Lu’u Lu’u 39

Advertisement

*39*

 

A hankali Musail ya mik’e tsaye ya tako zuwa gaban Zafreen ya kalleta yace “Na d’auka na raineki da kulawa, ki kashe ni ba damuwa, amma ‘yata ki rabu da ita ta rayu cikin farin ciki.”

Tsakiyar idonsa ta kalla tace “Ni ba’ yar ka ba ce? Idan ka san ba ka so na me ya sa ka yi cikina?”

D’auke idonshi yayi daga kanta yace “Ina so na ji daga bakinki, shin da hannunki a wannan harin ko babu?”

A hassale tace “Da hannu na a ciki, kuma da taimakon wad’anda ba ka tsammani na zartar da hakan, d’ayan ka kama shi yanzu sai kuma ni da ke gabanka, amma na biyun ina tabbatar maka zai ga bayankkkka…”

Duk da ta kai k’arshen kalmar amma marin daya mata ya gigita ta sosai, k’ara ta saki ta da durk’ushewa tana dafe kunci, da sauri Ayam da ta fi kusa da ita ta sunkuya ta kamata sannan ta kalli Musail dake huci tace” Pah, ka yi hak’uri mana.”

Tallabo fuskar Zafreen tayi dan ta ga ko bata ji ciwo ba, da k’arfi ta fizge fuskarta ta mik’e a hassale ta kalleshi sannan tace” Ko za ka kasheni ba zan canza k’udiri na a kan ka ba, mugu.”

Juyawa tayi da sauri zata koma d’akinta sai kuma ta tsaya cak sakamakon fadawan da suka shigo da gudu gudu suka jeru a bakin k’ofar, daga ganin dakarun zaka fahimci daga masarautar da suke, Juman da ta fi kowa gane su wanene tuni ta mik’e tsaye tana zazzaro ido tana kallonsu.

Babban dogarin cikinsu ne ya fara shigowa hannunshi rik’e da bindiga dan bada tsaro, a bayanshi tsofaffin suka shigo, cikin nutsuwa da shan k’amshi suke takon, saidai fuskarsu ta nuna alamun tashin hankali da jimami, rik’e suke da hannun juna cikin shiga ta alfarma, fararen kaya masu ado kamar ba gobe, inda Bilkees ke sanye da wani babban lullub’i har yana jan k’asa.

Advertisements

Saman fuskokin da suka sauke dubansu yasa fuskarsu ta canza daga alhinin nan zuwa murmushi dake bayyanar da tsantsar farin ciki da kuma annuri.

Umad da Haman da shi dai tunda ake tattaunawar nan bai ce uffan ba ne suka mik’e a tare saboda girmamawa, Juman na had’a ido da iyayenta wani dad’i ya lullub’eta, da gudu ba tare da jin ta manyanta ba ta isa garesu, tana zuwa ta sake k’urawa fuskokinsu ido, ba ta jira komai ba ta fad’a jikin mahaifiyarta wacce ita ma k’walla suka fara gangaro mata.

Cikin kuka mai tsananin gaske Juman ta furta “Mah, na yi kewarku sosai.”

Cikin kuka ita ma ta amsa da “Ni ma haka Juman, kin girma sosai.”

K’am k’am suke mak’ale da juna hakan yasa sarki Abdallah rumgume su gaba d’aya yace “Ni ne ba kwa k’auna kenan?”

D’an d’agowa sukayi suna had’a ido ta fad’a jikinshi tana sake fashewa da wani kukan, daddab’ata ya dinga yi yana share k’walar farin ciki shi ma yana fad’in “Shikenan ‘yata, ya isa haka, kukan ya isa haka.”

Da sauri Ayam ma ta matso ta rumgume Bilkees, sun jima haka kafin ta d’ago tana murmushi saboda abinda sarki Abdallah ke fad’i cewa “Mik’o min matata nan na rumgume.”

