Lu’u Lu’u 28

Advertisement

*28*

 

Yana shiga ciki d’akinshi ya wuce kai tsaye, ganin Zeyfi bata nan yasa ya mayar da k’ofar ya rufe, dan daya sameta korar kare zai mata dan ya samu damar yin abinda ya dace, da sauri ya cire hular kanshi ya d’auki na’urar nan ya shiga rubuta sak’o ga d’aya d’an lek’en asirin shi dake gidan sarki Musail.

Bai aje na’urar ba bai kuma rintsa ba kamar yanda bai yi wani abu da zai anfane shi ba, haka ya d’auki sama da awa d’aya yana jiran ganin dawowar amsar tambayarshi, sak’on na dawowa yayi gaggawar bud’ewa ya duba, ya d’an shiga tashin hankali daga bayanan da mutumin ya bashi, saidai kuma ya ji a ranshi su ma bayanan wasu makamai ne da zai iya sake tunzura sarakunan biyu su kaure da yak’i, dan haka ya jinjina kai yana fatan wayewar gari tare da d’an kishingid’awa kafin gari ya waye.

*Zaune* yake gaban sarki Abdallah kan kujera ya sadda kanshi sosai ya nutsu, cikin ladabi da girmamawa yace “Ranka shi dad’e, kamar yanda na maka alk’awari zan samo maka bayani akan halin da take ciki.”

Jinjina kai sarki Abdallah yayi yace “Na’am, an samu wani abu ne?”

Jinjina kai yayi yace “E ranka shi dad’e, an fad’a min tana cikin k’oshin lafiya tare da mahaifiyarta, sai dai kuma a safiyar da ta zo wani abu ya faru wanda a zahirance ya yi kama da tsautsayi.”

Da mamaki sosai sarki Abdallah yace “Mahaifiyarta kuma? Kana nufin Juman?”

Gyad’a kai yayi yace “E yallab’ai.”

Da sauri yace “To ta ya? Yaushe Musail ya fito da ita daga kurkuku?”

Advertisements

Cikin ladabi yace “Jiya ne yallab’ai bayan zuwan ita Zafeera.”

Jinjina kai sarki Abdallah yayi yana murmushi a zuciyarshi yana ayyana “Kenan shi ma kwarjininta zai iya tasiri a kan shi?”

Kallon Bukhatir yayi yace “Me ya faru to?”

Cikin nutsuwa yace “A cikin d’akin da aka sauketa ne za ta shiga ban d’aki tayi wanka, kafin shigarta sai d’aya daga hadiman daya had’ata da su ta fara shiga dan tabbatar da auna ruwan kamar yanda Zafeera ta buk’ata, a tak’aice dai mai martaba sai gawar matar aka fito da ita, wai wutar lantarki ce ta ja ta har ta rasa ranta.”

Lumshe ido yayi a hankali yace” Subhanallah, Subhanallah, lallai wannan kam tsautsayi ne a zahiri, amma a bad’ini da wata manufa a kai.”

Sake kallon Bukhatir d’in yayi dake fad’in” Hakane ranka shi dad’e, shiyasa nake so na bayar da wata shawara idan har zai yiwu.”

Cike da kulawa yace” Me kuwa zai hana Bukhatir? Fad’a mana na ji, kar fa ka manta kai d’an d’an uwana ne, kuma a yanzu dai a yanda komai ke bayyana kai ne magajin wannan kujerar ta wa.”

Da sauri Bukhatir ya d’aga kai ya kalleshi ba tare daya b’oye sha’awarshi ta son mulki ba yace” Na’am ranka shi dad’e?”

Jinjina kai yayi yace” Hakane, kar ka manta da mahaifinka yana raye akwai yiwuwar shi zai gajeni, to baya raye yanzu, ni kuma bana da d’a namiji, macen kuma tana gidan mijinta, ka ga kenan kai ne magaji na na gobe.”

