Lu’u Lu’u 21

Advertisement

*21*

 

 

 

Mai gadin dama yana d’akinshi, dan haka suka lallab’a inda Umad ya bud’e k’ofar suka fita a gidan, wani kyakyawan babur suka tarar a k’ofar, cikin salo da k’warewa Umad ya hau tare da saka hular kwano sannan ya mik’o mata ita ma, karb’a tayi ta saka kafin ta hau suka d’auki hanya.

 

A k’alla tafiyar minti talatin suka samu inda Umad kuma ya dakata a wata garage dake rufe, tana tsaye tana kallo ya bud’e k’ofar ya fito da mota k’irar benz bak’a wulik, saida ya koma ya rufe garage d’in sannan ta shiga suka kuma d’aukar hanya, awa d’aya suka share a motar nan suka isa wani k’arami kuma k’ayataccen gidan da ba zaka tab’a tsammanin wani daya tara kud’i sama da pan ko euro ko kuma dolar milyan biyar ba, dan k’arami ne sosai daidai da k’aramin ma’aikacin da buk’atar gida ba zata gaza samunsa ba.

 

Saidai a cikin gidan tsofaffi biyun ke rayuwa ko d’an aike babu, tsofaffi biyun sukan ware lokaci zuwa lokaci dan su keb’e kansu su samu lokacin farin ciki a tsakaninsu da kuma walwala ba tare da d’awainiyar al’umma ba, dan sarautar k’asar Egypt ba k’aramar sarauta ba ce kamar kowace, hatta da tsarin tafiyar da mulkin daban yake da na kowace masarauta kamar yanda tsarin shigarsu da yarensu yake daban.

 

Advertisements

Sau d’aya Umad ya buga k’ofar suka gane waye a k’ofa, tsohon ne ya k’araso cike da dattako da haiba ya bud’e, murmushi ne ya bayyana a fuskarshi sanda suka had’a ido da Umad, kaucewa yayi a hanyar alamar ya wuce sai ya rufe k’ofa, da fara’a Umad da kuma girmamawa yace “Barka.”

 

Kamar dai kowane sarki ko jinin sarauta shi ma da ido ya amsa mi shi tare da d’an murmushin gefen labb’a, kallon fuskarshi Umad ya sake yi yace “Ba ni kad’ai bane, na zo muku da wata kyauta ne ta musamman.”

 

Idonshi kawai ya d’aga zuwa bayan Umad d’in dan ganin menene, a hankali Umad ya rab’a gefe dan ya bashi damar ganin wacce ke bayanshi.

 

Suna had’a ido wani yanayi na musamman ya ziyarcesu a tare, sanyayye kuma k’akk’arfan fad’uwar gaba suka samu a tare, sai dai kuma wata irin alak’a mai k’arfin gaske da suka ji ta k’ullu a tsakaninsu lokaci d’aya.

 

Ayam kasa d’auke idonta tayi ta saki baki tana kallon tsohon kamar zatayi magana, sai take jin kamar fuskarshi ta mata kama da fuskar matar da take gani a mafarkinta, dan a duk sanda tayi mafarkin matar tana tashi ta kan kasa hasasho yanayin fuskarta, amma yanzu tana ganin tsohon saita ji kamar fuskar ce.

 

Daga can k’asar zuciyarta take jin wata narkakkiyar k’aunar tsohon da bata tab’a jin tana ma wani mahaluki a duniya ba, hakan yasa ta alak’anta ko ma menene a tsakaninsu to tabbas alak’ar mai k’arfi ce wacce ta isa ta sa su gauraya su zama dunk’ulallen abu.

 

Advertisements

A hankali ta tako ta shigo d’akin idonta akan na tsohon nan, yanda shi ma yake kallonta zai tabbatar maka abu iri d’aya suke ji a jikinsu da zuk’atansu, wasu k’walla ta gani a idon tsohon sun taru suna neman zubowa, cikin wata irin muryar kuka mai tattare da shauk’i tsohon nan ya bud’i bakinshi yace “Idan har abinda nake ji a yanzu gaskiya ne, hakan na nufin yau ni ne a gaban jikanyata? ‘yar da’ yata ta haifa?”

