Lu’u Lu’u 35

Advertisement

_Bismillahir rahamanir rahim_

*35*

 

Gyara tsayuwarsa yayi ya dafe k’ugu d’aya irin zai kirta rashin mutumci nan yana kallon k’wayar idonta yace “Ki zo kin ji ta mutu ne dalilin yankan da kika mata?”

Wur wur ta kalleshi tana wurga ido zuwa fa Juman da sarki Musail, k’are masa kallo tayi ta rik’e wayarta da kyau tace “Me kake fad’a ne haka?”

Rai b’ace ya girgiza kai tare da tab’a ta ya koma d’aya b’angaren ya tsaya, dan in takura kanshi wajen yin magana, to shakka babu kasheta zaiyi da marin da ba lallai ta rayu ba, idan kuma ta rayu ba zata rasa kamuwa da matsalar ji ba.

Juman dake ta kallon Zafreen d’in ce ta girgiza kai tace “Akane Zafreen? Yar uwarki ce fa.”

Wani mugun kallo ta mata kafin ta d’auke kan ta zuwa ga k’ofar da aka bud’e, a hankali aka turo gadon da take kwance a kai an mata allurar bacci da kashe zafin jiki kafin aka mat d’inki a wurin.

Duk rufa sukayi kan su har aka fito da ita gaba d’aya, kallonsu likitar tayi tace “Ba ta cikin had’ari yanzu, idan ta samu hutu zata wartsake.”

Dafe k’irji Juman tayi tace “Alhamdulillah.”

Advertisements

Turata aka yi zuwa d’akin hutu inda Juman ta bi bayansu, saida suka shige d’akin Zafreen ma ta juya a fusace ta bar wurin takalminta na k’ara, ita ma tana ficewa sai suka kalli juna Umad da Musail, kallo irin gwada gwa, hannu ya zura aljihu ya ciro makullin motar da ko ina yana tare da shi, mik’a masa yayi yasa hannu ya karb’a ba wanda yayi magana Musail d’in ya bar asibitin shi ma Adah ya rufa masa baya, suna fita b’angaren shi yayi yana bayar da umarnin “Adah ka kira min Khatar a b’angarena yanzu yanzu.”

Rusunawa yayi yace “To ranka shi dad’e.” Ya fad’a yana ratse hanyar da suke bi a tare.

*Suna* fita Umad ma kiran sarki Abdallah yayi ya fad’a masa halin d ake ciki, cikin tashin hankali sarki Abdallah yace “Ya take yanzu Umad? Tana ina?”

A sanyaye yace “Tana lafiya yanzu, ga ta can d’akin hutu.”

Ajiyar zuciya ya sauke yace “Alhamdulillah, na ji dad’in haka.”

A dak’ile Umad yace “Sai dai kuma akwai matsala.”

Nutsuwa yayi sosai yace “Wace irin matsala Umad? Me ya faru?”

A nutse ya sanar da shi abubuwan da suka faru daga zuwanshi, madadin mamaki da wasu tambayoyin sai kawai ya ji yana murmushi mai sauti yace “Umad, Umad, shi ne ka tare da amaryata ba sanarwa ko? To gobe zan shigo Khazira, shigowa ta farko bayan aurar da ‘yata, kuma a fadar Musail zan sauka dan a shirye na ke da shi, sannanba ni kad’ai ba har da sarauniyata, dan ita zata raka maka amaryarka d’akinta.”

Yar dariyar da bai zata ba ce ta kubce masa yana girgiza kai, shiru da dukansu sukayi ne yasa a tare suka d’auke wayar daga kunnensu.

*A* wajen Musail kuma yana tsaye a falonshi yana safa da marwa Adah ya dawo tare da Khatar, suna shigowa ya kalli Khatar saida ya zo daf da shi ya tsaya, rusunawa yayi yace “Sarki na ka ce in zo?”

