Lu’u Lu’u 37

Advertisement

_Bismillahir rahamanir rahim_

*37*

 

A hassale yace “Zan iya mana, zan iya, zan iya.”

Da gudu ya juya ya nufi hanyar d’akin na ta, Haman kuma k’arasawa yayi kusa da hadiman nan da suka lab’e bayan kujeru.

Daga waje kuma har yanzu sara da suka ake da harbi tsakanin dakarun sarki Musail da maharan nan, inda cikin k’warewa duk su ka yi nasarar kashe maharan sannan rabin su suka tunkari b’angaren sarki Musail, wasun su kuma suka shigo falon dan ba wa sarki da iyalinshi kariya.

Kasancewar Adah wanda ya san sarki Musail farin sani ne, sai ga shi cikin tawagar wad’anda suka shiga falon da kiyyar kare iyalinshi, yanda Haman ya saitasu da bakin bindiga yasa Adah saurin d’aga hannayenshi yace “Kar ka yi harbi, mu ne.”

D’auke bindigar yayi sannan ya matso kusa da su yana fad’in “Wannan harin fa? Daga ina haka?”

Da sauri Adah yace “Ba wannan lokacin, dole mu gaggauta ba wa iyalin mai martaba kariya kafin su cimma su.”

Sama ya tunkara zai hau tare da mabiyanshi sai Haman yace “Ina ga suna d’akin gimbiya Zafeera.”

Advertisements

Juyowa Adah yayi ya kalleshi sai kuma ya kalli wani yace “Ku biyu ku je d’akin gimbiya Zafreen, ku tabbatar babu abinda ya sameta, akwa mab’oya ta sirri a d’akin, ku yi k’ok’arin dubata a ko ina.”

Da gudu gudu suka nufi inda ya fad’a musu suna kuma rik’e makamansu a hannu, shi kuma tare da wasu suka nufi d’akin Ayam d’in dan ba ta kariya.

*Umad* na isa k’ofar d’akin ya tsaya tare da duba bindigarshi dan ganin alburushi na wa ya rage masa, k’waya biyu ne dan haka ya mayar ya sake d’anata, lumshe ido yayi yana jin yanda rad’ad’in nan ke ratsashi, bud’e ido yayi tare da jan dogon numfashi sannan ya sauke, a hankali cikin sand’a ya sake kawowa daf da k’ofar, d’an lek’awa yayi dan ganin k’ofar d’akin a bud’e take, saidai babu abinda ya gani, k’arar fad’uwar abu da ya ji tare da k’arar Ayam yasa yayi kukan kura tare da mantawa da komai ya danna kanshi cikin d’akin yana mai saita daidai kan mutum da bindigar.

Cak ya tsaya saboda ganin wata rufaffiyar fuskar da aka nad’e da rawani, wannan mutumin da ya shigo d’akin na jikin shi ga dukkan alama kuma ya kashe shi ta hanyar murd’e masa wuya.

Sakin mutumin yayi hakan yasa shi fad’uwa k’asa ba rai bare ya motsa, fad’uwar da ya yi tasa Ayam ta saki kwalbar turaren data d’auka dan kare kansu daga sharrin mutumin nan, amma kafin ta kai ga haka kawai ta ga wannan mutumin da fararen kaya ya fito daga wata k’ofar ta cikin d’akin da bata san da ita ba kawai ya damk’i mutumin nan, wanda da ita ce a k’alla zasu d’auki awa d’aya suna gabza fad’a, ita bata yarda ya kayar da ita ba, shi ma kuma bai fad’i ba saboda girmanshi.

Da sauri Umad ya tunkari inda take tsaye ya d’an shiga k’are mata kallo sannan ya kalleta yace “Ba abinda ya same ki?”