 

Ayam kam tuni k’walla suka zubo mata suka shiga wanke mata fuska wanda ita kanta bata san dalili ba tace “Ban san asalin me nake ji ba sanda na gan ka, amma dai ina jin daban a kan ka, waye kai ? Me ye alak’ata da gidan nan? Me yasa nake jin haka dana ganka?”

 

Wani lafiyayyan murmushi ya saki ya kamo hannayenta duka biyun zuwa ciki, bin shi ta dinga yi har saida suka shiga tsakiyar falon, dan yanayin ginin gidan sak irin zubin k’irar yan Turkey aka mi shi, tsohuwar data samu zaune a kan kujera ta kwanta baya sosai jikinta lullub’e da tattausan bargo ne ya nemi haukatata.

 

Sak fuskarta take gani a tsohuwar, abu kawai daya banbanta su shi ne ita yarinya ce ita kuma tsohuwa, ita ma mik’ewa tayi da sauri tana sake k’urawa fuskarta ido, irin dai abunda suka ji a farko haka yanzu ma suka ji, da sauri ta k’araso tana kallon mai gidan na ta tace “Habibi, kamar akwai wani abu tsakaninmu da wannan ko?”

 

Jinjina mata kai yayi sannan ya juya ya kalli Umad dake bayansu a tsaye, a hankali tsohuwar ta kai hannunta wuyan Ayam ta kama sark’ar nan tana kallo, fashewa tayi da kuka ba tare data saki sark’ar ba tace” Wannan sark’ar ba zan manta ranar da waccen azzulumin ya sakawa ‘yarmu ita a wuya ba bayan ya mana barazana da rayukanmu.”

 

Da k’arfi ta jawo Ayam suka rumgume juna tsam, Ayam da bata gama fahimtar me ke faruwa ba ita ma kukanta shiga rerawa, Umad kam wuri ya samu ya zauna k’afa d’aya kan d’aya yana kallonsu, sai tsohon ne ya rabasu ya ce su zauna, zaune tsohuwar tayi daf da Ayam ta rik’e hannunta gam kamar za’a rabasu, shi tsohon gefenta ya zauna suka sakata tsakiya.

 

Kallonsu tayi dukansu tana ziraro wasu hawaye tace” Alamu sai k’ara nuna min suke Habbee da Utais ba iyayena bane na gaskiya, sai dai kuma bana so abinda ak fad’a akan mahaifina na gaskiyar ya tabbata, da haka ya faru zan so na yi ta zama a cikin rayuwar nan mai kama da mafarki.”

 

A tare tsofaffin suka d’ora hannunsu a kan ta da niyyar shafawa, amma da suka ji a tare suka d’ora sai tsohon ya janye na shi ya bar na tsohuwar, cike da kulawa da k’auna tace” Ayam hak’uri zakiyi, haka shi ne jarabawarki kin ji.”

 

Kallonta tayi tace” Ku su waye?”

 

Ajiyar zuciya tsohuwar ta sauke ta nuna kan ta tace” Ni sunana *Bilkis* sarauniyar Egypt, wannan kuma *Abdallah* sarkin k’asar Egypt, mu iyaye ne ga mahaifiyarki wacce tayi nak’udarki wato Juman, gimbiyar Egypt sarauniya kuma a Khazira.”

 

Juyawa tayi ta kalli tsohon ta rik’o hannunshi tana kuka tace” Da gaske ku d’in ku kuka haifi mahaifiyata? Da gaske ne sarauniyar Khazira ta haifeni kuma ta bayar dani ga jakdiyarta?”

 

Jinjina kai yayi yace” Tabbas gaskiya ne, duk da bamu had’u da mahaifiyarki mukayi magana baki da baki ba, amma dai abinda aka fad’a miki gaskiya, mahaifiyarki tayi hakane dan kub’utar da ke.”