Fad’awa tayi jikinshi tayi luf abinta kamar za ta yi bacci. Musail da ya gama tsurewa a tsaye kallonsu kawai yake, mamakin yanda suka musu dirar mikiyar nan ya ke, wad’anda basu tab’a zuwa ba su ne yau suka zo? Zuwan ma kuma da wasu irin dakaru kamar ma su jiran ya k’i, ga shi sun musu wani irin zuwa da sassafe haka, gashi tashin hankalin da suka kwana dashi har yanzu gidan a hargitse yake, hadimai sun bazu ta ko ina ana ta gyaran gidan saboda kamewar da yayi, wannan hayaniyar ce ma da nisa a cikin abinda suke tattaunawa ya hanasu jin shigowar motocinsu sai kawai dirowar dakarun nan.

A hankali ya shiga takawa k’afafunsu na neman bijire masa haka dai ya kai kanshi gabansu ya tsaya, a ladabce abinda bai tab’a yi ba, hasalima bai gansu ba bare yayi sai gashi ya rusuna yana fad’in “Barkanku da zuwa masarautar Khazira.”

Sarauniya Bilkees da sarki Abdallah tare suka kalli juna, sai kuma Juman data kallesu ita ma tana mamakin abinda yayi, cike da dauriya sarki Abdallah ya gyad’a kai yana murmushi sannan yace “Muna godiya da wannan karamcin.”

D’an juyawa yayi ya kalli babban bafadenshi ya masa alama da ido, juyawa yayi ya umarci sauran dakarun da su fice, suna fita kuma Bukhatir ya shigo tare da Zeyfi su ma cikin shiga ta daraja, sannan mahaifiyarshi ta biyo bayansu da sauran yan uwa a k’alla goma.

Ido da Zafreen ta d’ora akan Bukhatir yasa ta waro ido tana kallonshi, satar kallon mutanen dake wajen tayi sannan ta kuma kallonshi bakinta d’auke da tambayoyi bila adadin.

Advertisements

Farin cikin daya kacame iyalin a lokacin na murnar ganin juna bayan shekaru masu tsayi, shi ya d’auke hankalinsu har Zafreen ta matsa kusa da Bukhatir daga bayanshi cikin rad’a tace “Me ka ke yi nan a daidai wannan lokacin? Baka san abubuwa sun lalace ba ne?”

Saida ya saci kallon mutanen ya ga babu mai kallonshi sannan yace “Na sani, amma dole ce ta sa na zo, sarki ya umarce ni ba yanda zan yi.”

Tsaki tayi cikin jin haushi tace “Kashh!”

Juyawa tayi ta nufi d’akinta ranta a b’ace sosai, da kallo Musail ya bita tare da k’ank’ance idonshi sannan ya saci kallon Bukhatir, k’wafa yayi a sanyaye tare da murmushin mugunta wanda shi kad’ai yasan ma’anarsa.

Da tsantsar farin ciki Juman ta kuma kallonsu da kyau tace “Mah, ya aka yi kuka zo nan haka ba sanarwa? Ya kuma na ganku gaba d’aya?”

Yar dariya tayi ta kalli Ayam dake gefenta ta dafa kanta tace “Shagalin bikin jikata muka zo.”

Da sauri suka shiga kallon kallo, duba da su ma akwai magana a bakinsu yasa Musail fad’in “Ranka shi dad’e, ina ga mu je b’angarena mu zauna, dan nan ana gyarawa, wata yar hatsaniya ce ta faru da tsakiyar dare.”

Cike da dattako sarki Abdallah yace “Mun samu labarin komai da ya faru, shiyasa ma muka taho da wuri haka dan tabbatar da kuna cikin k’oshin lafiya.”

Galala Musail ya kalleshi sanda yayi magana yana mamakin furucin shi, hakan na nufin shi ma yana da nashi d’an lek’en asirin a cikin fadarsa?

