Lu’u Lu’u 23

Advertisement

*23*

 

Saida suka d’auki hanya aka shaidawa sarki Musail Ayam tana hanyar zuwa, irin farin cikin daya tsinci kanshi baya misaltuwa, dan ganinshi kawai yake ya kasheta kuma ya ci gaba da mulkinshi a nutse.

A cikin k’ank’anin lokaci ya sa aka k’awata masarautar nan aka dinga shiga da fita ana shirin tarbanta kafin ta k’araso, duk da bai fad’a ba iya masarauta ne kawai, amma sai ga shi maganar har ta fita wajen masarauta mutanen gari sun fara d’auka suna yayatawa, kafin ka ce kwabo sai ga dayawa daga cikin talakawa sun fara cika k’ofar masarautar suna son ayi komai a gabansu.

Mutanen sun kasu uku ne, wasu so suke su ga yanda take kawai, shin ta kai irin kurantata da ake? Ko kula dai ba akwai nak’asu ta wani wajen? Wasu kuma har zuciyarsu suke son ganinta dan su saka mata albarka na sabon canjin da ake fad’a ita zata kawo shi, inda kaso na k’arshen kuma su yan kashe kwarkwatar idon su ne kawai, su ga da gaske ne ko kuma k’arya ce?

Tunda ta ji labarin wai Zafeera na hanyar zuwa, ta fito farfajiyar gidan ta ga an kacame sai kaye-kaye ake hankalinta ya rub’anya tashi, tambayarta bata wuce “Me yasa aka fi fifita Zafeera akan ta ba? Mutanen gari basu san ko kamanninta ba, amma daga cewa zata zo shi ne suke wani k’warya k’wayan biki? To ita me ye makomarta kenan?”

A zafafe ta juya zata koma ciki dan d’aukar wayarta ta kira wanda zai bata shawara, tana shiga falon sarki Musail ya fito cikin wani shiri da ita dai bata tab’a ganinshi haka ba, k’are mata kallo yayi cikin had’e kyakyawar fuskarshi yace” Ya ke kuma baki shirya ba? Baki san k’anwarki zata zo bane?”

Yamutsa fuska tayi tace” Sai me dan zata zo? Me ya dameni ni kuma?”

Tsaki ta ja zata wuce abinta yace” Zafreen.”

Nunata yayi da yatsa yace” Ya kamata kisan ni mahaifinki ne, ba komai ne ya fito bakinki zaki fad’a min ba, ki kiyaye gaba.”

Advertisements

Turo baki tayi gaba zata had’eshi ta wuce rai b’ace gana gunguni, saida ya ga b’acewarta ya shiga dogara sandarshi wacce tsabar alfahari yasa aka sarrafa mi shi iga da narkakken gwal, cikin takon k’asaita kamar wani d’an agwagwa ya dinga takawa yana k’arewa gyara da shirin da ake ga ma gidan.

*Giobarh*

Suna fita a gidan da sauri ya koma ciki yana danna kiran lambar Haman, cikin sa’a bugu d’aya ya d’aga, duk da hankalinshi tashe yake ta yanda gaba d’aya baya da nutsuwa, amma haka ya tattaro nutsuwarshi a dak’ile da yan tsirarun kalmomi yace “Hukumarmu tana da hannu a cikin sanarwar da ake a gidan telebijin ne?”

Cikin rashin tabbas Haman yace “Bana jin suna da hannu a ciki, saidai suna son sanin abinda ke faruwa.”

Cikin d’aurarriyar murya k’asan mak’oshi yace “Su kwantar da hankalinsu, yanzu haka tana daf da isa wajen mahaifinta.”

Da k’arfi Haman yace “Me? Kana nufin wai Khazira?”

“E.” Ya fad’a a take kuma ya kashe wayar, da kallo Haman ya bi wayar ya mik’e tsaye ya fara safa da marwa, rarako ido yayi yana tunanin inhar tana wannan babbar fada shi kam ta ya zai iya samun cikar buri sa ko kuma ya ce alk’awarin daya d’auka, ganin tunanin ba zai fisheshi ba yasa shi d’aga wayar ya danna wasu lambobi ya kira, bata jima tana kururuwa ba aka d’aga, shi ma hankali tashe ta yanda ya gagara b’oyewa a harshen larabcin parsi yace “Kinsan kuwa me ke faruwa ta wajen can? Ina ga kawai ki hak’ura da buk’atar nan ta ki, dan yanzu haka Zafeera tana hanyar zuwa Khazira dan had’uwa da sarki Musail, kinga kenan ba sai kin tiasta ni aurenta ba dan kasheta zai yi shi.”