 

Cikin matsancin kuka tace” To amma ce wa suke harda mahaifina ma cikin masu son kasheni, taya haka zai yiwu?”

 

Sarauniya Bilkis ce tace” Zai yiwu, musamman ga mutum irin Musail mai son kansa da zuciyarsa, babu abinda ba zai iya aikatawa ba dan ganin mulkinsa ya ci gaba da wanzuwa a doron k’asa.”

 

Kallon tsohuwar tayi tace” Kenan gaskiya ne yana son kasheni? Idan har shi ya haifeni da cikinsae yasa zai nemi kasheni?”

 

Ta k’arashe tana kallon duka dattawan, a nutse sarki Abdallah ya jawo kan ga ya d’ora a k’irjinshi ya shiga shafa kanta, a tausashe ya shiga fad’in” Shin yanzu lokacin da kike buk’atar sanin wannan ne? Me zai hana ki maida hankali kan mahaifiyarki wacce a yanzu take kurkuku a d’aure saboda ke.”

 

Da sauri ta d’ago ta kalleshi tace” Mahaifiya ta? Habb… Sarauniya?”

 

Jinjina mata kai yayi yace” Ita.”

 

A rikice ta mik’e tsaye tace” Tana ina yanzu? Me yasa take d’aure a kurkuku ? Wane laifi ta aikata?”

 

Mik’ewa Abdallah yayi ya kama hannayenta yace “Kwantar da hankalinki, babu laifin data aikata wanda ta cancanci wannan hukuncin, dama can shi ba adalin sarki bane, shiyasa yake ganin yaudara ce tayi data kub’utar dake daga sharrinsa.”

 

Sororo ta kalleshi tace “A tak’aice dai mahaifina ba mutumin kirki bane? To mahaifiyata fa? Ya zanyi ta kub’uta?”

 

Girgiza kai Abdallah yayi sai kuma yayi murmushi yana kallon fuskarta yace “Duk da kowa ya yarda ke ce mai kawo sauyi a k’asar, amma bamu san ta ina kuma yaushe ne hakan zai faru ba, da fari dai mu zuba ido mu jira mu ga e lokaci zai mana, daga nan sai mu san abun yi.”

 

Cikin fashewa da kuka tace “To amma a ce ba zamu iya cetota ba har sai abinda lokaci yayi da mu?”

 

Umad dake zaune yana ta kallonsu kamar ya samu wani kyakyawan film ne ya katseta da fad’in “Saboda shi lokaci ya fi komai adalci a rayuwa, shi ya fi yin sakamako mai kyau sannan ya hukunta kowa.”

 

Cike da tausayin kan ta ta koma kujerar ta zauna, a hankali ta d’ora kan ta a cinyar Bilkis tana shashek’ar kuka, shafa gashinta ta dinga yi tana fad’in” Kiyi hak’uri kinji, tsawon shekaru muka d’auka muna hak’uri mu ma, amma a yanzu zamu iya cewa komai ya kusa zuwa k’arshe.”

 

Kamo hannun Bilkis tayi ta rumgume shi a k’irjinta tace” Ku ma wai kun yarda ni yar baiwa ce? Wannan wace irin baiwa da zata saka kowa mararin halaka ka?”

 

Gyara zama Umad yayi ya kalli fuskarta yace” A duniya kowane d’an adam da kalar baiwar da ubangiji yake hallitarsa da ita, Allah shi ne yafi sanin daidai da kuma ba daidai ba, wani mutumin a zahirinsa k’ansk’antacce ne kuma fak’iri, amma a bad’ini ubangiji kan iya aje baiwar da babu mahalukin da ya ma ita sai shi, ko a cikin littafi mai tsarki akwai ayoyi da dama da suke fad’akar da mu girmama d’an adam ko baka san shi ba, haka ma a hadisai ingantattu akwai irin haka, k’aramin misali da zan baki shi ne akwai wani sahabin Manzon Allah (S.W.A) da Allah ya hallice da siraran k’wabri, sai wata rana yana nufo majalisar fiyayyen hallita, sai sahabai suka dinga masa dariya suna nuna k’wabrinsa, a take fiyayyen hallita ya fad’a musu cewa wannan k’wabrin da suke gani sirara kuma k’anana, sun fi *dutsen* uhud nauyi a sikeli wajen Allah, dan haka su daina raina hallitar ubangiji.”