Adah ne ya fara wucewa gaba sannan Musail suka fita a falon, cikin nutsuwa da kallon juna har suka shiga falon na shi, wanda babu wanda bai kalleshi ba saboda had’uwarsa da tsaruwa, wuri suka samu duk suka zauna, inda Ayam ke zaune tsakanin sarki Abdallah da sarauniya Bilkees akan kujera mai zaman mutum uku.

Juman kuma na zauna kujerar mutum biyu ita da Musail sai Adah dake tsaye a bayansu, sai Umad da Haman da Bukhatir suna k’asa kan carpet da sauran yan uwan Bukhatir maza da mata.

Juman dake kallon iyayen na ta ne ta fara cewa “Pah, ya aka yi kuka san abinda ke faruwa?”

Kallonta Ayam tayi tace “Ba wannan ba Mah, ya aka yi suka kan da maganar auren da ake fad’a a kai na?”

Hararanta Juman tayi tace “Kin manta kin bani labarin Umad ya kaiki wajensu? To ta ya ba zasu sani ba.”

Turo baki tayi ta d’ora kanta a kafad’ar sarki Abdallah, a tausashe ya saki murmushi cikin kamala ya fara magana a nutse “Na samu labarin abinda ke faruwa ne a tv a labarai safiya, ai abinda ya faru ya fi k’arfin yan jaridu da gwamnati suyi shiru, maganar aurenki kuma ai tun ranar da ku ka je ya fad’a mana.”

Jinjina kai duk sukayi sai Ayam data turo baki ta sake langab’ewa jikin sarki tace” Grand Pah, ni dai ku fad’a masa ban yarda ba, kawai ya auri yar uwata Zafreen, dan ita ce take son shi ba ni ba.”

Yar dariya sarki yayi tare da maida hankalinshi kan Juman dake fad’in” Baki isa ba yarinya, tunda mahaifinki ma ya amince to an wuce wajen.”

Yanda Bukhatir ke ta rarraba ido yana kallonsu ne yasa sarki Abdallah fad’in” Yawwa Bukhatir, ka san dalilin da ya sa tafiyar nan na ce sai da kai?”

A ladabce ya kalleshi cike da son b’oye damuwarsa yace” A’a ranka shi dad’e.”

A nutse yace” Na kiraka ne saboda ina so ka ganewa idonka, sannan ka rarrashi zuciyarka tayi hak’uri da abinda take so, sannan ka tuna da mahallicinka wanda shi ya k’addara faruwar hakan.”

D’agowa yayi ya kalleshi da kyau yana son k’arin bayani, a hankali sarki Abdallah ya jinjina masa kai alamar e sannan yace” Na san komai Bukhatir, na san dayawa daga abinda ka ke b’oyewa, tsananin son Ayam da ka ke da burin ganin ka mallaketa, idan da Allah ya rubuta matarka ce tabbas da mun yi farin ciki da haka, saidai Allah bai rubuta za ta zama ta ka ba, ka yi hak’uri da hakan ka d’aukeshi a matsayin k’addararka.”

Nunfasawa yayi sannan yace” Sai kuma soyayyar da ka ke wa kujerata, Bukhatir kai ne magajin wannan kujerar tun fil’azal, duba da ban da magaji ko magajiya, ina so in shaida maka daga yanzu da nake maganar nan na bar maka sarautar k’asar Egypt, ka zama sarki daga yau nad’aka kawai ya rage, saidai kafin hakan ta kasance sai ka min wani alk’awari guda d’aya a gaban duka mutanen dake wajen nan.”

Sadda kai Bukhatir yayi yana jin gaba d’aya tunaninsa ya tsaya cak, ya rasa da wanne zai ji, shin zai yi bak’in ciki da rashin Ayam ne? Ko kuma murnar samun wannan kujera da duk abinda yake dan ita yake yi? Duba da dama yana son samun Ayam dan ya yi alfahari da shi ya samu zab’abb’iyar, sannan ya buga k’irji a gaban sarki Musail yayin da zai nunashi da yatsa yace ya auri ‘yarsa da yake burin kashewa, sannan ya bata matakkan tsaro su zuba ido har su ga lokacin da’ yar zata kassara uban.

