Lu’u Lu’u 27

Advertisement

*27*

 

Waina idonta tayi tace “Mah, babu wani addini da nake cikinshi a baya, dan abinda su Mah (Habbee) ke bautawa ina ganin hakan kamar b’atan basira, a gani na ba ta yanda zan sassak’a ice da hannu na sannan na ce gareshi zan nemi biyan buk’atoci na, a k’arshe ma sai ta kai da kud’i kad’an zaka iya siyanshi a kasuwar sabah sannan ka kai cikin gidanka, sai nake ganin hakan gaskiya bai dace da mutum mai hankali da tunani ba, duk da ban rayu da su rayuwa mai tsayi ba saboda makarantar kwana dana dinga yi, amma dai a haka suna min fad’an na samawa rayuwata madogara, dan rayuwa babu addini tamkar rayuwa ne babu alk’ibla, amma kullum sai na fad’a musu zan yi idan har na samu addinin daya dace, dan kullum a jikina da kuma hangena nake samun yak’ini tabbas akwai wani buwayi gagara misali wanda ya cancanci dukanin mai rai da numfashi yayi bautarsa gareshi, and…a k’arshe dai na samu ta dalilin yallab’ai Umad, yana bautawa ubangijin daya dace, gareshi ni ma na karb’a, saidai yanayi yasa babu abinda ya koyar dani game da addinin, amma kakata ta koyar dani wankan tsarki, sannan ta fara min bayani akan rukunan musulunci guda biyar.”

Cike da farin ciki marar misaltuwa Juman ta rumgumota tace” Wow! Masha Allah, a gaskiya na ji dad’in haka sosai, sai kuma yanzu na fahimci kuskuren da na yi saboda rufewar da ido na sukayi na son ganin na ceci rayuwar ki, sam na manta da madogararki, na manta nayi tunani akan jigon rayuwarki, zan nemi gafarar ubangiji na kuskure na, sannan daga yanzu zan fara d’oraki daga inda kika tsaya.”

Cikin jin dad’i ita ma tace” Nagode Mah.”

Da sauri kuma tace” Dakata, dakata, na ji kin ce kakarki? Wace kakarki kenan?”

K’urawa fuskarta ido tayi tace” Mahaifiyarki, sarauniyar Egypt.”

Zaro ido tayi tace” Ina kika had’u da su Ayam? Iyaye na fa kika ce?”

Jinjina kai tayi tace” Yallab’ai Umad ne ya kai ni wajensu.”

Da mamaki tace” Umad? Wai me yake nema ne?”

Advertisements

Girgiza kai tayi tace” Ban sani ba ni ma Mah, amma ni yanzu babu ruwana da shi, dan yau da zan taho na shiga d’akinshi sai na samu wasu abubuwa da ke nuni da kamar wani ne ke shirya mana wani abu, ko kuma dai ana aiki a kan mu.”

Jim tayi tana tunani kafi’ daga bisani tace” To ko dai shi ma…”

Sai kuma tayi shiru, da sauri Ayam tace” Shi ma me? Mah ki fad’a min idan kinsan wani abu a kan shi.”

Girgiza kai tayi idonta na kallon k’asa tace” Um um! Ba lallai abinda nake tunani ba ya zama gaskiya.”

Cikin zumud’i tace” Duk da haka Mah fad’a min.”

Kallonta tayi tace” Kin gane ko? Zuciyata ce na ji ta raya min wasu abubuwa a game da yawan maganarsa da na ji kinyi, uwa uba kuma kika ce ya had’aki da iyayena, ina tunanin to ko dai shi ma ya shiga aiki irin na yayansa Urab ne?”

Kallon tuhuma Ayam ta mata tace” Mah, tambayarki fa nayi kuma ke ma kin tambayeni, wane aiki kenan?”

Cikin rashin tabbas tace” Jami’in sirri ne, a waccen lokacin jami’in sirri ne dake binciken manyan laifuka na k’asa.”

Jim tayi alamar tunani sai kuma ta jinjina kai tace” Lallai biri yayi kama da mutum, hakan na iya faruwa.”