 

D’orawa yayi da fad’in” Haka kuma akwai wani sahabin Manzon Allah (S.W.A) da Allah ya jarabce shi da shan giya, kullum ya zo majalisin annabi ya kan zo ne a buge cikin maye, hakan yasa kullum sai annabi ya sa an mishi bulala, wata rana sai sahabbai suka dinga aibatashi suna masa fad’an akan me zai sa ba zai daina ba? Suna ta aibata shi sai annabi ya dakatar da su ta hanyar fad’a mu su ya zasu taimakawa shed’an a kan d’an uwansu, su mi shi addu’a mana Allah ya shirye shi, dan shi wannan da suke gani yana son Allah manzonsa.”

 

Gyara zama yayi yace” Kinga kenan zunubin da yake aikatawa bai hana ubangiji ya wadace shi da baiwar son shi da kuma manzon sa ba, dan samun wannan soyayyar ma babbar baiwa ce wace ba kowa Allah ya yake ba wa ita ba.”

 

A nutse ya ci gaba da fad’in” Ayam manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a garesa ya fad’a mana, a cikin mutane akwai wanda da zai rantse ya ce za’ayi ruwa, to girma da darajarshi ya isa ubangiji ya tsallakar da rantsuwarshi ta hanyar kautar da shi daga yin kaffara, shiyasa babu kyau raina hallitar Allah kowace iri ce.”

 

Gyara zamanshi yayi sosai yana kallonta sanda take tashi zaune ta nutsu sosai tana saurarenshi yace “Ayam na yarda kina da baiwa ke ma, sai dai baiwarki ni a wajena a zahirance take, babbar baiwarki bata wuce canjin yare da ubangiji ya yassare miki kina yi ba, ke kan ki wani yaren baki san wane iri bane ko na wace k’asar ba, amma haka koke samun kan ki da shi a bakinki, inda aka samu matsala kuma shi ne da manyan dattab’ai suka shiga cikin lamarin baiwarki, hakan yasa aka dinga farfagandin zuwanki har maganar baiwarki ta fara zama kamar kasuwanci, da haka kuma sai mutane suka dinga yayatawa masu k’arawa na k’arawa masu ragewa suna ragewa, har aka tunbatsa baiwarki ta kai matakin da wasu suke ganin kamar zasu mayar dake waliyiyarsu, daga cikin masu nemanki dana tattauna da su burinsu kawai su had’a hannu da ke wajen hab’aka nauyin aljihunsu, ma’ana su mayar dake bokanya dan su dinga samun na kashewa.”

 

Wani dogon numfashi ya sauke ya dafe goshinshi yayi shiru alamar doguwar maganar nan tasa kan shi fara juyawa, Abdallah ne ya saki murmushi ya d’ora da fad’in” A wajensu babban malami Dhurani ma kusan haka take, malamin fada ne da mahaifinki ke matuk’ar yarda da maganar sa, saidai zan iya ce miki shi ne k’ashin bayan dake ingiza mahaifinki wajen ganin sun kasheki, dan kuwa ya san ko ba dad’e ko ba jima dole zalincinsu zai zo k’arshe, hakan yasa yake d’aya daga cikin masu son kasheki.”

 

Ajiyar zuciya sarauniya Bilkis ta sauke tace “Yarinyata, kinga tashi muje ciki ki huta, wannan labaran zasu iya tarwatsa miki tunaninki.”

