Lu’u Lu’u 36

Advertisement

*36*

 

Sai daf da yamma ta farka daga nauyayyen baccin, idonta ta fara saukewa akan Juman dake kusa da ita tana kallon d’inkin da aka mata a gefen wuyanta, cike da kulawa Juman tace “Ayam, kin farka?”

D’an rufe idonta tayi sannan ta bud’e kafin ta muskuta tana son tashi zaune, dage d’aya gefen na ta taji an rik’eta an rumgumata a k’irji da niyyar taimaka mata, k’amshin turaren ya fara kai mata a hanci, hakan yasa ta zabura ta d’aga kai ta kalleshi, iskan bakinshi ne ya fara dukan hancinta yanda iskar hancinsu ya daki na juna.

K’ok’arin janyexa tayi daga jikinshi da mamakin wane rashin kunya ne kuma haka? Sai sarki Musail daya mik’e a lokacin zai fita ya kalleta yace “Bari ya taimaka miki, jikinki ba k’wari.”

Yatsina fuska tayi ta d’an sake satar kallonshi, kawar da kai tayi tana kallon Musail ta d’aga bakinta da k’yar tace “Pah, ba na son…ganin sa a nan, please ka ce ma sa ya tafi.”

A take suka kalli juna Umad da Musail, da ido ya masa alamar ya tafi kawai, Juman kuma da mamaki tace “Me yasa Ayam? Ya zo taimaka miki ne fa.”

K’ofar d’akin aka bud’e aka shigo, kallon Haman d’in sukayi da ya shigo yanzu har da ita kanta Ayam, k’arasa zame jikinta tayi daga na shi tana kallon Haman tace “Ai ga mijin da zan aura nan, me zai hana shi ya taimaka min madadin mai kula da shi?”

Wani kallo ya watso mata daga tsayen da yake ba tare daya mik’e daga rank’wafawar da yayi ba wajen taimaka mata, sai kuma ya kalli Haman d’in dake ci gaba da takowa a hankali amma alamun tuhumar kansa sun bayyana a tare da shi, kallonshi yayi ya mik’e tsaye da kyau tare da zuba hannayenshi a aljihu.

Cikin kulawa Haman ya kalleta yace “Ya jikin na ki? Da sauki?”

Advertisements

Ayam ma kallon Haman d’in take dan haka kawai take jin haushin Umad da son ganin ta k’untata masa, amma da fari tana buk’atar ta samu lafiya kafin nan, k’wafa tayi a zuciyarta ta mik’awa Haman hannu tace “Dan Allah taimaka min, ina so zan shiga bayi.”

Ba tare da tunanin komai ba ko ran wani zai sosu ge da hakan, duba da tsarin da suke kai shi da Umad, da kuma yanda ya dinga jadadda masa shirin su kar kuma ya yarda ya kwafsa, sai kawai yayi azamar rik’o hannunta sannan ya matso daf da gadon.

Daga cikin aljihun ya nemi damk’e hannunshi ganin yanda gaban idonshi ya rarumi hannunta, wasu d’atattun yawu daya had’e yasa Musail waro ido da kyau ganin yanda mak’wallaton dake wuyanshi ya wani yi sama da k’arfi sannan yayi k’asa, a hankali ya taka zuwa kusan Umad d’in ya dafa kafad’arshi yana murmushin mugunta.

Suna kallo har ta sauko da k’afafunta ta saka takalminta suka nufi hanyar ban d’akin dake cikin d’akin, bud’e mata k’ofar yayi ta shiga sannan ya tsaya yana jiran fitowarta.

A wani hassale a kuma dak’ile Umad dake hango ta ya ma zai tsaya kuma a k’ofar? Sai ya jira ta fito ko me? Uzirin na ta zai saurara? Cike da takaici yace “Zo ko?”

Saida ya gyad’a sannan ya tako ya dawo gabansu ya tsaya, Musail da har lokacin bai d’auke hannunshi a kafad’ar Umad bane ya kalleshi cike da son k’ular da shi yace “Gaskiya dokin k’arfe, da ba buk’atar b’oye b’oyen ai.”