Da mamaki Juman tace “Amma kum…”

Bata gama fad’a ba aka bud’e k’ofar aka shigo, Juman na jin haka ta tabbatar da sarki ne, Ayam kuma juyawa tayi da sauri, tana ganinshi ta shiga k’ok’arin sauka daga kan gadon, da fara’a ya k’araso yana fad’in “Kaga ‘ya da uwarta, ana tattaunawa?”

Murmushi Ayam tayi a ladabce ta juya ta kalli Juman data had’e fuska tace “Mah zan fita, sai anjima.”

Advertisements

Da kai ta amsa mata alamar to, sannan ta mayar da dubanta k’asa tana sake cije fuska.

Saida ya ga fitar Ayam ya haura kan gado tare da fizgo gashin Juman cikin b’acin rai yace “Me kuke tattaunawa da ita haka tsawon awa d’aya? Gulma ki ke koya mata? Ko wani abu ki ke fad’a ma ta game da ni dan ta bijire min?”

Cike da bushewar zuciya ta fizge gashinta tana fad’in “E d’in, sai me? Tsoro ka ke ji ne kar ta san wani abu a kan ka?”

Hab’arta ya rik’o ya matse yace “Ki saurare ni da kyau, ko ki fad’a ma ta ko kar ki fad’a dai mutuwa za ta yi, dan haka ki shirya ganin gawarta gabanki.”

Murmushin mugunta tayi tace “Ka jaraba ka gani mana, me ye na fad’a min idan ka yarda za ka iya kasheta d’in, ka je ka jaraba ka gani.”

Jinjina kai ya yi yace “Shikenan za ki gani.”

Ita ma jinjina kai tayi tace “Za ka gani mana in shaa Allah.”

Sakinta ya yi ya sauka daga kan gadon ya juya zai fita sai kuma ya tsaya cak ya juyo yace “In shaa Allah? Ki sani na hane ki da yin duk wani abu daya danganci addininki, daga yanzu kuma bana so na sake ji.”

Da sauri ta sauko daga kan gadon tace “Saboda me? Ka fara jiyo k’amshin sub’utar mulkinka daga hannunka ne?”

Bushewa tayi da dariya tace “To ka ji wani abu da ba ka sani ba, ita kan ta wannan addinin take bautawa, kuma ina mai tabbatar ma ka lokaci kad’an ya rage ka fara ganin sahu sahun masallata a farfajiyar gidan ka.”

D’aga murya ya yi yace “Ba zai yiwu ba, sam haka ba za ta faru ba Juman, idan kuma haka ta faru sai dai in bayan ba rai na.”

A hankali ta d’auke kan ta ta furta “Ai dama haka aka fad’a ma ka, komai zai faru ne bayan ba ranka d’in.”

Da azama ya yi kan ta yana d’ga sandarshi da niyyar maketa, sai kuma wata zuciya ta horeshi tare da tuna mi shi Ayam, da k’arfi ya sauke hannunshi ya juya ya bud’e k’ofar da k’arfi ya fita kamar zai tashi sama.

Tana ganin fitar shi ita ma tab’e baki tayi ta gyara zaman mayafinta da kyau sannan ta fita, jakadiyar ta da hadima d’aya za su rakata tace “Ku barshi kawai, wajen ‘yata zan tafi.”

A ladabce suka amsa ma ta ita kuma ta wuce, dake ta san b’angaren sai gashi ta iso a sauk’ak’e, zaune ta samu Ayam kamar mai lissafin kud’i sai nuni take da hannaye, zaune tayi tana murmushi tace “Me ki ke yi haka?”

Murmushi tayi ita ma tace “Ba komai Mah, sannu da zuwa.”

Numfashi ta sauke kafin tace “Yawwa sannu.”

A tsanake ta kalleta tace “Yawwa Mah! Ina so ki d’ora min karatun nan daga inda kakata ta tsaya min.”

