Lu’u Lu’u 34

Advertisement

Bismillahir rahamanir rahim_

*34*

 

Fitowa tayi daga ban d’akin ta kama wuyan hannunta ba tare data mata magana ba, zafin da ta ji a hannun na ta yasa ta dafa wuyanta, kallonta tayi kamar zata fashe da wani kukan tace “Ayam kin ji fa jikinki zafi, me yasa wai ba zaki fad’a mana wanda ya miki wannan abun ba? Ayam har fa cikin gidan mahaifinki haka ta faru.”

A sanyaye sosai cike da kasala tace “Mahhhh! Karki damu kanki mana, ba abinda kike tunani ba ne.”

Da kallon mamaki tace “Haba Ayam, ni fa na haifeki da cikina, kallo d’aya na miki nasan wani abu ya faru dake.”

Cike da gajiyawa ta d’ora kanta a kafad’ar Juman tace “Mah zaune na ke so na yi.”

Janta tayi zuwa ban d’akin tana fad’in “A’a ba zama zakiyi ba, mu je kiyi wanka.”

Shagwab’ewa tayi tace “Amma kuma Mah sanyi nake ji.”

Ba fara’a a fuskarta tace “Haka zaki hak’ura.”

Advertisements

Suna shiga ban d’akin ta nuna mata bahon wankan tace “Cire kayanki ki zauna a ciki.”

Cikin dubara ta fara aje pant d’inta da har lokacin yake mak’ale a hannunta gam, a sanyaye ta shiga zame rigar jikinta har ta cireta gaba d’aya, k’arasawa tayi ta d’an taka tudun wajen da bai kai tudun matakala ba sannan ta fara zura k’afarta ta dama.

Da sauri ta cire tana furta “Washhhh!”

Juyawa tayi ta kalli Mah data matso kusanta ta kamata, kakkare jikinta ta fara yi tana fad’in “Mah dama baki fita ba? Please ki fita ki barni, ni fa ba yarinya ba ce.”

Ba ta kula da abinda ta ce ba sai kallon k’fafunta da take tace “Shiga ki zauna min.”

Cikin d’ari d’ari ta sake zura k’afafun har ta fara k’ok’arin zaunawa a ciki, tana zaunawa ta ji wani fitsari na neman kubto mata saboda zafin da ta ji na ruwan, a firgice ta mik’e tsaye tana shirin yin magana Juman tace “Bana son wasa Ayam, zauna min a ciki.”

Cikin kuka tace “Mah zafi wallahi, k’onewa zan yi.”

Harara ta dalla mata da Ayam d’in bata tab’a tunanin zata iya yin ta ba sannan tace “Zaki zauna ko sai na jefaki da k’arfi?”

Da sauri ta rintse ido ta fara sunkuyawa a hankali har ta zauna ciki tsumdum, bakin bahon ta rik’e gam gam idonta a rufe duk da haka tana jin suna cika da hawaye, kasa zama tayi wuri d’aya haka ta dinga motsawa tana ta yan dabaru saboda rad’ad’i take ji sosai, sannu sannu kawai ta fara ji zafin ruwan na raguwa saida ta ji ta zauna daidai ba tare data motsa ba.

Lura da haka yasa Juman a dak’ile ta mik’o mata farin towel tace “Tashi ki d’aura wannan.”

Karb’a tayi ta mik’e tsaye ta d’aura sannan ta fito, wata k’aramar buta mai ruwan gold ta k’arfe ta nuna mata tace “Sake kama min ruwa a nan.”

A sangarce ta kalleta tace “Again?”

Advertisements

Ba alamar wasa tace “Yeah, zuwa safe kuma da kaina zan kaiki asibiti a tabbatar min da lafiyarki.”

Numfashi ta sauke ita dai ta duk’a dan kama ruwan, wani sabulu ta mik’o mata na ruwa na kuma tsarki tace “Ki wanke da wannan.”

Karb’a tayi ta matsa sabulun a hannunta sannan ta shiga wanke gabanta da kyau, tana idawa ta mik’e ganin Juman ta fita tana fad’in “Sai kiyi wankan tsarki.”

*Sarki Musail* na fita daga d’akin kai tsaye b’angaren masaukin bak’in ya nufa, yana zuwa daidai k’ofar d’akin ya k’wank’wasa.

