Lu’u Lu’u 45

Advertisement

_Bismillahir rahamanir rahim_

*45*

 

Tattausan kayan bacci ya d’auko mata dogon wando da rigarshi mai k’ananan hannaye farare tas masu tambarin sunan Rundahao, saida ya zaunar da ita yana k’ok’arin kwantar da ita sai ta dage ta k’i kwantawa, zaune yayi yana fuskantarta, ita ma shi ta kalla a lokacin suka had’a ido, a tausashe yace “Saki abinda yake ranki Sajeeda, bari hakan a zuciya zai haifar miki da damuwa.”

D’aga mata gira yayi yace “Yi kuka, yi kuka ki k’oshi Sajeeda.”

Kamar ya bata lasisin sai kuwa ta fashe da kuka iya k’arfinta, take ya lumshe ido saboda ji yayi kamar ta karci zuciyarshi da k’arfe.

Jawota yayi jikinshi ya kwantar yana shafa bayanta alamar rarrashi, saidai bai ce mata k’ala ba ya bata damar kokawa dan rashin hakan zai zamar mata matsala.

Saida ta ci kuka mai isarta daga nan har bacci ya d’auketa tana ta ajiyar zuci, gyara mata kwanciya yayi ya rufeta da abun rufa sannan ya koma ban d’aki yayi wanka shi ma ya d’auro alwala ya dawo, sallaya ya shinfid’a sannan ya kabbara sallah yayi raka’a takwas sannan ya sallame, mik’ewa yayi ya sulale ya fice kai tsaye d’akinshi ya nufa.

Wudar ya samu idonshi rufe alamar bacci yake, saidai duk da ba wani tsaye yayi ya dubashi ba ya dai fahimci ba wani sauke numfashi yake ba, sharewa kawai yayi dan abinda ya fito da shi ba na wasa bane, mahaifinshi kuma yana ganin idan ma yayi gigin tashinshi zai kuma cakula masa lissafi ne da maganar matarshi. Dan haka ya rab’ashi ya wuce zuwa wajen da kayanshi suke ya canza sannan ya d’auki k’aramar bindigarshi ya saka a k’ugu sannan ya fita a d’akin a hankali.

Tunda ya duk’ufa a cikin gidan nan daga inda aka yi harbi har zuwa gawar wanda aka samu, dagewa yayi da taimakon su Haman da sauran tawagarshi har saida suka gano bakin zaren, daf da asuba ya dawo gidan ya shiga d’akinshi dan canza kayanshi, abinda ya fara tsaya masa a zuciya shi ne yanda ya bar mahaifinshi haka ma yanzu ya same shi, sai hakan ya d’an jefa masa shakku, tunda dai ai mai bacci ya d’an motsawa ko da cikin baccin ne har kwanciyarshi ta canza, bare kuma shi da ba lafiya ce da shi ba.

Advertisements

Da sauri ya k’araso gare shi ya kai hannunshi kan fuskarshi ya tab’a, sanyi k’alau ya ji kamar komai baya tafiya, da sauri ya sunkuya ya sake kai hannunshi kan wuyan shi ya tab’a, a rikice ya d’ago hannunshi ya rik’e wuyan hannun yana sauraren harbawar jijiyarshi, a kid’ime ya furta “Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un! Pah! Pah ka tashi ! Pah kar ka min haka kai ma dan Allah, ka tashi.”

Cakumar rigarshi yayi ya rumgume ya tusa kanshi ay k’irjinshi yan hawaye, mutuwa dole ce ga duka mai rai, saidai ya ji zafin ta mahaifinshi daya kasance ya tafi ba tare da ak’ida ba, sannan ya tafi da ciwon son matar da yake aure, sam hakan bai masa dad’i ba.

Masarautar Khazira dai sai ta sake rikicewa saboda mutuwar sarakunan nan guda biyu a lokaci d’aya, haka aka wayi safiyar gidan a kid’ime a kuma gigice ana ta shirin kawar dasu zuwa gidansu na gaskiya.

