Advertisement
*18*
Saida ta fita ne Umad ya kula da yanda ya ga mahaifiyarshi, da sauri ya zagaya b’angaren ta ya rik’o hannunta yace “Mahaifiyata kin tashi lafiya?”
Zuba mata ido yayi amma kuma yana fahimtar amsar da take bashi ta tafukan hannayensu, shafa kan ta yayi da ya ga an gyara mata shi yau sannan yayi murmushi ya mik’e yace “Mah ina zuwa?”
Yana fad’a ya nufi fita a d’akin sai ya ji sarki Wudar ya rik’o hannunshi, juyowa yayi suka kalli juna, a tausashe sarkin yace “Kasan wacece ita da kake bata umarni haka?”
Wani malalacin murmushi yayi yace “Na sani Pa.”
Yana fad’a ya zage hannunshi a hankali ya fice a d’akin, kayan daya tanadar mata ya ba wa d’aya daga cikin hadiman gidan ta kai mata a d’akinta, inda shi kuma yana fitowa daga b’angaren sa ya ci karo da amininshi Haman ya zo gidan.
Had’e fuska Umad yayi sosai ya tako kamar mai tsorontaka k’asar ya tsaya gaban Haman d’in dake jingine a motarshi, Haman kam dake k’are masa kallo ya san akwai abinda had’e fuskar nan ke nufi, amma sai ya dake ya mik’o masa hannu yana murmushi yace “Barka aboki.”
Hannun Haman d’in ya bi da kallo kafin ya kalli fuskarshi, kawar da kai yayi sannan ya mik’a masa hannun yana d’an jinjina kai, gyara tsayuwa Haman yayi yace “Wai me yake damunka ne?”
A dak’ile yace “Me ka gani?”
Advertisements
Da yar raha yace “Na ga kayi wani iri ne ai, kamar ba kayi farin cikin gani na ba, da wata matsala ne?”
Tsakiyar k’wayar idon Haman d’in ya kalla fuskar nan a murtuke yace “Haman, bayan ni da kai bana jin akwai wani da yasan inda Zafeera take, ya akayi a sanda nake can kuma sai ga mutanen Baba na?”
Sunkuyar da kai yayi yana k’yakyabta ido da sauri kuma ya d’aga kai yace “Kamar ya? Zargi na kake Umad? Na d’auka kafi kowa sanin ba mu kad’ai muke nemanta a lokacin ba.”
Jinjina kai yayi yace “Hakane, amma kuma mu kad’ai muka san gakamaimai inda take a lokacin.”
Gyara tsayuwarshi yayi ya d’an sassauta had’ewar da ya ma fuskarshi yce “Haman, kasan aikinmu aikin sirri ne, kuma zamu kai ga gaci ne ta hanyar Zafeera, a duniya babu wanda ya san sirri na sama da kai, kar ka yarda na fara d’ora alamomin tambaya a kan ka, hakan zai ruguza maka yardar daka samu a wuri na.”
Juyawa yayi zai nufi babban b’angaren yace” Muje ka ci abinci, sarki zaiyi farin ciki da ganinka.”
Da kallo Haman ya rakashi har ya shige ciki ya dain ganinshi, wani sakaran murmushi ya saki akn labb’anshi ya furta” Zamu gani Umad, zamu gani.”
Da sauri ya shiga taka matakalar ya shiga b’angaren shi ma, sai kuma ya samu Umad da sarki Wudar da kuma Joy zaune wajen cin abinci ana zuba musu, k’arasawa yayi a ladabce ya gaishe da sarki sannan ya masa izinin zama kusa da shi, yana zama kuma sautin tkalmin Ayam suka sanar da su zuwanta.
Sarki Wudar da Haman da kuma Joy ne suka bi ta da kallo, rigar yadin dake jikinta mai santsi da kauri da k’yalli-k’yalli zai nuna maka yadin babba ne, saidai d’inki ne simple babu kwalliya, rigar har kasa ta sauka ta bak’in yadin sai hannayen da suka matseta sosai har zuwa gwiwar hannunta, daga k’irjinta ma zuwa ciki ya matseta sosai sai k’ugun da aka fito mata da tsarin surarshi sai tayi kyau sosai.