Umad da fitowarsa kenan ya d’ora idonshi akan gadon, ganin bata nan ne ya firgita ya fara neman riga dan sakawa ya fita, yana tsaka da neman rigar sakawa ya ji an k’wank’wasa k’ofar, da sauri ya juya ya kalla sai kuma ya taka da niyyar zuwa ya bud’e da tunanin ko ita ce ta dawo, dalilin mantuwa ko dai ta canza shawara? Yana bud’ewa tsakninshi da mahaliccinsa ne saida ya ji fad’uwar gaba ganin sarki Musail a tsaye, sarki sarakuna mai ji da isa da k’asaita.

D’auke idonshi yayi ya mayar da duban k’asa, lura da ba tafiya zaiyi yanzu ba yasa shi rab’ewa, yanda hannayenshi ke baya duka ya goyasu cikin gadara ya fara takowa cikin d’akin, saida ya shigo Umad ya maida k’ofar ya rufe sannan ya juya yana k’arasa saka rigar dake hannunshi.

A ladabce cikin girmamawa ya kalli k’eyarsa yace “Yal’ab’ai lafiya?”

A hankali ya juyo ya sauke dubanshi akan Umad d’in, ba alamar wasa a tare da shi kamar yanda yanayinshi yayi daidai da wanda zai iya firgita mutum ya bud’a bakinsa da k’yar yace ” *Sadakin ‘yata na zo karb’a*.”

Murd’awa kayan cikinsa sukayi tare da hautsinawar da tasa ya dafe k’irji, a baibai ya kalli sarki Musail d’in yana neman k’arin bayani yace “Yallab’ai?”

A sanyaye ya dawo da hannayenshi gaba ya had’esu ya kuma tsatsareshi da ido sannan yace “Sadakin ‘yata na ce, ka manta da ka yi alk’awarin mallaka mata makullan motar da ka fi so wato Ferrari? Amma kuma har yanzu kana murzata ka manta da ba taka ba ce.”

Numfashi ya sauke kafin ya gyara tsayuwarsa yace “Na ga ka mori sadakinka, shiyasa na zo karb’an sadakin da kai na, dan nasan kai ma ka sani aurenka da *Ayam* ba nagartacce ba ne saboda dalili d’aya tak.”

Yanayin da yake kallo kamar na tsoro yasa sarki Musail yin murmushi ya sake gyara tsayiwa a gadarance yace” Dalilin shi ne a lokacin da Juman ta ba wa Habbee yarinyar nan, basuyi yarjejeniya kan ce wa idan sun samu mijin da ya dace su aura mata ba, sai gashi su sun aurar da ita babu amincewar iyayenta alhalin kuma mu na raye, dan haka a shari’ar musulunci ma auren nan bai yi ba.”

Yar dariya ya k’yalk’yala tare da fad’in” Amma ka kwantar da hankalinka, na yarda da kai ai, shiyasa ma ban kwance auren ba tun a inda aka d’aurashi ba.”

Da matsanancin mamaki Umad ya ji kanshi na neman yin bindiga yace” Yallab’ai, ta ya ka yi duk kasan wannan? Ka samu su Habbee ne?”

Bushewa yayi da wata dariya ya waro ido yana kallonshi yace” Samun su kuma? Bayan ka b’oyesu a fadar suriki na?”

Girgiza kai yayi yace” Umad! Umad! Umad, idan har zan fad’a maka abinda na sani a yanzun, to tabbas kan ka zai fashe.”

Cikin k’asaita ya maida hannayenshi bayanshi ya goyasu sannan ya kalli Umad fuska a had’e yace” Kafin ‘yata ta farka daga bacci ina son damk’ar sadakinta a hannu na, ko kuma rai yayi mugun b’aci, dan zan iya yin komai a kan ta.”

Tako d’ai d’ai ya fita a d’akin ya bar Umad da jimami, zulumi, tunani da kuma firgici mai d’auke da tsantsar mamaki, sai ma ya rasa ta inda zai fara tunanin? Ta ya haka ya faru? Ko dai tubka ya ke ta gaba ana warwara ta baya? Anya kuwa su Habbee babu alamar tambaya a kan su? Ko dai shi ma sarki Musail d’in akwai wani abu da yake b’oyewa?

Da k’yar ya k’arasa bakin gadon ya zauna, sai gashi madadin raka’a biyu daya saba yi kafin kwanciya bai tsaya yin ta ba, bai kuma d’auki na’urarsa ya fara binciken wasu abubuwa ba, sai kawai ya dinga tunani da k’walwarshi dan sai ya ji na’urar ma bai yarda da ita ba.

