Lu’u Lu’u 38

Advertisement

*38*

 

Gyara zama Umad yayi yana kallon Musail a shek’e cikin isa da k’asaita yace “Ina nufin mahaifiyarta, yallab’ai duk abinda ya faru jiya zuwa yau, yarinyar nan ce Zafreen, kuma ta yi hakane da taimakon wasu da suke da burin ganin bayanka, daga ciki akwai Bukhatir, wannan malamin da kuma tsohuwar hadimarka *Nanna*.”

Juman dake tsaye kallonshi tayi da mamaki amma kuma ta kasa cewa komai, cikin jin haushi Zafreen ta matso kusan Umad ta nuna shi da yatsa tace” Dama kai ne ka shiga d’akina ka min bincike? Akan wane dalili? Baka da wannan damar malam.”

Galala ya kalleta tare da d’ora k’afa d’aya kan d’aya yace” Ba yau na ke bincike a kan ki Zafreen, tunda na fara aiki na ke bincike akan duk wani dake zagaye da Ayam, sannan na kan dasa ayar tambaya akan duk wani dake da kusanci da ita, na nesa ko na kusa, musamman ma ke da kika sake tabbatar min da zargina ta hanyar shiga makarantar da ta ke.”

Kamar wacce kanta zai yi bindiga Juman ta dafe kai ta kalli Musail tace” Ban fahimci komai ba, Zafreen dama ba ‘yata ba ce?”

Wuru wuru ya fara yi da ido yana sinne kai k’asa, a gadarance Umad ya kalleta yace” Sarauniya dan Allah zauna, ni zan fad’a miki komai, dan na gaji da wannan nuk’u nuk’un.”

Da sauri ta zauna tana zuba masa ido dan abinda take son ji kenan, gyara zamanshi yayi a mutumce ba tare daya kalleta ba yace” Sarauniya, duk abinda zan fad’a miki abinda na ji ne daga bakin wacce abun ya faru da ita, ma’ana tsohuwar hadimarku Nanna Kapoor, ta fad’a min awa d’aya da rabi ne bayan kin haihu ita ma ta fara nak’uda, allurar da aka miki ta bacci ta sa baki samu damar ganin abinda kika haifa ba wanda bai zo a raye ba, a wannan tsakanin ita kuma ta haife abinda ke cikinta wanda sarki Musail shi ne musababbin shi, k’arfin mulkinshi ya nuna mata tare da mata alk’awarin kud’ad’e masu yawa idan har ta ba shi yarinyar da ta haifa, amma sai tayi taurin kai saboda soyayyar d’a da uwa, to fa hakan ne yasa aka koreta a wulak’ance sannan ya raba da yarinyar wacce aka baki a matsayin yar da kika haifa.”

Kallon fuskarta yayi cike da ladabi yace” Amma magana ta gaskiya ke namiji ma kika haifa ba mace ba.”

Yanda ta saki baki ta saki ido tana kallonshi, hawaye kawai ke malala a idonta, juyawa tayi ta kalli Musail tace” Da gaske ne abinda ya fad’a?”

Advertisements

Lak’was jikinsa yayi tare da komawa ya zauna kan kujera kanshi k’asa yace” Hakane, gaskiya ne abinda ya fad’a.”

Fashewa tayi da kuka tace” To amma me yasa? Me yasa ka rabata da ‘yar da ta sha wahala ta haifa? Ka san rad’ad’in da uwa take ji idan ta rasa abinda ta
haifa?”

A sanyaye Umad ya kalleta yace” Saboda soyayyarki ne sarauniya, a duk mutanen da na zanta da su abu d’aya suke fad’a min, sarki yana son sarauniyarsa fiye da komai.”

Cikin k’unar zuci da tsana Zafreen ta fara kuka tana kallon Musail tace” Kai mugu ne azzalumi, ka rabani da mahaifiyata saboda farin cikin matarka, kun banzatar da ni kun wulak’antani saboda son zuciyarku, ba zan tab’a yafe muku ba.”

K’ank’ance ido Musail yayi yana kallonta yace” Kenan saboda haka kike son kasheni?”

A harzuk’e kamar zata kai masa duka tace” Ba ma kai kad’ai ba, har da su duka iyalinka, dukanku na so kashewa, kuma sai hakan ya tabbata.”

A hassale Musail ma ya mik’e tsaye yace” Saboda me za ki had’a da su, ni ne na miki laifi, me yasa su zasu fuskanci hukuncin?”