K’arasowa tayi ta ja kujera kusa da Umad ta zauna, tana neman cire takalmin k’afarta, dan gaskiya bata saba saka wannan takalmin ba ko can dama, wasu lokuta tana sakawa ne idan zata tafi wani shagali ko kuma wani shagalin makaranta, duk da shi ma kad’an ne a aikinta ta saka riga da wandonta mai yagewa a gwiwa ko cinya ta saka takalminta k’afa ciki ta d’auresu tamau da zariyarsu, shiyasa yanzun sai k’afafunta suka fara ciwo saboda sakawar da tayi jiya da kuma yanzu.
Da kallo ita ma ta bisu d’aya bayan d’aya kafin ta dire a kan sarki Wudar tace “Barkanku.”
Da wani irin alfaharin jin kasancewa gashi ga Zafeera ya jinjina kai ya saki murmushi yace “Barka gimbiya ta.”
Advertisements
D’an yak’e kawai ta masa ta maida hankalinta kan farantin ta, a hankali ta saci kallon Umad da shi ma lokacin yake kallonta, amma suna had’a ido yayi gaggawar d’auke na sa ya wani yatsina fuska irin ko menene d’in nan? D’auke kan ta tayi ita ma ta kalli Haman, da fara’a a fuskarta tace “Amma kai balarabe ne?”
Da sauri ya aje kofin daya d’auka mai ruwa zai sha ya tsura mata ido, cikin zaro ido yace “Wacece ke kuma? Me yasa kika ce haka?”
Murmushi tayi tace “Alamunka ne ya nuna, kuma da alama larabcin parsi kake, idan ba parsi ba to Ourdu.”
D’ora yatsanshi yayi a goshi yana rarraba ido, zufa zufa yake jin tana neman wankeshi daga zaune, to ta ya ma ta sani lokaci d’aya haka? Ko fa Umad bai san asalin waye shi ba, ya ita take neman saka shi a uku haka? Sarki Wudar kam wani farin ciki ne ya lullub’eshi har ya kalli Haman yace “Ita ce fa, Zafeera.”
Tsoron da Umad ya gani a tare da Haman d’in a lokacin sai ya sake jefa masa shakku a kan shi, tar tar yake kallonsa yana kuma karantarsa, cikin i’ina ya kalli Ayam yace “Ke ce dama? Sannu ko, ai mun jima muna nemanki.”
Murmushi kawai ta masa ta d’ibi abincin ta kai bakinta, sam ta k’i yarda ta kalli inda Joy take, saidai tar take kallonta ta k’asan ido, tana kuma ji a jikinta irin mugun kallon da take bin ta da shi, gyara zamanta tayi ta kyab’e fuska kamar yarinya ta kalli sarki Wudar tace “Am yallab’ai, zan iya tambayar wani abu?”
Da fara’a yace “Zaki iya mana gimbiya, ai ki saki ranki kiyi duk abinda kike so, nan gidanki ne kuma masarautarki.”
Gyara zamanta tayi tace “Yallab’ai dama ina so ne nasan dalilin zama na a nan? Ina so na koma gida saboda ina karatu a can.”
‘Yar dariya yayi yace “Karki damu gimbiya, ki d’an bani lokaci kad’an, zaki san me yasa kike zaune a nan.”
Bud’a baki tayi a hankali tace “Amma…”
Sai kuma ta jinjina kai kawai tace “Shikenan.”
Sake kallonshi tayi tace “Yallab’ai me yasa madam take gida kwance madadin asibiti?”
Muskutawa yayi hana ci gaba da cin abincinshi yace “Bana jin akwai asibitin da ban fita da Kossam ba, amma magana d’aya ce ba’a san dalilin ciwonta ba, da fari tana magana, amma a k’arshe sai ta zo ta daina, boka ya fad’a mana sammu ne kawai aka mata, amma kuma shi ma ya kasa karya wannan sihirin.”
