Lu’u Lu’u 44

Advertisement

*44*

 

Saida ta dasa aya ya kalli idonta yace “Wani abu ne ya ke damunki to?”

Kyab’e baki tayi a sanyaye tace “Ni ma ban sani ba.”

Jinjina kai yayi ya d’an ja baya kad’an yace “To ci.”

Da sauri ta gyara tsayuwarta ta kai sandwich d’in nan data had’a baki ta gutsira, lumshe ido tayi tana taunawa tana jin dad’inshi a bakinta har kwanyar kanta, kallonta yake shi kuma ya gyara tsayiwarshi kamar ya samu tv.

Tana tsaka da ci ko rabi bata ci ba wata hadimar ta shigo ciki, da girmamawa ta sunkuyawa tace “Uwar gijiyata, mai martaba sarki na son ganinki yanzu.”

Kallon sandwich d’inta tayi sannan ta kalli Umad, ajewa tayi ranta a jagule sannan ta nufi hanyar fit, da kallo ya bita har ta fita sannan shi ma ya bi bayansu.

Tana zuwa ta samesu duk tsatsaye, da mamakin yanda suke tsaye wurin da kuma cika d’akin taron da ya sake yi da mutane wanda ke nuni yanzun kamar jama’ar gari ne kuma duk gasu tsaye ta k’arasa ta tsaya tsakiyarsu, gashi duk hankalin mutane ya dawo kansu yanzu, kallon Juman tayi tace “Mah, lafiya ?”

Lumshe mata ido tayi alamar lafiya lau, Umad ma na fitowa kai tsaye wajen grp d’inshi na aika ya nufa inda Haman ma na tare da su har kuma shugaban su da sauran abokanan aikin, shi ma dawo da hankalinshi yayi kansu saodai idonshi na kan Ayam, duk wani motsinta a idonshi yake wakana.

Advertisements

Sarki Musail ne ya d’anyi gaba kad’an sannan ya d’aga murya yace “Jam’ar Khazira d kewayenta, yau babbar rana ce a gareni da ku baki d’aya, rana da kuka jima kuna tsammanin zuwanta, ranar da wasunku suka shafe shekaru suna mafarkin tambayar yaushe za ta zo? To ga ta ta zo yau, yau rana ce da ni sarki Musail zan yi murabus daga kujerata, sannan na d’ora wacce ta fi cancanta, wacce ku ka dinga tsumayin ganin ranar da zata karb’i mulki daga hannu na, Zafeera.”

Ya fad’a yana juyowa inda take tsaye sai zazzaro ido take kamar ta had’iyi kunama, sake maida hankalinshi yayi kan mutane yace” Har cikin ziciyata na yarda da sabon tsarin da za ta gina muku, tun kafin na haifi abuta na san da zata kawo haske a k’asar nan, dan haka ina mai baku shawara da ku mata mubaya’a ku bita a cikin tsarin mulkinta, dan wainar da zata toya sai da ku zata toyata, idan har kun amince da haka sai ku fad’a mu ji.”

Cikin d’aga murya maza da matan suka amsa tare da d’aga hannunsu suka ce” Mun amince, mun amince.”

Murmusawa yayi ya juyo ya kalli Ayam ya kamo hannunta, irin tsoron dake fuskarta yasa shi d’an rusunawa cikin rad’a yace” Ke fa yanzu sarauniya ce, wannan fuskar tsoron na ki za ta sa talakawanki su rainaki, sannan su miki kallon wacce ba jaruma ba.”

A marairaice tace” Amma Pah ai dama ni ba jaruma ba ce ko?”

Girgiza kai yayi tare da lumshe ido yace” Ba dai ‘yata ba, da ba daga tsatsona kika fito ba, sai na yarda idan kin fad’i haka, now smile.”

Kallon mutanen tayi ta saki murmushi mai kama da kuka, kama hannunta yayi ya d’aga sama alamar ta karb’i mubaya’ar da suka mata, hakan yasa d’akin taro ya kwashi wani irin ihu mai k’arfi da hayaniyar mutane tare da tapawarsu.