Cikin fitar hayyaci tace” Saboda dalilinsu ka wulak’anta mahaifiyata, a da ina ganin kulawarka, amma daga ranar da aka haifi wannan…”

Ta fad’a tana nuna Ayam sannan ta d’ora da” Sai ka canza min, na d’auka kana son samunta ne dan ka cutar da ita, shiyasa har na yi yunk’urin taimaka maka, amma kwanaki kad’an da suka wuce na fahimci ba gaskiya ba ne, hasalima na gano kai ne ka ke bata kariya da kulawa.”

Kallon tuhuma da neman k’arin bayani ya mata, hakan yasa ta yin murmushin yak’e tace” E, na gano komai ai, ka tuna *Ahmad*?”

Rarraba ido yayi yana kallon k’asa, wata dariyar ta kuma yi tana fad’in” E mana, Ahmad ba, wanda yake isar da sak’onka a wajen su Habbee, na ganshi kuma ya fad’a min komai dake faruwa.”

Dafe k’irji Juman tayi ta mik’e tsaye tace” Me kike fad’a haka Zafreen? Me ya sako su Habbee a cikin wannan maganar?”

Advertisements

Wani kallo ta mata tace” Saboda ba ke kad’ai su ke wa aiki ba, har da shi ma Musail d’in.”

Da sauri Juman ta kalleshi tace” Da gaske hakane?”

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yace” Hakane Juman, lokacin da aka nemi Zafeera aka rasa hankali ya tashi matuk’a, dan yanda na shirya bata kariya ban shirya da b’atanta ba, sai nayi tunanin masu nemanta ne suka sameta, a kwana biyu tak aka nemo min inda su Habbee suke da yarinyata, dan na bata kariyae data dace haka na sa Adah ya kashe abokan tafiyarsa su uku sannan ya dawo min da labarin Ayam tana cikin k’oshin lafiya, daga lokacin na canza musu gari daga k’auye zuwa Larhjadin, wanda mak’iya da dama tunaninsu bai basu wanda suka sace Ayam za ta zauna gari kusa da Khazira ba, da wannan na samu nasarar saka ido a kan duk wani motsin Ayam, sannan na ke sa wa ana k’ara bincika min haka lokaci zuwa lokaci.”

Wasu hawaye Juman ta sako masu zafin gaske tace ” *Abban Ayam* kasan da haka me ya sa baka tab’a fad’a min ba ko sau d’aya? Me ya sa baka fad’a min kai ma so ka ke ka ceci rayuwar ‘yarmu ba?”

Girgiza mata kai yayi yana matso yar k’wallar data taru a kurmin idonshi yace “Ta ya zan fad’a miki a lokacin ki yarda Juman? Ba kya saurarata sannan kin tsaneni, bugu da k’ari kina kallona a matsayin wanda ke son kashe ‘yarmu.”

Numfashi ya sauke a nutse yana kallon k’asa yace “Bayan Dhurani ya sanar da ke fassarar mafarkinki, ni ma ya had’u da ni ya sanar da ni, saidai ya k’ara da fad’in wannan yarinyar da za’a haifa za ta zama tashin hankalina ce, ita ce mafarin rugujewata da kawo k’arshen mulkina, sannan ya fad’a min tabbas ita ce za ta zama silar mutuwa sannan ta kawo k’arshen mulkin zalincina, na ji ba dad’i sosai a lokacin sannan na shiga firgici na abubuwan daya fad’a min, sannu sannu na fara shiga damuwa na abinda ya fad’a min, haka na fara rasa nutsuwata saboda tunanin mutuwata, wata rana da yamma sai kawai na je fadar abun bauta Ghira dan na samu mafita a wajen Dhurani, a wannan lokacin ne na san komai na kuma fahimci komai, na samu malami Dhurani da waziri Khatar da biyu daga cikin fadawa na suna tattaunawa a kai na, kasancewata sarki ya sa masu gadin k’ofar kai tsaye suka bud’e min, shiyasa ba su tunanin wani zai iya shigo musu ba tare da izininsu ba, abinda na ji ya gigita ni, na shiga tsananin firgicin da ya fi wanda na zo da shi.”