Shaf ya manta da Ayam dake d’akinta, ya manta ita kanta a wani hali take na d’imuwa da kewa, sanda yake rumgume da Kossam dake kuka ne kawai abun ya zo masa a rai, da sauri ya d’an janyeta a jikinshi a ladabce ya mik’e da sauri ya nufi d’akinta.

A k’ofar shiga sukayi kicib’is da ita ta fito, sanye take cikin wani irin shiri na ban mamaki, sak ta fito a sarauniyarta ta k’asar Khazira, hatta da kambun da mahaifinta ya saka mata da sark’ar da ya so saka mata saida ta sako sannan ta fito, fuskarta kuma a tamke take ba alamar fara’a bare tayi wasa da wani.

Cak ya tsaya yana kallonta bakinshi da ya masa nauyi ya d’aga yace “Ay…ina zaki je? Ya haka?”

Ba alamar fara’a tare da ita fuska a gimtse tace “Zan je ga kujerar da mahaifina ya bari, ba zan zauna na yi ta kukan rashinsa ba, zan d’auki mataki akan wad’anda suka kasheshi.”

Hanya ta kama zata rab’ashi ta wuce ya rik’o hannunta, juyowa tayi suka had’a ido a d’an kausashe tace “Sake ni.”

Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya saki hannunta, juyawa tayi zata wuce a tsanake yace “Mahaifina ya rasu.”

Cak ta tsaya ta juyo ta kalleshi, sai ta ji ba dad’i sosai, a hankali ta tattare rigarta dake jan k’asa ta dawo gabanshi ta tsaya, kallon juna suke kalar zasu had’e kansu, a ladabce ta furta “Kai…ma ka yi rashin mahaifi? Yanzu mun zama…marayu kenan?”

Kuka ne ya k’wace mata da sauri ta fad’a jikinshi ta fashe da kuka, daddab’ata ya dinga yi yana fad’in “Shiiiii! Ki daina kuka kinji, In Shaa Allah Ayam ba zan bari ki yi maraici ba matuk’ar ina raye, ban sani ba dai ko ni…”

Bata sanda ta d’ago ta d’ora yatsarta a kan labb’anshi ba tace “A’a…”

Advertisements

Sai kuma tayi shiru ta sunkuyar da kanta, binta yayi da kallo yace “Uhum?”

Cike da kunya tace “Ba zamu zama marayu ba, muna da iyayenmu masu k’aunarmu.”

D’aga idonta tayi a hankali ta kalli k’wayar idonshi tace “Kuma ni ina da kai, sannan kana da…ni kai ma.”

Rintse idonshi yayi gam ya cakumi bakinta ya shiga tsutsa a zafafe saboda bai tsammani jin abinda ta fad’a ba yanzu, saida ya tsotse man data shafa a bakinta tas sannan ya saketa suna kallon juna.

Rufe idonta tayi ta sunkuyar da kai, amma sai ta ji idonshi na ta yawo a jikinta, da sauri ta wuceshi ta nufi hanyar fita har da d’an gudunta ta bar wurin.

Saida ya ga b’acewarta sannan ya girgiza kai yana murmushi ya bi bayanta dan ana shirin tafiyar jana’izar sakaranan na su ne ya kubto ya taho.

Dayawa sun so a tafi da Wudar zuwa kasarshi inda shi ma zai samu gatan da kowane sarki ke samu idan ya rasu, amma sai Umad ya ce tunda har ya mutu a nan to anan ubangijinsa ke son a binneshi, ba buk’atar sai an canza masa k’asa.

Saida rana ta hantse sosai aka yi bisar gawawwakin, inda Sarki Musail ya samu tagomashin da duk wani musulmi dake wurin ya sallaci gawarsa, sab’anin Wudar da d’aukarsa kawai aka yi zuwa makwancinsa.

Bayan an dawo daga bisarsu ana ta hada hadar karb’an ta’aziyya, Kossam kuma da hadimanta sun yi shirin komawa Giobarh dan tayi takaba a d’akinta, gaba d’aya cikin gidan shela ta karad’e kunnen kowa cewa sarauniyar Khazira na son ganin kowa da kowa a filin taro.