Har su Musail d’in da su Juman Abdallah duka dake nan tare da ita tapi suke mata suna murmushi, hadimai biyun dake tsaye gefe da wani abu kan faranti ne suka matso kusa, juyo da ita Musail yayi suka fuskanci juna yace “Gwiwarki d’aya k’asa dan karb’an kambunki.”

Idonta taf da hawaye tace “Pah kar ka d’ora min nauyin jama’a, bana da sha’awar hakan.”

Cike da k’auna ya shafa kumatunta yace “In Shaa Allah, da izinin Allah subhanahu wata’ala za ki iya Ayam.”

Tar tar ta kalli k’wayar idonshi cikin na ta, kamar sub’utar baki ba tare da tasan bakinta zai fad’a ba tace “To Pah *mijina* fa? Ya zan yi da aurenshi da ke kaina?”

Juyawa yayi ya kalli Umad, wani murmushin shak’iyanci Musail d’in yayi, yaron na birgeshi sosai saboda shu’umi ne, wato har ya gama kassara masa yarinyar sa dai ta ciki da ta waje ? Ajiyar zuciya ya sauke ya juyo ya kalleta yace” Kar ki damu da shi, ya amince da hakan.”

Advertisements

Sake langab’ewa tayi zatayi magana sai ya had’e fuska dole ta k’yale, a sannu sannu ta durk’usa yanda gaba d’aya rigarta ta rufe komai na ta ko k’afafunta ba’a gani, duka gwiwan ta durk’usa ta sunkuyar da kanta, hakan da tayi yasa Musail cire kambun dake kan shi na gwal ya d’ora mata kan babban mayafinta dake saman kai har yana jan k’asa, jin kambun ya hau kanta mutane kuma sun sake kaurewa da tapi da fad’in “Jinjina, sai kin yi sarauniya Zafeera, abun bauta ya tsareki.”

Sharrrr ! Hawaye suka wanke mata fuska, tallabota yayi ta mik’e ya d’ago fuskarta, girgiza mata kai yayi ganin tana hawaye yace “Bana so fa.”

Maida kallonshi yayi ga hadiman nan biyu da suka matso, bud’e kyalen sukayi mai k’yalli kalar ruwan zaiba, hakan ya bayyanar da wata kyakyawar sark’a mai kalar ruwan zaiba ita ma sai wani dutsi a tsakiyarta ja mai suffar kan zaki, d’auka yayi ya nufi wuyanta yana fad’in “Yanzu za ki zama sarauniyar Khazira, daga yanzu nauyinsu ya bar kai na zai koma kan…”

Sautin k’akk’arfan numfashin Musail ne kawai ya ratsa wurin amma ba’a ji k’arar harbi ba, Ayam dake daf da shi jinin jikinshi ne ya fallatsa zuwa fuskarta da jikinta baki d’aya, kafin ta fahimci me ya faru? Sai ihu da hayanyar mutane ce ta gauraye wurin.

Tartsatsin ihun Juman ne ya sa ta firgita ta juya ta kalleta sabda yanda tayi ihun ta fashe da kuka, hakan yasa a rikice ta kalli inda mahaifinta ke tsaye, saidai ina kwance ta ganshi sai neman rai yake amma yana k’i ya ma sa, sai numfashi yake sama sama yana had’iyar abu a mak’oshi, a hankali a hankali kuma idonshi sai suka fara lumshewa, labb’anshi ta kalla da yake furta “La’ilaha illallah, Muhammad rasulillah sallalahu alaihi wa’sallam.”

D’ago hannu yayi yana son rik’o hannun Ayam saidai take rai yayi halinshi, duka tana kallon komai dake faruwa, a gaban idonta har ya cika da kalmar shahada, sark’ar da yake shirin saka mata ta kalla wacce ya saketa ta fad’i k’asa.

Tunda suka ga abinda ya faru Haman da tawagarsu suka bazama da azama tare da sanar da hadiman sarakunan uku cewa su shiga ko ina su duba, Haman da wasu daga cikin yan tawagarsu da gudu suka haura ta inda harbin ya fito, saidai suna zuwa suka samu d’aya daga cikin fadawan sarki Musail kwance shi ma cikin jini an harbeshi, kuma ga dukkan alama shi ne yayi harbin dan kar ya tona asiri shi ma aka kashe shi.

