Advertisement
*20*
Mik’ewa yayi tsaye yana neman kamo hannayenta yace “Kwantar da hankalinki gimbiya, ki ban lokaci kad’an zan tabbatar miki da haka.”
Girgiza kai tayi kamar zata fashe da kuka tace “Yallab’ai ni kawai ina so na koma rayuwata ta baya, wannan labaran da kuke bani zasu iya saka zuciyata tarwatsewa, ta ya mahaifin daya kawoni duniya kamar yanda kuka fad’a kuma zai nemi kasheni?”
A nutse yana tsare fuskarta da ido yace “Saboda ci gaban mulkinshi ne, gimbiya Zafeera tarihin magabata ya nuna ke ce zaki kawo sauyi a k’asar nan baki d’aya, ba kuma zaki kawo wannan sauyin ba har sai mahaifinki baya kan karagar mulkinshi, to da haka ki fad’a min ta ya zai barki bayan ya tabbatar zaki kawo k’arshen mulkinsa?”
Dafe kanta tayi da hannu wasu hawaye masu zafi suka zubo kan kumatunta, cikin nutsuwa da sanyayyar murya tace” Da a ce zan kasance yar wannan sarkin da gaske kamar yanda kuke fad’a min, tabbas da na hak’ura da kawo sauyin nan dan kawar da duk wata hatsaniya tsakanin ‘ya da ubanta, da zan yi k’ok’ari na ga ran mahaifin nan bai b’ace ba bare har na taimakawa son zuciyarsa wajen yunk’urin kasheni.”
Murmushi yayi yace” Haka kike gani, shiyasa na ce ki bani d’an lokaci dan tabbatar miki.”
D’auke hannunta tayi ta kalleshi a marairaice tace” Yallab’ai zaka iya barina ni kad’ai?”
Cike da tabbaci yace” Me zai hana gimbiyata? Na barki lafiya.”
Juyawa yayi ya fita inda ta bishi da kallo har ya fice, a hankali ta lumshe idonta wasu hawayen suka sake gangaro mata, bud’e idonta tayi ta k’arasa gaban tagar ta bud’e labule, inuwar yammacin da shukokin da suka k’awata gidan yasa ta jin son kad’aicewa da kuma samun kyakyawan yanayin nan, sakin labulen tayi da sauri ta shiga takawa ta fita a d’akin.
Advertisements
Kallon fadawa da hadiman take ganin duk wanda suka had’e sai ya sunkuya ya gaisheta a yarensu na Gallois, har ta fita farfajiyar suna gaisheta, zagayawa tayi ta b’angaren hagunta ta k’arasa kusa da shukokin, wani dogon numfashi ta ja idonta a rufe sannan ta sauke numfashin tana mai bud’e idonta akan koreyan shukokin, sanyin mai d’auke da ni’imtacciyar iska sosai ya mata dad’i, rumgume hannayenta tayi tana sake sauke numfashi.
Sannu sannu ta fara shiga duniyar tunani har tayi nisa, a haka kuma tana takawa zuwa ga shukokin, saida ta d’aga k’afarta ta tsallake d’an dakalin da aka zagaye shukokin, shiga tayi ciki tana taka k’ananun ciyayin a rashin sani har ta taka mab’allin pampon dake ba wa shukokin ruwa a duk sanda lokacin ba su ruwan yayi, tana takawa sai kuwa tsinin takalminta ya dannu wasu k’ananun k’arafu na suka bud’e suka shiga feshin ruwa suna juyawa ta ko ina.
Zuwan abun bazata da kuma yanda ruwan ke fita kamar ruwan panpo na sama yasa ta zabura ta waro idonta, da sauri ta kalli k’asa dan tasan tabbas ita ce ta taka, tana ganin wurin ta sunkuya da niyyar kashewa, sai kawai ta ji daga bayanta wani bafaden yace “Ranki shi dad’e ki barshi zan kula da komai.”
Mik’ewa tayi ta fito ta shiga takawa da sauri tana tattaro rigarta tana matse dan har ta jik’e da ruwa, lokaci d’aya kuma tana mayar da gashinta baya tana matseshi shi ma.