Tarrr! Ta sauke idonta cikin na Joy da ita ma take kallonta kamar zata fasa ihu, girgiza kai kawai tayi tace” Zata samu sauk’i ita ma, amma da taimakonka.”
“Kamar ya?” Ya tambaya yana tsare ta da ido haka ma Umad dake neman gasgata mafarkinshi da kuma abinda malamin nan ya fad’a masa cewa _”Ban san gaibu ba, amma a d’an ilimin da Allah ya bani zan iya karambanin fassara mafarkinka Umad, a ganina kar ka cutar da ita saboda kana jin haushin mahaifinta kuma kana son d’aukar fansa a kan sa, a gani na zai fi kyau idan ka sameta ka kyauta ta mata, alamu sun nuna zata iya zama silar warkewar mahaifiyarki, dan ni kai na abinda na fahimta a ciwon mahaifiyarka da sihiri a ciki, kuma ko shakka babu a kullum ana sake sabinta mata wani mugun k’ulli, saidai Allah ya barwa kansa sani, shin wanda ta had’a jini da shi ne ko kuma daga nesa, abu d’aya da zan fad’a maka shi ne, da na kusanta ne ake samun nasarar cutar da ita.”_
Gaba d’aya ya tattara hankalinshi kan ta yana so ya ji me zata fad’a, a tsanake cikin ladabi tace” Ina nufin ka canza mata masu kula da ita, sannan ka kafa dokar hana shiga d’akinta idan ba kai ko d’anta ba, sannan duk abinda za’a mata anfani da shi misali ruwa ko abinci, to a tabbatar an duba lafiyar abinda zata ci sannan wanda aka yarda da shi ne zai bata.”
K’uri sarki ya mata yace” Gimbiya Zafeera, kina magana kamar kina so ki nuna kin gano wani abu ko kuma kina son fad’an wani abu ko?”
Sanyayyan murmushi tayi ta girgza kai tace” Babu abinda na sani yallab’ai, saidai lokaci d’aya na fahimci ana ciyar da madam gubar da a kullum take dad’a kassara mata gabb’an jikinta, imma a ruwa ko a abinci.”
Tare Umad da sarki suka kalli Joy, rarraba ido ta shiga yi tana kallonsu tace” A’a, ya kuke kallo na kuma? Wannan yarinyar fa na kula munafuka ce, tunda ta zo gidan nan take min wani gani gani, ta ya kuke tunanin zan cutar da yar uwata? Ita kad’ai fa ta rage min a duniyar nan.”
Ta k’arashe maganar tana fashewa da kuka, Umad da ya ji tuni zuciyarshi ta fara d’arsa masa shakkunta ne a mugun dak’ile yace” Goggo kin ji mun ce wani abu ne ? Kallonki fa kawai mukayi, miye na tsarguwa kuma?”
Dakatawa tayi da kukan ta kalleshi tace” Ni ba tsarguwa na yi, kula nayi kamar kun yarda da abinda da ta fad’a.”
Sarki Wudar ne ya tab’e baki yace” Idan ma aka samu da hannunki a rashin lafiyar matata babu abinda zai hanani hukunta ki.”
Da mad’aukakin mamaki ta kalleshi tace” Wudar, dama zaka iya hukunta ni?”
Da mamaki Umad ya kalleta jin ta ambace shi da sunanshi wanda bai tab’a jin haka ba, Haman da ke neman haukacewa daga zaune shi ma tsatsaresu kawai yake da ido yana neman dalilin da zai tashe shi a wurin nan kafin yarinyar nan ta masa *bankad’a*, dan ya kula daga cikin dalilin da yasa kowa ke nemanta akwai son fallasa abinda ke b’oye, tunda gashi har ta zak’ulo sirrin daya b’oye shekara da shekaru.
Sarki Wudar kam ranshi b’ace yace “Ko waye a duniyar nan zan hukunta shi indai akan matata ce uwar d’ana k’wallin k’wal a duniya.”