Girgiza kai tayi alamar e, sannan ta kalli Juman dake kusa da gado tana kallon mutumin dake gabanta, kallo ne take masa zuciyarta na bugawa sosai, jinin jikinta kanshi tsitsinkewa yake, kallon sani take masa ba kuma sanin shanun talla ba, farin sani mai sunan farin sani dake nuna kasan ciki da waje na mutumin, yanda take sororo a tsaye ta kasa gusawa har saida Ayam ta dafata cike da kulawa tace “Mah! Kina lafiya?”

Kallon Ayam tayi kamar wacce ta farfad’o daga doguwar suma, sai kawai ta girgiza mata kai alamar ba komai.

A hanzarce mutumin ya taka zai bar d’akin da sauri Umad ya rik’o hannunshi, hakan yasa mutumin juyowa ya kalli hannun Umad dake rik’e da na shi hannun, a hankali ya d’aga jajayen idonshi manya ya kalleshi, murya a dak’ile Umad yace “Wa ye kai?”

Maida kallonshi yayi ga k’ofa ba tare d ya ce komai ba, shiru yayi bai amsa ba haka kuma ba alamar zai amsa d’in, saidai da alama yana jiran ya sake masa hannu ne.

Sannu sannu Ayam ta fara takowa kusansu saida ta zagaya inda fuskar mutumin ke kallon k’ofa, d’aga kanta tayi kad’an dan ya d’an fita tsayi, ido cikin ido suka dinga kallon juna wanda su kad’ai ne suka fito daga fuskarshi.

Irin yanda ta tsareshi da idon nan sai ya samu gabanshi da fad’uwa, kwarjini da tasirin baiwar dake cikin idonta, sun dame na shi sun shanye duk da kuwa shi ya *haifeta*.

Advertisements

Waro idonta ta yi a sanyaye sosai cikin murya kamar ta rad’a tace ” *Pah*, Abba na, kai ne?”

Sai kuma ta k’ank’ance idonta ta ziraro da hawaye tace “Na sani dama, na sani babu ta yanda za ayi a ce mahaifina ne ke son kashe ni, Pah, yau gashi ka nunawa duniya kai masoyina ne, ka nunawa kowa da ke da tarihina zaka iya fansar rayuwata da na ka ran…”

Fad’awa tayi kirjinshi tana sake fashewa da kuka, da sauri Juman ta d’ago k’afarta ta nufosu, tana zuwa gabanshi ta tsaya ta sa hannu ta jaye rufin fuskar nan yayi k’asan hab’arshi, da sauri ta rufe bakinta da tafin hannu tsabar mamaki ta zaro ido, kyarma jikinta ya d’auka tana ci gaba da kallon fuskar Musail dake kallonta shi ma idonshi taf da hawaye yana shafa bayan Ayam dake rusa kuka.

Da k’yar bakinta ya iua fuska “Kai ne? Mu…s…”

Sai kuma ta d’ora hannunta a kan ta tare da ture d’an kwalin kan na ta, hakan ya bayyanar da dogon gashinta bak’i k’irin ya sauka a gadon bayanta, ganin yanda jikinta ke rawa kamar ba zata iya tsayaw da kanta ba sai kawai ya jawota ita ma ta fad’o k’irjinshi ya rik’eta tsam tsam.

Umad kallonsu yake bakinshi d’auke da manyan tambayoyi, saidai ba damar furta ko kalma d’aya a yanzun.

Kamar wanda aka tsikara Ayam ta d’ago ta kalli fuskar sarki Musail tace “Pah, yar uwata? Ta na ina?”

Da sauri shi ma ya dawo hankalinshi ya d’aga Juman daga jikinshi, da azamaya tunkari k’ofa zai fita sai kuma su Adah da tawagarsa suka shigo, duk tsayawa sukayi suna kallonsu, da ido Adah ya musu alama tuni suka zagayesu, cikin dakakkiyar murya Adah yace “Ranka shi dad’e babu abinda ya sameku?”

Girgiza kai sarki Musail yayi yace “Lafiya lau muke a nan, ina Zafreen?”

Adah ne yace “Na tura dakaru d’akinta, za su kula da ita.”