Wata irin ajiyar zuciya ya sauke tare da lumshe idonshi, wani sanyin dad’i ne ya ratsa zuciyarshi, farin ciki ya mamayeshi ta yanda yake ji kamar ya zumduma ihu, sarki Abdallah ne ya katse masa shauk’insa da fad’in” Ina jinka Bukhatir, me ye shawarar ta ka?”

Cikin farin ciki da jin dad’i yace” Ranka shi dad’e, a gani na rayuwar Zafeera ta na cikin had’ari, bai kamata mu sake yin shiru ba a karo na biyu, sarauniya Juman ‘yarka ce, amma azzalumin sarkin nan ya rabaka da ita ba dan ya fi k’arfinka ba, a gani na yanzu Zafeera ba yarinya ce da ya kamata mu sa ido ita ma har ya ga bayanta ba, a gani na me zai hana mu tunkareshi a wannan karon, ko ba komai zamu karya alk’adarinshi na jin cewa ya fi k’arfinmu.”

Tunda ya fara magana yake saurarenshi yana jinjina kai, saida ya dasa aya ya sauke numfashi sannan yace” Na ji abinda ka fad’a Bukhatir, amma ka bani lokaci zan yi shawara, abinda na yanke a kai zan nemeka.”

Advertisements

Rusunawa yayi yace” Godiya nake ranka shi dad’e, sai na ji daga gareka.”

Jinjina kai kawai yayi bai ce komai ba, mik’ewa yayi a ladabce yace” Na barka lafiya sarki na, a huta lafiya.”

Sake jinjina kai yayi yana kallo har ya fita daga falon bak’in na shi, a take ya tsunduma kogin tunani akan shawarar Bukhatir d’in.

 

*Khazira*

 

A wajen su Ayam lokaci mai tsayi suka d’auka suna karatu, Juman ce kad’ai ta tsagaita saboda lokacin sallah zuhur, tana duba agogo ta kalli Ayam tace “Yanzu tashi mu yi sallah, ba laifi mun sha karatu, fatana dai idan mu ka idar ki fad’a min ko da rabin abinda na sanar da ke ne.”

Jinjina kai tayi tana murmushi sannan suka mik’e, ban d’akin Ayam d’in suka shiga tare, tsayawa Juman tayi bakin k’ofa tace “Ki fara d’aura alwalar na gani komai yayi daidai.”

Da “To.” Ta amsa ta cire kallabinta data yana ta fara da wanke hannayenta da bismillah, a tsanake take kallonta tana gabatar da komai yanda ta koyar da ita, amma abun mamaki sai ga shi Ayam tayi komai yanda ta koya mata, za ma ka rantse da Allah ita ce ke koya mata, saboda yanda take wanke komai da kyau har zuwa inda aka ce d’in, ba wannan ya fi bata mamaki ba saida ta ga ta idar ta mik’e tsaye ta karanta addu’ar da ake karantawa bayan idar da alwalar ta d’aga hannu ta furta.

_”Ashhadu an la’ilaha illallah-wahdahu la sharika lahu-wa ashhadu anna Muhammad rasulillah.”_

_”Allahuma-ja’alni mina-tawwabina-waja’alni minalmutad’ahirina.”_
_”Subhanaka-lahuma wa bi hamdika, ashhadu an la’ilaha illa anta, astagfiruka wa atubu ilaikh.”_

Tana juyowa suka had’a ido ta mata murmushi tace” Mah na yi komai daidai?”

Da farin ciki tace” Ayam, ai daidan ma mak’ura ki ka yi, ta ya ki ka iya rik’e komai da na fad’a miki lokaci guda haka?”

Numfashi ta sauke tace” Mah, idan har akwai wata baiwa dana yarda ina da ita, to wannan ce ubangiji ya bani, a iya sani na ba’a tab’a maimaita min abu sau biyu ba.”

Dariya tayi ta jin dad’i sannan tace” Na ji dad’in haka, saboda haka ma zan had’aki da malami ku fara karatu daga daren yau, kafin nan da d’an lokaci ke ma ki fara koyarwa.”