Sanda mutane ke ta hayaniya wasu na son fita daga wurin wasu kuma suna lek’a abinda ke faruwa, lokacin Ayam ta dawo daga d’imuwar da tayi na wasu sakanni.

Da iya k’arfinta cikin siririyar muryar da Allah ya hore mata ta kwamtsa k’ara tare da dafe kunnuwanta ta durk’ushe a wurin, hannayenta bibbiyu ta kai kan gawar Musail ta fara jijjigawa da iya k’arfinta, da sauri su Bilkees da mahaifiyar Bukhatir suka rik’eta suna k’ok’arin jayeta daga nan, wani harbin bindigar suka ji hakan ya tilasta ma kowa tsayawa cak a inda yake yana zazzaro ido.

Zafreen ce rik’e da bindiga da alama a kid’ime take kuma ta sha wani abun, dan idonta sunyi jajir sai layi suke, kan Ayam ta nuna da bakin bindigar nan tace “Kar wanda ya motsa a inda yake, idan ba haka ba sai na harbeta.”

Cak kowa ya k’ara tsayawa har da Umad dake durk’ushe kan gawar Musail, cike da kulawa yake kallonta yana son hango ta yanda zai farmaketa ba tare da kowa ya ji rauni ba, sake jinjina bindigar tayi tace” Na ce kowa ya tsaya, kar wanda yayi yunk’urin wani abu, idan ba haka ba zan kasheta.”

Matsowa ta dinga yi sannu sannu tana yi tana kallon gabanta da bayanta, saida ta matsa har daf da Umad sannan tace” Ka ciro min kambun dake kanta.”

Da mamaki ya kalleta hakan yasa a tswace tace” Na ce ka ciro min kambun, ko kuma in tashi kanta da bindigar nan.”

Cikin rud’ewa Juman tace” Kin ga Zafreen, ita f…”

A tsawace tace” Shiru, shiru malama.”

Umad ta sake kallo tace” Maza ka yi abinda na ce.”

A hankali ya fara takawa ya nufi Ayam data tsaya kan k’afafunta amma hawaye na mata ambaliya, hannunshi ya kai ya d’auko kambun dake kanta wanda ya mata kyau sannan ya mik’o ma Zafreen d’in, karb’a tayi da sauri kamar zata had’a da hannunshi sannan ta saka a kanta, kecewa tayi da dariya sannan ta sake cewa “D’auko sark’ar ka saka min.”

Cike da taka tsantsan ya sunkuya ya d’auki sark’ar sannan ya mik’o mata, sake nuna Ayam tayi da bindigar tace “Ka saka min na ce.”

Gyara sark’ar yayi sannan ya saka mata a wuya, zai ja baya ya bata wuri saboda ganin Haman sun dawo daga neman maharbin nan, da ido ya mishi alamar su nutsu sannan suyi koma da baya su yi wata dabarar da zata sa kowa ba zai jikkatu ba, yana cikin masa magana da ido kawai ya ji Zafreen ta shak’o wuyan rigarshi cikin halin maye tace “Na ce ina sonka…ina son ka ama..babu wanda ya kulani, to na ji kuje ku rayu kai da ita, amma ka ga yanzu ni ce mai mulki, ni ce saraunyar Khazira yanzu, hatta…da mahaifinka ma..a k’ark’ashina yake yanzu, dan haka…”

Ba tare da tunanin komai ba ta d’ora labb’anta a na shi labb’an, kafin ya ankara har ta tsotsi bakinshi sannan ta raba bakinsu tana mashi wani mayataccen kallo tace” Ina son…”

Bindigar ta d’ora a cikinshi da niyyar ta harbeshi Ayam da ita duk su rasa, yana jin ta d’ora bindiga a cikinshi yayi sauri cikin dabarar fad’a ya juyar da hannunta zuwa cikinta, kafin ta ankara da ina bakin bindigar yake ta danna kunamar, hakan yasa ta tashi kanta da bindigar, take ta k’walalo ido ta jimk’e rigarshi sosai, sannu sannu ta fara sulalewa sai gata k’asa kwance cikin jini.