Da mamakin dake neman kasheta Juman tace “Wai me yake faruwa ne? Umad…?”

Kallonta Musail yayi yace “Kin tuna shi kenan? Na d’auka ba zaki ganeshi ba, saidai na manta akwai kamannin Urab a fuskarshi.”

Girgiza kai yayi da dariya irin na “Haba yara.” Sannan ya d’auke hannunshi a kafad’ar Umad ya kama hanyar fita, da kallo duk suka bi shi kuma kowa da abinda ke ranshi, Juman mamakin yanda ta ji yayi wasu maganganu yanzun take, ba ma yanzu na ita fa tun daren jiya duk ya sauya mata, wasu abubuwa yake yida suke sakata cikin rud’ani suna kulle mata kai, kamar ya san da faruwar komai? Kamar kuma yana hankalce da komai? To in hakane kenan me ye sunansu? Me suka aikata su? Me kuma zai aikata musu tunda ya san gaskiyar?

Haman kuma maganarshi a cikin tsoro ta antayashi, dan shi ma dai tunaninshi kenan, idan har ya sani wane mataki zai d’auka a kan shi? Me zai iya yi masa? A matsayinsa na wanda ya taimaka ana so a raina masa hankali, gashi shi kuma ko shirin bai gama sani ba, dan sai Umad na son wani abun ne kawai zai ce masa yi min kaza, amma har yanzu bai san dalilin zuwansu gidan nan ba da dalilin da yasa ya ce ya nemi auren Ayam, wacce a yanzu dai ya gama fahimta shirin shi na farko ba zaiyi tasiri na dan ita kanta Ayam d’in tsoronta yake ji, ama shiri na biyu na zai kasa aiwatarwa ba tunda ba shi kad’ai ke farautar wannan matakin ba.

A wajen Umad kuma kallon tsana ya bishi da shi da jin cewa lallai shi ya *kashe masa d’an uwa*, sannan a dalilin *mahaifiyar shi* ta fad’i sumammiya, wanda daga wannan ne suka rasa lafiyarta, sannan shi ne yayi dalilin mutuwar *mutumin* daya taimaka masa har ya samu masaniya akan inda zai samu Zafeera, haka kuma yanzun yake farautar rayuwar su Habbee dan ya kashesu, uwa uba kuma yake farautar masa mata, ita ma so yake ya hallakata.

Dan haka ba zai yiwu ba, tabbas ya zo gdan nan ne saboda Ayam, amma da niyyar ya k’ara samun wasu sirri da hujja da zasu nuna sarki Musail azzalumi ne sannan makashi, ba kuma zai bar nan ba har sai ya tabbatar an zartar masa da hukuncin da ya dace, ba zai tab’a bari burinshi da wahalarsa ta shekara da shekaru su tafi a banza ba.

Advertisements

Dalilinsa na shiga aikin hukumar sirri shi ne dan ya gano abinda ya faru a k’asar Egypt shekaru ashirin da shida, yana so ya san asalin abinda ya kawo wannan hatsaniyar, ya kuma samu da haka ya dinga bibiyar lamarin, hatta Ayam ya shiga rayuwarta ne a dalilin yayanshi.

Sai dai a kowane lokaci sarki Musail yana sake tabbatar masa shi mai laifi ne da baya son a tonaasa asirinsa, dan a lokacin daya gano wani muhimmin anfani da waziri Khatar zai masa, sai kawai d’azu ya ga gawarshi akan titi wanda Adah ya jefar, bayan ya bar wurin ne ya zo ya su a ya kuma tabbatar, dan haka yanzu makaminsa d’aya daya rage shi ne *Adah*.

Kowane sarki, kowane mai iko, kowane mai mulki yana da na hannun dama, kuma na hannun daman sarki Musail shi ne Adah, dan haka Adah ne harinsa na gaba kuma zai yi nasara wannan karan da yardar Allah.

