Lu’u Lu’u 40

Advertisement

*40*

 

Umad a fita daga nan d’akinshi ya nufa, iya abinda zai buk’ata kawai ya d’auka na daga kud’i da passeport d’inshi da kuma babbar wayarsa, fitowa yayi ya sa dreban gidan ya kai shi filin jirgi, yana shiga ciki dan samun izinin tafiya sai ga Joyran na jan k’aramar jakarta da sauri, da mamaki ya kuma dubawa da kyau dan ya tabbatar ita ce ya gani? Ko kula dai tsabar son had’uwa da ita yanzun ne yasa yake ma wasu matan kallonta?

Har ta d’an gitta ta gabanshi ta wuce sai k’amshin turarenta mai k’arfin gaske ya shaida masa tabbas ita ce dai wacce zaka tafi yanzu dominta, to amma me ya kawota nan? Kafin ya samu amsar ya taho sukwane yace “Aunty.”

Bata juyo ba saboda tunanin wa zai kirata da haka a nan d’in, saida ya matsa daf da ita yace “Aunty Joy.”

Da sauri ta juyo saboda d’aukar muryarshi da kuma tabbatarwa da ita dai a ke, suna had’a ido duk da hular dake kanta (hana sallah) da bak’in gilashi k’ato data saka saida ta ji gabanta ya fad’i har ta furta a k’asan mak’oshi “Umad kuma?”

Bai yi mamakin ganinta a wannan lokacin ba, saidai mamakin da ya ke shi ne hala bata san gogan na ta ya bar duniya ba?

Da mamaki da kuma rawar murya tace “Amm..Umad, me…kuma ka ke y…a nan? Ina nufin me ya kawo ka nan?”

Murmushi ya sakar mata tare da sunkuyawa yace “Ina kwana auntyna.”

Wani murmushi ta saki wanda kai tsaye daga zuciyarta ya fito sakamakon ganin ya gaisheta kamar yanda yake yi a da, kafin zuwa shed’aniyar nan ta lalata mata komai, damtsenshi ta dafa tace “Lafiya lau Umad, baka amsa min tambayata.”

Advertisements

Kallon k’wayar idonta yayi sannan yace “Aunty mun zo shak’atawa ne tare da abokaina, yanzu ma wani malaminmu ne ya zai zo saboda zamuyi yawan bud’a ido da shi, shiyasa na zo nan.”

Dariya tayi tace “Masha Allah, Umad kai dai baka son zama wuri d’aya.”

Wani malalacin murmushi ya mata bai ce komai na, rik’o jakarta yayi yana kallon fuskarta yace “Aunty ke fa? Me ya kawoki Khazira?”

Cikin kame kame tace “Uhmm..ka gane, ni ma dai na zo had’uwa da wata k’awata ne da mukayi karatu tare, tayi aure kuma ban samu na zo ba saboda hidimar kula da aunty (Kossam), shine yanzu na zo na mata murna.”

Jinjina kai yayi yace “Yayi kyau hakan, amma kafin nan aunty mu je na kaiki masaukinmu, dan kinga bai kamata ki d’ora mata nauyi ba ko?”

Da sauri tace “A’a a’a Umad, ai mun yi da ita zan sauka a gidanta, ka ga ba zata ji dad’i ba, kuma m ai zata turo drebanta ne ya d’aukeni.”

Cewa yayi “Duk da haka aunty na, mu je mu jira dreban, idan ya zo sai ya saukemu a masaukin.”

Yanda yayi gaba da jakarta yasa bata da wani zab’i sai bin bayanshi, gasu tsaye mutane na ta barin wajen amma su suna nan, tana son sanin ta yanda zata ribace shi ya bar wajen sannan ta shige taxi, amma ya gagara hakan, hatta ruwa da ta ce ya kawo mata da jakar ta ta ya tafi ya siyo ya dawo, k’arshe dai kallonta yayi yace “Aunty na, anya kuwa dreban nan zai zo?”

Dariyar yak’e tayi tace “To gashi dai shiru, amma zai zo, zai zo na sani.”

Girgiza kai yayi tare da tare taxi yace “Ba zai zo aunty, idan har tana ganinki da daraja ba zata yarda ta kasa turo mai d’aukarki kafin saukar jirginki ba, ni kuma ba zan tafi na bar nan ba na bar ki a tsaye.”

Tura jakarta yayi a boot ya bud’e mata gidan baya yace “Shiga aunty.”