Jiniyar motar kwana kwana da ta asibiti da suka ji ne yasa sarki Musail nufa hanyar fita, tareshi Adah yayi yace “A’a sarki na, har yanzu bamu tabbatar da tsabtace gidan nan daga mahara ba, ka jira anan tukuna.”

Wani jan kallo ya masa yace “Ba ka da hankali, ka san me ye nauyin al’umma kuwa?”

Da sauri ya fice a d’akin yana fad’in “Ka zauna nan ka kula min da iyalina.”

Fita yayi hakan yasa Umad da wasu daga cikin dakarun suka bi bayanshi, Adah kuma nuna wa su Ayam gado yayi yace “Ku zauna.”

Hannun Juman ta kama da kufin su zauna kamar yanda ya ce, amma sai Juman ta fizge da sauri ta fita a d’akin, da gudu gudu Ayam ta bi ta bayanta haka shi ma Adah ya bisu da sauri tare da dakaru ukun da suka rage tare da shi.

Yanda suka samu mutanen dake falon ne yasa suka dakata a nan, lokacin da jami’an kwana kwanan suke shiga da gudu da kayan aikinsu na kashe wuta, lokacin dogaran nan suka fito daga d’akin Zafreen suka tsaya gaban sarki Musail suka ce “Yallab’ai gimbiya Zafreen bata d’akinta.”

Cikin tashin hankali Musail yace “Kamar ya? Ta na ina?”

Girgiza kai d’aya a ciki yayi yace “Ba mu sani ba yallab’ai.”

A tsawace sosai yace “Maza ku nemo min ‘yata, ku nemota duk inda take.”

Da sauri aka sake bazuwa dan neman Zafreen, inda masu aikin kwana kwana da ke ta aikin kashe wutar nan, motocin asibiti ma da suka zo suna ta shiga da gadon majinyata dan duba ko akwai wanda ya jikkata.

Kan kujera Ayam ta zaunar da Juman da ta ga kamar akwai abinda ke damunta saboda yanda take kallon Musail da shi bai ma kula ba, ita ma zaunen tayi ta buga tagumi tana kallon shige da ficen jama’a.

Haka suka karad’e gidan wajen neman Zafreen amma babu ita babu dalilinta, da suka sake fad’a masa haka kamar zai yi hauka ya ciro wayarsa zai kira lambarta, cak Umad ya rik’e hannunshi, suna had’a ido ya girgiza masa kai a tausashe yace “Tana nan zuwa, za ta zo, yanzun nan.”

Da mamaki a fuskar Musail yace “Kamar ya? Ya aka yi ka sani? Ta na ina?”

Wani d’an murmushi yayi ya d’auke kan shi yace “Idan ta zo zaka ji.”

Jim yayi yana kallon sai kuma ya d’auke kai shi ma ya kalli Adah yace “Adah, duk inda Dhurani ya ke ka kawo min shi gabana yanzu yanzun nan.”

Da sauri Adah ya amsa da “Angama ranka shi dad’e.”

Duka dakarun suka bi bayanshi hakan yasa falon ya rage daga Musail sai Juman da Ayal sai kuma Umad, amma klwa ya fita wanda yasan ya ji ciwo yana gaban motar asibiti, wasu da aka harba kuma wanda harbin bai zo da ajali ba tuni an d’aukesu zuwa asibiti dan ceton gaggawa.

Cikin nutsuwa Umad ya shiga takawa zuwa d’akin baccinshi dan ya samu damar yin sallah subah da lokacinta ya yi, kamar jiran tafiyarshi suke Musail ma ya fita a falon ya nufi b’angaren shi.

Ganin su kawai suka rage Ayam ta kalli Juman ta dafata tace “Mah, me yake damunki ne?”

Kallon Ayam tayi ta k’ura mata ido, ta jima tana tunani tana kallon fuskarta sai kuma ta sauke ajiyar zuciya mai k’arfi, girgiza kai tayi tace “Ba komai.”

Jinjina kai Ayam tayi tace “Kin tabbata?”

