura mata ido tayi tace “Kina so kiyi magana ne?”

Sake damk’e hannunta tayi, jinjina kai Ayam tayi tce “Zaki yi magana, zaki samu lafiya nan kusa ke ma.”

Mik’ewa tayi tsaye ta kalli hadimar tace “Taimaka min mu gyara mata jikinta ta ci abinci.”

Zaro ido tayi hadimar tace “A’a ranki shi dad’e, ai babu mai alhakin bata ko da ruwa ne sai mai girma Joyran.”

A yatsine ta kalleta zatayi magana sai kuma ta ji Kossam ta sake rik’e hannunga gam a cikin na ta kamar za’a rabasu, kallonta tayi da mamaki ta kalli hannayen na su, nazartarta tayi sosai ta shiga karantar yanayinta, sai kawai ta kalli hadimar tace “Wacece haka kuma?”

Tausasa murya tayi tace “K’anwar sarauniya ce, ita ke kula da ita tsawon lokaci.”

Mik’ewa tayi daga rank’wafawar tace “Kuma dole sai ita ce zata iya kula da ita, babu wani wanda zai iya saka hannunsa da sunan taimako?”

A tsawace tace “Malama kama min ita.”
Da sauri ta matsa suka kamata ta dinga nunawa Ayam d’in yanda suke taimaka mata, har baki saida ta wanke mata da mai ta tsefe mata kai sannan tace ma hadimar “Samo mata kayan sakawa.”

Da sauri hadimar dake mamakin iko na wannan yarinya ita ma tace “Ai kayanta suna d’aya d’akin, mai girma Joyran ce tasa aka mayar da su can.”

A dak’ile fuska a had’e Ayam tace “Ai cewa na yi ki d’auko min, ba wai ki fad’a min inda suke ba.”

Da sauri ta juya ta fita ta shiga d’akin da aka sauke Ayam d’in, ita kuma abincin ta d’auka ta fara ba wa Kossam wacce k’arara zaka fahimci fuskarta bata cikin yanayin nan na dumkum data saba.

Duk da ta ji an bud’e k’ofar bai sa ta juyo ba dan tunanin ta hadimar ce, amma sai ji tayi an ce “Uban wa ya baki damar bata abinci?”

A gadarance kamar wacce ta tashi da ciwon wuya haka ta juyo ta kalli Joyran wacce tashin hankali ya bayyana a gareta k’arara, d’auke kan ta tayi ka rantse bata san da mutum a wurin ba tace “Kin ci sa’a d’aya an ce yar uwar madam ce ke, ba dan haka ba da na ce *uban ki*.”

Kossam kan ta saida mamaki ya bayyana a fuskarta, uwa uba kuma hadimar nan data shigo d’auke da kayan da Ayam d’in ta buk’ata, haka ma Joyran kusan jiri ta ji zai d’ebeta, yanda ta zazzaro ido ta k’ura mata su kamar wacce ke kallon gawa na motsi, sam mantawa tayi da a inda take me kuma take yi saida ta tsinkayi muryar Ayam a kunnenta tana fad’in “Ki daure ki k’ara kad’an madam, please.”

Da sauri ta zabura kamar wacce aka mara ta k’arasa shigowa d’akin, cikin tashin hankali da neman bala’i ta bige farantin abincin tana fad’in “Ke har kin isa? Wacece ke da zak…”

D’aga mata hannu Ayam tayi ta d’ora yatsa a labb’anta tace “Shiiiii!”

Kallon fuskar Joyran d’in tayi tace “Haka kawai na tsani tsawa, na tsani a d’aga min murya musamman a k’ok’on kai na, na rlk’oki kar ki jawowa kan ki mummunar safiya ta hanyar tak’alata rikici, ina so na kafa kyakyawan tarihi a gidan nan kafin na barshi.”

Juyawa tayi ta kalli hadimar tace “Kawo kayan ki taimaka min a saka mata.”

A tsorace cikeda girmama lamarinta hadimar ta k’araso jikinta har rawa yake ta aje kayan kan gado, a tsawace Joy ta kalli hadimar tace “Ke! Idan baki bar nan ba sai na tozartaki.”

Da kallo Ayam ta bi hadimar data fita a rikice ta rasa me zatayi, zagayawa tayi ta d’auki kayan ta warware ta tako zata koma inda take, cikin jin haushi Joy ta fizge kayan ta jefar a k’asa tace “Fita a nan malama, sannan ki ji da kyau.”

Tayi maganar tana nuna Ayam da yatsa, d’orawa tayi da “Daga yau sai yau karko sake shigowa d’akin nan bare ki k’araso gareta, babu ruwanki da abinda ya shafeta, idan kuma kika sake to ki sani ki ma zaki tsinci kanki a mugun hali.”