Dafa kafad’arshi yayi tare da zagayashi cikin tako d’ai d’ai yana fad’in “Khatar kasan wani abu kuwa? Na jima ina taraka, na dad’e ina rik’eka a zuciyata, amma alamu kullum nuna min su ke ni d’in nan dai ni ne zan ga bayanka.”

A rikice ya juya ya kalleshi cike da neman k’arin bayani yace “Ranka shi dad’e, ban gane ba? Me kake fad’a ne haka?”

Advertisements

Murmushi ya sakar masa tare da zagayowa gabanshi ya kalli fuskarshi yace “Kar ka damu, zaka fahimta yanzu.”

Ba tare daya d’auke hannun daga kafad’a ba yace “Khatar, nasan abubuwa da dama da kuka aikata min kai da Dhurani, tabbas ni mugu ne kuma azzalumi, amma ba shashasha ba, lalacewata bata kai matakin da zan so kashe ‘yata ta cikina ba saboda son mulki, hasalima yarinyar da kuke ganin kamar ina k’in ta ne, tsananin azababbiyar soyayya na ke mata, soyayyar da ko mahaifiyarta bana jin tana mata ita.”

Wani mugun kallo ya masa yace” Shi ne ka yi k’ok’arin kasheta? Kuma ma harda matata? Matar da na fi so a rayuwata?”

Girgiza masa kai yayi yace” Ka yi kuskure, ka yi kuskure Khatar.”

Hannu ya mik’awa Adah shi kuma ya ciro wuk’ar dake k’ugunshi ya mik’o masa, yana damk’e wuk’ar a hannu bai yi wata wata ba wajen rumgumo shi jikinshi ya burma masa wuk’ar nan a ciki, k’arar daha bud’a baki zai yi sai kuma Adah ya koma ta bayanshi ya murd’e masa wuya tsaf, daga haka suka gama da Khatar aka rufe babinshi.

Za a iya cewa mutuwar kare Khatar yayi, dan uamrni ya ba wa Adah a jefar da gawarsa nesa da nan inda kafin a gano shi ya kashe shi lokaci ya ja.

Fita yayi ya bar Adah na k’oknarin d’aukar Khatar dan cika umarninshi, Musail na fita asibitin ya sake komawa, lokacin da Adah ya fito da gawar Khatar yana son sakashi a bayan mota a daidai lokacin Umad zai koma b’angarensu dan fita shi da Haman, abinda ya gani yasa shi ciro wayarsa ya d’auki hoto a matsayin shaida sannan ya sa ido a kanshi har saida ya shiga motar ya tuk’a, yana fita a gidan Umad ma ya karb’i makullin wata k’aramar mota a hannu dreban gidan ya bi sawunsa.

A cikin asibiti kuma Juman ya samu zaune a kujera ta rabka tagumi tana kallon Ayam da ke bacci har ta k’ara fad’awa dama kuma ba kauri ba, dan tun jiya da ta zo gidan nan ba ta ci abinci ta k’oshi ba, bala’in gida da tashin hankali ya fi k’arfin tunaninta, gashi a kwana d’aya tak an hari rayuwarta sau uku kenan, ta ya mutum zai rayu a haka? Zulumi da fargaban kowane lokaci za’a iya farautarka sannan a kasheka, ai musiba ce babba kuwa, dan haka da ta ji sauk’in nan kawai d’auketa zatayi ta koma gaban iyayenta ita kanta zata fi samun nutsuwa.

Bakin gadon ya zauna yana kallon fuskar Ayam d’in, sauke numfashi yayi mai nauyi tare da laluba aljihunsa ya ciro makullin nan, mik’a wa Juman yayi yace “Idan ta dawo hayyacinta ki bata shi, mallakinta ne izuwa yanzu kuma ta cancance shi.”

A shashance ta karb’a tace “Na miye wannan d’in?”

Tab’e baki yayi yace “Ba ke kin tseratar da ita ba? Wace kariya kika bata bayan haka? Kawai kin had’a da mutanen da kike ganin kin san su ne a matsayin bayinki, hatta yanda zaki ji lafiyarta sai dai a baki labari daga bakin mutum hud’u, ni kuma kai tsaye nake samun labarin lafiyarta.”