Sake jinjina mata kai tayi alamar e, ita ma jinjina kai tayi tace “Mu je muyi sallah, na ga hasken alfijir ya keto.”

Jinjina kai Juman tayi kawai ta mik’e, tsoro da fargaban ko har yanzu wani abun zai iya faruwa ya sa Juman ta ce su d’aura alwala a ban d’akin dake falon kusa da gurin cin abinci, a nan sukayi alwalar suka fito, Ayam da kanta ta shiga d’akin Juman ta d’auko musu duk abun buk’ata wajen sallah.

Suna kabbara sallarsu motocin jami’an tsaro suka danno cikin gidan su ma, abun ka ga abinda ya shafi mulki da kud’i, sai gidan ya k’ara hautsinewa da hayaniya, inda yan kwana kwanan sukayi nasarar kashe gobarar ba tare da ta yi k’amarin da ta bar madafar ba, saidai d’akunan dake kusa da ita sun fara d’aukar bak’in hayak’i wasu kuma silling d’insu har ya fara kamawa da wutar, cikin sa’a dai babu wanda ya ji rauni daga wutar sai jakadiyar sarki da aka d’auka ranga ranga sakamakon hayak’in daya daketa saboda asim dake gareta.

Suna daf d gama sallar Musail ya shigo tare da sipetan (Inspector) jami’in tsaron da ke son yi ma kowa tambayoyi yanda hakan ta faru, inda sauran jami’an ke ta duba gawawwakin mutane suna d’aukarsu hoto da binciken k’wak’waf.

*Umad* ma na idar da sallah wayarshi k’arama ya rik’e ga hannu yana kallo, tunane tunane kala daban daban ne suka ziyartarshi a lokacin, yana so ya kira wayar tangarahon dake falo da kowane d’aki dan yayi magana da Mah d’inshi, jiya ta kasheshi da al’ajabi kafin bacci ya d’auke shi, sanda aka kirashi ya ga sarki Wudar ne, amma yana d’agawa ya ji muryar da tun yana shekara shida rabonshi da ita, saida ya jiri ya jefashi kan gado ya fita a hayyacinshi, sai ga shi yana zubar da hawaye abinda ya jima bai yi ba, ita kuma shi kuka aka rasa mai rarrashin wani.

Da k’yar Kossam ta rarrashe shi sannan ta tambaye shi inda yake, k’in fad’a mata yayi da fari sai dai kawai ya tabbatar mata yana lafiya, saida ta yi ikrarin zata nemeshi sannan ta je inda ya ke kad’ai ya fad’a mata yana Khazira, abinda ta fad’a masa a lokacin ta kuma kashe waya shi ne yasa shi shiga wani yanayi na daban, sai ya rasame zai yi a lokacin, gashi daya maida kira sai aka k’i d’agawa har ta tsinke.

Yana so ya ji da gaske mahaifiyarshi zata iya aikata abinda ta fad’a cewa ” *To ni ma zan zo Khazira gobe da safe, za mu had’u da kai sannan mu je masarautar Musail, zan nema ma ka auren ‘yarsa Zafeera yarinyar da ta kula da ni, kuma a dalilinta na samu sauk’i yau, na gani a mafarki na Umad, aurenka da ita alkairi ne.*”

Abinda ta fad’a kenan ta kashe wayar, ganin tunanin ba zai gyarashi sai ya kai hannunshi zai aika kiran, jin jiniyar motocin jami’an tsaro da ya yi yasa ya mik’e daga kan sallayar ya soka wayar aljihun wandonshi ya fita a d’akin da sauri.

Yana k’arasowa falon daidai da zuwan Haman, haka ma sarki Musail ya zauna kan kujera haka ma sipetan yan sandan, su Ayam ma suna sallame sallarsu suka gyara zama, kan kujera Juman ta zauna amma Ayam sai ta gyara zama a k’asa.

Jami’in ne ya kallesu a harshen slovaque yace “Ina tayaku jimami sarauniyata.”