*Washe gari* da k’yar ta tashi tayi sallah, a haka ma dan Juman ta bata magani tasha na rage rad’ad’i da zazzab’i, tana idar da sallah ta koma ta kwanta ta ja lallausan bargo ta rufe, da kallo Juman ta bita sannan ta girgiza kai, duba agogon d’akin tayi sannan ta mik’e daga kan sallayar, wayar fax d’in dake d’akin gefen gado ta d’auka, a nutse ta shiga jera lambar wayar likitarta sannan ta aika mata kira, saida wayar tayi k’ara kamar zata tsinke sannan ta ji an d’aga, cikin girmamawa da mutumtawa suka gaisa da juna kafin ta fad’a mata tana buk’atar ganinta gida, a ladabce ta amsa mata da “Shikenan ranki shi dad’e, in sha Allah zan shigo nan da wasu mintuna.”

Jinjina kai tayi ita ma tace “Nagode, sai kin zo.”

Aje k’aramar carbin hannunta tayi mai duwatsun irge talatin da uku sannan ta cire hijabinta mai riga ta nufi ban d’aki, wanka tayi kafin ta fito ta shirya a sauk’akakk’en shiri ba kwalliya a fuska, tana kammalawa ta fita a d’akin tare da sakawa k’ofar makulli dan sam bata yarda da gidan nan ba, cire makullin tayi ta tafi da shi zuwa madafa.

Shigarta yasa duk ma’aikata kama jikinsu suka dinga gaisheta, amsawa tayi a lokaci d’aya kafin ta nufi duk inda tasan zata samu abinda take da buk’ata, wata hadimar ce tace “Ranki shi dad’e me kike da buk’ata? Ki bari sai a had’a miki.”

Girgiza kai tayi tana yatsina fuska tace “A’a ku barshi, yanzu ni bansan da wa zan yarda ba a gidan nan, tunda har a cikin nan za’a kai min abinda aka saka guba, wato na ci da ni da ‘yata ba?”

Sake girgiza kai tayi ta shiga d’aukar k’wan da take son soyawa, duk jinin jikinsu suka sha suka ci gaba da aikinsu, mai dafa abincin mai martaba na kari daban, masu shara da goge madafar daban, masu dafa abincin bak’i ma daban.

*Bacci* ya fara d’aukarta daga ta cikin ban d’aki wani da bak’ak’en kaya da rufaffiyar fuska ya hauro ta siririyar tagar dake ciki, a daidai bahon wankan ya saukar da k’afafunshi dan kar ya fad’a ciki gaba d’aya, saida ya tabbatar ya tsaya da kyau sannan ya tsallaka bahon ya sauko, a hankali ya bud’e k’ofar ya shigo d’akin, ganin Ayam dunk’ule tana bacci ya lallab’a saida ya je daf da ita, hannunshi mai d’auke da safa bak’a da wani k’aramin abu kamar reza mai kaifin gaske ya ciro, sake matsawa yayi kusa da ita sosai ya d’ora a gefen wuyanta da niyyar ya mata mummunan yankan rago.

Saidai k’ofar da aka tab’a kamar za’a shigo ne yasa ya yanki wuyanta ba daidai ba, ganin jini ya b’allo daga wuyanta ita kuma ta farka a razane tana dafe wuya tare da furta “Auch!”

Da gudu ya juya zuwa ban d’akin inda Ayam ta zuro k’fafu da niyyar sauka ta bishi, sai kuma ta ji rad’ad’in wuyanta na k’aruwa, hannu ta kai ta murza wurin lemar da ta ji yasa ta dubi hannun na ta, zaro ido tayi ganin jini ne ya wanke hannunta, da sauri ta mik’e tana sake rik’e wurin gam ta tunkari k’ofar da kai tsaye ta ji ana bubbugawa.

Murd’a k’ofar ita ma tayi amma sai ta ji a rufe, jijjiga k’ofar ta dinga yi da hannu d’aya inda d’ayan ke kan wuyanta sai neman shure shure take, a gigice sarki Musail dake bakin k’ofar yace “Wai Juman ba zaki bud’e k’ofar ba ne?”

Daga bayanshi Juman dake tahowa d’auke da farantin abincinta ta furta “Gani nan mana sarki na.”

Ta k’arashe a aladabce saboda gilmawar hadimai ta ko ina da kuma masu kula da gidan, juyawa yayi da sauri ya kalleta da mamaki, saida ta zo daf da shi cikin rad’a yace “Ina Zafeera?”

Wani wawan kallo ta masa sanda take k’ok’arin zura makullin ta hudar k’ofar tace “Tana ciki.”

Cikin rad’a ya sake cewa “Me yasa kika barta ita kad’ai?”