Dariya tayi ita har hak’oranta suka fito waje kafin ta nufi wajen gado ita kuma ta k’arasa shiga ban d’akin dan yin alwalar ita ma.

Tana idar da alwalar ta fito ta samu Ayam zaune tana jiranta, ganinta yasa ta mik’e tana gyara kallabinta, kallonta tayi da kyau tace “Mu je d’akina sai na baki hijab ki saka, kafin jibi ke ma zan sa a kawo miki.”

Da “To.” Ta amsa suka fita a d’akin na Ayam suka nufi d’akin Juman d’in, hanyar da Juman ta biyo d’azu suka sake bi ta nan, a daidai corridorn da ba’a cika bi ba suka samu hadimai guda biyu suna sallah duk sun yane kawunansu da kallabin, yanda basuyi tsammanin zuwan wani ba a lokacin yasa da k’arfi suka juyo a tare sun ma manta da sallah suke.

Da sauri Juman ta musu alama da hannu tace “Ku ci gaba.”

Durk’usawa sukayi k’asa kawunansu sadde suna sauke ajiyar zuciya, ko ba komai sun san zasu tsira da rayukansu, tunda ita kan ta a b’oye take sallah a sanin da suka mata.

Da mamaki Ayam tace “Ku kuma me ye haka? Kuna ganawa da wanda ya hallici ita kanta uwae gijiyar ta ku, shi ne zaku wani tsaya rusuna mata?”

Murmushi Juman tayi jin abinda Ayam d’in ta fad’a tace “Ba wai gaisheni suka tsaya yi ba, sun tsorata ne saboda basu san wa ke tahowa ba.”

Da sabon mamaki tace “Kamar ya? Tsoro kuma a cikin bautawa ubangiji?”

Jinjina kai tayi ta kama hannunta suka nufi d’aki tana fad’in “Saboda a nan ba’a barin musulmi yayi ibadarsa yanda ya dace.”

Cak ta tsaya tare da d’an murza hannunta dake cikin hannun Juman har tayi nasarar raba hannayensu, idonta ne suka d’auki launi ja tsabar b’acin rai da takaici tace “Mah, idan sarki ba musulmi bane, me zai sa ya hana talakawanshi ‘yancinsu? Wannan ai tauye’ yanci ne ko a dokar k’asar nan, bare kuma a addinance.”

Girgiza kai tayi tace “A gaskiya Mah ba zan juri ganin haka ba, yanda kowane mai ji yana da addini yake bautarsa babu takura, ban ga dalilin da zai sa musulmi ma yayi bauta da takura ba, dan haka duka wani mai kad’aita Allah dake cikin gidan nan ya fito zamuyi sallah tare.”

Juyawa tayi da sauri ta kalli hadiman tace” Duk wanda kuka san addininmu d’aya da shi ku tara mana su a farfajiya.”

Da sauri Juman tace” A’a Ayam, kar ki fara da abinda zai saka rayuwarki a had’ari.”

Murmushi tayi tana kallonta tace” Mah, tun fa cikina na gudan tsoka nake cikin had’ari, bana jin kiramin had’ari a yanzu zai iya tsorata ni, dan da shi na girma.”

Bin bayan hadiman tayi da suka fita haka Juman ta bi bayanta jiki a mace tana mai k’arfafa zuciyarta cewa ba zata barta ita kad’ai ba.

Tsaye tayi farfajiyar ita da Juman yayin da hadiman maza da mata suka dinga b’ullowa daga kusurwa daban daban, cikin k’ank’anin lokaci sai ga hadimai gabanta guda goma sha takwas, kallonsu tayi da kyau tace “Dukanku kuna da alwala?”

Da “E ranki shi dad’e.” Suka amsa mata, jinjina kai tayi ta kalli wasu dogarai biyu maza tace “Ku samo mana babban carpet.”