D’an lumshe ido tayi ta gyad’a kai alamar ta amsa, d’orawa yayi da fad’a musu sunanshi da kuma aikinshi sannan ya ci gaba da fad’in “Me zaku iya cewa game da wannan abun da ya faru?”

A tare kuma a sanyaye suka girgiza kai alamar ba komai, gyara zamanshi yayi dan su fahimce shi da kyau yace “Am sarauniyata, ina nufin…”

D’aga masa hannu Musail yayi fuskarsa a had’e yace “Jami’i, ka dakatar da tambayoyinka har sanda mai laifin ya k’araso, su basu san komai ba game da abinda ya faru.”

A ladabce jami’in ya kalleshi yace “Ranka shi dad’e, muna so mu tattara bayanan da zamu samu wata makama ne, bincike muke so mu yi game da al’amarin nan, duba da cikin maharan duka dakarun masarauta sun kashesu, guda biyu ne muka samu a raye kuma mugun rauni ne a jikinsu, wanda kafin mu iya ji daga bakinsu zai d’aukemu kwana uku.”

Shirun da Musail yayi ya tabbatarwa jami’in ya yarje masa kenan ya ci gaba, sake gyara zamanshi yayi cikin kujerar ya juya ya kalli wata jami’a dake sanye da kayan aikinta hannunta rik’e da alk’alami da takarda yace” Ki d’auki duka bayanansu.”

Jinjina kai tayi tare da kafa alk’alaminta akan takardar tana kallon Juman da Ayam, a tsanake ya fara tambayarsu inda kowace tambaya da wacce ke amsa mi shi ita.

Umad na ganin haka ya nufi d’akin Zafreen, yana tura k’ofar ya shiga babu kowa a d’akin sai hasken fitila, d’akin shiru kuma a gyara tsaf babu wani abu da ya same shi, da hanzari ya nufi wajen drowerta ya bud’e, bincikawa ya fara yi yana d’add’aga kayan yana dubawa ko zai samu wata makamar.

A k’ank’anin lokaci ya hautsina d’akin da bincikenshi, har k’ark’ashin gado saida ya lek’a amma babu abinda ya samu, mik’ewa yayi ya rik’e k’ugu yana kallon d’akin, tsaki yayi zai fita na jin haushin bai samu komai ba, har zai fita sai kawai wani abu ya zo masa a rai, lokacin daya taka kujerar dake gaban madubi ya lek’a sama, daya sauko ya manta ya rik’e drower sosai ta yanda indai aje ne take to tabbas za ta motsa, amma sai ya tuna batayi motsi ba alamar a kafe take.

Da sauri ya dawo tare da dubawa, sai kuma hasashenshi ya bashi daidai, komawa yayo b’angaren shi na hagu ya tura kwabar zuwa dama, jin bata motsa ba yasa ya koma b’angaren dama ya tura zuwa hagu, sai gashi kamar k’ofa mai taya drower ta motsa k’ofa kuma ta bayyana.

Murd’a k’ofar yayi ya shiga d’akin mai duhu, wayarshi ya ciro ya kunna fitila da taimakonta ya kunne hasken wurin, hanya ce doguwa da zata kai ka har zuwa fita a bayan garin, wanda kowane d’aki na sarki da iyalansa akwai hakan.

A hankali ya fara takawa da san tabbatar tana ta fita ko kuma ta k’ofar gida, ya taka d’aya biyu kenan ya ji k’afarshi ta taka wani wuri kamar dai wanda ya rizga, cak ya tsaya ya maida dubansa k’asa d’aga k’afarsa yayi yana sake kallon wurin da aka d’an rufe da babban carpet, jaye carpet d’in yayi sai gashi tilles d’in da aka jera a wurin d’aya an d’orashi ne kawai.

Yana d’aga tilles d’in fari mai fad’i sai ga takardu sun bayyana da k’aramar wayar salula.

D’aukar takardun yayi ya fara dubawa, abinda ke ciki y so zautar da tunaninshi, dan haka yayi gaggawar maidawa ya aje sannan ya fito daga d’akin ba tare daya gyara komai a yanda yake ba.