Duk wanda ya ji haka yayi mamaki, saidai haka suka mik’e suna tunkarar filin taron dake d’aukar dubannin jama’a, hatta wad’anda ke kurkuku saida ta sa aka fito mata da su daga ciki har da Dhurani.

Ba iya talakawan garin ba ne kad’ai, har da manyan mutanen da suka halarci jana’iza sun zo su ji me zata fad’a, haka ma akwai wasu sarakunan na wasu garuruwan da masu garin wasu k’auyuka da dagatawansu, hakimai, malamai da dai sauransu.

K’us k’us k’us kawai ke tashi ana yi ana kallon kallo ana jiran fitowar ta, dayawa sun zo ne dan su ji me za ta fad’a haka me mahimmanci da sai yanzu za ta fad’eshi bayan mahaifinta yanzu aka kaudashi? Shin sabon tsarin da suke tunanin zata kawo musu ne za ta fara da gaggawa haka? Ko kuma dai game da rasuwar mahaifinta ne ?

Da gudu gudu fadawan suka fara shigowa suka layu a ind zata fito ta tsaya sun k’ame sos1i sun kuma cije ba wasa, hakan yasa kowa yayi shiru ya kuma nutsu aka zu a ido kan k’ofar da suka shigo.

K’was ! K’was! Sautin takalminta masu tsini suka shaidawa kowa shigowarta, girman kujerarta da d’aukakar da Allah ya bata yasa kowa dake nan hatta da Juman dake tsaye tana hawaye a jikin Bilkees, da ita kan ta Bilkees da Kossam sai da suka rusuna tare da masu rusunawa, wani irin kwarjini ne Allah ya bata, musamman yau data fito fuskar nan a had’e, dole duk wani dake k’aqa da ita ya bata girman da Allah ne ya mallaka mata.

Tsaye tayi inda fadawan suka gyara tsayuwarsu su ma kamar yanda take fuskantar mutane, kowa da kowa taje kallo kafin ta d’an gyara muryarta a nutse ta had’e tafukan hannayenta tace “Gaisuwa a gareku.”

Amsawa sukayi da “Gaisuwa sarauniyar mu.”

Yanda suka amsa kamar gurin zai tsage biyu, yanda ta sake nutsuwa tana kallonsu yasa su ma suka yi shiru suka maida hankalinsu kan ga.

A nutse cikin dattako da k’arfin hali tace ” Jama’ar Khazira, na san kowa na cike da son jin dalilin da ya sa na tara wannan taron yanzu da gaggawa, ba komai yasa na kira taron nan ba sai wasu abubuwa da ke kan faru.”

Gyara tsayuwa tayi ta kallesu da sigar mamaki tace” Shin mutanen Khazira zuciyarku ta mutu ne da har wasunku suke bacci da mafarkin ni Zafeera zan zo na canza muku rayuwarku? Wacece ni? Me kuka d’auke ni? Ni ma mutum ce kamar ku, me yasa da aka zauna aka fad’a muku tatsuniya a kai na kuma kuka yarda? Ba kowa ba ce ni kuma ban ga wata tsiya da zan iya tsinana muku ba, labarin zuwana duniya ya isa kunnen masu ci da ceto ne a cikin kowane irin addini tare da tasirantuwa kan son d’aukar fansa, hakan yasa aka k’ullawa iyayena mak’ark’ashiyar da su kansu suka yarda zasu haifi zab’abb’iya, ku ji da kyau, ni nan na fad’a babu wani zab’abb’e bayan fiyayyen hallita wanda ba’a haifa ba ba kuma za’a haifi kamar sa ba.”