Duk abinda ke faruwa tsaf a idonshi yana hangenta daga sashinta ta saman bene, da fari kam dariya ce ta kubce mishi, amma ganin zata koma inda ta fito tana matse kaya sai ya k’urawa duk wani namiji dake wurin ido yana son ya tabbatar da inda idonsu suke kallo, shin sun tsareta da ido sakamakon jik’ewar kayanta suna k’are mata kallo? Ko kuma dai hankalinsu na kan aikinsu kamar yanda suka saba? Saida ya ga shigewarta kad’ai sai kawai ya ji wata nutsuwa ta d’an sauko masa, ko ba komai yasan dai zata canza kayan jikinta.
A wani ikonce ya d’auke kan shi daga gurin yana had’e fuska ya mayar kan k’aramar na’urar dake hannunshi yana ta binciken abinda yake k’ara son tabbatarwa, dan shakkun da yake da akan Haman da wanda Ayam ta k’ara masa a kai yasa ya ji bai yarda da kowa ba hatta ita kan ta hukumar ta su bincike kan miyagun laifuka da hana ta’addanci.
Ko da ta koma d’aki wanka tayi gaba d’aya sai ta canza kayanta, yanzu kam riga da wando ne saidai basu da maraba da irin kayan yan Pakistan, dan har da mayafinsu su ma wanda ta rasa wa ya siyo mata kayan nan haka masu rufe jiki? K’arshe dai mayafin a kafad’unta ta daidaita ta d’orashi sannan ta fito a d’akin dan zaman haka kurum isarta yake, gashi ita ko gudu na tayi bare sauran motsa jiki.
Masu gadin dake tsaron k’ofar d’akin sarauniya wanda yau ne aka sakasu saboda alfarmar data nema gurin sarki Wudar d’in ta kalla tace “Zan iya shiga ciki?”
Jinjina kai d’aya yayi yace “Bayan shugabanmu sarki Wudar da yarima Umad, ke ce ta ukun da aka yarje mana mu barki ki shiga ciki, sai kuma jakadiyarta mai kula da ita.”
D’an murmushi tayi a hankali suka bud’e mata k’ofar ta shiga, yanda dai take da tabbacin zata sameta haka ta samu, kwance amma kuma idonta bud’e alamar ba bacci take ba, murmushi ta d’ora a fuskarta tana k’arasawa kusa da ita d fad’in “Sannu da hutawa madam.”
Zaune tayi bakin gadon daf da ita ta kamo hannunta kamar yanda tayi da safe ta rik’e jim, tsurawa fuskarta ido tayi tace “Kina da buk’atar wani abu ne?”
Kamar d’azu da safe sai kawai ta damk’e hannunta alamar e, jim Ayam tayi alamar tunani sannan tace “Abinci?”
Advertisements
Sarauniya Kossam k’ura mata ido tayi bata damk’e hannunta ba alamar a’a kenan, d’orawa tayi da fad’in “Ruwa?”
Shi ma dai shiru tayi, d’orawa tayi da “Zaki shiga toilet?”
Ganin dai ba amsa sai tayi saurin fad’in “Kin gaji da kwanciyar?”
Matsa hannunta tayi alamar e, murmushi ta fad’ad’a tace “Na gane, bara na samu wanda zai taimaka min sai mu fitar da ke waje.”
Mik’ewa tayi tace “Ina zuwa.”
Fita tayi a d’akin sai kuma tayi katarin had’ewa da wata hadimar, dakatawa tayi tace “Na ce ba, ina za’a samu kujera irin ta masu jinya?”
Jim tayi alamar tunani sai kuma tace “Ina jin akwai a d’akin ajiye kaya, da ana d’ora sarauniya a kai idan za’a kaita d’akin gashi.”
Jinjina kai tayi tace “Ok, ki kawo min.”
Jinjina kai ita ma tayi a ladabce dan dukansu an nuna musu mahimmancinta sannan tace “To ranki shi dad’e.”