A take, a bazata, kamar saukar aradu Ayam ta rulgume hannaye tana fad’in “Kamar yanda kika jefata kenan?”

Wani mummunan fad’uwa ne gabanta yayi ta rarako ido ta kalleta, take wani gumi ya shiga tsatsafo mata a goshinta zuwa wuya, tsatsareta tayi da ido ta sake gyara tsyuwarta tace “Ko kuma zaki jefani fiye da halin da kika sakata ne duk tsawon shekarun nan?”

Kame kame ta fara tana jujjuya kai tace “Ke ke..me kike…fad’a ne wai haka ? Baki da hankali da alama.”

Tana fad’a ta rab’ata zata fita a d’akin, ta kai daf da k’ofa kuma sarki Musail ya shigo daidai da Ayam tace “Ina da hankali, amma ki sani a cikin haukana zan bankad’o sirrin da kika jima kina b’oyewa ta hanyar wasar kura da rayuwar mutuniyar kirki.”

Rud’ewa Joy tayi ta kalli sarki Musail dake binsu da kallon tuhuma yana son sanin me ke faruwa, fashewa tayi da kukan makirci tana fad’in” Wannan ma ai tozartani kike yi, yar uwata ce fa, ya kike tunanin da hannu na a cikin rashin lafiyarta?”

Shigowa yayi yana kallon Ayam yace” Gimbiya Zafeera, me yake faruwa ne? Tana neman b’ata miki rai ne?”

Kallonshi Joy tayi da mamaki wato bai ma damu da damuwarta ba bare kukan da take, figaggiyar ma yake tambayar ko ana neman b’ata mata rai ne?

Ayam kam murmushin yak’e tayi tace” A’a ranka shi dad’e, ba komai muna magana ne.”

Kallon Joy yayi yace” Ki koma b’angaren ki, sannan ki kiyaye b’acin ranta, dan zan iya yin komai a kan ta.”

Kallon shi Joy tayi ta k’ara kallonshi sau ba adadi, sai kawai ta juya ta fita dan bata san me zata fad’a ba, tana fita kuma Umad na shigowa har ma yana gaisheta amma sai ya fahimci bata cikin hayyacinta, yana shigowa ciki ya zuba idonshi akan ta, duk da rigar bata fito da jikinta ba face k’afafunta da kuma fuska sai tafukan hannu, amma sai ya ji ya tsani tsayuwarta haka kuma a gaban mahaifinshi.

Bai kula da sarki Wudar dake tsaye ba haka mahaifiyarshi da idonta ke kan shi, fuskarsa a had’e ya kalleta yace “Malama ki je d’akinki ana kai miki kaya yanzu.”

Abun al’ajabi da mamaki daya kusan saka sarki Wudar suman tsaye shi ne yanda Ayam ta jinjina kai alamar to ta kuma kama hanya ta fice, sai ya ji ya fara kokonto ko dai ba ita bace, dan wacce aka fad’a fa komai matsayinka ita ce zata baka umarni kuma kayi jikinka na b’ari, hasalima ita waccen idonta kawai sun isa su saka mai aurenta durk’usawa kan gwiwoyinshi ya tambayi me take da buk’ata.

To amma kuma wannan ya d’anshi ya bata umarni haka ta bi? Duk da dai yasan waye Umad wajen tsare gida shi ma akwai izza da shan k’amshi inda a msarauta yake, to amma ai ta ta izzar ta dame ta shi ta shanye dan ita harda baiwa a lamarinta, uwa uba kuma sarautarta ta fi tashi k’arfi. (Idan har ta zama yanda kuke fad’a ai bata dace da zama matar kowa ba kenan, dole ta auri kan ta)

 

*Alhamdulillah*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 83

Advertisement *Page 83*   *********************   Tana k’uryar d’akin Umma taji sallamar shi, gabanta ya k’ara fad’uwa, haka…
Read More

TARTSATSI 41

Advertisement *Page 41* ****************** Malam ya mik’e tsaye yace da Aliyu ya kira su Abba minti biyu sai…
INAYAH
Read More

INAYAH 10

Advertisement 10_* *_Arewabook@Mamuhgee_* Tana isowa gidan tun a compound tasan Abbi yadawo gida sbd ganin sabuwar motarsa da…
Read More

TARTSATSI 33

Advertisement page 33* ********************* Nan take wani zazzabi ya rufeta, saboda lamarin na sadauki, ba k’aramin tsorata ta…
Read More

TARTSATSI 44

Advertisement *Page 44* ******************** Abba da kanshi yayi kiran Dr yace, yazo yana nemansa, ba tareda b’ata lokaci…