Ita ma mik’ewa tayi daga inda take tace” Ka tabbata?”

” Na tabbata man.” Ya fad’a cike da tabbaci, cikin saurin maganarta dake samo asali lokaci zuwa lokaci tace” Kana ji d’an uwa na, ba zamuyi sake da wannan al’amarin ba, tsakanin ‘ya da uba fa sai Allah, ba lallai sarki Musail ya kasheta ba kamar yanda kowa ke hasashe, ka ci gaba da saka ido akan su dan Allah, idan har shi bai yi wani yunk’uri ba kai sai kayi.”

Iska ya furzo yace” Yar uwata, kinsan abinda da kike nema na da shi akwai hatsari sosai, idan fa akayi rashin sa’a zan iya rasa rai na bayan na rasa abokina da kuma yardarsa.”

D’an tsaki tayi tace” Ka manta da Umad dan Allah, kai dai kayi komai da taka tsantsan kawai, babu abinda zai faru da kai, kuma kar ka manta ni ma a had’arin nake, amma a k’arshe idan mukayi nasara rayuwarmu ce zaga gyaru ni da kai.”

Jinjina kai yayi yace” Shikenan, zan ci gaba da jarabawa, ki kula da kan ki.”

Advertisements

Asanyaye ita ma tace” Ka kula da kanka kai ma.”

Da haka ya kashe wayar yana ajeta gefenshi ya dafe k’ugu yana tunanin lamarin shi kam, yana yi ne dai amma a tsorace yake musamman ma Umad shi ya fi d’aga masa hankali, idan har ya fahimci manufarshi wallahi kai tsaye zai iya harbeshi da bakin bindiga ba tare da ya ji ta bakinsa ba bare ya masa uzuri.

*Wajen* Umad kuma suna gama wayar jalabiyar jikinsa ya canza ya fito rik’e da makullin motarshi, cikin hanzari ya nufi inda ake aje motocin ya shiga motarshi ya bar gidan.

Tafiyar awa uku yayi kafin ya isa bakin ruwa (Beach), kai tsaye d’akin da aka k’erashi da nagartaccen katako, yana k’wank’wasawa d’aya yayi jim bai sake ba, yan sakanni aka bud’e k’ofar, da fara’a Habbee ta matsa gefe dan ya shigo tana fad’in “Sannu da zuwa yallab’ai.”

Ba tare daya kalli fuskarta ba yace “Yana ciki ne?”

“E.” Ta fad’a tana sake kaucewa a hanyar, shigewa yayi ciki amma yayi tsai yana duba ta inda zai ga Utais d’in, Habbee data rufe k’ofar kallonshi tayi tace “Yallab’ai me za’a kawo…”

Bai bari ta dire ba yace “Yana ina ne? Ki masa magana.”

A tsanake ta kalleshi tace “Yallab’ai kamar da matsala ko?”

Waina idonshi yayi alamar ya k’agu ba wannan yake son ji ba, jinjina kai tayi ta nufi d’akin baccin na su, tana kama hannun k’ofar zata bud’e Utais na fitowa daga ciki, juyowa tayi tana fad’in “Yawwa, dama yallab’ai ne ya zo.”

Da fara’a ya k’araso kusa da inda Umad d’in ke tsaye, d’an rusunawa yayi alamar girmamawa yace “Barka da zuwa yallab’ai, zauna mana.”

Ba tare daya amsa gaisuwar ba ko kuma tayin zaman daya mi shi ya kalleshi yace “Ayam ta tafi Khazira, na yi k’ok’arin hanata amma bata hanu ba, jikina yana bani akwai matsala babba, shiyasa nake so na ji daga gareku ta ya zan shiga masarautar nan ba tare da na samu matsala ba? Sannan na fad’a muku zaku bar nan yau d’in nan.”

Kallon fuskarshi Habbee tayi da tsoro taf a fuskarta tace” Me kuma yake shirin faruwa da gimbiyarmu? Ya akayi ta yi wannan kuskuren?”