K’ofar data bud’e ta kuma murd’a lokaci d’aya yasa ta zuro kai tana fad’in “Saboda ba jaririyar da zan goya ba ce a baya n…”

Turus ta ja ta tsaya sanda idonta suka gane mata Ayam durk’ushe cikin jini sai kawai ta saki farantin ta druk’ushe tana kiran “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un! Ayam me ya same ki?”

Da k’arfi ya shigo shi ma ganin wannan yasa ya sunkuya yana fad’in “Zafeera? Zafeera? Lafi…”

Sai kawai ya k’arasa kusan gadon ya fara waige waige, k’ofar ban d’akin dake bud’e ya shige yana ganin taga a bud’e ya juyo da sauri, cikin hargagi ya kalli Juman da daidai shigowar likitarta yace “Ku bata kulawar da ta dace, karki kuskura ki k’ara yin nesa da ita.”

Ficewa yayi daga d’akin ba tare daya kula da komai ba, likitar na duba yankan wuyan Ayam d’in ta kalli Juman hankali tashe tace “Sarauniyata, ya kamata mu kaita asibiti, tana zubar da jini dayawa da buk’atar a ma ta d’inki.”

Mik’ewa Juman tayi tace “To me mu ke jira? Mu tafi mana.”

Kamata sukayi suka fita da ita, cikin kid’ima Juman ta kalli wani bafade tace “Ka kira mana dreba ya kai mu asibitin cikin gida.”

Da sauri bafaden yayi abinda ta umarceshi, kafin su fita k’ofar falon har drzba ya paka mota, shiga sukayi inda ya kewaye shukokin nan sannan ya zagaya ta bayan gidan tafiya ce mai d’an tsayi idan a k’afa ne, yana aje su daga cikin asibitin ma kujerar marasa lafiya aka fito da ita aka d’orata suka shige cikin asibitin da tsarin gininta yayi kamar wani k’aramin gida mai kyau.

Suna shiga kai tsaye bloc aka wuce da ita dan kula da lafiyarta.

Tunda ya shiga fadarshi ya ja baki yayi shiru yana jin maganganun fadawan na tashi sama sama, bai ce komai ba sai zuba musu ido, bai kuma nuna yana cikin tashin hankali ba, saidai yana lura da yanayin kowa da kuma son ganin wanda yake zargi d’in ya shigo.

A hargitse ya shigo fadar yana kama babbar rigarshi, da sauri sarki Musail ya gyara zamanshi ya tsura mishi ido, kujerarshi ta kusa da sarki Musail d’in ya ja ya zauna yana kallonshi bayan ya rusuna masa.

A d’an daburce Khatar ya kuma kallonshi sannan ya kalli Dhurani a b’angare d’ayan kusa da sarkin sannan yace “Ranka shi dad’e, yanzu nake samun mummunan labari a cikin gida.”

Rik’e hab’a sarki Musail yayi a dak’ile yace “Wane irin labari kuma waziri?”

A sanyaye yace “Ranka shi dad’e, gimbiya Zafeera ce aka farmaketa a d’akin sarauniya, yanzu haka sun tafi asibitin cikin gida.”

A kasalance sarki Musail yace “Kenan bata mutu ba yanzu ma? Wai wane irin mutane ake ba wa aikin nan ne?”

Kaf fadar suka dinga kallo kallo sai Dhurani daya kalli sauran fadawan da basa cikin tsarinsu yace “Zaku iya jira a waje, da alama mai martaba na cikin alhini.”

Jiki a sab’ule cike da takaici suka mik’e suka fita, wanda ya rage Khatar ne da shi Dhurani sai kuma Adah, da sauri Khatar ya kalleshi yace “Sarki na, da alama akwai mai ruguza mana tsarinmu, jiya cikin dare mutanenmu sun ziyarci d’akin gimbiya Zafeera, amma basu sameta gaba d’aya, saidai ko ma waye ya kai mata farmakin nan yanzu, bana jin d’aya ne daga cikin mutanenmu, dan har yanzu babu wanda ya tuntub’e ni da maganar.”

Da mamaki Dhurani yace” To wa ye kenan ya yi?”

Girgiza kai Khatar yayi yace” Ban sani ba gaskiya, sai dai nan gaba zamu sani.”

A k’ufule sarki Musail ya kalleshi yana ji ya shak’i wuyanshi sannan bakinshi ya furta” Kai Khatar ‘yar ta wa kake so ka kashe? Yata ta ciki na? Shin me ta tsare maka a rayuwa?”

Amma sai ya dake yace” To wane irin hwanb’asawa kake game da lamarin? Ba dan ka ce na bar maka a hannunka ba, da yanzu na shak’e wuyanta.”