Juyawa tayi zata koma ciki tace “Idan kin d’auko ki kawo min d’akin madam.”
Da mamaki tace “Madam?”
Cikin fara’a tace “E, d’akin sarauniya ba.”
Jinjina kai tayi ta wuce da sauri dan cika umarninta, komawa tayi d’akin ta shiga kiciniyar kamata, da k’yar ta tasheta tayi zaune ta gyara mata lullub’in kan ta na kayan da tasa aka d’auko da safe aka saka mata.
Tana dawowa da kujerar masu tsaron k’ofar suka hanata shiga, k’wank’wasa d’akin sukayi Ayam ta lek’o, da kanta ta fad’a musu ita ta nemeta su kuma barta ta shiga dan ta kama mata sarauniya Kossam, suna shiga ciki suka kamata suka ciccib’a suka d’ora kan kujerar, robar ruwan dake aje Ayam ta d’auka ta d’ora kan cinyar sarauniyar sannan ta shiga turata a hankali suka fito.
Duk inda suka wuce sai an kallesu da mamaki, suna kaiwa k’ofar fita sarki Wudar da masu take masa baya zasu shigo ciki, da mamaki ya tsaya yana kallonta yace “Gimbiya ya haka?”
Kyab’e fuska tayi tace “Ta ce ta gaji da kwancin ne wuri d’aya, shiyasa zan fita da ita waje ta sha iska ita ma.”
Da mamaki sarki Wudar ya juya ya kalli waairi shi ma ya kalleshi sannan ya kalleta yace “Amma ta ya ya ta fad’a miki haka ? Ita da ba magana take ba.”
Sanyayyan murmushi tayi tace “Yallab’ai, tsawon shekaru kusan ashirin da bakwai mace na kwance babu lafiya, dan bata magana sai ku kasa fito da wata hanyar da zaku iya magana da iga dan jin damuwarta? Hakan sam bai yi ma’ana.”
Bata jira me zai ce ba kawai ta turata tare da rab’asu ta wuce suka fita, cikin dubara suka sauka a matakar k’waya d’aya dake akwai, suka sauka tayi kwana da ita inda ta nufa d’azu data fito.
A hankali saruniya Kossam ta lumshe idonta k’am, wani dogon numfashi ta ja a hancinta tare da sanyayyan k’amshin shukokin sannan ta fesoshi ta bakinta, har yanzu kuma idonta a rufe suke tana sauraren wannan danddad’an yanayin data jima bata ji irinshi ba, hatta da d’an ta Umad mai tsananin bata kulawar sai dai ya bud’e mata taga ko ya sa a bud’e da tunanin ta ga hasken rana ita ma dan k’warin ido, ko kuma ta shk’i wani iska na daban mai cike da yalwa da babu takura a ciki, amma yau ga shi wata daga zuwanta jiya yau ta fito da ita ta shak’i sabon iska mai tattare da nagartaccen oxygen.
Bud’e idonta tayi a hankali ta sauke akan shukokin duk da duhu ya fara yi, saida Ayam ta kai ta daf da wurin sannan ta dakata, zagayawa tayi ta durk’usa gabanta tana kallon wani bayyanannen farin ciki dake fuskarta tare da nuna jin dad’in fitowar ta waje, ita ma murmushi ta mata tace “Yanayin ya miki dad’i ko madam?”
Lumshe ido tayi alamar e, sake fad’ad’a murmushinta tayi tace “Da zan zauna a gidan nan da kullum na dinga fito da ke kema kina ca’za iskar shak’arki.”
Wani kallo sarauniya Kossam ta mata mai d’auke da alamar tambaya, fahimtar haka yasa Ayam fad’in “Ina son barin nan madam.”
Tsareta da ido tayi tana son tayi magana mai tsayi da ita sai dai babu baki, mik’ewa tayi tsaye ta dafa hannunta tace “Bari na d’an barki ki huta kad’an.”
B’angaren ta nufa zata koma amma lura da wani b’angare da bata san na waye ba? Kuma baya da kyalkyali kamar sauran yasa ta nufa can b’angaren, dan ko dogari babu ko d’aya a bakin k’ofar, tayi sa’a kuma k’ofar a bud’e take, tana kwank’wasa ta ji shiru sai kuma k’ofar ta d’an bud’e, a hankali ta tura ta shiga.