Jim tayi tana kallon fuskarta tace “Ayam, ya ki ka ga iyaye na? Suna cikin k’oshin lafiya?”

Cike da tabbaci tace “Mah suna cikin k’oshin lafiya, saidai na tabbata suna kewarki, zai fi kyau ki ware rana ki had’u da su ko da sau d’aya ne kafin waninku ya bar duniya.”

Jinjina kai tayi tace “Zan yi k’ok’arin haka In shaa Allah, ganinki ya haifar min da k’warin gwiwa.”

Da fara’a tace “Ni kuma idan za ki tafi wajensu to zan tafi tare da ke.”

Dariya tayi tace “To shikena’, yanzu mu fara karatunmu ko, dan ya kamata ki san mahaliccinki da kuma yanda zaki bauta masa.”

Daga haka suka shiga karatu ta dinga sanar da ita abinda ya kamata ta fara sani a farko.

*Giobarh*

 

Tunda suka had’u bai ce masa komai ba, yanda ya zuba masa ido tuni ya gigita tunaninshi yasa jikinshi kwasar b’ari da tunanin ya gama gano manufarshi, coffee da yasa aka kawo musu ya kasa kurb’ashi saboda baya da nutsuwa.

Ganin dai shirun ba zai fishesu ba yasa shi muskutawa yace “Umad ina saurarenka, me yake faruwa ne wai dan Allah?”

Ba tare daya daina binsa da kallon nan ba hannunshi tallabe da hab’arshi yace “Wani sabon aiki za mu shiga.”

Wata nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke yace “Haba Umad, yanzu abinda zaka fad’a kenan amma ka min shiru duk ka d’aga min hankali, ina jinka to me ye aikin?”

Gyara zamansa yayi ya d’auke hannunshi daga hab’ar ya sauke numfashi, cikin nutsuwa yasa hannu yana juya kofin dake d’auke da coffee yace “Na fad’a ma ka Ayam tana masarautar nan, kuma kafi kowa sanin had’arin hakan, shiyasa ni da kai zamu je fadar da nufin masu neman aurenta.”

Da k’arfi ya zaro ido yana kallonshi yace “Me?”

Zuba masa ido yayi amma bai ce komai ba, Haman kam firfita ya fara yi da hannunshi saboda gumin da yake ji, sai ya ke ganin kawai yasa da shirinshi akan Ayam d’in, yasan niyyarshi shi ma ta son aureta dan ya samar da farin ciki ga yar uwarsa.

Umad kuma daya gama karantar yanayinsa kuma dama tun ranar da Ayam ta fad’i abin nan akan Haman d’in ya samu shakku a kan sa, daga ranar ya fara saka ido da bincike a kan shi, yanzu haka dai zai iya cewa Haman a tafin hannunshi ya ke tsaf, kallon duk wani motsinshi yake.

Gyara zama yayi ya d’an sassauta had’ewar da ya ma fuskarshi yace “Haman na gama shirya komai, kai zaka shiga gidan a zuwan d’an kwamishin kud’i, saboda na samu labari sarki Musail na son k’ulla wata hark’alla da shi, kafin su had’u mu za mu gabatar da kanmu a zuwan masu neman auren d’aya daga cikin ‘ya’yansa.”

Da mamaki Haman yace” Dakata Umad, idan har sarki Musail na son had’uwa da kwamishinan kud’i, me zai sa mu yi kasadar zuwa gidansa kuma? Asirinmu zai tonu kuma rayuka zasu b’ace.”

Wani malalacin murmushi yayi yace” Tuni ai sarki mahaifina yayi magana da kwamishinan kud’in, ba matsala game da hakan tunda kai ne zaka je a matsayin d’ansa.”

A kid’ime yace” Me yasa sai ni to?”

Kai tsaye yace” Saboda ni akwai abinda zai kaini gidan.”

Murmushi Haman yayi yace” Idan na fahimta za ka shiga gidan nan ta hanyar d’ana tarko da ni, kana so ka samu damar yin abinda kake so a cikin gidan ta dalilin d’auke ma kowa hankali da sunan neman auren d’aya daga cikin yaranshi, hakane?”