Da sauri Khatar yace” A’ a yallab’ai, ai shi yasa na ce zan yi komai, kar ka d’auki matakin nan da hannunka, ina k’ok’ari a kai.”

Cikin d’aga murya yace” Wane k’ok’ari ka ke?”

Cikin ladabi yace” Yallab’ai ai jiya mun yi k’ok’arin ciyar da su guba a abinci, amma sai wani abu ya faru suka tsallake wannan tarkon…”

D’aga masa hannu yayi tarz da duk’ar da kanshi k’asa, k’afarshi dake sanye cikin takalmi masu kyau da k’yalli ya dinga buga k’afar d’aya bayan d’aya, wani huci ya fara jerawa yana saukewa, jikinshi rawa ya fara d’auka tsabar takaici da k’uluwa, d’aga kanshi yayi da sauri ya mik’e tsaye da wani irin sauri ya kama hanya ya fita tsabar haushi har k’afafunshi na hard’ewa.

Da kallo suka bishi har da Adah ma daya bi bayanshi da sauri yana hararen Khatar, kallon junansu sukayi Khatar yace “Me ya faru kuma?”

Girgiza kai Dhurani yayi yace “Ba na ce ba, ban dai fahimci komai ba, duba da ko halin da aka fad’a masa ‘yarsa na ciki bai damu ba.”

Cikin rad’a Khatar yace “Ko dai bai ji dad’i ba ne da na fad’a masa.”

Harara Dhurani ya wurgawa k’ofar kafin ya kalli Khatar yace “Rabu da shi.”

*Sarki Musail* na fita daga nan cikin sauri ya shiga takawa zuwa asibitin, da girmamawa Adah yace “Ranka shi dad’e, ka bari a d’auko mota.”

A hassale yace “Ni rago ne ? Na ce ba zan iya tafiya can d’in ba?”

Wucewa yayi kamar zai tashi sama Adah na bin shi, daf da k’ofar shiga Umad ya zagayo ta bayan asibitin shi maa kid’ime suka kacame, turus sukayi suna kallon juna sai kuma suka fara k’ok’arin shigewa.

Karo sukayi da juna hakan uasa Umad dakatawa Musail ya wuce sannan ya shige shi ma da gudu, inda suka ga Juman tsaye suka tsaya a tare suka had’a baki wajen fad’in “Ya jikin ta?”

“Ya jikin ta?” Kallon juna sukayi sai kuma suka kalli Juman da ta ja majina tace “Ban sani ba ni ma, tana ciki har yanzu basu fito ba.”

Lumshe ido yayi ya jingina a bango ya rumgume hannayenshi, k’ok’arin dakatar da zuciyarshi kawai yake akan abinda take raya masa, sam baya so ya fara d’aukan mataki sai ya ji halin da take ciki, indai har aka fito masa da gawarta yanzu, to shakka babu Zafreen ma za ta bi yar uwarta ba da jimawa ba, dan a dalilinta zai bayyana waye shi a duniya.

Tsantsar tashin hankalin shi ne rasa dalilin da yasa za ta yi haka, saboda sarauta ne? Ko kuma dai son zuciyarta? Ko kuma wani ya sakata? Girgiza kai ya fara yi a hankali idonshi a rufe yana jinjina lamarin.

Takon takalmin da suka ji a bayansu an shigo ne yasa su juyawa shi ma a nutse ya bud’e ido, zuba mata su yayi tun daga k’asan takalminta masu tsinin gaske bak’ak’e, zuwa dogon wandon jikinta daya kamata bak’i, sai rigar mai siraren hannaye ita m bak’a da gashinta data d’aure, dan kyau kam akwai shi, saidai kyan d’an maciji ne.

Sarki Musail ma kallonta yake da mamakin abinda ya kawota, idan har ta san me ya faru shi ne zata shigo haka? Ba wani alamar abun ya dameta a matsayin Zafeera na yar uwarta, girgiza kai shi ma ya d’auke kanshi daga kallonta, tana zuwa ta ja birki ta tsaya ta kalli Juman a shek’e tace “Mah, ta mutu ne?”

Wannan tambayar da tayi ita tasa kowa dake wurin kallonta, gyara tsayuwarsa yayi ya dafe k’ugu d’aya irin zai kirta rashin mutumcin nan yana kallon k’wayar idonta yace “…

 

*Alhamdulillah*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 63

Advertisement BABI NA SITTIN DA UKU Make hannun shi, tayi cike da matsanancin kunya dan sai yanzu ta…
Read More

TARTSATSI 9

Advertisement *Fage 9* ***************** Gwaggo tace “To sarakan zance akatse hirar hakanan, atashi kar ku bata mashi lokaci”…