Falon shiru hatta da hasken fitila ma ba mai haske bane sosai, tana cikin k’arewa d’akin kallo ganin wani sassauk’an tsari dake gareshi mai birgewa, ba zato ba tsammani ta a daidai k’aramin teburin tsakiyar da taga laptop ajiye ta ji tayi tuntub’e, tuntub’e kam ba k’arami ba dan abu ne ta ji tayi karo da shi kamar mutum, hakan kuma yasa ta tafiya gaba d’ayanta ta gaba har saida ta ji ta tsallake binda ke gaban na ta sannan ta fad’i, amma kuma ikon Allah sai ta ji bata kai k’asa ba an rik’eta, kuma ko shakka ba tayi cewa mutum ne ya rik’eta.
Umad dake zaune kan sallaya gama sallarshi kenan yana tasbishi da hailala da takbiri ya ji an k’wank’wasa d’akin, da ya ji an shigo kula sai ya fara tunanin kalar tijarar da zai saukewa ko ma wane/ce hadima ce suka shigo masa d’aki bai bayar da izini ba, kafin ya ankara shi ma ya ji an tokareshi a k’ugu da k’afa sai kuma ji da yayi ana neman tausheshi daga zaune, dan haka ya fahimci ko ma wanene bai san da shi ba, da sauri ya tare mai neman fad’o masa ko dan kar su kassara dukansu.
A cikin siririn hasken suka had’a idonsu, tsaf irin rik’on nan ne ya mata na d’aukar jarirai, k’afafunta a mik’e har rigarta ta d’an ‘dage zuwa gwiwanta, hannun na hagu kam a k’ amk’ame yake kan kafad’ar Umad duk ta zaro ido saboda tsorata da tayi.
A hankali ya sauke wani tattausan numfashi ya d’an lumshe idonshi sakamakon b’oyayyan k’amshin turaranta da baya tashi sosai sai ga wanda suka samu kusanci irin haka, dan kuwa rexona ne mai sanyayyan k’amshi da dad’i.
Lura da tayi har wani k’ara tallabota yake yi a jikinshi kamar zai rumgumeta yasa ta d’an muskutawa ta kyabta idonta tace “Yallab’ai.”
Wani luuuu yayi da idonshi da sukayi mi shi wani ruwa ruwa ya k’ara k’ank’ancesu, kamar wanda baya hayyacinshi sai ya knara kusanto da fuskarshi kusan ta ta, da sauri ta d’auke hannuta a kafad’arshi ta shiga yunk’urin tashi zaune.
A d’an zabure ya janye hannayenshi daga kumkuminta ya ja baya yana mik’ewa tsaye gaba d’aya, sai kuma ya had’e fuskarshi iya had’ewa ba alamar wasa, ita ma mik’ewa tayi tsaye tana gyara rigarta cikin raha take fad’in “Sannu yallab’ai, ka gafarce ni ban kula da kai bane sam, ashe dama nan ne sashinka?”
Kawar da kan shi yayi tare da zaunawa kan kujerar ya d’ora k’afa d’aya kan d’aya, a d’an kaikaice ya kalleta fuska a gimtse yace “Me ya kawoki nan?”
Kallon salayyar daya tashi tayi, a nutse ta kalleshi ta saki murmushi, sosai shigarshi ta birgeta ya had’e cikin doguwar riga kalar ruwan toka da kuma wata k’aramar hula a kan shi kalar kayan, girgiza kai kawai tayi tace “Ba komai.”
Takawa tayi zata wuce ta tsakanin k’afafunshi da k’aramin tebur d’in, saida ta wuce sai kuma ta juyo ta kalleshi tace “Yallab’ai, wai me yasa baka sakani a addinin nan na ka ba? Akwai wani sharad’i ne na shiga? Ko kuma dai saida tarin dukiya? Ka fad’a min na ji idan zan iya mana.”