Mamakin kalaman sarki Abdallah yasa Juman kallonshi da mamaki tace “Pah, wai dama Bukhatir Ayam yake so?”

D’an murmushi kawai yayi bai ce komai ba, maida hankalinshi yayi ga Bukhatir yace “Ba ka ce komai ba Bukhatir?”

Sake d’aga kanshi yayi a sanyaye yace “Nagode ranka shi dad’e, wannan karamci a gareni, Allah dad’a girma da lafiya.”

A hankali Umad ya kalli sarki Abdallah yace “Ranka shi dad’e, kafin ya d’auki wannan alk’awarin zan so sanin wani abu daga gareshi.”

Lumshe masa ido yayi dake nuna ba damuwa, kallon ju’a sukayi wanda hakan yasa Bukhatir had’e fuska yana jin tsanar Umad d’in har k’asan zuciyarshi, Umad kam ko a jikinshi duk da mugun kallon da yake masa, cike da dagiya da rashin tsoro yace” Bayan duk abubuwan da ka yi zamu iya cewa an yafe maka, amma laifin da yanzun kuka aikata babba ne, wanda yayi sanadiyar jikkatar wasu mutanen, tambayar a nan ita ce, shin ka yi hakane dan ka taimaki Zafreen ta cimma burinta? Ko kuma dai yarjejeniya ce a tsakaninku ta kowa zai cika burinsa dalilin hakan?”

Kallon Umad duka mutanen wurin sukeyi sai Bukhatir dake neman rikicewa a zaunen nan da yake, wuk’il wuk’il yake da ido yana son satar kallon mutanen wurin amma ya kasa, cike da borin kunya yace” Me kake fad’a ne haka? Ban san akan me kake magana ba.”

Wani murmushin rainin hankali Umad yayi ya d’auke kansa bai ce uffan ba, sarki Musail ne ya kalleshi yace” Umad, me kake son fad’a ne?”

Kallon Musail d’in yayi yace” Yallab’ai, kwana biyun da mukayi a nan na saka ido akan Zafreen sosai, hakan yasa na gano wata alak’a data k’ullu tsakaninsu su biyun nan, farmakin da aka kai wa Ayam a d’akinta wanda aka yanketa ma Zafreen ce ta yi, sannan harin da aka kawo yau ma, Dhurani da Zafreen da kuma shi Bukhatir ne suka d’auki nauyin maharan.”

Babu wanda bai kalli Bukhatir da mamaki da kuma jijjiga ba, inda mahaifiyarshi ta rabka salati tana fashewa da kuka, dafe k’irjinta tayi tana fad’in” Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un! Bukhatir wace riba za ka ci a cikin aikata hakan?”

Wuru wuru ya fara da ido yace” Nifa ban san akan me yake magana ba, ta ya ma zan iya aikata dan Allah?”

Shiru falon ya d’auka sai kallonshi kawai suke, a saib’ance Umad ya kalli Haman dake gefenshi, kallon da ya masa yasa gaba d’aya Haman ya ji fitsari na neman kubto masa ya zubo, hakan yasa ya bi Umad da kallo irin na ka taimake ni, idan ka san wani abu kar kayi magana a nan ka jira mu bar nan sannan.

A hankali Umad ya girgiza kan shi sannan ya kalli Zeyfi ita ma a daidai lokacin shi take kallo saboda yanda ta kula yana kallon Haman, suna had’a ido tayi k’asa da na ta tana jujjuya jakarta dake gabanta, sai kuma ya juya ya kalli Haman yace “Da ka fad’a ita d’in yayarka ce ai, ba wani abu ba ne dan kana son taimakon ‘yar uwar ka, ni kaina duk abinda na ke saboda d’an uwa na nake yi.”