Kamar zata fashe da kuka ta kalleshi amma haka ta shiga a dole saboda tana jin nauyin yi masa gardama, shiga tayi ta zauna ya rufe sannan ya shiga mazaunin gaba dreban taxi ya ja su zuwa titin da Umad d’in ya fad’a.

Advertisements

Da k’aramar wayarshi yake ta latse latse har suka yi nisa, Joy kam daga baya kamar zata fashe saboda takaici, k’eyarshi kawai take zabgawa harara kamar ta kashe shi, ga haushin da uwarshi ta k’unsa mata yau d’in, kawai ta sa hadimai na ta mata wani shirye shirye, data tambayeta ko lafiya ta ce zatayi tafiya ne, data tambaya zuwa ina sai cewa tayi “Bai dameki ba.”

Haka shi ma Wudar shirin ya gama tsaf ya ce ai tare zasu tafi, duk da ya yi tambayar har ya gaji cewa ta fad’a masa ina za ta je, sai kawai ta ce wajen d’anta Umad, yin me? Yana ina? Duk ta k’i amsa mi shi, hakan yasa yanzu dai kafin ta baro gidan ta baro hadimai na ta loda kayayyaki a moto wanda duk mai hankali ya gani zaka san neman aure ne za’a je yi, sai dai na wa? Kuma a ina? Bata sani ba, cikin wannan hada hadar ta kutso kai ta badd’a kama ta fita abinta.

Akan babban titin dake bayan filin jirgi motoci na police guda biyu suka tari gabansu, dole ta sa dreban tsayawa da tunanin laifin me ya yi kuma? Wace dokar ya taka ne haka mai girma a cikin tuk’i? Jami’ai hud’u ne suka fito daga motocin, sai jami’a mace d’aya data fito, cike da izza Umad ya fita ya bjd’e murfin da Joy ke zaune tana kallon me ke faruwa, amma sam hankalinta bai tashi na saboda bata ga abinda tayi ba.

Suna k’arasowa dukansu suka sara masa da girmamawa, da mamaki Joy ta kalli jami’an sannan ta kalli Umad da tunanin wa ye shi kuma a gwamnatance, hannunta Umad ya kamo sanda jami’ar ta k’araso ya karb’i ankwan hannunta, ba zato ba tammani ya mata awarwaro da ankwar nan a hannayenta, mamaki ne ya hanata katab’us sai kallonshi tana fad’in “Kai Umad, lafiya? Me na yi kuma? Me ye haka wai? Ka manta ko ni wacece?”

K’ala bai ce mata ba sai jan hannayenta da yayi saida ya sadata da motocin jami’ai ya dannata baya ta zauna sannan ya mayar ya rufe, gilashi ya ciro bak’i daga aljihunshi ya manna a idonshi, juyawa yayi zai shiga mazaunin mai zaman banza ya ji tana jijjiga tana fad’in “Kaiiiii! Umad, ka kunce min abar nan, me na maka ne wai?”

Shiga motar yayi ya ja wata raga dake tsakanin kujerar baya da kujerun gaba saboda baya da buk’atar hayaniyarta, saidai yana jin yanda take ta bubbuga motar tana hargagi, bai kulata ba saidai yana kallon wani jami’i da ya d’auko jakar Joy d’in a bayan taxin nan sannan ya biya mai taxin suka taho, tayar da motocin suka yi har da jiniya irin ta yan sanda sannan suka nufi babbar headquarter jami’an bincike na k’asa.

D’akin bincike suka ajiye ta, kalle kalle ta shiga yi tana ta jujjuyawa, d’akin studio ce ta musamman, dan iya maganarka kawai zaka ji sai wanda ke kusanka, amma ko iska bata shigowa daga waje bare ta fita, lullub’e yake da bak’in yadi mai kaurin gaske, sai wata faffad’ar taga wacce ita daga ciki kanta take gani ma’ana madubi, saidai daga waje jami’ai ne na musamman da na’urori a gabansu, inda daga nan suke iya sauraren duk abinda ke faruwa ko zai faru a ciki.

Kujera biyu ce wacce take zaune a kai sai wacce ke fuskantarta, inda k’akk’arfan teburin dakz gabanta aka d’aure hannayenta da ankwa mai d’an tsayi wacce ta fi wacce aka saka mata da farko.

Cikin hargagi ta fizgi hannayenta tana kwaroroton fad’in “Wai babu kowa a nan ne? Me na yi ne? Akan wane dalili zaku kawo ni nan ku a je? Ina buk’atar ku kira min lauyana.”