Murd’a k’ofar da Ayam ta yi ta sa suka kalli k’ofar, da sauri Haman ya d’aga k’afarshi da niyyar k’arasawa ya kamata duba da yanda ta ke tafiyar sannu sannu tana ciccije fuska, saidai kafin ya d’ora k’afar a k’asa Umad ya sha gabanshi tare da nufa inda ta ke, ya na zuwa bai tsaya komai ba ya rik’o hannunta sannan ya fara takawa da ita a hankali.

Cak ta tsaya tana kiciniyar yakice hannunta, jin ya rik’eta sosai yasa ta sake k’ok’arin kubcewa tana fad’in “L芒che moi ma main (sake min hannu na).”

Kallonta yayi, duk da fuskarshi a had’e take kuma ranshi a b’ace, amma dai sai ya ji ba buk’atar ya had’e mata fuska yayin da zai mata magana, dan haka a sanyaye ya furta “Ko mu je ki taka da kanki, ko kuma na taka miki k’afafun, wane ki ke so?”

Kamar jiranshi take sai kuwa ta d’aga murya har da lik’e ido tsabar masifa tace “Ba na so d’in, na ce ba na so, dole ne malam? Sake ni zan tafi da kai na.”

Sunkuyawa ya yi kamar zai gyara d’amarar takalminshi, kafin ta ankara sai ji tayi ya kwashi k’afafunta ya yi sama da ita, wutsil wutsil ta fara da k’afafun tana fad’in “Mahhh! Mah ki na gani fa? Ki masa magana mana ya sauke ni.”

Saida ya kawota kan gadon ya dire sannan ya rik’e k’ugu yana kallon fuskarta, wata masifa da ya ga tana neman koya daga jiya zuwa yau, rigimar da take neman d’orawa kanta, jinjina kai ya yi ba tare da ya d’auke idonshi daga kan ta ba.

Juman da abun ya d’aure mata kai ta rasa me za ta yi tunani a kai, ga wanda ya zo maganar aurenta, amma kuma ga wanda ke matse mata waje, kallonsu kawai take kamar bak’in fuska a gabanta.

Cikin takaici ta kalli Haman da shi ma mamakin yanda Umad d’in ke mata yake, cike da masifa Ayam ta nuna shi da hannu tace “Wai a haka ne za ka aure ni? Kana ganin abinda ya ke min amma ba za ka d’auki mataki ba.”

A fusace ta d’auke kai daga kallonshi ta furta “Banza kawai.”

A tare suka zaro ido, Haman kam sai ya ji ta muzantashi, amma ya zai yi tunda yar Musail ce, Umad kam shafa sajenshi yayi sannan ya kuma tsareta da ido yace “Me za ki ci?”

Harara ta wurga masa tace “Ban sani ba.”

Wani shak’iyin murmushi ya saki ya juyo ya kalli Juman kamar gunki da kuma Haman da ya d’an had’e fuska yace “Ku d’an ba mu guri sarauniyata, zan sa ta yi magana.”

Jinjina kai Juman tayi tace “Shikenan.”

Kallon Ayam tayi tace “Kar ki yi taurin kai kin ji, ki fad’a ma sa abinda ki ke so.”

Da sauri ta kalleta tace “Mah, Mah kar ki fita, jira ni to…”

Ta yi maganar ta na sauko k’afafunta za ta fita ita ma, hannu ya sa ya dangwarar da ita ta koma zaune, a hassae ta kalleshi za ta yi magana, amma ganin ba ita ya ke kallo ba sai ta yi shiru tana hararanshi.

Ya na ganin fitarsu ya juyo kan ta tare da zaunawa gefenta, fuska a had’e yace “Me za ki ci?”

Kallonshi tayi idonta taf da k’walla tace “U…mad, ka san dai idan na maka Allah ya isa za ta bi ka ko?”

Zuba idonshi yayi cikin na ta kamar zai yi dariya, sai kuma ya gyar zamanshi da kyau saboda hango irin abinda zai mata yanzun, cike da isa yace “Na sani, amma ba zan bari ki yi ba, idan ma kin yi babu abinda za ta min.”

Da alamar tambaya tace “Haka ka ce?”