Jinjina masa kai yayi yace” Hakane, dan haka ka shirya zuwa dare jirginmu zai sauka a Khazira.”

Zaro ido yayi yace” Zuwa dare? Da wuri haka?”

Mik’ewa yayi ya d’auki wayoyinsu guda biyu babba da k’arama da makullin mota yana fad’in” Me za’a jira kuma? Ka shirya kawai.”

Da kallo kawai Haman ya bishi har ya shige motarshi ya bar wajen parking d’in.

*Yana* isa gida kamar yanda ya saba b’angaren mahaifiyarshi ya fara nufa dan duba halin da take ciki, yana zuwa ya samu Joyran bakin k’ofar d’akin na ta tana ta rok’on masu gadin su barta ta shiga, tana ganin Umad ta gyara tsayuwarta ta shiga rera kukan k’arya tana fad’in “Yawwa d’an yar uwata, ka duba ka ga tsarin nan da aka yi, yar uwata data rage min a hanani ganinta, tunda yarinyar nan ta zo gidan nan ban sake saka yar uwata a ido ba, ka rok’esu su barni na shiga na ganta ko hankalina ya kwanta.”

Saida ya d’auke kai daga gareta ya had’e fuska sosai muryarsa ba alamar wasa sannan” Doka ce, daga ni sai mahaifina zamu ganta, idan na fitar da ita shan iska zaki iya hangota daga nesa.”

Yana gama fad’a mai tsaron ya bud’e k’ofa ya shige ya barta baki bud’e tana mamaki, dan kawai ta gama gane ta kare mata, sarki Wudae ya daina kulata, yanzu Umad d’in ma mai mata biyayya shia ya daina, duk a dalilin yarinyar nan? Juyawa tayi a fusace ta bar k’ofar d’akin da tunanin sake b’ullo da wata hanyar dan ba zata hak’ura ba.

 

*Egypt*

D’an dakatawa yayi daga danna na’urar da yake ya zubawa k’ofar ido, ganin Zeyfi ta shigo yasa ya d’auke kan shi ya mayar kan na’urar ya ci gaba da dannawa

Tana shigowa ta mayar da k’ofar ta rufe, hannu d’aya ta sa ta dafe bango d’aya hannun kuma ta sa a mad’aurin rigar dai dai k’ugunta ta warware k’ullin, cike da salon jan hankali ta cire rigar ta zubar da ita k’asa, hakan ya rage mata daga bras sai pant kalar ja da suka kamata suka mat kyau.

Duk da ba kallonta yake ba, amma ganin abinda take ta wutsiyar ido sai ya sa ya d’aga kai ya kalleta, wasu mayatattun yawu ya had’e kafin ya sake d’auke kan shi, hak’ik’a kam shi namiji ne mai buk’ata, kuma a yanzun daya gan ta a haka ta tayar masa da duk wata tsohuwar sha’awarsa daya jima bai sauke ba sakamakon rashin samun kwanciyar hankali, saidai a yanzun ma baya jin zai iya samun nutsuwar da har zai yi hak’urin ya gamsu, dan labari ya samu wai Zafeera tana wajen sarki Musail, shi da ya zuba kunnuwa yana jiran ya ji yak’i tsakanin sarki Musail da sarki Wudar, a cikin wannan tartsatsin shi kuma zai zagaya ya d’auketa ba tare da shan wata wahala ba, sai kawai ya ji wai tana can kuma babu abinda ya faru.

Ganin bai kulata ba yasa ta shiga takawa cikin kwarkwasa da kissa tana karairaya tana kashe masa ido, har saida ta hau kan gadon tana rarrafawa, k’afafunshi dake mik’e ta shiga shafawa tana sumbatarsu cike da k’warewa da son kai shi bango dan ya karb’i tayinta, d’aga jajayen idonshi yayi ya sauke kan ta, cikin dakusashiyar murya yace “Kk…e, la..fiya?”