Shirun da yayi yawa babu mai kulata ne yasa ta sake fizgar hannayenta har saida kujerar da take zaune ta motsa tare da fad’in “Banzaye kawai, sai kun yi nadamar ajiye ni a nan da ku ka y….”

Cak maganarta ta tsaya saboda k’ofar da aka bud’e aka shigo, Umad ne fuska kici kicin saidai akan bak’ak’en kayanshi ya d’ora wata bak’ar jacket mai d’an ratsin fari sai daga baya an rubuta Police da manyan harufa.

A gadarance ya k’arasa ya ja kujerar sannan ya ciro k’aramar bindiga daga k’ugunshi ya ajiye, zaune yayi ya rumgume hannaye ya jingina a kujera yana zuba mata idonshi da ba wani girma ne da su ba sai tarin kwarjini kamar na damisa, murya a dak’ile kamar saukan aradu yace “Magana ce za mu yi ba wasa ba, kuma duk abinda zai fito daga bakinki ya zama gaskiya, idan ba haka ba zan manta da wacece ke a gare ni na d’auki tsatsauran mataki a kan ki.”

D’ora hannayenshi yayi a kan teburin ya d’ag girarshi ta hagu sama yace “Kin fahimta?”

A hassale tace “Kai wane irin d’a ne? Ni fa k’anwar mahaifiyarka ce, Umad me na yi da za ka kawo ni nan?”

Had’e yawu yayi tare da sake tsura mata ido yace “Khatar ya fad’a mana kina da alak’a da harin da aka kai masarautar Egypt shekarun da suka wuce, me zaki ce a kai?”

Zazzaro ido tayi na mamakin ya kuma wannan maganar ta fito? Khatar? Ya aka yi Umad kuma ya san shi? Duburburcewa tayi ta kalleshi tace “Ka ga Umad ba zan yi magana ba, ina son ganin lauya na sannan.”

Wani jan kallo ya mata da yasa ta sadda kanta k’asa cikin dakakkiyar murya yace “Tunda kika ga na zo da ke nan kai tsaye, kuma na d’auko miki gundarin zancen a take, ke kinsan ba wasa ba ce ta kawoni, Joyran…”

Ya kira sunanta ya nunata da yatsa kafin yace “Ki bani amsar tambayata kafin na turo jami’ar da za ta bincika min ke yanda ya kamata.”

D’aga hannayenta tayi dake d’aure tace “Shikenan na ji, zan fad’a ma ka Umad, amma…”

Marairaicewa tayi tace “Kar ka bari kowa ya ji maganar nan Umad, ka ji?”

Jajayen idonshi kawai ya zuba mata yana kallo, cikin shashek’ar kuka na munafurci ta fara fad’in “Tabbas da taimako na a cikin kai harin nan, sai dai ba da makami ba ko wata hanya ta daban, mun kasance muna soyayya ni da Khatar tun a makaranta, sanda yaya Kossam ke d’aukar nauyin karatuna da duk wasu buk’atuna, sai na fara jin kishi a kan ta ina jin haushin me yasa ba ni ba ce a matsayinta? Wata rana na zo hutu Giobarh sai mahaifinka ya umarci da mu shirya za’a yi taro a k’asar Egypt, mun tafi cikin farin ciki tare da ku da kuma yaya Kossam, a Egypt sai muka had’u da Khatar shi ma ya aje a lokacin ba’a masa wazirin sarkin Khazira ba, duk sanda k’afa ta d’auke ni da shi muna tare muna soyayyarmu, a nan ne har na samu damar fad’a masa abinda na ke ji a zuciyata game da yar uwata, tambayar da ya min ita ce *”Me ki ke so a yi kenan?”*

“Sai na fad’a masa ina so na zama sarauniyar Giobarh, na zama mai fad’a a ji a masarautar, da fari ya nuna min kishinsa saboda mun yi alk’awarin aure da shi, amma washe gari sai ya zo min da maganar wai zai cika min buri na, da na matsa masa me zai yi ne sai ya ce min *”Sarki Musail ne ya nuna sha’awarsa ga ‘yar sarkin Egypt, saidai ita ta nuna bata son shi d’an yar uwarki (Urab) take so, kuma sarki Musail ya bani wuk’a da nama na yi duk abinda ya dace dan ganin ya sameta, dan haka zan jefi tsuntsu biyu da dutse d’aya.”*