Da ido ya mata alamar um! Rumgume hannaye ta yi a k’irji tace “Shikenan ka je na bar ka da…”

Shak’o rigarta ya yi da k’arfi hakan yasa ta kawo masa karo goshinsu ya had’e, kafin ta san dalilin da ya sa ya yi haka sai kuma ta ji d’umi a cikin bakinta, dan idonta rufewa sukayi sanda goshinsu ya kauru.

Tsutsar da aka mata a baki ne ya tabbatar mata da lallai fa bakinshi ne a na ta bakin, hannayenta biyu ta d’ora a k’irjinshi sannan ta sa k’arfi dan ta tureshi, gam ta ji ya sake nane mata ya lik’e, zaro ido tayi ta fara tureshi da k’arfi tana “Um..umum..umm…”

Irin tsutsar da ya ke mata kamar ta gayya dan sai ya yi kamar zai cire hak’orinta, sai kuma ya cabki harshenta ya na lalubar mata dadashi, saida ta ji leb’enta na zafi alamar azaba ta saki jikinta gaba d’aya ta bud’e idonta da ta lumshe, sharrr hawaye suka sauko a kuncinta, bud’e idonshi yayi da suka rikid’e suka zama ja sai rufewa suke k’arfi da yaji, ido cikin ido suka had’a ido hakan yasa ta kuma lumshe idonta ta masa alamar ka yi hak’uri yallab’ai.

Samun kanshi yayi da saisaita tsutsar da ya ke mata, a hankali a hankali ya fara mata yanzu har saida ita kan ta ta fara jin tasirin abun a jikinta yanda ta sakar masa bakin ta daina k’ok’arin k’wacewa, sannan ta lumshe idonta ruf tana sauke numfashi daga k’asan mak’oshinta.

Lis ya mata wanda hakan duk ya galabaitar da su, yana sakin bakinta mik’ewa yayi ya shiga takawa da mugun sauri zai bar d’akin har had’a k’afa yake, ita ma idonta a rufe ta jingina a gadon dan haka bata san ya fita ba, numfashi take saukewa sannu sannu har ta jawo pillow ta rumgume tayi shiru.

Wurin ranar asibiti su ka yi shitare da Juman da sarki Musail dake yawan lek’owa, sallah kad’ai take sauka daga gadon tayi ta koma ta zauna, abinda kuma Juman ba ta sani ba shi ne, sarki Musail da kanshi ya shiga madafa ya bayar da umarnin a dafa musu abinci sannan jakadiyarsa ta tsaya kan girkin, tare da alk’awarin idan aka samu matsala tabbas zai ganawa mutum azaba, amma sanda aka kawo abincin dukansu d’ari d’ari suke da abincin, saida ya d’auki cokali ya sa a bakinshi ya ci ta tabbatar ya had’e sannan kad’ai ta zuba ta fara ci, saida ta cinye da tsawon minti biyar kafin ta zuba ta ba wa Ayam.

Dariya yayi kawai yana girgiza kan shi sannan ya fice, sai yamma sosai aka sallameta inda suka koma masarauta a mota.

*Da dare*

A d’akin Ayam Juman ta kwanta bayan Ayam d’in ta yi wanka ta saka kayan bacci masu laushi, lafiya lau suka kwanta kuma gida ya yi shiru alamar ko wa ya kwanta dan ya huta ma ran shi.

*03:00* wata mummunar k’arar fashewar tukunyar gas ta sa duka mutanen gida farkawa a kid’ime, kuma daga d’akin abinci wannan abu ya fara, saidai a lokacin da turmutsutsun mutane ya fara cika gidan, sai kuma wutar ke dad’a yad’uwa a sauran sassa daban, a cikin haka kuma aka ji wata k’ara mai kama da jiniyar motar asibiti ta karad’e gidan wacce ke nuna lallai wasu sun karya tsaron gidan sun hauro ciki, sai kowa ya k’ara rikicewa ana ta neman mafaka inda mazan suka shiga neman makamai dan kare kansu da iyalensu da kuma sarkinsu.

Wad’anda ke cikin falon k’arar harbin bindiga suka ji daga waje alamar fa yak’i ne ke faruwa, kafin ka ce me an fara turo k’ofar falon, duk matan ihu suka saka suna b’uya mazan kuma suka sake rik’e makamansu a hannu suna jiran kar ta kwana.