Da gudu suka juya suka nufi wani b’angare, jim kad’an suka dawo sun d’auko babban carpet guda sun tallabo, suna zuwa suka bud’eshi aka shinfid’a a nan, duba taron mutanen tayi da suke kallon ikon Allah har yanzu suna tambayar kawunansu me zai faru tace” A cikinku wa zai ja mu sallah azahar?”

Kowa zaro ido yayi suka shiga kallon kallo, hakan yasa babu wanda yayi jarumtar nuna kanshi saboda tsoron me zai biyo baya, numfashi ta sauke ta kalli mazan dake gefe d’aya tace” Dukanku babu mai jarumtar da zai iya ne? Ko kuma mahaliccin na ku ne baku iya ganawa da shi ba?”

Shiru wurin ya d’auka sai kawuna da suka sadda k’asa, d’orawa tayi da” In dai har taron maza kamar ku za’a rasa wanda zai jagoranci dayawa zuwa ga ubangijin talikai, to ina ganin dukaninmu babu anfanin rayuwarmu, dan ni dai a wuri mutuwa da kima ya fi rayuwa da tsor.”

Shiru tayi na dak’ik’u, jim kad’an kam wani matashi d’aya daga cikin masu bawa shukoki ruwa ya d’aga hannu yace” Ni zanyi jagorancin gimbiya, ko da hakan zai sa na rasa raina.”

Da jin dad’i sosai ta kalleshi tace” Addininmu bai yarda mu jefa rayuwarmu had’ari ba, amma wajen kare mutumci, addininmu, dukiyarmu, iyalinmu, addini ya bamu dama mu yi komai, dan haka mu daina b’oye addininmu alhalin wanda basa da addinin ma suke bayyana na su.”

Ai kam gaba ya shiga inda dukan hadiman suka shiga daidaita sahunsu, mazan na gaba sai kuma tazarar da aka saka tsakaninsu da mata ta kusan k’afa shida zuwa bakwai, sallah suka fara a nutse inda duka matan kalluban kansu ne suka yane kansu da shi.

Sannu sannu hadimai da sauran dogaran gidan suka fara taruwa kallonsu, al’ajabi suke na ganin sabon abun, dan wasu basu tab’a gani ba ko da a b’oyen, saidai babu wanda yake jin zai iya tambayar wye silar wannan taro, dan kuwa kowa yasan bak’uwarsu ce, tunda haka bata tab’a faruwa ba har sarauniyarsu bata da wannan k’arfin halin.

Raka’arsu ta k’arshe ce sarki Musail ya fito daga k’ofarda zata sadashi da fadarshi, ganin wannan taro yasa shi tsayawa yana kallonsu, hankalinshi tashe yake kallonsu yana zazzare ido, bubbuga sandarshi ya dinga yi ya rasa me ma zai fad’a, musamman jin yanda gidan yayi shiru, su kuma masu sallar suka duk’ar da kawunansu ka rantse basa numfashi tsabar girmamawa, lallai ya tabbatar wanda suke bauta a gareshi na da mahimmanci a garesu, suna girmamashi kuma suna jin kunyarshi tare da k’ask’antar da kansu zuwa gareshi.

Juyawa yayi ya kalli sarki yak’i Adah dake bayanshi yace “Ka taho min da gimbiya Zafeera idan sun gama.”

Da sauri ya juya ya nufi shiga fadar, da mamaki Adah ya kalleshi yace “Idan ma ta gama ya ce? Lallai yarinyar nan barazana ce barinta a raye.”

Gyara tsayuwarshi yayi dan ya jirata kamar yanda ya ce, ya kai minti biyar a tsaye kafin ya ga sun fara tashi suna barin wuri ya k’arasa, a ladabce ya tsaya kusa da ita yace “Ranki shi dad’e gimbiya, mai martaba sarki na yana son ganinki yanzu yanzu?”

Jinjina kai tayi ta mik’e a hankali hakan yasa Juman ma mik’ewa da sauri ta rik’e hannunta, kallon Adah tayi tace “Lafiya Adah?”