Yana zuwa falon ya samesu yanda ya barsu, saidai a yanzun Dhurani na tsaye kan k’afafunshi yana fuskantar Musail, sai kuma Adah na bayan Musail d’in a tsaye, jiki a sab’ule ya k’arasa ya zauna kusa da Juman inda Haman ya ke, muryar Musail ya ji yana fad’in “Nagode jami’i, zaku iya tafiya.”

Jinjina kai jami’in yayi ya mik’e tare da juyawa suka fita, suna fita Zafreen na bud’o k’ofar d’akinta ta fito rai b’ace, ta fito ne da niyyar yin rashin mutunci ta ji wa ya shigar mata d’aki, dan ta wannan k’ofarf sirrin ta fita sannan ta dawo ta nan, amma ganinsu zaune babu mai magana yasa ta ja tsaki.

Tsakin da tayi shi ya dawo da hankalinsu kan ta har suka d’aga kai suka kalleta, ta juya zata koma Musail yace “Zo nan.”

Tsayawa tayi amma kuma bata juyo ba, a tsawace abinda bai tab’a mata ba yace “Na ce ki zo nan.”

Sakin k’ofar tayi ta turo baki ta shiga takowa da takalminta k’afa ciki, saida ta zo tsakiya ta tsaya tana yatsina fuska tace “Ga ni, me ye?”

A hankali Juman ta kalleta wacce tayi lak’was ta sare da lamarin Musail tace “Zafreen, mahaifinki ne fa, haka ya dace ki amsa masa kiran da ya miki?”

Juyowa tayi ta kalleta a wulak’ance tace “Ban saka da ke ba, ki bari na ji me zai fad’a min mana.”

Rai b’ace Ayam dake zaune k’asan carpet ta mik’e tace “Ke Zafreen, ya kamata kisane zai dinga fitowa daga bakinki, wannan iyayenmu ne, idan ke ba zaki girmama su ba to kar ki raina su a gabana.”

A hassale kamar dama jira take ta matso kusan Ayam tana fad’in “Me za ki yi? Idan na musu rashin kunyar me za ki yi?”

A hassale ita ma tace “Zan yi abinda ba ki yi tsammani ba ne, kuma ki jaraba ki gani.”

Waina idonta tayi ta ja tsaki tace “Ohh! Wai ni ban san ya aka yi kuka kub’uta ba, sai yaushe ne wai?”

Da mamaki Musail yace “Sai yaushe me?”

Daga zaune ba tare daya d’aga kai ya kalli kowa ba yace “Sai yaushe ne wai za ku mutu?”

Da sauri duk suka kalleshi sai Juman data dafe k’irji tace “Me?”

Sannan ya d’aga kan shi ya kalleta yace “Abinda take nufi kenan, sai yaushe ne za ku mutu ta gaji masarautar nan, ita da kuma *mahaifiyarta*.”

Ido Juman ta zaro haka ma Musail, Adah da kuma Haman da Ayam, da sauri Musail ya mik’e tsaye yana kuma zazzaro ido yace “Me ka ke fad’a ne haka? Kan ka d’aya kuwa?”

Gyara zama Umad yayi yana kallon Musail a shek’e cikin isa da k’asaita yace “…

 

*Domin samun lu’u lu’u ko badak’ala tuntub’i wannan lambar 94-98-56-52*

 

*Alhamdulillah*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
INAYAH
Read More

INAYAH 50

Advertisement 50_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Ringing biyu wayar tayi anty Hafsat ta dauka tana cewa” Dr Inayah majeed Yar gatan…
Read More

TARTSATSI 57

Advertisement Page 57*   ********************** Ana shiga asibiti da sauri aka shiga emergency da Sadauki da jamcy, and’auki…
INAYAH
Read More

INAYAH 18

Advertisement _18_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Washe gari da safe tana zaune dakinta tana waya da Dr farhat kan itama Nigeria…