Malaacin murmushi tayi ta kalli Ayam sama da k’asa tace “Har wannan ma zaka iya hukuntata akan Kossam?”
Wani abu Umad ya ji ya soki zuciyarshi da yasa shi wurga mata wani kakkausan kallo, Ayam kam mik’ewa tayi tsaye ta kalleta ta kalli sarki Wudar tace “Me kike nufi da abinda kika fad’a?”
A wulak’ance Joy ta gyara zamanta tace “Ina nufin…”
Tsawar da sarki ya daka mata tasa ta yin shiru ta kalleshi tana hararenshi, kallon su Umad yayi da Ayam yace “Ku jira a waje kun ji.”
A hassale Umad ya mik’e ya fita Haman da Ayam kuma su’a bayanshi, suna fita Haman kam bai yarda ya tsaya dan shi ma a tsorace yake, motarshi ya shiga ya tayar ya bar gidan, Umad na tsaye yana hangenshi har ya fita a gidan, bayanshi Ayam ta tsaya tace” Me nake yi a masarautarku?”
A hankali ya juyo ya kalleta, kawae da kai yayi a gadarance yace “A yanzu dai kam ban sani ba ni ma, tabbas mahaifina ma yana cikin masu nemanki, sai dai bansan me ye manufarsa a kan ki ba, mu jira lokaci kad’an kamar yanda ya fad’a mu ga me zai bayyana mana.”
Da mamaki a fuskarta tace “Ko da manufarsa zata iya saka rayuwata a had’ari kana nufin mu zuba ido har sai zai aiwatar zamu sani?”
Jinjina kai yayi ya juya mata baya yace “Kusan haka?”
Cikin jin haushi ta koma ta gabanshi ta fuskance shi bakinta d’auke da masifa da niyyar tace “Wai kai wanene? Me kake ji da shi? Kai bana son iskanci ka ji ko, ka d’auke ni a nan ka mayar da ni garina.”
Amma kuma yana saka k’ananan idonshi masu sirkin ja a cikin na ta sai kawai ta sunkuyar da kan ta muryarta a tausashe sosai tace “Kana yi kamar baka damu da rayuwata ba yallab’ai, idan hakane to ka maidani garinmu.”
Wata dariyar rainin hankali ya mata yace “Damuwa da rayuwarki? Oho na gane! Wato so kike nima kamar sauran marasa aikin yi, na dinga binki sau da k’afa ina washe miki baki, ina nuna miki babu kowa sai ke ko? To ba zai yiwu ba, ni ba sakarai bane.”
Da sauri ta kalli fuskarshi tace “Sakarci? Hakan wai shi ne sakarci? Yanzu idan da ni k’anwarka ce zaka yarda kana kallo mutanen da ban sani ba suna neman juya min rayuwata? Ko kuma da soyayua muke da kai zaka yarda a rabamu ne? Da kuma ni matarka ce fa a ce z…”
A mugun tsawace yace “Shiru malama.”
Zabura tayi tare da rintse ido gam ta k’ame wuri d’aya, k’urawa fuskarta ido yayi yanayin firgicin data nuna sai ya ji kamar yayi ta kallonta, sanyayyan murmushi ya saki a b’oye a zahiri kuma ya had’e fuska yace “Abinda na fad’a miki jiya ma baki yarda da ni ba, ya kike so na yi kenan?”
A take ta bud’a idonta tace “Ka kaini wajen iyaye na to.”
A shek’e ya kalleta yace “Wane daga ciki?”
Kallonshi tayi da fari da mamakin tambayar, sai kuma ta kawar da kai tace “Iyayena, wanda suka raine ni har na girma.”
Shi ma kawar da kan yayi yace “Suna cikin tsaro a inda suke, rayuwarsu na cikin had’ari, ba zan iya nuna miki su ba.”
Da mamaki tace “Me ya sa rayuwarsu a had’arin? Me suka aikata?”
Kallon fuskarta yayi ya saki murmushi mai ciwo, kamo sark’ar wuyanta yayi yace “Ina kika samu wannan?”