 

Kallon sarauniyar Umad yayi yace “Ku tayata farin ciki, d’azun nan ta karb’i addinin musulunci ita ma.”

 

Da farin ciki suka kalleshi tare inda sarauniya ta jawota jikinta tace “Kai amma na taya ki murna, hakan yayi kyau sosai.”

 

Umad ma murmushin yayi yace “Saidai ku fara d’orata kan abubuwa muhimman dya kamata ta fara sani, dan lokaci bai bani damar sanar da ita ko da wankan daya hau kan ta ba.”

 

Mik’ewa sarauniyar tayi ta kama Ayam suka mik’e tace “Karka damu kanka da wannan, yanzun nan zan taimaka mata tayi komai.”

 

Kamata tayi suka nufi d’aki suka bar su nan zaune, suna shiga ta saketa ta nufi ban d’aki ta d’auko farin towel ta kawo mata tace “Cire kayanki zakiyi wanka ne.”

 

Cike da kasala tace “A wannan daren?”

 

Murmusawa tayi amma ba tace komai ba sai kallonta har ta cire kayan ta d’aura wannan towel d’in, hannunta ta kama suka shiga ban d’akin, wata kujerar roba mai kyau ta nuna mata ta zauna sannan ta aje mata k’aramin bokiti da ruwa a ciki masu tsarki da tsarkakewa, sakata tayi ta cire towel d’in sannan ta ce ta d’aura niyya a zuciyarta zatayi wanka na tsarki na shiga addinin musulunci sannan ta fara da kama ruwa daga k’ugunta zuwa, a haka ta taimaka mata tayi wankan tsarki sannan ta d’aure jikinta da towel suka fito.

 

*Suna* shiga ciki Umad ya sake gyara zama ya sauke numfashi ya kalli sarki Abdallah, cikin nutsuwa da son fahimtar da shi yace “Ranka shi dad’e, akwai wani abun da ban fad’a maka ba, ban san ta ya zaka fahimce ni ba.”

 

Murmushi ya masa irin na babba da yaro yana d’an girgiza kai a tsanake yace “Yarima Umad, karka damu kan ka, ka fad’i abinda kake son fad’a, ai yanzu mun zama d’aya.”

 

Sunkuyar da kai yayi k’asa yace “Magana ta gaskiya an d’aura mana aure da ita, amma fa…”

 

Kallon sarki Abdallah yayi dan ya karanci yanayin daya shiga jin hakan, amma sai ya ga fara’a ce a fuskarshi da kuma mamakin dake nuna yana son jin yaushe haka ta faru? Sake sunkuyar da kai yayi alamar jin kunya yace” Ita kan ta bata sani ba, na yi hakane dan na tabbatar da zamanta a tare dani, dan na rasa wanda zan iya yarda da shi game da lamarinta bayan su Utais, su kuma a kowane lokaci za’a iya farmakarsu har da ita kan ta.”

 

Da tsantsar farin ciki sarki Abdallah ya dafa kafad’arshi yace” Masha’Allah Umad, ka yi aiki mai kyau gaskiya, hakan ya tabbatar min zaka iya yin komai akan jinkar nan ta wa.”

 

Da mamaki kad’an a fuskarshi yace” Amma yaushe haka ta faru?”

 

Da kunya ya amsa da “A ranar dana samu had’uwa da su Utais, shi ha ba ni aurenta kuma na karb’a, bayan su da kai yanzu dana fad’a babu wanda ya sani.”

 

Jinjina kai ya sake yi yace “Hakan yayi kyau gaskiya, saidai wani hanzari ba gudu ba.”

 

Wani azababben fad’uwa ya ji gabanshi yayi da bai san dalili ba, hakan ya bashi damar k’ure sarki Abdallah da ido yana jiran ya ji me zai ce, cikin dattako sarkin ya d’ora da “Ina ga me zai hana ka fad’a mata? Dan gudun samun wata matsalar.”

 

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana jin wani sakayau a zuciyarshi kafin ya jinjina kai yace “Insha’Allah zan fad’a mata, amma ba yanzu ba, ina jiran lokacin daya dace ne.”