Ana bud’e k’ofar aka shiga harba bindogogi ana ba da wuta ba kakk’autawa, sai ga mutanen nan ne dake rufe da fuskokinsu da bak’ak’en kaya sun shigo sun fi su ashirin.

Da azama suka shiga falon tre da da tsayawa waje d’aya, wanda ke gabansu da ya nuna shi ne shugaban tafiyar ne yace “Ku duba mana ko ina dan mu samota, ku yi aiki da jiki.”

Da azama suka shiga sassarfa suna fad’awa duk wani wuri da suka san d’aki ne, jim kad’an suke dawowa suna sanar da shi babu kowa a d’akin, hakan yasa ya kalli matan da suka rakub’e dan duk sun harbe mazan yace” Ke zo nan.”

Jiki na rawa wacce ya kira ta rarrafo ta durk’ushe gabanshi, cikin kakkausan murya yace” Ina Gimbiya Zafeera?”

Jiki na kakkarwa tace” Ban…ban…sani…ba”

Wani mahaukacin mari ya wanka mata a tsawace yace “Za ki fad’a min ko sai na kasheki?”

Ya fad’a yana nunata da bakin bindiga, fashewa tayi da kuka jiki na sake b’ari ta nuna masa kusurwar tace “Ta can ne.”

Juyawa yayi ya kalli yaran da suka dawo masa yace “Mu je.”

Tunkarar k’ofar suka yi duk da bindigoginsu a hannu, daga gefensu d’aya daga cikin yaran Umad yayi kukan kura ya naushe shi a baki, lokaci d’aya ya kama hannunshi mai bindigar ya murd’e tare da d’ora hannunshi daidai kunamar bindigar, kafin ya ankara ya saki alburushi ga d’aya mutumin dake gefen wannan, Haman da shi ma suka fito tare yana rik’e da bindigarshi da azama ya tashi kan yaran biyu hakan ya rage sai shugaban na su.

Umad ya saitashi da bakin bindiga kenan sai kuma wasu yaran suka fito wad’anda suka bazu neman Ayam, hakan yasa shi da Haman suka b’uya a k’asan matakalar da zata kai ka d’akin Juman, wuta suka dinga ba wa junansu aka dinga ba ta kashi, cikin taimakon ubangiji duk suka kashe yaran inda shugaban ya k’arasa shigewa wajensu Ayam.

Fitowa sukayi daga malafarsu suna kallon juna Umad yace “Ka gane, wad’annan mata ka tsaya tare da su, zan je na ji da wan…ahhhhhhh.”

K’ara ya saki sakamakon harbinsa da wani ya yi a bayanshi ga kafad’a, da wani irin salo da k’warewa Haman ya saita kan mutumin ya tasheshi a aiki.

Da sauri ya kalli Umad daya rufe ido hannunshi na jini yace” Umad, kana lafiya?”

Matse bakinshi yayi sosai ya daure duk da rad’ad’in da yake ji ya bud’a ido ya kalleshi yace” Lafiya lau na ke, zan je na duba kar ya cutar da ita.”

Cike da damuwa Haman yace” Ba za ka iya ba Umad, ka bari ni na je.”

A hassale Umad ya kalleshi yace”…

 

*Alhamdulillah*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 35

Advertisement *page 35* ******************** Umma da gwaggo haja da aunty amarya, sun k’ule falon na umma, sai hirar…
INAYAH
Read More

INAYAH 49

Advertisement Daga ita data fada har su duka dake gurin tsit sukai cikin jujjuya zancen. Batareda ya kalletaba…
A BAKIN WAWA 3
Read More

A BAKIN WAWA 22

Advertisement 22   Yana Jan Jan Dan ya taje, ta rike hannunsa,sabida wata irin masiffan zafine daya ratsata,…
Read More

TARTSATSI 75

Advertisement *Page 75*   *********************   Alhaji acikin b’acin ran da ya bayyana, akan fuskarshi k’arara yace:  …