Da girmamawa yace “Lafiya lau ranki shi dad’e.”

Kallon Ayam tayi fuskarta cike da damuwa tace “Ina jin tsoro Ayam, ina tsoron ko ya ga abinda ya faru yanzun.”

Murmushi tayi cikin nutsuwa tace “Mah, ki kwantar da hankalinki, babu abinda zai faru da yardar Allah.”

Zage hannayenta tayi ta saka takalminta sannan ta ma Adah alama da ido su tafi, wucewa yayi gaba ita kuma ta bi bayanshi har zuwa fadar, har lokacin kuma bata daina kalle kalle ba dan har yanzu tsarin ginin masarautar na bata mamaki yanda aka k’erashi.

Suna shiga fadar ta d’ora idonta akan sarki Musail dake zaune kan wata tamfatsetsiyar kujera ta alfarma hannunshi d’auke da sandarshi d’aya hannun kuma ya dafe hannun kujerar.

Dhurani ne kawai a zaune sai Khatar a gefenshi shi ma zaune, cikin nutsuwa ta k’arasa tsakiyar kujerun nesa da sarki Musail a ladabce tace “Pah, an ce kana son gani na?”

Cikin sanyi da taushi yace “Gimbiya Zafeera wa ya baki izinin tara min talakawan cen a cikin gida har ku dinga min wani surkulle?”

Da fara’a a fuskarta tace “Pah, ba talakawan gari ba ne, dukansu hadiman cikin gidan nan ne.”

Had’e fuska yayi yace “E na gani, tambayarki na yi wa ya baku izini?”

Da fara’a dai a fuskarta tace “Pah, ai domin ganawar bawa da ubangijinsa babu buk’atar neman izinin wani, da zaren yanayi ya bayyana ga bawa na lokacin ganawa da ubangijinsa, babu wani mahaluki da ya isa ya masa shamaki da hakan, indai ba mala’ikan d’aukar rai ne ya ziyarcesa ba.”

Cikin fushi da d’aga murya yace” Shiru! Kina so ki ce min akwai wani ubangiji ne bayan abun bauta Ghira?”

A take ta amsa da” Akwai, wanda ya hallici talakawanka, ya hallice ni kuma ya hallice ka, abun bauta Ghira ba komai bane kamar yanda ba kowa bane face marar anfanin da ba zai anfani ko da kiyashi ba.”

Dhurani dake gefe yna ta hararenta jin an tab’o huruminshi yasa shi mak’ale murya yace” Gimbiya Zafeera, shi wannan abun bauta Ghira da ki ke magana a kan shi, shi ne fa yayi komai da kike gani, da izininsa komai ke faruwa, da kuma amincewarsa ke kanki kike raye a yanzu.”

Wata malalaciyar dariya ta saki ta kalleshi da kyau tace” Sai kuma gashi a gidan dana rayu babu sassak’en gunkinshi, to kenan ta ya har ya rayar da ni?”

I’ina ya fara yana rarraba ido yace” E..to..ai buwayarshi…”

D’aga mishi hannu tayi fuskarta a had’e sosai tace” Dakata, buwaya da kake magana a kai ta Allah mad’aukakin sarki ce, da kuma wannan buwayar zan buwayeku har sai mutanen garin nan sun gane gaskiya sannan sun fara bauta ga addinin daya cancanta, da sannu zan fayyace musu ku d’in hadimai ne kawai ga k’irkirarren abun bauta dan cika tunbinanku da kuma aljihanku.”

Nunashi tayi da yatsa ta d’aga girarya d’aya sama tace” Daga k’arshe kuma, kar ka kuma saka min baki yayin da nake magana da mahaifina.”

Juyawa tayi kan saeki Musail da ya ji gabanshi ya fad’i na shakkun abinda zai fad’a mata, Khatar kam da sauri yayi k’asa da kanshi yana satar kallonta, dan shi kam haka kawai take tsoratashi tun had’uwarsu a Larhjadin.