” Na tambayeshi ban gane me ya ke nufi ba, sai ya ce min *”Yau da dare zan sa a kashe min d’an yar uwarki, hakan zai sa sarkina ya samu Juman, daga baya zamu bar duk shaidar da zata nuna sarki Musail ne yasa a yi wannan aika aika, kinga kenan mun haddasa gaba mai tsanani tsakanin masarautar Giobarh da masarautar Khazira, hakan zai sa sarki Wudar ya nemi d’aukar fansa ko ta ya ya, idan aka yi nasarar cin Giobarh da yak’i, a k’arshe za’a kafa sabuwar daula a Giobarh kuma ke zaki zama sarauniyarta, idan kuma aka yi nasara akan Khazira…”*

“Da sauri na tambayeshi to me zai faru? Sai ya ce *” Zan zama sarkin Khazira, ke kuma sarauniyar gaba d’aya Bussam, ya kika gani ?*”

” Na ji dad’i sosai har cikin zuciyata, hakan yasa na yi dogon tunani a lokacin sannan na bashi ta wa shawarar na ce *”Madadin ka sa a kashe Umad shi kad’ai, me zai hana ku d’auki hayar mahara da dama su kawo hari aasarautar nan yau cikin dare?*”

“Tambaya ta ya yie ye anfanin yin haka? Sai na ce masa *” Idan fa aka yi rashin sa’a aka kama wad’anda kuka turo, to shakka babu zaka kwana a ciki, dan gidan nan yanzu baibaye yake da hadimai da dogarai saboda yawan safakunan dake ciki, amma idan mutanen dayawa kuma kan mai uwa dawabi aka yi, to kai tsaye ba za’a zargi wani sarki ba, dukansu zasu dinga wa juna kallon kallo ne, a cikin hatsaniyar kuma sai a kashe Urab, ni kuma nasan mutuwar Urab daidai take da mutuwar Kossam, dan tana matuk’ar son yaron, kaga ni kuma ta wannan hanyar zan k’arasa kassara rayuwarta.*”

” Haka muka kwana da shirinmu, kuma mun yi nasarar aiwatar da abinda muka tsara, a hakane aka kashe Urab kisan wulak’anci, wanda sanadiyar haka mahaifiyarka ta yanki jiki ta fad’i, ba’a iya aiwatar da komai ba dan masarutu da dama sun rasa mutanensu a lokacin ko da kuwa hadimi ne, ni kuma daga lokacin sai…”

Fashewa tayi da kuka na gaske ta sunkuyar da kanta, wani wawan buga teburin yayi da yasa ta zabura kamar zata tashi tsaye, wanda hakan yasa fitsarin da take ji ya banko a guje ya taho mata daga zaunen da take, kwararararan da ya ji abu na zuba a k’asa yasa ya d’an yi jim yana saurarawa, a hankali ya tura kujerar da yake zaune baya sannan ya d’an lek’a, da sauri ya kalleta ya girgiza kai yace “Ina jinki.”

Yamutsa fuska tayi ta matse k’afafunta kanta k’asa saida ta gama tsiyaye fitsarin tas sannan ta d’ago a hankali ta kalleshi, a kausashe ya kuma fad’in “Ina saurarenki.”

Cikin sanyayyar murya tace “Wajen boka na kai yaya Kossam a India, nan ne aka bani maganin da kullum nake saka mata a abinci sannan nake shafa mata a jiki duk kwana uku, da wannan ne ta kasa anfanuwa tun daga waccen ranar sai jiya data tashi kamar a mafarki, kuma na samu abinda nake so, sai dai sarki Wudar bai aureni ba haka ma Khatar, sannan duk yanda na so na kashe mahaifiyar abun ya gagara, dan wani boka ma fad’a min yayi idan na matsa ni ce zan rasa raina, dan ita kam mutuwarta ba yanzu ba, amma dai ni da mahaifinka mun zama abu d’aya, a shekarun nan da aka d’auka ni da shi kamar mata da miji ne, saidai ban tab’a yarda shi ko Khatar da ke kawo min ziyara lokaci lokaci ba na d’auki cikin d’aya daga cikinsu, saboda ba wannan bane a gaba na, saida na fara gajiya da k’aryar da Khatar ke yi min a kullum cewa zai aure ni, sannan na dakata da d’aukar allura har na samu ciki da shi, sai kuma na yi k’ok’arin d’orawa Wudar saboda ina so abinda zan haifa ya zama magajin wannan masarautar, dan na fahimci Khatar ba zai tab’a zama fiye da waziri a masarautar Khazira ba, wannan shi ne abinda ya faru Umad, tunda na fad’a maka ka yafe min ka ji, kar ka hukunta ni dayawa.”