Cikin nutsuwa Utais ya kalleshi shi ma yace” Gaskiya bansan ta wata hanya da zaka iya shiga ba tare da ka samu matsala ba, dan ko masu fitar da sirrin masarauta wad’anda aka sani ne kuma suke ciki shekaru da dama.”

Dafe k’ugu yayi yana nazari sai kuma ya jinjina kai yace” Ku shirya zan wuce da ku na aje ku sai na wuce.”

A d’an d’arare Utais yace” Zuwa ina kuma yallab’ai?”

Saida ya juya zai fita yace” Zaku tafi Egypt tare da sarki Abdallah, nan ne zaku fi samun tsaro da kulawa, ina jiranku a waje.”

Kallon juna sukayi saidai babu mai bakin magana, juyawa sukayi suka shiga d’akinsu dan tattara abinda zasu iya su wuce, dan wannan karan ma ai da sauk’i tunda shi zai tafi da su, waccen had’uwar ta su ta farko da saida ya gama tsoratasu da maganar yan sanda suka fita a gidan, suna hanyarsu ta zuwa wani wurin kawai mota ta tarbi gabansu aka ce su shiga, shi ne aka kawosu nan ba tare da sanin ina suke ba saida ya zo suka ganshi kad’ai hankalinsu ya kwanta.

*Khazira*

Da k’yar mutanen dake k’ofar gidan suka gusa aka shigo da motocin, Ayam da ke cike da zulumin abinda ta gani a d’akin Umad sai ta manta da komai tana kallon mutanen suna ta rububi da tururuwar lek’a a cikin motar kamar dai wacce ta aikata wani laifi yan jarida na son jin ta bakinta, motocin na shigewa masu gadin suka gaggauta mayar da k’ofar suka rufe, hakan yasa wurin k’ara kaurewa da hayaniya da cecekucen mutane.

Daidai k’ofar shiga b’angaren suka paka motar da take ciki, daga ciki da take zaune ta kalli k’ofar, dattawa ne a k’alla su bakwai cikin shiga ta alfarma, k’arewa fuskokinsu kallo take ta ga ko zata ga mahaifinta a ciki, bata ganshi ba sai Khatar data gani wanda ba zata manta fuskarshi ba, bud’e k’ofar motar da akayi yasa ta dawowa daga hangen data tafi.

A hankali ta zuro k’afarta mai d’auke da farin takalmi k’irar shelar na mata, yanda suka ma siririyar k’afarta kyau abun sha’awa, kafin ta zuro d’ayar dattawan nan suka juya suna kallon mai fitowa, ita ma bin bayansu tayi da kallo.

Take ta ji gabanta ya tsananta fad’uwa ganin mahaifin na ta, hular kansa da sandar hannunshi, ga wata kabceciyar sark’a a wuyanshi, hannunshi dake rik’e da sandar ya mak’ala wata agogo ga zabuna kuma kaf kayan nan duk narkakken gwal ne dan nuna alfahari da k’arfin mulkinshi, kyakyawar fuskarshi take kallo, shin gyara da kulawa ne yasa yake d’an matashi? Ko kuma dai matashin ne a gaske? Dan fuskarshi babu farin gashi ko d’aya, idonshi manya masu kyau da d’aukar hankali zagaye suke cikin bak’in kwalli daya masa rau a ido, shauk’i da kuma soyayyarshi da ta ji a lokaci d’aya yasa ta k’arasa fita a motar da sauri.

Tsaye tayi tana ta had’iyar kukan dake son kubce mata tana kallonshi har ya tsaya a kan matakalar, a hankali ya sauko k’afarsa kan matakalar ta farko, sannan ya sauko d’ayar ma a matakala ta biyu har ta d’aya inda sukayi kusa sosai, a hankali ta lumshe ido take kuma hawayen suka biyo kumatunta.

Tabbas gana jin soyayyar su Utais da kuma shak’uwa na wad’anda ta fara bud’a ido ta gani a duniya, amma soyayyar wad’anda take gani yanzu sai take sake gasgata abinda ake alak’anta ta da su d’in, kallon farko data musu take jin wata bayyanannar soyayyarsu a zuciyarta, sai ta kasance mai son zama da duka iyayen na ta dan ta ji me ke faruwa a cikin rayuwar ta? Tana son tasan asalin gaskiyar komai? Dan har yanzu kanta a kulle yake game da wasu abubuwan, musamman da aka ce mahaifinta ya rufe mahaifiyarta saboda ita, to saboda me?