Cike da k’arfin hali sarki Musail yace “Kinga Zafeera, ba’a son sake ganin wannan taron da kika min yanzu a cikin gida na, idan ba haka ba kuma zaki tilastani na d’auki mataki a kanki.”

Sakin murmushi tayi tace “Shikenan Pah ba za’a sake ba, amma tunda ka ce a cikin gidanka ne baka so, ka ware mana waje na musamman da zamu dinga yin ibadarmu hankali kwance, ko kuma mu koma babban gida dukanmu.”

Cikin b’acin rai kamar zai cijeta yace “Ke kina lafiya kuwa? Ina fad’a kina fad’a?”

Yar dariya tayi ta girgiza kai tace “Pah, ba kana fad’a nake fad’a ba, sai bayan ka fad’a nake fad’a.”

Had’e dariyar tayi ta saka murmushi a fuskar sannan tace “Zan iya tafiya Pah?”

Wani huci ya shiga saukewa kafi ya d’aga hannu ya mata alamar ta fita kawai, dariya tayi irin ko a jikinta nan tace “Nagode.”

Saida ta kalli Khatar da kanshi ke k’asa kafin ta saki murmushi ta fice a fadar, cikin farin ciki da jin babu abinda zai faru ta samu Juman tsaye tana jiranta inda ta barta, kama hannunta tayi suka nufi b’angaren Juman d’in tana tambayarta “Me ya faru a ciki? Ya gani ko?”

Ba alamar damuwa tarz da ita tace “Ya gani, kuma babu abinda ya fad’a, zamu ci gaba da taimakon Allah.”

*Tana* fita Dhurani ya sauke numfashi ya kalli Adah daya rik’e hab’a, sarki Musail kuma saukowa yayi daga kujerarshi yana fad’in “Ina! Ta ya haka zata dinga faruwa? Ya zanyi yanzu?”

Dhurani ne ya kalleshi yace “Ai matakin kawar da ita kawai zamu d’auka ranka shi dad’e, dan in ba haka ba labarin nan ya kusa tabbata a kan mu.”

Cikin k’araji sarki Musail yace “Amma ai tun zuwanta na shirya hakan dan mutuwarta ta zama kamar had’ari, da zuwa yanzu jana’izarta muke gabatarwa.”

Khatar ne ya d’aga kai ya kalli saeki Musail d’in yace “Sarki na, ku bar min komai a hannu na, ni zanyi wannan aikin.”

A haukace Musail ya kalleshi yace “Kai da ta shigo nan kanka ke k’asa, ta ya ne zaka kashe mana ita?”

D’an murmisawa yayi yace “Mai martaba, ai *wata kokowar* (wanda bai siya ba ya siya ba, mai nemanshi ya tuntube ni, akwai cakwakiya) bata buk’atar jarumta, tunani take da buk’ata.”

Dhurani ne yace “Hakane kuma, ina ga a bashi dama ranka shi dad’e.”

Jinjina kai yayi yace “Shikenan, sai ka jaraba mu gani me zaka iya.”

Shi ma jinjina kai yayi yace “Nagode ranka shi dad’e, daga yanzu zuwa daren yau zaku ji kukan hadiman da suke tare da ita.”

Daga haka su ma zaman na su ya k’are dan abinda ke damunsu kenan, sun zauna ne da niyyar tattauna maganar ruwa da ta zo mishi da ita, amma bala’in da ta zo da shi ya girmi waccen sai ma ya mantar da su gaba d’ayansu.

 

*Alhamdulillah*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 66

Advertisement BABI NA SITTIN DA SHIDA Mikewa Gidado yayi shima ya fita, baki daya ya bar masarautan, inda…
INAYAH
Read More

INAYAH 39

Advertisement _39_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Koda garin ya waye daga ita har ‘yarta  gabaki daya jikinsu kurajen cizan sauro sun…