Kallonta yayi duba da ta zo da maganar da yake son yi mata tuni a kan ta, dan abun farin ciki da alfaharinshi ne a dalilinshi wani ya karb’i addinin musulunci, nuna mata gefenshi yayi alamar ta zauna, da zumud’i ta zauna tana kallon fuskarshi, a nutse cike da dattako da shan k’amshi na jinin sarauta daya gama ratsa duka sassan jikinshi ya kalleta kamar wata wacce ke bashi haushi, da k’yar ya d’aga labb’an yace “Da gaske kina son shiga?”
Jinjina kai tayi tace “E, ina so sosai.”
A hankali ya d’an jinjina kai sannan yace “Akwai sharad’i, sharad’in kuma shi ne ki tabbatar da zuciyarki kike so ba wani ne ya tilastaki ko kuma wani dalili na daban, sannan addinin musulunci addini ne da bai yarda da ka shiga yau kuma anjima ka ce zaka fita ba saboda wani dalilin, saboda haka ma har aka tanadi hukunci mai tsaurin gaske akan duk wanda yayi ridda, ma’ana ya bar addininsa da gangan.”
Cike da tabbaci tace “Na yarda da sharad’in yallab’ai, ba zan tab’a fita ba, kuma da gaba d’aya zuciyata zan shiga.”
Jinjina kai yayi ya numfasa yace “Shikenan zaki shiga ke ma, amma fa idan kin shiga akwai abubuwa dayawada zaki koyesu daga gareni, kinga kenan babu maganar tafiya gida.”
Tsam ta kalleshi da mamaki tace “Kamar ya? Hakan na nufin zan ta zama a nan kenan?”
Hararanta yayi yace “Ke kuma baki son haka ko?”
Turo baki tayi gaba tace “E gaskiya, na fi so na koma gidanmu ni ma.”
Murya k’asan mak’oshi yace “Kuma kina da dalilin zama a nan?”
Tab’e baki tayi tace “Ni dai yanzu fad’a min yanda anyi na shiga addinin nan.”
A nutse yace “Ki fad’i abinda duk na fad’a.”
Jinjina kai tayi ta k’urawa labb’ansa ido, a tsanake ya shiga furta mata kalmar shahada tana maimatawa har suka kai k’arshe, kallonta yayi da sanyayyan murmushi a fuskarta yace “Alhamdulillah, yanzu ke ma kin zama kamar ni, ma’ana kin musulunta.”
Da farin ciki ta bud’e hannaye da niyyar ta rumgume shi alamar nuna farin cikinta na zamowar silar shigarta addinin, sai kawai ya d’aga mata hannu fuska a had’e yace “Dakata, hakan da kike shirin aikatawa yanzu haramun ne a addinin ki, duk namijin da tsakaninki da shi akwai yiwuwar aure, to hakan laifi ne dan shed’an zai iya shiga tsakaninku.”
Da alamar tambaya tace “The devil?”
Jinjina mata kai yayi yace “Yes.”
Mak’ale kafad’a tayi tace “Ok, i got it.”
Gyara zama tayi tace “To yallab’ai yanzu ya zan…”
Sai kuma ta zaro ido ta mik’e da sauri tace “Ohh! Na manta na bar madam a waje.”
Juyawa tayi da gudu ta fita a d’akin inda ya bita da kallo da tambayar “Wace madam kuma?”
Mik’ewa yayi da d’an sauri ya bita dan ganin wacece kuma a wane hali ta barota d’in, hangensu a gefen flower yasa shi k’arasawa da sauri, yana zuwa da mamaki ya durk’usa ganin mahaifiyarshi sai murmushi take saki yace “Mah, ya akayi kika fito?”
Idonta ta d’aga ta kalli Ayam data mik’e tsaye ta had’e hannaye kamar wata mai tsaron lafiyarsu, d’aga kan shi yayi shi ma ya kalleta sannan ya kalli mahaifiyar ta shi yace “Mah, kin ji dad’in hakan ne?”