Numfasawa yayi sosai sannan ya d’ago ya kalli Juman dake ta shashek’ar kuka Ayam na durkushe gabanta tana rarrashi yace” A nan na ji duk shirin da suke na ganin bayana ne, suna shirin kashe ni dan su maye kujerar mulki na, sannan su d’auki fansa akan laifin da ni ban san ya faru ba sai a tarihi, amma sai gashi da taimakonsu suna tunzurani ina aikata abinda al’ummata zasu k’i ni su kuma kirani da azzalumin sarki, juyawa na yi a wannan lokacin na koma saboda kaina daya fara sarawa, saboda abinda na ji malam Dhurani ya fad’a, cewa ya fad’a min k’arya akan yar cikina da za’a haifa, tabbas baiwarta gaskiya ce, saidai batu na zata kasheni ta ruguza mulkina k’arya ne, shirinshi ne kawai saboda yana so na kasheta da hannu na dan kar ta kawo masa targand’a a cikin lamuransu, na jima da jimamin wannan lamarin a rayuwata, daga baya kuma bayan tattaunawa da zuciyata da kuma shawarar da amintacce na wato Adah ya bani, sai muka fara buga wasar daidai da na su, inda a zahiri na ke nuna musu na tsani Zafeera kuma kasheta shine burin rayuwata, amma a bad’ini ina kulawa da matata da kuma abinda yake cikinta, wanda wasu lokuta da gangan na ke fad’in magana marar dad’i duk dan tunanin abinda zai je ya dawo.”

Sosai Juman ke kuka haka ma Ayam data girgiza kanta tana hawaye tace” Ban tab’a yarda ba har zuciyata cewa wai mahaifina zai kashe ni, duk da ban san shi ba kuma ban tab’a ganinshi ba, amma dai na ji a zuciyata ban gamsu ba, ashe duk makirci ne, kuma aka yi sa’a ya mamaye duniya har kowa ya yarda da hakan.”

Yanda jikin Dhurani ke rawa ne yasa shi yin zaune k’asa d’abas kamar an hankad’ashi, zufa yake sosai yana ta zazzare ido, cikin magiya da rawar murya yace” Ran…ranka shi…dad’e, ka min…rai, na tuna.”

Girgiza kai Musail yayi yace” Ba na kiraka nan dan na yafe maka ba ne, dole ka fuskanci mutuwa Dhurani, zunubinka babba ne.”

Kallon Zafreen yayi yace” Abinda ya faru tsakani na da Nanna ba abu bane da kowa ya sani, ta ya kika san labarin mahaifiyarki?”

Kafin ta yi magana Umad dake k’are mata kallo a lalace yace” Dhurani ne, gashi nan gabanka, shi ne ya busawa labarin rai, saboda yayi anfani da ita ta yanda zata zama barazana a gareka, kuma yayi nasarar samun haka tunda har yanzu burinta bai wuce ta kasheku ba sannan ta maye abinda take ganin na ta ne.”

A hankali Musail ya kuma kallon Dhurani yana jinjina kai, murmushin yak’e yayi yace” Kun k’irk’iri labari, sannan kun aiwatar da wasan, ku kuka samar wa da kowane jarumi rawar da zai taka, sannan a bayan fage ku kuke taka taku rawar.”

Cikin takaici da hargagi Juman ta nunashi da yatsa tace” Amma Dhurani Allah ya isa tsakani na da kai, ba zan tab’a yafe maka ba bak’in munafiki, dama abinda ka shirya mana kenan? Ka tunzura mijina da labarinka na k’arya hakan yasa na dinga jin haushinsa ina wasan b’uya tsakani na da shi.”

Jan majina tayi ta kalli Musail tace” Indai har abubuwan da suka faru sa saninka, kenan ka san da zuwana a lokacin da kuke tattaunawa kan yanda zaku kashe Zafeera bayan na haifeta?”

A hankali ya gyad’a mata kai alamar e tare da fad’in” Ina sane na tura jakadiya ta turo min ke, saida na tabbatar na ji takon tafiyarku sannan na fara magana tsakanina da Dhurani, na kusan kinji saboda yanda kika canza min daga lokacin, saidai ban san me kike shiryawa ba har sai ranar da na ji daga su Habbee cewa ke kika saka su.”

A hankali Umad ya kalli Musail d’in yace” Shiyasa ka san komai kenan? Hatta da aurena da… Ayam?”

K’uri kowa ya masa da ido yana kallo kamar wanda ya fad’i wani mugun abu ban da Musail kawai, shi ma Umad bai yarda ya kalli kowa ba sai dakewa da yayi ya buga fuska, a sauk’ak’e Musail ya jinjina masa kai alamar e, sannan ya gyara zamansa ya kalli Adah, nuna masa Dhurani yayi yace “Ka kai min shi kurkukun Sabah.”