Mik’ewa yayi tsaye yana kallonta yace” Juman, ni ba wawan uba ba ne, ki daina min kallon da ki ke min, ya isa haka.”

Cikin d’aga murya tace” Ba zan daina maka ba har sai ranar da na tabbatar baka neman ‘yata da sharri, me yasa wai ba zaka hak’ura da burinka na son kasheta ba? Ka barta ta rayu ni kuma na maka alk’awarin d’auketa daga nan tayi nesa da kai da sarautarka.”

Gyara tsayuwa yayi da kyau cikin isa da fitar da kowane harafi yace” Kin d’auka sanarwar da aka dinga yi daga gwamnati saboda mahimmancinta a gare su ne ? Ko kad’an, ni ne na yi haka dan na jawota gare ni, daga yanzu kuma ni ne zan dinga kareta har sanda numfashi zai bar gangar jikina.”

Juyawa yayi zai zauna kan kujerar dake gefen gadon na zaman mutum uku, rik’e hannunshi tayi tace” Kamar ya zaka kareta da kan ka? Ba kai kake son kasheta ba?”

Tsaki yayi ya bige hannunta tare da zaunawa kan kujerar yana sake kallon fuskar Ayam, komawa tayi ta zauna ita ma tana kallonshi sai tunanin abinda ya fad’a take yi, sai dai sam zuciyarta ta kasa yarda da abinda ya fad’a, dan ita a ganinta abubuwan da ke faruwa har yanzu bai d’auki mataki d’aya ba a kai.

 

*Giobarh*

 

Abun al’ajabi ne tashin sarauniya Kossam da k’afafunta a safiyar yau, abun kamar al’amara, ba taimakon kowa ba kuma sanin kowa haka aka wa yi gari aka ganta da k’afafunta kamar yanda take a da shekaru da suka wuce, kowa kallonta yake kamar ya ga sabuwar hallita har sanda sarki Wudar ya zo inda ta ke da mamakin da ya fi na kowa.

Ido cikin ido suke kallon juna amma mamaki ya hanashi magana, d’an murmusawa tayi a ladabce tace “Mamaki ko? Ba abun mamaki ba ne.”

D’an jujjuyawa ta fara kamar tana neman wani kafin ta kalleshi tace “Ina yarinyar nan?”

K’asan k’afafunta ya kalla ya dai tabbatar ita ce sannan ya kalli fuskarta, da mamaki yace “Wai…ya haka? Kossam, ya haka ta faru?”

Murmushi tayi mai tsadar gaske tace “Wannan yarinyar ce, a duk inda take yanzun na tabbatar suna tare da Umad, na ga hakan a mafarki na kuma na gasgata.”

A kid’ime ya zaro ido yace “Me? Umad? Da Zafeera?”

Da mamaki da kuma fara’a ta kalli fuskarshi tace “Zafeera? Ita ce dama? Sunanta kenan?”

Hankali a tashe yace “E, amma me ya had’ata da Umad kuma?”

Girgiza kai tayi tace “Ban sani ba, amma dai akwai wani abu dake faruwa a tsakaninsu.”

Da k’arfi cikin rud’u yace “Baki sani ba?”

Cike da izgili ta d’aga kafad’a alamar e ta juya zata fita tace “E, ban sani ba, amma yanzu zan sani tunda na samu lafiya.”

Fita tayi daga falon ta tunkari b’angaren Joyran, a hankalce take tafiyar tana kallon k’afafunta da mamakin yanda farat d’aya ta tashi yau, haka kawai a mafarkinta ta ga wannan yarinyar da kuma Umad, hak’ik’a tun ranar da yarinyar ta hana kowa shiga wurinta sai amintattunta, tun ranar Joyran bata sake shiga d’akinta ba, abincin da take bata da abinda take shafa mata a jiki duk ta daina, tun daga ranar ta fara jin canji a jikinta, daren jiya kuma bakinta ne ta ji yana tirsasata tayi magana, haka kawai ta fara d’aga harshenta da a baya kamar shi ne aka danne aka hana mata magana da shi, amma sai ta ji ya saki har ta fara furta sunan d’anta Urab da kuma Umad.