Wani abu da Ayam ta lura da shi shi ne d’anta Umad da ido take amsa mishi magana sab’anin ita, da ido ta ga ta amsa mi shi alamar e, murmushi ya saki ya jinjina kai sannan ya juya ya kalli Ayam a sanyaye yace “Nagode da kulawarki a kan mahaifiyata.”
Girgiza kai tayi tace “Kamar mahaifiyata take ni ma, nauyi ne a kai na.”
Kallon da suka bita da shi yasa ta jin ta tsargu, musamman ma sarauniya Kossam da ko k’yabtawa ba tayi, hakan yasa ta d’an rusuna tace “Zan barku, idan zaka tafi ka kirani sai na mayar da ita ciki.”
Da sauri ta shige b’angaren nan tana jin gabanta na bugawa haka kawai, b’angare d’aya kuma zuciyarta na son kulawa da matar.
Tana b’ace ma ganinsu sarauniya Kossam ta kalleshi tana murmushi, da ido ta masa alamar” Yarinyar.”
Sannan ta d’aga yatsunta biyu da k’yar a mugun wahalce tayi alamar” Kirki.” Ma’ana” Yarinyar kirki ce.”
Sannan ta nunashi da yatsa ta kuma nuna hanyar da Ayam ta bi sannan ta nuna yatsarta mai d’auke da zobenta na aure.
Wani irin k’walalo ido Umad yayi ya k’ura mata, a d’an rud’e yace” Mah! Kina nufin fa…?”
Sai kuma ya girgiza kai yana d’an k’ank’ance idonshi, nufinta fa ya *aureta*, ya auri Ayam take nufi? To ta ya zai fara fad’a mata ya aureta dan ya kareta? A ladabce ya mik’e tsaye ya koma bayanta kawai ya kama hannayen keken kujerar ya dinga turata zuwa ciki ba tare da yace komai ba, dan kai tsaye ba zai ce komai ba har sai ya ga abinda Allah ya yi.
*01:20*
Juye juye take a cikin baccinta tana mai fatan ta farka daga mafarkin da take na matar dake ta mata magiyar ta taimaketa, kamar daga sama ta ji an daddab’ata, a zabure ta farka tana zuba idonta akan wanda ke gabanta, ba dan fuskarshi a bud’e take ba da ba zata ganeshi ba, da mamaki tace “Yalab’ai, kai ne yanzu?”
D’ora yatsa yayi a labb’anshi yace “Shiiiii!”
Jefa mata kayan hannunshi yayi yace “Saka wannan muje.”
Da kallo ta bishi ganin ya nufi taga madadin k’ofa, zura k’afafu yayi alamar dai dirawa zai yi ta nan kuma ta nan d’in ya shigo, da sauri ta sauka daga kan gadon ta warware kayan, cikin dubara ta saka ba tare da d’ar d’ar ba dan ya juya mata baya ne, tana sakawa ta kalli kanta ta madubi, sak shigarshi da ta ta iri d’aya ce, bak’ak’en kaya na sanyi masu hula da bak’ak’en takalmi, matsawa tayi kusa da shi tace “Na shirya.”
Juyowa yayi ya kalleta, murmushi ne ya kubce mi shi ganin kayan na shi sun mata yawa amla kuma sun mata kyau, tana kallo ya sauka daga tagar amma bata ji alamar an dira ba, hannu ya zuro mata ta mik’a masa ta haura ita ma, saida ta lek’a ne ta fahimci ashe tsani ya d’ora a wurin, takawa sukayi har suka sauka tana nan kafin suka shiga ta shukoki suna sand’a har suka isa bakin babbar k’ofa.
*Ki hanzarta ki biya na ki idan baki biya ba, domin samun na ki tuntub’i wannan lambar 94-98-56-52*
_Masu buk’atar ci gaban *BADAK’ALA* ku aje hankalinku, tabbs akwai labari kuma shi ma da gaske ya faru, saidai ina so ne na ga adadin mabiya *lu’u lu’u* dan bana so na rikita kai na sannan na shiga hakk’in wanda suka biya kud’insu._
*Alhamdulillah*
GIPHY App Key not set. Please check settings