Da sauri Dhurani ya mik’e yana fad’in “Ba zai yiwu na Musail, akan me zaka k’ask’anta ni haka? Ka sani wasa kake da wuta kuma zata k’ona ka.”

A hassale ya kalleshi yace “Na yarda Dhurani, amma dole ka fuskanci k’ask’anci a rayuwarka kafin ka mutu.”

Cikin fitar hayyaci ya fara fizge fizge saboda rik’eshi da Adah yayi yana fad’in “Musail sai na kasheka, sai na kasheka zan ji sauk’i a cikin zuciyata, kamar yanda babanka ya kashe min kakana, dole kai ma ka mutu mutuwar wulak’anci.”

Da kallo suka bishi har Adah da wasu dogaran suka d’auki suka fice da shi, da mamaki Ayam ta kalli Musail tace” Pah, me yake magana a kai ne wai? Wacz d’aukar fansa?”

A tsaanake ya kalleta yace” Mahaifina ya kashe kakansa lokacin da kakanshi Allah ya masa baiwa kwatankwacin ta ki wacce ake alfahari da hakan, saidai kakan na shi yayi anfani da haka ta hanya marar kyau, a wasu k’auyukan talakawa na fama da matsalar ruwa, mahaifina ya rok’i alfarmarsa ya bayar da wani filinsa da bincike ya tabbatar za’a samu ruwan da gaba d’aya gari zai sha ya wadatu, amma ya k’i a lokacin, saida mahaifina ya siyi filin da manyan kud’ad’en da suka wuce k’a’ida, sun yi hakan a sirrance kamar yanda mahaifina ya buk’ata, sannan ya aje takardun filin na k’warai a hannunshi bayan sun saka hannu, hakan yasa har yanzu mutane ke ganin kamar kakan Dhurani shi ne ya zamar musu silar samuwan wannan ruwan, inda suka girmamashi suka d’aukakashi ya zama waliyinsu, hakan da ya faru shi ne mafarin matsalar da ta sa mahaifina ya kashe shi, saboda mahaifina yana da adalci ba kamar ni ba da zalinci ya fi yawa a mulkina.”

Numfasawa yayi sannan ya cigaba da fad’in” Lokacin da mutane suke girmama suke zuwa da matsalarsu dan ya magance musu, lokacin ne k’anwar mahaifina ita ma ta je dan ya mata addu’a a gaban bak’in gunkin da suke bautawa dan ta samu miji tayi aure, saboda tun bayan mutuwar mijinta tana zaune gida babu aure, saidai madadin ya mata addu’a sai ya mata fyad’e, sannan ya tsorata da fad’in idan ta fad’a abun bauta zai la’anceta ba kuma zata ga biyan buk’ata ba, k’anwar mahaifina ba lusarar mace ba ce, dan haka ta tureshi daga jikinta sannan ta tabbatar masa zata fad’a dan mahaifina ya k’watar mata ‘yancinta, jin haka sai ya tsorata ya kamata ya kuma shak’e wuyanta, bai saketa ba saida ya ga ta daina shurawa kad’ai alamar ranta ya bar gangar jikinta, da taimakon yaronsa na hannun damansa suka binneta a gonar wani manomi, saidai da ubangiji ya tashi kawo k’arshenshi, a sauk’ak’e aka tono gawarta saboda mammalakin gonar da ya ga abinda bai tab’a gani ba kuma ba shi yayi ba, bayan an tonone aka ga gawarta wacce lokacin hankalin masarauta ya tashi ana ta nemanta, wannan dalilin ne ya hassala mahaifina ya sa jami’ai a cikin lamarin, to fa shine da aka gano gaskiyar maganar ta hanyar amintaccen yaronsa kawai mahaifina ya cire masa kai ba tare daya jira hukuma ta d’auki matakin daya dace a kan shi ba.”

Jiki na kakkarwa Juman ta kalleshi tace” Ba wannan ba, maganar aure… Ayam da Umad…me hakan yake nufi?”