*Wani* murmushin mugunta ya saki wanda ya sake bayyana kyawunsa, saida ya shanye komai dake zuciyarsa da fuskarsa a lokacin ya bud’e hannayensa da fara’a akan fuskarshi yace “Gimbiyata, ashe dama zan ganki ido da ido?”

Kamar wani ne ya ingizata sai kawai ta fad’a jikinshi ta fashe da matsanancin kuka tana fad’in “Pahhhh!”

Duk da idonshi k’amas suke ba alamar hawaye, amma haka ya k’ak’aro kukan makirci ya dinga kukan k’arya yana sake k’amk’ameta a jikinshi yana daddab’ata da fad’in ” ‘Yata, nayi kewarki sosai, na kasance cikin jiranki a kowace safiya, kowace fitowar rana kowane dare, nayi kewarki sosai.”

Ita ma k’amk’ame shi tayi tace “Ban sani ba Pah, bansan komai ba, Pahhhh!”

Raba jikinshi yayi da na ta a zahirance wani mugun kallo ya mata, amma sam Ayam bata d’auki haka a matsayin wata manufa marar kyau a zuciya ba, d’an juyawa yayi ya nunawa dattawan fadarshi ita yace “Ga ‘yata, ku gaisheta.”

Dukansu sai gani tayi sun rusuna kawunansu k’asa wasu na mata kirari da mai girma yar mai girma, wasu kuma suna gaisheta a ladabce musamman ma Khatar da baya fatan ta gane shi, da mamaki take kallonsu ta d’auka ai ita ce zata gaishesu da girmamawa saboda girmansu, tana cike da wannan mamakin ta ga ya sake nuni da hannunshi yace “Ki karb’i gaisuwa daga wajen jama’arki, shekaru suka d’auka suna bauta ga sunanki.”

Juyawa tayi inda yake mata nunin, take ta bud’e baki ta sake shi da alamar mamaki tana zazzaro ido, kafatanin fadawan gidan ne da hadimai da dogarai sama da guda d’ari suka jeru a bayanta kayansu kala d’aya duk sun k’ame sun rattab’e hannaye kamar wasu gunkaye, a tare duk suka rusuna kamar sunyi ruku’i suka fad’a a tare da “Barka da zuwa gimbiyarmu.”

Ganin babu wani yunk’uri da tayi yasea sarki Musail janyota jikinshi ya kwantar da kanta a k’irjinshi, a kunne ya rad’a mata “Ki musu murmushi, sannan ki d’aga musu hannu.”

Murmushin yak’e ta musu ta d’an d’aga hannu ta musu bye bye tace “H…hhi.”

Ta gefen ido ya wurga mata wata harara jin yanda muryarta ke rawa, jinjina kai yayi ya kalli fadawan yace “Gimbiyar Khazira mai girma Zafeera ta saka muku albarka, ku je ku ci gaba da ayukanku.”

Tare suka sake rusunawa suka ce “Godiya muke shugabanmu.”

Juyowa yayi da ita a hankali tana ga jikinshi har yanzu suka nufi ciki, had’a ido ta sake yi da Khatar hakan yasa ta nunashi da siririyar yatsarta tace “Kai ne?”

Da sauri ya rank’wafa yace “Ni ne ranki shi dad’e, tuba na ke, ki gafarce ki abisa abinda ya faru.”

Ajiyar zuciya ta sauke ta kalli k’ofar shiga falon da mahaifin na ta ke neman shiga da ita, k’arewa komai kallo take tana ganin ikon Allah, lallai anyi almubazzaranci wajen kera masarutar nan, dan kud’in da aka kashe abun har ya wuce d’aukar tunanin mai hankali, sai kuma yanzu ta yarda da abinda sarki Wudar ya fad’a ce wa idan ta zo msarautarta zata gani.

A babban gurin cin abincin suka zauna, duk da ta d’anyi kalle kalle a masarautar Giobarh da gidan Bukhatir, amma kam wannan gidan ya dame wad’ancen dole ta saki ido tana kallo, har aka kawo abinci aka zuba a plate na alfarma masu tsada da k’yalli bata sani ba tana ta kallon komai da take ganin kamar da gwal aka yi shi, dan ko kujerun d’aukar ido suke kuma kalarsu kalar ruwan gwal ne, shiyasa take ta tamtama da tunanin ko gaske ne ko kuma zubin ne aka musu na gwal.