Kallon hannunshi tayi dake rik’e da sark’ar tace “Iyaye na suka bani.”
“Tun yaushe?” Ya tambaya yana tsareta da ido, ba alamar tabbaci a tare da ita tace “Ban sani ba nima, na ganta a wuyana ko da nayi wayo.”
Murmushi yayi yace “Wannan sark’ar a ranar da aka haifeki aka saka miki ita, Ayam karki dameni da son ganin marik’anki a yanzu, duk tambayoyin da kike da muradin yi musu kina da amsoshinsu idan kika aje hankalinki, ki nutsu ki fara tariyar alak’arki da su, dan su basu d’aukeki a ‘yar da suka haifa ba sai yar da sarauniyarsu ta haifa, ma’ana gimbiyarsu.”
Matsawa yayi daf da ita ya saki sark’ar yace” Kina son ganin abun mamaki a rayuwa?”
Idonta ta zuba cikin na shi tace” Ina son abubuwan mamaki a rayuwa, idan ban k’aru da ilimi ba na kan samu alfanu a tare da hakan.”
Jinjina kai yayi yace” Idan kowa yayi bacci zan tasheki sai mu je wani wuri.”
Da mamaki tace” Me yasa sai kowa yayi bacci? Me yasa baka son kulani a gaban mutane?”
Juyawa yayi yana fad’in” Saboda tsaro ne.” Da kallo ta bishi har ya shiga wani b’angaren da take tunanin na shi ne.
A ciki kuma suna fita a hassale sarki Wudar ya rik’o hannun Joy yace” Me kike so ki tabbatar a haka? Me ye na k’ok’arin fad’a musu abinda ba yanzu na ke da niyyar fallasa shi ba.”
Jujjuya masa baki tayi ta fizge hannunta tace” Wannan kuma kai ka jiyo, amma ka sani inhar zaka dinga nuna ban da mahimmanci yanzu a gareka to abinda zai dinga faruwa kenan.”
Nunata yayi kamar zai tsone mata ido yace” Ki sani ke baki isa ki lalata min shirina akan Zafeera ba, kina gani akan idonki zan aureta kuma babu yanda zakiyi.”
Rai b’ace tace” To ko ka shirya hujojjin da zasu kareka daga zargi da jifan mutane, dan tabbas zasu san meye alak’ata da kai, sannan su san bayani a game da sabon yarimansu dake hanyar shigow duniyar.”
Tab’e baki yayi yace” Ki sani zaki burmawa cikinki wuk’a ne, na farko ke ce zaune a gidana, na biyu babu wanda ya tab’a gani na a b’angaren ki musamman da dare, na uku kowa dake gidan nan ya shaida irin shigar da kike yi, sannan ki tuna wani abu! Gimbiya Zafeera ta fara bayyana mana wani abun wanda shi ma zai iya sake jefaki bakin al’ummata.”
Yana fad’a ya juya ya bi ta k’ofar da zat sadashi da fadarshi dan gudanar da mulkinshi.
*Khazira*
Sarki Musail na shigowa suka had’a ido da Bukhatir, cak ya tsaya ya furta “Bukhatir?”
Mik’ewa Bukhatir yayi yana murmushin munafurci yace “Ranka shi dad’e, barka da shigowa.”
Takawa sarki Musail yayi yana k’arasa shiga ciki yana fad’in “Bukhatir, me ya kawoka gida na? Me kake yi a nan? Dama kai ne bak’on da ya zo?”
Dhurani ne ya kalli sarki Musail yace “Shugaba me yake faruwa? Ka san shi ne dama?”
Kallon Dhurani kawai yayi bai ce komai ba ya sake matsawa kusa da Bikhatir, a kausashe yace “Me ya kawoka nan Bukhatir?”
A ladabce dan ya samu abinda ya ke so ya sunkuyar da kai yace “…
*Kuyi hak’uri da wannan, na so ya fi haka wallahi.*
*Alhamdulillah*
GIPHY App Key not set. Please check settings