Bata tanka masa ba saida ta zo daf da k’ugunshi ta dinga zura hannu a cikin bargon daya d’an rufa zuwa k’ugun na shi, dake gajeran wando ne jikinshi mai roba hakan ya taimaka mata wajen zura hannunta ciki, tana tab’o kayan arzikin ya d’an zabura yana fad’in “Ke wai lafiyarki k’alau, me ye haka?”

D’ago narkakkun idonta tayi cikin muryar d’aukar hankali tace “Idan baka so ka dakatar mana.”

Aje na’urar yayi yasa hannayenshi da k’arfi ya fincikota, kamar wanda zai cinyeta sai kuma ya cabki leb’enta ya had’a da na shi ya shiga tsutsa da sauri sauri, dake abinda take so ne sai kawai ta shiga biye masa suka dinga yamutsa junansu, sunyi nisa sosai suna neman gangarewa kawai k’aramar wayarshi tayi kururuwa.

Da sauri ya d’ago dan wannan kiran sarki Abdallah kad’ai ke da wannan k’arar, hakan kuma ya tabbatar masa da ya zo kenan? Zunbur ya sauka daga kanta daga shirin neman hanyar da yake wawuro wandonsa ya maida ya d’auki wayar, saida ya nutsu ya saita kanshi ya tabbatar ba za’a gane komai ba kafin ya d’aga ya rangad’a sallama tare da d’orawa da fad’in “Allah ya ja zamaninka mai martaba.”

Zeyfi data tashi zaune kallonshi take ranta b’ace tana fatan wayar nan kar ta nesanta ta da shi, sai kuwa ji tayi yace “To mai martaba, gani nan zuwa in shaa Allah.”

Da sauri ya shiga gaggautawa yayi wanka ya fito yana shiryawa Zeyfi ta sauko daga ka gadon ta d’auko doguwar rigarta ta bacci ta saka, k’arasawa tayi kusa da shi tace “Ina kuma zaka je mijina?”

Cikin b’acin rai da jin haushi yace “Ban gane ina zan je ba? Ina zamanki ne a gidan nan? Kuma ina kunnuwanki suka je lokacin da nake wayar da baki isa ki gane da wa nake yi ba?”

Kwalbar turarenshi ya d’auka ya feshe jikinshi sannan ya d’auki k’aramar hula bak’a mai kyalli ya saka, juyawa yayi zai fita ta sake fad’in” Wai ina zaka tafi cikin daren nan?”

Nunata yayi da yatsa yace” Idan kika sake min magana sai na dalla miki mari.”

K’wafa yayi ya juya ya zura wasu silipas ya bud’e d’akin ya fice, wani wawan tsaki ta ja ta cije yatsarta cike da takaici kafin ta bar d’akin.

Yana fita k’ofar gidan ya samu bak’ar mota reng rover a pake, dreban motar ne ya fito ya bud’e ma Bukhatir d’in k’ofar baya ya shiga sannan ya mayar ya rufe ya tsaya bakin mota dan ya jirasu.

Wani irin zama ne yayi a cikin motar na ladabi da girmamawa, ya kasa d’aga kan shi bare ya had’a ido da sarki Abdallah, a haka suka gaisa ya masa sannu da zuwa da tambayar “Ranka shi dad’e ai bansan kana hanya ba, da na d’aukoka da kai na daga airport.”

Murmusawa yayi cike da dattijantaka yace “Kar ka damu Bukhatir, da ina so a san zan dawo, da na kiraka a waya.”

Da giramawa ya fad’i “Hakane ranka shi dad’e, Allah ya k’ara maka lafiya da nisan kwana.”

“Ameen.” Sarki Abdallah ya fad’a yana jinjina kai a hankali, shiru motar ta d’an d’auka na wani lokaci kafin sarki Abdallah yace “Bukhatir, ka san me yasa na ta so da kai na na zo yanzu?”

Girgiza kai yayi yace “Ban sani ba mai martaba, sai dai na shiga zulumi da tunanin me ya hana sarkina zaunawa a d’akinshi na alfarma ya jira na d’an lokaci ni na sameshi.”