Kallonsu aka fara yi suma har Bukhatir da ya kalli Umad yace “Waye d’an uwan na ta?”

Banza Umad ya masa dan shi ma haushinsa yake ji saboda soyayyar da yake ma Ayam, maida kallonshi yayi ga Zeyfi yace “Ke me ye had’inki da wannan?”

Cikin turo baki gaba tana sissine kai tace “D’an uwa na ne.”

Da sauri ya kalli Haman sannan ya kalli mahaifiyarshi yace “Mah, dama tana da d’an uwa da ban sani ba?”

Tab’e baki mahaifiyarshi tayi tace “Ban sani ba nima sai yanzu, ai ba ni na had’a aurenka da ita ba, mahifinka ne kuma baya raye.”

Da mamaki yace “Amma ai Pah ya fad’a min kafin ya rasu cewa na rik’eta amana ni kad’aita gareta tunda iyayenta suka rasu.”

A sanyaye Zeyfi tace “Ya fad’a maka hakane saboda haka d’in ne, Haman tun yana yaro ya bar gida saboda basa shiri da mahaifinmu, kullum cikin fad’a suke akan sab’anin ra’ayi, dan haka wata rana ya ce zai bar gida su manta da shi, cikin hushi mahaifinmu ya ce ya fi ruwa gudu, sannan shi ma ya sa a ranshi kamar bai tab’a haihuwar d’a namiji ba, wannan dalilin yasa nake ni kad’aita, saidai ni ban yada zumuncin dake tsakani na da d’an uwana ba, muna had’uwa a kai a kai sannan muna waya ma, saidai mahaifinmu ne sam ya k’i hak’ura, amma mahaifiyarmu ma sukan gaisa da shi ta waya, har ta rasu tana binsa da addu’ar alkairi, sab’anin mahaifinmu da ya rasu yana hushi da shi.”

Musail ne ya kalli Umad da kulawa yace” ka yi maganar d’an uwanka, Umad fansa kake son d’auka har yanzu?”

D’aga ido yayi ya kalleshi yace” A gaskiya yallab’ai na shiga aikin bincike ne saboda kawai na samu hujjar da zan gurfanar da kai a gaban kotu na kashe min d’an uwana, amma yanzu…da na fara sabawa da Ayam kafin na san wacece ita, bana jin zan iya yin wani abu na k’i ko wanda zai cutar da kai, sai dai kawai ina so ‘a san dalilin da ya sa ka kashe min d’an uwana, shin saboda ka auri matar da take son sa ne?”

Girgiza kai Musail yayi yace” Umad ba ni na kashe maka d’ an uwa ba, hasalima ban da hannu a cikin kashe shi, kawai tarkon mak’iya na fad’a kuma sun yi nasara.”

Da mamaki duk suke kallon kafin sarki Abdallah yace” Kana so ka ce duk hatsaniyar da aka tayar a ranar baka da hannu a ciki?”

Girgiza kai yayi ya kalli Umad yace” Ka tuna labarin dana fara baku d’azu? Sanda na je fada wajen Dhurani, to ai bayan maganar Zafeera na samu suna tabttaunawa kan yanda suka tsara wannan farmakin, lokacin da na buk’aci auren Juman ban samu ba na shiga cikin damuwa da b’acin rai, hakan yasa na shawarci Dhurani da Khatar, nan suka zugani suna nuna min bai kamata na nemi wani abu na rasa ba, sai Khatar ya ce na bar komai a hannunsa zai d’auki mataki, ba tare da sanin abinda zai aikata ba kawai na bashi umarnin yayi duk abinda zai sa Juman ta zama ta wa, to a nan ne suka tashi hatsaniya wanda a cikin wannan hatsaniyar suka yi nasarar kashe Urab, kuma a yanda na ji suna fad’a a ranar Khatar ya y hakan ne saboda cika burin wata masoyiyarshi.”