 

Jinjina kai yayi yace “Shikenan, amma dai ka kula, kar ka tsaya jiran lokaci kuma wani abun ya b’ullo.”

 

Murmusawa yayi a zuciyarshi yace “Hakan ma ba zai faru ba.” A zahiri kuma bai ce komai ba.

 

*Man d’umi* ta bata ta shafe jikinta da shi kafin ta mayar da kayanta suka fito, zaune suka samesu suna shan shayi suna ta murmushi alamar hira suke kuma tana musu dad’i, zaune sukayi inda Ayam ta kalli Umad cikin muryar data disashe tace “Yallab’ai yaushe zaka tafi gida? Dare fa yayi sosai, ko nan zaka kwana ne?”

 

Kallonta sukayi dukansu inda sarki Abdallah ke sakin murmushi, cike da raha da nishad’in daya jima bai samu irinsa ba yace “Ai d’aki zamu ware muku na musamman ke da shi.”

 

Zaro ido tayi sai kuma ta kawar da kan ta ta tab’e baki tace” Ka daina fad’in haka.”

 

Dariya suka saka inda sarauniya Bilkis ta jawo kanta ta d’ora a cinya tace” Rabu da shi kinji, kwanta ki huta.”

 

Sarki Abdallah ne yace” Wane hutu kuma bayan yanzu zasu koma.”

 

Da sauri Ayam ta mik’e zaune tace” Me? Yanzu kuma? Ni gaskiya babu inda zan tafi, na zo kenan kawai shi ya tafi.”

 

Satar kallonta yayi ta gefe ido lokaci d’aya kuma ya d’auke kan shi, sarki Abdallah ne yace” Kin fa san duk sanda zai zo nan to ya kan faki ido ne, jimawar ta su a nan zai karkato da hankalin mutane da dama, kuma kinsan ba kowa ya san muna nan ba.”

 

Jinjina kai tayi tace” Hakane, amma ina so na zauna da ita.”

 

A nutse yace” Zaku zauna idan da rai, amma mu yi addu’ar komai ya daidaita tukuna.”

 

Jinjina kai tayi kamar zata fashe da kuka ta kalli fuskar Ayam ta shafi kumatunta tace” Allah ya miki albarka, ki kula da kanki kinji ko.”

 

Ita ma kamar za tayi kukan ta jinjina kai alamar to, mik’ewa tayi a kasalance ganin shi ma Umad ya mik’e, rumgume juna sukyi da sarauniya sosai har da matso k’walla, da k’yar suka rabu sannan ta juya ta rumgume sarki Abdallah, daddab’a bayanta yayi yace “Ki kula da kanki.”

 

Jinjina kai tayi ta d’ago daga jikinshi ta kalli fuskarshi, dariya tayi ta jawo farin gemunsa tace “Ina son wannan.”

 

D’an dungure mata kai yayi yace “Ja’ira, gemun na wa?”

 

Dariya tayi ta d’an mak’ale a jikin sarauniya tace “To ai yayi fari ne sosai.”

 

Dariya suka saka gaba d’aya sai Umad daya murmusa yana girgiza kai dan shi ma abun ya birgeshi sosai, kallonta sarki Abdallah yayi yace “Kin san shekaru nawa ne a kai na kuwa?”

 

Da yar harara ta kalleshi tace “Zasu fi d’ari ne?”

 

Jawo hannunta sarki yayi hakan yasa ta tahowa kamar zata fad’a masa, sai kuma ya turata a k’irjin Umad yana fad’in “Kaga rabani da ita ku tafi kafin gari ya waye mu ku.”

 

Tsit sukayi suna kallon juna saboda tana fad’owa sai ya d’auka ko zata fad’i ne sai ya rik’e k’ugunta gam da hannunshi, jim sukayi suna kallon juna sai kuma ta d’an shiga k’ok’arin zamewa, da sauri ya saketa tare da juyawa yace” Saida safenku.”