Jinjina kai sarki Abdallah yayi yace “Hakane, abu ne mai mahimmanci da ya shafi rayuwata, shiyasa na kasa hak’ura gari ya waye.”

Numfasawa yayi a hankali yace “Bukhatir, ka san da na had’u da ‘yar’ yata wato d’iyar Juman Zafeera?”

Da sauri ya d’ago kai ya zuba idonshi cikin na shi, amma da sauri ya sadda kan shi yana mai jin gabanshi na tsananta fad’uwa, hatta da jikinshi saida ya ji ya fara kyarma zai d’auki rawa, yanda ya kasa furta komai yasa sarki Abdallah d’ora da fad’in” Na had’u da ita, kuma na yi farin cikin haka, saidai akwai wata babbar matsala.”

Da k’yar ya bud’i bakinshi yace” Sarkina wace irin matsala kuma?”

Jim sarki Abdallah yayi sai kuma yace” Kamar yanda ka sani ne daga haihuwarta zuwa yanzu ta rayu cikin had’ari, amma ubangiji yana kareta daga sharri duk wani mai sharri, ban tab’a jin d’ar a lokacin da aka rasata ba, amma a yanzu ina jin zuciyata ta kasa samun sukuni saboda inda ta kai kanta.”

A ladabce Bukhatir yace” Ina ta kai kanta haka ranka shi dad’e?”

Shiru sarki Abdallah yayi kamar ba zai yi magana ba, can ya numfasa yace” Wajen mahaifinta, sarki Musail.”

Da sauri ya kalli sarki Abdallah duk da dai yasan da maganar, amma dan kar ya saka mishi wani shakku yasa shi fad’in” Wajen sarki Musail? Kasheta fa yake son yi?”

Jinjina kai yayi yace” Sanin haka yasa hankali na ya kasa kwanciya.”

Shi ma jinjina kai yayi tare da tunanin bari ya fad’a masa shawarar da shi kan shi ya yanke a kan ta d’in, kallonshi yayi a hankali yace” Sarki na, kwanciyar hankalinka shi ne kwanciyar hankalin duk wani dake k’asar nan, ka kwantar da hankali, ni na ma ka alk’awarin zuwa safe zan samo maka labarin yanda take ciki, daga haka kuma sai mu san abun yi, dan gaskiya zamanta a can akwai had’ari.”

A tsanake ya kalleshi yace” Ka tabbata zaka iya yi min haka Bukhatir?”

Jinjina kai yayi yace” In shaa Allah sarki, wannan alk’awari na ne a gareka.”

Jinjina kai yayi a hankali yace” Shikenan Bukhatir, na yarda da kai, ina jira na ji daga gareka.”

Da haka suka rabu ya fito a motar su kuma su ka bar unguwar yana mai jin ya fara samun nutsuwa a zuciyarshi.

 

_Ga duk wanda bai siyi *lu’u lu’u* ba ya hanzarta ya siya dan fara samun *Badak’ala* nan kusa_

 

*Alhamdulillah*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
INAYAH
Read More

INAYAH 29

Advertisement _29_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Qarfe goma da minti arbain su Umma yaganah da Inayah suka fito tana shirye cikin…
KALLABI
Read More

KALLABI 59

Advertisement BABI NA HAMSIN DA TARA “Sakarai dalla matsa min, kasan waye shi? Idan ya dawo masarautar nan…
KALLABI
Read More

KALLABI 47

Advertisement BABI NA ARBA’IN DA BAKWAI Haɗe hannun shi yayi yana kallon ta, cikin murmushi ya saka hannun…
Read More

TARTSATSI 2

Advertisement page 2* Salma tayi xurum Tayi kallon yar uwartata, cikin yan dakikan mintunan da basu gaxa biyu,…
INAYAH
Read More

INAYAH 34

Advertisement _34_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Umma Hadiza hankalinta yagama rabuwa daban daban, Tana buqatan fuskantar MAJEED akan abinda yayi na…