A sanyaye muryarta na rawa tace” Duk wasu abubuwa da nake yi ko ake gani a tare dani ba komai ba ne fa ce k’udurcewa da kukayi a ranku lallai ni d’in zab’abb’uyarku ce, idan har akwai wani abu da zan iya cewa ubangiji ya min da ba kowa ya ma ba, ba zai wuce canza yare da na ke yi ba musamman idan raina ya b’ace ko kuma na shiga mamaki, bayan wannan babu wani abu daya zama daban da na ku yan uwa na, da wannan nake kira gareku a matsayinku na mutane masu daraja, ku mik’e tsaye ku saka yayanku su yi karatu, ta hakane ci gaban da kuke tsammanin zan kawo muku ni kad’ai, bilyoyin matasa irina zamu kawo muku shi, ku kashe Zafeera a zuk’atanku, ku manta da wata Zafeera a shafin zuk’atanku, ku dage sannan ku maida tunaninku ya zama yanda zaku kawo ci gaba da hannayenku a k’asarku, jiran wani ya kawo maka ci gaba shi ke mayar da kowace k’asa baya, amma idan kai mai k’asar kayi tunanin ciyar da k’asar ka gaba, to za ka cimma nasara.”

Gyara tsayuwa ta sake yi tace” Jiya zuwa yau ne kawai ‘ake sarauniyar Khazira, kafin mahaifina ya bani mulkin nan na fad’a masa bana sha’awarsa, dan na fi buk’atar siyasa akan sarauta, a yanzun ina sarauniya ne kawai dan na fad’a muku ku tsaya da k’afafunku sannan ku tsayar da shugaban da kuka ga ya cancanta ya mulkeku, amma ni Ayam…zan ajiye mulkin nan sannan na tafi tare da *mijina* dan na masa bauta a gidan aurenmu, ina fata ba zaku fahimce ni ba daidai ba? Sannan ba zaku kirani marar adalci ba, na sani ta ko ina wani babban matsayi ne ke bibiyata, amma dai mulkin Khazira ya fi k’arfin iyawar Ayam, duba da yanda mahaifina ya rayu a tsakanin makirai, wanda hakan yasa ban rayu tare da su ba sannan aka dinga farfagandin cewa mahaifina yana son kashe ni, sannan ni ce zan zama silar mutuwarsa…”

Hawaye ne suka sauko a kumatunta ta d’an sunkuyar da kai, jima kad’an ta d’ago ta share hawayen tace” Na yarda a wannan karan, na yarda ni ce zan zama silar rasuwarsa, tunda gashi duk ni na jawo komai….”

Fashewa tayi da kuka ta sunkuyar da kanta, a hankali ta d’auke kambun da yake kanta ta d’ora akan farantin da wata hadimar ta matso tana fad’in” Ba zan iya rik’e wannan ba, gashi nan a ba wa wanda ya cancanta.”

Yanda abun ya daki zuciyar kowa yasa talakawa wasu suka fara kuka suna fad’in” Hugabarmu kar kiyi saurin d’aukar wannan matakin, zamu so ki mulke mu kamar yanda marigayi yayi mahaifinki, zamu zama masu biyayya a gare ki.”

Girgiza kai tayi a sanyaye tace” Idan har akwai wani abu da zan iya yi muku a yanzu bai wuce na baku shawara kan ku samu madogara, ku samu ak’idar data dace da ku, nufina ku shiga addinin musulunci, dan shi ne zai haska muku rayuwarku har ku kai ga gacin da kuke da buk’atar kai wa.”

Wasu ne suka amsa da” Addinin musulunci?”

Jinjina kai tayi tace” Addini na, addinin mahaifiyata, addinin mahaifina kuma addinin mijina, duk da mahaifina yana addinin musulunci, bai samu damar janyo ra’ayinku ba saboda magauta, amma ni ina mai baku shawara da in kun ji zaku iya ku shiga, dan addini na ba addini bane da ke tilasta wanda baya ra’ayi shi ga, sharad’in shi dai ne idan ka shiga baka fita, idan kuma ka fita bisa bayar da mashirmancin dalili to hukuncin kisa na hawa kan mutum.”