K’asa da sama ya harareta ya ture kujerar ya mik’e tsaye, bindigar ya d’auka ya sa a k’ugunshi yace” Mak’iyi na nesa ba wuya ka shawo kansa, amma mak’iyi na kusa ya fi kowane illa, shi mak’iyi zai iya dawowa masoyinka wata rana, amma mai maka hassada har abada baya tab’a canjawa, a haka za ki k’are Joyran, babu nan kuma babu can, doka ce za ta d’auki matakin daya dace a kan ki ba ni ba, dan waccen harin da kuka sa aka kai, yayi sanadiyar rayuka da dama, daga ciki kuwa har da yayana da nake matuk’ar so, sannan har da mahaifin shugaban hukumar nan ta mu, d’aya ne a cikin manyan bak’in da suka halarci taron.”

Juyawa yayi ya fice a wurin duk da yanda take k’wala masa kira tana ya yafe mata kar su d’aureta, ba za ta iya rayuwa a d’aure ba wa ye wa ye, haka yana fitowa jami’an dake nan wanda duk suka ji tattaunawarsu suka dinga sara masa wasu kuma na bashi hannu, shugabar hukumar kan shi hannu ya bashi suka gaisa bayan ya share k’walarshi yace “Nagode Umad, yau ta dalilinka na gano wanda suka kashe min mahaifina, atisayen *lu’u lu’u* ya zo k’arshe.”

Murmusawa yayi yana mai danne k’unar dake cikin zuciyarshi na rasa yayanshi yace “Nagode yallab’ai, ina neman wata alfarma?”

Da fara’a dattijon yace “Ba komai, fad’i buk’atarka.”

Kan shi tsaye yace “Ina so zan d’auki hutu.”

Dariya yayi ya bubbuga kafad’arshi yace “Ai ko baka nema ba, abu ne da muka tanada maka tun kafin zuwan ranar nan.”

Jinjina kai yayi yace “Nagode yallab’ai.”

Girgiza kai yayi yace “Ba komai Umad….am…yarima Umad, zuwa dare zaga ka takardar izinin hutunka a e-mail d’inka.”

Jinjina kai yayi sannan ya ciro bindigarshi ya aje akan d’an teburin dake kusa, da mamaki dattijon yace “Baka buk’atarta daga yanzu kenan?”

Murmushi yayi yace “Hutu zan yi yallab’ai, da kuma cin…amarci, ba karan batta ba.”

Bushewa duk wurin sukayi da dariya har wasu na tsokanarsa dama yana da aure ne, abu d’aya ya fad’a musu shi ne “Ina gayyatarku dukanku wajen shagalin biki na a fadar Khazira.”

Daga haka ya juya ya fita a gaba d’aya headquarters duk da yana jin tsiyar da wasu ke masa wai hala yar sarki ya kwashe? Wasu kuma suna fad’in ko dai ma *lu’u lu’un* atisayen na su ya d’auke kacokam.

馃グ *Mu sha kodumo, In Shaa Allah gobe za ku ji ni shiru saboda zamu yi tafiya amma ta wuni d’aya zuwa Katsina, ina baran addu’arku guy’s.*

 

*Alhamdulillah.*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
Read More

TARTSATSI 1

Advertisement *Page 1* Yanmatane su biyu gefen titi suna tafe suna hira tsakaninsu kasa kasa wanda idan ba…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 3

Advertisement €pisode 3…………….✍️ Kanshi ya ɗago yana kallon yanayinta, ya fuskanci akwai tashin hankali muraran shimfiɗe cikin ƙwayar…
Read More

TARTSATSI 37

Advertisement *page 37* ******************* Salma cikin farin ciki, taje ta adana kud’inta, zuciyarta fal farinciki, don ganin takeyi…
KALLABI
Read More

KALLABI 62

Advertisement BABI NA SITTIN DA BIYU Sosai ran Aminatun ya b’aci akan Anum kuma taki yarda ta ga…
KALLABI
Read More

KALLABI 67

Advertisement BABI NA SITTIN DA BAKWAI “Kayi shiru Insha Allah ba zasu kuma maka dariya ba, zan saka…
KALLABI
Read More

KALLABI 60

Advertisement BABI NA SITTIN CIF _Assalamun Alaikum yan uwa Barka da warhaka, Nagode sosai Alhamdulillahi jiki an murmure,…