Gyara zama ya kuma yi wanda Ayam ta kalli Umad ba ko k’yabtawa tana jira ta ji me mahifinta zai fad’a, cikin nutsuwa Musail yace” Tun daga sanda ya fara shigowa rayuwarki na samu labari daga gurin masu bibiyarki ba dare ba rana, da kallon fuskarshi a allon wayata da aka turo min na san ko wanene saboda kama da yake da sarauniyar Giobarh da kuma yayanshi Urab wanda na kasa yayin neman auren mahaifiyarki, bayanan da suka biyo bayan hoton su suka tabbatar min da kokonto na, bincike na sa aka min sosai a kan ka har saida na san abubuwa uku game da kai masu mahimmancin da ba kowa ya sani a ge da kai ba, na farko shi ne musulunta da ka yi iyayenka basu sani ba, na biyu kuma shi ne aikin sirri da kake da hukunmar binciken miyagun laifuka, na uku kuma shi ne k’udirinka akan Ayam, da haka nasan ranar da ka je gidan su Habbee ka kuma nemi aurenta a wajensu.”

Da sauri Ayam tace” Pah ban gane ba? Ya nemi aurena kamar ya?”

Jinjina mata kai yayi yace” Hakane, ya nemi aurenki a wajensu, duk da ba amincewarki a ciki, amma ni na yarda da shi saboda mutumin kirki ne, zai kula da ke Ayam.”

Kallon Umad tayi d kanshi ke sadde yana wasa da yatsun hannunshi, a sanyaye ta furta” Ta ya haka ma zata faru? Bayan babu soyayya a tsakaninmu.”

Murmusawa Musail yayi yace” Zaku saba Ayam, da sannu za ki so shi, amma dai ba zan miki dole ki zauna da shi ba, dan na fi kowa sanin illar haka, akwai zuciyar da kyautatawa bata sa ta tausasa.”

Had’a ido sukayi da Juman da sauri tayi k’asa da na ta tana mai jin kunyarshi, muryar Zafreen suka ji dake tsaye tace” Duk wannan ba shi zai sa na saurara ba, ka rabani da wacce ta haife ni, sannan ita ma ta rabani da wanda na ke so.”

Ta k’arashe tana duban Ayam da ita ma ta kalleta a lokacin haka a Juman, da mamaki Juman tace” Wa ye kike sl da ta rabaki da shi haka?”

Nuna Umad tayi tace” Wannan ne.”

Kallon Umad sukayi da yayi kamar bai san suna yi ba, Juman ce tace” Amma ai ita ma bata sani ba, ki bi komai a hankali mana Zaf…”

D’aga mata hannu tayi tace” Kinga ni ba da ke nake ba, hak’uri na hak’ura da shi dole, tunda na ji ya rabata da budurcinta daren shekaran jiya, amma ku sani wallahi ba zan rasa abunda nake so ba ni kad’ai, dole dukkanmu mu rasa wani abu da muke so.”

Mik’ewa Juman tayi tana kallonta tace” Kamar ya? Me kike nufi?”

Tab’e baki tayi tace” Ina nufin dole na kashe yarinyar nan sannan na kashe shi shi ma..”

Ta k’arashe da nuna Musail, da sauri Ayam ta mik’e tsaye tana fad’in” Idan ina raye ba zaki kashe mahaifina ba, idan kuma ni zaki kasheni saboda Umad ne, to ki d’aukeshi na bar miki, ni ba wani damuna yayi ba…”

Ta k’arashe maganar da kallon gefen da Umad yake, duk da kansa a k’asa yake amma saida ya dakata da matsa hannayenshi da yake yana taune leb’ensa yana nanata kalmar *ba damuna yayi ba*.

A hankali Musail ya mik’e tsaye ya tako zuwa gaban Zafreen ya kalleta yace “…

 

*Ki garzayo ki biya na ki.*

 

*Alhamdulillah.*

Leave your vote

-1 Points
Upvote Downvote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
KALLABI
Read More

KALLABI 15

Advertisement BABI NA SHA BIYAR* Wani jan numfashi take cikin tsananin tsoro da tashin hankali, idanun ta sun…
Read More

TARTSATSI 90

Advertisement   *Page 90*   **********************   Hajiya zulai tana k’are sambatun nata, dannawa kulsum kira awaya, jiki…
A BAKIN WAWA 3
Read More

A BAKIN WAWA 6

Advertisement 6 Sai 8pm suka isa, Ummusalma tayi bacci har tagaji ,gawata azababbiyar yunwa da takeji, babu abun…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 20

Advertisement €pisode 20…………….. Yau bobbo ya tashi da matsanancin zazzaɓi sabon mafarkin Nahad da yayi , Mamma dake…
Read More

TARTSATSI 16

Advertisement Page 16* ******************** Dr sadik ya Kalle ta dakyau yace “Tunda har nazo, dole in saukar da…