Cire sark’ar nan tayi ta mik’awa wata hadimar, sake had’e hannayenta tayi za ta musu sallama, sai kanta ya sara da k’arfi sosai, d’an lumshe idonta tayi sai kuma ta bud’e ta kallesu da kyau, a sanyaye sosai yanda ba kowa ya ji me ta ce ba tace” Na barku lafiya.”

Bud’e ido tayi sosai ta taka k’afata ta kuma juya da niyyar barin wurin, mugun jiri ne ya kwasheta sai kuwa ta sulale tayi k’asa ta fad’i, musulman ciki ne suka furta” Inna lillahi wa’inna ilaihi raju’un!”

Inda hadiman dake kusa da ita suka rufa a kan ta, da gudu Juman da Kossam du sukayi kanta.

*Umad* dama bai halarci taron ba yana d’akinshi yana kallon komai ta na’ura saboda tunda ya ji maganar taron hankalinshi bai kwanta ba, dan haka ya dasa na’urar d’auka yake kallo ta computer, ganin haka kuma shi dai bai ga alamar harbi ba haka kuma ba alamar wani abu daya faru.

Da mugun saurin da bai san yana da shi ba ya mik’e da gudu ya fito a d’akin ya nufo d’akin taron, yana zuwa ya ratsasu ya wuce ya tallabeta ya mik’e, da sauri su Juman duk suka rufa masa baya suka bi bayanshi har saida ya kai ta d’akin Juman din ya sauke a kan gado, da azama ya kalli Juman yace “A kira likita.”

Zaune tayi kusan Ayam d’in tace “Ina zuwa.”

Ruwa ta kai hannu ta d’auka dake gefen gadon cikin jug na tangaran fari k’ar da shi ta zuba a hannunta sannan ta shafa mata a fuska, a hankali ta fara motsawa har ta bud’a idonta, ajiyar zuciya suka sauke inda Juman ta d’an bud’a idon Ayam d’in, jim tayi tana kallo sannan ta kawo hannunta ta kalli tafin hannunta.

Murmushi ta saki hakan yasa Ayam kallonta Umad ma haka, cike da jin kunya yace “Mah, me ya sameta ne? Ko farmaki ne aka kawo mata ?”

Mik’ewa Juman tayi tsaye ta zagaya bayanshi tana murmushi tace “Farmaki ne.”

Hankali tashe yace “To amma daga ina haka?”

Gimtse bakinta tayi ta matsa kusan Kossam da ita ma ta zabge sakamakon mutuwar na ta mijin, cikin kunne ta rad’a mata magana hakan yasa suka saki murmushi duk da halin alhinin da suke ciki, matsawa Kossam tayi kusanshi ta kama kunnenshi ta murd’e tace” Ja’irin yaro ashe abinda ka zo ka yi kenan? To farmakin daka kai mata waccen daren ne ya bayyana kan shi.”

Juman da Bilkees duk k’yalkyalewa sukayi da dariya, shi kuma sam bai fahimci inda suka dosa ba dan haka ya kallesu da mamaki yace”…

 

*Ku yi hak’uri da wannan, sannan kuyi hak’uri da ji na shiru kwana biyu, matar yayana ta haihu shiyasa.*

 

*Alhamdulillah.*

Leave your vote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

GIPHY App Key not set. Please check settings

You May Also Like
A BAKIN WAWA 3
Read More

A BAKIN WAWA 23

Advertisement 23   Kwanciyarta Kenan tana Shirin gyarawa da kyau tayi bacci, marairaice wa tayi, tace’ ban iya…
Read More

TARTSATSI 74

Advertisement   *Page 74*   Yana nan azaune yana tunanin miye hakan kuma, wari Salma ina bazaiyiyu ba,…
Read More

TARTSATSI 28

Advertisement Jiki a sanyaye umma ta shige d’akinta, tana tunanin wannan rigima da takunno masu, wadda takeso ta…
NAWA BANGAREN
Read More

NAWA BANGAREN 6

Advertisement _*Wannan littafin daga farkonshi har ƙarshe sadaukarwa ne gare ka Hayateeynah (my Eternal love) ka ji daɗinka*_.…