 

Bai k’ara juyowa ba bare wani ya masa magana har saida ya fita, jiki a sanyaye ta bi bayanshi tana d’aga musu hannu, yana shiga motar ita ma ta bud’e ta shiga, saida suka ga tafiyarsu sun hau titi kafin suka rufe k’ofar suka koma ciki.

 

Ta yanda akayi suka zo nan ta haka suka koma gidan, saidai suna isa asuba tayi fadawa har sun tashi kowa ya fara shirin tsayawa kan aikinshi, wanda da musulmai ne da sallah suke a lokacin, ganin mutane na ta shawagi yasa Ayam rik’e hannunshi gam a matuk’ar tsorace tace “Babu ta yanda zaka barni na shiga ni kad’ai, kawai mu tafi tare ka rakani.”

 

K’ok’arin k’watar hannunshi yayi yana fad’in “Sakeni malama, sallah zan yi.”

 

“Nima ai sallar zanyi, muje idan ma kasheni za’ayi a kashemu tare.” Tayi maganar tana jan shi zuwa ciki, ba yanda ya iya haka ya dinga binta har suka taka matakalar d’aya ta tura k’ofar suka shiga dan masu tsoron k’ofar basu iso ba, falon shiru babu motsi kuma babu haske, hakan yasa shi zame hannunshi ya nuna mata hanyar yace “To wuce.”

 

Kallonshi tayi sai kula ta juya zata tafi, juyawa yayi shi ma zai fita suka ji muryar sarki Wudar yace “Daga ina kuke yarima?”

 

Cak ya tsaya ya rufe ido alamar sam bai so haka ba, ita ma da sauri ta kalli inda ta ji sautin, zaune ya ke ya saka tv gaba saidai bata san kallo yake ba ko kuma akasin haka, gyara tsayuwarta tayi tana kallon Umad daya juyo a hankali ya kalleshi shi ma.

 

Sosa k’eyarshi yayi cikin rashin gaskiya yace “Am.. Pah, dama…”

 

Da sauri Ayam tace “Yallab’ai ai kasan ni d’in dama na saba tashi a cikin bacci, wasu lokuta ma doguwar tafiya nake yi ba’a sani na ba, yanzu ma haka ce ta faru sai dai nayi sa’a ban yi nisa ba na had’u da d’anka, shi ne ya dawo dani.”

 

Kallon Umad tayi ta yatsina fuska tace” Wannan baiwar ita tafi bani wahala kam, ina tsoron wata rana na b’ata a haka.”

 

Juyawa tayi zata haura sama tace” Saida safenku, nagodz d’an yallab’ai.”

 

Da kallo sarki Wudar ya bi ta har ta fara hawa saman, a kunyace Umad ya kalli mahaifin na shi yace” Sorry…”

 

Bai k’arasa fad’an abinda ya ke son fad’a ba ya tsaya cak, da sauri ya rab’a mahaifin na shi tare da k’arasawa gaban tvn, d’aukar remonte d’in yayi ya k’ara sauti, sunan da aka ambata wato *Ayam Utais* yasa ita kanta Ayam dake neman hayewa gaba d’aya ta dakata ta juyo ga tvn.

 

Da sauri ta shiga saukowa ta dawo suka k’urawa tvn ido, sanarwa ce ta b’atanta daga gwamnati, inda aka nuna canal Jacob da su Deeyam duk suna bayar da shaidar abinda suka sani, ba wannan ne ya d’aga musu hankali ba kamar kud’in da aka fad’a gwamnati ta sa zata bawa duk wanda ya kawo ko da labarin inda take.

 

Cikin rad’a Ayal ta matsa daf da Umad tace “Amma ai baka fad’a min gwamnati ma nema na take ba?”

 

Shi ma cikin rad’ar yace “Ni la bansan daga ina aka samu wannan kusurwar ba, ko me ye tasu manufar su kuma?”