Tsakiyar dare tana bacci sanda mafarkin nan ya zo mata tana ganin hoton fuskar yarinyar da kuma d’anta a gefenta, yanayinta ya nuna kamar shagwab’a take dan tayi takwaf takwaf da fuska ne, amma bata tantance ba kawai ta ji ta zumduma ihu da ya sa ta tashi daga baccinta a firgice, mantawa tayi da larurarta kawai ta mik’e tsaye tana zazzare ido, saida ta hangi kanta a madubi ne sannan ta kula ita ce fa a tsaye, tsaye kan k’afafunta yau? Sai kawai ta shiga takawa tana godiya ga abun bautarsu tana mai son sake ganin yarinyar nan da har yanzu bata san ko da harafin farko na sunanta ba.

Joyran na tsaye tana ta kai da kawo da wayarta a hannu tana fad’awa k’awarta cewa “Ki taimaka min k’awata ki je ki samu mutumin nan ya min wani sabon aikin, nan da India ai ba wata tafiya ba ce, kuma zan d’auki nauyin komai na tafiyar ta ki, kin ga na rantse miki ina cikin tashin hankali.”

Jim tayi alamar gana sauraren abinda ake fad’a daga can, da sauri ta d’auka da fad’in” Ba zaki gane ba k’awata, komai fa nema yake ya lalace a nan, kinga dai kwana uku kenan ban ba ta abinci ba bare na saka maganin, gaba d’aya yarinyar nan ta lalata komai, yanzu haka Wudar d’in ya juya min baya, jiya ya shigo yana son na bashi had’in kai, na d’auka zai sake dawowa saboda ba zai iua hak’ura da ni ba, amma kuma har yanzu bai waiwaye ni ba, gashi Khatar ma da ya ce zai turo min kud’i har yanzu shi ma bai turo ba.”

Marairaicewa tayi tace” K’awata, idan har lamarin nan ya lalace na rantse miki barin garin nan zan yi, tattarawa zan yi na koma can gurin Khatar, dan cikinsa ne a jikina.”

Daga bayanta ta ji an ce” Ki bar nan ki je ina ‘yar uwa?”

Da k’arfi ta juyo tana zazzago idonta dan tabbas tasan murya da jimawa, ganin Kossam tsaye gabanta ta k’are mata kallo tas, sai kawai ta saki wayar ta fad’i k’asa da k’arfin tsiya tace” Kossam? Ke ce a kan k’afarki? Ta ya ya? Bayan bokan nan ya fad’a mana haka zai faru ne kawai idan sauyi ya zo.”

Saida taa gama fad’a sai kuma ta fahimci me ta aikata, wata dariya Kossam ta dinga shek’awa kafin ta girgiza kai tace” Haka ya fad’a? Da alama kun jima baku had’u ba ko? Tunda bai fad’a miki sauyin ya zo ba.”

Rarraba ido ta fara yi tare da k’ak’aro murmushi tace “Amm..yaya…ba fa abinda…nake nufi ba kenan, kawai dai…”

Shiru tayi ba tace komai ba, da fara’a a fuskar Kossam tace “Na fahimta, yanzu dai barin garin nan ba shi ne mafita ba, ki zauna tare da ni, zan ji dad’i sosai.”

Juyawa tayi zata fita sai kuma ta tsaya ta kalleta, a dak’ile tace “Cikin jikinki, me yasa kika so d’orawa mijina da farko? Amma yanzu kuma daga bakinki na ji asalin na wa ye.”