Muryarshi ta tsinta yana fad’in “Ki ci abinci gimbiya.”

Da sauri ta kalleshi sannan ta kalli sauran kujerun guda goma cas amma su biyu ne kawai, d’an kallonshi tayi a sanyaye tace “Pah! Ina Mahh?”

Fuskarshi ta ga ta fara canzawa sai kuma ya wayance yace “Ki ci abinci, zaki ganta.”

Kallonshi tayi da tunanin kenan har yanzu tana rufe? In kam hakane dole tayi wani abu a kai, ajiyar zuciya ta sauke a hankali tace “To yar uwata fa?”

Murmushin yak’e ya mata yace “Tana shiryawa ne, zata zo yanzu.”

Jinjina kai tayi ta fara cin abinci sannu sannu, tana ci tana k’iyasta kud’in da aka kashe wurin dafa abinci da kuma dad’inshi, cikin k’agauta ya sake fad’in “Ki yi sauri ki ci abinci, bayinki na jiranki zasu rakaki sashenki kiyi wanka, talakawan gari suna waje suna jiran jin wani abu daga bakinki.”

Kallonshi tayi da mamakin jin furucinshi kamar na wanda baya taula kalamansa, jinjina kai kawai ta sake yi alamar to, shi kuma kallon fuskarta yayi sanda ta kalli plate d’in gabanta, harara ya sakar mata yana k’aramar k’wafa a ranshi yake ayyana” Babu ta yanda za’a yi ki zo cikin sauk’i, na tabbata wata k’ulalliyar suka k’ula miki ki zo ki min, kafin ki aiwatar zan kasheki ni kuma, mutuwarki kuma zata zama kamar had’ari babu wanda zai tuhume ni.”

Sam mantawa yayi da maganar zuci yake har saida ya furta” Tsinanniya kawai, ki mutu ko na huta.”

Da sauri ta d’ago jin yayi magana amma ba ta ji me yace ba tace” Pah magana kake?”

Da sauri ya girgiza kai yace” A’a karki damu, idan kin kammala ki je kiyi wanka ana jiranki.”

Lura da tayi kamar a matse yake da tayi wankan yasa ta cire hannunta a abincin ta ja kujerar ta baya tace” Zamu iya tafiya?”

Hadiman dake gefensu ya kalla yace” Ku rakata zuwa b’angaren ta,ku tabbatar kun kula min da yarinya.”

Rusunawa sukayi sosai su ukun kafin su rufa mata baya d’aya a gaba, wata duniyar aljannar suka kai ta a matsayin masaukinta, nan ma lokaci ta b’ata tana k’arewa sashin kallo, d’aya daga cikin hadiman ne tace” Bari na duba ruwan da aka had’a mi idan bai huce ba.”

Zata shiga ban d’akin Ayam tayi saurin cewa” Baki ji ba.”

Tsayawa tayi ta amsa, a nutse tace” Karki saka min ruwan mai zafi.”

Jinjina kai tayi tace” To bari sai a canza.”

Ban d’akin ta shiga inda d’aya daga ciki ta mik’owa Ayam babban towel sai k’amshi yake, tana shirin kallabin data yana a kai suka ji ihun wacce ke ban d’akin nan, da gudu suka shiga su ukun dan ganin ko lafiya, ai kam daf da bahon ruwan suka ganta hannunta d’aya a cikin ruwan wutar lantarki sai janta take.

Hankali tashe Ayam tace “Ku samo mana busashen abu.”

Da gudu suka fito ita kuma tana kallonta sai kakkarwa take, saidai ina kafin su dawo har rai yayi halin sa.

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 37

Advertisement *page 37* ******************* Salma cikin farin ciki, taje ta adana kud’inta, zuciyarta fal farinciki, don ganin takeyi…
Read More

Lu’u Lu’u 29

Advertisement *29*   Kamar jiranshi ake ya koma b’angaren shi Adah ya mik’o masa wayarshi yace “Yallab’ai ana…
IDON NAIRA
Read More

IDON NAIRA 2

Advertisement *_IDON NAIRA_* _Mamuhgee_ _Arewabooks@Mamuhgee_ *_Zafafa biyar 2023_*   2 A hankali Zainab tafara girma tare da samun…
Read More

TARTSATSI 10

Advertisement *Page 10* *************** Umma da hafsa suka bita da kallo har ta shige daki, Hafsa Tayi hanzarin,…