 

Cikin rad’a tace “Ka binciko to, dan sam bana son rigima da gwamnati, saboda na tsani dokokinsu da kuma kurkuku.”

 

Juyowa sarki Wudar yayi ya kallesu yace “Me kuke tattaunawa?”

 

A tare da alamar rashin gaskiya suka amsa da “Ba komai.”

 

Jinjina kai yayi ya sauke numfashi ya kalli Ayam yace “Ba lallai mu wayi safiyar nan lafiya ba, dan jiya mahaifinki ya mana barazana kan cewa zai yak’emu.”

 

Da mamaki suka kalli juna ita da Umad kafin ta kalleshi tace “Akan wane dalili?”

 

Kallon Umad yayi sannan ya kalleta yace “Saboda ke.”

 

D’an k’ura masa ido tayi hankali tashe tace “To me ye abun yi?”

 

Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyin gaske sannan yace “Kasa bacci na yi daren yau, shiyasa kuka sameni a nan ina ta tunanin mafita, mafita kuma d’aya ce zata sa ki kub’uta daga hannun mahaifinki, sannan ki samu dalilinki na zama a nan cikin aminci.”

 

Girgiza kai tayi tace “Me ce ce wannan mafitar? Ka fad’a min ni kuma a shirye na ke inhar zata hana jinin mutanen. Da basu ji ba basu gani ba zuba.”

 

Tsakiyar idonta ya kalla tare da kawar da duk wani fargaba da tsoro sannan yace “Mafitar ita ce *ki aure ni*.”

 

Wani irin zaro ido tayi ta ja baya tana kallonshi a gurgunce, girgiza kai ta fara yi alamar sam ba zata iya ba, kai sam ba zata iya ba.

 

Umad kam wani bahagon numfashi ne ya taho masa da babu gaira babu dalili, wanda ya tabbatar da yana tsaka da cin wani abu ne da ya sark’e, a wani bala’in’en kallo ya dinga watsawa mahaifin na shi, wani abu yake d’an ji kad’an hak yana neman taso masa daga zuciyarsa a game da mahaifin na shi mai kama da jin haushi haushi da takaici takaici, sai yayi kamar zai yi magana sai kuma ya dakata, tabbas a razane yake kuma hankalinshi a mugun tashe yake, sai ya rasa dalilin samun kan shi a wannan yanayin da yayi a lokacin, shin kishin mahaifiyarsa ne yasa shi jin haka? Ko kuma dai martabar aurensa dake kan ta ne yasa ji haka a kan maganar?

 

Kallon Ayam yayi yana son jin me zai fito daga bakinta, yanda tayi sororo ta sauke idonta k’asa tana ta wainasu ya tabbatar masa da tunani take.

 

Da sauri ta d’aga kan ta ta kalli sarki Wudar ita ma da shi ma yake kallonta, cikin raunatacciyar murya tace “…

 

 

 

*Mai son samun na ta ta min magana akan wannan lambar 94-98-56-52*.

 

 

 

*Alhamdulillah*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 34

Advertisement *Page 34*   ******************** Abangaren Hafsa kuwa koda Asuba tayi taji sauk’in zazab’in da ya kafceta, a…
A BAKIN WAWA 3
Read More

A BAKIN WAWA 6

Advertisement 6 Sai 8pm suka isa, Ummusalma tayi bacci har tagaji ,gawata azababbiyar yunwa da takeji, babu abun…
IDON NAIRA
Read More

IDON NAIRA 15

Advertisement *_Arewabooks@Mamuhgee_* 15 Babu komai na abinci a gidan tunda ba kowa Dan haka sai data fita ta…
KALLABI
Read More

KALLABI 53

Advertisement BABI NA HAMSIN DA UKU Yadda ta kuma rikice mishi, ya sashi kifa kanta yana jin babu…
Read More

TARTSATSI 10

Advertisement *Page 10* *************** Umma da hafsa suka bita da kallo har ta shige daki, Hafsa Tayi hanzarin,…