Jaye jikinshi yayi hakan ya sake haifar da turmutsutsu, a nan ma dai yau saida aka kira ambulance da suka tafi da gawawwakin, saidai ko ba komai yanda Musail ya cika da kalmar shahada haka gawarshi ta samu mutuntawa har da zubar hawayen talaka, inda aka kaisu mutuwa kafin gari ya waye a kaisu gidansu na gaskiya, mutane kuma suna ta cecekucen waye ya kashe sarki Musail? Wanda ba’a gano hakan ba, saidai ko ma waye an tabbatar ba zai wuce da hannun Zafreen d’in ba.

Juman da Ayam sun gigice musamman Ayam da ke d’auke da jinin mahaifinta a jikinta, Juman kalamai d’aya take ta fad’a a bakinta har yanzu shi ne “Mah ko gafararsa ban rok’a ba, ban nemi yafiyarsa ba akan abubuwan da na masa, ya sadaukar da rayuwarsa a kai na da ‘yata, ya zauna da mak’iyanshi da murmushi a fuskarshi, na nuna masa k’iyayye ya had’e ya shanye Mah, ya zanyi yanzu? Ya zanyi Mah? Ina son mijina, wallahi ina son mijina.”

Ayam kuma wuri d’aya kawai take kallo sai in ta k’yabta da k’yar, hakan yasa Bilkees ta kalli Umad tace” Ka je da ita d’akinta, ka kwantar mata da hankali, ni zan zauna da Juman a nan.”

Jinjina kai yayi sannan ya kama hannun Ayam bata ma san yayi ba har suka je d’akinta, zaunar da ita yayi bakin gado ya shiga ban d’aki, ruwan wankan ya had’a sannan ya fito ya kamata, saida ya tsayar da ita tsakiyar ban d’akin yace” Ki yi wanka ga ruwa nan, idan kin kammala ki d’aura alwala.”

Shiru kamar bata san yanayi ba, dan haka ya juyo ya fito daga ban d’akin ya rage kayan jikinshi sannan ya koma.

Duk da ta fahimci singlet da dogon wandonshi ne a jikinshi, amma sam hankalinta ba nan yake ba, musamman bandejin dake nad’e tun daga kafad’arshi zuwa hannu wanda Haman ya cire mishi harsashin da aka harbe shi ranar nan, duk d tana jin kamar ta tambayeshi, amma ina gaba d’aya komai na ta ne ya tsaya.

Gabanta ya tsaya k’ik’am ya fara zare mata zip d’in riga, da a hayyacinta take ba zata tsaya ba a yanda suke d’in nan, amma sai gashi ya rabata da komai ya rage daga pant d’inta sai bras farara k’ar da su, jawota yayi jikinshi kamar ya rumgumeta sannan ya b’alle mata bras, tana jin haka wasu hawaye masu zafi suka taho mata har suka sauka kan kafad’arshi.

Cire mata yayi sannan ya sunkuya ya zage mata pant d’in, shi kanshi sai yake jin wani nauyi nauyi, watak’ila dan ko waccen ranar bai wani ganta sosai ba ne, yana ajiye kayan ya jata zuwa k’asan shower ya sakar mata ruwa masu d’umi.

Wanka ya mata da sabulu tas sannan ya d’aura mata towel suka fito har yanzu tana nan kamar gunki, kan gadon ya zaunar da ita sannan ya d’auko man da ya gani ya zo ya fara shafa mata, jefi jefi ya kan kalli fuskarta, amma yanda idon nan nata masu abun al’ajabi suka yi ja sai yake jin tsoron kallonsu, gashi shi take kallo bata ko k’yabtawa sai an d’auki lokaci.

 

*Alhamdulillah.*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
A BAKIN WAWA 3
Read More

A BAKIN WAWA 22

Advertisement 22   Yana Jan Jan Dan ya taje, ta rike hannunsa,sabida wata irin masiffan zafine daya ratsata,…
KALLABI
Read More

KALLABI 19

Advertisement BABI NA SHA TARA *WANNAN PAGEN NA KUNE MUTANEN BAFFA’M DA YAR KWAILAR SHI MUSAMMAN AUNTY SA’A…
Read More

TARTSATSI 30

Advertisement *Page 30* ******************* Sadauki ya kalleta dakyau yace “Ina saurarenki dafatar dai duk abunda zai fito bakinki…