Shiru ya yi inda Umad ya kalleshi yace” Masoyiyarshi kuma? Wa kenan?”

Kallon Umad d’in dake nuni zai fad’i abu marar dad’i sannan yace” Ban san cikakken labarin ba, amma idan ka samu k’anwar mahaifiyarka za ta sanar da kai komai.”

Zaro ido yayi yace” Joyran?”

Jinjina masa kai yayi yana kallonshi shi ma, wuri wuri ya fara da ido yana rarrabasu, ba zai ce k’arya ba ce kai tsaye tunda har ua gane tana neman da mahaifinsa, saidai me ye ribarta a cikin aikata hakan? Ta yi ne dan ta samu mahaifinshi? Ko kuma dan ta mulki gidan kamar yanda ta yi kafin zuwan Ayam ta samarwa gidan ‘yanci?

Zunbur ya mik’e yana laluba wayarsa a aljihu, da sauri ya fice a falon ya barsu da bin shi da kallo, saida ya b’ace ma ganinsu sarki Abdallah ya kalli Bukhatir yace “Zamu dakatar da nad’aka matsayin sarki har sai mun tabbatar da baka da laifi.”

Ajiyar zuciya Musail ya sauke ya kalli sarki yace “Yallab’ai, ina rok’onku da ku yafe min abisa abubuwan da suka faru, sannan zan so ku huta yanzu, zuwa dare zamu tattauna akan wata magana mai mahimmanci.”

Kallon Juman yayi dake gefenshi sannan yace “Abinda ya shafi tsakani na da ita, da kuma tsakani na da Ayam.”

A sanyaye sarki Abdallah ya gyad’a sannan yace “Ba damuwa komai ya wuce, saidai zuwan nan na mu kamar yanda na fad’a shagalin bikin Ayam ne ya kawo mu, dan haka za’a fara shagalin nan daga gobe, dole k’asar nan ta shaida ana bikin ‘yar gata, ya ga sarki Musail sannan jikanya ga sarkin Egypt.”

Murmushi Musail yayi yace” Duk yanda kuka yi d’aya ne, Allah nuna mana.”

Da mamaki sarauniya Bilkees tace” Wai ko dai ka musulunta ne kai ma?”

Sunkuyar da kai yayi irin a gaban surukan nan ya shafa kanshi kawai bai ce komai ba, mahaifiyar Bukhatir ce ta d’ora da basu hak’uri akan abinda Bukhatir d’in yayi sannan ta nema masa afuwa da fad’in shi kad’ai ne babba daya rage musu, kar su rabasu da shi, hannu bibbiyu sarki Musail da Abdallah suka karb’i k’orafinta kafin zaman na su ya k’are.

Masaukin bak’i aka kai su sai sarki Abdallah da aka keb’e musu wuri na musaman sannan aka shiga had’a musu girki na musamman da karin kumallo.

 

*Alhamdulillah.*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

Lu’u Lu’u 20

Advertisement *20*   Mik’ewa yayi tsaye yana neman kamo hannayenta yace “Kwantar da hankalinki gimbiya, ki ban lokaci…
Read More

Zee Baby Book 1 Page 50

Advertisement 👉🏻50* ….”inajin wani irin farin ciki mara musaltuwa. Yayana kaima kanaji.?sansanyan Murmushi yayi ya sakarmun kiss akunne.…
INAYAH
Read More

INAYAH 11

Advertisement 11_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Washe gari ba wani dogon walwala ta tashi Saima guraren 9 ta tashi Dan tun…
INAYAH
Read More

INAYAH 50

Advertisement 50_* *_Arewabooks@Mamuhgee_* Ringing biyu wayar tayi anty Hafsat ta dauka tana cewa” Dr Inayah majeed Yar gatan…