Girgiza kai tayi cike da takaici tace “Ban tab’a tsammanin haka daga gareki ba, Joyran kin ci amanata kuma kin zalince ni, amma…”

Jinjina kai tayi ta cije leb’e tare da juyawa ta fice a falon, tana ganin fitarta ta d’ora hannu a kai ta durk’ushe ta fashe da kuka tana fad’in “Na shiga uku ni Joyran, me na aikata haka? Ya zan yi yanzu?”

Kamar an tsikareta sai kuma ta zabura ta mik’e tana rarumar wayarta a k’asa ta shige d’akin baccinta dan had’a kayanta, dan ba zata k’ara awa d’aya gidan nan ba sai ta barshi, matsala d’aya shi ne isashen kud’i da bata da a hannu, amma duk da haka zata harhad’a kan kud’ad’enta da kuma siyar da kadarorinta in ya so ta kama gabanta.

*Egypt*

 

A falon na alfarma mai d’auke da mafiya dattijai suka gama tattaunawa, sun jima suna hirar data shafi ci gaban talakawa akan tallafin da masarautar zata bayar na ilimin yara k’anana.

Bayan sun kammala duk da ya gaji sosai yana kuma buk’atar hutu, amma haka ya sa aka shigo masa da Bukhatir, zaune yayi d’aya daga kujerun wanda suka tashi a ladabce, cikin girmamawa yace “Ranka shi dad’e ka ce ka na son gani na, ina fata dai lafiya?”

A sanyaye ya sauke numfashi yace “Bukhatir, na kiraka ne dama akan tafiyar da nake so na yi gobe.”

D’an kallonsa yayi sai kuma ya sadda kanshi yace “Tafiya kuma sarki na? Zuwa ina?”

A hankali ya furta “Khazira.”

Da sauri wannan karan ya d’ago ya kalleshi yace “Khazira?”

Jinjina kai yayi a hankali yace “E.”

Sunkuyar da kai yayi yace “Amma yallab’ai komai lafiya? Tafiya Khazira haka kai tsaye?”

Jim yayi yana sauke numfarfashi kafin daga bisani yace “Lafiya ba lafiya ba, zan je ne dan gudanar da shagalin bikin jikata.”

Da wani mamaki ya d’aga kai ya kalleshi yace “Jika kuma? Zafreen ta samu mijin aure ne?”

D’an murmushi yayi a hankali yace “Ba Zafreen ba ce, Zafeera, ko kuma na ce Ayam.”

A gigice ya d’aga kanshi ya kalleshi, cikin fitar hayyaci da mantawa yace “Zafeera ce za ta yi aure? Ina raye?”

Da kallon tuhuma sarki Abdallah ya kalleshi d kuma mamaki yace “Kamar ya kana raye? Kana son ta ne?”

K’iri k’iri ya masa da ido yana kallo ba rusunawa, sai ya ke ji kamar ya hau sa da duka ma, yanda shi ma ya ga yana kallonshi yasa sarki Abdallah fad’in “Lafiya dai Bukhatir?”

Da sauri ya sauke kanshi k’asa yana girgizawa yace “A’a, a’a ba komai.”

Jinjina kai yayi yana murmushi yace “Shikenan, ka je ka shirya tare da iyalinka za mu tafi, sannan a can gida ma (gidan iyayen Bikhatir) ka sanar da su, zamu tafi a jirgin safe in sha Allah.”

Nauyayyen numfashi ya sauke yana jinjina kai amma bai ce komai ba, dan abun ya fi k’arfin yace komai, irin yanda aka shammace shi haka sai ya ji kamar zai mutu.

 

*Alhamdulillahn*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
INAYAH
Read More

INAYAH 20

Advertisement _20_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Ranarda tafara fita aiki tareda Safnah sukaje sbd driving din Nan Sam batajin Zata iya,…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 13

Advertisement £pisode -13………… Babban parlorn gidan ya shiga ,masha Allah gidan ya tsaru ƙarshen mataki , parlorn wani…
INAYAH
Read More

INAYAH 41

Advertisement _41_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Ahankali Haj umma ta qaraso tana kallon babyn hannunsa a Rikice tace” MAJEED babyn waye…